⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 7: Chapter 7

A DISTANT BROTHER
Safiyyah ta wayi gari yau da farin ciki, da tsayuwar zuciyarta wuri guda akan aurenta da Zayyan Bello, bayan kammala istikharar da Malam ya bata, ta jinan duniya ba wanda take so sai Zayyan. Da hantsi ya dubi ludayi, Yaya Sheikh ya fado mata a rai, kawai sai ta kira wayarsa. A kokarinta na son shaqa masa takaici irin wandayake shaqa mata duk sanda yace bata iya gayu ba babu saurayin da zai kwasheta. Kwana biyu tayi kewar Yaya Sheikh don ya dade bai kirata a waya ba, ana I gobe daurin aurenta da Zayyan tana ciki wani irin madaukakin farin ciki, tayi mamaki da ko Allah ya sanya alkhairi Yaya Sheikh bai bugo ya ce mata ba, sai ta yi kundumbala ita ta kira shi.
Ridhwan Abubakar Dandume (Sheikh) yad aga wayara Safiyyah, ko gaisawa bata bari sun yi ba cikin tsokana take gaya masa;

“Yaya Sheikh ko kasan? I have finally found my Soulmate, a cikin HIJABI! (A karshe dai gashi ta samu abokin rayuwa cikin sutturarta ta hijabi), da yake Yaya Sheikh kullum baya rabo da yi mata gorin bata da mashinshini ne saboda bata gayu irin na ‘yammatan yanzu, sai fama da Hijabi, shi ko a kafa aka daura masa ita zai kwance ya yar, ya zura da gudu saboda rashin iya gayunta.
Ya kan yawan ce mata, shi in ya tashi aures ai mace sai mai kyalli da daukar ido da iya daukar jambaki, gazal da jagira da iya saka suttura kadai zai aura. Wadda I ta shigo wuri sai an san ta bayyana.
Wadda in ya ganta zai ji sanyi daga duk wani bacin rai saboda haduwarta da iya gayunta.
Kullum abinda yake fada mata kenan in yaso tsokana da son kular da ita. Kai kace ‘yar mace da dan namiji suke ba ‘yan maza zar ba.
Don haka da dariya sosai yau itama take ramawa inda, take gaya masa Zayyan dinta ya fishi komai, ya fishi kyau Ba-Rumeh ne, kuma Uwa Uba yana matukar sonta a hakan da take cikin Hijabin, gashi ya fishi iya gayu da iya daukar wankan da yake mata gori…..ya-yan-yan”.
Safiyyah sai ji tayi shuuuu! Kamar an katse wayar, kuma daga ranar bata kara samun Yayan nata Ridhwan a waya ba, sannan bai kara kiranta ba ko da wasa. Wannan abu ya bata mamaki, don ita wasa take masa, at least yaji inda dadi irin gori da cin fuskar da yake mata kullum.

Koyaushe ta kira wayarshi bata shiga, but to her utmost surprise (ga babban mamakinta) sai taji yana hira dasu Ammi lokaci-lokaci akan shirin auren nata.
Har Ammi ta gaya mata cewa ya aiko da gudunmuwar kudi mau kauri yace a hada ayi mata kayan daki. Abin ya sosa mata rai, me Yaya Shaikh ke nufi da yanke alaqarsu kuma bazai mata ko fatan alkhairi tsakaninta da shi ba?
Kenan ita blocking dinta yayi daga wasa ko me?
Itama daga ranar sai kawai tayi zuciya ta rabu dashi, bata kara gwada kiran Yaya Sheikh a waya ba.
**** **** ****

AURENSU
Ahankali Zayyan ya kara lumshe idanunsa, ya cigaba da tariyo abubuwan da suka faru dasu bayan nan shi da Safiyyah. To cut it short, yayi nasarar samun auren Safiyyah (at a very tender age) daga shi har ita suna tsakiyar shekarun kuruciya, in her teens shikuma in his twenties.

Irin auren nan na mutanen da ga ‘ya’yansu, da ake kira AUREN GATA shi mahaifinsa Baba Bello yayi masa da Safiyyah kamar yadda ya alkawartawa Mama, cewa zai masa auren gata, to ya cika wannan alqawarin, domin Baba shi yayi masa komai na hidimar auren nan including lefe, wanda Malam yaki yarda a kawo yace can in sun hadu a gidan auren su ya bata amma ba a gidansa ba.
A kullum sanda Baba yake raye, yana kara jaddada masa da ya rike Safiyyah da amana, ‘yar masu dattaku ce itace asalin ‘yar manyan mutane, kuma matar rufin asirinshi ce. Baba Bello ya kan ce “na saka himma na aura maka itane bisa ganin dacewarta da kai da nagartar gidan data fito, da kuma uwa-uba karfin sonta dana gani a tattare da kai, ba tareda na jira lokacin da ya dace ace kayi aure yayi ba”.
Baba ya kara ce dashi “ya aura masa ita da wuri ne don kada ta kubuce masa.

Domin mata irin Safiyyah da suka fito daga tsatson kwarai tamkar allura cikin ruwa ne wato na mai tsananin rabo ne”.
Bazai taba mantawa da ire-iren wadannan kalaman na mahaifinsa akan Safiyyah ba, masu sawa kullum yake kara ganin darajarta da kimarta a bayan ran Baba. Yake kuma girmama kowanne kankanin al’amarinta.
Da amincewar mahaifin Safiyyah da nasa dari bisa dari aka daura aurensa da Safiyyah… aure mai dimbin tarihi. A wannan lokacin da tunaninsa ya zo nan, murmushi ne ya kubce masa daga kwancen da yake, sakamakon tuno wani abun da ya faru bayan daurin aure.
Wato tun daga lokacin da aka daura musu aure sai Safiyyah ta canza masa, ya rasa gane kanta, duk ta damu, ta shiga kunci marar dalili.

Har ta kai da cewa ta rokeshi kan bata shirya tarewa ba, tana so ya roki Malam da Baba a bata lokaci, saboda gabadaya auren da yuwuwarsa yazo mata ne bagatatan, bata yarda da yiwuwar komai ba sai data tabbatar ya tabbata din. Wato an daura shi, tunda gashi har Malam da Limamin garin Dandume da ya zama Alwalinta sun kirata sitting room din Malam na soro a ranar bayan an watse, sun damka mata sadaqinta na aure a hannunta.
A baya Safiyyah kallon komai take kamar wasan film, wato daga haduwar ta da Zayyan har zuwa gajeruwar soyayyarsu sun faru kamar kiftawar ido, zuwa daidaitawar iyayensu, zuwa maganar auren data bullo duk bata yarda dasu ba sai bayan ta tabbatar an daura mata auren shaidu sun shaida, tun daga nan ta shiga damuwa, ta fitini kanta ta fitineshi shima da rokon alfarma na rashin son tarewa yanzu.
Da farko tace masa ya roki a barta sai ta gama jarrabawar karshen zangon da zata fara, ta huta ta nutsu bayannan, duk ta dauka Zayyan zai ce a’ah, ganin yadda yake ta dokin tarewar tata, tunda Malam yace biki ba’a gidansa ba saidai in ta tare suyi can a gidansu, amma sai taji kawai ya amsa inda ya ce mata cikin lallashi da tausasa kalami.

“sophie, kinsan burina kawai in mallake ki mu rayu tare ko, daga wannan banida wani sauran buri a duniya sai na fatan gamawa da iyayena lafiya.
Kuma gashi Allah ya cika min wannan burin, alas! Ya mallaka min ke Safiyyah, bada tsumi ko dabara ta ba.
To gaggawar me zan yi kuma a kan tarewarki, ai anyi mai wuyar, don haka ki kwantar da hankalinki ni ta fannina “no haste”, na baki damar tarewa a gidana a duk lokacin da kika shiryama hakan.
Zayyan will be patiently waiting for you to come (Zayyan zai jira isowarki cike da hakuri)”.

Daga ranar da aka daura auren su ne ya soma kiran ta da suna “Sophie”, ya cire mata suna “Hijabie”, don a cewarsa yanzu babu sauran Hijabi a tsakaninsu!.
Wasa-wasa har ta gama jarrabawarta Safiyyah tana dojewa tarewarta, Malam da Ammi ma basu matsa mata ba, don wani zazzabi zazzabi ta soma a tsaitsaye, irin na sabon aure.
Kannenta da Ammi kadai ke zuwa saye sayensu a kasuwa na ‘yan kayan dakinta da kayan kitchen, da suka tsara za’a yi mata daidai karfinsu.
**** **** ****

Yau Zayyan ya zo ya samu Mama a falonta, ya zauna gefenta yana sosa kai, ta harareshi ta ce “Baffana, tunda aka daura maka aure ka daina zama muyi hira ko? Ka daina samun lokacin hira dani da kannenka, bini-bini kullum kana hanyar Dandume, Dandume dai, ina ka fito Dandume, Ina zaka, Dandume.
Ni ko dana ga Safiyyar nan a hoto, yadda ta gigitaka ta tafi da imaninka haka na dauka zata fi haka cika ido da daukar ido don kwalisa, sai naga abu ‘yar firit, fuska salalam ido ba ko tozali, sai dogon hanci da manyan idanu kwala-kwala kamar na mage, in ce ko sune kadai suka burgeka?

Gaka Baffana masha Allah katoto da kai (giant), amma sai ka dauko mace ‘yar firit, siririya kamar karan raken takanda. Ai da ka nemo mai dan kumari kamarka da yafi”.
Shi abinma sai ya bashi tsoro, don dai shi, Lillahi wa Rasulihi bai ga makusa tattare da halittar Safiyyah ba in ka cire rashin kwalliyarta kuma wannan ra’ayi ne, shima yanason kwalliya amma yasa a ransa a matsayinsa na namiji, shi zaiyi shaping mace a gidansa yadda yakeso ta mike amma hakan sai a hankali in akayi la’akari da irin background dinda ta fito, ya kan rasa gane ina Mama ta dosa kullum akan maganar Safiyyah, bata taba yabawa ba!
Kullum sai ta samu abun kushewa a aurenta take barinsa ya bar dakinta, bata taba godewa halarcin Safiyyah gareshi ba na yarda da tayi ta aureshi yana dalibi, itama daliba, ba ko tunanin aikin me zaiyi ya ciyar da ita, shi ko da wannan aka barshi Safiyyah ta gama masa komai, tunda ta aureshi bisa yarda da soyayya tun bai zama abinda ya zama yau ba. Safiyyah matar sirri ce, abokiyar rufin asirinsa.

Yadda take tashen kyawunnan da kuruciyar nan da kokari a karatu a ABU, da irin maneman da ya kasa a kanta, manyan mutane masu zuwa wurin mahaifinta, shi ya san mutum ko shine hasidin iza hasad, ba zai ce Safiyyah bata da kyau ba sai Mama Gwanin na Iya, wai ‘yar firit ba kumari, to dambe zasu ke yi da zai dauko dirkekiya? Don haka ya kan rasa gane ta ina Mama zata yabi wani abu akan auro Safiyyah da yayi, wanda shi yasan daga shi har mahaifinsa basu saka son zuciya cikin al’marin ba sai kwadayinsu da asalinta (nasaba) da training dinda ta samu. Yace “amma Mama kinsan ba kullum nake zuwa Dandumennan ba, ko bayan daurin aure sau biyu kawai naje, mahaifinta mai ka’idane, baya son zaryar maza a gidansa, ni kuma ina kiyayewa.
Ban daina zama hira daku ba Mama. Na maida hankalina wajen hattama (project work) dina don na samu na yi submitting a sallameni, shiyasa bana iya zaman hirar yanzu, kullum ina library fa Mama, itama Sophie ba son tarewar take yi ba”. Ya karasa maganar cikin damuwa da jin tausayin kansa.

Mama ta yarda, don ta san Zayyan a dabi’arsa baya karya, baya munafurci ko nunkufurci, in yanason abu yana so kawai, sannan rawar kafarshi akan Safiyyah ita ta san gaskiya da sauki akan ta mazan da suka yi sabon aure, ko don bai san me auren ya kunsa bane at all sabon shiga ne? Tunda har ya bar matarsa sama da sati biyu da daurin aure a gidan iyayenta ba zancen tarewa wai tana jarrabawa, itama jan magana ne kawai don taji dadin bakinta, amma ta san ba Dandume yake zuwa ba.
Yana Zaria can cikin makaranta kodayaushe, ya hada hankalinsa wuri guda ya kammala rubutunsa a wannan dan tsukin, don Baba Bello ma ya gaya mata kwatankwacin abinda Zayyan din ya gama fada mata yanzu, cewa Baban Safiyyah dan ka’ida ne, baya barin Zayyan zuwa zance barkatai. Ya kuma hana suyi mata lefe ko bikin bidi’o’in ‘yan boko. Koda aka daura auren ma yace shi in ba Safiyyah tarewa zata yi yanzun ba, to Zayyan kada ya dinga yi masa zarya ya cigaba da zuwa sati-sati bisa ka’idarsu yadda suka saba.
Mama tace a ranta tabdijam! Baffa an debo aure gidan Alarammomi fiyeda haka ma za’a gani ne.
Malam ya baiwa Ammi kudi masu yawa kasancewar yana noma yana fidda amfanin gona duk shekara, sannan yana kiwo, ga gudunmuwar da Sheikh ya aiko musamman don auren kanwarsa Safifi. To kacokam abinda Malam ya fidda wannan shekarar a kan kayan dakin Safiyya ya karar dashi.

Ya hana Ammi sayar da filinta, yace ta ajiyewa kannenta suma ba jimawa zasu yi ba a gaban su, tunda duk suna sakandire yanzu.
Ammi ta cigaba da shirye shiryen tarewar Safiyyah a hankali, ta sayi wannan ta sayi wancan ta adana, yayinda Safiyyah nata dokin ga tarewar kullum raguwa yake yi. Bata san meyasa ba, kawai taji bata son tarewar (not because she doesn’t love him).
In da namiji daya data fara ji a ranta duk duniya to Zayyan Rafindadi ne, amma sam taji bata so ta tare a gidansa bayan an daura musu aure.
Wasa-wasa saida aka share watanni biyu da daurin aure amma Safiyya taki ko zancen tarewar nan ayi mata.

Duk wani uzuri na duniya Zayyan yayi mata a matsayinsa na sabon ango mai hakuri da iya controlling eager dinsa. Already Baba Bello ya kama musu dan gidan da zasu zauna a Zaria, kusa da makaranta, har su kammala, amma Safiyyah ta ki.
Malam da Ammi tun basu damu ba, don suna ganin makon gida ne ke damunta da sabo da ‘yan uwanta, har abin ya fara damunsu suka sakawa Safiyyah ayar tambaya.
Malam yace addu’a ya kamata suyi mata, watakila shaidan ya shiga lamarinta
Ita kuma Safiyyah a karan-kanta ta san ba wani shadani akanta, ba komai ya hanata son tarewar ba face maganganun Anti Dije da suka tsoratata.
Tun bayan da aka daura aure in suka zauna itada Antin a gidanta, ba abinda Anti Dije ke mata sai fadakarwa irin ta Aunties mata kawayen ‘ya’yansu, kuma shaqiyyan iyaye. Fadakarwar Antin akan daren farko ne, tace dare ne na musamman ga kowacce amarya, bla bla bla……ga ire-iren abubuwan da suke faruwa cikinsa.

Anti Dije tace “akwai abubuwa masu ban tsoro da Sanya razani ga diya mace a cikinsa”.
Tun bayan da aka daura aure Antin marikiyarta ta Zaria bata da aiki sai yi mata irin wannan hudubar akan shiga gidan aure, da koya mata abubuwan da ya kamata ta sani, a matsayinta na farin shiga, kuma sabuwar matar aure a halin yanzu, wadda ba jimawa zata bi sahun sauran iyaye mata, har Anti Dije tayi kuskuren fada mata yadda ake shan wahala a wannan daren ga budurwar da ta kai mutunci, wasu har sai an musu dinki ko ruwan zafi, sannan tace in ta warke kuma sai harka ta balle a koma soyayya, nan ta shiga koya mata salo-salo na shimfida da sauransu baro-baro.

A matsayin ta na karamar uwarta mai shirin kaita dakin miji, Anti Dije da karambani irin nata taga ya kamata ta koyar da diyar tata duk wannan. Kada ta barta a dukunkune taje ta rasa yadda zata yi. Don ta tabbata Safiyya banda text books dinta na Architecture bata karanta littafan soyayya koda na turanci ne. Kuma ta san Ammi bazata taba yin irin wannan hirar da itaba.
Amma ga Safiyyah diyar Ammi da Anti Dije, maimakon hakan yayi amfanin da ake zato, wato ya zama karin ilmi a gareta da wayar da kai, sai ya zama akasin haka, duk Aunty Dije ta hargitsa mata tunani akan aure. Ta koma anticipating ranar first night dinta shine kwatankwacin ranar mutuwarta.

Domin daga hudubobin Anti Dije Safiyya ta fahimci ai wata sabuwar rayuwar ce ke jiranta daban da wadda suke yi da Zayyan kafin aure, Anti Dije ta yi instilling tsoro mai yawa a Safiyyah, don sai ta kai ta kawo ko cewa akayi Zayyan ya zo sai gabanta ya yanke ya fadi, sai kuma taji bacin rai wanda har a fuskarta sai ya nuna.
Tayi ta tambayar kanta ta yaya ma za’ayi ace abubuwan da Aunty Dije ke fadi zasu faru tsakaninta da abokinta Zayyan, ai akwai kunya, kasancewar hirar soyayya da kauna data karatu ce blah… blah… kawai tafi gudana a tsakaninsu (very pure gist) koyaushe Zayyan bai taba wuce limit dinsa ba.

A takaice Aunty Dije ta gama nuna mata cikin rashin hikimar zance akwai muhimmin abinda ke jiranta duk ranar data tare daga salihin mijinta dan mutanen Rafindadi, wanda take yiwa kallon aboki, masoyi, amini. Bayan daurin auren har wasu magunguna ta soma bata masu dadin ci na “Bojuwa Herbals” wato kayan gyaran auren nan na musamman na kawarta (Aunty Surayyah Halin Yau 08032773332) tace rayuwa ce zasu fara wadda sai an kai zuciya nesa, saboda nauyinta. Tace mata wannan shine zahirin auren hakikaninsa, asalin abinda ya saka mata tsoron tarewar gabadaya.

Duk da Zayyan bai taba nuna mata wani abu daban mai nuna hakan ba, tun kafin ayi auren da bayan an daura shi, bayan an daura ma rage zuwa yayi, amma Anti Dije tasa mata tsorata dashi sosai kamar mala’ikan da ke jiran ta shiga gidansa ya dau ranta, da take gaya mata abubuwa kuru-kuru, abinda Ammi bata taba zama ta gaya mata ba, saboda kunya da fulatanci irin na iyayen da, kuma ita bata kawaye bata kuma karance-karancennan na zamani da ire-irensu. Antin nata Dije tayi mata (sensitization) ne na kai tsaye (ba cikin hikima ba).
Kamar ace Anti Dije irin matan nan ne masu barin zance da rashin sakaya shi cikin hikimar harshe, har cewa take da Safiyyah idan ta nuna bata son hirar.

“To nifa ban gane ba Safifin Ammi, wai kina nufin shi Zayyan din bai taba nuna miki yana bukatar komai daga gareki bane tun daurin aurennan ko yaya ne?
To idan yazo Dandumen haka kuke wuni baya komai a gabanki sai zuba zance kamar lalataccen famfon I love you na fatar baki?
Safiyyah ta dukunkuna fuska tace “Anti meyasa kike min haka ne? ni Zayyan bai taba yimin irin wadannan zantukan na rashin kunya da kike min ba”. Anti Dije ta kai mata dundu tace “nice mara kunyar? To ko dai baida lafiya? Koda yake fa irin shi in sun samu wuri, sun fi kowa jarabar matansu, tunda Ustazi ne, to ke wai kin dauka in kun tare ma haka zaku cigaba da zama cikin ustazancin kamar wasu muharraman juna ko yaya? Da zaki ce ina miki rashin kunya, ko ba kya son lectures din da nake miki hakkina ne in miki”.
Ko tace cikin jimami “Allah Sarki diyata Safifi, duk wannna hirar soyayyar da ake sha a waya (is different) fa da irin abinda nake gaya miki, duk da na fahimci kamar Zayyan din baya da rawar kai irin na angwayen zamani, amma zaki ce na gaya miki irin shi sun fi kowa fitina da an shiga gidajensu.”.

Hakan kullum kara ruda Safiyyah yake yi duk duk tabi ta tsorace, ta kidima kanta da auren bakidaya, don Anti Dije ta sakata a kwana, ta jefata a tsoron masoyinta yanzu, ya zama last person data ke son jin sallamarsa gidansu.
Da tunanin Zayyan zai canza daga yadda ta sanshi zuwa marar ta ido, da zarar ta saka kafarta a gidan shi kullum take kwana take tashi.
Safiyyah dai irin ‘yammatannan ne kifin rijiya, ko kawaye bata dasu, watakila shiyasa ko kwalliya bata iya ba, gata dai a jami’a, amma bata deviating daga abinda ya kaita, kamar bata san wasu ‘yammata na existing a jami’ar ba. Kannenta su Sabah ne manyan kawayenta, sai ko Anti Dije da ta maye mata gurbin uwar daki kuma karamar Goggonta, ‘yan ajinsu tsakaninta dasu gaisuwar mutunci ba wata hira makamanciyar wannan irin ta sa’o’In juna, ita Anti Dije a wurinta abin kirki take yi, bata san ta saka mata shakku da wani bahagon tunani na daban ba, a kan cewa Zayyan zai canza daga nunkufurcin sa na ustazi zuwa devilish duk ranar data tare.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *