Chapter 10: Chapter 10
Muhammad Farsi. Yana isa kamar yadda yake cewar ya kagauta lokacin nan yayi ita ma sarauniya Siyamata saka hadimanta mafi kusanci da ita cewar a duk lokacin da waziri ya iso su sanar mata domin ta gaggauta fitowa dakin gani, aikuwa yana bargar ajiyar dawakai sai ga wani cikin masu yiwa Sarauniya hidima daga wajer gidan Sarki ya zo ga Waziri ya sanar da shi cewar yayi maza ya isa dakin gani tana saurarensa a can. J
Batare da bata lokaci ba ya isa wannan guri. Babu wani dogon bayani ko gaisuwa ta dubi Waziri Ja’afar ta ce “Muna cikin babbar matsala da musifa abu biyu ya faru a lokaci guda wadanda dukkaninsa asara ce mu a wajenmu, Yarima Yazid yayi mummunan kuskure inda ya je ya fafata da Benjamin harma sun yiwa juna rauni, labara ya zo mana cewar Yarima Abbas ya isa birnin Shamnum ya kuma gyara dukkanin matsalolin da muka kunna a cikin birnin abin tashin hankali ace Sarki ya gano muna da hannu wajen zuga Waziri Ja’afarda mahaifiyar yarima Hilal, idan har Sarki Muhammad ya ji wannan a lokacin da ya nemo lafiyarsa kashinmu ni da kai ya bushe sannan burinmu a kan Yarima Yazid bazai taba yiwuwa ba, abu na biyu kuma yanzu haka Sarki ya fara zargin akwai wani kulli da aka yi masa amfani da shi dan dauke hankali a kan mulkinsa da yake yi kasalada gajiyawa da rashin maida hankali da aka yiwa kwakwalwarsa aiki, ya fara tunanin neman magani don ya ce dani zai nemi magani har ma a jiyan ya fita da yammaci na sa abin bayansa bai tsaya ko ina ba sai gidan Shuhul Islam, bayan nan kuma suka zaga gari suka dawo gida, yanzu ya kai Waziri Ja’afar mene ne abin da kake ganin za mu yi domin magancematsalolin nan da za su saka mu asarar duk tanadinmu?”
Waziri Ja’afar yayi a jiyar zuciya gami da cewa “Ranki ya dade akwai babbar barazana da matsaloli da sai mun yi da gaske za mu iya kawo karshensu, abu na farko shi ne rashin kwarewa ne muraran yarima ya aikata wajen fito na fito da Benjamin, abu na biyu kuma ba mu isa mu hana Sarki neman magani ba, idan har muka ci gaba da hanawa ko Magana da likitocinsa ba kowane likita bane zai ji shakka ko tsoronmu kamar yadda na baya suka yi, ba ma musan a ina zai samu likitan ba bare mu yi tunanin wasu dabarun tsoratarwa ko zuba dukiya don hana aikin na
hakika, a shawarce mu ja da baya, matukar ba so muke mu kwana kiyama ba, mu taya Sarki neman magani idan ya so daga baya sai mu sake sabon shiri”.
Tun da ya fara Magana zufa take keto mata domin ta san dama zai iya biyowa ta wannan bangaren domin shi kansa ta siye shi ne ta dalilin zai ci gaba da zamaa matsayinsa na waziri matukar in Sarki ya mutu danta ya zama Sarki, tana amfani da shi ne saboda soyayyarsa da mulki da kuma kudi, da mugun kishin da yake da shi ga duk wadda yaga ya fishi kusanci da Sarki, sannan ta sa Sarki ya yafe masa kurakure masu yawa.
“Kana ganin idan Sarki ya dawo hayyacinsa, zai ci gaba da zama da kai amatsayin wazirinsa bayan akwai korafe korafe akanka da dama,, ka da ka manta badakalar kasuwa, masarautar Shamnumda hadakar da kake yi da kafurai”.
Ya dube ta cike da mamaki, ya san ta san yana da alaka da shamnum da wasu korafe korafe amma bai san ta san badakalar da yake yi a kasuwa ba, da kuma hadaka da yake da su da kafurai. Nan take hankalinsa ya tashi ya bude baki zai musa mata “Waziri Ja’afar babu wani taku da kake yi a cikin masarautar Bahara da ban san da it aba, na zabeka ne saboda na san za cika min burina na ganin mun gaji sarautar bahara daula ta dawo hannun dana, idan har ka ce zaka juyamin baya kwana biyu uku kacal yayi yawa kanka zai rabu da gangarjikinka domin kalma daya tak na sanar da sarki na kafa shaidun na gaskiya kashinka zai bushe, ka ci gaba da amsarumarni daga wajena mu gudu tare mu tsira tare”.
Ya saka babbar rigarsa ya share gumin da yake tsattsafowa daga jikinsa hankalinsa ya kara ta shi y ace “Ranki ya dade wane ni na juya miki baya, baki fahimce ni ba ne…. ”
“Na fahimceka, tunda za ka ci gaba da zama da Sarki a matsayin waziri baka da damuwa, za ka koma kalallaba Yarima Abbas ka dinga yi masa biyayya domin ganin cewar ya taka matsayin zama Sarki daga nan shikenan ka tafi kabarmu duk ukubar da ta zo kan mu za ta afka, idan har ka yi ganganci to la shakka kwana uku kacal mutuwa za ta yi maka sallama”.
Ta na fadin hakan ta mike daga inda take bata kara saurarensa ba ta wuce cikin gida, jikinsa a sanyaye haka ya mike lallai mata shaidanu ne na gasken-gaske zikirin shaidancin matan nan da su ya isa fada kwata-kwata jikinsa babu kwari.
Tun a daren jiya da Jarumi Umar ya dawo daga fafatawa da Mangalawa ya zamana cewar cikin kauyen Nur suke cikin shirin domin suna da tabbacin matukar sun fahimci daya ne daga cikin kauyan ya yake. su,to babu shakka za su biyo sahu, don haka tun daga farkon shigowa garin aka kara masu tsaro da masu kai rahoton farmaki, saboda kasancewar cikin shiri.
Lokacin da Umar suka kadaita da mahaifinsa sai ya ce “Ya Abbana, ka yi sani cewar zan iya ja da bataliyar Mangalawa guda ni da abokaina, akwai yara kanana da mata a cikin birnin nan, saboda haka zama na a tare da ku akwai babban hatsari, musamman in sun gano cewar ni din danka ne, zai fi kyau da muhimmanci na fita daga garin nan na nausa wani
wajen yadda za su biyo bayana…” Abdullahi ya jinjina kai game da duban dan nasa ya ce “Ya kai dana, shin baka yi sani cewar rayuwa kashi biyu ta kasu ba, rayuwa ko mutuwa, Mangalawa sun iso cikin yankin Bahara da mayaka runduna runduna, wannan alama ce ta gagarumin yaki ya tunkaro kasar Bahara, sulhu da Mangalawa ba zai taba zama alkairi ba, domin idan har Mangalawa sun nemi a yi sulhu wahala suka sha kuma sun nemi sulhu ne domin a kyale su su je su kara shiri. Allahi ya ji kan Sadauki Nabaru, a waccan lokaci tarihi ya nuna cewar kada a bar kowane Bamangale a doron kasa, matukar bai yi imani da ubangiji musulunci ba domin ba za su taba saduda ba, a lokacin da yaki ya ci su aka kashe sama da kaso takwas cikin goma na mayakansu, sai suka yadda da a zauna a yi sulhu, wadda a wannan lokacin idan da an yake su an gama da babin wata fitina, amma Ahlul kitab su ne suka yi uwa da makarbiya wajen tabbatar da wannan sulhu, a lokacin da Nabaru ya fadi gaban Sarki na wancan lokacin ya ce ka da a taba yadda da wannan sulhu tunda an nemi a farko sun ki suka fito yaki aka yake su. Amma Sarki da yake yana son zaman lafiya yana ganin abin kamar aikin gama ya gama an riga an ruguje su, sai ya yadda da sulhu tun kafin a je ko ina ana samun matsaloli kadan kadan daga Mangalawa, da suka tumbatša sai da suka nemi yadda za ayi a kasa dukiyar kasa a basu kasansu nan ma aka yi musu lamuni, akan wannan haraji an sha samun sabani da su, amm son zaman lafiya ake biye su, saboda a zauna lafiya. Yau ita ce ranar da irin Sadauki Nabaru suke gudu. Na tabbata ba alkairi ne ya kawo su Bahara ba, masu leken asirinmu sun tabbatar mana cewar sun kewaye kauyekan sashin nan domin su mamaye su, da tsokanar fada za su fara, don haka koda kayi yaki da su ko baka yi ba na san za su zodomin tuni labara ya zo sun bazo a ko ina, sai dai wata dabara ta zo min cikin raina yanzu a game da batunka”.
Hakimi Abdullahi ya jinjina kai ya ce “Ka tafi izuwa Kogon Sulkui kai da abokan tafiyarka, domin janye su daga cikin kauyen nan, saboda yara da manya za mu biyo sahunka ni da mayaka a yi karan batta a can, zanyi haka ne domin mu magance shirinsu na afkamana gari”.
Koda Jarumi Umar ya ji wannan batu sai dadi ya kamashi ya ce “Na ji dadin da ka fahimce ni ya mahaifina, zanyi duk mai yiwuwa wajen ganin na tsere musu har mu hadu a can Kogon Sulkui.
Koda gama fadin haka sai ya mike cikin sauri ya fita ya samu abokansa ya tabbatar musu da cewar mahaifinsa ya aminta da shawararsa batare da sanin kowa ba suka haye dawakai suka nufi hanyar barin gari tare da neman hanyar da ‘yan leken asirin Mangalawa suke labe domin gano waye Umar daga ina yake ina zai je.
A lokacin da umar ya baro inda ya yake su a jiya kamar ya san cewar su biyo sahunsa sai ya sauka daga kan dokinsa adai-dai mararrabar hanyar da zata sadaka da hanya uku. Ya yanken reshen katuware bishiya ya saka igiya mai tsaye ya daure reshan sannan ya daure a kogunsa yadda zai zama yana janye da bishiyar idan yana tafiya a dokinsa har zuwa inda zai je batare da sun tantance sawayen dokin ba zai kasance yana tafiya reshen yana share sawayen dokin sannan sai ya ki bin mikakkiyar hanya yake bi ta tsakankanin koramai da ciyaye a haka ya je har gida, wannan dalili ne yasa da suka zo suka kasa tantance inda za su samu Jarumi Umar.
Don haka ba za su tafi ba saboda suna zargin hanyoyin da yabi suna cikin hanyoyin da suke wannan waje to amma rashin tabbas yasa suka tsaya suna jiran abin da hali yayi don basu isa su koma su sanarwa da Shugabansu cewar basu ga wannan Jarumi ba domin amsawar mutuwa ce a gare su suna kwance cikin kwantan bauna irin na Mangalawa masana sirrin jeji sai suka ji sukuwar dawakai da karfi tana kusanto in da suke nan suka kara sunkuyawa kasa domin a tunaninsu wata runduna guda ceke tafe, bisamamakinsu sai suka ga wannan Jarumi da aka turo don zuwa bin diddiginsa a gaba wasu majiya karfi Jarumai na biye da shi suna sarrafa dawakai kamar tun da suka zo duniya basu da aiki sai tukin dawakai, sun wuce wajen kamar walkiya, aikuwa batare da bata lokaci ba suka kama dawakansu suka bi bayansu, basu suka daina binsu ba har sai da suka tabbatar da cewa sun isa Kogon Sulkui. Daga can nesa da su suna kallon lokacin da suka shige cikin wannan kogon.
Koda ganin wannan ala’amari suka tsaya a can nesa sai daya daga cikin dakarun Mangalawa y ace “Mutum daya ya komaga Rundunar Ulgurt ka sanar da shi cewar ga inda wannan Jarumi yake don haka muna
saurarenku a nan idan kuma sun matsa daga nan wani daga cikin mu zai babu yadda za mu bari su bibiye su yayin da wasu za su jira harku kara so, bace mana”.
Suleman wani tsohon hakimi ne da a yanzu babu wani daga cikin masu mulki a daular Bahara da suka kaishe tarin shekaru don a kalla ya kai kusan shekaru dari da biyar mayaki ne na kwatace a zamani Sarki Farsi saboda haka yanzu ya kasance wani mutum mai fadi a ji a dukkanin Daular Fansi saboda girmansa da kuma dattako irin nashi. Hakimi Sulelam Bn Auyub na zaune a kofar gidansa bisa wani dakali da ya saba zama da jikokinsa yana musu tarihi sai dakaru da ke kewaye wajen don yin aikinsu, masu fita gona, masu fita kiwo duk in sun fito su kan zo su yi gaisuwa sannan su wuce.
Yana nan zaune ya ji ihun mutu ne da guje guje dawakai jin hakan ke da wuya ya mike tsaye ya kuma fara tattara ‘yan kanun jikokinsa da tattabekunnensa yana tura su zuwa cikin gidansa.
Domin tun da ya ji wannan amsa kuwa ya san cewar hari ne aka kawo musu. Batare da bata lokaci ba dakaru suka cika a gabansa domin tsare lafiyarsa ya zare wata takobinsa domin shirin fafatawa da wadan nan mahaya da suka shigo cikin garinsa. Lokacin da yayi ido biyu da Mangalawa sai hankalinsa ya tashi ainun take ya umarci daya daga cikin dakarunsa cewa ya je ya sanar da Kauyen kusa da su, daga nan ka wuce har babban birnin domin sanarwa da Sarki halin da muke ciki idan har ba a kawo dauki ba Dakarun Mangalawa za su iya nasara akan mu”.
Yana gama fadin hakan dan aikin yayi sauri ya dauki doki ya sulale ya bar garin, tuni guri ya yamutse da azababben yaki, babu ji babu gani ake dauke ba dadi ya tsananta Hakimi tare da iyalansa da dakaru suna kokari kare martabar garinsa, yayin da Jagoran dakaru na uku Barroji Ujjakallah, da runduna ta bakwai Salkaf, duk a cikin tawagar da Bagulbasi ya taho da ita daga yankin Mangalawa domin rushe musulunci a doron birnin Bahara baki daya su mamaye birnin kamar yadda suka sha alwashi shekaru masu yawa da suka shude.
Rundunar ta uku da ta bakwai runduna ce aka zabo manyan saboda kowann Kwamandan yakinta jajurtacce ne kuma mai cikawa ne batare da matsala ba, don haka Bagulbasi ya turo shi yankin nan domin ya shafe su, ya zama shine misali na farko da za su fara aikatawa a birnin amma cikin umarnin a taho masa da Hakimi Suleman Bin Ayyub saboda tsohowar gabar dake tsakaninsu ta kin yadda da a yi sulhu a wancan shekaru sunan bature
Suleman yana kan allon mangalawa saboda su ne suka so a mamaye su a kashe kowa a lokacin da suka kare a filin yaki dan haka dole sai an tara ire irensu waje guda an gurfanar da su gaban Dodonsu kafin a shanye jininsu.
Batare dabata lokaci matansa barori da dakaru da duk wani mutum yaro ko babba aka kashe shi cikin sa’a uku suka babbaki gari ko ‘ina ya zamana yana ci da wuta.ba tare da kakkautawa ba, abin bau tausayi dakarun Mangalawa take gawarwaki suke yi suna shewa da murna cin nasara a karon farko.
Ba tare da bata lokaci ba suka dauki Hakimi Suleman suka daure shi a jikin doki suka ja shi domin komawa masaukinsu, don gurfanar da shi wajen shugaban tawaga.
Sarki Muhammad Farsi na zaune a fada kamar kullum domin ‘ya’yansa ne za su gabato da irin kwazon da suka aikata a aiken da yayi musu sai ya zamana fada ta cika makil har a saman bene ta wata ‘yar kofa Sarauniya Siyama na zaune tare da hadimanta suna kallon abin da ke faruwa a fadar Kamar kullum aka bude da addu’a sannan aka gabatar da Yarima Yazid yayi bayanin a game da aiken da aka yi masa zuwa Birnin Haiman, zuwa ga Benjamin, dukkanin abin da ya faru ya ci gaba da zayyanowa Sarki da wakilai na birnin da Hakimai tsoffin da manyan dattawan Sarauta suna kallo kuma suna saurarensa. Mahaifiyarsa gumi ne yake tsirfo mata domin ta san cewar lallai akwai damuwa duba da yanayin da take kallon fuskokin mazauna fadar Sarki musamman Dattawan fada. Sai da ya kare da yin bayaninsa tsaf mai rubutu yana rubutawa kamar a al’adance duk wani abu da aka zauna a fada ana tattaunawa z aka samu ana rubuta shi cikin wasu na’un fatoci falli falli.
**
Lokacin da Yazid ya gama jawabansa sai hankalin kowa ya koma kan Yarima Abbas a lokacin da ya fito ya tsaya ya fara karanto al’amarin da ya faru a birnin Shamnum da yadda ya gudanar da komai cikin nasara kuma aka zartar da hukuncin da ya dace, abin da ya rage ya barwa mai martaba Sarki Muhammad farsi don haka a cikin fadar duk wani mai kallon mulkin birnin a matsayin tsira ne ga al’ummar duniya ba domin wani buri na tara dukiya ko burin son mulki ba sai fuskarsa ta cika da murmushi jin cewar lallai Sarki ya samu magaji, musamman dattawan birnin da Ulama’u wato Malamai magada annabawa.
Duk inda ran Siyama da na Waziri Ja’afar ya kai yayi mummunan faduwa, kuma zuciyarsu cike take da kuna da zafi mara misaltuwa. Sarki ya bawa Yarima Abbas umarni da ya koma ya tsaya a matsayarsa. Domin *bature
ci wasu su zo su ci gaba da karanto al’amuran na yau da gobe abin da ya gaba da wakana kenan har ya zama an zo kan Sarki zai yi jawabinsa,
wadanda duk wani dake cikin wannan fada abin da yake so ya ji ke nan. Sarki Farsi ya mike tsaye cikin juriya yana mai fuskantar jama’a ya fara da cewa “Masarautar mu, ta wanzu cikin shekaru shekaru masu yawa da kafuwa, an zubar da jini makiya Allah, wadanda ‘yan uwa ne a gare mu,* an zubar da jinin kafurai Mangalawa da sauran Bokaye ‘yan tsibbu wadanda suka saka birnin mu a gaba suna son ganin karshensa, cikin ikon Allah da taimakonsa mun rusa birane mun kama birane mun musuluntar da al’umma a ban kasa fiye da kima, mun yi aiki kafada da kafada wajen jaddada Kalmar Allah.
Ina ba da tsohon labari ne da tun kafin zuwana duniya, zuwan dukkanin wasu da suke nan duniya, mun jera da iyayenmu mun tari bataliyar mayaka daga Rum, mun tare bataliyar mayaka daga hindi, mun tare bataliyar mayaka daga sassa na duniya anyi hadin gambiza domin a kawar da Daularmu, amma cikin ikon Allahu mun zamar musu gagara badau. Ina daga cikin zababbun jarumi da sunansu ba zai taba gogewa ba a doron kasa a can nahiyoyin kafurai da yahud domin irin nasarar da na samu a kansu.
Na zama sarki saboda bunkasar jarumtaka ta, na zama zakara fidda gwani a jerin dakarun birnin Bahara, zamowa ta Sarki labarin da bunkasa ya ci gaba, amma lokaci ya wuce an fara samu sauye sauye na daga ci gaban musulunci, lallai Zakin da ya rayuwa a baya, zai ci gaba da wanzuwa a nan gaba, domin akwai bayin Allah da suka rayuwa suna kyautatawa suna aikin kirki amma a karshen rayuwarsu suka juya ba suka koma shaidanu, wa’iyazubillahi Ya Allah ina rokonka karshe na ya zama ya fi farko na kyawu, ya ubangiji ka agaji ne ka karfafeni domin na ci gaba da dira birnin Bahara a kan tafarki gaskiya da sauran kasashen duniya mu ci gaba da yadawa da’awa mu kai musulunci inda bai je ba”.
Ya zare takobinsa a dai-dai wannan lokaci ya daga sama yayi kabbara nan take wajen ya kaure da Kabbara “Allahu Akbar! Allahu Akbar!! Allahu Akbar!!!
Guri ya dauki shiru bayan an kaure da kabbara ana sauraren Sarki Muhammad Farsi. “Mun yi aike ga Benjamin yayi rashin ladabi ga dan aikinmu, duk da dan aikin ya kasance jinin sarautar birnin Bahara, wannan kuskure ne a gare su, kuma tsokanar fada ce bisa gayya a ka yi, ya zama dole mu kwace Hairama domin ta dawo karkashin ikonmu.
Babu musayar zance a tsakaninmu, babu yarjejeniya ko zama ashimfidar sulhu face kaifin takobi ta ratsa jini da tsoka domin mu kausasa su fahimci har yanzu Bahara na nan a raye bata mutu ba, tabbas sai an nufi Rum da gungun zunzurutun gawarwakin sama da dubu.
Daga karshe ina mai sanarwa ga shugaban dakarunmu ya tura sako zuwa kowanne kauye cewa za a aje a kwace hairam, domin In danka mulkinta ga dana Yazid.
Birnin da suka zubar masa da kima da mutumci zai zama jagoran birnin anan da kwana biyar masu gabatowa”.
Gaban gimbiya Siyama ya kara faduwa hankalinta ya kara dugunzuma dogon burinta na ganin danta ya mallaki birnin Bahara ya na neman ya salwanta saboda tabbas aka danka masa mulkin Haiman shi kenan sai idan har rabo ya rantse na tabbatuwar sa Sarki. A hargitse ta fice daga cikin dakin da take iya juyo maganganun da ake a zaman fada ranta a bace suka koma cikin gida.
Daga wannan Sarki ya sallami kowa domin tun daga yau ba sai gobe ba a fara shiri duk wani mayaki ya gyara takobinsa duk wani maharbi ya gyara kwarinsa, mai duba lafiyar dawakan birnin ya ci gaba da aikinsa, makera masu kera makamai su wanzu batare da sun hut aba wajen samar da sabbin makamin yaki. Domin yaki babu fashi, don haka gari ya rikice da zaryar bakin kauyekan nesa, mata suka wanzu suna yiwa mazajensu shiri, mazaje suka dukufa wajen ganin sun barwa iyalinsu abin da za su ci su sha har Allah ya dawo da su, masu rauni suna kuka rabuwa da iyalansu. Yara wadansa karfinsu bai kai a fita yaki da su ba hankalinsu ya tashi suka koma gefe suna kunci da takaici domin babu yadda za su iya har sai jarumi ya kai shekaru ashirin a dokar birnin kafin a fita da shi yaki.
Sarauniya Siyama ta rasa tsuntsu ta rasa tarko dole ne ta yi wani abin da zai haddasa dakatar da fita wannan yakin saboda yinsa babbar asara rayuwaka za a yi wanda kuma tana da tabbacin sai an yashe birnin Haiman an kwace shi ya kuma karkashin kulawar mijinta, tabbas yin hakan babbar asara ce a gare su, dole tana bukatar yin sirri da babu wani mahaluki da ya sani a cikin birnin Bahara, dole
za ta fita ta gana da mahaifinta don ta san shi ma yanzu ya san yakin sannan hankalinsa yana dugunzume kamar yadda nata dugunzume me, dole ta shirya fita domin ganawa da shi ko da wata dabara da za ta hana wannan fita yakin.
Ta kai gauro ta kai mari tana zagaye tana son ta samu yanay? mai kyau don ta tsayar da tunani da za ta yi amfani da da damarta kafin lokaci ya kure mata.
Yanzu ne maso ma labarin Daular musulunci



