⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 4: Chapter 4

“Dole in yi kuka Inna, domin ya cike min wani gurbi a rayuwata na Uba-mahaifi. Yayi min kaunar da bayan iayayena babu wanda yayi mini. A yau Allah Ya karbi ransa, a kan idona. Dole in kokawa gushewarsa a doron kasa.
Sannan ya hadani da wani al’amari mai nauyi; kula da dukiyar marayunsa. Ga shi ina auren ‘yarsa, ba don haka ba da ba zan damu ba.
A daidai lokacin da nake kokarin janye jikina daga cikin dukiyarsa, sai ya daura mini nauyin ta gaba daya (dungurungum). Inna yaya zan yi? Nauyin mai girma ne! Tunanina da karfin Zuciyata sun kasa dauka”.
Inna tasa bakin zaninta ta share hawayenta, domin ta fahimci abinda Zahraddeen ke koka mawa.

Ta ce, “Bari in shirya mu tafi, jeka taho da ita ta samu makokin mahaifinta. Tunda har ka yi alkawari, to ka daure ka cika, ka yi komai da zuciya daya, ka daina la’akari da abin da mutane za su ce a kanka, domin shi dan Adam ba a iya mishi.
Amma idan sun ce a raba gado shi kenan, sai ka kula da na ‘ya’yanshi kadai. Idan kuma su ma sun fi son dukiyarsu a hannunsu, babu alkawarin da zai ce dole sai ka rike, tunda hakkinsu ne ba naka ba”.
Ranshi ya dan samu nutsuwa daga kalaman Inna. Ya mike ya nufi sashensa yasa mukulli ya bude kofar glass wadda za ta sada shi da falon, yasa kai dauke da sallama a bakinsa.
A nan falon ya ganta a kwance a doguwar kujerar hutawa (sofa) tana barci sadidan, lokaci na farko kenan da ya samu damar kare mata kallo, sanye take da riga da wando na Pakistan ruwan ganye, kanta babu kallabi, ta daure gashinta da koren ribbon mai girma.
Fara ce sol doguwa, don ta fi Safah tsayi kadan, ga dogon hanci da karamin baki. Ba ta da yawan sumar kai kamar Safah, sai dai ba ta a layin marasa gashi.

Hasken fatarta ‘natural’ babu alamun shafe-shafe. Ya ji wani tausayin ta ya tsirga masa, sannan wani sabon al’amari ya soma samun muhalli daga can karkashin zuciyarshi.
Maimakon ya tashe ta sai ya samu kanshi da zama a gaban kujerar da ta ke kwance, ya dade yana kallon ta yana jin wani irin sanyi a zuciyarsa, domin akalla ko babu Alh. Aliko, a yau ya yi farin ciki da karbar auren diyarshi. Ji yayi kamar ya sunkuya ya sumbaci siririyar fatar bakin ta. Yana kuma tattara kalaman da zai gaya mata ta shirya su tafi Kaduna yanzunnan batareda hankalinta ya tashi ba. Tunda jiya ya tafi, kuma aka’ida in ya tafi sai karshen sati yake dawowa.
Domin ko ba komai yana tare da jininshi da za ta dinga tuna masa da shi yana yi masa addu’a. wadda kila watarana …. zata haifa masa jikan Aliko, …… yasa masa suna Aliko. Ya dora shi a kujerar ofishin Aliko…….. ya gaya masa ko wanene Aliko.
Ko yaushe ce wannan ranar? Ya tambayi kansa. “Allah Shi Yafi kowa sani”. Ya baiwa kansa amsa.
Ya yi ta maza inji mata ya kama tafin hannunta. Ta yi saurin bude idanunta ta ga Zahraddeen ne yau zaune a gabanta, har da kama hannun ta, mutumin da ko kyakkyawan kallo bai taba yi mata ba.
Ta riga ta fassara shi da mutum ‘mai girman kai’, (dama an ce gwano baya jin warin jikinsa. Takori )
Rana ta farko tun zuwan ta gidan da ya yi mata murmushi. Ya ce, “Sorry, kina barci na tashe ki. Ki tashi mu wuce Kaduna yanzu”.
Kallon rashin fahimta ta yi mishi. Bai bari sun sake hada ido ba ya wuce dakinsa, tana so ta tambaye shi ba’asi ko da cikin tsiwa ne babu fuska.
Ta mike ta yi dakinta don ta canza kaya tana cewa a ranta, “Allah Yasa gajiya yai da auren ta zai mayarwa da iyayenta ita”.
Tana gidan gaba na motar Inna na baya, tunda suka dauko hanyar Kaduna bayan gaida Inna da ta yi, ba ta ce uffan ba.

Ta lura daga shi har Inna basu da walwala, don basa cewa komai. Ita Inna carbin hannunta take ta ja, shi kuma gaba daya ya tattara hankalinsa a kan tukin da yake yi.
Faduwar gabanta ya kara tsananta, ta samu kanta da satar kallon sa lokaci-lokaci, ko zata iya karanto dalilin tafiyar ta babu-gaira babu dalili, kallon da a da ba ta taba yi masa ba.
Gayen ya hadu karshe, ga iya shiga ta ‘suit’, da shaddah, kai har ‘white cotton laces’ ma da ‘white materials’ na maza masu taushi da santsi yana yin amfani dasu dinki Mohammed, idaniya basa gajiyawa da kallonshi har ga maza ‘yan uwansa ba mata kadai ba, ga yawan sumar jiki data kai, ga wani kwantaccen saje da ya aje a gefen fuskarshi wanda ya hade ya zagaye da gashin bakin kuater million din sa. Baida hasken fata sai hasken boko, dangayen gaske, mai kwarjini na ban mamaki.
Sai dai ba ta taba ganin shi cikin rashin walwala da rashin kuzari irin wannan ba. Idanunshi a rikide sun koma brown daga farare sol. Ta ji wani sabon al’amari yana fizgar zuciyar ta, tsigar jikinta na tashi.
Ta cigaba da satar kallonsa yana sauya kaset daga wakar larabawa zuwa addu’ar tahajjud din Sudaith. Ji take kamar ta dora kanta a kafadun mijin ta, ta ji dalilin damuwar da yake ciki, ta kuma rokeshi gafarar babban gorancinta na shirme da rashin hankali irinna yaran goye, inda hali ta rungumeshi, ta shaki wannan ‘dior’ din mai kokarin janye numfashin ta a kullum mai shi ya doso ta.
“Ya ilahi!” ta furta a hankali, tareda kai hannu ta dafe kirjin ta, sabida karfin bugunsa daya karu. Me ke damu na ne akan Zahraddeen a yau? Juyowar nan da za ta yi sai idanunsu cikin na juna, ya yi maza ya daure fuska, ita kuma duk kunya ta kama ta, tunda ya kamata tana mishi kallon kurillah kamar bata taba ganin shi ba, kallon da baya jin ko Safah da yace yana so itama tana so ta taba yi mishi sabida batada ketare kallon muslunci, amma sai ta yi saurin dauke kanta ta mayar tagar damanta, kirjinta ya cigaba da bugawa fat-fat-fat, cunkushe da al’amura masu dimbin yawa.
Ko da suka isa bakin layinsu ta hango cincirindon mutane a kofar gidansu ba karamin kaduwa hantar cikinta ta yi ba.
Ta dubi Zahraddeen da sauri nan ta ga idanunshi sun cicciko da kwallah, yana dubanta kamar ya riketa ya hanata fitar, kamar ya riketa ya lallasheta, in zai iya ya gaya mata da bakinsa, zata fi fahimta fiye da ta ji al’amarin daga tsakar ka, a sukwane ta bude murfin motar ta fita da gudu ta doshi gate din gidansu ba tareda ta bi ta kansa ba.

Ba abin da ta kawo cikin ranta sai Hajiya Mama ce Allah Ya yiwa rasuwa.
Sai dai kuma da Hajiya Maaman ta fara cin karo, a lokacin da ta sanyo kai babban falon Mami, saura kadan su kara.
Ai Safah na ganinta ta taho da gudu ta rungume ta, ta saki wani irin kuka mai gigitarwa. Cikin kukan da karkarwar jiki ta ce,
“Mun zama marayu Marwahh, yau babu Daddy….ya tafi….ya tafi….ba zai kara dawowa ba!!!”
Sai ita ma ta rushe da kukan da bata taba yi a rayuwarta ba.
Nan komai ya dawowa kowa na gidan sabo, sun tabbatar maraici ya same su, mai daci da wuyar mantawa.
Daddy Uba ne da babu kamar sa, an edemplary Dad!. Ya tsaya tsayin-daka wajen inganta rayuwarsu ta kowacce hanya.
Don haka mance ciwon rashinsa a zuciyoyinsu ko barin kewarsa wani abu ne da ba zasu taba iyawa ba.

****

Duk wani wanda yake da alaka dasu ya zo musu ta’aziyya, kama daga ‘yan’uwansu na Yola, malamai da abokan karatun su.
Ranar sadakar bakwai anyi addu’o’i na musamman, anyi sadaka kowa ya kama gabansa, sai wadanda abin ya shafa.
Idan ka ga Safah da Marwah a wannan lokacin gaba daya sunyi sanyi, kamar idan ka sanya musu dan yatsa a baka ba za su ciza ba.
A ranar da daddare Baffan Alh. Aliko wato Baffa Sufyan da Hajiya Mama wuni suka yi neman layin Imam, amma basu samu ba.
Mami ta yi kuka har ta gode Allah saboda rashin samun Imam a yau, Baffa Sufyan ya kira su family meeting wanda ya bukaci Zahraddeen ma ya halarta tunda shima yanzu ya zama ahalin gidan kuma babban Yaya a gare su tunda ba imam.
Maganar gado ce ake yi, kowa ya fadi ra’ayinsa na yadda yake son rabon gadon ya kasance.
Baffa ya yi shiru yana sauraron kowa. Safah da Marwah sun ce basa bukatar komai na gadon mahaifinsu sun barwa Mami.
Hajiya Maama kuma ta ce ta barwa Imam da Shahida kason ta. Mami ta ce “Ayi haka Hajiya? Su ma suna da gado, wanda har yau ba a taba komi a cikinsa ba, wanda ya bunkasa ya hayayyyafa a bankunan Turai sabida dadewar da aka yi ba’a taba shi ba.”.
Ta ce, “To ni me zan yi da kudi? Gida ko mota Zainabu? Shekaru nawa suka rage min IN BI BAYAN Zubairu da Aliko a duniyar bayan shekaru tamanin?”
Sai da suka gama Baffa Sufyan ya yi murmushi ya ce, “ duk na ji ra’ayoyin ku. Shi gado wani muhimmin abu ne wanda Ubangiji Subhanah da kanSa Ya raba shi a cikin Alkur’ani saboda muhimmancinsa.
Don haka dole za a raba a baiwa kowa kason shi, in yaso sai kowa ya yi yadda yake so da shi, imma za ku bari Zahraddeen ya ci gaba da juya muku kamar yadda marigayi ya ce ko za ku siyar ku sayi hannun jari, ko kuyi gararin gabanku. Don haka za mu raba gado kowa ya yi yadda yake so da nasa”.

Dukkansu sun gamsu da bayanin Baffan, don haka a washegari aka raba gadon kamar yadda musulunci ya tsara.
Hajiya Maama ta zabi yin sadakatul jariya da nata, wato gina masallaci, kai tallafi ga gidan marayu da nakasassu, tare da gina makarantar Islamiyyah.
To haka Mami ta zabi yin sadaka da sayen hannun jari, yayin da a take Safah da Marwah, suka bi umarnin mahaifinsu suka damkawa Zahraddeen nasu takardun a kan sun amince ya ci gaba da juya musu, sun amince ya cigaba da daukar albashinsa da Daddy ke bashi a ciki, sun amince ya zama Yayansu na jinni har zuwa ranar da Allah zai juyo da hankalin Imam gida.
Karfe hudu na yamma Zahraddeen ya shigo cikin gidan, lokacin Safah da Marwa na daki suna kara kokawa junansu.
Safah na bata labarin yadda Imam ya sake ta, wanda ta san har da bakin cikin wannan al’amari ya yi sanadiyyar ajalin Daddy da halin da take ciki a yanzun na nadama da dana sani, uwa-uba soyayya mara algus da ta kanannade zuciyarta a lokacin da Imam din ya tafi ya bar ta, koko tace, damar ta riga ta kubuce mata bakin alkalami ya riga ya bushe. Tunda ko yana nan din me zai kuma shiga tsakanin su? Sai ido. Sai gaisuwa ta muslunci in ya kai zuciya nesa.
Ta yiwa ‘yar’uwarta nasiha sosai ta ce ta godewa Allah ta kuma godewa Daddy ta kama mijin da Allah Ya bata tun ba ta zo tana irin nadamar da take yi a yanzu ba.

Ta taushe ta da cewa, duniya ba komai ba ce tamkar matafiyi ne a kan tafarki. Daddy kadai ya isheki misali. Ko ince Ubangiji Ya dauke abinSa ne, don mu hankaltu. Mu gane gatan da yake cewa yayi mana mun ki yarda da gangan sabida kuruciya da son zuciya. Ta ce ki duba ki ga mene ne Allah Bai baiwa Daddy a duniya ba? Wace irin shahara ce Daddy bai yi a Nigeria ba? A yau yana ina? Ya tafi ya barsu a inda ya same su, ya tafi inda abinda ka shuka shine kadai jarinka.
Bai tafi da gidajen ba bai tafi da motocin ba. Bai tafi Birtaniya ba bai tafi Bournmouth ba; karkashin kasa ya tafi cikin yadin likkafani daidai dana kowa, babu AC babu katifa. Sauran al’amarin tsakanin sa da UbangijinSa ne, to haka kowa fah…..!!!
Kina kin Zahraddeen ne kawai based on hierarchy of social class, nakasunsa a wurin ki shi ba dan wani bane ba kowa bane face wani matashi mai tarin ilmi, mai neman na kansa a karkashin mahaifinki ta hanyar gajiyar ilmin sa don dai banace kwadayi kike ba, na wani wanda ya fishi abin duniyar. Amma ba don yayi lacking anything a rayuwa ba. Marwah me kike so a namiji, sabida Allah me kike so da Zahraddeen baya da shi?
To bari in gaya miki gaskiya in baki gode rahmar Allah da zabin Sa ba, zaki godewa azabarsa a ranar da baki da sauran wata dama da za ki gyara kuskurenki kamar yadda nayi. Kukan kurciya jawabi ne, mai hankali kadai ke ganewa….”
Marwah ta share hawayen idonta jikinta ya yi sanyi sosai. Wani irin sanyi da bai taba yi a rayuwarta ba

Mami da Shahida ya tadda a falon, ya zauna bisa kilishi suka kara yiwa juna ta’aziyya, sannan ya ce da Mami, “Ko za mu iya tafiya yanzu? Gobe litinin ina son ta koma makaranta gobe”.
Mami ta ce, “Hakan ya yi, Shahida kirawo ta su tafi”.
A yadda Shahida ta gansu face-face da hawaye ya taba zuciyarta, ‘yan kannen nata sun sanya ma ransu damuwa mai yawa. Basu taba bata tausayi ba sai yau.
To ai gara su suna da Mami da za su rika gani su ji dadi, su kuwa fa? Ta juya musu baya tana dauke nata hawayen da ‘yan yatsunta ta ce.
“Marwah fito ku tafi mijinki na jiran ki”.

Da kyar ta shiga toilet ta wanke fuskarta da sabulu ta fito ta tadda su a falo cikin shirinta rataye da jakarta.
Zahraddeen ya riga ta fita, bayan ya yiwa Mami sallama ba tare da ya iya hada ido da Marwahn ba, saboda shi yanzu matsanancin tausayin su yake ji, duk wasu makaman yakin day a tanada don dai-daita sahun matar tasa, ya nemesu ya rasa, yadda suka shaku da mahaifinsu har ya fi shakuwar su da Mami.
Mami ta daga ido ta kalle ta, idanun sun yi jawur sunyi luhu-luhu, duk da wanke sun da ta yi da sabulu.
Ta yi mata kallo na zuciya da zuciya, wato kallon kauna na da da mahaifi. Suka yi sallama ta bi bayan Zahraddeen. Mami ta kasa ce mata komai. Banda “agaida Hajiya Binta”.
Yana cikin motar kafarshi daya a waje yana danna wayarshi ya hangota ta fito, ya mika hannu ya bude mata gaban motar ta shiga ya rufe suka dau hanya.
Tunda suka hau titi babu mai uhm, babu mai umh-umh a tsakaninsu. Da shirun ya ishe shi sai ya danna sautin Sudais cikin suratul An’am.

Tafiya suke sannu-sannu, domin Zahraddeen baya gudu sosai. Ya kara karfin A.C din motar ya rufe tagogin motar wadanda suke bakake wulik (tintic), ba mai iya hango mutanen da ke ciki.
Duk wasu kudurarrika na batanci da yake dasu a kanta, sai ya neme su ya rasa, sai tausayin ta da yake ji kamar-kamar me, zuciyarshi tayi laushi da yawa, yana tuna lokacin da shima ya rasa nasa mahaifin (the same feeling…).
Karo karatun ma ya fasa, zai tabbata a serbant din Alh. Aliko Dankasa muddin rayuwarshi. Zai kula da diyarshi duk da cewa ba ta son shi, ya ji ya yarda ya amince (shi yaron Babanta ne) kamar yadda take ikirari. Sai me?
Yana yin ‘parking’ cikin garejin shi ta dauki Jakarta ta fice ba tare da ta ce da shi komai ba, ta wuce cikin gidansu ainahin sassan Inna ba flat din su ba. Bata taba shiga ba, bata san hanyar ba, sa-kai kawai tayi.
Ya kashe motar ya fito rike da hularshi a hannu da briefcase ya doshi dakin Innarshi, ya sha mamaki ganin Marwah a dakin Inna suna yiwa juna ta’aziyya.
Da kuzarin shi ya shigo, amma ganin Marwah yau a dakin mahaifiyarshi sai ya ja ya yi turus a bakin kofa yana kallon ta, don bai san da wacce ta zo ba.
Inna ta ce, “Ka zo ka tsaya mana kerere a ka, in shigowa za ka yi ka shigo, in fita za ka yi ka fita”.

Ya saki fuska sannan ya juya ya fice ya nufi sassansu zuciyarshi ta yi mishi sanyi a karo na farko tun zuwan ta gidan. Ba mamaki mutuwar mahaifinta ta fara ladabtar da ita.
A yau sai ya samu kansa da zama a falon, don kawai yana son ya ga gilmawar ta, daga shi sai singileti da wandon shan iska (short niker) samfurin Adidas, ya jona kettle ya hado ruwan gahwa (coffee) a kofin tangaran ya zauna cikin kujera yana kurba kadan-kadan yana duba wayar hannunsa, amma a zahiri hankalinsa baya kai, yana kan kofar falon.
Da an dan jima sai ya dubi kofar shigowa ko za ta shigo, amma shiru. Shi kanshi ya kasa gane kanshi a kwanakain nan, matarshi yake ji sosai cikin zuciyarshi tun bayan rasuwar Alh. Aliko.
Can sai gata ta shigo rike da mayafinta da jakar hannunta. Ya daga shanyayyun idanunshi a hankali yana kallon ta yana kurbar coffee.
Kallo daya ta yi mishi ta kau da kai, don ji ta yi kunya ta kama ta, don bata taba ganin namiji haka ba. Amma shi din bai gane hakan ba. Ko kuma ya gane din ba damuwarshi bace.
Ta zube shirgin hannunta ta yi kicin don ta samarwa cikinta abin da zai ci, don Inna danwake ta yi mata tayi ta ce a koshe take, don ba za ta iya jefa wadannan lunkuma-lunkuman abubuwan a bakinta su wuce makogwaronta ba.
Yana nan zaune duk kamshi ya cika masa hanci, Marwah rainon Mami ce ta fuskar girki na zamani kala-kala, ba wanda ba ta iya ba.
Inda ta sha bamban da Safah kenan, ita sai karatu da son tsarge jarrabawa.
Ta debo danyen nama a firiza ta zuba a na’urar nika nama ta markade shi sannan ta juye a frying fan ta sanya albasa, maggi da tafarnuwa da curry ba tare da ta zuba ruwa ba, ta sa wuta kadan sannan ta kawo green beens kofi daya ta zuba ta rufe.
A gefe ta kwaba fulawa ta yi falle-falle da ita ta hau gashin pita-bread wanda za ta ci da sauce din.

Cikin Zahraddeen in banda kugi ba abinda yake, ga wani irin kamshi ya cika shi. Shiru-shiru ba ta fito ba ta barshi sai hadiyar miyau yake, dama muguwar yunwa ta sa shi shan gahwar, tun karin kumallon da yayi a Kaduna bai kara sanyama cikinsa komi ba.
Can sai gata ta fito da plate a hannunta da robar lemon Mountain Dew za ta wuce dakinta, sai ya sha gabanta.
Ta dago ido ta dube shi sai ya rausayar da kai gefe ya lumshe lumsassun idanunsa, sannan ya budesu ahankali a kanta a lokacinda ita kuma ke ta kokawar kawas da ido daga gareshi.
“Ni baki bani ladan ganin ido ba!”.
Harara ta zabga mishi ba tareda ta yarda ta dubeshi ba. Sannan ta ce, “Ban girka da kai ba, ko da ni nake baka abincin?”
Ya yi murmushi ya karbe ‘plate’ din hannunta, ya bata hanya ya koma kujerar tsakiyar falon hankalinsa kwance ya soma cin abinsa.
Karshen kulewa ta kulu, ta juyo ta koma kicin ta juyo sauran a wani ‘plate’ din ta zauna nan cikin kichin din tana ci, kada ya sake kwacewa wahalarta ta zama haramiyarta, sai gashi ya shigo.
Daga bakin kofa ya tsaya hannun shi daya ya sanya jikin kofar kicin din, ya rike fankon filet dinshi da hannu daya……. ya mika mata plate din, fuskarsa dauke da wani kayataccen murmushi wanda ya fitar da annuri mai yawa akan fuskarsa, da sabuwar soyayyah dankare cikin kwayan idanunsa. Kamar almajiri yana bara;
“I’m asking for more….Maa!!!”

Yadda ya yi maganar cikin kwantaccen sauti, duk sai ya bata dariya, yana iya hango siririn murmushi, a siririyar fatar bakinta, amma ba ta ce da shi komi ba, har ya saki kofar ya karaso ya tsugunna a gabanta, kamin ya zauna sosai ya sanya hannu cikin ‘plate’ dinta suka ci gaba da ci tare.
Wannan girki dai, bata koshi ba ko kadan. Itama yunwar take ji dole dai ta hakura ta kyaleshi. Don bata son magana ta tsawaita a tsakaninsu don ta lura yau dai neman shiri yake. Ta kowacce fuska alamu sun nuna. Da suka kammala hannunta ya kama ya wanke mata a cikin ‘sink’, bai cika hannun nata ba, janyo ta ya yi da hanzari suka nufi bed room dinta.
Ta ce, “To cika ni guduwa zan yi ne?’
Ya sassauta rikon da yayi mata amma bai cika ta ba. Zama ta yi a gefen gadonta ta kwace hannunta, ya jawo stool din madubi ya zauna a kai daf da ita yana fuskantar ta.
Ya ce, “Bayan rashin SO, girl,… sai mene ne matsalarki a zama dani?”
Yadda yake magana kadai ya saukar mata da kasala, balle yadda hucin sassanyan numfashinsa ke dukan fuskarta. Ta samu kanta da rikicewa ta kasa amsa mishi tambayarshi.
Ya ce, “Ke nake sauraro?”. Tareda daga girar shi sama kadan, alamar sauraron.
A hankali ta dago ta dube shi, abinda ta gani cikin kwayar idonshi ya sanyata kokonton anya Zahraddeen ne? Kwayar idanunshi ta nuna wani mutum da ke fama da azabtacciyar soyayya da kauna mai yawa, (yet he’s not weak), amma dai kamar ba Zahraddeen din da ta sani ba, mai ji da kai da rashin son wargi.

Sai ita ma ta yi cooling, gwiwoyinta sun sage, ta ce, “Ni na ce bana sonka?”
“Kwarai kin ce ba kya sona, saboda ni yaron Babanki ne. BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE koh? Ko ba haka kika ce ba? Kunnuwana suka jiye min, ba wani ya taso ya gaya min ba”.
Za ta yi magana ya katse ta.
“…… Ba na kalubalantar ki, not eben a little, na yarda na amince in cigaba da zama YARON KI (serbant), kuma MIJINKI, (husband) mahadin rayuwar ki (life-mate) kamar fiyayyaen halitta da Uwargidansa Nana Khadijah Bint Khuwalid, idan har za ki bani wannan gurbin, zan samu Marwanatuh?”
Kunya ta kama ta. Kamar tace da kasar ta tsage ta shige. Magana zarar bunu….ta riga ta fita.
Wannan ba itace tarbiyyar da mahaifin su ya dora su akai ba. Ta tuno dukan mutuwan da Daddy yayi mata a lokacin da tayi wannan furuci. Ashe Zahraddeeen din ma ya ji. Sai ta soma kokarin yin repenting. Ta yi murmushin yake ta ce,
“Idan ni na ce bani son ka, kaima ai bani kake so ba, Safah kake so, aka lika maka ni, don haka bai kamata ka ga laifi na ba.
Soyayya ba lallai ta faru a sanda aka so faruwarta ba. Ita wata irin aba ce da ba ruwan ta da lokaci, matsayi da dangoginsu. Abu ce wadda ke faruwa a duk sanda ta so, ta gudanar da tunani ta sarrafa gangar jiki (duba littafin ALHERI). In hakane kenan banida laifi don nace bana son wanda na san ba so na yake yi ba”.
Ya ce cikin murmushi, wanda ya kara kawata kyakkyawar fuskarsa.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *