⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 3: Chapter 3

 FARKON FARI

Garin Dandume gari ne da Allah yayiwa albarkar noma da yalwar lafiyar kiwon dabbobi. Galiban al’ummar Dandume manoma ne da ‘yan kasuwar gona, sannan da makiyaya, Dandume tsohon gari ne dake cike da tubarrakin manyan malamai na addinin musulunci kamar dai mahaifin su Safiyyah.
Safiyyah ta taba bashi labarin cewa ita FGGC Bakori tayi, kuma ta yi nasarar lashe jarrabawar JAMB da tayi a boye bada sanin mahaifinta ba, saboda ya sha alwashin shi aure yakeso zai yi mata da zarar ta gama karatun sakandire in dai miji ya bayyana, saboda shi Malami ne na kwarai, bazai lamunci komai ba sai tafiya gidan aure bautar ubangiji.
Cikin ikon Allah kuma ta samu ta haye Jamb din, da yakkyawan maki mai burgewa. Tace hatta form din Jamb din, dan uwanta “Yaya Shaikh” ne ya saya mata a boye.
Kasancewar ita da Yaya Sheikh kusan a komai bakinsu daya cikin gidansu, sun saba su kashe su rufe itada shi, ba tareda ko Malam da Ammi sun sani ba, sun kasance aminai ne bayan ‘yan uwantakar jini mafi kusanci dake tsakaninsu.
Itada Yaya Sheikh (‘yan maza zar suke). Da mahaifinsa mai rasuwa Malam Abubakar da mahaifinta Malam Usman uwar su daya ubansu daya.

Bayan rasuwar mahaifinsa ne Malam Usman ya dauke shi hannunsa, sai ya damka shi a hannun Ammi, wato mahaifiyarsu Safiyyah, kasancewar shikadai iyayensa suka haifa.
Daga ita har Yaya Sheikh, duk suna da ra’ayin tayi karatu boko har zuwa jami’a, akan passion dinda take so tun tana karama, Safiyyah tana na yarinya ba abinda ta kware a kai a makaranta irin ‘Zane’, kasancewar Art class tayi, ba abunda bata iya zanawa yayi kyau ya bada suffa mai ma’ana ba, wanda yake sabanin ra’ayin mahaifinta, da suke kira “Malam” wanda kasurgumin Shaihun Malamin addini ne. Ya kan ce shi bai ga komai na amfani a cikin Zane-Zanen da take cika musu bango dasu ba.
Safiyyah ta cigaba da bashi labarin cewa, “saboda haka sabanin sauran ‘yammata irina da iyayensu ke raye har zuwa wannan lokacin, zaka ga iyayen ne da kansu suke fafutukar nema musu gurbin karatu a jami’a bayan kammala sakandire, don basa son ajiyesu a gabansu basa komai, “amma ni Safiyyah abin ba haka ya kasance a gareni ba, na san na shigo jami’a ne kawai (by chance)”.
Wato ta samu shiga makarantar ne bisa yardar Ubangiji, da ya riga ya rubuta mata ita a kundin kaddarorinta, cewa zata yi boko mai zurfi ko Malam baya so, da kuma karfin addu’ar data kwana yi akan mahaifin nata, kafin ta doshe shi da takardar samun gurbinta a safiyar ranar da sakamako ya fito.

Tace tayi addu’a sosai, ta kuma sa kananan kannenta uku mata Sabah, Rayyah da Rayha sun tayata, wadanda akwai ratar shekaru biyar tsakanin ta Sabah, sauran biyun kuwa wajen shekaru bakwai da takwas ta babbasu, tace sun taya ta addu’a ta basu sadakar cakulet sukayi ta murna, akan Allah ya dorata akan mahaifinta ya lamunce mata zuwa jami’a a birnin Zazzau.
Malam ya riga ya horesu da yin addu’a da tsayuwar dare cikin talatainin dare, akan kowanne lamari suke so Allah ya shige musu gaba a kai, don haka shima Malam bai tsira ba, a cewarta ta kai kararsa sunansa ne gaban Ubangiji akan bukatarta da zazzafar addu’a har da sadaqah wa kannenta.
Mahaifinta Shaikh Usman Ameen Ladan Dandume, fitaccen malami ne na addinin musulunci a kauyen Dandume, ba malamin allo bane malamin buzu ne, dake karantar da magidanta da samari, kowa ya san zaiyi wuya a rikon addini irin na Malam Usman ya bar babbar diyarsa taje jami’a har wani gari wai Zazzau, ba tareda igiyar aure a kanta ba. Tunda shi da kansa yake bada fatawa ga iyaye maza dalibansa a kauyen Dandume, ta hanasu barin ‘ya’yansu mata sakaka a jami’o’i batare da aure ba.
Malam Usman sananne ne a wurin tsaurin tarbiyyah, mutum ne mai kokarin kiyaye dokokin Ubangiji a gidansa, don ya kiyaye hadisin da yace “in kuna tsoron bazaku iya adalci ba, ku auri dai-daya”, shiyasa har zuwa yanzu da ya cimma shekarun girma, furfura ta sauka, bai kara auren wata mace bayan Amminsu Safiyyah ba, an sha kawo masa sadaqar ‘yammata iri iri daga kauyukan Katsina daban daban baya amsa, saboda Allah shaida ne akan Mallam yana mutunta Ammi, yana martabata, yana mutuwar sonta, duk da kasancewarta uwar ‘ya’ya mata zallah a gareshi. Bata taba haihuwar masa Da namiji ba.

Tun kafin a haifi su Safiyyah malam na rikon Dansa Ridhwan da suke kira “Yaya Shaykh” wanda ya kasance da ga dan uwansa Abubakar da ya rasu a hatsarin mota, mahaifiyar Ridhwan kuwa tun wajen haihuwarsa ta koma ga Ubangiji, don haka Sheikh maraya ne, Ammi ce ta raine shi da nonon shanu. Bai tashi ya san wasu a matsayin iyaye ba bayan Ammi da Malam.
Har ila yau Malam nada wani yaro almajirinsa da ya rika kamar Da mai suna Haroun, yaron da aka kawo masa almajirci daga Geidam ta jihar Yobe.
Don haka a lokacin da tayi jarrabawar (jamb) ta kuma ci, sai Yaya Sheikh ya nemo mata gurbi a ABU ta hanyar wani almajirin Malam mai yawan zuwa gidansu gun Malam wanda ma’aikacin ABU ne (non-academic staff), Malam bai sani ba haka Ammi daga sanda taje ta rubuta jarrabawar har gashi ta ci, daga ita har Yaya Sheikh sun san sun yi karambani, amma sun yarda addu’a bata bar kowa ba, basu taba tunanin Malam zai barta zuwa jami’a har a wani gari can, bama cikin Katsina ba, ba kuma nasu garin Dandume ba.
Ita kuma Safiyyah Allah ya sani, tun tasowarta babu makarantar da take burgeta take bata sha’awa a fadin Najeriya irin Jami’ar Ahmadu Bello, wannan ya samo asali daga kanwar mahaifiyarta Anti Dije dake aure a Zaria, kuma tayi aiki a ABU kafin ta bar aikin ta zauna a gida, a lokacin da Anti Dije ke can tana yawan zuwa hutu wajenta, Anti Dije na yawan bata labarin garin Zaria da manyan makarantun dake kunshe cikin garin. Ta kan ce “Zaria gidan ilmi ce kacokam! In kin tashi karatu Safiyyah ki taho Zaria, don samun kwali mai nagarta, saboda babu jami’a mai tsohon tarihi a arewa kamar Ahmadu Bello.

Ta san dai akwai taimakon addu’arta, domin ta roki Allah idan karatunta alkhairi ne ya baiwa mahaifinta ikon barinta salin-alin cikin sauki, idan kuma babu alkhairi kada Allah ya bata ikon tambayarsa ma, ta yiwa Ubangijinta alkawarin kare mutucinta dana addininta dana iyayenta, in har Malam ya lamunce mata zuwa karatun, ta hanyar yin shigar da zata kare martabarta data addininta, ta tsarkake idanun maza a kanta, wadda a cikinta suka taso itada kannenta mata dama, wato shiga ta kamala (Hijabs), ta yiwa Ubangiji wannan alkawarin tsakaninta dashi cewa karatu kadai zai kaita Zaria, bata da wata manufa bayansa, muddin ta samu yarjewar Mallam in ta shiga ABU bazata canza halaye da dabi’unta daga yadda suke a Dandume ba.
To shi Ubangiji a kullum niyya yake dubawa da tsarkin zuciyar bawa kafin ya amsa masa addu’a. Cikin hukuncin Ubangiji Allah ya amshi rokonta, don yaga tsarkin niyyarta karatun ne kawai a ranta. Malam Usman Dandume ya sahale mata zuwa ABU babu ja’in’ja.
Yace ba don komai ya amince ba sai don cewa itace babba cikin ‘ya’yansa, kuma dukkansu ‘ya’yansa mata ne, mata kuma masu rauni ne da kaunar juna by nature dinsu, don haka itace uwar kannenta da zata dauki takalihunsu ranar da basa nan shi da Ammi, ko ranar da karfinsu ya kare tunda basu da Da namiji a cikinsu bayan Yaya Sheikh, don haka dole ya bata damar yin ilmin addini dana zamani, a matsayin jarin da zai iya bata kadai itama ta basu (kannenta).

Malam ya rufe zancensa da cewa “kowa yayi da kyau ya sani Safiyyah, in bana ganinki Allah daya halicceki yana ganinki, ya kuma san irin tarbiyyar dana baki da abinda zaki je ki aikata a bayan idona”.
Wanan ne yasa Safiyya zama wata irin Kamilah, khashi’ah, khalisah, kamammiya, zaqaqura, zealous (mai himma) kuma smart a jami’ar. Take yin rayuwarta daidai da ita, ba rawar kai ba kidifiri. Ba karya ba kawayen banza, ba sakin fuska ga kowa walau mace walau namiji, Safiyyah taki sabo dakowa, don ma kada a abokantaketa a bata mata tunani, a shiga lokacinta, na abinda ya kawo ta, yasa hatta matan ma bata kulawa ba maza kadai ba, lokaci abu ne mai matukar muhimmanci a gurin Safiyyah, da bazata iya karar dashi akan kawancen makaranta ba, idan kuma hanya ta kure kun hadu Safiyyah zata yi maka sallama ta musulunci shikenan.
Kullum fatanta Allah ya fiddata kunyar Mallam, da yardar da yayi ma tarbiyyar da ya bata.

Safiyyah kyakkywar ba-katsina, kalar fatarta kamar ruwa biyu, hancinta da bakinta kamar na mutanen kasar Habasha (Ethiopia) ga wadatar sumar kai data gira. Ga lumsassun idanu masu matukar daukar hankalin wanda duk ta kalla dasu ba maza kadai ba.
In har bai manta ba, silar haduwarsu kenan, watau zuwanta jami’ar Ahmadu Bello da shekara daya da ‘yan watanni, tana kokarin shiga aji na biyu wato (level two).
Daga wancan lokacin zuwa shekaru goma da doriyar watannin da suka shude da yasan Safiyyah, to a jami’ar Ahmadu Bello ya fara saninta, ya kuma ganeta ne daga uniqueness na sautin muryarta (in’ina ce da ita), sautin da ya bambanta dana sauran mata, har kuma zuwa inda yau ke motsi, bai manta sautin in’inarta da yaji na farko shi yasa shi juyowa ya kalleta ba.
In’ina ba dadin saurare gareta ba, amma shine sautinta daya fara shiga kunnensa ya zauna, har gobe sautin yana nan a kunnensa, yana shawagi a kwakwalwarsa, yana masa amsa-kuwwa, don shi dadi sosai in’inar tayi a kunnensa, his fondest memories da ita kenan a kullum; (in’inarta).

Sautin da har yanzu ya kan sake yi masa amsa-kuwwa, lokaci- zuwa lokaci, idan ya tuno Safiyyah, bai mance shi ba, kuma bazai mance din ba, domin dadin da sautin in’inar yayi masa yaki bacewa daga cikin memory dinsa.
Wani irin sarkakken sauti Safiyyah keda shi, mai ‘yar gargada (stammering) wanda dai-daikun mutane kadai Allah yake jarrabta da ita.
In’ina wata lalura ce ta furta magana da kyar, ko kana yi tana makalewa, ko kuwa hardewa da ‘yar gargada haka, kana yi kana kwatota daga makoshinka da kyar, kamar yadda Ubangiji ya jarrabci AnnabinSa Musa (A.S).
Sautin nata mai tashi ne da rangwamen amo, kuma cike da zakin murya irinna ganiyar ‘yammatanci, irin dai na budurwar dake ji da kuruciyar ‘yammatancinta, (in her teens), hakika Safiyyah ta yi nasarar shiga jami’a da wuri, su ake kira JJC (Johnny just come).
Don a lokacin Safiyyah bata fice shekaru goma sha takwas a duniya ba, inma ta kai din.

Ranar da ya fara ganinta, tun kafin ya ga fuskarta shi in’inar ya fara ji, shine abu na farko da ya ja hankalinsa tamkar maganadisun mayen karfe zuwa gareta a ranar, saboda (peculiarity) din dake cikinsa, ‘yar gargadar maganarta ta masa dadin ji. Inda yaji tana maimaitawa Librarian din dake kula da (reserve section) cikin tukewa da kokarin shanye fushinta, saboda cewa da yayi wai shi baya gane me take cewa.
Kamar zata yi kuka ta sake cewa taqarqarewa tana fizgo maganar da kyar, ta ce cikin in’inarta….
“Malam…, nace-nace maka…. “Architecture, Form, Space, and Order (Frank Ching, 1979)” zaka dauko min.
“Me kike cewa ne?”
“Kayi hak-kuri….ni…ni… stammerer ce, I don’t feel repeating it again”.
Zayyan sai ya samu kansa da yin murmushi daga kwancen da yake a rigingine, yana iya hango fuskarta cikin damuwa a lokacin cikin wani sako na kwakwalwarsa, kamar a lokacin Sophie take furtawa librarian din bazata maimaita ba. Exactly over a decade now da faruwar hakan amma komai dawo masa yake tamkar a yanzu yake faruwa.

Ya juya ya sake gyara kwanciyarsa, wannan karon akan ruwan cikinsa yayi folding hannayensa a saman kansa ta baya, ya kara nausawa cikin dogon tunanin nasa.
In’inar kawai yake tunawa da bege da kewa mai yawa, kamar Safiyyah bata cikin gidan nasa a halin yanzu, bayan shine da kansa ya buyar mata cikin wani hali na rashin yarda da hukuncinsa.
“She looks so naïve and innocent budurwa tun a lokacin, amma kuma tawayar tangardar harshen ya zame mata cikas ga cika “Classy Babe (hadaddiyar budurwa”.
In ta fadi abu kuma aka ce ta maimaita ba’a gane ba, bayan hararar da zata zabga maka kamar idanunta zasu fado kasa, har kwallahr bakin ciki take yi mai zafi. Don me zaka ce baka gane ba?
Ya fara son Safiyyah daga rana ta farko da ya fara haduwa da ita. Wani abu kaman dai “Love at First Sight” ko me? Wanda yayi ta ‘nurturing’ dinsa yana nunar dashi a kasan ransa shikadai, kuma har gobe bai gama rainon nasa ba, don kullum kara tsiro yake da fidda sabuwar yabanya, yana bude sabbin rassa da sababbin ganyaryaki sabbi gadagal! Na son Safiyyah a zuciyarsa. Musamman a halin yanzu da yake tantama kan ingancin abinda ya aikata mata, da sunan nema mata maslaha a zaman aurensu.
Shi da kansa ya san bai san da kalmar da ya kamata ya suffanta ko ya kamanta ko ya kintatawa mai karatu girman matsayin soyayyar Safiyyah a zuciyarsa da cikin rayuwarsa gabadaya ba, koda harshen da zai iya bayyana girman son da yake yi mata ba yadda mai karatu zai gane, da girman matsayinta cikin rayuwarshi da duniyarshi tun daga ranar ba.

Kawai ya san cewa duk wani so na gaskiya da duk wata kauna ta hakika da Da namiji na kwarai irinsa zai iya yiwa diya mace, to shi Zayyan Bello, nashi son ya kare ne akan Safiyyah Usman Dandume.
Saboda ya so ta ne a lokacin da zuciyarsa babu nauyin komai a cikinta sai zallar kuruciya, soyayyah ce ta samartaka zallah irinta isowar shekarun hankali wato cikakkun shekaru na cikar balaga, wadanda a su ne namiji ke fara gina matakan rayuwarsa, babu nauyin iyaye da ‘yan uwa da yazo ya hau kansa daga baya.
Babu komai a ransa a lokacin sai katon fili fetal! Wanda zuciyarsa ta shimfida ma Safiyyah koriyar darduma akai, ta feshe dardumar da turaren nan na kauna da soyayya na “Sandalia” tayi mata maraba da sauka, gurbi ne dama wanda ya tanada ya ajiye musamman domin soyayyar iyalinsa kadai, amma bayan wannan babu nauyin kowa da komai a cikin zuciyarsa a daidai lokacin.
‘Yar mutanen Dandume, ta shigo rayuwar samartakarsa tun yana rubuta ‘final project’ dinsa a jami’a.
Hakan ne yasa lokacin da Safiyyah ta iso rayuwarsa daga haduwarsu ranar nan a (University Library), nan da nan tayi maza ta shige sukuf! Cikin ransa, ta baje kolinta ta hanyar mamaye ko’ina ita kadai, bata bar masa kowanne kankanin sako da zai sanya tunanin komai bayan nata ba. Har wani lokacin ya kan kirata da suna (Cinye Du) a cikin ransa, don hakika duka zuciyarsa Safiyyah ta cinye, ta mamaye ko’ina ita kadai. Ba wadda zai iya kara so kuma, bayan so na farillah, wato na Mahaifiyarsa Mama Fatu, da kannensa uku da Yayyensa biyu duk mata.

Uwa-Uba ka cire son da yake yiwa mahaifinsa (his beloved Baba Bello), wanda bazai shiga cikin kwatancen bama to duk sauran girbin dake zuciyarsa ‘yar mutanen Dandume ta cinye.
Ya fara son Safiyyah ne tun mahaifinsa Arch. Bello yana raye, lokacin da shi kansa daukar nauyinsa akeyi da komai na karatunsa, wato Baba ke daukar takalihun komai nasa, tunda dan lelen cikin mata ne shi, abin nufi shikadai Mama Fatu ke da, a matsayin Da namiji, Yayyensa biyu mata ne haka kannensa uku duk mata ne, gashi da tarin da basira a karatu, Zayyan nada rawar kan kuruciyar samartaka ta samari ‘yan bana bakwai tsararrakinsa a wancan lokacin, zaka ganshi kullum cikin nutsuwarsa da tsafta da gayu, very reserved and smart dashi, dalibin shekarar karshe a karatun digiri na biyu a lokacin yana rubuta thesis dinsa.
Dan kimanin shekaru ashirin da bakwai da haihuwa.
Saboda irin gatan da Baba Bello ke gwada masa, tunda ya gama digirin farko ya saya masa wani lafiyayyen (Bike) na yayin samari, mostly ‘yan gata na lokacin kadai ke iya hawa ‘Bike’ dinnan da ake kira (LIFAN), wanda dashi yake shanawarsa yana fantamawa da abokansa a tsakiyar ABU.

Daga nesa in ka hango shi akan ‘bike’ dinnan yana zuga gudu a cikin harabar makarantar, iska na cika rigarsa, ko idan ya shigo farfajiyar tsangayarsu a kan babur din, sai ka so kara yi masa kallo na biyu, domin zaiyi maka matukar kama ne da jarumin wasan kwaikwayon nan na kasar Hindi; Bollywood actor, Abhishek Bachchan. Saidai ace Abishekh ya fishi zama jajawur ya fishi nannadadden gashin kai. Shi Zayyan Ba-katsine ne kuma Ba-rume, wanda ya tsotso nasa ussin kyawun da hasken fatar daga Rumawan jihar Katsina.

Mahaifinsa Arch. Prof. Bello Rafindadi, dan asalin shiyyar Rafindadi ne ta jihar Katsina, shine (Chancellor) na farko na Jami’ar Umaru Musa ‘Yar Adua, sanda aka budeta.
Mahaifinsa Prof. Bello Shi ya zaba masa tafiya Jami’ar Ahmadu Bello, yana kammala karatun sakandirensa a Barewa College, babu bata lokaci ya samu admission, don shima Baba Prof. can yayi nasa digirin na farko, sauran kuma a UDUS, Baba Bello yana da burin dan shi Zayyan ya karanci abinda shima ya karanta ya samu daukaka, arziki, shuhura da cigaba mai yawa akan profession din, watau “Architecture”.
Burinsa tun a lokacin shine Zayyan dinsa ya gajeshi akan komai da yake kai, kasancewarsa Da namiji tilo daya mallaka cikin tarin ‘ya’yansa mata.
**** ***** *****
Jim kadan bayan ritayarsa daga aikin gwamnati, Baba (Prof) Bello Rafindadi, ya koma harkar contract na zanen gidaje da ginasu da bada hayarsu, harkar da ake kira (Real Estate) irinna zamani a manyan biranen kasar nan.
Baba Bello ya samu tsundumawa a wannan harkar ne ta hanyar amininsa Arch. Murtala Babangida Masari, wanda shi ya jima a harkar (Real Estate) da gwamnatin Najeriya, Alh. Murtala bai taba aiki a jami’a ba, sai a harkokin real estate. Alh. Murtala Ya tara arziki mai yawa a real estate business.

Baba Bello yana yawan cewa.
“Zayyan gashi dai shi daya a gabansa tilo, amma daya ne tamkar da dubu”.
Kasancewarsa ya taso namiji daya a cikin ‘ya’ya mata biyar, yasa Zayyan ya tashi da dabi’ar yawan tausayawa ga mata, duk inda ya ga mace babba ko yarinya yana girmamata, in da halin taimako yana taimaka mata, ya iya hakuri da halayensu sannan duk dabi’un mata na rauni da kyuya Zayyan ya sani, ya kuma iya tafiyar dasu, tunda gabansa da bayansa duk ‘ya’ya mata ne a dakin Mama Fatu. Mace daya tal da Baba Bello ya aura a lokacin rayuwarsa.
Har Mama Fatu ta gama haife – haifenta wato ta iso (menopause) bata taba yin tsarin iyali ba, Zayyan kuma bai samu kani namiji ba, sai kanne mata uku.
**** ***** *****

SHEKARA TA 2012
Itace shekarar da ya hadu da Safiyyah. A wancan lokacin, wajejen shekarar ta dubu biyu da goma sha biyu, mawuyaci ne ka samu yarinya mai kananun shekaru mai kamun kai da tsare mutuncin gidansu a jami’ar Ahmadu Bello, kamar Safiyyah Usman Dandume, wadda ake kira Safiyyah Dandume, ta shigo jami’ar da shekaru goma sha bakwai kacal. A halin yanzu kuma ta shiga level 2 tana neman cika sha tara.
Safiyyah Dandume, ta riga ta siffanta kanta da dabi’u na kamun kai a idon kowa, da suttura ta mutunci, ta hanyar yin kyakkyawar shiga ta kamala, don haka mazan banza shakkar dosarta ma suke, haka kawayen banza don babu fuskar neman kawance da ita, a cikin ‘yammatan dake tashen kokari a karatu a tsangayar ‘Architecture’ Safiyyah Usman Ladan, tayiwa kowacce yarinya a department din zarrah, ta yiwa tsararrakinta da abokan karatunta da yawa fintinkau wajen maida hankali ga abinda ya kaita, in akayi jarrabawa ta karshen zango da (CGPA 4.50) take fita. Kullum addu’arta da fatanta shine cikawa Malam alkawarin data daukar masa, na cewa karatun jami’a bazai sa ta canza dabi’un ta da halayenta masu kyau daya riga ya santa dasu ba.

Kai shi bama wannan labarin da yake yawan ji akanta bane abinda ya fara attracting dinsa ga Safiyyah ba, irin saurin maganarta dinnan (in’ina) da take masa dadin ji, Safiyyah ga ga sassanyan kyau, ga rangwada irin ta ‘yammata, wata irin rangwada ta halitta Safiyyah keda ita cikin Hijabi, komai nata Zayyan ya rasa mai yasa, ko ba mai kyau bane shi kyau yake masa, ya kuma burgeshi, ya kara kawatar da ita a zuciyarsa.
Bai manta ba. A ranar da ya fara ganinta Safiyyah a kule take, kuma a harzuke da malamin labirare dinsu, amma duk da haka tana kokarin shanye harzukarta, saboda cewa da yayi bai gane in’inarta ba, so take malamin labiraren ya dauko mata wani littafi daya shafi abinda take karantawa, tana so zata zauna a labirare tayi Assignment, ta fada har sau biyu amma mutuminnan yace wai ya kasa gane me take fada da gangan da iya shege, kyakkyawan bakinta kawai malamin labiraren ya kurawa ido, sabida saurin bakinta na halitta mai hade da hardewa da tangardar harshe.

Shikuma Zayyan dake bayansu yana jira ta gama shima ya karbi nasa, tun bata rufe baki ba shi ya gane me tace, ko don shima littafin da ya zo nema din kenan?
Yana jin su itada malamin labiraren suna magana, Safiyyah tana kara cewa bazata maimaita ba, shikuma librarian yana faman cewa “Na’am?? Hajiya sake fade inji?”
Hakan ya tunzura Safiyyah taji haushi sosai, har kwallah ta cicciko a idonta, ta kwanta a kasan kwayan idanun nata, kiris take jira ta zubo akan kundukukinta, a can baya Malam mahaifinta kullum da safe yana karanta ayar;
“Rabbish’rahly sadry, wa yassirly amry, wahlul uqdatan min lisany, yafqahu qauly…..”.

Yana tofawa a ruwa yana bata tana sha sanda tana yarinya, shine ma ta samu saukin in’inar, amma duk da haka abin bai tafi gabadaya ba, saidai ya ragu sosai. Tunda har in ka saba da ita data fada zaka gane.
Tausayinta Zayyan yaji ya kama shi, ganin tana neman barin wajen cikin kufula, ya tuna wani abokinsa a sakandire mai suna Saleh Wangara shima haka yake da in’ina (stammerer), sai ya samu kansa da yanke shawarar saka musu baki, wanda hakan ba halinsa bane shiga maganar da bada shi akeyi ba.Amma kwarai yarinyarta bahi tausayi.

Zayyan sai ya samu kansa yana maimaitama malamin labirare me yarinyar nan take cewa, cikin nitsatstsen lafazin Ingilishinsa.
Ganin cewa yarinyar ta zo wuya har tana hadiye hawaye da kyar, tana kuma kokarin barin wajen don haushi, ba tareda an bata littafin ba.
Kawai daga bayanta taji mutumin dake tsaye a bayanta yace ma Librarian din cikin nutsuwa; Tana son ka bata.
“Architecture, Form, Space, and Order” na (Frank Ching, 1979)”.
Abinda bakinta ya kasa fada correctly.

Kuma abinda ta fada din kenan a zahiri, sak babu bambanci, shida bada shi take maganar ba, tsaye kawai yake a bayanta, yana jira ta gama ya karbi nasa, ya gane furucinta, amma librarian dinnan don yasa ta tayi ta maimaita magana yana karewa dan kyakkyawan bakinta da motsin siraran labbanta da suka sha ‘wetlips’ mai santsi kallo, suna sassarfa da hardewa da juna, wajen yin furuci shiyasa yace wai bai gane ba.
Aka dauko littafin aka miko mata, kamar tace a mayar ta fasa, sai kuma ta kasa musamman da suka hada ido da wanda yayi mata ‘speech interpretation’ din. Kallon da yake mata na lallashi ne, mai nuna cewa kada ta yi fushi, ta amsa tayi karatunta.
Sai tayi masa kallon Rahma itama. Ta kuma kasa tankwabe lallashin dake cikin idanunsa. Ya fahimci hakan, sai yayi mata murmushi na Sanya salama. Yace.
“ki karba ko?”

Ya tsareta da kyawawan Katsinawan idanunshi, hakan yasa sai ta kasa kin karba, domin zai zama kamar ta gwasile wannan taimakon nasa da kulawar nasa ne.
A hankali ta amsa, bakinta na kokawa da halshenta wajen motsin fizgo kalmar.
“Na – gode sosai fah!”.
Sai tasa kai ta wuce su, zuwa ainahin cikin dakin karatun, kai tsaye Safiyyah ta wuce zuwa wata corner a can kuryar library din, inda a can ta saba zama duk sanda ta shigo cikin dakin karatun.
**** **** ****

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *