Chapter 5: Chapter 5
Tunaninsa ya mika ya tafi ga ainahin asalinsa, tushensa da tarihin iyayensa.
Iyayensa duka Katsinawan Dikko ne na asali, gidan mahaifinsa babban gida ne ginin zamani, yana nan daga farkon shigarka shiyyar Rafindadi, wanda a yanzu ya zama ‘landmark’ na kwatancen kowanne gida a unguwar, misali da ka ce “layin gidan Bello Rafindadi” ko yaro karami zai nuna maka. Mahaifinsa Arch. Bello dan asalin shiyyar Rafindadi ne, gabansa da bayansa can aka haifeshi, iyayensu da kakanninsu sune tushen kafa/assasa Rafindadi a Charanchi.
Gidan Bello Rafindadi ya fita dabam ne a unguwar kasancewar yafi duk wani gida a unguwar girma da fadi da daukar hankali, kai har ma da kyawun tsarin gini, wanda akayi bisa doron ilmin abin, don hatta ginin gidan, Prof. Bello Rafindadi shi da kansa ya zauna ya zana ya tsara ya kuma gina abinsa daidai da yadda yake so, kuma daidai da yawan ‘size’ din iyalinsa.
Tsohon dan bokon da a halin yanzu yayi ritaya. A can baya kafin ya mallaki wannan gidan da suke ciki shida iyalinsa suna zaune a karamin gidansa na gado duk a unguwar ta Rafindadi.
Arch. (Prof.) Bello Rafindadi ya rike mukamai iri-iri a jami’o’in arewa, mukami na karshe da Baba Bello ya rike shine na “Chancellor” a jami’ar Umaru Musa ‘Yar Aduwa, Katsina.
A lokacin nan da Zayyan ya gano Safiyyah, Baba Bello bai jima da yin ritaya daga aikin gwamnati ba.
Bayan ritayarsa, Baba Bello bai zauna a gida ba kamar sauran retirees, don har lokacin da sauran karfinsa da koshin lafiya, in ka ganshi ma bazaka yi tsammanin yanada shekarunsa ba sabida yadda yake kula da lafiyarsa, yana barin koyarwar jami’a sai ya koma kacokam ga harkar karbar kwangilar gini data zana gidaje, ginin ma’aikatu da ginin Estates ga gwamnati.
A hankali ya soma samun kwangila sosai daga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Katsina, bisa taimakon abokinsa amininsa tun na kuruciya kuma ubangidansa a harkar Zane da gini, wanda shi ya tsunduma shi a harkar kwangilar gine-gine, kuma shi yake taimaka masa wajen samun wadannan kwangilolin, wato Alhaji Murtala Masari.
Bada jimawa sunan Baba Bello ya kara fita a Katsina a matsayin babban contractor na gine-gine da zane-zane ga gwamnatin jiha data tarayya.
Arch. Bello da maidakinsa Hajiya Fatima, wadda kowa yake kira da “Mama Fatu”, suna tare tun aurensu na saurayi da budurwa, duk wani fadi tashin rayuwa na Baba ya sameshi ne tareda Mama Fatu. Haihuwarsu ta farko sun fara ne da haihuwar yara mata har biyu, kafin su samu haihuwar Zayyan a matsayin namiji na farko, kuma Da na uku a gidansu.
Babbar Yayarsu Zayyan Yaya Zubaidah tana aure ne a garin Batsari, sai Yaya Zubaina ita kuma a Kano take aure. Zaituna da Zahra da Hatoon ‘yammatan Mama duka suna gaban ta, Zaitoon da Zahra suna jami’ar Umaru Musa, a mataki da tsangaya daban-daban yayinda autar Mama Hatoon take ajin karshe a sakandiren ‘yammata ta FGGC Gusau.
Shine Da na uku kenan a gidansu, wanda ya biyo ‘ya’ya mata biyu a haihuwa, uku kuma suka rufa masa baya shikuma.
Mama Fatu sautari in tana hira da manyan kawayenta zaka ji tana fadin Baffa wato (Zayyan) ya iya zama da mata, don cikinsu aka haifeshi, cikinsu ya tashi, ya san halinsu ya san rauninsu, yana yawan tausaya musu”.
Wani Zubin kuma Mama kan ce “ko wacece tayi sa’ar zama matar Baffa ta huta. Don zata ji dadin zama da shi, ya iya kula da mata tun yana yaro. A cewar Mama da wuya ya zama mijin mace daya, wato bazai iya zama da mace daya ba, don ya riga ya saba da zama da mata da yawa. Wannan hasashen Mama ne a matsayinta na Uwa, domin hakika Zayyan yanason sisters dinshi, yana tarairayar bukatun ‘yan uwansa mata fiyeda komai. Duk wani aiki mai wahala na kitchen ma baya barinsu suyi, shi yake karba yayi mata, daga yayyen nasa har kannen nasa sunada matsayi mai girma a gunsa.
Ya zamanto tun daga kan Hatoon Mama Fatu bata sake ko batan wata ba, gashi Hatoon nada shekaru 18 a halin yanzu.
Tun fil azal a bayyane yake ga kowa cewa Baba Bello na matukar son Mama Fatu. ‘Yar lelen shi ce ta ko’ina, yana ji da Mama Fatu ya tsoka daya a miya, bai taba tunanin yi mata kishiya ba kuma bai hada matsayinta dana kowacce mace a gurinshi ba.
Mata irin Mama ake kira shalelen maigida, bata laifi a gun Baba Bello, saidai kuskure, wanda yake mata uzurin shi komai girmansa a koda yaushe.
Baba baya yiwa Mama iyaka da duk abinda ya mallaka. Komai ya samo nata ne da ‘ya’yanta, danginsa duka a cewarsu sun gama sallamawa Haj. Fatu Prof. Bello ta mallakeshi daga kai har kafa. Kowa dai ya san yadda matan Rumawan Katsina suke dauke hankalin mazajensu da yadda suka iya biyar da mazajensu ta hanyar mulkar gidajen aurensu tsaf.
To Mama Fatu ta kasance daya daga cikinsu, irin matannan ne ‘yan hutu wanke goma tsoma biyar a gidanta, dari bisa dari mijinta Baba Bello ya tsaya mata saboda son da yake yi mata yasa ya sakar mata komai nasa.
Kowa ya shaida cewa sun fahimci juna itada Baba fiyeda duk yadda ake zato, ba wanda ya isa ya kushe halin Mama a gun Baba Bello yanzu za iyi hannun riga dashi, Mama tana da kirki iya kirki, amma fa a zahiri, Mama Fatu macece mai son kanta kwarai da son ‘ya’ya har ya wuce kima, in kana son zaman lafiya da ita kada ka taba mata ‘ya’yanta ko kace ga laifinsu, ‘ya’yanta sun fi na kowa matsayi a gunta. Bata da kara sai keke-da-keke in dai akan ‘ya’yanta ne.
Rayuwa ake ta hakika wadda babu karya a zaman Baba Bello da Mama Fatu. In yana dashi ta sani, haka in babu ta sani. Sun taso tun kuruciyarsu a haka cikin son juna, ya hadu da Mama ne a garin Rumah da yaje wani aikin koyarwa na sa-kai (voluntary teaching) bayan kammala sakandirensa kafin fitowar admission dinsa zuwa jami’a. Baba yana matukar tattalin Mama da tattalin farin cikinta, zamu iya cewa a takaice Baba Bello shine komai dinta a duniya.
Saboda Bello ya Aureta tun bata kare makarantar gaba da firamare ba, amma da taimakonshi da tsayuwarshi akanta sai da ta kai har matakin NCE, tana karatun NCE tana haihuwar yaranta a jejjere.
Baba Zayyan baiyi wasa da tarbiyyar yaranshi ba ko kadan, duk da anso a samu matsala ta fannin Mama Fatu, ta kasance me matukar rauni akan tarbiyyarsu saboda soyayyarsu, don ko Baba ne yake musu fada wani lokacin zaka ga ranta yana baci, hancinta yana bubbudewa tana wani irin canza fuska da cin magani. Baba ya karanci halin matarshi tsab, don haka sauda dama baya musu fada a gabanta saidai ya kebe dasu, duk da baya son bata mata rai yana yawan tsawatar mata akan sangartar da take yiwa yaran, musamman auta Hatoon da ta haifeta a shekarun girma, tana da rauni akan tarbiyyarta, shiyasa yarinyar ta tashi a sangarce, don zaki ga wani abun ma tsoron idon Baba ne yasa takeyi ba tsoron Mama ba.
Ko akan zuwa islamiyyah Baba ya sha tasa su Zahra a gaba ya kora su da dorina, ko yaje makarantar yasa a zanesu tsaf, amma fa a bayan idon Mama, don in sunce wa Mama sun gaji bazasu je Islamiyya ba, nan da nan zakaji Mama na fadin “to a barwa gobe”, in kuwa makara sukayi nan zaka ji tace bazasu je ba, ba gardin da zai bugar mata diyoyinta, su zauna a gida suyi bita su huta sai gobe. Zafin neman ilmi ba shi ke sawa ayi kudi ko ilmin ba. Ita ai NCE kawai tayi, me ta rasa a rayuwarta?
Mai cin abin hannun Mama kuwa sai ‘ya’yanta. Mama akwai rowa.
Baba duk inda zai taka a fadin kasar nan da Mama Fatu yake zuwa, don haka ko a cikin tsararrakinta zaki ga ita tana da wayewar kai sosai, sakamakon zama da rikakken dan boko irin Arch. Bello Rafindadi, sun yi yawon bude ido ita dashi sosai a gari-gari a cikin kasar Nijeriya, duk wani wajen hutawa da buda ido a arewaci da kudancin kasar nan Baba da Mama sun taka shi. Haka siddan zasu dauki hanya su tafi suyi sati a Yankari itada Baba in suna son hutawa daga haniyar gari data kacaniyar yaransu.
Rufin asiri daidai misali a lokacin Baba Bello nada shi, kuma mutum ne da bai san dadin abun hannunsa ba, me son ‘yan uwanshi da na Mama Fatu, a wurin shi da danginshi da nata duk daya ne.
Gidanshi ya kasance ‘open house’ ga kowa nata da nashi.
Kai tsaye bazaka ce Mama bata da kirki ba sai ka zauna da ita, halinta ya bambanta dana mijinta Baba Bello sosai.
Shi Arch. Bello kowa ya shaideshi da hakuri, kuma mutum ne mai sanyin hali da yawan kyauta, ma’abocin tawali’u, mai faram-faram da rashin nuna bambanci cikin mu’amalar shi da kowa da ya rabeshi. Amma wani nakasun Mama Fatu shine, mace ce mai nuna bambanci tsakanin mai shi da mara shi cikin mu’amalarta, mai nuna iko da mulki ga wadanda ke karkashinta da dangin mijinta. Gata da izza, fadin rai da saurin daukar zafi (saurin fushi akan ‘ya’ya) bata kara ko kadan a kansu, tamkar ba bafullatana ba.
Har dai in aka zo batun lamarin Baffanta, nan zaka ga rashin fulako gun Mama. Mama bata kawaici a kansa sam, duk yadda kake da Mama kada ka sake kace ga laifin Baffa, gara ita ka bata mata daka batawa Baffa, in har kana son zama lafiya da ita. Kusan haka take behaving akan auta Hatoon ma. Kada ka sake ka taba auta in kana son Mama ta cigaba da bude maka hakoranta.
Wannan yasa Hatoon ta tashi a yarinya mai shegen ji da kai da tsokanar ‘yan uwanta, ga yawan shagwaba da yawan raini ga Yayyenta, da rashin jin maganar kowa har Maman kuwa, Baba kadai take shakka a gidan sa Yaya Baffa, sabida Mama ta daure mata gindi, kowa yazo da korafi akan auta yanzu zata tare mata fadan ta ara ta yafa.
Mai dan dama-dama a hankali da cikar tarbiyyah cikin ‘ya’yan Mama Fatu mata to Yayarshi Zubaina ce, Zubaina ta kan dade bata zo gida Rafindadi ba, don mijin ta irin mazan nan ne masu mugun kulle ga matansu, suka kuma isa dasu.
In ka cire Zubaina kafatanin duka ‘yammatan Mama halayenta suka debo. Yaya Zubaida kuwa ai makwafin Mama kenan a halayya da dabi’a. Zubaina ce kadai mai hangen nesa cikinsu saboda mijin data aura malamin makaranta ne duk ya canza halin Zubaina zuwa irin wanda yakeso bayan ya aureta.
Mama ana yawan zugata da cewa ‘ya’yanta mata ai jarin ta ne, tunda Allah ya bata su kyawawa tamkar ita ta kera abinta don kyawun sura, wannan yasa Mama ta dora buri sosai a kansu, da zuwan aurensu Zahrah, burinta kadai suyi auren hutu a inda zasu huta itama ta karu, ba irin auren da Baba Bello yayima Zubaidah da Zubaina ba, suma kuma su Zahran saboda yawan hudubobin Mama na kada su sake su kawo mata dan (I love you) ko mai fama da alli yasa suka tashi da burin sai wanda ya kama kasa ya tsaya da kafafunsa zasu aura, wannan yasa har gobe ‘yammatan Mama babu suna nan zube a gabanta, babu mai tsayayyen saurayi, kowa yazo Mama zata ce bai isa ba, me yaci balle ya basu? Gashi dai har Zaitoon da Zahra sun fara jarrabawar shiga aji na uku a jami’a yanzu babu tsayayye.
Mama da ganin ta ka san an zuba kyau a zamanin ‘yammatanci an kuma yi ruwan idon samari kafina tsaya akan Bello Rafindadi, kuma har yanzu in ka dubi Mama zaka ganta da kyanta da gayunta, ga koshin lafiya da kuzari, gata da ingarman jiki, saboda samun kyakkyawar cima da take yi da kulawa daga Baba Bello, wanda zai iya kwana da yunwa ita ya bata, kyawun surarta bai buya ba har yanzu, duk da a halin yanzu Mama ta baiwa 60 baya.
Mama tayi aikin koyarwa na lokaci mai tsaho a babbar makarantar ‘yammata ta gwamnatin jihar Katsina, bayan ta haifi auta Hatoon sai ta bar aikin, ta karkata kan kasuwancin atamfofi da lesika da mayafai na matan zamani, kuma kasuwancin sai ya karbi Mama sosai fiyeda koyarwar. Don a karshe daga shagon cikin gida har ta kai ga bude shago a kasuwa, na atamfofi da lesika, inda take harkokin kasuwanci bisa kulawar ma’aikatanta.
Shi dai ya san babban nakasun Mamansu Hajiya Fatu, wanda Babansu ya sha gaya masa baya so, a matsayinsa na da daya namiji garesu sai ya zama babban aboki ga Baba wanda yake tattaunawa dashi akan komai da ya dameshi, Baba ya sha gaya masa abinda baya so a tareda Mama shine halinta na raini da take nunawa ga na kasa da ita, in har ta fika arziki to kuwa dole zata rainaka, ko daga kalaminta. Bazata taba hada kafada da kai ba, wada ‘ya’yanta mata kusan duk sun dau wannan halin, basu da mai tsawatar musu su ji sai Baba Bello da kansa. Ko shi Zayyan din in yayi yunkurin ladabtar da kannensa nan da nan Mama zata taka masa burki.
Zayyan ya sake juyawa wani irin juyi mara dadi akan makeken ni’imtaccen gadonsa, sai ya ja numfashi ya sauke a hankali cikin tunanin sha’anin gidansu, ya kuma kara da lumshe idanunsa yana mai fuskantar ceiling. Baya son tuno duk abinda ya shafi Baba Bello yanzu, domin yana yi masa fami akan warkakkeen gyambon rashinsa dake ransa ne, amma ya zama dole yake tuna Baba da rayuwarshi tare dasu bakidaya, su kuma dinga dawowa cikin tunaninsa lokaci zuwa lokaci saboda Baba Uba ne da babu irinsa a wannan zamanin. Daga nan Zayyan ya kara nausawa cikin tunanin da ya samu kansa, duk a kokarinsa na son nemo adalci ga kansa, da maidakinsa Nana Safiyyah a daren yau ta hanyar yiwa kansa (self-judgement and self-evaluation), bayan tuni aikin gama ya rigada ya gama, ko yace bakin alkalami ya gama bushewa.
**** **** ****
ARanar, abinda ya faru bayan ya dawo daga Dandume shine, ya dawo gida da farin cikin amincewar iznin neman auren Safiyya da mahaifinta Mallam Usman ya bashi, kai tsaye bai tsaya ko’ina ba sai falon Mamanshi Haj. Fatu.
Yana saka kafa a falon Mama, bakinsa dauke da sallama cikin doki da kaikayin baki, da kafafun Hatoon ya fara cin uban karo a bakin kofa, suka tadiye shi har suka kusa fadar dashi a kasa.
Haushi ya kama shi. Ya juya ya kalleta da manyan idanunsa, tayi shame-shame a bakin kofa wai ita tana azumin ramuwa, lokacin ana gab da shan ruwa, autar Mama ta kai makura wajen galabaita, don kuwa azumin ma saida taji wa’azi a radio na hukuncin marasa ramashi sannan ta fara ramawa lokacin azumin bana saura kadan ya kama.
Hatoon ta kusa kayar dashi a kasa sosai, a fusace yasa kafa ya shureta da karfi, nan da nan Hatoon ta saka karar kiran Mama, tace da karfi “Mama kizo. Yaya Baffa na dukana!”
Sai ga Mama ta fito daga daki da sauri jin sautin kukan Hatoon, kamar wadda aketa duka, shurinta kawai yayi da kafarsa, amma ta bare baki tana kukanta na sangarta mai ban haushi, Mama tana ganin sa a gaban Hatoon ta ce.
“Ha’an! Tunda naji kukan Hatoon alhalin tana azuminnan da sanyin yammacinnan na san anci zalinta da mangaribar fari, kuma ba kowa bane sai kai Baffana, to juya ka bar min falo, tunda bani na kiraka ba”.
Zayyan bai damu da fadan da Mama ta rufeshi dashi ba, don inda sabo sun saba, haka bai ji gargadinta na ya koma inda ya fito bata gayyatoshi ba, sai ya shigo falon ya zauna ya harde kafafunsa yana hararar Hatoon, yace “zaki tashi daga wannan banzar kwanciyar a bakin kofa, ko sai na babballaki in yaso kiyimin ihu da hujja? Yanzun don Allah da kin kayar dani fa?”
Mama tace “a’ah fa. Baffa ka san Allah, tunda dai bamu kira ka ba, kuma ba maganar arziki ce ta kawo ka ba, to ka koma inda ka fito ka saurarama Hatoon, bana son diban albarka akan yarana ka sani daga kowa har su da kansu kuwa, me ta tare maka haka kake neman cinyeta?
Ina dalilin wannan tsangwama? Azumi fa take yi, in baka tausaya mata ba, ai baka hantareta ka hau shurinta daga shigowarka ba”.
Ba don Mama bace take maganar nan, tabbas da ya kaiwa bakin Hatoon kyakkyawar mahangurbar da zata kumbura mata bakin, don yana kallonta tana gatsina baki irin dai wanda ta saba yiwa yayyenta in taji Mama na tare mata fada a wurinsu.
Kwafa yayi, yayi shiru ya rabu da ita, don in ya sake ya tabata zai fuskanci fushin Mama, haka kawai tasa an gwasale masa farin cikin da ya zo a cikinsa.
Don haka yace. “Mama kiyi hakuri, ni ba maganar wannan sakaryar ‘yar taki ce ta kawo ni ba, in fact, ko me zaki yimin yau a kan ta bazan ji haushi ba, bazan kuma wani damu ba, tunda ai na riga da nasan kinfi sonta a kaina, to na me zan damu don kin koreni a gabanta?
Ni ranar yau daban take a wajena; ina cikin matsanancin farin cikin da sakarcin Hatoon yayi kadan yasa inyi fushi yau.
Mama ta samu wuri ta zauna cikin rashin kulawa da zancen tace “to yaya akayi?” Yayi murmushi cikin ‘yar alkunya da sosa keya kafin yace.
“Mama ni yau nayi gamon alkhairi fah, irin albarka, tsatson martaba, yau dai Allah ya nufa na isa ga gidansu “HIJABIE!!!
Na kuma gabatar da kaina ga mahaifinta”.
Mama na wani irin yamutsa fuska da baki cikin gatse tace “wacece haka? Wane irin suna ne Hijabie ni ‘ya su? Sunan yanka ne ko sunan rana ko hijab da ake sakawa aje masallaci yin sallah?”
Ya sunkui da kai jin abubuwan da Mama ta zano, kafin yace “Mama Yarinyar nan mai hijabs da jilbaabs da nake yawan baki labari ina haduwa da ita a school Library?
Kuma alhamdulillah mahaifinta ya bani damar fara saka kai ga neman auren ta”.
Budar bakin Mama Fatu sai cewa tayi “lallai Baffa ka girma! Ni yau naga abinda ya girmeni, kai nan har wani aure ka isa Baffana? Nawa kake? Cewa nake ko 27 Baffa baka kai ga rufawa ba? Tukunnama, diyar waye a Katsina ita Hijabie din? Ina nufin WAYE UBANTA?”
Tunda a halin yanzu me ka aje, me kuma kake dashi da zaka baiwa iyali, aikin me kake yi da zai rike maka aure?”
Mama Fatu ta tambaya da accent dinta na Katsinawan Rumah. Cikin balbaleshi da fada da tada jijiyar wuya.
Zayyan saida ya bari Mama ta kai aya, tunda yasan halin kayarsu, sai ya kwantar da murya don ya riga ya san halin Mama na saurin daukar zafi da izgili, cikin lallashi yace,
“ba sunanta Hijabie ba Mama, nine na saka mata hakan sabida kyawun da Hijab da jilbab ke mata.
Sunanta Safiyyah, diyar Malam Usman Dandume, mahaifinta babban Alaramma ne (Shaihun malamin addini) mai bada karatun addini ga magidanta da almajirai a garin Dandume”.
Abinda shi bai fahimta ba tun a lokacin shine; wannan matsayin na mahaifin Safiyyah da shi yake ganin abin alfahari ne da bugun kirji wajen zaben abokiyar rayuwa da yayi, a wurin Mama Fatu shine first disappointment (sagewar guiwa na farko) data fara samu akan Safiyyahrsa, na kasancewarta ‘yar malamai, wanda ko kusa baya cikin tsarinta kuma bai zo cikin tunaninta ba, na irin surukan data ke burin hada zuri’a dasu, sannan gata ba ‘yar manyan ‘yan boko da sukayi shuhura a bokon ko wasu masu dukiya ba, domin nan take Mama cewa tayi tun kafin ya gama rufe bakinsa.
“Hadin gambiza Baffa?! Wannan shi ake kira hadin gambiza.
Me ya hada dan Furofesa da diyar alaramma na kan buzu kuma?
Kai Baffana bana son rigima mai lasisi. Haka kawai inje a tattofe min kai da laqanquna a rubuceka a minjaye a shanye, a mallake min kai ko a rabani da kai, kai kadai dinnan namiji danake dashi a cikinsu?
To bada ni ba gada makabarta. In ka ganni a lahira kaini aka yi. Kai kenan kwalli dayan da Allah ya bani a matsayin da namiji, maimakon ka kawomin matar da zan yi alfahari da tinkaho da ita da iyayenta kai kuma ka samu ta sakawa a gaban mota, a kara maka karfi, wadda zan dinga zuwa da ita a gidan biki ina nunawa kawayena a matsayin surukata, yarinya ‘yar hutu da za’a cika mana gida da duma-duman ‘royal furniture’ a dinga bamu kujerar Makkah duk shekara nida kai, da yayyenka, ba tare da la’akari da namu samun ba, a kuma baka gwaggwaban jarin da zaka kafa kanka kafin ka samu aikin yi, sai ka bige da kawon diyar gidan alaramma?”.
(A saninsa wannan shine mafarin rashin kaunar Mama da Safiyyahrsa. Domin tun ba’a kai ga auro Safiyyah ba, ba’a kai ga an zauna da ita anga kalar halinta ba, kasancewarta diyar Alaramma da yace kadai gidan da ba mamora (ta bakin Mama), yasa Mama tun tashin farko ta tsani zancen aurenta, ta kuma ki jinin asalinta, ta gwasile shi nan take, ta sassage masa gwuiwa a kanta.
Haka Mama ta cigaba da sakin maganganu na ba’a da raini da shagube ga zabinsa, irin wadanda zasu sa shi kansa yaji Safiyyah ba ajin aurensa bace, amma ina! Baffan Mama ya riga ya kamu iya wuya, maimakon hakan sai ji yake Safiyyah tana kara kawatuwa da kwanciya masa a rai, tana kara burgeshi tareda kara nabba’a a birnin ransa.
Hatoon dake gefe shame-shame a kwance, amma tsaf ta kafa kunnenta a kansu tana sauraronsu shi da Mama, tun tana gintse dariya da ganin yadda Yaya Baffa ya muzanta a gaban Mama, har a karshe tace me zatayi ba fashewa da shaqiyyar dariya ba! Ganin Yaya Baffa yanata karkarwa don Mama tace diyar Alaramma ba cikin zuri’arta ba.



