Chapter 9: Chapter 9
Sai zuciyar tata ta bada amsa da cewa, “A’a, ba za ki iya ba, saboda shine jigon rayuwarki a yanzu, uba, Yaya, guardian, kuma masoyin da kike so fiye da son da kika yiwa duk wani da namiji a duniya.
Ba lokaci daya kika so shi ba kamar Zahraddeen da Lamido, kin so shi ne a hankali, a dalilin hakuri da juriyarsa a soyayya, jajirtacciyar zuciya mai son farin cikin ki.
Ya sake ki ne a bisa bukatar kanki, don ki yi rayuwarki freely wadda babu takura a zuci ko soyayyar tirsasawar iyaye kamar yadda kika ce. In yaso shi ya yitashi rayuwarsa a haka, meaningless! Idan har hakan zai sa ki yi farin ciki.
Bai kamata ki ga laifin Imam ba a kan ko me ya yi miki a yanzu. Ya ma saka miki da ALHERI ne tunda ke da tsiya kika saka masa soyayyar shekara ashirin da ya yi miki.
Ya kula da lafiyarki da aljihunsa da lafiyarsa, ya so abinda kika haifa da waninsa kaunar da bai iya boyewa. Ya ciyar, ya tufatar da ita, ba don bata da shi ba, sai don yana ganin it’s his duty yin hakan (hakkinsa ne). Tunda cikin gidansa take rayuwa.
“Idan baki farantawa Imam ba, baki gode masa ba, to don Allah ki daina kuntata masa, ko da ba zai aureki ba”.
Wani bangare na zuciyar ta ya nasihantar. Jikinta ya mace murus, ko carbin da take ja ta kasa.
Daidai lokacin da Mami ta yi sallama ta shigo mata da nata kalacin, tunda itama ta ki fitowa.
Ai Shukrah na ganin Mamanta ta soma zillo daga bayan Mami tana kiran “Mummy-Mummy”.
Ta mika hannu ta karbota daga bayan Mamin ta rungumeta tana ta yi mata gwalantunta wai Mami bata bata nono ba, tana ta kuka amma ta ki bata.
Dukkansu dariya suka yi mata. Su uku suka yi kalacin, sannan Mami ta ce da ita,
“Ki canza riga ki je ki duba Imam, yana can kwance babu lafiya yau ko fita ba shi da niyyar yi”.
Ji ta yi gabanta ya yi wata irin mummunar faduwa, ta dan fiddo ido har da dafe kirji ta ce, “Amma shine baki gaya min ba tun dazu Mami da kika shigo?”
Ta ce, “Na bari ne ki karya kumallo don mai yiwuwa in na gaya miki ki ce abinci za ki ci, tunda ba damuwa kika yi da shi ba”.
Ta ce, “Haba Mami, ai lafiya na gaba da komai. Kuma na ce miki ban damu da shi ba Mami? Shine dai bai damu dani ba”.
Mami ta mike tana hada tangarayen tana fadin, “Oho muku, ku kuka sani, ki hanzarta don da alama yana jin jiki”. Ta fita rike da hannun Nadiya.
Ai Mami na bada baya ta janyo Abaya ta zura a kan rigar barcinta. Ba ta sani ba ma a bai-bai ta saka ta zura silipas ta fice har tana tuntube.
Karo na farko da kafarta ta taka master bedroom din Imam tun zamanta a gidan.
Ba kyawun dakin ne ya girgizata ba, a’a, dukiyar da aka kashe wajen zuba kayan alatun dake cikin dakin.
Katifar ta ruwa ce wadda ko allura bata huda ta, labulaye farare kal masu kauri saboda sanyi. Furnitures din ma farare ne kal da ba ta taba ganin irinsu ba.
“Ko wa ya zabo masa? Oho!” Ta ayyana a ranta.
Ta kai kallon ta ga gabas maso kudu na dakin, wani tafkeken hoto ne window size cikin frame, in ba ta manta ba hotonta ne ranar da suka je mishi bikin kammala kiaratu a Loughborough, a lokacin tana youngish Safah ba yanzu da ta zama Mummy ba.
Lallai soyayya bata tsufa, ni kaina ban yarda ba da, amma yanzu na yarda. Safah da Almustapha kallon-kallo kawai suke yi, idanun kowanne ya raina fata cike da tausayin dan’uwansa.
As a proffesional Medical Doctor, a take ta gano cewa ba wani ciwon hakori a tare da shi, kawai (he is helpless) a cikin soyayyar da yake yi mata.
Tunda Mami da Hajiya Mama duk sun ki shiga al’amarin. Mami na bin bayansa kan cewa Safah ba ta damu da shi ba, shi yake kidansa yake rawarsa, ya fita hanyarta kawai.
Yayin da Haj. Mama ke goyawa Safah baya, tun ranar da ya yi kuskuren furta abinda ya furta, cewa ta yi ya je ya kawo wadda ba Bazawara ba, amma musulma mai daura zani ko ‘yar waye babu ruwanta za ta yi fatan alheri.
Ita kuma Safah tunda ta warke, ta kuma yaye ‘yarta, to ya mai dasu gida ta samu Bazawari dan’uwanta ta aura wanda zai kalleta da daraja tunda darajarsu daya.
Idan kuma ta kara fusata sai ta ce, “Shi din banza? Me yake da shi banda mota? Safah (Deputy president) ke son aurenta a zawarcen nata, don sun takawa maganar birki ne.
Imam dai ya yi dana sanin wannan furuci nasa ya fi sau shurin masaki, domin Hajiya ta dauka da zafi, tsoho da korafi kullum yi take, to an ce magana zarar bunu ta riga ta fita.
Tsayin mintuna biyar suna kallon junan. Kafin Safah ta sauke idanunta kasa. A kasalance ta karasa gaban gadonshi ta zauna a bed-side ta ce.
“Ya Imam, Mami ta ce baka da lafiya ko?’
Daga mata kai ya yi, sai ta dawo kusa da shi ta zauna ta ce, “Bude bakin in gani”.
Kamar wani rakumi da akala sai ya hangame bakin. Ta yi amfani da hasken wayarsa ta lelleka ta dudduba ba ta ga komai ba, sai lafiyayyun hakora garai-garai dasu kamar kankara. Da alama ma ba da jimawa ba likitan hakori ya yi musu flushing.
Ta ce, “Ni kam ban ga wani hakori mai ciwo ba. You habe healthy teethes. To ya ya kake jin ciwon?” Sai ya dauki hannunta ya dora a santar zuciyarsa, still bai yi magana ba.
Babu shakka ta ji irin bugun da zuciyarsa ke yi a kowacce dakika, wadda ba ta raba dayan biyun hawan jini ko alamun kamuwa da ciwon zuci a dalilin damuwa da kuntatawa zuciya, wajen danne mata abinda take so, ta hanyar sanya karfi (by force) ba da lallashi da maslaha ba.
A yau Safah ta nemi jan ajinta da miskilancinta da ma JI DA KAN ta rasa, lallashin Imam take da harshe mai taushi da kalami mai sanyi.
Mai neman kuka ne aka jefe shi da curin kashin awaki. Sai kara sangarcewa yake yi yana kara gigitata.
Har brush ita ta yi mishi, ta zuba mishi mouth wash a bakin ya kuskure. Abincin da Mami ta ajiye a baki take bashi da ‘yan yatsunta.
Ita ta zabo mishi suit din da zai sanya kamar wata amaryarsa cewa take, “Yau har ofis zan raka ka, ni zan tuka ka. Don Allah ka daina kwanciya zuciya mara juriya tana danne ka.
MAZA gwagwarmaya suke da ita basa barinta ta yi nasara a kansu. Ni na san Ya Imam mai juriya ne a kan komai, idan ya zauna soyayya ta rafke shi a daki ina na ga karfin gwiwar kiransa da BABBAN GORO? Sai dai in ce KARAMIN GORO!”
Girgiza kai ya yi bai yi zaton tana magana haka ba. Tana da karancin furuci edcept for something that is bital. Babu mamaki itama soyayya ce ta bude mata baki.
Ya ce, “Kin ga gadon barcina yau kam, dole ki ce ina soyayya. Yo soyayya har an fiki? Dubi rigarki”.
Ta yi saurin kallon rigar tata, a bai-bai ta sanya ta sabida gigicewar an ce bashi da lafiya.
Ta tsuke baki ta yi mishi kallon nan da take mishi ta kashe bakinsa. Kasa yin magana ya yi amma ya damke hannunta ya runtse ido.
Ta ce, “Haram!”
Ya yi saurin sakin hannun nata. Ya ce, “Na tuba! Na bi Allah wanda Ya halicce ki Ya halicce ni, ya sanya soyayyarki a zuciyata”.
Ya mika mata hannun daman shi,
“Kin amince mu manta komai? Mu sake zama cikin inuwar aure a KARO NA BIYU? Mu karasa sauran guntuwar rayuwar da ta rage mana? Mu raini SHUKRAH-NADIYA, kamar tare muka haife ta???’
Daga kai kawai ta yi ta mika masa nata hannun. A yayin da hannun nasu ke sarke. Sai ya ce,
“Allah Ya ji kan LAMIDO! Ina yi miki ta’aziyya. Na samu labarinsa sosai a bakin Zahraddeen, ina rokonki alfarmar ki so ni ko da rabin-rabin son da kika yi masa…..”
Hannu ta kai ta toshe masa baki, kawai sai ta fada jikinsa tana kuka.
“Yaya Imam ban san da bakin da zan gogewa zuciyarka wannan zargin na rashin so daga gareni ba.
Na so ka sanda ban taba yiwa kowa a rayuwa ta ba. Amma abin haushin shine, ta baya ta rago na yi, na fara sonka ne a yayin da zuciyarka ta riga ta yi amanna da cewa bana son ka.
Wallahi na fara sonka ne so na soyayya a ranar da zamu rabu. Shekaru takwas na kwashe ina korar maza, na kasa son kowa, zuciyata da kwakwalwata suna gaya min wata rana za ka dawo gareni amma baka dawo din ba.
Na yi aure da Lamido don in huta da fadan Mami da gorin Hajiya Mama, amma ba don na gaji da jiranka ba Ya Imam. Ko a ranar da na bude ido na ganni gidan Lamido na tunaka, na yi dakacen da ba shi da amfani…….
A hankali na gane Lamido is a nice person, sannan soyayyar da yake yi mini ba mai fassaruwa ba ce. Sai na so shi a hankali, na kuma fahimci cewa jiran tsammanin warabbuka bai dace da diya mace ba.
Ko kai ka zauna da Lamido na awa daya sai ka so shi, saboda halayensa masu nagarta da karfin addininsa. Sai kuma kaddarori iri-iri suka yi ta fada masa wadanda duk masoyinsa dole ya tausaya masa.
Lamido ya sha wuya a hannun matarsa saboda ya aure ni (ta gaya masa komai). Har ta zamo sanadin ransa.
Don haka dalilai da yawa ne suka yi sanadin soyayyata ga Lamido, amma ba don na daina tunaka ba. Ko na daina sonka.
Ina rokon ka da ka goge wannan zargin rashin son da kake yi mini. I LOBE YOU BERY BERY MUCH….!!!”
Sai ya kankameta suka yi ta fadawa juna sirrin zuciyarsu, kowanne maganganu ne na tsohuwar soyayya yake korawa dan’uwansa. Wadda a yau ta zamo sabuwa dal! A cikin ledarta.
Tun Mami na jiran fitowar likitar da hakorin da aka banbaro har dai ta yanke shawarar zuwa ta ga halin da suke ciki ko ciwon ya yi (worsen) ne (ya munana) a tafi asibiti tunda ba kayan aiki gare ta a nan ba.
Da budewarta, da shigarta da fitarta duk basu sani ba. Ta koma falo ta zauna ta zuba tagumi tana mamakin yaran zamani dake yiwa Ubangiji abinda suka ga dama.
Tunani ta yi ko ta dauko bulala ne taje ta yi musu sittin-sittin ne? ‘Yan banzan yara suna son juna amma suna wahalar da zukatansu, ita ma suna wahalar da ita.
Gara kawai ta yi maganinsu, watakila bulalar ba ta hau kansu ba, tunda ba ta ga komi ba bayan runguma. Ita kuma ba ta san hukuncin runguma a musulunci ba.
Tana nan zaune ta saka ta warware duk ita kadai, sai gasu sun fito Safah rike da brief case da mukullin mota.
“Mami zan dribing Ya Imam to office, jikin bai gama murmurewa ba”.
Ta balla mata harara, duk sai jikinsu ya yi sanyi.
Ta ce, “Ku zauna mu yi magana”.
A gabanta suka zube dukkaninsu.
Sai ta mike taje ta taho da Hajiya Mama, suka zauna dukkaninsu. Ta ce, “Hajiya zauna sosai ayi maganar nan a gabanki.
Yaran nan sun rainani, basa ganin kimata, sai tamaula suke min da hankali don sun ga babu Daddy…..”
Nan ta soma kuka. Hajiya ta ce, “Yi hakuri Zainabu, fitar hawayenki a kansu musiba ce ba karama ba garesu. Gaggauta ki yafe musu kome suka yi miki kafin mala’iku su rubuta”.
Mami ta ce, “Na yafe musu, amma wallahi yau za a yita ta kare ba za su sa min hawan jini ba in ji da abin da ya dame ni”.
Hajiya ta ce, “To sun gode. Yanzu me aka yi?”
Ta ce, “Shi ya ce ba sonta yake ba, ita ta ce min Sulaiman ta zaba ta aura tunda ba sonta yake yi ba. To mene ne dalilinsu na yin soyayyar shan minti?”
Ai ba Safah da Imam kadai ba, hatta Hajiya Mama muguwar kunya ta kama ta. Su kuwa kara bajewa sukai a kan kilishi kamar su ce da kasar ta tsage su shige, ko dagowa sun kasa yi. Harshensu ya sarke balle ya furta kalaman kare kai ko jumlar “ba haka bane”.
Hajiya Maama ta ce,
“Zaynabu kai! Wace irin magana ce haka mara dadin ji? Na shaidi yaran nan, wallahi ko Imam zai yi ba dai da Safah ba, babu wata kyakkyawar alaka tsakaninsu, sai dai ko da su Barbarar tasa, amma ba dai Safah ba”.
Mami ta gaggalla musu harara ta ce, “Gasu nan tambaye su. Me suke yi a daki tun dazu daga zuwa duba hakorin karya? Ra’ayal aini na gansu”.
“In za su yin su wawayen ina ne da za su bari ki gane?”
“Rabu da’ya’yan yau Hajiya, sun fi iyayensu wayo da zallar rashin tsoron Allah. Don haka na gaji, jibi insha Allahu za a daura aurenku in ya so ku kashe kanku don soyayyar ko kiyayyar ko sakin rashin hankali irin wanda ka saba ka gudu a nemeka a rasa.
Duk shirin da na ke yi da kai daga yau na daina. Sannan ba ni kara kwana uku a kasar nan sai ka maida ni gida, in ba haka ba ku ga tsiya irin tawa, don wallahi bulalar mazinata zan muku tunda nan kasar arnan basa bin shari’ah….” Ta ci gaba da kuka.
Ji da Imam ya yi Mami ta dauki zafi sosai, kuma ta soma sakin layi. Sai ya motsa kafarshi ya ce, “Mami ba fa haka bane, wallahi-wallahi ba haka bane. Ki yarda da kanki da tarbiyyar da kika bamu.
Kada Allah ya bani tsawon rai da lafiyar da zan nemi jinina da kazantacciyar mu’amala. Ban taba ba, ko da can balle yanzu da na mallaki hankalin kaina.
Babu komai tsakanina da Safah sai rashin fahimtar juna, wadda alhamdulillahi a yau mun gano inda matsalar take, we only misunderstood each other, but today we bury the hatchet (mun manta baya).
Cikin kyautayi da alfarmomin ku da basa karewa a garemu muke mika ban hakuri gare ki a bisa laifuffukanmu da kurakurenmu.
MADALLAH…. dake wannan Uwa da ALLAH Ya bamu, ma’abociyar YAKANAH da TAKAWAH. Duk wani duty na UWA -MAHAIFIYA, a garemu kin cika shi.
Ki yi farin ciki, cikin ‘ya’yanki babu lalatacce ko wanda ya karkace daga tarbiyyarki, sai KUSKURE, wanda babu dan Adam din da yake sama da aikata shi”.
Jikin Mami ya yi sanyi, ta dago Safah dake ta kuka ta rungumeta a jikinta tana share mata hawaye da tafukan hannayenta.
Hajiya Mama banda albarka babu abinda take sanya musu.
Shukrah ta tako dabas-dabas da tafiyarta da ba ta gama yin kwari ba, ta hau jikin Mamanta itama tana taya Mami sharen hawayen, tana fadin
“Mami ce ko? Tofo in rama miki”.
Sai ga Safah tana dariya. Shukrah na yi, Mami na yi. Yayin da Babanta ya dauketa daga cinyar Maman ya dorata a kan wuyansa.
“Shukrah-Nadiya, Uwa fa bata fi Uwa ba, nima ina son Uwata yadda kike son taki, ba zan bari ki doke ta ba”.
****
Aiyaka fasahar da Allah Ya baiwa Almustapha Zubair Dan-Kasa, ya yi tunani iyaka tunani, bincike iya bincike kan hanyoyin da zai bi ya maido ‘Dan-Kasa Motors’ gida Nigeria amma ya rasa.
Ci gaban namu har yau bai zo nan ba, abin tambayar anan shine, yaushe Nigeria za ta ci gashin da Allah Ya bata?
Kasa ce mai cike da albarkatun kasa musamman man fetir, “the problem is with our leaders, they don’t know how to harness the resources abailable, in ka ga talaucin da ake yi a cikinta (North and South) da dilapidated infrastructure sai ka tambayi kanka, ina shuwagabanninmu ke kai arzikin kasar Nigeria?”
Wannan ce tattaunawar da suke yi shi da Saifuddeen Aliyu Dambatta, a wani restaurant da ke cikin masana’antar ‘Dan-Kasa Motors’ dake Wilshire, Blbd, CA, cikin birnin Los-Angeles.
Saifuddeen ya kai tambulan din sassanyan lemun inibi bakinsa. Ya kurba ya aje akan gilasahin dake gaban su. Ya ce,
“An ce an bamu ‘yancin kai, amma ba a daina bautar da al’ummar mu ba.
Mun fi Bature fasaha amma bamu ishi shuwagabanninmu kallo ba, balle su ankara da muhimmancin matasanmu su tallafa musu su samu ingantaccen ilimi.
In ka ga dan Nigeria na karatu mai kyau, to tabbata aljihun iyayensa da motsi, motsin talaka kuma ko oho. Da ya yi, da kar ya yi, duk daya.
Imam ya ce, “Za ka sha mamaki in ka ga bakaken fatar dake aiki a kamfanin nan. 40% Nigerians ne. Idan suka soma zana maka mota wallahi ta fi ta wani Baturen.
Ba zan taba mantawa da wani hazikin Basakkwace ba da muka yi aiki da shi a GM, (general motors), shine ya yi designing din motar nan da ta girgiza Turawa, wato ‘Chebrolet’.
Gashi nan sun rike shi, Nigeria bata san ana yi ba. Banda ‘yan jarida da suka zakulo shi suka fadawa Hausawa, wallahi da ba zamu taba sanin da shi a Amurka ba”.
Haka suka yi ta tattauna al’amarin, har lokacin tashi ya yi suka nufo gida. Bayan sun ci delicious din da Mami ta shirya musu, nan falon suka zauna suna sauraren labarun duniya suna ci gaba da tattaunawa.
Shukrah ta tako ta zo ta rungume Babanta, kafin ya dauke ta Saifuddeen ya riga shi.
“What a kissable toddler!” Ya fada yana kissing goshin ta. Imam yayi dariya.
Uwar ta fito, ta yi shiri cikin atamfa Ghana wad koriya shar da mayafin da ya dace da ita, da mukullin mota a hannunta don yanzu Imam ya sakar mata mara, nan ta tadda su.
Ta yi smiling ganin Shukrah na ta sharo masa labari.
Ta ce, “Barka da dare, Yaya Saifuddeen ina Rukayyah?’



