⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 13: Chapter 13

Ya tafi da tausayin Mama fal a ransa, da damuwar ganin su Zahra duk sun rage karsashi da kidifiri, wannan fallin nasu na gayu da iyayin ‘yammatancinsu duk babu shi yanzu, walwala kanta ta kaura a gidan Mama da ‘ya’yanta. In ka dauke Hatoon babu wani mai walwala a cikinsu.

To kafin ma Zayyan ya saka ranar zuwa Lagos gun aminin mahaifinsa Baba Murtala shi ya zo da kansa har Zaria ya same shi tareda Lauyan Baba Barr. Abba Gana Shattima. Sun tattauna extensively, an kuma tattaro dukiyoyin Baba na gida dana banki da wadanda ke hannun Baba Murtala wadanda Zayyan kansa bai san dasu ba, don haka ya sha mamakin jin abinda Baba ya bari ya kuma jinjina amana irinta Baba Murtala don shi ko sau daya Baba Bello bai taba gaya masa yanada dukiya mai yawa cikin dukiyar Murtala ba.
Ya kara jin gudun duniya ya shigeshi, da tsoron tara dukiya.
Mutuwa mai tonon asiri! Ashe har Estates Baba Zayyan ya gina ga gwamnatin tarayyah da ba’a kai ga biyanshi kudin kwangilarsa ba, sai yanzu da ya rasu, Baba Murtala ya tsaya tsayin daka yayi fafutuka aka biya magadansa.
Baba baya tattauna harkokin business dinsa da shi dan sa Zayyan saida Baba Murtala kadai, ko mai yasa? Ko don ya san baya ra’ayin business din? Zayyan a lokacin bai takura kansa da dogon nazari akan dalilin da yasa Baba Bello baya gaya masa samunsa ba, a take ya baiwa kansa amsa don ya dade da sanin doctrines din Baba Bello fiye da kowa;

Shi ya san ba don komai Baba yayi hakan ba sai don yafi so ya koyi dogaro da kansa, ta hanyar amfani da ilminsa bada dukiyar da waninsa ya tara ba.
Kuma alhamdulillah Baba yayi nasarar tsayar dashi akan kafufunsa, ta hanyar bashi ilmin addini dana zamani, don tuni ya tashi daga Asst. lecturer zuwa cikakken lecturer a ABU yanzu.
Aka tattara dukiyar baba Bello waje daya da taimakon mai shari’a da lauyansa aka rabawa iyalinsa gadonsu bisa tsarin addinin musulunci.
Inda kamar yadda addini ya tsara shi ya tashi da kason da ya rubanya na ‘yan uwansa mata. Mama kuma ta karbi tumunin takabarta.
To bayan gama rabon gadon ne Mama ta tara yaranta mata duka suka yi (closed door meeting), suka amince da shawarar da Mama ta kawo musu.
Mama ta kira Zayyan a washegarin ranar data zauna da yaranta mata, suka zauna daga ita sai shi, bayan sun gaisa yaci abincin data aje masa ta tabbatar ya samu nutsuwa, sai tace masa.
“Baffana, nida ‘yan uwanka Zubaida, Zubaina, Zaitoon, Zahra da Hatton, mun yanke shawarar damka maka ragamar komai namu a hannunka, wato mun maido kason kowaccenmu hannunka, a sake cure dukiyar nan waje daya in yaso ka cigaba da juyata kamar yadda Babanku ke yi a harkar Real Estate.

Da sauri ya dago ya dubi Mama a rikice, ta bude ido sosai tace “Eh, haka nake nufi ka bar aikin gwamnati, muna son a matsayin ka na Da namiji kai kadai a cikinmu ka dora mana daga inda Babanku ya bari”. Ta soma matsar kwalla da gefen hijabinta.
Tana cewa “ni ban ga me kake samu a koyarwar nan ba, ni ban saba da wahala ba haka ‘ya’yana, dole ka taimaka mana kada rashin Babanku yasa mu ragaita, kaga dai dukiya in ba juyata ake ba bata da albarka, nan da nan za’a nemeta a rasa. Ni dai ka ajiye aikin gwamnati, kazo ka zame min Bello Rafindadi tunda dai ga jari ya bar mana”.
Zayyan a wannnan lokacin sai ya karaya, har fiyeda kima, irin abunda yake gudu kenan tun rasuwar Baba. Ya san duk nauyin gidansu kansa zai dawo. Mama ta manta kama da wane bata wane.
Dama har lokacin cikin dimuwar yawan dukiyar da Baban ya bari yake. Yana ganin bazai iya da wannan nauyin da Mama da ‘yan uwanshi ke son dora mishi ba.
Arch. Bello Rafindadi, bayan kasancewarsa tsohon dan boko tofa rikakken dan gwagwarmayar kasuwancin gine-gine ne. Baya taba tsugunnawa a waje daya, duk inda ya samu kwangilar zane ko gini zai je yayi a cikin Nigeria.
Shikuwa ya riga ya san kansa cewa shi malamin makaranta ne, wanda samunsa duka ya ta’allaqa ne ga albashinsa na wata. Bai taba mafarkin zama irin Babansa a harkarsu ta kasuwanci ba, ko zama dan gwagwarmayar neman kudi kamar Baba Bello, wanda ba abu ne mai sauki da zai iya ba a halin yanzu.

Da karyayyar zuciya da kuma sanyin murya Zayyan yace da Mama cikin bijirewa.
“Mama naji bukatarki data ‘yan uwana mata, amma ina baku hakuri, wannan wani nauyi ne mai girma kuke son dora min da bazan iya dauka a halin yanzu dana samu Rauni a zuciyata ba, tunda nauyi ne na dukiyar marayu kin ga, ina tsoron wani abu ya samu dukiyar ‘yan uwana a hannuna saboda tsautsayi ko sakaci na, tunda kinga ba wai na iya harkar bane, ban kuma taba gwadawa ba.
Ni a ra’ayina da dai kin bar kowaccen su ta juya dukiyarta da kanta, tayi sana’ar da take so da kasonta, nikuma zan taimaka musu da shawarwari da goyon baya duk sanda suka bukata”.
Amma Mama tace “a’ah, sam ban yarda ba, ni da kai kanka da su ‘yan uwan ka mata duka abu guda ne, ba kuma ‘yan Uba kuke ba balle kace min zasu zargeka, hadin kanku nake so a duniya tunda baku da wanda yafi muku junanku, shiyasa nace a hade komai wuri daya a damka maka.
Da a samu riba, da ayi asara duk daya ne a wajenmu, indai dukiyar nan a hannunka take Baffana bamu da haufi kaji?!”.
Zayyan ya buga ya raya akan bazai iya ba, Mama Fatu ma ta kafe akan bakanta. Tace “zamusa kafar wando guda nida kai in ka ki jin maganata”.
Don haka da damuwar wannan maganar da sukayi da Mama ya juyo Zaria a ranar. Har yace sai ya kai kararta gun Baba Murtala.
***** ***** ****
Kwana biyu kullum Safiyyah cikin damuwar nan da kuma tunanin nan take ganinsa ciki, tun dawowarsa daga Katsina, ta kuma fahimci (family issue) dinsu ne, shiyasa bata tsananta masa da tambayar abinda ke damunsa ba, kuma bata saka baki ba, tunda shima bai sakata a cikin sha’anin ba.

Ko a daren ranar ma tana ji yana waya da Yaya Zubaina akan wata bukata da Mama ta saka shi da bazai iya ba, taji Zubaina tana kara tabbatar masa sun riga sun gama shawara shi zai ja ragamar dukiyar Baba, bata son wata magana daga gareshi bayan wannan, kada ya zama raggo mana?
Zubaina ta kare da cewa “Ita ba haka tasan Zayyan dinta ba, rashin Baba duk ya salube jarumtakarsa”.
To sati biyu bayan nan, da ya dan samu nutsuwa don Mama da ‘ya’yanta duka sun dage akan bakansu, ya gayawa Safiyyah zai je Lagos gun aminin Baba, kuma zai kwana uku don bazai yiwu ya dawo a washegarin ranar ba tafiyar motar haya ce.
Tunaninsa a lokacin shine yaje wurin Babansu Alh. Murtala, ya kai karar Mama dasu Zubaidah, kan suna son dora masa nauyin da bai shirya dauka ba, ya kuma nemi shawararsa kan batun.
Kasancewar ya san Baba Murtala a matsayin mutum mai amana da rikonta, mai son cigaban Baba Bello da zuriyarsa da zuciya daya ko ba’a fada ba, duk shawarar daya bashi zata zama mai amfani ce a gare shi fiye da tasu Zubaina.
Safiyyah ta kwana yi masa shirin tafiya Lagos, a washegari sukayi sallama ya tafi kamar bazasu rabu ba, soyayyar Safiyyah da Zayyan kullum kamar a ranar suka fara ta, basa taba gundura da juna da nuna ma juna so da kulawa, sai ka zauna kusa dasu zaka gane tamkar ‘tube’ da ‘tyre’ suke rayuwa.

Koda Zayyan ya isa Lagos cikin motar haya ta luxurious, unguwar Ikoyi ya nufa wato inda gidan Baba Murtala Masari yake, kyakkyawar tarba Baba Murtala yasa aka shirya masa da masaukin da zai sauka tun kafin isowarsa.
Sauka irin ta Dan da ka haifa a cikinka, ka kuma dade baka ganshi ba, ita Baba Murtala ya shirya masa.
Aka kaishi dakin baki ya ci abinci ya kintsa, tare da Baban suka yi sallahr maghriba da isha’i a jam’I, sannan suka zauna a falon Baba Murtala don tattaunawa, ya fara gaya masa abinda ke tafe dashi, wato rigimar Mama data ‘yan uwanshi, na sai ya kwafe musu Baba, ya koma sana’ar da Baba ya bari da dukiyarsu.
Ya gayawa Baba Murtala shi bai taba sha’awar wata sana’a bayan koyarwar da yake yi ba. Kuma bashida ra’ayin tara dukiya a rayuwarsa, don a ra’ayinsa ma nashi kason da aka bashi ya yanke shawarar Mama zai hadawa ta hada da tumunin takabarta ta kara jarin kasuwancinta.
Yace. “A komai yana so ya gaji Babansa, amma banda a harkar irin neman kudinsa na rashin hutu da tara dukiya, baya kuma son yayi disappointing Mama da ‘yan uwansa in bai zame musu abinda suke hange a juya dukiyarsu ba”.
Baba Murtala sai yayi murmushi, ya sake murmusawa, don ya lura rashin mahaifinsa ya karya lagon jarumtar Zayyan da yawa, ta wani fannin kamar mara sauran ‘hope’, a rayuwa, wato ya maida kansa (hopless) wanda bazai iya tabuka komai ba, tunda ya rasa source of inspiration dinsa Baba Bello.

Daga ranar Alhaji Murtala ya sha alwashin zamewa dan amininsa Zayyan UBA mahaifi. Uban da zai karfafa shi a rayuwa har zuwa nasa karewar numfashin, sannan ya zame masa ubangida na kasuwanci.
Ba abinda yake bukata a lokacin irin soyayyar Uba da ya rasa, wanda ita kadai zata karfafeshi a yanzu, ta dawo da jaruntakarsa.
Don haka Arch. Murtala Babangida Masari, ya dafa kafadarsa ya ce dashi cikin yin kasa da murya.
“Faduwar wani tashin wani ce my son Zayyan, kada ka taba bari faduwar wani naka ta zama faduwarka.
Dama wannan ranar nake jira, wato rana irin wannan da zaka tako ka zo gabana da kanka ba tareda Fatuma ta turoka ba, ka nemi zama cikakken ‘Architect’ makwafin mahaifinka a gabana.
Hajiya Fatu dasu Zubaina sunyi abinda ya dace. Ka sani Bello ba raggo bane, na kuma tabbata bai haifi raggo ba”.
Yayi murmushi ya cigaba “hakannan Bello bai abota da ragwaye a sanina dashi tun muna makaranta, in yaga baka da kokarima baya kusantarka, kada rashinsa ya maida kai ragon maza kaji ko Zayyan, ka mike ka zama mai zafin nema irin Babanka, duniya bata aure da ragwaye yanzu, shi namiji rayuwarsa duka ‘yar gwagwarmayar nema ce, in dai da dama kuma da nasibi. Balle kai gashi kana da damar, a gefe kana da ni, Babanka Murtala. Allah kuma yace tashi in taimakeka, sai ka shiga da kwarin guiwarka ka gani idan akwai nasibi a ciki ko babu.

Dama jira nake komai ya lafa ka kuma kara samun nutsuwa, sannan in nemoka ko baka zo ba. Duk da dai inada kyakkyawan fata, na cewa zaka zo din watarana.
In ce da kai, ka zo mu cigaba daga inda muka tsaya ni da mahaifinka. Ka mayemin gurbin abokina Arch. Bello.
Nima cikin kewar rashinsa nake cigaba da nawa harkokin. Mahaifi ko kwasar kashi yake a matsayin sana’a yana so Dansa ya gaji wannan sana’ar, in dai ta halal ce.
Da na Zayyan, ka zo a dama da kai a harkar “Real Estate”, ka kutsa cikin profession dinka da kyau ka yishi practically, ka zama Professional Architect dinda duniya zata san da zamansa, kamar mahaifinka. Wato ka zama cikakken magaji ga Bello Rafindadi, akan komai nasa.
Ina kara jaddada maka, “mutum ko kwasar kashi ce sana’arsa, zai so ace dan sa ya gajeshi a kanta”.
Ita wannan harkar ta gine-ginen gidaje da zana su da bada hayarsu, wadda ta zame mana silar alkhairi nida mahaifinka, ba kamar aikin koyarwar daka saba da shi bace, harka ce da babu hutu a cikinta kuma wadda ke bukatar tsayuwar daka da cinye lokaci, dole sai ka zage damtse ka kuma jajirce sannan zaka ci ribarta.

Amma harkace ta ilmin zamani dake kawo alkhairi sosai ga mamallakanta.
In da ka san irin wahalhalun da muka sha ni da Bello, da fadi tashin da muka sha akan harkokin nan kafin mu kawo wannan matakin, zaka fi yarda kada abar sana’ar ta bi ruwa a cinye jarinta a wasu abubuwan daban, tunda Allah yasa akwai namiji a cikinku”.
A nan Baba Murtala ya shiga baiwa Zayyan tarihin struggle din Babanshi Bello Rafindadi, wajen gina abinda ya tara da guminsa, yace bai dace ya yarfe wannan gumin ya zubar ba, tun yana malamin jami’a a mataki na farko Bello yake koyarda Zanen gidaje mai ban mamaki ga dalibansa, ya kara da bawa Zayyan nagartattun shawarwari akan yadda ake cimma nasarar harkar REAL ESTATE, ya kuma ce ya zo su tsunduma cikin harkar tare, zai kama hannunsa zai masa jagora.
Har zuwa sanda zai gama gane kan harkar “Real Estate Business” bakidayanta sannan ne zai saki hannunsa, ya barshi ya cigaba da tsayawa akan kafarsa.
**** **** ****

A takaice wannan shine mafari, sila, kuma tushen kafuwarsa, da silar arzikin da yau yayi cikin dan lokaci da fitar sunansa a harkar Real Estate.
Arch. Zayyan Bello, ya shiga harkar da kafar dama kamar, koma fiye da mahaifinsa Arch. Bello Rafindadi.
Duk wata hikima da baiwa ta mahaifinsa sai ta yi hijira ta dawo cikin kansa kamar yadda dukiyarsa ta dawo hannunsa.
Don kuwa a gaba kadan, bayan kamar shekaru biyu da farawarsa, Arch. Zayyan yayi resigning daga aikin koyarwarsa da jami’ar Ahmadu Bello.
A lokacin tuni Safiyyah tayi graduating (ta kammala digirinta na farko) itama a fannin nasu na Architecture, har tayi hidimar kasa duka a Zarian. Safiyyah na gama makaranta Zayyan ya bar Zazzau ya koma Abuja, inda acan ne Baba Murtala yake kokarin kafa Zayyan akan harkar zanen Estate da karbar kwangilar gina su da bada hayar su.
Kuma acan ne duka harkokinsu suka fi karfi yanzu. Duk da Baba Murtala iyalinsa suna Lagos yana yawan zaman Abuja yin harkokin kwangilar gine-ginensa.
Saida ya dan fara kwari a harkar ya soma tunanin dawo da Safiyyah kusa dashi don su bar Zaria gabadaya. Da farko Zayyan ya fara da kama musu shida Safiyyah dan madaidaicin gida flat a wani (block of flats) mai daki uku da falo a Jabi.
Estate din da Zayyan ya fara zanawa ya kuma gina na farko mallakinsu ne shida ‘yan uwansa mata, wato hadakar dukiyarsu ce su duka, a jihar Katsina suka samar dashi, a can ya fara gina Estate, don akace kowa ya bar gida gida ya barshi, wanda suka sakawa suna; “BELLO RAFINDADI ESTATE”.

Sai suka zuba ‘yan haya duk shekara Mama da ‘yanuwanshi na damkar makudan kudade, shi da Safiyyah ne suka zauna sukayi ta musu, (debate), akan sunan da ya dace a sakawa Estate dinsu na farko, har a karshe suka ambaceta da ‘surname’ dinsu gabadayansu, watau “Bello Rafindadi Estate”. Anan GRA Katsina.
Zayyan ya muskuta daga kwancen da yake, yana cigaba da dogon tunanin da yake yi…. wani lokacin har yana matse kwallah, wani lokacin kuma yayi murmushi duk shi kadai.
Safiyyah have immensely contributed a lot to his achievements and successes (Safiyyah tayi matukar bada gudunmuwa ga nasarorinsa da abubuwan da ya cimma na nasara a rayuwarsa). Domin a duka wadannan lokutan Safiyyah na tare dashi cikin halin dadi dana babu dadi, against all odds ta tsaya a gefensa, kuma tana kula da rayuwarsa da cikinsa da lafiyarsa da bukatunsa na Da namiji cikin kauna da soyayyah.
Ta taya shi raba dare suna ‘sharing idea’ da musayar fasaha, inda zaka gansu sun zauna a falonsu sun baje takardun Zane a gabansu cikin dare, kamar abokan aiki ba mata da miji ba, suna tsara Zanen Estate tare, tareda da shirya time-table na yadda zasu gudanar da kwangilolin ginin gidajen da suka samu su aiwatar dasu bi da bi cikin tsari da sarrafa hikima.
**** **** ****
Bazai manta ba, shi da ita ne suka raba dare a wani dogon dare mai dumbin tarihi tarihi suka samar da ‘idea’ din kirkirar “SUNSET ESTATE”.
Wanda zai zama mallakinsa ne shikadai watau ba tareda dukiyar ‘yan uwansa a ciki ko mahaifiyarsu ba. Cewa suka yi bari su hada duk wata fasaha da suke da ita ta ilmin Architecture a kan Estate din, da duk abinda Zayyan mallaka ya sayar ya saka a cikin capital dinsa ta ginin da zasu yi, su yi Estate din amma wannan karon a matsayin nasa shikadai.

Saboda shekaru uku bayan kama harkar ‘real estate’ da yayi dukiyarsu Zubaida ta rubanya a hannunsa, kusan kashi hudun yadda ya karbeta daga hannunsu, kowaccensu ta mallaki Estate nata na kanta yanzu a Katsina, haka shima yanada Estate sun kai hudu a Katsina, hakika Allah ya sanya masa hannu da nasibi a harkar ‘real estate’, da kuma taimakon Baban kwarai Baban marayu, Alhaji Murtala Babangida Masari.
Bayan ya tsayar da idea din yin nasa Estate din na kansa, bisa shawara da gudummuwar Safiyyah, sai yaje ya samu Mama Fatu akan yana son gina Estate nasa na kashin kansa a Abuja.

Mama Fatu bata hanashi ba, ta dai ce in dai zai cigaba da rikewa ‘yanuwansa mata nasu Estates din, ita bazata hana shi yin yadda yake so ba. In kuma Safiyyah ce ta zugo shi akan ya ware dukiyarsa daga Katsina ya mayar Abuja don tana bakin cikin yana kulawa ‘yan uwansa da Estates dinsu a Katsina, tana so ta janyeshi gabadaya ya maida hakalinsa a Abuja, to tayi a banza, tunda dukiyarsa dai zata taba zama tata ba, tunda gata nan har yau sai cika masai da kashi ta iya, ko gudan jini bata taba ajiye masa a kasa da sunan dansa ba.
Maganar ta dade tana masa yawo a kai, amma bai ce komai ba. har yaushe akayi auren da za’a soma cewa Sophie bata haihu ba?
Bisa shaidun da suka kamata wato Lauyan Baba Barr. Abba Gana Shettima da Baba Murtala da Mama, Zayyan ya zame komai nasa daga cikin na ‘yan uwansa su Zubaidah, amma zai cigaba da kula musu da komai nasu. Mafari kenan na fara samuwar assasa tubalin ginin SUNSET ESTATE a unguwar Guzape.
Bisa zane da tsari irinna zamani, wanda yayi amanna bai taba yiwa kowa irinsa ba. Kuma anyi ittifaqin bai dauko samfurinsa daga ko’ina ba. A’ah, zallar idea dinsu ce shi da Safiyyah.
Domin sun kure duk wata fasaharsu ta Zane a kansa shida Sophie. Shi da Safiyyah suka samar da SUNSET ESTATE. Bayan shekaru biyun da suka dauka suna raba dare akan zanensa, tareda tsara proposal din ginin, komai na shirye-shiryen ginin ya kammala a shekara ta shidda da aurensu, sai aka fara gina ‘Sunset Estate’.
**** **** ****

Mu karasa a littafi na biyu.
Tare suke.
Sumayyah Abdulqadir
07030137870
(whtspp only).
PAID BOOK

Assalamu alaykum TAKORITES.
Kafin mu fara ina farin cikin tallata muku Hajiya Aisha Umar Dauda mai A&A Incense & Collections.
Dealers ne nadukkan kayan Oriflame Products & GHT Products. Sanan suna da Room Freshener, Toilet Cleaner, Tiles Cleaner, Glass Cleaner, Dish Wash, Hand Wash, Shoes & Bags, Hand Made Shoes, Atamfa, Shadda, Materials, Kid’s Wears, Electronics, Perfumes and many more.
Domin sayen daya ko sari ana iya tuntubarsu a;
No.1 Beside Lolo Dakare’s Filling Station Hajj Camp, Katsina State.
Suna aikawa ko’ina. Ko a tuntubesu kai tsaye a wannan lambar waya don saka order.

08067303736
08054647489

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *