Chapter 10: Chapter 10
Cikin mamaki ya dubi abokinsa, “How dare she know Rukayyahh???’
Ya yi murmushi idanunshi a kanta, ya ce, “Ina zuwa haka?”
Ta ce, “Saloon zani, tun kaina bai soma kyankyasa ba. Haka kawai an kama mutum dan Adam an kulle shi a gida kamar wani barawo a hannun mata”.
Ta juya ga Saifuddeen,
“Am a bery big fan of Takori. Na karanta ALHERI!”
Ya ce, “Haka Rukayyah ke wuni karatun Takorin nan, na rasa wane irin labari take gaya muku, ta zuki ta malle, ku kuma ku hau ku zauna kamar a gabanku ake yi. Zan sa ido a kan zuwanta wajen Rukayya, don na lura duk sanda ta zo, to sai Rukayya ta canza taku. Soyayya kamar ta kashe ni”.
Suka dinga dariya har ta fice ta barsu da Nadeeya, tana cewa,
“Bye-bye Mummy”.
Kafin ta dawo Saifuddeen ya tafi masaukinsa a Rodeway Inn.
Washegarui ya wuce Lagos su kuma a ranar ne Imam ya dankawa kowacce passport dinta suka soma shiri za su taho a washegari.
Duk dokin Safah na son dawowar da tafiyar ta kankama sai ta ji ba ta son tafiyar. Hankalinta ya tashi sosai da tunanin iyayen Nadeeya za su iya kwace ta, musamman idan suka ji cewa aure za ta yi ta sake dawowa.
Hatta Mami sai da ta ankara da damuwarta. Ta ce,
“Ba a kallafa rai kan abinda ba’a da iko da shi.
`Mutuncin yaro shine gidan ubansa, kuma mutanen nan duk wani karamci sunyi miki. Kema ki yi musu, tunda sun nuna hakan suke so.
Ki yi tunani, in rashi ne to sun fiki. ‘ya’ya biyu maza jigon gidansu ne suka fadi. Don haka wannan yarinyar wani nau’in farin ciki ce a garesu. Ke za ki yi ta haifar wasu, su kuwa fa?”
Ta share idonta da tishu ta ce, “Mami SABO ne!”
Mami ta rungumeta, “Zai wuce a hankali idan kika ga kin tara ‘ya’ya”.
Sun sauka ranar Asabar a Abuja, kai tsaye gidan Shahidah suka sauka, mai ‘ya’ya uku a lokacin, biyu maza mace daya.
Shahidah ta rasa ina ta-ka-saka-ina-ta-ka aje da iyaye da ‘yan’uwanta. Nan suka shiga hidima dasu ita da maigidanta. Kwana daya sukai suka karaso gida.
Gidansu na nan kulle yadda suka barshi, da yake maigadi yana nan da mai kula da shukoki, kuma Imam na biyansu ta banki. Gidan ma fes suka same shi, sun gyare shi fes.
Kwana biyu sukai suna hutawa sannan suka wuce Chikun gidan Baffa Sufyan, family house din su Alh. Aliko kenan.
Washegari Baffa Sufyan wanda ya manyanta wanda ya kasance kani ne ga mahaifin su Alh. Aliko, ya daura auren Almustapha Zubair Dan-Kasa da Safah Aliko Dan-Kasa a kan sadaki mai albarka, wato mafi kankanta.
Mal. Abdulkarim da sauran kannen Lamido maza sun halarta. Karshen karramawa Imam ya yi musu. Da za su koma tikiti ya yankar musu suka juya har da Shukrah-Nadeeya.
Don haka gaba daya amaryar yau an kasa gane mata. Duk ta birkice, kuka take tana karawa.
Ba don bata son auren ba, sai don rabuwar Da da mahaifi. Dan ma dan kankani who need an edtreme mother care….. kamar Nadeeya.
Ita take kalla ta tuno Lamaido. Ta yi masa addu’a, ita take kalla ta ji sanyi irin wanda iyaye ke ji a kan ‘ya’yansu.
To ya za ki yi? Amarya sai hakuri (Takori).
Mami ta yi waya da mutanen Malta, ta sanar dasu daurin auren ‘ya’yanta a karo NA BIYU.
Shima Imam ya yi waya da Zahraddeen, sunyi murna sosai, sannan basu ce za su zo ba. Ana tsakiyar walimar da Mami ta shirya a nan gidansu sai gasu dukkansu kamar an koro su. Zuwa na bazata, wanda ya kara armasa al’amarin.
Inna ma ta zo washegari ta yiwa Mami Allah ya sanya alheri, ita da Rabi’a da Umma. Washegari suka koma.
Zahraddeen da iyalinsa ma kwanaki uku suka yi. Rana daya suka bar Kaduna da ango da amaryar. Su suka hau mai zuwa Holland, su kuma suka hau na inda suka fito.
A cikin jirgin amaryar da angon like suke da juna. Duk da cewa jikin amaryar a sanyaye yake na angon ma haka.
Har kullum wannan abin na yawo a zuciyarsa yana tokare mishi a kahon zuci. Abin nan dai da Hajiya Maama ta gano.
Don haka daga shi har ita idan ka lura babu walwala da nishadi na sabbin ma’aurata a tare dasu. Dari-dari suke da juna.
Ita gani take kamar aurensu akwai kwaruwa a ciki, a matsayinsa na wanda bai taba dandana aure baa, ya auri wadda ta dade a cikinsa, har da haihuwa. Kawai sai ga hawaye suna zuba daga idonta.
Hannunsa kawai ta kama ta ce,
“Don Allah Ya Imam kaima ka yi irin na Zahraddeen ka auri Samry ko Barbara ko wata budurwa mu zauna tare. Gani nake na kwareka”.
Sai ya kama dariya ya rungumeta sosai, ya ce, “Ni din ko? Ashe saurayi ne tuzuru ba? Kar ki damu, na fiffige ‘yammata har ba adadi, wannan abin ba zai dameni ba. Nima Bazawarin kan titi ne in ji Hajiya Maama……..”
Ta hau dukan kirjinsa da hannayenta biyu tana shagwabar da bai taba gani a diya mace ba.
Don haka a daddafe Imam ya jure nisan wannan tafiya ta Paris suka shigo, tafiyar 11 hours daga Paris.
Sanda suka iso Beberly Hills inda gidansa yake karfe goma sha biyu ne na dare. Bacci ne dankam a idanun kowannensu.
Don haka dakinta na da ta nufa, shima ya nufi nasa. Wanka kawai suka yi da yake babu yunwa a tare da kowannensu, sai kawai kowa ya bi lafiyar gado.
A rayuwar da Safah ta yi da Lamido, bata taba cin wani abu wai don neman karin ni’ima ko something associate, other than wanda likita ya yarda da shi kamar fruits, fresh milk, honey (zuma), farfesun kifi ko na kaji ko zabi, yawan shan ruwa, cin cukwi, dabino da kwakwa, ta duk hanyar da za su sarrafu.
Don haka yanzun ma ba ta manta ba, balle a inda suke da abubuwan tantsan fiye da namu. Wato ko kayan marmarinsu bula-bula (riped)ne nunannu da suka bambanta da namu sun wadaci mai cin su.
Tana jin sanda Imam ya shigo dakin don ganin ko ta tashi da safe, ta yi lamo a kan pillow kamar mai barcin gaske. Tana jin sanda ya sunkuyo ya sumbaci goshin ta, ya mayar mata da gashinta da ya bazo a kan fuskarta baya, sannan ya fita.
Sai bayan fitar tasa ne ta tashi ta yi wanka, da yake ta samu ta yi sallar asubah tuntuni. Walha ta gabatar domin hantsi ya dubi ludayi.
Ta shirya cikin suit din Marc Jacobs mai dogon hannu da dogon siket bakake wuluk da kwalliyar silber. Sai ta dora mini hijab fari sol dan Saudiyyah, ta zabo farin flat shoe ta saka bayan ta tabbatar akwai kudi isassu a katuwar bakar jakarta samfurin Gucci.
Sanda ta fito dattijuwa Suzana na ta goge-goge, suka gaisa ta yi musu sannu da dawowa, sannan ta kawo mukullin mota ‘sportist camry ‘ta bata, ta ce in ji Oga ko za ta bukaci fita.
Ita da har ta shirya public bus za ta je ta hau ko ta yi shatar tadi saboda kayan da za ta sayo.
Don haka ba karamin dadi ta ji ba da Suzana ta bata wannan sako, sai tasa hannu cikin jaka ta fiddo kudi ta bata, ta ce ta yiwa yara sayayya in ta gama aikinta ta tafi. Suzana ta yi ta godiya.
A zamanta na shekaru uku ba kadan a LA (Los Angeles) waje dai-dai ne bata sani ba, don haka kai tsaye ta nufi babbar kasuwar kayan abincin LA da ake kira Farmers Market.
Ita wannan kasuwa, kasuwa ce ta kayan abinci zallah na kowanne ethnic group, wanda manoman California ke shigowa dasu. An bude ta a watan Yuli, 1984.
Akwai food stalls, sit down eateries, prepared food bendors da sauransu. Kasuwa ce mai tsohon tarihi a LA, kuma bangare ce na tourist attraction. Babu irin kayan abincin Amurka da babu, tun daga American Cuisine, Latin-American, African da kuma Asian Cuisines.
Tana nan ne kan titin Fairfad Abenue cikin kauyen Fairfad din Los-Angeles. Duk abin da take so ta samu har ma da kari. Kankana rusa-rusa, cukwi irin nasu (rake), kayan yaji su kanimfari da ma wadanda ba ta zaci samun su ba tunda na surkukin Africa ne.
Ba ta iso gida ba sai bayan la’asar. Ta nika na nikawa, ta cakuda na cakudawa. Ta ki cin komai ta maidasu abin cinta da shanta. Ta jera su cikin firji a kicin.
Karfe shida daidai Imam ya dawo a yunwace matuka, yana ajiye bakar brief case dinsa ya cire kwat ita ma ya ajiye, kai tsaye kicin ya dosa.
Ya bude firij ya ga an cika shi da gyararrun kayan marmari, ya dibi iya wanda zai iya sha ya nufi falo.
Ya gane ta fita kenan tunda da safe da ya fita bai gansu ba, shi kuma bai aiko kowa ya kawo mata ba. Suzana ba zama take ba da ta gama ayyukanta tafiya take yi.
Sai da ya ji sassaucin yunwar cikinsa sannan ya nufo dakinta, sai ya same ta a kan sallaya tana sallar la’asar da ta risketa a hanya.
Gadonta ya haye ya yi dai-dai, daga shi sai dogon trouser din dake jikinsa baki na Jeans, ko sallame sallar ta kasa yi sai jan tahiyar take don ta yi tsawo.
Ya Imam ya zama surukin da ko ido ta kasa hadawa da shi, idan ta yi tunanin cewa wai ta san namiji har ta haihu da shi, shi da yake gaba da ita da shekaru masu tazara bai san komai ba.
Wane irin kallo yake yi mata? Don haka ne ko da ta sallame sallar wata ta tayar ta yi ta dungurawa tana sallamewa har dai ya juyo ya dubi sashen da take.
Ya ce,
“Ba a yin nafila bayan la’asar, lokaci ne na masu ibadar bautar rana. So sallame haka ki sama min abinda zan ci”.
Dole ta sallame din ba tare da ta cire hijaab dinta ba ko ta bar kan daddumar, ta ce da shi (kai a sunkuye) “Me za ka ci?”
Ya ce, “Me zamu ci dai, don wallahi sai kin ci, kayan marmari ba abinci bane. Kayan tarbar maigida ne ko?”
Ya fadi cikin dariya da tsattsareta da idanu. Ta kunshe baki, “Ni ban ce ba”.
Ya ce, “To na ji baki ce ba, tashi yi min edpress akuyar cikina ba ta jure wannan azabar”.
Dariya ta yi kadan, ta mike ta linke hijabin tasa a sif ta rufe, kayan da ta dawo kasuwa ne dasu a jikinta tana son canjawa amma babu hali.
Kamar ya san tunanin da take yi kenan, sai ya dirgo daga gadon ya fice yana cewa, “Komai wayon amarya dai ta riga ta zo hannu, sai in mai ita ne bai ga dama ba”.
Hararar shi ta yi ta gefen idonta, yasa kai zai fita yana son ya yi dariya, ciki-ciki ta ce, “Me za ka ci?”
Don ya kureta, don ya san girki is out of her hobbies sai ya kakalo popular French recipe ya ce, “Poulet en papillote chicken packets and moshrooms”.
Ba ta ko juyo ba ta nufi kicin. Shi kuma ya yi amfani da damar yaje ya yi wanka yai sallah, yana kan keken motsa jiki short nicker ne kadai a jikinsa sai farin cambus da ya daure kafafunsa ciki. Haka nan sai zufa yake.
A lokacin ne ta karaso ta ce, “Na gama”. Tare da nuna masa tebur.
Mamamki yai bala’in kama shi lokacin da ya yi arba da recipe din cikin tsari mai ban sha’awa. Ya ce, “Brabo!”
Sai ta yi murmushi ta raba ta gefenshi za ta wuce, caraf! Ya riko hannunta ya zaunar da ita bisa kafafunshi.
A baki yake bata abincin tana ci kamar ba ta so, ba tare da ya damu da ya fara kuenching tashi yunwar ba.
Abincin ya yi mishi dadi ainun yadda baya zato, domin dai shi da abincin Mami da na restaurant ya dogara. Yau sai ya samu canji wajen dandano da gardi mai tafiya da zamani. Kamar mai wani nasibi cikin hannayenta da ta sarrafa abincin dasu.
Imam dai kokari yake amma tsohuwa mai shekaru 80 ta fishi nutsuwa, inda duk ta yi cikin gidan binta yake yana kalenta da magana.
Wani ta daga kai ta ce eh, a’a, wani ta share. Karfe goma sha biyu na dare agogonsu na can wanda ya yi daidai da karfe hudu na yamma namu na gida Nigeria.
Ta fito wanka ta zuba nighties farare sol, ta debo wasu turaruka da suka yi mata a wani kantin kusa dasu (coach poppy, fressia blossom) da kuma wani Boss Femme (for women) ta feshe jikinta da shi.
Tana tufke gashin kanta wanda ke ta sheki da nashi kamshin na daban na kumfar head and shoulder. Imam ya turo kofar dakin ya shigo cikin pyjamas ruwan makuba cikin nashi sassanyan kamshin.
Ya rufe kofar ya maida bayansa ya jingina da kofar. Ya runtse idanunsa yana tuno abubuwa da dama.
Wai sai yau ne ya zama cikakken mutum daidai da kowa, amma wai a duk tsayin shekarun da ya yi sunansa incomplete, kuma wanda darajar ibadarsa ba ta kai ta mai aure ba.
Shi din a yau saurayi yake, domin a tsayin rayuwarsa tun daga kuruciya har girma bai taba yin zina ba. Sai ‘yan kurakurai da babu yadda dan Adam zai yi dasu.
Sai ya karasa da sassarfarshi ya rungume matarshi, rungumar da bai taba yiwa kowa irinta a duniya ba.
Hot kisses kawai yake blowing a kowacce gaba mai bukatar hakan a jikinta. Safah bata haihu ba, fida aka yi mata, don haka jikinta tsam-tsam yake.
Ta yi shayarwa ta kusan shekaru biyu, amma ko kadan halittar kirjinta ba ta sauya komai ba. Domin Mami ta kula da wannan, ta hanyar traditional method (kunun alkama, ko kunun farar shinkafa).
Koma dai ya ya ne, Imam ya yi sabuwar rayuwar da bai taba yin irinta ba. Yau ya kira yi Safahn da yake kira Bazawara da sunaye da dama. Wanda Safah ta rokeni da in suturta sirrinta. A kwanaki uku da suka biyo baya, amarci ne ake zubawa zallah.
Ta yarda ta amince cewa shi din ma Bazawarin kan titi ne kamar yadda ya ce, domin abubuwa da yawa idan ya yi, ita edpert ko edperienced a fannin bata san su ba.
****
Shigowar shi kenan a yau da yamma daga ofis, don yanzu karfe biyar yake dawowa maimakon shida. Shigowa ya yi da World Atlas ya dora a cinyoyinta mai dauke da ‘Map’ na dukkan kasashen duniya, tun daga Africa, Europe, America, North America, South Korea, Asia da UAE ta zabi inda za su je honey moon dinsu.
Gilashinta tasa fari kal tana dubawa sosai. Baiwar Allah, sai ta nuna Saudi-Arebia.
Hakan aka yi, sati na zagayowa suka tashi zuwa Saudiyyah daga nan. Idan Safah tana Dawafi addu’arta itace Allah Ya yi gaggawar bata ‘ya’ya marasa adadi da YA IMAM. Ya albarkace su da ilimi da fasaha irin nasa. Ya basu zuciyar jin kai da kyautayi ga iyaye da ‘yan’uwa kamar ALMUSTAPHA ZUBAIR DANKASA.
Idan Safah da Marwah take cewa take “Ya Allah ka albarkace ni da samun tagwaye mata domin akasarinsu masu jin kan uwa ne, in sa musu suna SAFAH DA MARWAH. They would be brainlliant insha Allahu kamar YA IMAM”.
Rannan bata san cewa sambatunta ya fito ya shiga kunnuwan Imam ba. Ai da suka koma masauki ta gayawa aya zakinta. Domin cewa ya yi “Nothing worth comes easy”. Wato ba za ta samu ‘ya’yan masu daraja da sauki ba sai an ci wuya ake samun su.
Kai Imam ba dama ne. Kuma ga dukkan alamu Allah Ya amsa addu’arta, domin ba ta baro Saudiyyah ba sai da cikin ‘yan biyu wata biyu.
***
MURFI
Nadeeya Nasir Abdulkarim, ‘yar shekaru goma sha shida, dalibar ajin karshe a Nigerian Turkish, ta ajiye Nobel din da ta gama karantawa ta dubi mahaifiyarta da ta bata tana murmushi.
“Mummy kun ga rayuwa”.
Ta ce, “Mun ganta kam Shukrah-Nadeeya, itama ta ganmu, mun sha gwagwarmayar soyayya a cikinta. Mun shiga ko’ina a duniya mun yi rayuwa, mun bi mahaifinmu mun kuma ga falalar biyayya ga iyaye.
‘Ya’yanmu goma kenan ni da Ya Imam, in an hada dake sha daya. Mami ta yi aure a Kaduna tun bayan komawarsu da wani manajan Zenith Bank, kuma ta ci gaba da haihuwa.
Hajiya Maama ta dade da rasuwa, amma fa bayan ta goya ‘ya’yan mu ni da Ya Imam. A wata sabuwar gwamnati da ta hau ta General Abdulsalami Abubakar, ta yi afuwa ga ‘yan fursuna, ciki har da Danejo, domin ita Inna Shatu tun a can prison ta rasu.
Tana nan tana bin kwararo-kwararo tana tsince-tsince, kwanan bola da wanka a kwatami. A lokacin ‘ya’yanta Fahad da Fa’ik sun kawo karfi, su suka kama ta suka kaita gidan mahaukata suna biyan komai na kula da ita.
Marwah da Anisa sai son barka, sun cikawa Zahraddeen gida da kyawawan ‘ya’ya maza da mata, abin alfahari ga iyayensu.
Masha Allah Lakuwwata illa billah!
Nan na kawo karshen labarin BABBAN GORO. Na godewa TAKORITES…. Dake biye da rubutuna babu gazawa.
Sai mun hadu a RAYUWAR RAYHANAH nan ba da jimawa ba cikin yardar mai duka.
Ina kuma baku hakuri game da tsoffin littafai na da nace za’a same su an samu dan tsaiko ne amma suna nan tafe ko wane nan lokaci daga yanzu.
RAYUWAR RAYHANAH!
Sabon salon rubutu ne da Takori bata taba yin rubutu irinsa ba.
A sa’ilin rubuta littafin RAYUWAR RAYHANAH, bana sanin sanda hawayena suke zuba. Ba don komai ba sai don tausayin Rayhanah mai matsalar da ba a san ranar warkewarta ba. Ga talauci, ga maraici, ga cukurkudaddiyar soyayyar mutum biyu.
Rayuwar Rayhanah zai zo da sabon salo, irin salon da babu a SIRADIN RAYUWA, TUNA BAYA, GIRMA YA FADI. ALHERI, ALKAWARI BAYAN RAI, A BARI YA HUCE, YAKANAH, WASAN KANIN MIJI, ZUCIYAR MUTUM ko AMANATA.
Yana zuwa bada jimawa ba Insha Allahu.
WA-BILLAHI TAUFEEK



