Reads
40
Rating
Chapters
13
Time
3h 38m
Kawar Zuciya Book 1 Hausa Novels By Sumayyah Abdulkadir
Language:
Hausa
Synopsis
Sunan da yake kiranta dashi kenan, a duk lokacin da yake cikin shaukin begenta, da lokutan da kewarta da tunaninta suka addabeshi, ko in yana magana da wani a kanta ko ‘yan jarida in dai zai ambaceta to in sha Allahu zaka ji yace “My co-architect”. Wannan ya faru ne (bayan barinta rayuwarsa) sai wannan inkiyar daya bata ta zame masa abin ambatonta dashi, abin tunawa da ita, idan yana zancenta, baya ambatar sunanta na hakika saidai “My co-architect”. Sau tari kuma ya kan ambaceta da wannan sunan ne a duk lokacin da tunanin gwagwarmayarsu tare a rayuwa yazo masa, cikin fadi tashin neman ilmi,
Reads
40
Rating
Chapters
13
Time
3h 38m



