Chapter 3: Chapter 3
Ta so ta baiwa Inna amsa ko don Zahraddeen ya jiyo, sai kuma ta fasa, a sabili da sabon kudurinta na yakice Zahraddeen daga zuciyarta ko tana so ko ba ta so.
Don haka ba ta ga me ya yi mata zafi da rayuwarshi ba. Sai ta shige kicin don ta yi kalaci, ta debi soyayyar Agada (plantain) mai yawa, da soyayyen dankalin Turawa, da kunun alkama, ta ja kujera ta zauna ta sa musu ido.
Ga mamakinta duk da yunwar da take masifar ji ta kasa cin ko loma daya. Sai ta sa kanta cikin cinyoyinta ta fashe da kuka
Karfe takwas da rabi Zahraddeen ya yi musu sallama zai wuce, bayan ya barwa Inna komai da za a nema.
Tuni ya yiwa jaririyarshi huduba da sunan Inna. Inna har kukan dadi ta yi tana shi masa albarka.
Daddy na ta kuka sai ya bishi. Yau ma kamar kullum kalaman nan ya gaya masa, wadanda inda sabo to yaron ya saba jinsu daga bakin mahaifin nasa.
“I’m bery sorry my darling Daddy, I’ll be back to you soon……”
Da kyar Inna ta rike shi yana kuka yana birgima kamar ransa zai fita.
Zahraddeen abin so ne, ba ga ‘yammata kadai ba, har ma ga matan aure marasa kamun kai. Ga iyalinsa abin so ne abin kwatance.
A wurin matarsa abin tinkaho ne da za ta iya lika shi a goshi da ana likawa, ta shiga ko’ina tayi alfahari da zamantowarshi miji a gare ta.
Ba wai don kyawun sura kadai ba, ‘a’a, sadauki ne a nuna so da kauna ga iyalinsa. Jarumi a fannin SOYAYYAH da idan yana son mace, hatta farcen jikinta sai ya shaida.
Ta fannin kulawa a garesu da bukatun rayuwa kuwa, Marwah mantawa take ita ‘yar Aliko ce, domin a daidai wannan lokacin da Zahraddeen ya zamo wani kusa a cibiyar kasuwancin kamfanonin saka sittiru na Geneba, baya ga albashin da yake shiga account dinsa na kamfanonin Dan-Kasa da yake jagoranta. Idan bai fita kudi ba, to bazata fishi ba.
Runtse ido da yakeyi a kan mata kala-kala ma kadai wani babban jarumtaka ne da ba kowanne namiji dake mataki irin nasa ne zai iya yi ba.
Wannan tunanin da Marwah ta yi sai ya fara kawo sauyi cikin ranta a kan muguwar akidar da zuciyarta ta dora ta a kai, a yau ta tabbatar ya zama mugunta ga ANISA, wadda ba ta ci mata ba, ba ta sha mata ba. Da shikansa Zahraddeenin. Sannan ba ta yi amfani da kalmar nan da ake fadi ba, wato ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne.
Da hadisin da ya ce ‘imanin dayanku baya cika……….. Ta zama azzaluma, ta zamo muguwa ga ‘yar’uwarta Musulma.
Ta so kanta da yawa, KISHI ba hauka bane. Don ko Zahraddeen bai furta yana son Anisa ba, a yau ta karanto cikin ido da gangar jikinsa ta yi masa kadan (ba ta isarsa), balle kuma cikin wannan halin na biki da ta ke ciki.
Ta sani Zahraddeen zai iya hakuri da komai, amma ban da wannan. Gabanta ya ci gaba da faduwa da ta jiyo shesshekar kukan Anisa.
A lokacin yana kokarin saka takalmanshi rufaffu bakake da ya tube a kofar dakin Inna, zai wuce ta kicin sai ya tsaya a kofar kicin din jikinsa a bala’in sanyaye.
“Kuka Anisa? Me aka yi miki?”
Dagowa ta yi ta zuba mai harara, ta murguda baki ta ce, “Ina ruwanka da kukana? Allah ka dauki raina in bi Badijo in huta”.
Ta rarumo faranti ta maka masa a goshi ya kare, ta dauko katon kwanon samira ta daidaici kafadarsa ta maka masa. Ta ci gaba da rarumar duk abin da ya zo hannunta, muciya, bulugari, ludayi tana kwala masa yana tarewa yana fadin “Ke Anisa? Baki da hankali ne?”
Ta ce, “Bani da shi, sanda ake rabon shi ubana bai kaini ba”.
Kafin ya yi aune hannunta ya kai kan zaftareriyar wukar Inna, ta yo kansa da wukar ta ce, “Ko ka tafi ka barni ko in caka maka, in yaso nima a kashe ni”.
Sai ya shigo kicin din gaba daya, cikin zafin nama ya rike ta yana kokarin kwace wukar ta ki saki, idan kuma ya takura, to la-shakka shi ko ita, wani ya zaftare hannunsa.
Sai ya rungumeta da karfin gaske ya cika hannun ya ce,
“To gani kashe nin”.
Sai ta saki wukar tana kuka, a lokaci guda tana kokarin kwatar kanta daga tsattsauran rikon da ya yi mata.
Dukkansu haki suke kamar wadanda suka yi gudun mita goma. Juyowar nan da za suyi suka yi ido shida da Inna, Marwah, da Nura.
Marwah ta mika mata wata karamar troller da Abaya da mayafinta kirar Oman ta ce, “Ungo sanya ku tafi”.
A razane duka suka dube ta. Sai ta yi murmushi wanda da gani ka san na karfin hali ne.
Ta ce, “Ku tafi don Allah kada ku yi missing ebening flight it is past eleben fah”.
Inna ta ce, “Sannu ‘yar albarka, ku fito min daga kicin kada ku yi min kisan kai a gida”.
Marwah juyawa ta yi ta koma daki. Ya yi tsaki zai wuce ya ce da Inna, “Da wannan mahaukaciyar? Allah Ya tsareni”.
Inna ta ce, “Allah yasa daga turu ta fito wallahi bar min gida za ku yi, ba za ku yi min kisa a gida ba”.
Sai ya sa kai kawai ya yi waje jin Inna na rantsuwa. Nura na cikin motar yana jiransa, don shi zai kai shi filin jirgi.
Gaban motar ya bude ya zauna dafe da kansa dake sarawa tamkar ya tsage gida biyu. Inna ta sako Anisa a gaba da jakar da Marwah ta hada mata ta bude mata kofar baya ta shiga.
Ta ce, “Allah ya kiyaye hanya”.
Nura ya ja mota suka fita.
Inna ta koma cikin gida tana ce da Marwah, “Allah Ya tallafi zuri’arku, ya kyautata gabanki da bayanki, ya kara kaunarki a zuciyar mijinki.
Kin yi min abin da na kasa saboda kunyar kwayar idanunki, sai ki yi jegon ki cikin salama suje can su karata. Muma mu zauna bakinmu alaikum”.
Marwah dai murmushin karfin hali take, don haka Inna na ba da baya ta soma share hawaye.
Amma sai ta kawar da komai da ta yi wani tunani guda daya, wato dauki (taimako) ne Allah Ya kawo mata.
Da Zahraddeen ya dinga mu’amala da matan banza gara su hada kai ita da Anisa su tallafeshi, su taimaki juna. Ta sani tanada matsala a fannin auratayya wadda ta san ko Zahraddeeen bai fada ba tanada raki kuma tanada karancin sha’awa, ita dai barta a romancing a yi ta romancing ko za’a kwana a hakan bazata gaji ba, yayinda Zahraddeen din a lokuta da yawa sai ya hada da magiya, lallashi, wani sa’in har da hawaye, sannan take kai zuciya nesa tayi don samun rahmar Allah amma physical need dinta is bery low.
To dama haka ne, duk dan adam ai tara ne bai cika goma ba. Sai kuma in akan-karan kanta ne abin ya zo mata, (wanda ana dadewa hakan bai faru ba), to fa duk inda yake cikin duniyar nan zata bishi ko ta nemo shi koda Geneba ne.
Ko babu komai tana da guarantee a kan cewa yarinyar ba za ta cuce ta ba, ba za ta cuci Zahraddeen ba. Tsakaninta da Allah take son shi, gata ‘yar uwarsa da jininsu ke cakude da na juna.
Cikin kwayar idon Anisa kadai ta hango kaunar jaririyarta. Kauna ta jinin ‘yan uwantaka irin wadda Allah ke sanyawa a zukatan bayinSa da suke jini daya, Me za ta yiwa Inna a duniya ta biyata abinda take mata? Banda ta kaunaci nata da zuciya daya? Ta tayata su sauke alkawari da rikon amanar da Allah Ya dora musu.
Mene ne duniya? Guda nawa take? Balle jin dadin dake cikinta? Sama da wannan ma ta san ba wani abu Anisa za ta gutsira a jikin Zahraddeen ba. Duk wata kuruciyarsa ta kwashe ta, duk wata soyayyar da zai nunawa wata diya mace, wallahi ba za ta kama farcen wadda yake yi mata ko ya yi mata ba.
Sai ta fara neman abin da zai kau da hankalinta daga kansu. Ta soma neman ‘yar’uwarta a waya don ta sanar da ita ta sauka lafiya, amma har yau ta kasa kama layinta balle na Lamido.
Sai ta kira Mami da Shahidah, Mami ta ce, “Inna ta gaya mata haihuwar ai, yanzu haka suna kan hanyar tahowa Zaria, har sun iso Jaji”.
Ta gayawa Inna, tuni Inna abin nema ya samu wato hidima da jama’a. Kafin su iso sai ga Rabi’a ta iso da yaranta da mijinta da ya kawo su.
Sai dai shi bai dade ba bayan ya ga jaririya ya yiwa Inna barka sai ya tafi, da alkawarin dawowa daukar su bayan suna.
Rabi’a ita ta kamawa Inna, nan da nan suka kammala abinci na alfarma da Inna ta shirya musamman don bakin nasu.
Sanda su Mami suka iso azahar ta wuce, anan ne Mami ke gaya mata su Safah suna Miami Lamido babu lafiya.
Kusan Marwah har ta fi Safah damuwa da ciwon Lamidon. Wuni ta yi abun na damun ta a zuci. Tana son ta ji lafiyar tasa, Safah ba ta hawa (any social network) kuma ba ta da lambarsu ta can Miami.
Don haka ta ci gaba da tsimayen kiran Safah, ba ta san ba ta da kwanciyar hankalin da za ta tuna da wani abu a duniya wai shi waya ba.
Kwanan su Mami biyu suka koma Kaduna, yarinya ta ci sunan Inna Fatima Binta. Hajiya Maama kullum cikin ciwon kafa take, shekaru sun tura. Kullum karfinta kara karewa yake. Don haka ta daina fita. Shekaru da girma na aiki a jikinta matuka, domin shekarunta tamanin da uku a duniya.
Don tana cikin kyakkyawar rayuwa ne ya sanya jikinta bai nuna hakan. Ga karfin imani da kula da addini wadanda duk suna kara lafiya.
Haka suka ci gaba da jegonsu cikin kwanciyar hankali, kullum sai Zahraddeen ya kirasu ya ji lafiyarsu. Har kukan Fati sai an sa masa ya ji, sannan ne hankalinsa zai kwanta.
****
Zan so hasko muku rayuwar Zahraddeen da kanwarsa kuma amaryarsa a hanyar tafiya Lagos .
Da suka bar Zaria ba Abuja ya nufa ba, dama Lagos zai je akan harkokin DAN-KASA HOLDINGS na man fetur da suke son kara bunkasawa a birnin Ikko ya zamana zai dan jima acan. Don haka jirgi suka hau daga Kaduna.
Karon Anisa nafarko kenan da hawa jirgin sama a rayuwarta, don haka da jirgin ya soma ruguginsa, ba ta san sanda ta kankame Zahraddeen ba.
Zahraddeen bai yi magana ba, sai da jirgin ya daidaita a cikin gajimare, serbice suka soma turo troller din abinci sai ya ce,
“Dagani haka zan ci abinci, Bakauyar banza!”
A ranta ta ce, “Eh, na ji dai”.
A fili kuma ta zumbura baki ta juya mai keya.
Bai kara kallonta ba sai ya ji tana yiwa daya daga cikin masu rabon abincin masifa wai don me za ta ba ta naman Alade (Pig). Ita Musulma ce rainon Musulmi. Matar ko Hausa ba ta ji amma ta lura ta bata mata rai ne. Sai ta hau sorry-sorry, sannan ta bata menu don ta zabi wanda take son ci ta kawo mata. Don ta fahimci korafinta kenan.
Kamar gaske sai ta karba tana dubawa, sai ta nuna mata (pork-tendertoin), da rawar jiki matar ta juya da naman kaza nikakke (grilled chicken nugget) da ta ki ci, ta kawo mata farfesun Alade. Domin a first class suke komai suke so za a basu. Zahraddeen dai yana gefe bai yi magana ba, amma dariya da haushi suna nema su kashe shi.
Ya ga da gaske cin aladen nan za ta yi kuma alhaki zai hau kansa. Sai ya karbi takardar ya sunkuyar da kai (studying the menu). Ya ce ta koma da wannan ta kawo mata (roasted chicken) gasassar kaza.
Har suka sauka a filin jirgin saman Murtala Mohammed bai kara kula ta ba.
Direba daga office dinsu na Lagos na jiransa, ya kwashe su zuwa inda aka tanadar masu masauki tun kafin zuwan nasu.
Wanka ya fara yi sannan sallah, ya yi shiri cikin kananan kaya ya fice. Bayan ya yi umarni ga yaronshi Stebe ya yi girki mai kyau ya bata.
Yadda ya fita ya barta haka ya dawo ya same ta, ko kayan jikinta bata cire ba ba’a maganar wanka, tana zaune cikin 3 seater tana barci. Ga jakar kayan da Marwah ta bata a gefe ko zugeta ba ta yi ba, balle ta ga mene ne a ciki, ga abincin da Stebe ya jera a dining da ya duba sai ya ga ko budewa bata yi ba.
Tausayi ya kama shi, don ya san bai bata daki ba kafin ya fita. Ya zube shirgin da ya shigo dasu daga Shoprite ya soma tashinta.
“Anisa….ke Anisa, tashi mana. Ya kike barci a zaune sai wuyanki ya sankare?”
Ta yi mika sosai bayan ta bankaro mai kirji ta yi hamma, sannan ta yi farr! Da lumsassun idanunta a kansa. Ya yi hanzarin kau da kai ya koma fada tamkar wani laifi ta yi masa.
“Don me za ki hau barci a kujera ko abinci baki ci ba, balle sallah da wanka. To ba zan dauki kazanta ba. Tashi maza ki je ki wanka ki brush ki fesa turare sannan ki yi ta barcin, kin ji na gaya miki”.
Ya cilla mata mukullin daya daga cikin three bed rooms din flat dinsa. Ta dauki jakar da makullin ta doshi daya daga cikin dakunan da ba ta san kowanne ne mai makullin ba.
Ta yi ta gwadawa har daki daya ya bude, a ranta tana cewa,
“Mafadacin banza wanda in bai likawa mutum laifin da ba nashi ba baya jin dadi.
Ko yaushe ya bani mukullin dakin oho! Da zai hau ni da fada. Ai ko wannan galleliyar matar tasa ba za ta gaya min yadda ake wanka ba, mu da muka taso da yin wanka a kogi ma ba a famfo ba”.
Zahraddeen na jin kunkuninta sai ya yi maza ya shige dakinsa kada ta ga dariyarsa. Yarinyar nan ko bai so ta don komai ba, personality dinta da gabuntarta na sa shi dariya da nishadi.
Tunda ta shiga dakin ba ta fito ba tana can tana murna da abubuwan da Marwah ta hada mata cikin jaka da ba ta taba ganin irinsu a rayuwarta ba.
Ta saka wannan ta kalli kanta a madubin dogon yaro ta cire ta saka wannan. Wasu tsala-tsalan rigunan barci ne (nighties) design daban-daban, kala daban-daban.
Turarukan cool water (Dabidoff) set daya, brush, maclean din signal, mouth wash da fresh mint kala-kala.
Ga kuma dinkakkun kaya marasa nauyi, atamfa, material da swiss lace uku. Nata ne ta dinka musamman don ta yi fitar suna dasu ba ta taba sawa ba, ga saitin kayan make up da mayukan pond’s flawless masu kara kyau da taushin fata.
Ga Anisa da son kwalliya, don haka a tsayin daren baki dayansa kwalliya take tana sakewa.
Abincin da Stebe yake hadawa yana ajewa haka yake kwasar kayansa yadda ya barsu. Iyakaci in ta ji kishi ta bude dan karamin bed side fridge din dake gefen gadon da ya zam nata ta kwankwadi jusi da fresh milk ba abinda ya dame ta.
A haka suka kwashe sati guda, Anisa ba ta da aiki sai wanka akai-akai kamar agwagwa. Ta yi kwalliyarta da kayan kishiya (kamar yadda take kiransu), ta yi feshe-feshenta ba kuma don Zahraddeen ba, ita kawai nature dinta ne yin kwalliya, ba kuma don Zahraddeen ya yaba ba.
Ta san ba shi da lokacinta, saboda in ya fita tun takwas na safe ba ta kara ganin kalarsa sai dai ta ji shigowar motar daga dakinta wajejen goman dare.
Wani lokacin ma sai ta yi barci. Shi ko kalaci a ofis yake yin abinsa. Sai dai yana tabbatar da lafiyar ta, cikin dare yana lekata ya ga ta yi barci tana shan A.C, idan zai tafi ofis ma yana kula da tashin ta lafiya.
Sannan ya umarci Stebe da ya dinga girka mata abinci mai kyau kullum duk ranar da ba ta ci ba ya gaya masa.
Ta hakan ne Stebe ya gane Anisa ba ta da cin abinci, sai shaye-shayen jusis da madara da su Hollandia. Sai yasa Stebe yake yawan cika firji dasu, kuma ya ce ya rage yawan abincin da yake dafawa a daina zubar da abinci., tun lokacin da ya gaya masa abin da take tsakura baya fin loma biyar.
Kan ka ce meye wannan, cikin watanni biyu kacal sai ga Anisa jiki ya canza completely, farinta da taushin fatarta sun fito. Jikinta ya zama smooth kamar ‘yan matan dake rayuwa a Switzerland. Budurcinta ya kai ya kawo har ta tumbatsa, dukiyar Fulani kamar sa tsaga rigarta. Ba ta yi kiba ba, sai gogewa da ta yi, ta zama looking takeaway (in ji Marwah), wato kamar a sace ta a gudu.
Abu daya ne Anisa take da nakasu a kansa, wato gyaran dogon gashinta. Ba ta iya ba, ba ta san ya ake yi ba, kuma ya fi karfinta.
Ba ta wanke shi balle (steaming ko relading). Sai dai kawai ta tattara ta kulle ko da danshi ba ruwanta, gashin ya yi ta rima.
Rannan Stebe na kicin ta shiga fuska murtuke (kamar yadda take mai kullum), amma na yau ya fi na kullum.
Stebe bai jin Hausa, ta tsaya a kofa ta ce, “Kai Stebe!”
Ya juyo da sauri “Yah Madam!”
Ya kame a tsaye. Ta ce, “Meye fassarar sunanka?”
Ya ce, “I donno Madam”.
Ta ce, “Kai dan wane Kabila ne? Yoruba, kanuri, Fulfulde, Igbo, Itsekiri, Ibra ko Ibibio?”
A nan ne ya dan fahimce ta, ya ce, “Ibibio”.
Ta ce, “Allahnka nawa?”
Sai ya dauka cewa shekarunsa ta tambaya. Ya ce, “Twenty fibe”.
Sai ta nuna masa hanyar kofa ta ce, “Jeka, daga yau kada in kara kanin kafarka cikin gidana, ba zan zauna da mai Allah ashirin da biyar ba”.
Stebe bai ji ta ba, amma ya fahimci korarsa ta yi. Nan ya kai gwiwoyinsa kasa yana afi yana hurwa yana magiya ta barshi da hanyar samun abincinsa. Yana yiwa Oga biyayya baya bata masa rai, ita ma baya bata mata. Idan laifi ya yi mata ta gaya masa zai gyara.
Ta harde kafa a jikin cabinet tana taunar cingum kas-kas-kas bakinnan ya sha jambaki jawur radau dashi, tana cewa,
“Wallahi sai ka tafi, in kuma ka ki in ce da Yaya Dini ka bugeni a duwawu”.
Daidai lokacin da Zahraddeen ya sawo kai ya jiyo muryar Stebe a kicin kamar yana kuka. Don haka da sauri yayo kicin din, kalamanta na karshe a kunnensa.
Sai jin muryarsa ta yi cikin kunnuwanta, “Bari ni in fara bugun mazaunan naki kafin shi ya buga”.
Ya kwanto belt dinsa ya zuba mata, ta yi tsalle ta yi gefe ta soma kuka. Ya dubi Stebe da har lokacin yana durkushe abin tausayi, domin dai shi madam Babba ba ta taba yi mishi haka ba in ta zo Lagos, ya lura kuma ta fi hankali da imani.
Ya ce, “Jeka sai na neme ka”. Da sauri ya mike yana ta godiya ya fita.
Ya daga belt din ya kara zuba mata a baya, ta rike wajen tana kuka ta ce, “da sannu Allah Zai saka mini”.
Duk sanda aka ambaci “ALLAH” to Zahraddeen ba shi da sauran kuzari. Sai ya juya ya fita yana dana sanin abinda ya yi, wato dukanta a gaban yaronsa, a matsayinta na matar aure a gare shi.
Ta gabansa ta wuce zuwa dakinta tana ta kuka, sai ya mike ya bita, karo na farko tun zuwansu Lagos da ya shiga dakin.
Wani irin sassanyan kamshi na sprays da turarukan da take amfani dasu ba control da rabar iya kwandishan mai karfi shi ya fara ratsa jikinsa da hancinsa. Turare yana tada sha’awa, kuma yana kara dankon kauna.
Tana zaune a bakin gadonta fuskarta cikin tafukanta tana kuka, wata irin doguwar rigar barci ce a jikinta ruwan hoda, wadda ba ta boye komai na halittarta ba.
Ya tuna shi da kansa ya zabowa Marwah rigar a wani boutikue a Paris, bata taba sawa ba. Sai ya ji idanunsa a yau na kunyar sake hada ido da MARWAH, a lokacin da ya janyo Anisa jikinsa yana lallashinta.
Gaba daya ya susuce a lokacin da sanyin fatar jikinta ya shafi nasa. Hannunsa ya kai cikin yatsun hannunta mai laushi kamar auduga. Sai ga Yayan dake masifa da rashin mutunci ya koma sambatu. Wannan wace irin yarinya ce kamar ba’indiya? Ba ta da maraba da wata jarumar India da ya taba gani a Cardiff (Amisha Patel).
Al’amuran da suka biyo baya ba za su fadu ba. Abinda ya sani shine, shi ya raba Anisa da budurcinta, ta yin amfani da karfin da Allah ya hore masa na namiji (by force) ba tareda tausayawa ko concern ba.
Sai da ya nutsu ya dawo hayyacinsa ya fahimci aika-aikar da ya yi, kwana suka yi basu yi barci ba tana ta kuka banda Allah Ya isa ba abinda take masa duka ya karba yana ta lallashin ta da dukkan iyawarsa. .
A kwanakin da suka biyo baya, Zahraddeen lallaba Anisa yake yi tana kara botsarewa, tunda ta fahimci ashe tana da amfani a bayan idon matarsa.
Ita da Rabi’a ta kwadaitar da ita al’amarin ashe ba haka yake ba. Ta ki yarda sam ko kusa da ita ya zo. Ta tubure ita lallai ya maidata wajen Inna. Amma da ya sayo tsaleliyar Blackberry ya kira mata Innar ta ji muryarta ya kuma danka mata sai ta bada kai bori ya hau, ya ci gaba da kwasar ni’imar da Allah Ya bashi, ba tare da ya yi zato ba.
Ai fa tunda Anisa ta yi waya aka manta da zancen komawa gidan Inna, shi ya zauna ya hada mata ya nuna mata komai yadda za ta fahimta.
Bata fahimci komai ba ban da yadda za a danna kira (green botton) bayan an saka lamba.
Nura aka fara kira da ta roki Zahraddeen ya ba ta lambarsa.
Sanda ya dauki wayar bai san waye ba, sai ji ya yi ta ce, “Kai da Allah bakauye how far?”
Nura ya tintsire da dariya ya ce, “Fine my wife, ya masifaffen mijinki?”
Anisa da baki babu linzami ta ce,
“Kai da Allah ya daina masifa ya zama dan kirki, har Ice-cream yake sayo min”.
Ya ce, “Banza, don yana sayo miki Ice-cream shi kenan sai ki yi zaton yana sonki?”
Ta ce, “Kai da Allah yanzu fa ko magana zai min sai ya make murya kada na ji haushi nace ya maido ni wajen In……..”
Fizge wayar ta ji anyi, sannan ya bita da hauri da kafa da bakin cober dinsa da bai cire ba, ta tuntsura cikin kujera babu shiri ta zuba ihu saboda azabar da ta ji a kwaurin ta.
Ta ce, “Wayyo Allah……, wayyo Bodijo”.



