⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 6: Chapter 6

Cikin wannan lokacin gaba daya, Imam da Mami ke jinyar Safah. Marwah kan zo ta yi kwanaki ta koma.
Ganin al’amuranshi na shirin durkushewa a dalilin rashinsa, sai ya yi magana da likitocin Safah kan zai fita da ita. Suka shirya takardun komai, ya hada passport din Mami da na Hajiya Mama ya nufi Abuja.
Cikin sati biyu su Mami suka yi sallama da kowa, ‘yan’uwa da abokan arziki, Marwah na kuka ‘ya’yanta na yi. Gidan rufe shi akai da manya-manyan (padlocks) domin tafiya ce da babu ranar dawowa.
Ya dai yi alkawarin zai kawowa su Malam Abdulkarim abinda Safah ta haifa su ganshi da zarar haife shi. Da an yaye shi/ta za a basu jikansu kamar yadda suke so.

Hajiya Nadeeya da Mami sun sha kuka. Zahraddeen kansa ya koka har ya gode Allah. A duk sanda ya tuno Lamido da halin rai kwakwai mutu kawai da Safah ke ciki, kuma cikin kudurar Ubangiji wai da ciki.
Don haka a ganin Zahraddeen rangwamen Imam ne rashin sanin Lamido! Sai dai ya ji a bakin Mami, Shahida da maigidanta sune ‘yan rakiya don su ga muhallinsu.
Ranar alhamis ashirin da tara ga watan Mayu suka daga Amurka. Sun sauka birnin New York jirgi ya huta, sannan suka daga Los Angeles a yammacin ranar juma’a. Lafiya suka sauka a babban airport din Los-Angeles..
Motocin da suka zo dibarsu kadai da bakake da jajayen ma’aikatan sun basu tsoro. Domin in ka kalli Imam din a haka yadda ya maida kansa Sufi (Sufism) ba za ka ce ya mallaki naira goma ba.

Da suka shiga farfajiyar gidansa a Beberly – Hills, Hajiya Maama kuka ta saka, ta ce, “Anya Almustapha ba cinikin sassan jikin mutane kuke yi ba?”
Shahidah da Hafizu suka sa dariya. Imam ko kallon ta bai yi ba, abinda ya dame shi ya dame shi, wato halin da Safah ke ciki a asibiti. Allah-Allah yake a sauke su ya bude musu gidan su shiga ya juya.
Domin tun daga filin jirgi motar asibitin Good – Samaritan (daya daga cikin manyan asibitocin Los-Angeles) ta yi gaba da Safah cikin ambulance aka dora a inda aka tsaya.
Kwanan Shahidah da Minister Hafizu bakwai a guest house din Imam suka juya gida Nageria. Suna masu yiwa Safah fatan alheri da samun lafiya.

Kowannensu da dalleliyar mota kirar jiya-jiya (2015 Sonata Genesis) wadda bata kai ga isa kowace kasa ba, daga kamfanin Dan-Kasa Motors.
Gida ya rage sai Mami da Hajiya Mama, wadda ita ma kwararrun likitoci ya debo mata har gida suke kula da ita. Don ta ce ba shegen da zai kaita asibiti, ajalinta take jira ya risketa a daki cikin bautar Ubangiji, ba akan gadon turawa ba.
Imam kan ce da ita,
“Wai ke wa ya ce dake shekaru sune mutuwa? Kina ina jarirai ke mutuwa su bar tsoho? Kina ina ‘ya’yanki masu kuruciya suka mace suka barki? Kina ina Da yake mutuwa a cikin uwarsa tun kamin ya zo duniya???
Don haka don Allah don Annabi ki saurara mana da zancen mutuwa haka nan muji da abin da ya dame mu”.
****
Mami da Hajiya Mama rayuwar dadi da kwanciyar hankali suke yi. Cikin ‘yan watanni Hajiya Mama ta yi kwari tana takawa da kafafunta ta shiga ko’ina a gidan aljannar duniyar da suke ciki.
Lallai gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, idan suka tuno gidansu na Kaduna. Aikin Mami a gidan kawai shine GIRKI, ta dafa musu abincin da suke so traditionally (a gargajiyance) ba kwabe-kwaben Turawa ba.
Tuni an sallami kukun Imam. Duk da yanayin kayan abincin akwai bambanci babu irin abincin Hausawan da bata iya sarrafawa da nasu kayan abincin.
Lokaci-lokaci Imam kan kaita ta ga Safah wadda a hankali take samun sauki. Duk wani ciwo na jikinta ya kame sai tabo, kumburin kanta saboda buguwa ya sace, fuskarta ta sabe.
Kasusuwan kafarta ne basu gama daidaituwa ba. Cikinta watanni takwas ya fito kuru-kuru cikin dogayen rigunan da ake sa mata tana daga kwance, yana ta wutsilniyarsa a dalilin good anti-natal care da yake samu.
A lokacin ne suka soma koya mata tafiya da karafa. Safah na ganin Imam da Mami ta kuma san a asibiti suke na jar fata, amma bata san ina ne ba. Wa ya kawo ta? Yaushe Imam ya dawo? Ina Lamido? Tambayoyin da take yiwa kanta kenan cikin zuciyarta amma ba ta taba furtawa ba.
Iyakacinta da Imam,

“Ya kike jin jikin? Mobement din baby fah?”
“Alhamdulillahi, yana ta motsi”.
Daga haka sai ido. Ya kalleta ta kalle shi, ta kau da kai ko ya kau da kai. Ba cewa ta tafas bayan wannan.
Amma tana hira da Nurses dinta sosai, musamman Mrs. Wilson wata Baturiyar Moscow, aiki ya kawo mijinta Dr. Wilson asibitin, ita din kuma ta yi karatun Nursing a nan Los Angeles da ta gama ya samar mata aikin take yi. Za su yi shekaru daya da Safah.
Yau ma Mrs. Wilson ce ke koya mata tafiya da sanduna, dai-dai lokacin da motar Imam ta sawo kai asibitin.

Mami na zaune a gaba, tun daga nesa Mami ta fara fara’ar ganin Safah na tafiya. Ta fito dauke da kwandon kayan abinci, Imam ya karbe ta suka doshe su, bakin Mami ya ki rufuwa.
Imam tsayawa ya yi jikin motarsa ‘Ford -Mustang’ yana kallon Safah ta cikin glasses din idonsa farare sol, a lokacin da Mami ta cika tambulan da kunun gyada tasa mata a baki.
Babu abinda ya canza na halittarta daga yadda ya santa, kullum kuma kamar kara mata kuruciya ake. (She is looking fresh and youthful). Tun dawowarsa bai taba yi mata kyakkyawan kallo ba sai yau.
Yarinyar da ta juya duniyar rayuwarshi, ta sanya mishi bakin cikin da babu wanda ya taba sanya mishi ko da misalinsa, amma matsayinta a zuciyarshi daidai da rana daya bai taba canzawa ba.
Yarinyar da ta hana mishi dandana ni’imar da Allah Ya yiwa aure. Ita tana can ta yi aurenta da wanda take so, suka ci kuruciyarsu, har ga rabo Allah Ya basu.
A duniya akwai wanda ya karya zuciyarsa kamar yadda Safah ta karya?

Hankici yasa ya dauke hawayen da suka tsatstsafo a idanunsa yana mai tausayin kansa. Bai da Uwa, bai da Uba, baida Alh. Aliko, bai da sa’a a soyayyah…..!!!.
Mami sai neman motar Imam ta yi a filin wajen ta rasa, ba ta ga kuma lokacin da ya tafi ba, tunda motar ba ta da hayaniyar komai.
Mami da dare ya risketa a asibitin, sai public bus ta bi ta koma gida. Tana kakabin ina Imam ya shiga babu amo babu labari.
Da ta iso gida Hajiya Mama ma cewa ta yi ba ta ganshi ba. Amma ta ji shigowarsa. Kusufa-Kusufa Mami ke lekawa na gidan har lambu da swimming pool babu Imam.
A wani dan karamin daki dake matsayin rest room dinsa ta same shi ko kayan jikinsa bai cire ba. Ya yi barci kamar barcin mutuwa, kwalaben giya birjik ga wani irin amai da ya sharkaba a gefe, da shishar wiwi da lofe ta Turawa.
“Innalillahi wa’inna ilaihir raji’un!”

Kawai Mami ke ambato, tareda toshe hanci. Da sauri ta koma dakinta ta rufe, ta jingina da kofar tana hirji da kokarin daidaita numfashinta.
Ya kamata tuntuni ta yi tunanin wasu muhimman al’amura tun dawowar Imam gida, amma ba ta yi ba sakamakon wadannan al’amura marasa dadi da suka yi ta faruwa da su.
Mene ne ya hana Imam yin aure? Mene ne ya lalata suffarsa da walwalarsa alhalin yana cikin wannan daular rayuwa? Idan neman mata yake tunda suka zo ba ta taba ganin alama ba, idan neman maza yake babu wanda ya taba biyo shi gida nemansa, daga gida sai ofis babu inda yake zuwa. Duk wanda yake mu’amala dasu mutanen kirki ne masu iyali.
To me ke kuenching physiological need dinsa?
“Giya!”.
Zuciyarta ta bata amsa a hankali.

Mami ta dauki abin shara da abin kwashewa ta nufi dakin hutawar tasa. Ta share aman, ta kwashe kwalaban, ta bude dan karamin firjin ta gansu a jere kala-kala masu karshen tsadar duk ta kwashe su ta kai bola.
Ta dawo tana goge dakin da omo mai kamshi saboda hamamin da karnin aman da yake yi.
Tana cikin gogewar Imam ya farka. Bai fahimci komai ba, don garau ya tashi babu damuwar komai a tare da shi.
Ya ce, “Haba Mami, wannan ba aikinki bane, ki bari Suzana ta zo ta yi mana”.

Mami kanta na kasa sai a lokacin ya ga hawaye ke diga daga idonta. Ba ta kuma bari sun hada ido ba ta dauki bokitin omon ta fita.
Sai jikinsa ya yi sanyi, ya soma wani tunani daban kuma. (A asibiti ya baro ta, ya zo ya yi ta drinking).
Ya kama kansa da hannayenshi biyu dake neman tsagewa. A fili ya ambaci “Lahaula wala kuwwata illabillahil aliyul azeem!”
Da gudu ya bude firjinsa ya ga wayam! Bari kawai ya je ya amsa laifinsa, ya ba ta hakuri. Ya yi alkawarin daga yau ba shi ba giya, insha Allahu!!!. Sai dai soyayyah da kishin su halaka shi.
Ya murda kofar dakin Mamin cikin sallama, tana sallah bisa sallaya, sallar da ita kanta ba ta san adadin raka’o’in da take yi ba, addu’a kawai take cikin sujjadarta a fili.

“Ya Allah bani na haifi Imam ba, amma amana ne a gareni. Fushina da shi hakika za ka iya kama shi da shi. Na roke Ka, Ka sassauta fushina a kansa, ka daidaita rayuwarshi kada ka kama shi da laifin da ba halinsa ba, zuciya ce ta ingiza shi.
Ya Allah wannan bawa naKa maraya ne, mai neman kauna da tausayin iyaye. Ina kaunarsa ina tausayinsa yadda harshena ba zai iya bayyanawa ba.
Ina rokonka ka bani ikon kawo farin ciki cikin rayuwarsa, ka fahimtar da shi zuciyar Safah a kansa……..’

Iya abinda ya iya ji kenan, sai ya yi baya ya kulle kofar ya koma dakinsa. Ya bude firjin babu giya, sai ya zaro taba ya soma tada gajimare.
Mami ta yi fami a kan gyambon da ake fama da shi.
Me ya kawo ambaton Safah cikin addu’arta? Wato Mami ta fahimci har yanzu yana SON Safah? Soyayyar Safah ce ta tsunduma shi a gurbatacciyar rayuwa???.
Me take nufi da Allah Ya fahimtar da shi zuciyar Safah a kansa? Tana nufin Safah na son sa? A’a, ba zai taba yarda ba. Muguwa ce, azzaluma ce, kanta kawai ta sani. Ba ta da tausayi ko miskala zarrah.
Ban da ta zame masa dole kuma mijin ya rasu, babu abin da zai sa ya taho da ita, balle ta dawo cikin rayuwarshi. Ta je can ta karata da wanda take so.

****

Washegari bai nunawa Mami komi a fuska ba, gaishe ta kawai ya yi, ya yi kalacin da ta shirya masa na funkaso da miyar kaji da kunun tsamiya.
Bai ce komi ba ya wuce ofis, zuciyarsa na cewa ‘Kaddara Mami an amsa addu’arki, babu ni babu GIYA, insha Allahu. Safah ko ita ta yi saura a ‘ya’ya mata bata da abin da za ta birgeni da shi, ba abinda zan yi da ita. Kwanan nan zan yi aure insha Allahu kafin ta fito daga asibiti.

“Auren huce haushi????”
Wani bangaren na zuciyarsa ya yi gaggawar halarto da wannan tambaya.
Tsaki ya yi, “Koma na mene ne zan yi aure, budurwa ba bazawara ba wadda wani can da bai san darajarta ba ya gama kwashe alfarmar ta”.
Mami ba ta gayawa Hajiya Mama wannan zance ba, ta barshi a ranta tana ta ci gaba da addu’a.
Sunyi waya da Zahraddeen a ranar yake tambayar lafiyar Safah, ya kuma gaya mata an yiwa Daddy shayi (kaciya), an kuma yiwa Fati Birthday one year.
Yanzu haka kuma suna nan suna ta shiri za su koma Ibadan daga Lagos zasu yi wani aiki da refinery na Ibadan.
Mami ta yi fatan alheri cikin wasa kuma ta ce, “Kada a kai min maigida garin Yarabawa ya taso da Yarabanci. Ita wannan kodaddiyar dai a tafi da ita”.
Zahraddeen na dariya ya ce da Mami, “Ai kishiyoyin naki yawa garesu, wannan scan din ma ya nuna baby girl ce”.
Mami na jin kunyar wai wani cikin Marwah ke da shi amma shi Zahraddeen ko a jikinsa don idan yana tare da Mami ji yake kamar Yayarshi.
Baya iya boye mata komai. Yanzu ma wata muhimmiyar magana yake gaya mata. Ya nutsu sosai ya ce.
“Wallahi Mami wani al’amari ne ya sawo kai, wato Deputy President abokin Lamido………”
Mami ta ce, “Sulaiman?”

Ya ce, “Haka sunan yake, Sulaiman Yakasai. To ya yi tattaki ya taddani har Lagos da wata muhimmiyar magana”.
Mami ta ce, “Uhm!”
Ya ci gaba, “Ya zo ne yana kamun kafa dani in kawo shi gareku yana son auren Safah da zarar ta haihu idan Allah Ya bata lafiya”.
“Wata sabuwa!” In ji Mami.
Ta ce, “Zahraddeen bari zancen nan ka ji, ni kadai na san halin da nake ciki a yanzu…….ka bashi hakuri domin mutumin kirki ne, mun kuma yaba da kaunar da yake yiwa Lamido.
Zamu ci gaba da yi mishi addu’a Allah Ya saka mai da mafificin ALHERIN Sa. Amma Safah bazata yarda ta aure shi ba tana ganin Imam single.
Shima kuma ba zai yarda ba kada in je ya halaka kansa a banza. Sai dai zuciyoyinsu sun ki daidaito, kowanne wani tunani ne daban a ransa game da dan’uwansa bayan kuma duka abu guda ne wato, soyayyah.
Shi Imam gani yake Safah ba ta son sa, bai san cewa in akwai wanda Safah ke so a duniya bayanshi yake ba.
Kuskure ne da kuruciya kawai ta yi. Yanzu abinda ke gabana shine Allah Ya daidaita su kowa ya huta nima in dawo gida in samu miji in yi aure…..”
Ta share hawaye da habar zaninta

Zahradeen ya girgiza kai, lamarin su abin tausayi ne. Allah Ya yi musu arzikin da su kansu basu san iyakarsa ba, gashi kuma Yana yi musu jarrabawa kala-kala wadda sai mai karfin imani ne kadai zai iya jurewa.
Da kyar ya ce, “Mami addu’a zamu ci gaba da yi Allah Ya warware mana, ita kuma Allah Ya bata lafiya.
Ga ‘yar’uwarta ma ba ta cikin kwanciyar hankali tun tahowarku, hankalinta ya gaza kwanciya, cewa take idan an ce mata Safah tana jin sauki ba a taba hadasu a waya sunyi magana ba. Wai idan ita ma ta rasu ne ake boye mata, to ba a son ta.
Ta ce Ibadan din ma ba za ta bini ba sai dai in tafi da Anisa ita nan za ta taho”.
Mami ta yi murmushi ta ce, “Safah ta Marwah, me za ta zo ta yi mana? Ta zauna ta kula da ‘ya’yan da Allah Ya bata, ta ji kansu kamar yadda aka ji kanta.
Ta yi bautar aure wanda shine bautar Ubangiji. Ga kishiya ta gari Allah Ya bata tana binta kamar ta yi mata sujjadah. Ga albarkar Uwa irin Inna Binta, ga gwarzo kuma sadaukin masoyi. Ka gaya mata wannan. Safah za ta kirata kwanan nan”.
Cike da murmushin jin dadin yabon da ya samu daga surukarsa, Zahraddeen ya aje wayar Mami, ya juya ya dubi matarsa Marwah dake gefensa a kwance tana jin duk abinda suke tattaunawa shi da Mami, kasancewar murya a waje (handsfree) suke maganar.
Ita ma sai da ta murmusa domin kalaman Mami sun sanyaya mata rai. Ta mike ta shige cikin kirjin Zahraddeen, gwarzo, sadauki in ji Mami. A hankali ya yi mata kyakkyawan masauki a kirjin nasa, duk da tirtsetsen cikinnata da ke tokare shi.
****

IMAM
Ga Imam can ya tafi neman aure a wani kauyen Ingila Banbury. Akwai wani abokinsa Joseph da suka yi karatu tare dan asalin kasar Kenya, akwai wata kanwarsa Regina da ta like masa lokacin suna karatu sai ya aure ta.
Ba irin wulakancin da bai yiwa Regina ba amma har yau da take da shekaru talatin da shida bata yi aure ba saboda ya ki auren ta. Tafi kama da black Americans fiye da Kenyanz, domin a nan iyayensu suka haife su.
Ya hada kaya cikin karamar troller wadanda za su yi masa kwana uku. Ya ce da Mami zai yi balaguro na kwana uku. Mami ta kura masa ido ta kasa karanto komai cikin kwayar idanunsa.
A sanyaye ya yi kasa da kansa, don har yau kunyar Mami ba ta sake shi ba tun ranar da ta kama shi drunkerd, red-handed. Ta juya ta ci gaba da abinda take yi idanunta cike taf da kwallah.
Domin dai tunanin Mami ya ba ta zai yi tafiyar ne inda ba za ta sa masa ido ba ya kwankwadi barasarshi kwana uku, don ta tabbata a cikin gidan ya daina kam.
Imam ya karasa gabanta ya kai gwiwoyinsa kasa,
“Ki yafe min Mami ki yi min kyakkyawan zato. Na san abinda kike tunani, wallahi ba haka bane. Tafiyar da zan yi alheri za ta zame mana daga ni har ku, insha Allahu”.
Ta yi saurin kama hannunsa ta mikar da shi tsaye,
“Ina za ka je?”

Ya ce, “Banbury”.
Mami duk yawonta a kasashen duniya ba ta taba jin wani gari Banbury ba.
Ya ce, “Ba lallai ki san garin ba Mami, kauye ne”.
Bata takura da bincike ba ko son kure mutum, tunda bai fadi abinda zai kai shin ba, baya bukatar ta sani ne.
Ta ce, “Allah ya kiyaye hanya”.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *