⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 4: Chapter 4

THE STAMMERER

Yau karo na biyu kenan da ganinsa da “Stammerer” (sunan da yaji malamin labiraren ya kirata kenan rannan bayan wucewarta), yau ma tazo dakin karatun kamar yadda ta saba, ta shige can kuryar da take zama, ya riga ya gane yanayin maganarta na halitta kenan (stammering) tun daga ranar farko da ya fara ganinta, wanda bazai gaji da cewa shi yafi komai daukar hankalinsa a kanta ba, fiye da kyawun surarta, ya kuma zame mata symbol a wurinsa, wanda duk inda yaji sautinta nan da nan yake gane itace, ko in yaji mai irinsa ya tuno ta, ya kuma fahimci cewa a tsangayar da yake ta ‘Architecture’ itama take karatu, saidai undergraduate student ce ba kamar shi da yake postgraduate student ba, ya gane hakan ne daga wannan littafin da tasa aka dauko mata rannan.
Kullum yana shiga library ne don yin research da rubutu, baya son karatu cikin hayaniya sam, idan ya shiga yana samun can wata corner ne shima a can karshen dakin ya zauna inda ba’a iya ko hango shi sosai, baya son idan yana karatu a katse shi, shiyasa baya yin karatu a (tutorial) da ‘yan ajinsu. Hakan ya maida shi ‘regular visitor’ na library din, saboda a lokacin yana bincike yana rubutun (final project) dinsa na kammala digirinsa na biyu.

Yana matukar shiri da Librarians da sauran ma’aikatan dakin karatun, idan ya shiga karatu sallah kadai ke fito dashi, wani lokacin zaka samu har gyangyadinsa yake yi in ya gaji da karatun a corner dinsa, duk da Zayyan mutum ne mara yawan sakin fuska ga mutane da karancin far’a, amma fuskarsa wani lokacin da walwala, ko babu far’a, hakan kuma baya nufin shi miskili ne, a’ah, kamewa ce kawai ta halitta da rashin son daukar wargi, duk da haka in dai zai ga ma’aikatan library din sai ya gaisa dasu cikin sakin fuska, wannan ne yasa duk suka saba da shi ya zama shima kamar ma’aikaci ne a cikinsu ba dalibi ba.
Yanzu ya lura da wani abu, duk sanda ya shigo library ya zauna a corner din zamansa, yana yawan ganin wani (pink travel mug) a desk din da yake gaban nasa, mamallakiyar wannan ‘travel mug’ din itama ya lura ‘regular visitor’ ce kamar shi. Bayanta kawai yake iya hange kullum tana sanye da Hijab ko jilbaab. Har a ransa ya saka mata suna ‘Hijabie’ domin ya fuskanci ma’abociyar suturta jikinta cikin Hijabi ce, kullum cikin kyawawan Jilbaabs ko Hijabs yake ganinta, wata shiga da kannensa su Zahra sam basa yin kwatankwacinta. Kuma shigar ba karamin kyau take yi mata ba (a idonsa).

Ba koyaushe yake ganinta ba amma dai tana yawan zuwa, idan ya hangi (pink travel mug dinnan) ya san ta zo kenan, koda bata wajen, to ta dan tashi zuwa sallah ne.
Da alama shayi ko coffee ne mai zafi a ciki, kuma idan ta saka littafinta a gaba to ko juyowa bata yi.
Ba ruwanta da duk abinda ke wakana a cikin library din. Sai ya kasance shikuma a rayuwarsa he’s in love with such kind of serious and decent charcter, shiyasa take burgeshi deep down inside him, yake girmamata a kasan ransa, ba tare da ya san kamannin fuskarta ba.
Watarana ya shiga research kamar yadda ya saba, sai ya ga seat din ‘Hijabie’ babu kowa, sai ko ‘Pink Travel Mug’ dinta na gado ajiye a wurin.

Sai yaji idanunsa na kewar ganin bayanta da ya saba gani in tana karatu, kawai yaji sha’awar zama a wajen nata, sai ya zauna (for a change). Don shi dai a duniya yarinyar nan da yanayin sutturarta da decent nature dinta, duk suna matukar tafiya dashi.
Yana tsaka da aikin gabanshi sai yaji kamar tsayuwa a bayan shi. Ta zo zama a gurinta, sai taga wani zaune a gun, bayan kuma tayi shaida a wajen da littafinta da Mug dinta, sai ta tsaya kyam, ya dago a hankali ya dubeta.
Nan da nan ya ganeta ashe yarinyar nan ce mai in’ina, ita keda Pink Travel Mug. Yayi mata sallama hade da murmushi, yace “na zauna miki a wajenki ko? Sorry!”
Yana dagowa dinnan nan take ta gane shi, (her speech interpreter)!. Itama sai tayi murmushi, da sasssarfar maganarta tace
“so, it is you?”

“Ashe baki da mantuwar fuska?”
Ta sake yin murmushi tace “Ba sai ka tashi ba, tunda ai wajen na kowa ne, babu mai (permanent seat) a wajennan, kawai sabo ne yasa nake zama anan din, bakomai Mr, bari na juya na nemi wani wajen, Nagode”.
Sai ya hau tattara takardunsa daga kan desk din, yace mata “ayi haka? Hijabie, zo kiyi zamanki. Mai waje ya zo mai tabarma sai ya nade ko? Kayan aro baya rufe katara”.
‘Yar dariya Safiyyah tayi tace. “bafa sunana Hijabie ba Mr. Library. Sunana Safiyyah Usman Dandume”
Zayyan yace “madallah da Nana Safiyyah, ni kuma Zayyan nake, sunana Zayyan Bello, ba Mr. Library ba”.

Sosai ya bata dariya ta kuma yi zaman ta a wajenta daman tafi son wajen, ta saba da seat din sosai.
In bai manta ba, daga nan tushen alaqarsu ya samo asali tsakaninsa da Sophie. And in no time, sabo mai tsanani ya shiga tsakaninsa da Safiyyah, kowanne ya shiga yaki da halinsa akan dan uwansa; abun nufi, Safiyyah ta cirewa kanta rashin kula mutane da rashin son yin mu’amala dasu akan Zayyan, shikuma ya cirewa kansa fuskar rashin walwala da sakin fuska in dai yana tare da Safiyyah a makaranta, to kuwa zai nemo walwala duk inda take ya sakawa kyakkyawar fuskarsa, a haka har suka fara sabawa outside library.
Kasancewar duk suna karkashin tsangaya guda hakan yasa suna yawan haduwa shi da ita a department dinsu, kuma gashi sun fito jiha daya, sai suka kara zama abokan juna, kuma abokan karatu na sosai ga junansu.
Duk da haka Safiyyah na kaffa-kaffa bata bari wata hira ta hadasu bata karatun da ya kawota ba. Shima kuma Zayyan Bello haka. Kullum kara wayar mata da kwanya yake akan dabarun dake cikin ilmi Zane. Har aka zo gejin da tafi jin dadin koyarwar Zayyan, fiye data dukkan Mallamansu.

Bata san ma ya akayi shi ta saki jiki dashi har haka ba, alfarmar da bata yiwa kowanne da namiji a fadin jami’ar nan ba. Kai har mata ‘yan uwanta, Safiyyah bata sakewa dasu, kamar yadda ta samu kanta dumu-dumu da sakewa da Zayyan Bello. Wadanda sun riga sun nada mata rawanin mai girman kai.
Har wasu ‘yammatan masu kishin irin kyawun surar da Allah yayi matam, da yadda take jan attention din maza akanta cikin Hijabi, su kan yi gulmarta da cewa, ita ba ‘yar kowan kowa, ba sai kafirin girman kai.
Rashin yawan far’arsa ko kadan baya damunta, don ta gane nature na halittarshi ne haka, ba kuma miskilanci bane, amma akwai shi da dadin mu’amala ga wanda zuciyarsa ta amincemawa yayi alaqa dashi kamar yadda ta amince da ita Safiyyah. Tarin nutsuwarsa da yawan kokarinsa a karatu, sun taimaka gaya wajen sakewar Safiyyah dashi, don ta tsani alaqa da miskilin mutum ko dakikin dalibi.

Wani abu a halayyar Safiyyah shine; in dai kana da kokarin da zata amfana dashi a karatu, to kowanne irin hali gareka zata iya tafiya tareda kai salin-alin.
To hakan ce ta faru tsakaninta da Zayyan Bello, Zayyan bashi da far’a, baida walwalar fuska ko kankani, babu kuma fuskar wasa a tare dashi, amma akwai tsantsar kokari da fasaha a ilminsu na Architecture, da ba duk dalibai keda su ba, ga yawan kamewarsa daga kule-kulen ‘yammata da abokai barkatai shima, wadannan sune manyan dabi’unsa da ke burgeta dashi, suka kuma bashi (100% acceptance) a wurinta. Dama an ce sai hali yazo daya ake abota.
Ya zamana Zayyan na taimaka mata sosai a harkar karatunta, a matsayinsa na gaba da ita a shekaru da matakin karatu a lokacin.
To shi dai Zayyan daga karshe bai tsaya batawa kansa lokaci ba, ko yaudarar kansa na tsayin lokaci, kamar yadda Safiyyah ke yaudarar kanta da cewa abokantaka ce ta karatu a tsakaninsu, ya tara hankalinsa waje daya ya gayawa kansa gaskiyar cewa ainahin son Safiyyah Dandume zuciyarsa ke yi, so tsantsa kuma na zallar soyayyar Da namiji ga ‘ya macen data dace da duka burikansa, babu wani friendship ko makamancinsa a zuciyarsa gameda Safiyyah, bayan So na sahihiyar soyayya a ransa.
Da yaga zai Takura, da tunanin ta yadda zai bullowa Safiyyah, saboda ba fuskar hakan a wurinta, tunda har ta kai shi ga kasa karatu yanzu da raba dare cikin tunanin Safiyyah Dandume, haka zai kwana yana juyi a kan gadonsa cikin shakkar yadda zai tunkareta da zancen SO.
Kwarjinin da Safiyyah ke masa ba kadan bane, ya yarda Hijabi sutturah ne kuma kamala ne da Karin mutunci ga diya mace, da ke saya mata martaba da kwarjini a idon maza, in dai don Allah take saka shi, daga lokacin ya fahimci cewa lallai son Safiyyah azimun ne a ransa, kullum kuma son nata karuwa yake yi cikin ransa.

Safiyyah ce kadai burinsa a halin yanzu, kuma wani babban kuduri da yake son cimmawa a rayuwa yanzu shine aurenta.
A zahiri, wani abu da bai taba planning dinsa nan kusa ba shine “aure”, tunda ko a makaranta yake har yanzu bai ko kammala rubuta final project dinsa ba, balle ayi batun neman aiki dana abun rike iyali, wanda kullum Mama Fatu ke kwakwazon sai ya samesu wato sai ya tsaya da kafafunsa kafin ta samo masa matar aure daidai da ra’ayinta.
Amma duk Safiyyah ta canza komai yanzu, ta birkita lissafinsa ta yi katsalandan cikin kowanne irin tunanin hankali daya mallaka, da kutsowar cikin zuciyarsa da rayuwarsa. Don haka bai wani tsaya jinkirin da zai zama batawa kansa lokaci ba, ya yanke mai fishsheshi ba tareda ya nemi shawarar kowa ba.

Yaga gara ya badawa idonsa toka kawai ya cire shayin Safiyyah da kwarjininta ke saka masa daga idanunsa, ya furta mata zahirin abinda ke zuciyarsa in yaso duk yadda Safiyyah ta karbi al’amarin zai jure ya iya karba.
A washegarin ranar da ya yanke wannan shawarar da zuciyarsa suna tafe shi da Safiyyah a hanyar zuwa tsangayarsu bayan sun fito daga library, labarin kannenta take bashi da suka zana jarrabawar (jsce) a yau wato Sabah da Rayha, Zayyan ya dubeta admiringly ko yadda take labarin cikin wahalar in-ina kara sonta yake yi, bai iya ya bari ta gama bashi labarin ba ya katseta.
“Hijabie, ina son zuwa gidan ku fa!”. Safiyyah ta dubeshi da dan mamaki da dan tsoro a idanunta, saida yaji tsigar jikinsa ta tashi, tace “gidanmu? To me akeyi a gidanmu Mr. Library?”
Ta bashi dariya sabida tsakaninta da Allah ta shiga damuwa da jimami. Don ta san halin Malam sarai, sanadin haka zai iya katse karatun, don wannan ba shine alkawarin data daukar masa ba kafin ya barta tazo makaranta.
Zayyan ya samu sa’a mai ban mamaki a kanta da ita kanta take mamaki. Yayi magana cikin sauti na kwantar da hankali, ganin yadda kalamanshi suka sa ta shiga rudu, yace,
“Safiyyah, mu zama frank da junanmu, zumuncinmu nida ke mai ma’ana ne a wurina, mai nufin yada kyakkyawar yabanya, kuma shine abinda zai kawo ni gidanku gaban iyayenmu”.
Safiyyah ta gyara zaman hijab dinta a kanta, ta langabar da kai tace “idan kuma Malam yace wanene kai? Ko meye tsakaninmu idan kaje me zan ce masa? Ka dai bari sai na sanar dasu a gida tukunna, don Babana Malami ne babba, baya bari azo masa gida haka kawai babu dalili”.

Zayyan ya kankance ido yayi mata wani shanyayyen kallo da bai taba yi mata ba, yace “ai nima ba hakanan zan zo ba Hijabhie, ba haka kawai ce zata kawo ni gaban Malam ba, banza tana kai zomo kasuwa ne?
Safiyyah stop kidding and joke apart pls, Hijabi na dake ajiye a gidansa nake so in dauke abina.
A takaice zan iya cewa soyayyah ce ‘yar gaske, wadda ta dabaibaye ni, da neman irinsa mai albarka zai kawoni gidansa.
In kika ga kare na sunsunar takalmi ki tabbata dauka yake so yayi Safiyyah!?”

Safiyyah ta rufe ido da hannayenta da suka sha adon jan lalle, taji kunya matukar gaske ta lullubeta, rana ta farko da wani namiji da zuciyarta ta riga tayi na’am dashi ya furta mata kalmar SO a tsanake, tace cikin jin nauyi da farin cikin da take kokarin dannewa, don gabadaya sai yau tasan ashe itama ta fara kamuwa da son dan ‘little gentle’ saurayi Zayyan din, ba haka kawai zuciyarta da ruhinta suka sake dashi cikin dan kankanin lokaci ba, SO ne gangariya, dan asali na hakika Allah ya gittar a tsakaninsu.
Don haka cike da jin kunya Safiyyah ta sunkuyar da kai tana kokarin hada kalmar da zata bashi amsa wadda bazata nuna eager dinta ko amincewarta farat daya ba, tace a hankali.
“Amma dai ka fara bari in sanar a gida first, cewa kana so kazo ka gaida Malam, in yaso ya baka iznin zuwan, saboda kafin Malam ya barka ka zo wajena fa sai ka je ka fara samunsa takanas, ka zuba gwuiwa a kasa ka gabatar da kanka da dalilin zuwanka, ya baka yardarsa, da lokacin da zaka dinga zuwa, wannan shine, bisa tsarin gidanmu.

In ba haka ba zuwanka kai tsaye zai zame min matsalar da zata iya yin sanadin karatuna”.
Zayyan dai ya fahimci ya zo gida na mutunci da tarbiyyah irin wanda yake fatan samarwa ‘ya’yansa. Kuma aka ce labarin zuciya a tambayi fuska, ko daga idanunnan na Safiyyah masu nuna yawan jin kunyarsa yanzu, da jin nauyinsa tuntuni, yau kuma gabadaya sun kara canzawa da yawan kaucewa haduwar idanunsu. Uwa Uba, amsar da ya samu daga gareta yanzu, ya san Safiyyah tayi na’am da shi dari bisa dari ko bata furta kai tsaye ba.
Don haka shikuma bai yi kasa a gwiwa ba, ranar Juma’ah kwana uku da yin wannan maganar tasu, bayan an sauko daga masallaci ya sake daukar wanka na musamman, daman dai shi Zayyan kowa ya shaida ma’abocin iya daukar wanka ne, ga iya sanya hula a kan goshinsa, ya dauki karin hular Zanna Bukar da ake yayi a lokacin, da karin gugar shaddarsa ta yayi, ya fesa turare sannan ya fito daga dakinsa ya nufi cikin gidansu, nan yayima Mama sallama kan zai je unguwa, har Mama tana tsokanarsa ko daurin auren babban amini Habibu zai je ne? Irin wannan kashe hula a goshi Baffana? Murmushi yayi bai ce komai ba, don abu na karshe da Mama zata kawo a ranta shine Zayyan dinta zai iya kallon wata mace da sigar soyayyah balle har yace yana so, sabida kamewarsa da dattakunsa na halin manya irinna mahaifinsa, ya fita ya kama hanyar Dandume a motar haya bayan ya rufe dakinsa dake BQ na gidansu.
A ranar Safiyya na gida tazo yin hutun karshen mako, tunda bata da lecture ranar Juma’ah tun sassafe ta kamo hanya ta taho gida, kasancewar a Zarian tana zama ne a hannun Antinta Dije dake aure a Tudun Wadar Zaria. To kusan duk bayan sati biyu zata taho Katsina a ranar Juma’ah, ta dawo Zaria Lahadi da yamma.

Zayyan koda kuskure bai gaya mata a wannan satin zai zo ganin mahaifinta ba. Don haka ita kanta bata san da zuwansa ba ko alama. Tama manta da zancen da sukayi dashi kwanaki uku da suka gabata.
Tun daga zauren farko da ya iso Safiyyah ta shaki wani kamshin turare data yiwa farin sani amma ko kusa bata kawo shi bane a zauren gidansu, har cikin gidansu turaren Zayyan ne mai dadin kamshi na Ultraviolet (Paco Rabanne), Zayyan Bello ya iso gidan ne ta hanyar bin adireshin da Safiyya ta kwatanta masa tun daga tashar Dandume aka dauko shi a babur har kofar gidan, don haka bai sha wahalar samun gidan Alaramma Usman Ladan ba.
Kasancewar mahaifinsu Safiyya sananne ne kuma fitaccen malamin addini a ciki da wajen garin Dandume, don haka Zayyan yana sauka a tasha yayi tambaya sai aka hadashi da mai babur ya dauko shi, bai sauke shi a ko’ina ba sai kofar gidansu Safiyyah.
Da yake yammaci ne na Juma’ah magidanta na unguwar ya tarar tare da Malam din, suna daukar karatun yammacin Juma’a yadda suka saba, kowanne magidanci da irin littafin da Malam yake karantar da shi. Zayyan sai ya shige cikin daliban malam masu daukar karatu ya zauna ya saje dasu abinsa, duk da shine kadai yaro matashi a cikinsu, saika rantse dalibin malam ne saboda yadda ya nutsu yana sauraren karatun da Malam ke badawa.

Malam na lura da bakuwar fuskar, mai zubin kyawun fulanin Rumah daya cakude da kamannin ‘yan Rafindadi ma’abociyar kuruciya a cikinsu, ya ga kuma shi bashi da littafi a gabansa amma ya tattara hankalinsa ya nutsu yana sauraronsu. Hakan yasa lokaci zuwa lokaci Malam na daga ido yana kallonsa yana cigaba da bada karatu. Bai kula shi ba, har sai da ya gama da dalibansa gabadaya.
A karshe aka yi tamabayoyi akan darussa daban daban da aka karantar, sannan aka yi addu’a ga iyali da al’ummar musulmi da kasar bakidaya, aka shafa tare, yadda Malam da dalibansa suka saba kullum, kowa ya soma kokarin saka takalminshi don barin zauren gidan Mallam.
Shi kam Malam har lokacin yana zaune akan buzunsa yana musabihar sallama da dalibai masu ficewa, Zayyan yana zaune gefe a inda yake tun shigowarsa, bai yi niyyar tashi ya karasa gaban Malam ba, kuma bashida niyyar tafiya.
Ya rasa ta ina zai fara, gabatar da kan nasa ko gaida Mallam din? Kamar yadda Safiyyah ta gaya masa ko waye Babanta, yaga har fiyeda hakan, yaga dattaku da tarin ilmin addini, don gabadaya kamilin dattijon Malam Usman wanda fuskarsa ke cike da farin gemu zagaye da farin saje yayi masa kwarjinin da ya hana shi ko motsi. A hakan kuma duk da alamun tsufa mai nagarta dake tareda Mallam, wanda bai yi yawan da za’a kira shi tsoho can ba, sai farin gemun da ya nuna shekaru sun tura, duk da hakan Alaramma yana dan diban kama da kyakkyawar diyarsa Safiyyah sosai.

Har saida Malam ya gaji da sauraronsa yayi magana don yana so ya shiga cikin gida, yace dashi cikin mutuntawa da tausasawa.
“Samari, ina fatan lafiya? Ko zan san daga ina kake? Ban wanye da kai sosai ba, kuma naga kai baka dauki karatu ba”.
Zayyan ya muskuta ya gurfana gaban Mallam, kamar mai neman gafara, yayi ta maza kansa a sunkuye cikin kunya yace,
“Allah gafarta Mallam ni Danka ne, sunana Zayyan Bello, nazo daga unguwar Rafindadi ta nan cikin Katsina, musamman don in gaisheku in samu albarkarku, in kuma gabatar da kaina a matsayin mai So da kauna ga irinku dana tsinta a jami’a mai albarka, wato diyar wajenku Safiyyah, wanda nake fatan ya kaimu ga zama abu guda, cikin yarda da amincewar ku, da sanya albarkar ku.
Idan Mallam yayi min izni, ina so na saka kai ga fara neman aurenta”.
Ya kara dukar da kai cikin dar-dar, na fargabar amsar da zai samu daga dattijon.
Malam Usman ya dubi Zayyan wanda kansa ke sunkuye, tsantsar hankali da ladabin da ya nuna masa, da nutsuwar dake tattare da zancensa, sannan appearance dinsa bai nuna duniyanci ba, a’ah appearance ne na samari masu tarbiyya da kula da addini ya gani a tare da Zayyan, sune kuma abinda suka dauki hankalinsa matuka akan yaron, suka canza tsohon tunaninsa nan da nan suka juya kudirin daya dade dashi a ransa bai taba gayawa kowa ba.
Ga yaron da kyawun fuska dana kirar jiki irin na zaratan mazan Rafindadi son kowa. Masha Allah dashi.

Mallam ya nisa sannan yace “samari na ji bayanin ka, madallah da hankali irin naka da baka tare Safiyyah a hanya da maganar soyayya ba, a’ah sai kayi tunanin ka zo gare ni, ni mahaifinta ka nemi iznina.
Wannan ya nunamin kalar tarbiyyarka. Da wannan halin kwarai daka nuna na ladabi da sanin girman iyaye, ni kuma na baka iznin ka dinga zuwa ganin Safiyyah sau daya a sati, idan ta zo nan gida hutun karshen mako da take zuwa har ku daidata kanku.
Samari ban yarda ka dinga tareta a wurin karatunta ba, yin hakan karya dokata ne, sai a nan gidansu kadai, kodayake ta kan yi sati biyu bata zo ba, amma dai in har ta zo gida, na yarje maka ka dinga zuwa wajenta, anan zauren na yarda ku dinga zantawa, idan kuka daidaita kanku na kuma gamsu da nasabarka, to ni bani da abin cewa sai binku da kyakkyawar addu’a da fatan alkhairi”.
Dattakun mahaifin Safiyyah da wannan tsaftatattar Malanta da ya gani mai girma, ya kara masa kaimi da ninkin son hada iri da mahaifin Safiyyah.
Don haka a ranar bai ko nemi ganin Safiyyah dake cikin gidan ba, bayan sun gama magana da Alaramma Usman sai kawai ya juyo gida cike da wani irin farin ciki, da doki da zumudi mai yawan gaske, ya isa gidan iyayensa a Rafindadi. Ya san daga Baba har Mama zasu yi farin ciki da irin gidan daya nemo aure.
**** **** ****
WANENE ZAYYAN?

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *