Chapter 6: Chapter 6
Nasrin da Malaika suka zazzare ido gami da dafe kirji.
Nasrin ta tambaya “Me yasa kika aikata wannan danyen aiki?”
Dr.Hala ta yi murmushin takaici ta ce, “sharrin zuciya, dan haka aka ɗaure ni na tsawon shekaru dakyar aka samu aka fito da ni bayan na shekara biyar cur a gidan yari. Dan daurin shekaru sha biyar aka yanka min da aka sami canjin Gwamnati na sami alfarma.
Na dawo ‘yar shaye-shaye saboda bakin cikin rayuwa kullum a buge nake hakan ya sa kowa ya tsane ni, Kakata kadai ke kaunata ko da yaushe tana yawo a gidan rawa (club) tana kamo ri dan acan nake kwana a buge.
Watarana nasha na bugu ina tukin mota na yi mummunan hatsari a take kafata ta hagu ta tsinke a take ta fita daga jikina. Yanzu haka bani da kafa sai ta karfe da ita nake amfani.” Ta bude musu kafar ta sa hannu ta kwance kafar sai ga kafar karfe a hannunta. Malaika ta daka tsalle ta fado kan Nasrin ta kankame ta tana salati. .
a tana salati
cinud teed
Hankalin Nasrin ya tashi ta fara karanto “Innalillahi wa’inna ilaihi raju’un. Allah Ka sa mu gama da duniya lafiya. Allah Ya sa mu yi kyakykyawan karshe.’ ”
Dr.Hala ta ɓarke da kuka yayin da Nasrin da Malaika ma suka rungume juna suna kuka. Har na wani lokaci.
Malaika ta koma kan kujerarta ta zauna ta yi tagumi tana kallon kafar karfen da Dr.Hala ta wurgar a kasa tana ta godewa Allah a zuciyarta da Allah Ya barta da kafafuwanta da hannayenta ba’a gutsiri komai daga jikinta kan ba.
Dr.Hala ta ci gaba da cewa “a sanadiyyar wannan bakin cikin ya sa Kakata ta hadiyi zuciyata ta rasu, na zamanto sai ni kadai a gidan daman ‘ya’yanta da jikokinta sun tsane ni sai tsanar ta karu suna kirana da wacce ta kasha musu uwa.
Hakan ta sa suka kore ni na haɗo na dawo Najeriya garin Babana Babana Adamawa, Alhamdulillahi! Yana nan a raye tare da iyalansa matansa uku da yara ashirin da hudu.
komawa jami’a na zama Ya yi murna da ganina anan na sake tabbar likita (consultant) na fara aiki a asibiti. Na yiwa kaina faɗa na daina shan komai sannan na koma ga Ubangijina gaba daya na koma bautarsa ina tuba akan Ya yafe min kurakuren dana tafka a baya. Allah mai jikan bayinSa Ya sa na sami nutsuwa sannan ya hore min arziki da hanyoyin daukaka da samun kudi. Na yi tashe a garinmu a babban asibiti saboda na san abinda nake yi, na san makamar aiki har na bude asibiti nawana kaina. Daga baya na shiga harkar siyasa na san manyan gwamnati har na dawo Abuja da zama na kuma sami sukunin tafiya Amerika na karo karatu har Allah ya kawo ni wannan matsayi ina kusa da shugaban kasa.”
Akt Nasrin ta langwaɓe kai ta ce, “Allahu Akbar! Yaya batun aure kuma da haihuwa?” Dr.Hala ta girgioza kai ta ce, “Allah bai sa ina da miji a duniya ba, babu irin kokarin da banyi ba, haka mahaifina da abokan aikina duk mai kaunata sai ya yi kokarin hada ni da wani mu yi aure amma sai Magana ta fara nisa sai su
fasa. An ce bakin aljani ne, an ce asiri ne amma ni na yarda da cewa daga Allah ne. Yanzu ina da shekaru hamsin da hudu ban taɓa aure ba har na fitar da rai, bana bukatar in yi auren ma. Na riga na nakasa duk sanda aka hango kafar karfe sai su gudu ina zargin wannan ma yana cikin matsalata.’ ”
Nasrin ta dora hannu aka zata fasa ihu ta daure ta sauke hannun, hawaye na zuba daga idanuwanta.
Dr.Hala ta matse hawaye ta ce “Malaika! Tun ranar da na fara ganinki na ke fada a raina DA MA NI CE ke kina da yaranki a gidan mijinki. Ni na rasa wannan kuma ya wuce ni har abada, bazan taɓa yin aure ba balle ir haihu. Ba zan taɓa dawowa daidai ba kamar ki tunda na rasa kafata na zama gurguwa. Ba ni da masu gadon uwar dukiyar da na tara saboda Mahaifina ya tsufa lokaci kawai yake jira babu abinda zai yi da dukiyata sai dai yaransa su gada wadanda ba kaunata suke yi ba ko kadan. Ni kadai mahaifiyata ta haifa ta tafi ta bar ni. Amma ina tallafawa marayu da gajiyayyu kuma ina rike su har in aurar.”
Kuka ya ci karfin Dr.Hala har ta kasa ci gaba da magana.
Nasrin ta zabura ta je ta dauko kafar ta mikawa Dr.Hala ta ce, “ki mayar da kafarki kada ki damu lilkita na ki mai sauki ne idan kika ji labarin Dr. Jalo.
Da Dr.Jalo zai ganki da sai yace’DA MA shine ke, saboda shi baya tafiya, baya iya tsayar da fitsari da bayan gida, ya rasa Lakarsa wanda bana tunanin akwai maganin da za’ayi masa ta dawo dai dai har abada.” ”
Dr.Hala ta tsagaita da kukan ta kuarawa
Nasrin ido sanan ta tambaya “waye Dr.Jalo? Nasrin ta ce, “wani abokina ne da muka hadu a facebook kuma Allah Ya jarrabe ni da matukar kaunarsa sai bayan da muka ga juna sannan na tabbatar da yadda yake. Likita me ya kamata ya yi ya sami sauki ko kuma ina ya kamata ya je ayi masa aiki ya warke? Ina son Jalo zan iya salwantar da duk abinda na mallaka da wanda iyayena suka mallaka dan in ceto rayuwarsa. وو
Malaika ta zabura ta kalli Nasrin cike da mamaki ta sake gasgata cewar lafiya ta fi
komai muhimmanci a duniya ba kuɗi ba. Ta. sake yarda babu abinda ya fi soyayyar gaskiya dadi a duniya hakika Nasrin tana kaunar Jalo sona hakika, ba dan kudinsa ba, ba dan kyawunsa ba.
Dr.Hala ce ta katse tunanin da Malaika ke yi ta ce, “maganar gaskiya idan Laka ta taɓu sai dai dibaru,shawarar da za ki bashi ita ce kice masa idan ya sami kamar awa guda ya yi kokari ya mike tsaye yana dogara sanduna yana jan kafafuwan tunda kin ce hannayensa suna amfani. Ya kokarta ya shiga bandaki ya sa hannu ya matsa cikinsa da karfi da mararasa ya turo bayan gida da fitsari su fito sai ya koma bayan kamar awa gida ya sake komawa ya yi haka zai yi ta yi. Za ki ga ya daina amfani da katata kuma zai daina zubowa ba tare da ya shirya ba. ”
Nasrin tana sauraronta tana gyada kai da alama ta fara jin farin ciki a kalla dai zai rage wani abu na alamar samun sauki. Ma’aikata suna ta safa da marwa suna
jere musu abinciccika kala-kala akan tebur
DAMA NICE… amma tashin hankali ya hana gaba dayansu ci. A haka suka yi sallama suka tai.
Dr.Hala ta bawa Nasrin sakon daloli da iyayenta suka aiko mata da kayan jarirai na Zainab, ta bawa Malaika atamfa super Holland kyauta.
Su na godiya suka tafi suna tafe a mota kowaccensu ta yi jugum babu wacce ta ke iya magana. Haka suka shiga gidan Zainab sokoko babu laka a jikinsu, kallo daya Zainab ta yi musu ta tabbatar suna cikin damuwa amma ta yi zaton fadan suka tafka a hanya.
Bayan Nasrin ta zazage sakon a gaban Zainab sai farin ciki ya kama Zainab. Ta tambaya lafiya ta gansu basa walwala. Nasrin ta bata labarin Dr.Hala gaba daya, sai Zainab ta gigice ta daga hannu sama ta na yiwa Allah godiya da Yaba su rai da lafiya da abinda lafiyar zata ci.
Gaba dayansu suka yi tagumi ba tare da wani ya iya ci gaba da magana ba har zuwa lokaci mai tsayi. Malaika ta fasa kuka ta ce, “na ko yi
darussa, na lura da cewa damuwar masu kudi
har ta fi ta mu ta talakawa. Wallahi a zatona masu kudi ba su da matsalą ko kadan sai na iske ko da yaushe idanuwansu suna zubar da hawaye har ma suna sha’awar da DA MA su ne mu, tabbas lafiya itace komai. Zan koma gida in zauna in yi hakuri da yadda Allah ya ajiye ni.’
Nasrin ta matse hawaye ta ce, “nima zan bar kasar nan jibi in koma gaban iyayena in zauna bazan iya jira har sai na gama bautar kasar ba. Na rasa farin cikin rayuwata Dr.Jalo, na ji gaba daya rayuwata a Najeriya bana jin dadi. Zan koma in da Allah ya ajiye ni in ci gaba da addu’a Allah ya hada ni da farin cikin rayuwa amma kudi ba komai ba ne idan babu farin ciki babu lafiya.”
Su ka yi tagumi ba tare da sun iya magna ba. Can Nasrin ta mike ta dauki mukullin mota ta shiga daki ta dauko passport dinta da Jakarta ta fito da alama wajen sayen tikiti zata tafi ta fice da sauri.
Malaika ta tashi ta tafi tana haɗa kayanta a cikin akawati da alama ta yiwa kanta fada ta ga bala’in da ya fi nata.
Washe gari da safe misalin karfe takwas na safe Malaika ta tashi ta shirya ta fito da akwatinta ta bubbugawa Nasrin kofa, kasancewar Nasrin din ma ba bacci take yi ba tana ta waya da Jalo tunda asubah. Ta shaida masa shawarwarin da Dr.Hala ta bayar, kuma ya yi Amanna.
Daga karshe ta yi masa sallama a kan washegari zata bar kasar nan ba zata dawo ba, amma ta yi masa alkawarin yin bincike a game da masu irin larurarsa in har an sami mafita zata ciko a kai shi zata dauki nauyin yi masa aikin.
Ya yi mata godiya sosai gami da yi mata fatan alkhairi. Ya nuna matukar damuwarsa da ya rasa ta amma ta ce kada ya damu akwai waya akwai facebook ko da yaushe zasu din ga haduwa.
Bugun kofar da Malaika ke yi ta sa ta katse wayar ta je ta bude sai ga Malaika a tsaye
a bakin kofa da akwatinta da alama ta shirya tafiya gida.
Nasrin ta yi mata iso ta shigo ta zauna a sanyaye, bayan sun gaisa sai Malaika ta fara magana cikin marainiyar murya.
Ta ce “Nasrin! Na gode da kulawarki. Na gode da jahadin da kika yi akaina har sai da kika ga na fahimci rayuwa. Ina miki fatan ki gama da duniya lafiya ki sami rabauta da aljanna. Na gode da dukka hidimomi da kika dade kina yi min. Na gode da jajircewa da kika yi akan kokarin gyara aurena da Shamaki. Lallai na zalunci kaina, shamaki bai cuce ni ba ni na cuce shi. Idanna fada miki cin mutuncin da na yi masa kafin ya rubuta min takardar saki hakika bana jin har abada zai iya yafe min ya dawo ya ci gaba da zama da ni.”
Malaika ta rushe da kuka yayin da Nasrin ma hawaye yana surnanowa daga idanuwanta ta kurawa Malaika ido ba tare da ta san abinda zata fada mataba. Sai girgiza kai ta ke tamkar kadangaruwa.
Malaika ta ci gaba da cewa, “abinda ya fi tayar min da hankali ma shine yadda iyayena
Jamilu Umàr Tanko JUT
suka tsine min, auren Uwata da Ubana ya rabu a dalilin na zaɓi in taho Abuja akan na ki yin biyayya a maganarsu naki yin zaman aure. Na shiga a uku na lalace, ta inazan fara harhado rugurgujajjiyar rayuwata alhali ta rugurguje?”
Nasrin ta taso da sauri ta dafa kafadar Malaika tana lallashi ta ce, “tabbas kin tafka kuskure amma ba ki makara ba tunda iyayenk: suna raye kuma Shamaki yana raye na san ba yi aure ba kuma har yanzu na san yana sonki, zai yi hakuri da ke saboda yaranki da kuma kaunar da yake yi miki.’
Malaika ta goge hawaye ta ce, “Allah Ya sa hakan, amma tabbas Shamaki ya yi fushin da bai taɓa yi ba, ya yi furuci a gaban kowa furicin da bai taɓa yin irinsa ba. Ya jawowa kansa bala’ai da tsinuwar ubangiji ta tabbabata akansa in har ya kara zama da ni, yace ya hakura da ni in har ya cika dan halas a cikin uwarsa da ubansa. Na shiga uku na lalace Nasrin yayazan yi?”
Nasrin ta girgiza kai ta matse hawaye ta ce, “kada ki damu, ki je kiyi ta addu’a, kuma ba da baki za ki fada musu kin shiryu ba
kamata ya yi su gani da idanuwansu su tabbatar kin canja sai su tausaya miki su yafe miki.’ ”
Malaika ta surnano da hawaye ta ce, “ki yafe min Nasrin na jawo miki zargi da zagi a wajen Shamaki da iyayena. Gaba ɗaya suna zarginki da ke kika hure min kunne har suna kiranki da karuwa mai zaman kanki.”
Nasrin ta girgiza kai ta ce,”ba komai Malaika na yafe miki, na yafe musu suma kuma In sha Allah za su gane gaskiya.” ”
Nasrin ta dauko kudi naira na dukan Naira dubu ashirin ta bata ta ce ta je ta yi jari, sannan ta dauko mata kaya kala uku masu kyau a cikin nata da take sawa ta bata, da yake kirar jikinsu daya.
Malaika ta yi ta godiya matuka sannan suka dingumo suka fito zuwa dakin Zainab suka iske ta a kwance ita kadai. Malaika ta durkusa ta gaishe ta gami da yi mata sallama. Zainab ta yi mata fatan alkhairi sannan suka fito, Narin ta dauki motarta ta kaita tasha ta shiga mota ta zauna, suna dagawa juna hannu suna zubar da hawaye da alama kowannensu tana kukan rabuwa suna kuma kyautata zaton a
yau wannan rabuwa ta su itace ta karshe ba zasu kara ganin junansu ba..
Allah sarki sabo turken wawa! Bayan mota ta cika direba ya tashi mota suka fara tafiya sai Malaika ta runtse ido hawaye zazzafa ya fara kwaranya daga. idanuwanta, kamar daga sama ta ji an mika mata hankici. Tana daga ido sai ta ga mutumin da ke kusa da ita ne ya tausaya ya bata dan ta goge hawayenta. Amma fa ta yi matukar razana a lokacin da ta yi ido hudu da shi, Shamaki ta gani fuskarsa cike da damuwa. Ya kawar da kai gefe dan baya so ‘yan cikin motar su fahimci wani abu. Mamaki mabayyani ne yake kwaranya daga fuskar Malaika ta kasa tantance daga in da ya diro. Shin binta yake yi a baya ne ko kuwa Katari aka yi? Shin daman Shamaki ya taɓa zuwa Abuja ko kuwa biyo ta ya yi kawai? Shin sonta yake yi har yanzu ko kuwa so yake ya damke ta da laifi dan ya fadawa duniya koi ta wacece? ” tana wajen Shamaki sai
Amsar tambayar dai kash! Ba ta ga fuskar jero masa wadannan tambayoyi ba.
isa garin Kano.
Bai ce mata uffan ba itama haka har suka
*** *** *** ***
Washegari da daddare da daddare Zainab da maigidanta Salis suka kai Nasrin filin jirgi na Abuja tare da rakiyar kawarta Dinah.
Tabbas Nasrin ta dage sai ta tafi Amerika amma tana ta kuka kamar an yi mata dole, Zainab da Dinah ma suna taya ta yayin da Salis ya dinga basu hakuri amma sun kasa dainawa. Nasrin tana ji a ranta kamar idan ta tafi mutuwa zata yi ba zata dawo ba, haka Zainab ma tana ganin kamar idan ta zo haihuwa mutuwa zata yi ba zasu sake haduwa ba. Bakin cikin Dinah kuwa shine ga aurenta ya zo. ba za’a hada aurenta da na su Nasrin ba dan gaba daya sun gama ɓaɓewa da Fu’ad an rabu.
Babu yadda zasu yi dan jirgi baya jira dole suka saki Nasrin ta wuce ciki ta karɓi (boading pass)na tafiya. Tana tafe tana waiwayensu suna waiwayenta suna dagawa
juna hannu, yayin da hawayen da yake
kwaranya ya yawaita.
Allah sarki rabuwa ba mutuwa ba!
***
*** ***
Nasrin ta shiga cikin Jirgi ta zauna kafin a gama shigowa ta jawo wayarta ta kira Dr.Jalo, tana jin muryarsa sai ta fashe da kuka. Shima kukan yake yana mai yi mata nasiha akan ta zama mai hakuri da tawakkali.
Ya shaida mata yadda yake ji idan ya tuna rayuwarsa ta baya a lokacin da yake da lafiya yana takawa kamar kowa dan haka kada ta zamanto mai yiwa Allah butulci dan Ya hada su kuma Ya raba su a sanda Ya so. Ya yi mata fatan alkhairi itama ta yi masa amma ta roke shi da ya bar cikin dajin ya koma gida ko asibiti, bata jin dadi idan ta tuno irin masifar wahalar da ta baro shi a cikin dajin nan. Ya yi mata alkawarin za su koma gida su zauna su jira ranar da Allah (SWA) Zai yanke musu wannan wahala itace ranar da Allah Zai dauki rayuwarsa. Ya na da tabbacin mutuwa ita kadai
ce hutu a gare shi. Kuka ya hana su ci gaba da yin waya sai ta katse.
Ta kira Mahaifiyarta ta shaida mata har ta shiga jirgi idan sun karaso a zo a dauke ta a filin jirgi. Hakika Momi ta yi farin ciki da jin haka ta yi mata fatan Allah Ya kawo ta lafiya.
Daga karshe ta kira Dr.Hala ta shaida mata yau zata koma Amerika, tana fatan idan ta shigo kasar zata neme ta. Dr. Hala ta yi alkawarin yin haka ta yi mata addu’a gami da fatan alkahairi.
Ta na kashe wayar sai ga kiran Dina, Nasrin ta amsa da sauri, Dina tana Magana cikin lallashi ta ce “Nasrin! Ki yi hakuri idan kin je ku daidaita da Fu’ad ku yi aurenku. Kin ga wanda kike so din ya nakasa ba yadda zai yi ya aure ki, Fu’ad ne kadai ya dace da rayuwarki shine wanda za ki ji dadin zama da shi dan hutu ke ma ‘yar hutu. ”
Nasrin ta fusata ta ce, “Dinah, Wai shin kin manta ko waye Fu’ad? Kin manta cin mutunci da rashin kulawar da yake yi min? Kin manta da cewa idan na aure shi bakin ciki zai tula min saboda girman kai da ji da kan da N.
yake yi min? Kin manta da tulin ‘yan matan da yake da su a turawa da bakaken fata amma duk da haka ki ce in aure shi? Ba ruwana da abinda yake da shi in har ba ni da kwanciyar hankali da farin ciki a ransa. Allah shi Ya san dalilin da Ya hada ni da Jalo kuma ya raba mu. Allah Shi yasan dalilin da Ya mayar da Jalo nakasasshen da ba zai iya moruwa ba. Na rasa nutsatstsen saurayi, mai kamala da sanin ya kamata. Na rasa wanda na ke so kuma wanda yake sona. Kawata! Ki yi min addu’a Allah Ya ba mu yadda za muy da ni da Jalo amma ba Fu’ad ba.”
Dina ta yi kasake tana gasgata maganar
Nasrin ba tare da tana da bakin gyarawa ba. Ta yi ajiyar zuciya ta gyada kai ta ce, “haka ne kawata, Allah Ya bawa Jalo lafiya Ya zaɓa miki abinda ya fi alkhairi a rayuwarki. Ina yi miki addu’a Allah ya kai ki gida lafiya ki same su lafiya. Ki gaida Mummy da Daddy dan Allah.”
Nasrin ta ce “zasu ji. Amin. Na gode. *** ***
DAMA NI CE
Jirgi ya lala sama yayin da Nasri ta rutse ido sai hawaye ya surnano mata, kamar daga sama ta ji an nanika mata hankici a hannunta tana bude ido ta dubi mutumin da ya ke zaune a gefenta ne ya bata, tabbas ta firgita ta gigice a lokacin da suka yi ido hudu da Fu’ad.
A Sai ta zazzare ido saboda mamaki gami da fargaba mai tsanani. Da alama yagama jin wayar da duk ta yi da su Jalo, ya gama jin wayar da ta yi da Dinah. Sedeg nen sonsand
Ta dube shi sai ya yamutse fuska ya kawar da kai gefe ya sha kunu ransa a ɓace. Lallai dole ransa ya ɓaci da jin irin wadanan munannan kalamai da ta furta akansa.(TUL)
Abin tambaya shine caman Fu’ad yana kasar amma bai zo ya neme su ba kuma bai faɗawa kowa yana nan ba? Shin me ya kawo shi kasar, uzurinsa ne ya kawo shi ko bibiyarta yake yi?
Rigiji gafji! Wani kaya sai amale! Basu kara cewa juna uffan ba har suka isa kasar Amerika.
| Txost rem!! ulims!|
Kash!
Anan zan dakata mu hadu a littafin DAMA NI CE… Kashi na
Mu ji yadda zata kasance.
*Tsakanin Nasrin da Dr.Jalo
*Tsakanin Malaika da Shamaki da
Iyayenta.
*Tsakanin Nasrin da Fu’ad.
*Tsakanin Nasrin da Mahaifiyarta.
*Yaya rayuwar
kasance nan gaba?
kowannensu zata
Ku biyo ni ku sha Labari.
Ta ku har abada
Jamila Umar Tanko.
A DADE ANA YI SAI GASKIYA. Ina makaranta da ‘yan kasuwa? Ina masu sayen daidai ko sari? Inamasu neman littattafan JUT gaba daya tun daga kan ‘KWANA ASHIRIN DA HUDU’ zuwa ‘DA MA NI CE’ marmaza ku garzayo shagona mai suna
‘ADON DAWA BOOKSHOP’ da yake layin layin ‘yan littatfai ‘yan littatfai SABON GARI KANO. KASUWAR
Farashi cikin sauki. sauki.
Abubakar akan
A tuntubi
wannan lamba domin neman karin bayani.
Sai kun zo.
MATA ADON GARI IN BA KU BABU GARI, IDAN KUN YI YAWA GARI YA BACI.
*Idan kina neman shawara akan zamanki na aure.
*idan kina da matsaloli ta kowanne ɓangare. *Idan ki na da korafi.
*Idan mai gida baya jin daidai.
*Idan fatar jikinki tana neman gyara.
*Idan ki na so ki rike kamshi na ciki da waje.
*Idan abubuwa sun motse ki na so ki ciko.
*Idan ki na bushewa.
*Idan kina so ki zama marubuciya. *Idan ki na neman shawara akan sana’a dan taimakon kanki da kanki.
MACE SAI DA GYARA Ka da ki bari ki zama bora, ka da ki bari Oga ya raina ki, ka da ki bari kishiya ta raina ki. Yanzu ba’a kishin fada sai dai a yi kishin gyara da kyautatawa Mai gida. Ga wata dama ta samu JUT ta bude kofar ba da shawarwari da bada
gudunmawar abubuwan gyara, a tuntuɓe ni a wannan layi .
TSARABA:
Ki nemi tumatur mai kyau ki raba gida biyu ki goga a fuskarki kafin ki shiga wanka. Ko ki matse tumatur a cikin ‘peak milk’ sai ki goga a fuska da wuya. Ki bari bushe sannan ki murje tas. Idan kin shiga wanka kada ki wanke fuskar da soso, kada ya
ki saka ruwan zafi idan za ki wanke fuska
da sabulu da ruwan sanyi za ki wanke.
Za ki ga yadda fuskar zata din ga gyalli kamar tangaran. Fuska bata son jagwalgwalo da yawan taɓawa. Haka a guji dafke-dafken mayuka daban daban a fuska.
Masha Allah!
Allah Ya sa mu dace. Amin!



