Chapter 1: Chapter 1
JAMILA UMAR TANKO DA MA NI CE
HAKKIN MALLAKA(M): SHEKARAR BUGAWA:
NA’URA MAI KWAKWALWA:
FADAKARWA:
Wannan labarin na gaskiya ne, kuma an yi shi ne da yarda wadanda abin ya shafa. Idan waniya ji labarin ya yi kama da nasa/ko nata, katari aka yi ba da shi/ita ake ba.
GARGADI:
Ba a yarda wani ko wata ya wanki wannan labarinta kowacce siga ba, tawajen juya shi zuwa fim haka ban yarda a rubuta wannan liittafin a ‘social network’ba: face book ko whatsapp, ba Duk masu tare da izinin marubuciya ba. ma bada rubutawa ba da saninmu suke yi ba kuma bada yawunmu ba. Yin haka za’a fuskanci fushin hukuma idan kuma aka yi a boye ban sani ba Allah Ya na gani, dan ba karamin kashe mana kasuwar littafi ake yi ba. Dan Allah jama’a a dinga kula da hakkin mutane a kiyaye.
DA MA NI CE…
SADAUKARWA: Bans W chash on ide Amina Hassan Abdulsalam (AHA) del i svinsw
bed fy sie isted
TUKUICI:
sw strays ad
Daukacin dukkanin’yan arewa masu kishin arewa. Fatan Allah Ya bawa kasarmu zaman lafiya.
GODIYA TA MUSAMMAN GA: Sani Manaja Misau Hauwa’u Umar Gajo (Yelleman) Jibrin Umar Tanko
DA MANI CE…
BABINADAYA:
LITININ KARFE TAKWAS NA SAFE
KANO
Wata Zankaɗediyar mata ce ta gifta a cikin wata tsaleliyar mota, akan titin Nasarawa G.R.A, Kano. Hakika matar nan ta hadu, ga kudi, ilimi, ga kyawu duk daga Rabbil samawati.
Malaika a zaune take donono a bayan Babur ana ta zuga gudu da ita, amma bata cikin hayyacinta, bata kara sanin inda hankalinta yake ba tun sanda ta yi arangama da wannan Zankaɗediyar matar da ta gifta ta gabansu a cikin tsaleliyar mota.
Ta zama tamkar mutum-mutumi, ta daskare kamar kankara, ji take tamkar ba’a cikin wannan duniyar take ba. Tunani ya wurga ta wata sabuwar duniya, dan haka bata sake fahimtar abubuwan da suke faruwa a gabanta. Jirgin tunani ya lula da ita duniyar gajimare, ta
hango ta har ta zama waccan matar itama ta shige cikin tsaleliyar mota tana juya sitiyari. Malaika bata farfado daga duniyar tunani ba sai da ta ji muryar mijinta yana kwaɗa kiran sunanta. Ta yi firgigit ta dawo duniyar da take sai a lokacin ta ga ashe har sun shigo cikin sibitin Nassarawa. Da ta ganta a bisa Babur sai ta ja dogon tsaki, ranta ya ɓaci dan ita tunani ya kai inda tayi male-male a cikin jirgin sama ma ba a mota ba.
Kallo daya Shamaki ya yi mata ya tabbatar ciwonta na tunanin‘kanzon kurege’ ya tashi.
Ya harare ta ya girgiza kai, yace “amma kina tare da wahala in dai yanzu ma tunanin nan kike mai kama da mafarki. Na yi miki nasiha, na yi miki fada, na yi gargadi amma duk a banza. Allah Shike azurtawa, Shine mai talautawa, ki gode maSa da Ya baki lafiya Ya rufa miki asiri, Ya baki miji mai zuciyar nema dan ban taɓa barinki da yunwa ba. Ya baki yara uku biyu masu lafiya daya ne mai sikila, amma sai Ya bamu hali da damar jigilar kawo
DA MA NI CE… shi asibiti, Ya bamu kudin siyan magani. Ba ma bara, ba ma rokon wani ya taimaka mana.” ” Malaika ta ji nasihar mijinta tamkar zaginta yake, ranta ya ɓaci, ta turo baki gaba ta kawar da kai gefe, sai kuwa idanuwanta suka dira akan tsaleliyar motar Zankaɗediyar matar nan data hango a kan hanya ashe itama asibitin zata je. Sai Malaika ta shiga murmushi tana yi mata kallo tamkar ta hadiye ta. Tuni ta manta akwai wani bawa a kusa da ita yana yi mata magana.
“Tsarki ya tabbata ga Ubangijin daya halicci wannan mata mai kyau da kudi. Wannan idan ba minista bace to matar minista ce. Zankadi! Ga kyan fuska, ga dirin jiki, ga ilimi. DA MA NI CE….” Malaika ta faɗa a bayyane ba tare da tasan zancen zuci ya fito sarari ba. Yayin da take kallon matar tana murmushin kauna. barari ba. da take att
Sanda matar ta fito daga mota ta zo ta gifta ta gefen aalaika, sai Malaika ta lumshe Laren jikinta. ido ta shaki kamshin “Hakika kudin mai wannan mata a cikin masu ‘yar gayu ce.
“Dama in zama kamarki.” Malaika ta fada cikin rada Shamaki. amma karab a kunnen
Sai ya ji tamkar ya dora hannu a kai ya rusa ihu amma ya daure, ya girgiza kai ya saka hannu a aljihu ya ɗauko kudi Naira dubu daya ya mika mata, shima bata san yana mika mataba har sai da ya nanika mata a hannu, tana can tana kallonMatar nan.
Ya fada a fusace “ki je ki bi layi da sauri, da na yi niyyar jiranki har ku gama in mayar da ke gida, amma naga alamar kin shiga layin da zaki ci gaba da ɓata min rai gara in kin in kin gama ki hawo adaidaita sahu ki dawo gida. ”
Ta kalli kudin ta jujjuya ta yamutse fuska ta ce “a dubu zan yi kudin adaidaita, in
sayi magani in yi cefane? Cafdijam.” Yace “kada ki sayi magani ki kawo min katin da daddare zan saya a kemis din unguwarmu, muna saka ran karɓar albashi yau.” Malaika ta wuce a fusace tana zunkuda goyo tana gunguni, ta ce “Allah Ka raba ni da auren talaka, komai babusai kullum an jira ”
albashi.
”
Shamaki ya daɗe a tsaye yana kallonta cike da takaici. Ji yake tamkar ya dauko hankali da tunani ya cusa a cikin kwakwalwar matarsa. Yana kallonta bata nufi layin mararsa lafiya ba, ta nufi ofishhin da wannan matar ta nufa. Ya san magana zata je ta yi mata idan taga fuska sai ta tambayi lambar waya da adireshi. Ya san ko ya bi ta, ba zai iya hana ta abinda ta yi niyya ba, dan bata ganin girmansa saboda shi talaka ne.Ya ji kwalla ta cika masa ido ya hau kan babur dinsa a sanyaye ya burga ya yi gaba.
da Gudu yake ta shararawa a hanya dan tafiyar ta sa da yawa daga nan zuwa Jami’a (B.U.K) ba karamar tafiya ba ce, ga go slow a hanya kasancewar yau litinin maʼaikata wa da ‘yan makaranta sun firfito. Tabbas ya san ya rasa laccar karfe takwas zuwa tara sai dai ya sami ta karfe tara zuwa goma shima sai ya yi da gaske sannan zai samu. ph
DA MÁ NI CE…
MALAIKASHAMAKI Zuciyar Malaika cike da fargaba ta nufi ofishin da haɗaddiyar matar nan ta shiga amma sai ta tsaya a bakin kofar ta kasa shiga don ta na jiyo muryarta ta na magana da maza likitoci cikin harshen nasara, nan ma suka tafi da imaninta dan tana so ta ji ana ragargazaryaren Nasara abin yana bata sha’awa.
Kwatsam! sai ga wata burdurwar yarinya mai dankaren kyau, ilimi da gayu, ta ci ado da dankareren leshi ko gyale bata yafa ba tana tafe, tana rangwada tamkar ba zata taka kasa ba. Da alama a cikin hutu ta taso, dan babu alamar wuya a tare da ita. Ta na rataye da jakar ‘lap-top’ a kafadarta, tafiya take ta na amsa waya, wayar ma abar kallo ce, ta zamani.
Da ta zo daf da Malaika zata wuce sai Malaika ta zabura ta dafa kafadarta, ta ce
“sannu kawata. Dan Allah ina da tambaya.” Kyakykyawar budurwa ta yi mamaki bata san sanda ta katse wayar da take yi ba, ba tare da tayi sallama da shi ba.Ta zubawa Malaika ido tana jiran ta ji tambayar. .
DA MA NI CE T Malaika ta yi murmushi ta ce, “sunana Malaika Shamaki. Ke fa, yaya sunanki?”
Ta kalle ta, amma bata yi mamaki da yawaba kasancewarta ‘yar jarida watakila ko ta santa a talabijin ne.
hakoranta Budurwar ta yi murmushi fararen suka bayyana, ‘yar siririyar wushiryarta ta haska ganin Malaika, ya yin da gefen kuncinta dukka biyu suka loɓa (beautiful points), Kamshin cigam din bakintamai kamshin minti ya buso cikin hancin Malaika. Malaika ta ce, Sunana Nasrin Abdul- ”
Nasir.”
Malaika ta zabura ta ce, “cancandi! Sunan ma irin na ku na ‘yan gayu. Kina aiki anan ne? Ko mahaifiyarki ce naga ta wuce yanzu? Dan kuna kama wallahi.”
Tabbas Nasrin ta ga rashin kamata a wadannan tambayoyi amma ta daure kasancewar ta san darajar dan Adam, bata wulakanci.
Sai Nasrin ta yi murmushin karfin hali ta girgiza kai ta ce, “aiki na zo yi daga NTA
”
DA MA NI CE talabijin Abuja, ni ‘yar jarida ce, zan yi hira da wannan bakuwar ne da kike fada. ”
“Ita wacece a kasar nan? Ta yi kama da Minista ilimi.” In ji Malaika.
Nasrin ta yi dariya ta ce, “ministan ilimi ai namiji ne. Wannan babar likita ce, ‘yar Nigeriya ce amma a Amerika ta fi zama. Me kike nema ne?”
Malaika ta yi murmushi ta ce, “Yarona sikila ne jiya ba mu bacci ba, ki rokar min ita ta duba shi, ke kuma ki dauke mu a jarida ki yadawa duniya ko za’a bamu taimakon kudi in kai shi turai, na ji an ce ana zuke jininsu a zuba wani saisu warke gaba daya.”
Dariya ta subucewa Nasrin ba tare da ta
yi shirin yinta ba. Ta dafa kafadar Malaika ta ce “kawata, ki je wajen likita ya duba shi wannan bakuwa ba mararsa lafiya ta zo dubawa ba. Ta zo ne akan binciken makasudin ɓarkewar cutar sakarau data bulla a wasu wurarena garin nan. Daga America aka turo ta.” Malaika ta ji dadin da ba zai masultu ba,
yau ‘yar gayu ta dafa kafaɗarta.
NI CE… Sai ta washe baki ta ce, “cafdijam! Ashe babba ce sosai, likitan likitoci za kice min. ki yi min hanya in ganta mana.” ”
DA MA
Nasrin ta fara fahimtar cewa bada me cikakken hankali take tsaye ba, sai ta girgiza kai ta fara tafiya.
Malaika ta zabura ta rike hannunta ta ce, “yah ke ma’abociya kyau da ilimi! Ki saurare ni mana, ki fahimci in da na sa gaba. Ki yi hira da ni a nuna ni a talabijin nima, dan duniya ta san mu talawa muna shan wuya.
Dariya ta kwacewa Nasrin ta kama haɓa ta fada a bayyane cikin mamaki “ikon Allah, Allah mai halitta kala-kala. Ke kuma hira kike so ayi da ke duniya ta ganki.
Dai-dai lokacin wasu maza biyu suka tunkaro su dauke da manyan kyamarori, Usman da Ishak, da alama abokan aikin Nasrin ne. Su ma suka ja suka tsaya a in da suka ga Nasrin, suna tambayárta meyasa ta tsaya anan? Nasrin ta yi dariya ta ce, “kawa na yi
yanzun nan tana so ayi hira da ita, ɗanta yana da sikila.”
Usman ya girgiza kai, yace “ba da masu sikila za muyi hira ba da masu sankarau ne. ”
Ishak yace, hira da ita mana.’ ” “ai duk ciwo ne za mu iya
Nasrin ta ce, “hakika mun yi babban kamu dan wannan matar zata iya magana sosai, na ji muryarta da zaki kamar ganga. Hajiya Malaika kin iya turanci?”
Malaika ta yi dariya ta gyada kai ta ce, “zan iya, irin na mu na Hausa dai.” Gaba ɗaya suka tuntsire da dariya.
Nasrin ta dafa kafadarta ta ce, “ki jira ni to in shiga in gama hira da Dr. Hala Hamma Yaro. Dan kada ta tafi kin ga takanas dan ita muka zo Kano.” ”
Malaika ta yi musu jinjina da hannu, ta yi dariya ta ce, “Allah Ya tsare min ke. Sai kun fito, ki gaishe min da ita sosai.”
Nasrin da abokan aikinta suka tura kofar ofishin suka shiga gami da yin sallama.Fiye da mintina talatin basu fito ba Malaika kuwa na nan a tsaye akan baranda bata tafi ba, haka ta ma manta da abinda ya kawo ta asibitin.
Da ta ji shirun ya yi yawa sai ta tura kofa ta shiga ofishin kanta tsaye, tana tafe tana sanda har ta isa wajen wata kujera,Likitoci biyu su na ta yi mata nuni da hannu ta koma amma ta ki, babu wanda ya yi magana saboda an ɗora kyamara akan Dr. Hala tana bayani, yayin da Nasrin na kusa da ita tana mata tambayoyi.
Malaika ta sami waje ta zauna bata damu
da hararrar da likitocin nan suke yi mata ba. Ta na zama ɗanta yace bai san zance ba, ya fara yunkurin kuka, nan da nan ta sauke shi ta kafa masa nono a baki. Ita fa a dole sai ta ga kwakwaf.
Tana kallonsu tana murmushi abinda ta ke gani a talabijin yau gashi a fili.
Da aka kammala hira da Likita kafin a rufe kyamara Nasrin ta taso da sauri ta ce da su Usman masu dauka su juyo su dauki hirarta da Malaika. Har za su yi mata musu, Nasrin ta ce su dauka kawai zata fada musu dalili idan an gama.
Malaika aka gyara riga da mayafi aka juyo da fuskar tamushashshan jaririnta ana murmushi.
Dr. Hala ta gyara gilashi ta zubawa Malaika ido tana kallo cike da mamakin yadda ta shigo ofishin ba da izini. Sai taga kamar da akwai alamar sanayya a tsakaninta da ‘yan jaridar, dan haka ta rage mamakin.
Turancin dai ba laifi, ta yi kokari ta yi bayanai akan ciwon ɗanta, ta kara bayanai akan gwamnati ta shigo cikita taimaka.
Da aka gama sai Dr. Hala ta kira Malaika kusa da ita, tana mata tambayoyi akan ciwon danta cikin rada. Gami da karbar dan ta dudduba shi, ta bata shawarwari.
Malaika fa ba sauraron abinda Likita take fadaba take, sarka, dan kunne da zobunan lu’u lu’u (Diamond) din jikin Dr.Hala kawai take kallo, har da bude baki, suna ta walwali suna haske saboda kyau. Da likita ta gama bayani sai Malaika ta nemi data bata lambar wayarta.
Likita ta girgiza kai ta ce bata da takamaimiyar lambar waya guda daya,kullum canja layi take yi.
Malaika bata ji dadi ba, ta tashi ta goya ɗanta ta karasa wajen Nasrin, wacce ke zaune tana ta rubuce-rubuce akan tebur,Malaika ta tambaye ta lambar wayarta, Nasrin ta yi ta hanya-hanya bata so ta bayar amma da ta ga Malaika ta dage har ta fito da kujajjiyar wayarta zata dauki lamba sai Nasrin ta bata, burin ta kawai Malaika ta kara gaba dan ta bar su, su yi aikinsu.Farin ciki ya cikawa Malaika kalbi, ta tafi tana godiya.
Har ta jima da fita sai gata ta dawo, daya daga cikin manyan likitocin daya jima yana jin haushinta sai yanzu ya sami damar more bakinsa. Dr.Gumel ya yi mata tsawa gami da balbale ta da fada har da kunfar baki.
ya ce, “Malama! Kina damunmu mu na aiki sai shige da fice kike yi. Wai shin waya baki izinin shige da fice a cikin ofishin nan?” Dr. Gume]
Malaika ta fusata ta harare shi, ta yi gatsine ta ce, “Malam, ba wajenka na zo ba,
Jamila Umar Tanko (JUŤ)
manyan ma basu yi min magana ba, ‘yan kasar waje wadanda Amerika da Obama su ka san da su, sai kai da kake tare da ni a Kano. ”
Gaba daya aka yi carko-carko ana kallon Malaika. Tabbas bata san da wa take magana ba, da ta san ko shi waye ba zata faɗa masa haka ba. Dr. Gumel likitan da ake ji da shi ne a kasar nan,ta fanni dashen koda.
Sai ya kasa magana ya ci ganba da karatun jarida. Nasrin ta ji kamar ta barke da kuka dan Malaika ta dame ta, ta fada cikin shagwaɓa da takaici, “Malaika me zan yi miki kuma?” Malaika ta washe baki tayi dariya ta ce, “yaushe za’a saka hirar da muka yi? Dan in gani, kuma awacce tasha za’a nuna?”
Nasrin ta ce “hunda kina da lambar ”
wayata za mu yi magana a waya. Malaika ta gyada kai ta ce, “zan kira ki idan na fitazan saka katin Naira dari biyu dan mu dade muna hira. kin ji kawata.” Malaika ta juya ta nufi kofar fita, har ta isa bakin kofa ta juyo ta harari Dr.Gumel ta ce
“ɗan bakin ciki sai ya mutu, Allah ne Ya hada ni da haɗɗun ‘yan gayu babu mai raba mu.” ”
Sai kowa ya bude baki yana kallonta cike da takaici, Usman ya zabura zai yi mata magana, Dr. Gumel ya yi masa nuni da hannu, alamar ya yi shiru ya kyale ta. Bayan ta fita suka tuntsire da dariya gaba dayansu, sun yi Amanna tana da taɓin hankali, dan haka sun yi mata uzuri.
MALAIKA SHAMAKI
Sai yanzu Malaika ta tuna abinda ya kawo ta asibiti, rashin lafiyar ɗanta. Ta ɗauko katinta daga jaka ta tafi da sauri tana ta salati, tabbas ta san ta makara dan karfe takwas ake gama karɓar Katina, gashi yanzu karfe goma daidai. Tana isa ta iske dandazon mata suna
tsaye a layi, wajen babu masakar tsinke. Dakyar ta kutsa ta cusa kai cikin ofishin duk da carin da mata na kan layi suke yi mata bata kula su ba. Ma’aikaciyar jinya (Nurse) ta tare ta da sauri ta tambaye ta, ina zata je? Sai Malaika ta mika mata katinta wai a taimaka mata.
Ma’aikaciyar jinya ta harare ta sama da kasa ta watsar, gami da yi mata tsawa ta ce, “Sannu isasshiya, sannu shafaffiya da mai, sai yanzu za ki zo? To an rufe karɓar kati sai gobe, idan goben ma baki zo da wuri ba sai wani satin. ”
Malaika ta harare ta,kama kugu ta murguda baki ta ce, “Toh mai gadin kofa ke ba likita ba kin fi likita zakewa. Da irinku ne likitoci da karasa marar lafiya za ku yi saboda babu imani da tausayi.” •
Wata mata dake kan layi ta zabura ta dafa kafadar Malaika ta ce, “haba baiwar Allah! Yaya zaki dinga zagin mata akan aikinta?”
Malaika ta juyo ta sauke kwandon masifa akan matar da ta yi magana. Nan da nan waje ya hargitse aka dinga hayaniya, gaba ɗaya Malaika aka bawa rashin gaskiya sai kadan ne suka bi bayan Malaika, su ma irin matsalarsu daya da ita sun zo a makare an ki karbar katinsu.
Malaika ta hada hayaniya har likitocin da kansu suka firfito suna bada hakuri.Daga
karshe dai aka tantance Malaika ce ta hada rigima, amma dan a zauna lafiya aka karбi katinta tare da na sauran amma da sharadin ba za’a gansu ba sai bayan azahar. Su ka yi amanna suka koma gefe suka zauna, har yanzu bakin Malaika ya ki mutuwa.
Fadi take ita ba talaka ba ce, wata talaka bata isa ta taka ta, ta kyale ta ba. Mamaki ya kama jama’a suna ta kallon koɗaddiyar atamfar da ke jikinta amma tana fadin ba su san ko ita wacece ba, ita da manyan likitoci ta ke kawance ba da Nurses ba.
Ma’aikaciyar jinya ‘Nurse’ dai ta fahimci Malaika ba sa’ar yinta bace, taga alama ta dame ta, ta shanye ta a fagen tsiwa da zakin murya, da alama ‘yar ta kife ce. Ta fara zargin ko tana shan benelyn dan yanzu an ce har da matan aure ma sha suke, dan haka duk wanda ya kula ta ma zai zama mahaukaci.Ta kyale ta, tama daina kallon inda take, dan har yanzu Malaika harararta ta ke tana nuna ta da hannu tana murguda baki.
Nasrin, masu kyamararta, Dr.Gumel da Dr. Hala ne suka biyo kan barandar da su
DA MA Malaika ke zaune zasu wuce da alama dakin kwanciyar mararsa lafiya suka nufa. Da suka hango Malaika ta tunkaro su cike da fara’a, gaba ɗayansu babu wanda gabansa bai fadi ba, suka yi turus. Musamman Dr.Gumel yana tsoron kada ta tara masa jama’a.
NI CE…
“Lah kawata Nasrin Abdul Nasir.” Malaika ta faɗa gami da rungume Nasrin.
Nasrin ta yi murmushin karfin hali ta ce, “sannunki. Kin sami ganin likita?”
Malaika ta ce, “Eh an shiga da katinmu, dan da har waccan ‘yar bakin cikin zata hana mu ganin likita wai mun makara.”
Ta nuna Ma’aikaciyar lafiya ‘Nurse’ yayin da Nasrin da Nurse suka haɗa ido, sai kunya ta sa Nasrin ta sunkuyar da kai kasa, kuma ta gaggauta barin wajen kamar yadda Dr.Gumel ya yi gaba da sauri bai tsaya ba.
Nasrin ta na tafe tana magana ta ce, dawo wajenki anjima. “zan
Dadi ya kama Malaika ta koma wajen zamanta ta zauna tana murna tana korawa jama’ar wajen bayani, tana mai gabatar musu
karya wajen
da su Nasrin har da karin gabatarwar. Ta tabbatar musu da su kunna labaran tara yau zasu ġa hirarta a talabijin din NTA.
Ma’aikaciyar jinya ‘Nurse’ ta juyo da
sauri tana kallon Malaika kan ta ya ɗaure. Malaika aka harari ta,tamurguɗa baki ta ce “kalle ni da kyau ni ba karamar mace bace, kin dai gani da idanuwanki ko ni wacece. Kuma idan karya nake ki kunna talabijin yau ko gobe idan baki gan ni a labarai ba ki kira ni makaryaciya. Ni talaka baya yi min raini, dan shi ba koman-komai ba ne.”
Malaika dai bata kara ganin Nasrin ba,sai bayanla’asar sannan likita ya ganta. Ta je har ofishin bata gansu ba, ofishin ma a dates. Ta karade asibitin nan kakaf tana nemansu bata gansu ba. Ta je wajen da Dr.Hala ta ajiye motarta ta ga wayam babu mota, sannan ta tabbatar sun shanmace ta sun arce.
Shamaki ya kira wayarta fiye da sau ashirin bata dauka ba, ta ga kiran ta ki ɗauka dan bata san me zata ce masaba. Ta tari a-daidai-ta-sahu (Napep) ta tafi cikin fushi dan ba ta
ji dadin rashin yin sallama da su Nasrin bad an tana saka ran samun kudi a wajensu. Unguwar Dorayi ta nufa anan take da zama, sai da suka yi faɗa da mai adaidaita sahun a hanya dan yace ta koma tsakiya tayar gefe daya bata da iska. Ta fara fada wai ita bata son harkar talauci yana neman kudi amma ya kasa canja taya. Mai a-dai-dai-ta-sahu (Napep) ya ji lafazan Malaika suna yi masa shawagi a kwanya, sai ya saita mudubi ya kara kallonta dan ya tantance mai kudi ya dauko wacce motarta ta sami matsala a hanya ta rufe ta hau babur dinsa, ko kuwa talaka ‘yar uwa ce take kasassaɓar magana?Ai kuwa daga dukkan alamu ‘yar uwa talaka ya hanga, kososuwa irinsa. Bai san amsar da zai bata ba, suka ci gaba da tafiya yana jira ya ga ta nuna katon get, sai gashi ta ce ya ajiye ta a kusa da bola, ya kaita har kofar gidanta ta shiga, nan ma ya sake gasgatawa ‘yar gidan malam shehu ce dai.
Ko ba komai ta barshi da zulumi da sunbatu.
Yana ta ambaton “Allah mai halitta!'”
Ta na isakofar gida tun daga kofar gida ta fara jiyo ihun karamin ɗanta yayayyen ‘Kasim’ ta shiga da sauri ta iske shi a zaure a zaune akan foh, yayin da babban ɗanta’Aliyu’ dan shekaru biyar yana dakan yaji a turmi a tsakar gida.Shamaki ya yi dagaje-dagaje da bakin gawayi yana dafa wake da shinkafa. Malaika ta dora hannu aka tana shirin kur❜ma ihu, ta daure dai ta fasa, ta sauke hannun.
Ta fada a bayyane “wallahi talauci bai yi ba.”



