⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 4: Chapter 4

LABARIN MALAIKA: • Yace “Malaika Dahiru Muntsira, garinmu daya layinsu a bayan layinmu yake,tare muka tashi mun girme su amma dai dukka an yi wasa tare. Babanta Malam Dahiru shine mai garin garinmu Kuma yana da mata huɗu da yara da yawa, ko a ɗakin su Malaika ma su tara mahaifiyarsu ta haifa.” Nasrin ta cika da mamaki ta bude baki ta
kasa rufewa dan mamaki.

Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “Allah ya jikan Malam Dahiru.”
Shamaki ya zabura, yace, “ai bai rasu ba yana nan ya dai tsufa, ai ita ‘yar gatace da uwarta da ubanta a raye. ”
Sai Nasrin ta zazzare ido tana mamaki dan ta fara jin banbance-banbance a tsakanin labarinsu, tabbas akwai makaryaci a cikin su biyun nan amma dai bari sai taga abinda zai turewa buzu nadi.
Ta yi gyaran murya ta ce, “Allah na zaci ya rasu ne, Allah ya kara girma.” Shamaki yace, “Amin. To kasancewar mu a kauye, dan sarki da talaka duk talawa ne kowa na yakin neman abinda zai ci, suma a gidansu akwai tsabar gero da masara ammafa mahadin dahuwa kowacce ita zata nema da yaranta. Haka muka taso kuma muna jin daɗin rayuwarmu kamar kowa, Allah ya jarrabe ni da son Malaika itama tana sona sosai har ma fiye da yadda nake sonta. Ban taɓa yin budurwa ba a rayuwata sai Malaika ita kadai na taɓa ji ina so har a cikin raina, haka itama ni kadai take kulawa. Mahaifinsu yana tilastawa ‘ya’yansa
sarki ai

_ mata da maza su yi makarantar firamare kasancewarsa mai gari dole sai an ga yaransa suna zuwa makaranta sannan ‘yan gari zasu yarda su bar nasu ‘ya’yan su je, dan haka Malaika ta gama firamre tas, ni na je na sami babanta na bashi shawara ta tafi sakandire ni zan dinga yi mata siyayyar makaranta da yake Makaranta kwana ta ci.
Ya amince Malaika ma bataso na lallashe ta, dan bata son ɓacin raina aka kaita makarantar kwana ta garin ‘Dan zabuwa’ nan kusa da garinmu.Garin kwaki, Kanzo, maggi, man gyada, gishiri sune dai siyayyar nake siya mata, idan ya kare ta yi min wasika wani Malamin makarantarsu ya kawo min in siya in bashi ya kai mata. Idan kuma ranar ziyara ta zo wato bisiting ni nake je mata, kawayenta kakaf sun san Malaika da Shamaki, dan soyayya ma haka ta mayar da sunanta a makaranta ba’a kiranta da Malaika Dahiru. A garinmu kowa ya san soyayyata da ita, samarin da suke sonta da yawa mun sha tare ni dambe a hanya suna ganin a dalilna ta ki su, haka itama ta sha

dambe da ‘yan matan da suke matukar sona bana kula su.
Ina sana’ar Rake bana tsinanawa kaina komai a jikin Malaika nake karewa, dangina suna ta zagina hatta mahaifiyata sai da ta fara jin zafin haka takan kira ni ta yi min fada, ina tabbatar mata wani abin ma karyar ‘yan gari ne ba ayi ba.
Sai da na zamar da Malaika abar kwatance a cikin kawayenta, ni ne dinkunan sallarta, ni ne ankon bikin kawaye da danginta, ni ne kudin kashewarta, ni na bata jarin da take sayar da wainar fulawa da awara a kofar gidansu idan tadawo hutu. Malaika tana da kokari matuka kuma na yi kokarin koyar da ita abubuwa da yawa idan an yi hutu, hatta turanci ni nake koya mata. Har ya zamanto ta fi kawayenta iya turanci, sai ayi ta mamaki idan aka ji tana turanci.
Tana matukar jin maganata kasancewar tana da tsiwa da taurin kai dan wani lokaci sai mahaifiyarta ta kira ni a kawo min kararta in yi mata fada sannan ta bar abinda ta ke yi. Tana aji hudu na sakandire Mahaifinta yace ta isa

aure za’a cire ta in zo in aura idan kuma bana so zai yi mata miji, dan ya ji na fara rokarsa ya bar ta, ta kamala sakandire. akan
A dole na fito aka yi aure daman na daɗe ina taron kayan auren. Dakin kasa guda daya jal Kakana yaba ni,anan muka zauna shi kuma da matarsa suna cikin daki daya. A haka muke zaune ban dade da yin aure ba na sami aiki a Bichi ake biyana albashi daga nan rayuwarmu ta dinga ci gaba. Mun fi karfin ci da sha da sutura sannan a hankali na yaɓe gidan kasarmu da siminti, na cire katagar kara na yi Katanga ta bulon kasa, muka ci gaba da zama na soyayya har Allah Ya ba mu haihuwa yaronmu na farko Aliyu, muka haifi na biyu na saka masa sunan kanina Kasim.
A lokacin ne abokina yaba ni shawara muka je muka zana jarabawar Jamb, muka cike B.U.K. Abokina ya SO in karanci Likitanci(Medicine) na ki amincewa saboda shi ya san zan iya amma ni ina ganin ba ni da damar da zan jure karatun likita saboda ga iyali, ga aikina, zan fito in je neman abinda zan ci dole. Na cike kos din Biochemistry, Allah

cikin ikonsa ranar jarabawar Jambmuka je muka zana kuma na ci da yawa, abokin na
kuwa bai ci ba. Nan da nan da gudu suka ba ni abinda na zaɓa daman sakamakona na sakandire ya yi kyau. Na nemi izini daga wajen aikinmu suka bar ni na tafi da albashina (inserɓice) ko da yaushe da babur dina nake zuwa daga Bichi zuwa Kano, in yi lacca in koma, da na ga da wahala sai na yi adashi na hada da rance na zo na kama mana gida anan Kano,a unguwar Dorayi akan Naira dubu talatin da biyar haya a shekara.
Na dauko iyali muka dawo yanzu haka muna cikin shekara ta biyu kenan, anan aka haifi dan autan danmu Ahmad, kuma Allah Ya yi shi yana da sikila. Gashi dai ana ta faman zirga-zirgar zuwa asibiti.’
Nasrin ta yi shiru tana mamaki wannan labari mai kama da almara, ta ji talauci tsantsa dan ita bata san irin wannanrayuwar ba. Ta yi ajiyar zuciya ta ce, “idan na lura Malaika na sonka kuma tana yi maka biyaya ko? Menene laifinta yanzu?”

Ya yi dariya yace, “Jama’a da yawa tun a garinmu suna ta maganar cewa Malaika tana yi musu kallon banza, dan ta auri miji yana yi mata hidima, da na fara aiki ta fara miya da nama sai abin ya karu har ‘yan uwana da ‘yan uwanta suka shiga layi suna ta jin haushi wai Malaika na wulakanta su in an je gidan sai taga ḍama ta kalli mutum, in dai ba da kai zata karu ba bata kawance da kai. Ni dai ban gani ba dan bata yi a gabana, in na tambaye ta ta ce karya ne. Na yi faɗa da jama’a da yawa akan sukar Malaika a gabana. Abin nata bai giga ba sai da muka kauro Birni inda ta hadu da wayayyu, masu arziki sannan halinta ya fito fili karara, dan a kauye kowa babu, balle ta sami mai kudi ko ‘yar gayun da zata makalewa. Idan dare ya
yi sai taga kowa a unguwar yana kunna Inji, sannan ta lura ashe sai a haske ake rayuwa, taga kullum matan birni idan zasu fita kwalliya suke ci ba’a saka koɗadiyar atamfa ta ce itama sai ta yi haka, taga wasu motarsu suke shiga akai su unguwa ba kamar a kauye ba da sayyada ko da acaɓa ake fita, nan ma ta ce itama sai ta yi haka. Ta ga ana zuwa

CE… Dubai da Saudia ayi sayayya itama ta fara
DA MA NI
sha’awar haka. Akwai wasu masu arziki a kusa da mu a gidan ta tare nan take ganin kayan kyalkyalin duniya, kafin aka yi faɗa kaca-kaca ta daina shiga. Ta koma gidan wasu masu kudi a tsallaken titinmu nan ma aka yi fada ta daina shiga, ni kuma ta zo ta sauke min kwandon masifa sai na yi kudi da karfin tsiya dan adaina yi mata gori.
Tun daga nan nake yi mata nasihaamma tamkarzugata nake yi, yanzu data hadu da ke abin ya ci tura ta sake barkalewa.Nasrin ki taimaka ki nunawa Malaika yadda rayuwa take, na tabbatar ke kanki a danginku akwai talakawa dole wani ya fi wani. ”
***
Nasrin ta yi shiru tana tunani ta rasa abinda zata ce, bayanansa kamar da kamshin gaskiya na Malaika ma ta gasgata dan in har karya take yi ba zata dinga sharɓar kuka haka ba. Me yasa Malaika zata yi mata karya? Ko
.

me yasa Shamaki zai yi mata karya? Dole a cikinsu akwai makaryaci.
Nasrin ta gyada kai ta ce, “tabbas uwa ɗaya uba ɗaya ma dole a sami wani ya fi wani arziki, Shamaki ka ci gaba da hakuri. Kenan yanzu albashinka na can kauye da shi kadai ka ke cin abinci?”
zama Ya gyada kai yace “Eh! Naira dubu sha takwas ne kacal kafin wata ya zagayo sai na ci bashi na bawa Malaika, gashi na koma makaranta siyan Handout, da yawa ma ‘yan matan ajinmu da nake koyawa karatu su suka dauki nauyina ni kuma na bawansu, assignment da aattendance dinsu nine dan ba zuwa suke yi ba kullum, to a haka muke rayuwar gashi an hana Acaɓa a Kano balle in yi da babur dina, amma na kan fita wajen gari in yi acaɓa ma wataran. Ni dai fatana in kyautatawa Malaika kada ta tafi ta bar ni.” Nasrin ta cika da mamaki ga shamaki ma yana kokarin kece mata da kuka kamar yadda
Malaika ta yi mata.
Ta yi tagumi ta yi shiru tana saurarensa wani abu take ji yana yi mata yawo a cikin

ta kwakwalwarta. Ta yi ajiyar zuciya ce, “kenan kai dalibi ne a B.U.K ba Malami ba?”
alhali Shamaki ya fara mamakin tambayar nan ya fada mata komai.
Ya gyaɗa kai, yace, “ai na faɗa miki in
da nake aiki, anan kuma karatu nake.” Nasrin ta gyara zama ta yatsune fuska ta ce “ka fara tunanin kara aure ne ya sa Matarka da rashin samun zaman lafiya a kishi junanku?”
Shamaki ya yi dariya ya ce, “Aure? Ina ta kaina auren me? Ko kadan bana taɓa sha’war yiwa Malaika kishiya. Ina son Malaika har cikin raina bana son ɓacin ranta, ta kasa yarda. Da ina da kudin da ya kai cikin duniyar nan, da zan juyewa Malaika dan ta yi farin ciki.”
Sai Nasrin ta ji gabanta ya faɗi ta faɗa cikin firgici “Shamaki ka tabbatar abinda yake rankaka ke fada min?”.
Ya yi dariya yace, “Baiwar Allah baki san ni ba, ban san ki ba amma na kwashe sirrina kacokan na faɗa miki. Wallahi ban da

ke duk duniya ban taɓa irin wannan hirar da kowa ba dan ke ma na san zaki taimake ni ki fahimtar da ita. Kin ga yanzu ina Laɓel , karatu ya yi nisa saura shekara daya in gama, gidana ba nutsuwa ina tunanin yara bana iya zama a makaranta in yini ina karatu, ba dan ma kwakwalwar mai dauka da wuri ba ce da tayaya zan din ga hayewa jarabawa, kuma ban taɓa samun carryoɓer ba, babu kuma dalibin daya fi ni ci a department dinmu.”
Nasrin ta gyada kai ta ce, “dakyau Shamaki na jinjina maka, in Allah Ya so zan taimaka maka cikin dabara zan fahimtar da matarka ba tare da ta san mun taɓa magana da kai ba.”
Ya ce “na ji dadi na gode.” Nasrin ta ce, “tambayata ta karshe itace shekarun Malaika nawa? Naka nawa?”
Ya yi murmushi ya ce, “Shekarun Malaika ashirin da shida, ni kuma talatin da biyu. Ke fa shekarunki nawa?”
Nasrin ta yi dariya, ta ce, “ni saʼar Malaika ce shekaruna ashirin da biyar, gobe ne Birthday dina. Na gode sai anjima.”
Jamila Umȧr Tanko (JUT)
DA MA NI CE.. Nasrin ta kashe waya tabar Shamaki a zaune yana ta murmushin jin dadi shi kadai. Ji yake tamkar matsalarsa ta zo karshe, gyara ya zo Malaikarsa zata shiryu. Ya yiwa Nasrin addu’a Allah Ya bata dama da ikon shawo kan Malaika. Dan tunkarar Malaika da zunmar gyara abu ne mai wuya dan bata jin Magana.
Ya isa gida da murna ya iske Malaika cikin farin ciki, hatta cimar gidan ta canza abinci da kaza ta yi musu, sai ya ji gabansa ya fadi ya tambayi in da ta sami kudi ta sayi kaza, ko zakka makwabcinsu ya yi musu daman ya saba basu?
sai Malaika ta ce kawai ya ci ba sai ya tambaya ba. Shamaki ya girgiza kai ya ce ba zai ci ba ya sani. Ta gyara zama ta yi fari da ido ta dauko wayarta ta bude sakon Nasrin ta nuna masa. Ya kalla ya dubaba tare da ya gane ba. Ta yi masa bayani kati ta turo mata na Naira dubu uku.
Sai ya ji jikinsa ya yi sanyi ya fara tunani aransa “anya Nasrin gyara zata yi ko kuwa ɓata min mata take? Na fara nadamar labarina dana

kwashe na faɗa mata ɗazu. Ashe ta turowa
matata kati sannan ta kira ta ji ta bakina.’ ” Sai ya shiga zulumi yana mai tsananin takaici, yaga dakyar ya nemo Naira ɗari biyu ya bayar a yi cefane,yanzu ta zo ta turo mata da dubu uku. Yanzu ta ina Malaika zata ga mutuncinsa? Ta ina zata ji maganarsa? Ta ina zai hanata ta hanu ? Me yasa ba zata yi sha’awar ziyartar Nasrin a Abuja ba? Shiyasa ta fi sha’awar saki maimakon zama da shi dan ta koma ta zauna da Nasrin.
“Malaika kada in kara ganin kin kira Nasrin balle ki roke ta kati.” Shamaki ya fada a fusace.
Malaiaka ta zabura ta taşhi tsaye cikin tsiwa ta ce “Lallai ma, au haka zaka ce? Bakin ciki ne abin dan kaga na sami mai taimaka min? Wallahi baka kaunata saboda baka kaunar ci gabana. Babu mai raba ni da Nasrin Aminiyata.”
Sai ya fusata ya kai mata hannu kamar zai mare ta, ya fasa.Tayi tsalle ta faɗa kan kujera tana makerketa ta zaci dukanta zai yi.

CE… Ya fice daga gidan a fusace, Malaika ta tashi tsaye ta tsaya a falo ta kama Rugu ta rasa abinda yake yi mata dadi zuciyar ta na tafasa ga tukikin masifa ya taso mata amma babu abokin fafatawa.
DA MA NI
Tsaki take tana kwafa tana fadin “cafdi jam! Ashe za’ayi ta yau a gidan nan. Daman ka mare ni da ka mari aurenka wallahi. Nasrin kuwa bazan rabu da itaba sai dai ka mutu.
Shamaki bai shigo gida ba sai da daddare bayan Sallar isha’i, ya shigo da fara’a ya iske yara sun yi bacci sai Malaika a zaune a tsakar gida tana cin tsire.
Ya yi sallama bata amsa ba, ya yi dariya yace, “kaga madam an sami kudi ana ta cin dadi bayan kaza ma kuma tsire ake ci, ai dadin zai yi yawa a rage na gobe mana. Ke kaɗai za ki ci dan rashin imani sai da kika bari yara sun yi bacci, ni bana nan?”
Ta yi kamar ba da ita yake ba ta dinga kai tsoka lunkuma-lunkuma bakinta. Ya ga da gaskę cinyewa zata yi ya zabura ya kai hannu zai dauki yanka ɗaya, ta dɗauke namanta da

sauri ta juya baya ta cinye tas ta wurgar da takarda, ya zaci wasa ne.
Ya ce ta dauko masa abincinsa na ɗazu zai ci. Ta harare shi ta ce “ai ka yiwa kanka wallahi mun cinye tas ka je ka nemi abincinka. Tunda kai ba’ayi maka gwaninta, kamar wacce ta samo kudin haram har da kin ci kuma wallahi duk ran da ka dake ni ka daki aurenka.” Shamaki ya zauna ya yi shiru yana
kallonta yunwa yake ji ta gaske kuwa, dan tun kokon safe ne a cikinsa gashi ba shi da ko sisi. Bashi da karfin yin magana ma balle fada, sannan ba ya son ma a kara tayar da zancen dan daga baya da ya huce sai ya ga bai kyauta ba kamata yayi ya yiwa Nasrin kyakyawan zato tunda taimakawa ta yi.
Ya yi ta karanto istigfari a cikin zuciyarsa. Duk abinda Malaika take fada masa kalma daya yake faɗa yana ta nanatawa kamar karatu “yi hakuri, yi hakuri, bazan sake ba.”
Har sai da Malaika ta ji ya fara bata tausayi sannan ta daina tsigale shi. Ya tashi ya fitą kofar gida ya je wajen mai shayi da biredi na kan kwanar gidansu anan ya ci bashi ya cika

cikinsa ya dawo gida. A ranar dai Malaika bata kula shi ba, baya ta juya masa ya gaji da magiya ya rabu da ita. Asuba ta gari!
***
Shamaki ya shiga cikin matsananciyar rayuwa, ko inaba dadi, can garinsu yana kula da mahaifiyarsa wacce bata da komai tana neman taimako, kannensa gaba daya babu mai shi babu wanda ya yi karatu a jikinsa ma suke nema, ‘ya’yansa abin tausayi ya kamata an saka su a makaranta amma suna zaune a gida, ga marar lafiya kuwa wani lokaci sai dai a hakura a zuba masa ido yana ta kuka babu kudin magani, Malaika abar kaunarsa ta tsane shi ta juya masa baya, ya manta rabon da ta masa hira mai dadi.
Baya gushewa da yin tsayuwar dare da addu’a yana kuka yana faɗawa Allah. Ya na nemawa Malaika gafara da shiriya dan baya fatan Allah Ya kamata da laifin kin yiwa miji biyayya da butulcin da take yiwa Ubangiji.
Jamila Umar. Tanko (JUT)
Malaika kuwa ga ni take kamar duk rashin gata da rashin sa’a akanta ya kare, gani take tamkar ta rako mata duniya. Idan ta tsaya a titi ta hango mace ta na kotsewa a cikin mota mai kyau ta gani ta fada sai ta ji ta tsani kanta. Dan haka itama rayuwar ta yi mata kunci bata walwala ko kaɗan.
Al’amarin Nasrin kuwa ta shiga rudani matsalar Malaika da Shamaki ta tsaye mata a rai, ta shiga aikin tunanin tantance waye mugu a cikinsu kuma waye ya yi mata karya, a haka dai kowa ya nuna mata shine abin tausayi dayan ke cutarsa. To Allah Shine Masanin badini da Zahiri.

BABI NA BIYAR
ABUJA:
D a misalin karfe goma na dare Nasrin tana sanye da kayan bacci tana kwance akan gadonta tana ta danna Computer ta har yanzu dai tana biye da Dr.Jalo mutuminta, ta ga ya yi sababbin rubutu ya turo. Tana ta bibiyarsa a hankali tana karantawa sai ta ci karo da wani rubutunsa wanda ta ke neman karin bayani akai, yadda ya yi rubutun ma kai kace da Shamaki da Malaika yake, ma’auratan da suka kasa fahimtar juna. Sai ta je ta yi comment a kasan posts dinsa. Bai bawa kowa amsa ba, dan ta iske dariruwan mutane da suka tofa albarkacin bakinsu, mata da maza suna ta mahawara. Gogan naka bai tanka ba shi dai ya zuba bayanai ya kara gaba, ya bar mutane da hayagaga. .
Ta dubi lokacin da ya turo sakon, a ranar ne da safe.Ta dauko wayartą zata kira shi sai ta

kalli agogo ta ga dare ne bai kamata ta kira mai aure da daddare ba dan ta tabbatar yana da mata kada ta hada su fada. Ta dubo cikin hotunansa ta ga ya sake ‘profilepicture’ dinsa, tabbas ya yi kyau matuka kamar ka kira shi ya amsa. Idanuwan nan dara-dara, hanci doɗar, hakora a jere reras gwanin ban sha’awa ya saka wani farin gilashi wanda ya yi masa kyau, kana ganinsa kaga cikekken likita, likitan da yasan abinda yake yi. Ta dade tana kallon hoton nan a ranta tana mamakin yadda ta sami mutumin da yake birge ta.
Dr.Jalo ne kaɗai mutumin data taɓa haduwa da shi take binsa ya ke ja mata aji. Shima babban abinda ya birge ta shine tunaninsa da fasaharsa lallai duk wanda Allah ya bawa fasahar rubutu ko ta magana lallai ya godewa Allah, ba kowa ne yake samu ba kuma ba’a saya a kasuwa, haka ba’a koyo a makaranata.
“DA MA NI CE Dr.Jalo! Dr.Jalo.” Ta fada abayyane a lokacin da ta ci gaba da kallonsa.

Tana cikin wannan hali sai gashi ya hau facebook. Ta zabura ta bishi ta ‘inbod’ ta masa magana. Salama ce da gaisuwa ta tura masa, nan da nan ya amsa mata. Sai ta yi mamaki. Daga nan da kwarin guiwarta ta tura masa jinjina da yabo akan rubuce-rubucensa. Sai bai bata amsa ba kuma tana ganinsa ‘online.’ Ta sake tura masa cewar tana so su dinga gaisawa ya dinga bata shawarwari. Bayan ta jima da tura sakon bai bata amsa ba ma sai ya sauka daga facebook din ma. Ta san kuwa ba zai dawo a yau ba, ko ya dawo ba zai bata amsa ba.
Ta ji kwallar takaici ta surnano mata ta fara tsanar kanta da kanta ma da ta ke jawowa kanta wulakanci, tana mamakin masu wulakanta mutane dan sunga mutane suna sonsu. A sanadiyyar Allah Ya yi musu wata baiwa, tabbas ita bata da wulakanci tun ma bata fara hulda da mutane haka ba, yanzu data fara harkar rahotannin nan ana nuna ta a talabijin ta samu masoya da yawa da suke turo mata da sakonni ta waya ko ta Email dinta. Tana kula

kowa yadda ya kamata shiyasa kula Malaika har suka ma ta tsaya ta
saba. Ta fara ji a ranta ba zata kara kula Dr.Jalo ba bare ya sake yi mata wulakanci, eh yana da kyau, yana da ilimi, yana da kamun kai , yana da aji, watakila attajiri ne ko dan gidan attajiri. Sai aka yi yaya kuma? Da me ya fita? Koda ace ya tara duk wadannan abubuwan da aka zano Nasrin tana da linkin nasa.Ta fara tunanin kai zuciyarta nesa ta manta da matsalar mutumin da bata sani ba.
** *** ***
Washe gari da safe ta shirya zata fita wajen aiki ta jawo computer ta zata kashe saita
iske amsar Dr.Jalo da asuba ya turo mata. Ta ji dadi a ranta harda rufe ido da budewa dan ta gasgata ba mafarki take yi ba ido biyu ne.Ya tabbatar mata yana farin cikin haduwa da ita kuma kada ta damu a shirye yake ya bata shawara koma wacce iri ce.Hannunta na rawa ta rubuta masa godiya da

nuna farincikinta. Baya kan layi amma ta san
idan ya dawo zai gani. Ta fito falo tana walwala har sai da Salis da Zainab suka fahimce ta, yau tare da su ta karya kumallo saɓanin idan ta fito da fushi bata tsayawa ta ci abinci.
Zainab ta harare ta, ta ce kin yi chats ko? Kin ji wani abu mai dadi dan nasan baki da abokai sai a socoalNetwork kullum kina kan computer, haka kawakenki mutanen ɓoye ne duk anan ku ke haduwa.”
Salis da Nasrin suka kwashe da dariya.
Nasrin ta ce, “ka ji wai muatanen ɓoye
kamar wasu aljanu.”
Da suka gama cin abinci Salis da Nasrin kowa ya dauki jakar laptop dinsa ya fita, Zainab ta rako su har wajen motocinsu kowannesu ya shi tsaleliyar motarsa ya nufi wajen aiki.
Sai yamma kuma ko da magriba, Zainab ita kadai ta ke yini kuma bata sha’awar ‘yan aiki saboda matsalarsu ta ishe ta.
Nasrin ta isa ofis, basu zauna ba yau, suka fita da motar ofis dauko rahotanni, acan ta yini basu dawo ofis ba sai da yamma likis

DA MA NI CE イ wayarta ma a ofis ta bari a caji, ta zo ta iske missedcalls Malaika babu adadi bata damu ta kira ba dan ta san kiran kawai take yi dan bata da abinyi. Kullum sai ta kira ta ta ishe ta da surutu marar maʼana. Dan haka ba zata kira ta ba itama sai ranar da bata da abinyi, sai su haɗu su yi ta hirar rashin abin yi. Kafin ta tafi gida ta bankaɗo Facebook dinta sai kuwa taga mutuminta yau ‘yan siyasa ya ragargaza ya kawo musu misalai da manyan ‘yan siyarsar kasashen da suka ci gaba wadanda suka san darajar bil’adama. Ya kawo misalai da ‘Nafsin Mandela’ da ‘General Muhammad Buhari’ zo kaga ruwan yabo da jinjina da ake yi masa. Nasrin ma ta shiga ta zankada turanci irin na su na gwanaye, ta yabi gwaninta Dr.Jalo, ta yaba masa akan fadar gaskiya komai ɗacinta.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved