Chapter 5: Chapter 5
“in haka ne, we habe the same problem, sai mu kirkiro SON mu taru mu rufawa juna asiri, ta hakan ne kadai zamu sanya marigayi farin ciki a kushewar sa.
Auren mu babu rabuwa, (mutu-ka-raba ne). In haka ne kenan dole mu mance baya (past), mu fuskanci gaba (future), mu yi gini a kan sabuwar rayuwar da muka tsinci kanmu (present), ba tare da waiwaye ba!”.
Ba ta amsa ba, amma zuciyarta sanyi take, haka fuskarta ta nuna sassauci. Soyayyar mijinta na kutsawa har cikin bargo da kasusuwanta. Ashe wannan shine ZAHRADDEEN din da take kalubalantar Safah a kan ta so shi? Ashe ita soyayyar baka saninta sai ta zo kanka? Ashe Zahraddeen din ba’a sonsa ba’a saninsa sai an dan yi kyakkyawar mu’amala dashi, koda ta dan lokaci ce? Ashe wannan itace SOYAYYAHr da Safah ta dandana, amma take ganin bekenta akan rashin alkawari???
Zata iya fassara tata soyayyar a yau da ‘definations’ da yawa, wadanda neither Safah nor Zahraddeen edperienced it. Sai ta sunkuyar da kanta, ta kasa hada ido da Zahraddeeenin….… wanda ke kallon yanayinta, yana binta da ido, da zuciya, yana karantar weakness dinta; tana da karfin hali, tanada tsiwa, tanada son aji (class) amma bata da power a fannin soyayya (abin nufi, bata iya fin karfinta bata da juriya a fannin ta, mijin aurenta zai iya gane hakan, zai iya yin amfani da hakan ya cutar da ita batareda ta kare kanta ko ta ankara da hakan ba), irin su ne ake cewa da wuya su fada a soyayyar, amma in ta samesun, ko ta zo kansu, to basu iyata ba, suna yin ta ne (wholeheartedly).
Murmushi yayi, murmushi mai mika bukatar miji zuwa ga matar sa….kowanne sassa na zuciyar ta da gangar jikinta na kaduwa, kaduwa mai ban mamaki irin wadda bata taba ji a rayuwar ta ba.
Kamar yasan abinda take ciki, (kodayake ya sani din), zai iya cewa nashi ya fi nata, tunda ita mace an halicceta da kawaici da alkunya, wanda shi baya dashi. Sai ya mika hannu ya kama hannunta biyu hagu da dama, ya mikar da ita tsaye. Dukkansu dogaye ne tsayinsu daya, fadin kirji kawai ya fita.
Lokaci na farko da ya jata cikin jikinsa, a hankali ya rungume ta. Ya sanya hannu cikin sumar kanta cikin wani salo na kwarewa da sanin weakness din duk wata lafiyayyar mace. Banda karkarwa da bari ba abinda take yi cike da tsoro, fargaba da razana na rashin sabo. Sai dai duk wata gaba ta jikinta ta amshi sakon da Zahraddeen din ke aikawa ta cikin gashin kanta zuwa sassan jikinta. To such an edtent that, lamarin ya zo wani ‘limit beyond her capability to ignore….’ (ya zo wani mataki da bazata iya hanawa ba).
Karo na farko a rayuwarta da ta tsinci kanta a wata duniya ta daban, da bata taba tsintar kanta a ciki ba.
****
“Kalli ‘ya’yan hutun, da hutun bai sa su sun kaucewa tarbiyyah ba! MADALLAH da wannan Uba nagari. Allah Ya nuna maka aikin ka har makwancinka.”.
Haka Zahraddeen ya fada cikin zuciyarsa, yana rungume da amaryar tasa, wadda yake kallo tana barci sadidan cooly, ta hasken farin wata wanda ya ratso ta cikin shara-sharan farin labulan dakin barcin ta.
Ya rungume matarshi sosai, cike da so da kauna, hadi da godiya ga Allah tare da yiwa Alh. Aliko addu’a. Wannan ta mallaki duk abinda yake so matarshi ta kasance tana dashi. Koma fiye. Ya yarda soyayyah is not the most important thing in marriage (ba itace abu mafi muhimmanci a cikin aure ba). Akwai wasu abubuwan da yawa bayan ta; neman zabin Allah a duk sanda maganar aure ta taso, albarkar iyaye, bin shawarar na gaba (musamman Uwa), da rashin nuna gaggawa akan abinda mutum yake so.
Ta yi juyi a hankali ta bude idanunta wadanda ke cike da barci da gajiya, suka hada ido kunya ta kama ta, Zahraddeen din sai ya kara lumshe mata idanun, ta sunne kanta cikin yalwatacciyar sumar da ta cika kirjinsa.
Zuciyarta fal da so da kaunar mijinta, wanda ya siye duk wata soyayya da Allah Ya halittawa dan-adam cikin zuciyarsa a dare daya kacal. Ta ta lumshe ido, hawaye suka zubo, zuciyarta cike fal da so da kaunar mijinta da ya mamaye 90% na zuciyarta, cikin dan lokaci kalilan.
Bayan ta gama wanka ta yi sallah ba tare da ta cire hijabin sallar ba ta cimmasa a kicin yana ta kiciniyar sama musu abin karin kumallo, yana sanye da wasu ‘pj’s’ ruwan makuba. Kanta a kasa ta shigo kicin din ta ce,
“Da ka bari zan yi”.
Ya aje dankalin da ke hannunsa, ya iso gareta ya zagaye ta da hannayensa ya kwantar da kai a kafadunta.
“Ya zan dora miki gajiya the whole night (a tsayin daren bakidayansa) kuma in dora miki aiki? Hakan zai zama injustice (rashin adalci)” cikin matsananciyar kunya tace
“Na hutasshe ka. Ka je zan karasa. Wannan ba aikin ka bane. Ban taba ganin Daddy yana taya Mami aiki a kicin ba, ni nake tayata, nida su Dije” dariya ta bashi amma bai bata ba, kallonta kawai yake yi, sai tasa hannunta cikin nashi ta karbi wuka da dankalin dake hannun shi. Ya harde a gefe yana kallon yadda take girkin ta cikin kwarewa, mamaki fal ransa, don bai zaci ko kicin tana shiga ba. A yadda yake kallon takunta, ya kuma fassarata.
Don ko sanda suke off campus ya lura Biola take sawa tayi mata komai. Ya cigaba da kallonta cikin yin obserbations masu yawa akanta, kamar wani ‘psycho-analytist’ koko ‘behabioural analyst……..’.
Ta juyo suka hada ido, har zuwa lokacin ya kasa dauke ido a kanta.
Cikin shagwaba ta ce, “Ni dai don Allah ka tafi, idan kana kallona haka sai kasa na kone ko na yanke”.
Ya yi dariya ya juya zai fita yana cewa, “Na fita,your edcellency!” (Wato ranki shi dade).
Shower ya je ya sakar ma kanshi, sannan ya fito ya shirya cikin kananan kaya na Hilfiger, yana tazar sumar kanshi ta shigo dauke da katon tray, ta ja tebir ta dora tana satar kallon shi ta gefen idonta. Ba karamin burge ta Zahradden dinnan yake yi ba, wajen dressing, ba tun yau ba, tun sanda yake zuwa zuwa gidansu na makaranta, domin mutum ne da ya san sirrin dressing na western ne ko namu na Hausawa.
Duk irin dresing din da ya yi kuma, karbar jikin shi yake ya dace da zubin halittar shi, kara juyawar nan da za ta yi suka yi ido hudu tayi saurin dauke idonta. Da sassarfa ta juya zata fice, ya riko gefen mayafinta, batareda ya juyo ba.
“Ba inda za ki sai kin gaya min me kike kallo?”.
Cikin sauri da sarkewar murya ta ce, “Ni ba abinda nake kallo…”.
Sai ya rungume ta, yana kwaikwayon ‘yar muryar ta yace
“….da abinda kike kallo. Zahraddeen kike kallo. Kuma shi din mijinki ne, mahadin rayuwar ki na har abada!
Babu laifi a cikin hakan. Kalleni ki more, nima tube wannan zurmemen hijabin in kalleki cikin hasken safiya in more……, wata rana irin yau na zuwa da zaki bude ido ki ga kin cika gidannan da ‘ya’yan Zahraddeen har ki aurar dasu ki goya jikokinsu. To wace kunya ce ma ta rage afterall abinda ake ma kunyar Zahraddeen ya kawar dashi gabadaya jiya.??? ”
Ya fadi, tareda juyowa gabadaya, domin da ya juya mata bayane rike da gefen mayafin nata. Kamar ta rafsa ihu don kunya. Alkunyar ta na burge shi. Ya janyota ya rungume gabadaya. Ya soma kissing karan hancinta da bakinta yana gaya mata kalamai masu nauyi da suka fi karfin biro ya rubuta. Sai bayan wani lokaci ne ya bari suka yi kalacin tare.
Ta koma kicin ta dauko fulas din da ta zubawa Inna don Rabi’a ta koma makaranta, ta je ta kai mata har dakinta ta gaishe ta.
Ba karamin jin dadin hakan Inna Binta ta yi ba, don dama ita bata dauka da zafi ba, bata sa mata ido ba, tunda tasan yadda auren ya kasance. Ramar da Zahradeen ke ta yi a lokacin ita tafi damunta, ita da kanta ta lura yarinyar ta sauko don kanta.
Ta janyo kula cike da kosai da soyayyen dankalin hausa tace ko zata diba, tace “na koshi Inna, amma bari na kaiwa Yayan Rabi’a ko zai kara” ta debi kadan a filet ta rufe. Ta sanar da ita yau za ta koma makaranta.
Inna ta yi musu addu’a mai yawa, ta koma sassanta, ta tarar da Zahraddeen ya gama shiryawa ita kadai yake jira.
Ta dauko jakarta da mayafi da wasu takardu cikin file ya janyo kofar, suka yiwa Inna sallama bakinta ya ki rufo da ganin sauyukan da ba ta zata cikin dan lokaci ba.
Tabbas mutuwar mahaifinta kadai yasa ta shiga taitayin ta, ita kanta Marwah yanzu duniyar tsoro take bata, saboda rashin tabbas na rayuwa da ta gani.
Shi ya taya ta ta gama registration dinta na sabuwar shekara, duk da a makare ta zo, ya maida ita gida. A ranar ya juya Kaduna, don yana da aiyukan dake jiran shi a ofis masu dimbin yawa, ya bar mata motarsa daya don zuwa makaranta.
****
To haka rayuwarsu ke garawa, cikin nasarori da falalar Ubangiji iri-iri. Shekara kwana ga mai yawan rai, a yau ne ake yaye daliban Jami’ar Ahmadu Bello na wannan shekarar, ciki har da Safah Aliko Dan kasa, wadda ta karbi kwalin MBBS mai daraja ta farko, tuni ita Marwah ta karbi kwalinta tun shekaru biyu da suka wuce, don nata karatun bai kai tsayin na Safah ba. Ita ta fito da kwali mai matsayi na biyu.
Cikin farin ciki Hajiya Zainab ta rungume ‘yar ta, Zahraddeen na daukar su a hoto da digital. Har suka zo gida farin cikin da suke ciki a yau ba zai fasaltu ba.
A daren ranar suka juyo Zaria wato shi da tashi matar, duk yadda Marwah ke so ya barta ta kwana dasu Mami ya ki amincewa, tana ta kumburi kamar ta fashe da kuka, ya bude mata kofar gidan gaban motar ta shiga ta zauna.
Ya yi murmushi ya ce, “Kwanan ne ba zan iya ba Marwah, ni sai ki barni in ragaita?”
Ta zumbura baki ta harare shi yana dariya ya ja motar aguje suka harba kan titi.
Karfe goma na dare suna cikin gida, sun dade a dakin Inna ana hirar yadda taron ya kasance, sai da Inna Binta ta kore su ta ce suje su kwanta.
***
Likitar hakorin Dr. Safah Dan Kasa da mai harhada magungunan (Pharmacist) Marwah Aliko Dan Kasa sun zauna sunyi shawara a tsakaninsu cewa, za su sayar da wani kaso na gadonsu su bude babban asibitin hakori (pribate). Kuma Zahraddeen ya goya musu baya.
Bayan kammala karatunsu a asibitin koyarwa na gwamnatin tarayya dake Zaria (ABUTH). Da taimakon malamansu da sauran manyan likitoci ‘yan’uwansu. Dan Kasa Dental Hospital ya samu kafuwa cikin dan lokaci kalilan, a garin Kaduna.
A lokacin sun bar Zaria, sun bar Inna da Rabi’a wadda ta fitar da miji a wannan watan, an sanya kwanakin bikin watanni biyu cif!
Nura yana tare dasu a Kaduna, domin ya gama sakandire ya fara karatu a Kaduna State Unibersity.
Zahraddeen na cigaba da sauke wannan nauyi da Alh. Aliko ya aza masa, dukiyoyinsu suna hannun sa har kawo wannan lokacin cikin AMANA sai bunkasa suke, abin kamar a jinin sa yake, komai kara hauhawa yake. Kuma baya wasa da hakkin Allah cikin dukiyarsu. Su kansu bazasu iya iyakance abinda suka mallaka a duniya ba.
Saidai fa daya alkawarin da yayiwa Daddy har yau yana nan yana yawo a kwanyarsa, yana masa kuda a kunnuwansa, wa zai aura, don ya cika wannan alkawari? Matarshi ta ishe shi ta kowanne bangare, tun bayan da suka shirya baya ko iya daga ido yayiwa wata diya mace koda kallon kirki. Matsalarsu daya ce wadda Zahraddeen din shikadai ya santa, matsalace wadda ta shafi auratayya, ba kuma wata gagarumar matsala bace da ta gagari a yi solbing dinta, tunda babu yadda za’ayi ace dan adam ya rayu ba tareda wani nakasu ba. Kowanne dan-adan tara ne bai cika goma ba . Ga Matar tashi da bala’in kishi, duk sakatarorin shi mata da abokan aiki saida ta san yadda tayi ta raba masu wajen aiki. Ta maye gurbinsu da karti.
A lokacin ne suka kara bude DAN-KASA INDUSTRIES na sakar tufafin auduga wanda ke da reshe a Geneba, wanda suka bude da sunan Zahraddeen halak-malak ba tareda shi din ya sani ba. Har sai lokacinda ribar da kamfanin ke samu gabadaya ta soma tittida cikin account dinsa, ya yi kokarin yin musu, amma ‘yan biyun suka fashe mai da kuka, wai in Daddy ne yayi masa kyauta domin nuna godiyarsa abisa wani kokari ko taimako da yayi masa ya ji dadi, ya amfana har fiyeda yadda yayi zato, yayi masa dan ihsani domin domin ya nuna jin dadinsa ko godiyarsa, zai maida masa ne yace ba za ya karba ba? Sai albashi kawai? Da haka suka rufe bakin sa domin ya kasa cewa komai.
Shi kuma ya yi amfani da wannan damar ya koma karo karatun PhD dinsa a babbar Jami’ar garin Geneba. Wanda ke karkashin kasar Switzerland. A lokaci guda kuma tareda bunkasa ayyukan kamfanin DAN-KASA INDUSTRIES. Zuwa rassa guda biyu daya a Munich (Germany) daya a Zurich (the greatest city of Switzerland).
Likitar, (Safah) ta dauki kwararrun likitocin hakori, musamman abokan karatunsu na jami’ar Ahmadu Bello. A gefe guda na ‘Dan-Kasa Dental Hospital’ tankareren dakin shan magani ne (pharmacy) wanda ke dauke da duk wani nau’in magani na gida da waje, wanda ake shigo dasu kai tsaye daga kasar India, mallakin Marwah Aliko Dan-kasa.
Zuwa wannan lokacin Marwah ta gama mallake zuciyar mijinta da kyawawan halaye, biyayya, soyayya da kyautatawa. Ta yadda har ya zamo cikin nadamar alkawarin da ya yiwa Alh. Aliko na cewa zai kara aure, wai aure na soyayya a cewar Alhajin, domin matarshi ta ishe shi, ba shi da gurbin da zai iya jogana soyayyar wata diya mace. To shi yanzu wajen wa zai je yace yana son ta? Kallon mata yake a dage, a kaikaice (basu da abinda za su ja hankalinsa kansu). Har ya ke tambayar kansa ashe dama ‘your first lub might not necessarily be your true lub???’
Marwah bata bi Zahraddeen Geneba ba, sakamakon tsohon cikin da take da shi na haihuwa yau ko gobe. Suna gidansu na Malali a Kaduna. A lokacin Zahraddeen yana can sai Inna Binta ce ta dawo gidan dan kula da ita. Duk wata kulawa da ya kamata uwa ta gari ta yiwa diyarta Inna Binta na yiwa surukarta.
Ranar wata litinin a lokacin watanni Zahraddeen biyar a Geneba, nakuda ta tashi gadan-gadan, Inna ta kira Nura a waya ta ce maza ya zo ya fiddo mota su tafi asibiti.
Ko kamin Nura ya zo faya ta fashe, kan kyakkyawan yaro mai kama da ubansa a komai ya sako kai. Haihuwa mai matukar sauki Allah Ya bata, sai Inna ta shiga hamdalah, ta yanke cibi ta zaro mahaifa ta kunshe.
Duk wani taimako da ya dace ita tayi mata, sanda Nura ya fiddo mota suka je asibiti an tabbatar da koshin lafiyarsu ne kawai itada jaririn. Tareda basu magunguna na karin lafiyarsu. Inna ta yi mata wanka da tawul ta wanke jariri, ta shirya shi cikin kayan sanyi.
Nan da nan ta hau damun kunun kanwa, gasa nama da farfesu don maijegon ta samu ruwan nono da karfin jikinta. Ta aika aka samo runhu daga Zaria don fara wankan jego.
Mami da iyalanta tare da Hajiya Mama sai zuwa suka yi suka tarar da maijego da jaririnta fes dasu, su kansu sun gamsu da kulawar da Inna ke mata babu wanda ya ce zata koma gida wanka.
Mami don kunya ba ta dauki jaririn ba, sai Aunty Shahidah da Safah ke rige-rigen dauka. Suka sunkuto shi suka kawo shi cinyar Mami. Hajiya Mama ta ce, “A’a, ku yi a hankali kada ku karya shi ko ubansa bai ganshi ba, sun san zafin abinsu, kun san kuna son dan kuka zauna a gabanmu har yanzu gotai-gotai da ku kuna gantalin aiki da karatunda bashi da karshe?”
Suka sa dariya, Safah ta ce, “Here comes Daddy!”. Wato ga Daddy ya zo.
Mami ta ce, “Da yake ke kika haifar musu dan da za ki sa masa suna? Ni matsa nan kada ki taka ni”.
Marwah ta yi murmushi ta ce, “Allah Mami sunan Daddy za a sa, Deen ba zai ki ba. Kullum addu’arshi kenan Allah Ya sa namiji ne mu samu mai sunan Daddy”.
Yana tsaka da daukar lacca ya ji shigowar sako ta hanyar blackberry messenger cikin wayarsa, ya duba sai ya ga image ne ya shigo.
Ya bude yana kallon photocopy dinsa cikin mamaki, wani kosashshe kuma lafiyayyen jariri kamar yayi kaki ya tofar, ya tabbatar ‘Aliko’ ya zo. Ya lumshe ido ya yi murmushi ya sumbaci hoton jaririn. Karfe shidda na asubahin washegari shine mutum na farko da ya doka musu kofa.
Inna da ke lazimi bisa sallaya ta mike ta nufo kofar cike da mamakin wane ne zai zo musu a daidai wannan lokacin. Sai ta ga Zahraddeen rataye da falmaran din bakaken ‘suit’ da yake sanye dasu, a daya hannun kuma karamar jaka ce ta matafiya da jibgegiyar rigar sanyi wadda daga ganinta kasan daga cikin kankara ya fito. Kai kace wani haifaffen Afro-American ne. Wato irin bakaken fatar nan haifaffun Amurka wadanda iyayensu haifaffun can ne tun lokacin cinikin bayi.
Wadannan bakaken sun fi turawa kyau, sun fisu daukar hankalin mata, ga tsayi ga zati, ga koshin lafiya ta ko’ina. Sannan ga hutu a jikinsu kamar basa taka burbushin kasa.
Ta kama baki tana murmushi domin ba ta zace shi ba, don ko jiya da dare sunyi waya da shi bai ce da kowa zai zo ba.
Ta bashi hanya ya wuce ciki ta rufe kofar, ta dube shi suka yi dariya irin ta Uwa da danta. Ya zube yana gaishe ta, ta wuce daki ta barshi tana cewa.
“Kai! Yaran zamani da son ‘ya’ya sai a barku”. Shi kam murmushi yake ya matsu ya ga kyautar da Allah Ya bashi.
Tana shayar da Babyn ya murda kofar ya shiga, idanuwa shi fes a kansu. Abinda ya fara ce da ita shine; BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE……takawarki lafiya matar Zahradddeeeeeniiiii…” Har da dan rankwafawa, da jinjina ta girmamawa.
Zumbura mishi baki tayi
“ka ga Allah ka bari bana so!”
Sai ya tafi da sassarfa yana dariya ya hada su ita da bebin ya rungume su. Tsayin minti goma Zahraddeen ya kasa sakin iyalinsa, idon sa kawai ya rufe yana sakin ajiyar zuciya akai-kai, yana yiwa Alhaji Aliko addu’a ne batareda ita din ta sani ba. Saida babyn ya soma motsin matsar da akai masa sannan ya sake su.
Ya ce,
“na bari, bazan kuma TUNA BAYA ba. To amma Takori tace TUNA BAYA SHINE ROKO. Shiyasa na tuna din. Anyway kin biya ni Marwahhh….. (rana ta farko daya kirayi sunanta deeeeeeply a tsayin rayuwarsu) irin wannan ‘bouncing baby’ haka? (Ya fadi hakan cikin kokarin shigar da kwayar idanunshi cikin nata).
Har ban san da wace kalma zan nuna godiya ta ba”. Ya sake fada, yana kokarin su hada idanun amma ta ki. Ta mike zata fita, don ita kadai ta san me ta gano cikin kwayan idanunnan nashi, wadanda daga cikin su yake fara sauya tasha a salon soyayyarsa, amma sai ya riko hannunta don ya gane tafiyar zata yi, ba tareda ta juyo ba ya cigaba da Magana “Marwanatouh Allah Ya barmu tare cikin ALHERInsa, har zuwa ranar da muka daina numfashi”.
Ta daga mishi kai, yace “ban ji kin ce amin ba” Murmushi ta yi, ta juyo ahankali ta kwantar da kanta a kafafunsa. Jaririn na bisa cinyoyinsa. Ya zuba mishi ido kamar zai hadiye shi. Still hannunta cikin nashi bai cika ba.
“Guduwa zaki yi ki barni ko Marwanatuh? Alhalin tsallake komai nayi, nazo don muyi celebrating farin cikin mu mu ukku? Dubi nan…” ya nuna mata babyn, “me ya fishi dadi a rayuwa?
He’s a life-time companion 2 his Dad (Zahraddeeni), his pet, his friend and a Dad’s pride. In ban kare yinin yau da darensa da Uwarsa a gefe na ba, cikin sanyata farin-ciki, na wahalar dana bata wajen daukar cikinsa, rainon cikin sa da nakudar haifeshi…., celebration din will be incomplete, …..yet meaningless…….. !!!
Ya fadi cikin murmushi, cikin wata irin murya mai taushi dake nuna yana yin maganar ne tun daga karkashin zuciyarsa.
“Wata ukku, ban gan ki ba, ban ji dumin jikin ki ba ‘apple of my eyes….(the one I lobe most) ” ya fadi yana kokaerin dago habarta dake sunkuye,
“ga Da na yau a hannu na jikan Alh. Aliko, wanda zan dora a kujerar Aliko….., in gaya masa kowanene Aliko….., in sa masa suna Aliko…., inyi ta addu’a ya debo halayen Aliko…. If u did not join me in my celebration you might not run away from me……. Banda Allah wa zai maka wannan kyauta? Farin cikin dana ke ciki a yau Marwanatouhhh, ban taba tsintar kaina acikin irinsa a tarihin rayuwata ba….. so plz join me…..!!!”. Ya fada kasa-kasa, tareda aje Dan a gefe, ya mikar da ita tsaye ya rungume sosai, kamar ya maida ita cikin jikinsa su zama mutum daya, ya soma ‘kissing deeply’ irin yadda bai taba yi ba.
Cike take da kunyar iya shegen da ta rinka yi masa a baya, shine abinda ya sa ta kasa kallon idanun sa, yau ga dan sa ya fito daga jikinta tana shayarwa daga jikinta, domin cikin fadin duniyar nan a halin yanzu ba abinda take so sama da mijinta, da rabon da Allah Ya basu.
Shiyasa aka ce in zaka yi kiyayya ka yi ta saisa-saisa, haka in zakayi soyayya itama kayi ta tsaka-tsaki, don baka san me gobe zata haifar ba.
Ta tabbata Daddy gata ya yi mata, ta yarda ta amince da hakan yanzu, hakan da Aunty Shahidah tayi ta gayamata, amma ta ki sauraronta da gangan, da ina za ta samo miji irin Zahraddeen a wannan zamanin?



