⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 5: Chapter 5

Nasrin bata kula ta ba ta shirya tsaf da wata atamfa doguwar riga da dan mayafi ta hada kayanta gaba daya.
Sannan ta juya ta harari Malaika ta ce “in kin ga dama ki tashi mu tafi.’ ”
Malaika ta yi zunbur ta mike har da murmushin dadi, su na fitowa suka ga mai maganin yana zagaye daki-ɗaki yana bada magani, Nasrin ta kalle shi sama da kasa ta kamanninsa sak na Bokaye ko riga babu a jikinsa sai fata da gashin kaza a ko ina da a jikinsa, guru da laya a hannu da kafa, daga shi har makarbansa abin tsoro. Tabbas babu alamar musulunci anan, sai tafara tunanin yadda aka yi Jalo ya yarda ya zo nan neman maganai da iliminsa da komai. Ta kudiri niyyar sai ta yiwa jalo magana akan wannan.
Nasrinda Malaika suka nufi dakin Jalo suka shiga da sallama, abin mamaki sai ga Malaika tana washe baki ta ji za’a tafi gida, ta gaishe su da fara’a ta jawo kayanta tana hadawa.
Nasrin ta mika musu Biredi da butter Mama da Malaika ne suke ci suna korawa da

lemo da ruwa. Jalo ya na azumi bai ci ba, Nasrin kuma ta ce ta koshi. Gaba daya hankalinta a tashe yake babu abinda take sai kallon Jalo tana ganin idan suka rabu yanzu har abada ba zasu kara haduwa ba.
Ya kula da haka sai ya zare farin gilashin da ke fuskarsa ya dube ta ya yi mata lallausan murmushi ya ce, “Nasrin! Na san abinda ya ke damunki. Kada ki damu Ubangijina Yana tare ta ni, Shi ya ɗora min Shi zai yaye min. Ya fi ki sona kuma ko dukka duniya zasu taru akaina bazan ji sauki ba in dai ba Shi Ya so in warke ba.”
Nasrin ta surnano da hawaye ta ce, “Zamanku anan ne ya fi damuna, kuma yanzu na ga Mai baku magani sai nagan shi da siffar Bokaye.’ ”
Jalo ya gyada kai yana kallonta yace “Nasrin! Magani kawai yake bani sassake ne babu wani abu bayan wannan kuma ga Mama nan ita take kuka idan na ce ba zan zo ba. Kar ki damu Insha Allah ba zan ɓace hanya ba.’ Nasrin ta gyada kai sannan ta langwaɓe kai hawaye na zuba, kuma bakinta yana ta ”

rawa da alama tana so ta yi wata magana ta
kasa. yana kallonta Nasrin ta zura masa ido tana kallo shima hawaye ke Zuba daga idanuwansu su dukka. Sai suka juya suka kalli Mama wacce tashin hankali ya hanata ci gaba da cin abinci.
Mama ta tashi da sauri ta fice tana hawaye ta basu waje, amma kuma ta laɓe a inda zata dinga jiyo abinda zasu ce.
Malaika tana zaune tana cin biredi tana kallonsu da alama itama tana jin tausayi duk da bata san ciwon da Jalo yake yi ba, ta ga alama dai baya iya tashi tsaye.
Can jimawa Nasrin ta sunkuyar da kai kasa tana tunani, sannan ta sake ɗagowa ta dube shi cikin sanyayyiyar murya ta ce, “Dr. Jalo!in tambaye ka wata alfarma zaka yi min?”. Ya dago da sauri ya dube ta cike da mamaki ya yin da kwakwalwarsa ta kasa tuno masa alfarmar da zai iya yi mata yana zaune a cikin kashi da fitsari. S

Nasrin ta dago ta dube shi ta yi magana cikin sanyayyiyar murya ta ce, “Za ka taimake ni ka aure ni?”
Sai ya ji gabansa ya fadi, ya zazzare ido ya na kallonta.
Ta sake cewa “ina sonka a yadda kake Jalo.”
Sai ta fashe da kuka shima hawaye ya na zuba daga idanuwansa.
Ya girgiza kai yace, “Nasrin! Ina tunanin har yanzu baki gane halin da nake ciki ba, ai babu maganar aure a tare da wanda lakarsa ✓ bata aiki.’ ”
Ya ɗaga mata ledar fitsari da take jikinsa, wato katata.
Ta yi sauri ta sunkuyar da kai kasa ta fashe da kuka. Yayin da Malaika ta kura ido tana kallonsa sai yanzu ta gane abinda yake faruwa.
Nasrin tarusa kuka ta faɗa cikin ɗaga murya “ina sonka a haka, na yarda zan zauna da kai a haka. Jalo ban san soyayya ba sai da na hadu da kai tun ma ban taɓa ganinka ba. Haka kuma da ka kula ni na ji farin cikin da

ban taɓa ji ba. Da na same ka da larura babu abinda ”
ya canja, ina sonka har yanzu.’ Ya girgiza kai yana kuka ya ce, “Nasrin! Na gode. Ba zan taɓa mantawa da ke ba a rayuwata ba. Ke ce mace ta farko da kika taɓa sona na tsakani da Allah ba dan kyawuna ba, ba dan kudina ba, ba dan martabata ba. Na fi bola abin tsantsani amma duk da haka kika ji kina kaunata.’ ”
Kuka ya ci karfinsa yayin da Nasrin ma kukan take. Mahaifiyar Jalo tana laɓe a bakin kofa tana rusa kuka dan duk tana jin abinda suke cewa.
Mamaki ya hana Malaika rufe baki jira take ta ji Jalo ya amince ta tashi ta rike Nasrin ta ce baza’ayi wannan taɓargazar a gabnta ba. Sai Allah Ya sa bai amince ba sai ta ji dadi, amma tà fara tuhumar Nasrin da ciwon taɓin hankali tunda take son mai larura kuma talaka duk da kyau da dukiya da Allah ya yi mata. Nasrin ta sharce hawaye ta ce, “tun da
nake a rayuwata ban taɓa ganin mutumin da ya taɓa birge ni irinka ba, a koda yaushe ina cewa

‘DAMA NI CE Jalo, da ma in zama kamar ka, Da ma in kasance tare da kai.. . .”
Ya yi sauri ya katse ta yala magana cikin kuka ya ce, “ni nake sha’awar DA MA NI ne Nasrin, dama in zama ke, Dama ni ne nake da lafiya kamar ki. Kada ki yi fatan ki zama ni. ”
Nasrin ta ce, “Allah Ya na sonka kuma Allah zai baka ladan tawakkali. Ka yarda in kasance tare da kai Jalo, na yarda na hakura da komai na jin dadin rayuwa.”
kuka. Mahaifiyarsa ce ta shigo da sauri tana
Ta rungume Nasrin ta ce, “Nasrin ina kika shiga tuntuni, baki hadu da Jalo ba? Da ace mun san ki ada da bai auri Rayyana ba. ‘DA MA ke ce’ uwar ‘ya’yansa mun san zaki zauna da muda amana, nasan za ki zauna da mu a cikin kowanne irin hali muke ciki. Mun gode da kauna, amma Allah bai ga damar ku zauna tare ba tunda kun hadu a kurarren lokaci a sanda Jalo ya zama hoto.” ”
Su dukka ukun kuka suke yi.

Nasrin ta kara kankame Mama ta ce, “Kada ku hana ni zama da zaɓin rayuwata, ui na zabe shi a haka zan zauna da shi har lokacia mutuwata”
.” Mama ta girgiza kai ta ce, “mu ma bamu ki ki ba amma shi kansa Jalo ba zai yardaba, haka nima ba zan yarda ba balle iyayenki. Haba Nasrin kada ki makance alhali kina da idanuwa, kada ki zama kurma alhali kina ji da kunnuwanki, kada ki haukace da gangan alhali kina da hankali. Ba kya ganin halin rashin lafiya da yake ciki?Ba ya bukatar mace yanzu ma da a rayuwarsa. Mun godewa Allah Yabashi dama ya yi aure ya yi aure ya haifi biyu kafin ya zama haka. Ni ce ya zame min dole ni uwara, na kashe aurena dan in zo in zauna da shi. Ina addı:’a Allah kada Ya dauki raina da wuri dan in zauna da dana in ci gaba da kula da shi. Ina addu’a kada Allah Ya dora min ciwon da zan kasa kula da Jalo.” Jalo ya rike kai ya yi kuka ya gaji, ya
dago ya dube su ya ce, “Allah kada ka fara kashe Mamana kafin ka dauki raina.”

Mamaki ya hana Malaika rufe baki da alama itama ɓurbushin tausayinsu ya rufto mata.
Ta tashi tsaye ta fita da akwatinta ta dauko jakar Nasrin ta fito da ita sannan ta fita ta tare Masu acaɓa biyu dan suna ta shigowa da mararsa lafiya. Ta yi ta kwallawa Nasrin kira ta zo su tafi, amma Nasrin batagama yin sallam? tana tare da su Jalo. ba ya
h Nasrin ta durkusa a gaban Jalo ta kudi. bata account number sa zata turo masaidi yana Ya girgiza kai yace baya bukat yiwa ‘yan siyasa rubutu suna nsa yadda ya kamata. Addu’arta kawai ke bukata shima yana nan yana yi matatan alkhairi ta sami miji
na gari.
Nasrin ta shaida masa gara ta koma Amerika wan mahaifanta ta zauna acan ba zata sake dawowa Najeriya ba kuma zata ci ko Allah Zai sa ta sami asibitin da suka kware akan ɓangaren ciwon. gaba da bincike akan ciwonsaima zata ci
Ya yi mata godiya sosai, Malaika ta zo ta ja hannunta suka fito, Mama tana biye da su

tana kuka tana godiya, ya yin da Jalo ya kece da kuka ya dafe kai ya ji son Nasrin tamkar ya fasa masa kahon zuciya, amma babu yadda zai yi ne.
Nasrin ta kwaso kudin Jakarta kakaf ta bawa Maman Jalo kadan ta rage na motarsu, ta ce Mama ta yi mata kokarin neman lambar Account ta turo mata zata taimaka musu da kuG. Ma’aikata suka rugo da gudu suna yi mata allama,nan ma ta tuna da wasu kuɗaden a wani diihun Jakarta ta kwaso ta yi musu rabon dubu-dubu, sai murna ta kama su.
Nasrin da suka hau acaɓa suka tafiyayin da kuka ya tokare Nasrin, dadi ya ruftowa Malaika ta shaki iska mai sanyi.
A cikin motarsu dagadda zuwa Abuja ne Nasrin ta bude wayarta ta hau facebook anan ta ga rubutun Jalo. Tabbas ya yi rubutu karara akanta suna ne kawai bai ambata ba.
Amma ya suffanta ta da mace ta gari kuma duk wanda ya aure ta ya yi dace a duniyarsa da lahira. Daga karshe ya yi mata addu’a Allah Ya bata dukka alkhairan da suke cikin rayuwarta ta duniya da lahira. .

Nasrin ta
tsinci Kanta tana mai
murmushi mai hade da hawaye, Malaika tana gefe tana harararta dan ita haushi take bataba tausayi ba.
Kafin su shiga Abuja Nasrin ta yiwa Zainab waya ta shaida mata sun kusa shigo Abuja ta aiko direba ya zo ya ɗauke ta a tasha. Dan haka suna sauka suka hango Direba yana jiransu, ya zo da sauri ya ɗauki jakunkunansu ya saka a but suka shiga mota suka nufi gida. : Nasrin ta kula Malaika tana ta fara’a tana yi mata hira dan a shinya, amma
Nasrin ta gama harka da ita har abada, tasan itama zata guje ta idan Allah ya dora mata larura ta rashin lafiya ko ta talauci. Dan haka Malaika ba abokiyar zama ba é

BABI NA GOMA SHA BIYU
ed climb shansind an olay ABUJA… ediyszust
shunda ght be any
Suka isa gida, Zainab ta tare su da fara’a tana yi musu tsiya tana kiransu da aminan juna, ayi faɗa a
sy hose ab as sy transtil Nasrin ta sha kunu bayan sun gaisa tay wuce cikin dakinta ta yi wanka ta canja kaya ta
shirya.
fito ta nemi shaya
ta iske Malaik
sha saboda yunwa take ji,
ta yi zubin abinci da karig
uku, sai turawa kawai take yi tana ci tanag murmushi tana zare ido.
Zainab ta ta shaidawa Nasrin cewars Dr.Hala ta dawo daga Amerika shekaranjiya, Iyayensu sun bada sako ta kawo musu dan haka ta je ta karɓo musu.
Nasrin ta ce gobe zata je ta karbo musu, Insha Allah.
Zainab ta sami waje ta zauna a kusa da Nasrin Wacce take lasar romon farfesu ba tare

da ta iya cin naman kazar ba. Zainab ta shiga jero mata tambayoyi akan in da suka je?
Nasrin ta yi shiru ta ki yin magana sai can jimawa sanda ta ga damar bata labari sannan ta fara bata labarin Jalo, hawaye na zuba daga idanuwansu su dukka, daman Zainab uwar tausayi har tafi Nasrin tausayi.
Suka sha kuka,Malaika tanazaune a gefe tana kallonsu ta na mamakin yadda masu kudi suke zubar da hawayensu a banza akan talaka. Da Nasrin ta gama abinda take yi a falo cewa Zainab ta nunawa Malaika boskwata(Boy’s Quarter) dan batason damu, ta
ba zata kara zama daki daya da Malaika ba. Nasrin ta shiga daki ta kulle kanta tabbas ba zata fito ba sai gobe. Bayan ta idar da sallar isha’i ta jawo wayarta ta ga kiran Jalo har sau uku nan da nan ta bi baya ta kira shi. Bayan sun gaisa ta bashi hakuri akan bata kusa da wayar ne a sanda ya kira. Ya tambaye ta gajiyar hanya sannan suka yi sallama suka kashe waya.
Ta hau facebook akan computer ta, ta sami lokaci a nutse ta karanta sannan itama ta

suffanta shi da Miji na gari mai sanin y
kamata ta tura masa. ya Ta kira Dina ta bata labarin abinda faru a Jalo da yadda suka iske shi. Sai hankalin Dina ya tashi matuka ta dauki dogon salati da kururuwa. Nasrin ta kasha wayar da sauri tana zubar da hawaye. Ta kwanta ta yi shiru tana tunani, bata san sanda bacci ya dauke ta ba saboda gajiya. Bata farka ba sai da asuba bayan ta idar da sallah ta koma bacci sai karfe goma sha biyu ta tashi ta yi wanka ta shirya ta fito, dauke da mukullin mota zata je gidan Dr.Hala, ta yiwa Zainab sallama ta fice. zaro gyale da gudu ta
Sai ga Malaika ta biyo bayan Nasrin tana yi mata magana, Nasrin bata kula ta ba ta shige mota ta kunna sai g Malaika ta daka tsalle ta shige gidan gaba. Ta dubi Nasrin ta yi murmushi ta ce, “Kawata wai har yanzu fushin kike yi min? Dan Allah ki yi hakuri.” ”
Nasrin ta dube ta da gefen ido ta kawar da kai gefe ta ci gaba da tukinta, daMalaika ta ishe ta da magana sai ta kure rediyon motar da karatun kur’ani. Basu tsaya a ko inaba sai a

ya Asokoro kusa da gidan shugaban kasa, gidan Dr.Hala kenan.
Nan fa Malaika ta bude baki tana kallo fuskarta cike da farin ciki.Suka wuce kai tsaye cikin katafaren get din gidan amma ba’a bude masu har sai da aka kira Dr.Hala a waya, ta ji muryar Nasrin sannan ta yarda a bude musu su shigo.
Malaika dai bata daina yi da bakinta ba. Tana faman santi tana kiran “Allahu akbar! Allahumma arzukuni. Wayyo arziki.’ ”
Haushi ya rufe Nasrin ko kallonta ba ta yi ba ta fito ta shiga gidan, Malaika tana biye da ita da sauri har suka isa katafaren falo mai kama da aljannar duniya. Nan fa Malaika ta yi ta taɓe-taɓe abubuwan da bata taɓa gani ba. Aka turo ‘yar aiki aka ce su shigo daki.
Suka wuce zuwa wani katafaren daki wanda girmansa ya kusa kaiwa gidan malaika gaba daya.
Setin gado ne da kujeru a gefe ga kayan kallo ga sanyin Ac da kamshi ko ta ina. Sai yanzu Malaika ta gane wacce suka zo gidanta. Ashe wannan hadadiyar matar nan ce

likita da suka hadu a Kano. Tabbas mafarkin ya fara zama gaske gata, ga hadaddiy dattijuwa. Ta kudiri niyyar ba zata fita daga gidan nan ba sai ta yi mata kwanaki biyu sannan ta nemo mata aikin yi koda na kula da gyaran daki ne.
Su ka zazzauna akan luntsumaluntsuman kujeru suka duka suka gaishe ta Ita dai Dr.Hala bata ma gane Malaika ba sai da ta ishe ta da surutu da kwatance sannan ta shaida ta. Haushin Malaika ya na ta nukurkusar Nasrin, sannan ta gyara zama ta fara tambayar Dakta lafiyar iyayenta.Dr.Hala ta fayyacewa Nasrin farin cikinta yadda Mamarta ta karɓe ta.Nasrin ta ji dadi da ta ji haka suka ci gaba da hira.
%. ‘Yan hidimar gida suna ta sintiri suna jere musu kayan marmari na ci dana sha a gabansu.
Dr. Hala ta duba agogo ta zare gilashin dake fuskarta ta ce, “bari in yi alwalla. Ku sha lemo barizan yi sallah.’ ”
Tamike a nutse ta tura kofar katafaren badaki sai kamshi ne yake busowa, Malaika ta

kama baki tana kallon aljanar duniya, daga nan ta sake gasgatawa kudi ya yi a rayuwa dan haka ko ta hali kaka sai ta nemo shi.
Ta damu Nasrin da surutu amma ba ta tanka mataba, lemo ta zuba kaɗan a kofi ta sha ta ci gaba da karatun jarida, yayin da Malaika ta yi goho ta dinga aika kayan dadi zuwa ga birnini tunbinta, Nasrin tana harararta da gefen ido amma bata yi mamaki ba kauyanci da jahilci ne babban ciwon da yake damun Malaika.
Dr.Hala na fitowa daga bandaki Nasrin ta shiga don yin alwalla itama. Malaika ta gyara zama tana murna ta sami damar yiwa Dakta Magana son ranta.
Malaika ta kalle ta, ta yi mata murmushi ta ce, “sannu ranki ya dade. Ki godewa Allah dan Allah Ya yi miki komai a duniya, DAMA NI CE ke.”
Dr.Hala ta dube ta ta yi murmushi ta ce, “Hmmm! Malaika! Ni kuwa tun dazu nake kallonku ina cewa a raina DAMA NI CE ku, kar ki yi fatan ki zama ni. Ki tambaye ni me yaşa nace haka?”

Malaika ta gyara zama ta na murmushi kai ka ce anyi mata albisuir da gidan aljanna saboda tana magana kai tsaye da mai kudi.
Malaika ta ce, “Me yasa kika ce haka? Dube ni fa talaka, ba ni da ko sisi ciki da waje, ba ni da gida ko fili balle Motar hawa, ba ni da kayan sakawa sai tsummokare. Allah Yaba ni miji talaka, ga yara sun taso a cikin talauci, iyayena a kauye talakawa ba su da komai…. “”
Dr.Hala ta yi dariya ta girgiza kai ta ce, “Allah sarki, ‘DAMA NI CE’ke. … Amma bari in nuna miki wani abu da za ki tabbatar da abinda nake nufi. kin gani.”
” Malaika ta juya da sauri ta kurawa Dakta ido tana kallon abinda ta nuna mata, sai idanuwanta suka hango mataabinda ya gigita ta, Malaika ta kwalla ihu ta tafi a guje ta nufi kofar bandaki wajen Nasrin, suka ci karo da Nasrin tana fitowa.
Malaika ta rirrike Nasrin jikinta yana rawa ya yin da hawaye yake zuba daga idanuwanta. Muryarta na karkarwa ta ce, “Nasrin! Zo
mu bar gidan nan yau idanuwana sun hango

DAMA NICE
abinda ban taɓa gani ba. Ashe haka masu kuɗin suke? Gara in koma kauye wallahi bazan zauna a gidan nan ba. Ke dai ki zo mu tafi zan fada miki abinda na gani.’ ”
Nasrin ma ta gigice ta rirrike Malaika tana tambaya ta ce, “meya faru? Me kika gani? Fada min mana.” ”
Malaika tana hawaye tana nuna Dr.Hala hannunta na karkarwa ya yin da Nasrin ta dubi Dr.Hala ba ta ga komai ba, Dakta dai tana sallah amma a zaune akan kujera.
Nasrin ta juya ta dubi Malaika, taga har yanzu jikinta rawa yake kuma ta na ja da baya ta ki sakin jiki. Daga nan Malaika ta buɗe ɗaki ta fice da gudu ya yin da Nasrin ta bi ta da gudu tana so ta damko ta amma ina Malaika ta wuce falo uku sannan ta keťa kicin, ta gangara farfajiyar gidan, ta na dankara gudu gami da ihu ta na neman agaji.
Nasrin tana biye da ita da gudu itama tana neman agaji tana cewa “a tare-a tare”
Nan da nan ma’aikatan gidan da masu gadi suka kawowa Nasrin dauki, aka dinga tsere da Malaika tuni ta yi tsalle ta kama get
|

tana neman hanyar dira, saboda ta ga halaka. Haka aka damko ta aka sauko da ita, nan take ihun da take yi ya karu kai kace ido ake kwakwale mata.
Nasrin ta rasa abinda yake yi mata dadi Malaika ta kunyata kwarai, koma dai me ta gani bai kamata ta tayarwa da kowa hankali haka ba. Tabbas Malaika ta zame mata annoba a rayuwarta, hawayen takaici ne kawai ya ke kwaranya daga idanuwan Nasrin. Tana ta addu’a a zuci Allah ya rabata da Malaika dan ta zame mata barazana a rayuwarta.
Dakayar aka samu Malaika ta nutsu ta daina ihu, Nasrin ta kama hannunta suka shiga cikir falo amma fa Malaika ta ki yarda ta koma cikin dakin likita saboda tsoro. Nasrin ta shiga dakin Dr.Hala a sanyaye ta iske ta har yanzu tana salla a zaune akan kujera. Ta shinfida abin sallah ta tayar da ikama. Bayan sun idar sun dade suna ta kwararo addu’oi kowacce tsakaninta da ubangijita take karanto abinda da ya dame tana neman agaji a wajen Rabbil samawati.Bayan sun shafa sai suka kalli juna +

suka yi murmushi a lokaci guda sannan suka gaisa.
Nasrin ta ce, “Mummy Hala kina jina da kawata ta firgita ta fita da gudu ko? Me yake faruwa ne?”
Dr.Hala ta kyalkyale da dariya ta ce, “ina Malaikar take?”
Nasrin ta nuna da yatsa ta ce, “tana falo ai ba zata shigo ba.”
Dr.Hala ta ce, “mu je falon in bata labarin rayuwata ko zata daina sha’awata.’ ”
Suka fito falo suka iske Malaika ta yi tagumi, tana ganin Dr.Hala sai ta zabura ta gyara zama ta sake takurewa.
Bayan sun zazzauna akan kujera kowaccensu tana kallon Malaika tana dariya, sai Malaika ta zaci sun shiryo wani abu ne da za’a cutar da ita ta fára tunanin ma ko a gidan yankan kai take. “.
Dr.Hala ta dubi Malaika ta kira sunanta cikin marainiyar murya ta ce, “Malaika! Na fi sha’awar rayuwarki akan rayuwata shiyasa na ce kada ki yi fatan ki zama ni. Ga kudi ina da shi, ga kyau ina da shi amma bana jin daɗin

rayuwata. Da za’a kwace komai a bani lafiya kamar ki da na ji dadi, da za’a kwace dukiyata a bani haihuwa kamar ki da na ji dadi, da za’a Kwace dukiyata dukka a ba ni miji kamar ki da na ji dadi.”
Sai Nasrin da Malaika suka hada ido suka juyo gaba daya suka kalli Dr.Hala a lokaci guda, cike da dimuwa.
Hala ta surnano da hawaye ta sunkuyar da kai kasa ba tare da ta kara cewa komai ba. Hankalin Nasrin ya tashi.
Ta gyarazama ta fada cikin harshen Turanci ta ce, “Mummy ki bamu tarihin rayuwarki saboda ya zama darasi a rayuwarmu, musamman Malaika da take ganin kamar kudi ya fi komai muhimmanci a rayuwa.
LABARIN DAKTA HALA Ta ce,”sunana Hafsat ana kirana da Hala kasancewar Mahaifiyata balarabiya ce yar asalin kasar Turkey, Mahaifina bafillatanin Adamawa ne.
Ya je karatu can suka hadu suka yi aure aka haife ni, a wajen haihuwata ta rasu ta barni

a hannun Mahaifiyarta dan haka a hannun Kakata na girma.”
Nasrin ta gyara zama ta langwaɓe kai cike da tausayi. Ya yin da Malaika ta fara jiyo harkar Jajayen fata a ta san tabbas Babanta mai kudi ne.
Dr.Hala ta ci gaba da cewa “Mahaifina ya dawo kasarsu Najeriya ya yi aure-aurensa amma ya kan zo ya ganni jifa-jifa nima na kan ZO.
Na tashi a kasar Turkiya a in da na yi karatuna gaba day daya, na tashi a cikin rashin kwaɓa babu tarbiyya, na hadu da saurayin da nake matukar so mai suna Jaddi tare muka yi karatu a jami’a babu abinda muke yi sai watsewa, na sha yin ciki ina zubarwa ashe kwayayen haihuwar gaba daya na zubar. Na aaawa ashe zama cikakkiyar likita amma babu aure na zaci Jaddi yana so na ne da gaske kuma zai aure ni amma ya ki aurena, kullum yana yi min karyar zai aure ni amma daga karshe na ji labarin ya auri wata a ɓoye. Hakan ya sa na hargitsa na je na cinnawa gidansa wuta ya kone shi da amaryar amma ba su mutu. “

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Home
Account
.st0{fill:#000000;} PDFs
Chapters
Loved