⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 2: Chapter 2

“THE ARCHITECT”

Tsaye yake jikin ‘railer’ din data kare wata matattakala daga dan saman tudun katon jan dutsen cikin ‘park’ din Sunset Estate, dutsen yana bulbular da ruwa garai-garai kodayaushe. Ruwan sai kaga yayi tsiriii zuwa sama, sannan ya gangara ya sauka kasa a hankali, one of the very fabulous moments dinsa shine duk yammacin da yake kasancewa a nan gurin, idan rana ta tafi zata fadi cikin Estate dinsa.
A daidai wannan lokacin tunanin yadda sabuwar rayuwarsu zata fara a yau kawai yake yi, yana kuma kallon kudurar Ubangiji dake cikin faduwar rana, wanda yayi daidai da jin faduwar gabansa, in ya tuna me zai je ya zo masa daren yau.
Zuwa yanzu ya tabbata gidansa ya cika makil, taf da mata, daga bangarori daban daban.

Kusan zuwa wajennan ya zame masa dabi’a ko in ce al’ada, tun tarewarsu a cikin Estate din bayan kammaluwar gininsa da bikin bude shi. Sau tari, a duk yammaci irin wannan daga misalin karfe biyar na yamma zuwa shidda da kwata, in dai har yana gari, kuma baya wani muhimmin aiki a gida, ya kan zo wannan wajen ne ya tsaya, yayi ta kallon faduwar rana a cikin Estate dinsa, yana reflecting rayuwarsa, sannan ya karewa gidajen da ya zana da kansa kallo na sha’awa da alfahari da kai, hakan yasa ya zama mai yawan godiya ga Allah, a bisa baiwar da yayi masa ta hikima da arzikin da ba kowa yayiwa ba.

A dai-dai lokacin ya kai duba ga agogon ‘Cartier’ na bakar fata dake daure a damtsen hannunsa mai cike da lallausar gargasa, agogon har dan nitsewa yayi cikin gargasar data cika farar fatar hannunsa. To haka yawan gargasar yake a duk ilahirin jikinsa, shi mutum ne bafillace, mai yawan sumar jiki, musamman a gashin kansa da kirjinsa da zaka ga har dan murmurdewa take yi irin na fulanin asali. Ma’ana dai ya kasance kyakkyawan mutum mai wadatar sumar jiki data gashin kai ne.
Kyallin da agogon dake daure a hannunsa keyi kadai ya isheka kimanta daraja da kimar agogon hannun nasa, musamman ga maza irinsa ma’abota masu amfani da dukiyar da Allah ya basu wajen kawata kwalliyarsu da tsadaddun agogo a jikinsu, yanada yawan tsafta da iya sanya suttura ta kamala, ya iya ado da kwalliya ta ‘yan gayun maza, mai burgewa da ban sha’awa, amma a dressing dinsa da wuya ka ganshi cikin kananan kaya ko ‘Suit’.
To yau ma sanye yake da wani rantsatstsen (sky-blue filtex) yadi na musamman na kasaitattun maza. Yayi matukar yin kyau a cikinsa, kalar yadin ya haska shi, ya fiddo kwarjininsa da ilhamarsa, sai annuri yake fitarwa daga fararen idanunsa. Tsammani zakayi saurayi ne mai shekaru 27 ba magidancin da ya doshi shekaru 40 ba.

Zuwa yanzu ya san gidansa ba masaka tsinke, don haka ya yanke shawarar barin Estate din gabadaya.
A lokacin rana ta gama faduwa, gari ya fara yin duhu, maghriba ta kawo kai.
Sai ya baro wajen da yake tsaye, a kasa ya taka zuwa masallaci, da zummar ya samu jam’in sallar magariba a masallacin Estate din.
Daga nan zai dauki motarsa da ya baro a parking lot na masallacin, tun bayan fitowa sallar la’asar, gara ya wuce gidan Baban Abdallah, don gujewa taron dandazon mata da hayaniyar su a cikin gidansa.
Bayan an idar da sallah sai ya fito ya shiga motarsa da ya faka a kofar masallacin. Ya juya kan sityari a hankali, sannna ya tuka a tsanake ya hau bisa titi kafin ya saki motar a guje.
Yana tafe akan titin da zai kai shi unguwar Life-Camp daga Guzape, a hanya yake ‘making comparisons’ a cikin ransa da idanunsa da zuciyasa. Wato yanzu da yake wuce manyan unguwanni daban-daban na cikin kwaryar Abuja, ya kasa ganin kamar, ko misalin Estate dinsa a komai, balle wanda ya kama kafarsa, ko ace ya dokeshi a kyawun tsari da na fasali.
Ko don wannan kadai yana alfahari da kasancewarsa mamallakin Sunset Estate, mai ilmin zanen da babu na biyunsa a kwarewa a Arewa, yana kuma godewa Ubangiji akan baiwar nan da yayi masa, wadda ba duk mazan arewa ba, kai ba duk kai ba, ba kuma kowa ba!!!
**** **** ****

A gidan Habibu yasha zamansa. Suka sha hirarsu ta tsoffin abokai, duk dai akan lamarin iyalinsu. Bashi ya baro gidan ba sai misalin karfe goma sha biyu na dare, ya san dai zuwa yanzu kowa ya watse, na cikin gidan kuma duk inda suke sun gaji da jiran dawowarsa sun dade da kwantawa barci. Maigadinsa ne ya bude masa kofa, ya shigar da motar ciki a hankali, sannan ya adanata a muhallinta na dindindin watau (parking lot din gidansa).
Ya jima sosai zaune cikin motar, kamar ba zai fito ba, har sai kayi tsammanin ko barci ya dauke shi ne, domin tunda ya kwantar da kansa bisa sityarin motar, bai kara dagowa ba, saboda gajiya da damuwa da sukazo lokaci daya suka yi masa rubdugu.
Akalla ya dauki tsayin kusan awa daya da rabi a wannan yanayin, cikin tunani da damuwa da suka ziyarce shi nan take. Sannan a hankali ya lumshe dara-daran idanunsa, wadanda a yanzu gajiya ta canza launinsu zuwa ‘brownish’ haka, daga farare kal dinsu da kowa ya sani, kafin daga bisani ya daure ya kashe injin motar, ya dan jingina bayansa da kujerar motar kirar bakar Bugatti (Centodieci).
Ya fito a kasalance, rike da babbar rigarsa a hannun damansa, an yi mata dinki da shudin zare mai turuwa na alfarma, a kansa shudiyar hula ce (Tonak) ta yayin samari da magidanta, kayan sun matukar karbarshi, sun fiddo zahirin asalin kalar kyakkyawar fatarsa, wadda ta kasance wankan tarwada mai haske. Domin baza’a kirashi fari sol ba.

Idanunsa saye cikin farin gilashi mara mazagayi (Cassie Rimless) wanda bai boye damuwar dake cikin idanunsa da suke lumshewa da budewa da kansu ba, wanda yanayi ne na halittarsu hakan.
A tsanake ya doshi hanyar shiga cikin gidansa, shiru kake ji kamar babu wani mahaluki dake raye a cikin tsararren gidan, mai lamba ta farko a unguwar ‘Sunset Estate’ watau (No 1. Rafindadi Close).
A daidai wannan lokacin baka jin komai a Estate din sai haushin karnukan gadi (Security Dogs) dake tashi nesa kadan dasu, hakan yake kasancewa a Estate din kullum idan dare ya tsala, karnukan sunta zuba haushi kenan marar dadin ji, musamman ga wanda ya debo gajiya da damuwa, yake bukatar hutun jiki dana zuciya harma dana kunne kamarsa. Wato yafi son yaji ko’ina shiru.
A haka ya cigaba da tafiya a hankali, bayaso taji dawowarsa, domin ji yayi ya rasa duk wani karsashi nasa na Da namiji, tunda ya hango tagar dakinta a bude, duk da ance faduwar gaba asarar namiji…. Shi dai yau gabansa faduwa yake, don haka, so yake ya kebe kansa kawai.
Ya kasance mutum ma’abocin iya takun tafiya ta nutsuwa da aji na musamman (classic gait), kasancewar sa wankan tarwada mai haske yasa fatarsa ta kasance mai santsi, kamar mai shiga wankan inji, har wani dan jaja-jaja zaka ga kalar fatar fuskarsa nayi na hutu zallah.
Abokansa na kuruciya idan yana tafiya ta gabansu, wani kirari zakaji sun rufeshi dashi.
“…Takunka dabam ne Baffan Mamanshi…., Farar aniya da farar zuciya, sai Baffah ..… Shalelen Mamanshi an buga an barka Zakin duniya, kanin Zubaina da Zubaidah, Yayan Zaytoonah da Zahrah, na “Sophie” bada kanka a sare kaje gida kacewa Mama ya fadi kawai!”.
Domin tun yana makarantar sakandire Baffa mutum ne shi mai yawan taimako, da yawan jin kan na kasa dashi, shine suke ce masa Baffa mai farar aniya da farar zuciya. Ga dai shi da rashin walwala a fuska, amma hakan bai hana shi zamowa mutum mai yawan kyauta da kyautatawa kowa da nagartattun halayensa ba.

Tun kuma a wancan lokacin kowa ya san irin yadda Mamansu ke son shi, Mama bata kara a kan Baffanta, domin ya ci sunan marigayin Babanta. Sannan shikadai ne namiji cikin ‘ya’yanta.
Arch. Zayyan Bello Rafindadi kenan, wanda dan asalin jihar Katsina ne. Kasancewar Zayyan sunan Kakansa na wajen Uwa yaci, shine Mamansa da kanta take kiransa “Baffa”. A wannan shekarar Zayyan ya cika shekaru talatin da bakwai da haihuwa.
Zayyan rabinsa Ba-rume ne rabi kuma haihuwar asalin shiyyar Rafindadin birnin Katsina.
Idan nace “Ba-rume” ina nufin Arch. Zayyan, ta bangaren mahaifiyarsa Hajiya Fatima da kowa ke kira (Mama Fatu), Rumawa ne.
Shiyasa daga kallo na farko zaka ganshi da zubin kyawunsu da fasalin tsayin mazan Rumawa, amma Zayyan bashi da tsagin gefen fuskarsu saboda ta dangin uwa ya gado su bata uba ba, mutum ne mai cikar zati da tarin kamalar dake bayyana yawan sallah da kula da ibada, zaka shaida hakan daga tabon sujjadah baki turarre dake saman goshinsa, bazaka ce shi miskili bane, don rashin walwalarsa ba yana nufin miskilanci bane. Kawai za’a ce Baffa baida far’a.
Mutum ne mai iya sarrafa kansa gaban kowa, sannan mutum ne da ya iya jan zaren ‘class’ dinsa, watakila wannan shine abinda ke hana a gane walwalarsa, amma dai Baffa ya kanyi walwalar idan ta kama da ‘yan uwansa mata, watau dai faram-faram dinsa yana yinsa ne a inda yaga ya dace yayi kawai.

Arch. Zayyan, mutum ne mai kiyaye tsaftar jikinsa, zaka shaida yawan tsaftarsa ko daga faratansa da kullum suke a gyare tsaf-tsaf, Zayyan dan gayu ne sosai wanda ya kware a iya daukar wanka, sannan da iya karya hula akan goshinsa, kowa ya shaida kuma mutum ne da ya iya zaben sutturar data dace dashi a kowanne yanayi. Kwalliyar da yayi yau kadai, ta gama fallasa iya dressing dinsa.
A irin tafiyar da Baffa ke yi, sam baya bari takun shi ya bada sauti, don baya so Sophie tasan da shigowarsa ko dawowarsa gidan a wannan lokacin. To balle kuma….
Kai tsaye sassan shi na cikin gidan ya nufa, maimakon inda ya dace ya nufa a yanzu, ba tare da ya kalli kowanne sashe na bangarorin gidansa ba, wanda yake (fully detached duplex), shi kansa ya san inda ya nufa din, wato side dinsa, ba can ya kamata ya dosa ba.
Amma Baffa ji yake ba abinda yake da bukata yau irin kadaicewa, ba don komai ba sai domin ya samu damar da zaiyi sahihin tunani akan abinda ya aikatawa rayuwarsu, a matsayin warwara ga tarin matsalolinsu. Yana so ya nutsu, sannan ya tantance, yayi kyakkyawan nazari akan rayuwarsu shi da Safiyyah.

Babu wani doki ko farin ciki ko far’a a tare da Baffa, irin na kowanne sabon ango, wadanda dasu ya kamata ace ya shigo gidan.
Idan ka lura sosai ma zaka gane idanun Baffa a rufe suke don tsabar damuwa, suna kara lumshe kansu da kansu wanda nature dinshi ne haka.
Yazo zai shige sitting room dinsa kenan sai yaji tamkar motsin bude tagar Sophie ta falonta na sama.
Saidai kuma hakan baisa ya juyo ko ya tsaya ba, saboda baya da kwarin guiwar yin ko dayansu, wato tsakanin tsayawar ko juyawar, saima cigaba yayi da tafiya harda kara sassarfa saboda ya buya daga idanun iyalin nasa.
Yasa mukullin dake hannunsa ya bude kofar bangarensa ya shige, sannan ne ya samu ya saki ajiyar zuciya, tareda juyawa ya kulle kofar shigowa katafaren falonsa nasa.
Baffa bai tsaya a falon ba, kai tsaye (masterbedroom) dinsa ya wuce, ya fada kan gadon dakin yayi dai-dai da kafafunsa akan makeken gadon na alfarma, bayan ya jefar da babbar rigarsa da jakar ‘laptop’ dinsa da ya riko a gefen gado.
Ya juya ya sake gyara kwanciyarsa sosai, wannan karon rigingine ya koma, ko takalman kafarsa sau ciki da safar kafarsa bai iya ya ciresu daga kafafunsa ba, a haka ya kwanta.
Zuciyarsa cike da taraddadin da ya ninka na baya, da ya tuna dole dai da safe zai ga Safiyyah ya fuskanceta, wai meyasa madadin ‘contentment’ irin na samun cikar buri daya kamata ya kasance a ciki sai taraddadi ya maye gurbi? Wadanda ba shi ya kamata ace ya kasance cikinsa ba yau, tunda dai gashi at long last, ya samo maslaha ga matsalarsu shida Safiyyah.

A yau zai iya cewa ya ceci aurensa da “Safiyyah” daga tangal-tangal din da yakeyi, da kuma sauran matsalolinsu masu zaman kansu. At long last, ya ceci aurensu na tun tali-tali, aure mai tarin albarkar iyaye irin nashi da Safiyyah.
Shi da Safiyyah are more than husband and wife, they are each others’ ALTER EGO, sun riga sun yarda sirrin juna ne sannan barin rayuwar junansu. To mai yasa zai shiga damuwa kuma akan hukuncinsa? Hukuncin da bisa yardarta ya aikata shi? Tunda kuwa ko babu komai, daga yau ya ceci wannan dadadden auren na tarihi da soyayyah daga rugujewa, da kuma duk wata barazanar dake hanasu kwanciyar hankali shi da Safiyyah?
Akalla dai zai iya cewa daga yau yayi maganin duk wannnan bacin ran da tsangwamar da Safiyyah ke kwankwada dare da rana a gidansa.
Kuma insha Allah zai tsaya yaga cewa ya cikama Safiyyah dukkan alkawuran da ya daukar mata.

A tunaninsa yanzu kam ai za’a sakar ma Sophie mara, tayi fitsarinta peacefully, kamar kowacce mace mai iko a gidan mijinta, a saka mata rigar ‘yanci, da bata taba sakawa a idon Mama ba, shima kuma zai samu kwanciyar hankalin da ya rasa shekara da shekaru, a dalilin damuwar Safiyyah data Mamansa, tunda finally yayi abinda ake son yayi, kuma Safiyyah ta amince.

Amma me??? Duk da yaqinin nan da yake dashi na samun maslaha da warwarar matsalolinsu na shekara da shekaru, ya rasa meyasa hankalinsa yaki kwanciya da al’amarin kuma, watau bayan tabbatuwarsa. A lokacin da bakin alqalami ya riga ya bushe.
Duk juyin da Zayyan yayi a kan gadonsa ya rasa me yasa sai yaji rashin cikar kwalitin (ingancin) maslahar nan na mintsininsa ta ko’ina….
Yana fata da addu’ar Allah yasa maslahar da ya kawo din bai rikide ya koma biggest mistake of his life ba, madadin samo warwarar matsalarsu shi da Safiyyah.
Bai san meyasa yake ji a ransa kamar wani babban al’amari ne ya tunkaroshi ba kuma, wanda zai canza musu tsarin rayuwa bakidaya, wato kamar ya ballo hadarin da zai dokeshi daga sama, wanda zai sake ‘worsening’ komai ya dagula al’amuran, maimakon kawo maslahar da ake nema.

Don dai shi ya san Sophie itace SOUL dinshi (ruhinshi) bakidaya.
Sophie itace soyayyar dake zuciyarshi gabadaya, tabbas kwanciyar hankalinsa yana cikin nata kwanciyar hankalin.
Farin cikinsa har kullum, yana danganta shi ne da farin cikin Safiyyah. Sannan a kullum yana jingina sukunin ransa da nata sukunin ran.
To amma anya Sophie na cikin sukunin rai yau? A wane hali take? A rayuwarsu ta aure kakaf! Basu taba raba shimfida ba in dai yana gidan. Anya maslahar nan da ya samo mai bullewa ce dasu duka?
Kuma shin maslahar nan zata baima Safiyyah hakikanin farin ciki da ‘yancin da yake hango mata sanadinta? Sannan shin maslahar zata haifar da Da mai ido a garesu bakidaya???
A wannan gabar Zayyan ji yayi kansa ya kara yi masa nauyi, kamar yadda zuciyarsa ma tayi duhu, tayi nauyi cikin rashin sanin abinda ya dace yayi kuma. Domin tunanin halin da Safiyyah zata kasance a daren yau kadai ya jefa shi a rudani, wanda hakan ya jefashi a dogon tunani da dogon nazari irin mai nisan zango, irin wanda ya jima bai yi irinsa ba..

Daga wannan lokacin, a kwancen da yake bisa makeken gadonsa, cikin wani hali na kaka ni kayin zuciya da kwakwalwa, Arch. Zayyan Bello Rafindadi, ya rintse idanunsa ya shiga tunanin baya, komai ya soma tariyowa cikin idanunsa daga kwakwalwarsa, tamkar a majigin sinasinan cinema rayuwarsu ta baya ke wulgawa a idanunsa yanzu, tamkar wulgawar hotuna cikin faifan bidiyo, komai ya shiga dawo masa daki-daki tamkar a yanzu komai yake faruwa…..
Zayyan ya tafi ‘down memory lane’ wato ya tafi ga tunani da tariyo dukkan rayuwarsu ta baya shi da Safiyyah, tun daga samartaka, dating dinsu, har zuwa maganar aurensu da iyaye maza sukayi uwa sukayi makarbiya, da abinda ya wakana cikin rayuwar auren.
Watakila ta hakanne kadai zai samo hakikanin maslahar da yake laluben nemo musu, ta hanyar baiwa kansa assignment a tsayin daren yau bakidaya, mai karatu kuma yayi musu alkalanci na adalci shi da Safiyyah, ta hanyar tarawa da debewa tsakanin matsalarsu da maslahar da ya samo.
Wadda har zuwa yanzu yake tantamar cikar ingancinta koko yace still, maslaha bata kai ga samuwa ba, in kuma aka ture komai aka ce maslaha ta samu gareshi, to ga ita Safiyyah din fa???

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *