Chapter 8: Chapter 8
Sai ta cewa kanta ashe auren ana yinsa ne don wata manufa, tarewarta kuma na nufin a zubar mata da kunyarta ta diya mace, to bazata je ba.
Har ila yau Anti Dije ta nuna mata kamar taci wani bashi ne nasa a kanta, da zata biya koda tsiya koda arziki da zarar ta tare din.
Bawan Allah Zayyan yana can ABU yana fama da akalami bai san da aika-aikar da Anti Dije ta gama yi masa ba, bai san ta gama jika masa garinsa ba, ta hanyar yiwa amaryarsa famfon ilmi da wankin kai ba.
Ya kammala project ya mika. Duk da haka bai koma Katsina ba yana Zarian yanata shirye-shiryensa na tarewar Sahibah Sophie, bai fasa ba, sayo wannan yau sayo wancan gobe yana kara kawata dan gidan nasu, duk don tanadin zuwan Safiyyah.
Mama da kanta take tambayar Zayyan ya taji shiru, sai yaushe ne Safiyyar tasa “fi-sauran mata” zata tare ne???
Rasa mai zai gayawa Mama yayi, sabida ya biyewa son ran Safiyyah da yawa, shi kansa ya rasa inda Safiyya tasa gaba akan batun tarewarta. Yau tace ciwo, gobe tace jarrabawa. Kuma duk tayi su ta gama.
Don haka a karshen wannan makon da yazo Dandume, aka yi masa masauki a inda suka saba zama wato dakin bakin Malam na soron gidansu Safiyyah.
Safiyya ta fito ta sha Jilbab dinta kamar ba amarya ba, kai shi hijab dinnan fa ya fara daina burgeshi yanzu, ta tsugunna da murmushi a gabanshi tana zuba masa ruwan randar Ammi mai sanyi data debo a jug a tambulan mai garai-garai.
Tace “wai fa daga Zaria kazo ko? Sannu kaji! Ka sha hanya”.
Ya dubeta da kasan idanu rabin jikinsa kwance cikin kujera one seater guda daya dake dakin, sonta da kaunarta kullum karuwa suke yi a ransa, musamman saboda yawan kunyarta dinnan da har gobe taki barinta, da kalamanta na hankali cikin in’ina, sannan da hankalinta irinna tarbiyyar tsoffi, daga Malam har Ammi sun manyanta sosai kuma tarbiyyar manya suke yiwa ‘ya’yansu, shiyasa kullum ya ganta gabansa tana masa magana cikin in’inarta da taushin murya sonta da kaunarta karuwa suke a ransa su ninka na baya.
Komai Safiyyah tayi na manyancennan nata burgeshi take yi, amma yau jilbab da hijabs din sun fara gimsarshi. Fisabililllahi ace wai har bayan daurin aure matarsa ba zai ganta cikin kwalliya ba???
Yau sai ya hade giran sama dana kasa ya fito mata a Mr. Zayyan dinsa sak, namiji irin kowanne, yace cikin dakewa da shanye shakkarta, wanda kwarjininta ke sabbaba masa a kullum har yaji ba kowanne irin zance zai iya dosarta dashi ba.
Amma yanzu fa?
Ya hadiye miyau yana kallon pinky lips dinta da kullum suke bashi sha’awa. Yace.
“Sophie, yau daya dai a ajiye Hijab dinnan a gabana mana, in ga “Hijabie” dita a zahiri babu Hijabin?”
Ta yi maza ta kalle shi da mamaki, sai ya lumshe mata ido yace cikin kwantar da murya. “ina nufin don ki sha iska. Dubi fa yadda yake faman saka ki zufa har a goshi, to ina ga cikin jikinki? Duk da fankar nan dake faman filfilwa Safiyyah gumi kikeyi? Shi Hijabin na dauka na fita ne kawai amma banda a cikin gida a gaban miji?”.
Taji kunya da murmushi sun kamata a lokaci guda. Ranar farko kenan da ya taba cewa yanaso ya ganta babu hijabi, ya kuma hada da kiranta da suna ‘Sophie’ duk don ya tausasawa yardarta, sai taji sunan yayi mata dadi yau fiyeda sanda ya fara fade, saboda ba wanda ya taba kiranta da ‘Sophie’ din ta wannan sigar ta lallashi da Zayyan ya furta yau, very loving and so romantic daga zuciya har bakinsa, hakan yasa Safiyyah jin kanta yayi girma, irin na macen da miji ke lallashi kan tayi masa abu, taji kamar sunannan da Zayyan ya lanqaya mata yanzu, yafi na kowacce mace dadin furtawa (Sophie).
Duk da haka Safiyyah sai ta turo baki gaba, sannan a shagwabe ta dubeshi cikin marairaicewa “ai ni sam ban saba cirewa ba, sai in a dakina nake kona Ammi. Saboda inna cire hijab ko a gaban mata ‘yan uwana nake, sai in jini kamar tsirara”.
Zayyan yace a ransa “tabdijam! Akwai aiki ja, a gabana ashe”, kafin ya samu abin cewa Safiyyah ta kara da cewa cikin irin zancen zucinnan da ya fito fili “kwatakwata ni in ba a cikin gidanmu bane, a dakina kona Ammi, bana iya cirewa. To balle kuma a gaban katon namiji kamarka”.
Abin ya bashi dariya sosai amma ya gintse ya shanyeta yayi fuska, ya dan zamo daga cikin kujerar da yake kwance, ya riko hannunta dake zuba ruwa a tambulan bata san sanda ta saki kofin ba ruwan ya bare, jikinta ya hau rawa, Zayyan bai damu da reaction dinta ba ya kura mata ido, so inviting… tuni Safiyyah ta hau barin jiki, bai damu ba ya ce a tausashe.
“Sophie, nine katon namijin???
Ni ko???”
Ya fada yana nuna kansa da dan alinsa. Idanunsa na neman nata. Ta ji wata irin kunya ta kamata, ta rufe ido da hannu dayan da bai kama ba tana cewa “to da menene? Ai kayi biyuna a girma da tsayi, you are a giant!”.
Zayyan ya murmusa cikin kallonta, Mama na yawan cewa shi kato ne amma yau na Safiyyah yasa ya ji mazantaka ta karu masa sosai, a hankali ya sakar mata hannu, a sanyaye yaja baya ya koma cikin kujerarsa sosai, ya soma kokawa da emotions. Sai kawai zancen zucinsa ya fito fili a lokacin.
“Baza ki san ni katon bane sai ranar da kika bar gaban Mallam zuwa nawa gidan. Idan na tube a gabanki kika ga girman kwanjina da kaurin ‘muscles’ dina.
Daga ranar wannan hijabin na Safiyyah da acan baya yake burgeni ya daina burgeni kenan, sai dai ‘lingerie’ da ‘yan ‘nude nighties’ kawai nake son gani a jikinki Sophie!”.
Ya kare zancensa da wani irin lumshe idanu kamar mai hasaso ranar kasancewar hakan. Safiyya ta zaro ido tana dubansa a tsorace, sannan ta bude baki, nan ya gane ta ji zancen zucinsa. Sai ya fashe da dariyar basarwa, ya yunkura ya tashi zaune sosai ya dubeta cikin ido yace.
“Sophie kenan, to wai ke in tambayeki mana? Me kike nufi damu ne?
Nufinki a haka zamu dauwama? Ai hakan ba mai yiyuwa bane a rayuwar zahiri tunda muma ‘yan adam ne.
In kuma a haka kike nufin zamu cigaba da rayuwa har zuwa yanzu, rayuwa irinta wa da kanwa, sai ince you are totally mistaken.
Maganar gaskiya kawaici na ya fara karewa akan mara tausayin amaryar nan tawa Safiyyah.
Nima fa mutum ne, kuma in gaya miki mai cikar lafiya mai bukatar kulawar matarsa kamar kowanne namiji, amma ni sai zabga min kebura ake cikin ruwan sanyi.
Kafin muyi aure ne nake saurayinki, wanda bashi da kowanne hakki a kanki, mai iyaka dake a cikin mu’amala, amma yanzu Zayyanu ne mijin Safiyyahtu, Baban yaranta masu zuwa nan gaba kadan in sha Allah, kinji ko Sophie, don haka ki saki jikinki dani haka, Allah ya halatta min in ganki babu Hijabin. In kuma taba duk inda nake so a jikinki don hutu jin dadi na.
So yau daya dai, daure ki cire min shi in samu inga halittar matata Safiyyah babu Hijabi, ko in taso yanzunnan in cire miki shi da kaina”.
Safiyyah ta sunkuyar da kai cikin jin nauyi da kunya da wani irin abu da ya soma yanyame ruhin jikinta, Zayyan yace “kinsan har suna nasaka miki kuwa a wajen Mama, I used to call you ‘Hijabie’, duk sanda na ce Hijabie Mama ta san ke nake nufi, because these hijabs are your main characters dana fara ankarewa dasu a tare dake, kuma shine babban abinda ya fara fizgata zuwa gareki bayan in’inar. Amma daga yau su koma na fita school don Allah”.
Kunya sosai ta kama Safiyyah, haka ya ci gaba da kasheta da zance yau mai narka zuciyar mace yasa tayi laushi, har mamaki take wai Zayyan ne, sai murmushi take tana rufe ido in ya fadi wani abun mai nauyi, da ya matsa da son ta cire hijabin sai ta hau buga kafa a kasa cikin tabara tana cewa cikin shagwaba da rigima.
“ni dai bazan iya cirewa ba, ka barni da abina, bana so, kana bani kunya Zayyan…”.
Zayyan wanda a lokacin duk ta kara rikita shi da wannan salon shagwabar da bai taba gani a tareda Safiyyah ba, har dasu shura kafa irin na rigimammun yara, ba shiri yace ya hakura, domin ta tabo wani irin feeling da bai taba ji ba a kasan ransa, ya daga mata hanauwansa sama cikin saddaqarwa da bada kai, yana dariya yana cewa “nayi saranda Sophie! Na yarda ni Zayyan mijin Ustaziyyah ne, to yaya zanyi da ustaziyya ta? Daina borin haka kinji! Na hakura na bar miki abinki, ince ko shikenan zance ya kare?”.
Ita kanta Safiyyah sai da ya bata dariya, yadda ya biye mata hadda saranda. Ta lura da yadda jikin sa ke dan rawa a lokacin, amma bata fassara hakan da komai ba, amma fa Zayyan yau an shiga yanayi, gabadaya ta lura yau Zayyan wani kallonta yake so inviting with great admiration. Yayi kuta yace,
“Amma ba komai kiyi lokacinki ne, nima nawa lokacin na zuwa, kowa da ranarsa, tawa ranar na nan tafe.
Ranar da bazan saurari wannan shagwabar ba nima, balle in yi la’akari da ustazancinki, kaina kawai zan taimaka. Kaina zan so nima a ranar, zaki ce na gaya miki.
Kiyi shagwabarki da ustazancinki ki gama su a Dandume, tunda gidan Malam ne ba nawa ba, don haka banida ‘say’ sai abinda kikace kika kuma zaba mana, tunda ni na biyo ki gidanku yanzu dole ne in bi duk abinda kika gindaya min”.
Ya karasa da muryar da dole Safiyyah taji tausayinsa.
Safiyyah ta hau dariya tana cewa “au abin haka ne? In da kara ga Malam ai kaima nan gidanku ne “Habiby!”.
Ya ji wani irin tashin tsigar jiki, ya dai daure yace “ba wani Habiby, tunda guduna kike a gidanku Safiyyah, da gidana ne kin isa ince ki cire min hijabi kice a’ah ba’ayi yakin duniya na uku ba???” Safiyyah sai dariya take har hakan yasa Zayyan ya shagala cikin kallonta, ‘she looks so cute’ in tana dariyar in’inarta.
“Mu bar zancen wasa Sophie, yau zuwa nayi inji gaskiyar yaushe zaki tare a gidanki? Hatta Mama ta magantu, tunda har tayimin magana cikin kosawa akan batun tarewarki.
For God’s sake kince “exams” kuma na tabbata an gama. Safiyyah kince rashin lafiya, kuma gashi kin murmure, for God’s sake yaya kikeso inyi da raina da tunanin Safiyyah tana Dandume, ni ina Zaria nikadai, sai faman rungumar pillow da tumurmusar katifa nake, alhalin na san inada Safiyyah ta kuma zama mallakina?”
A yadda yayi maganar idanunsa kai tsaye suna kallon nata saida ya bata kunya sosai, da tausayi kuma duka a lokaci guda, domin damuwarsa ta fito karara a sautin nasa, sannan cikin lallashi da ban baki yake maganar.
Abinki da So, koko ince soyayyah ta hakika mai saurin karya zuciyar mace, Zayyan ne fa! Wani mutum guda daya da ta fara sanin so a kansa, batare da ta san ma menene son ba, kawai ta samu kanta da sabo dashi farat daya, ya shige ranta sukuf! Duk a lokacin da bata yi tsammani ko taba hakaitowa ba.
Itama tasan ba wai bata son Zayyan bane, ba kuma ta daina son sa bane bayan an daura musu aure, kawai Anti Dije ta tsoratata da aure ne gabadaya.
Safiyyah sai ta samu kanta da yin saranda, ta hanyar cewa “Shikenan na daina, duk lokacin da iyaye suka sake sakawa bazan kara musawa ba, kayi hakuri, ka ji Habiby?”.
Zayyan ya ji wani irin dadi ya ratsa har ransa, sai kawai ya taso daga kishingidar da yayi cikin kujera ya dawo yayi zaman Rakuma dirshan a gabanta. Ya daga tafukan hannunta ya saka fuskarsa a tsakaninsu, santsin sajensa dake kwance gefe da gefe na kyakkyawar Barumiyar fuskarsa yasa saida tsigar jikinta ya tashi yarrr! Shikuma duk sai ya susuce, ya rikice irin na rashin sabo da kusantar jikin mace, tasowar wani sabon al’amari a tare dashi yasa ya kai tafin hannunta saman lips dinsa ya sumbata for the first time, idanunshi a lumshe yace.
“baki bukatar bani hakuri, amarya ai bata laifi ko ta kashe dan masu gida, that’s my beloved Sophie, ni kadai na san irin tanadin soyayyar da nake mana, nagode Safiyyah kinji, once again nagode kuma in sha Allah bazaki taba nadamar hada rayuwa dani ba, nayi miki wannan alkawarin, in sha Allah Safiyyah”.
Tunda Zayyan ya samu wannan damar, yau sai ya dukufa lallashin ‘yan kayansa da alkawura da kalamai masu dadi har Safiyyah ta fara kwantar da hankalinta a kan tarewarta, ta dan saki jikinta dashi kadan, hannunsa sarke cikin tausasan yatsunta suka shiga hira a hakan. Kai a karshe ma basu rabu ba a ranar, saida Zayyan ya san yadda yayi da dabara da hikima ya raba jikinsu wuri guda karo na farko a tarihin soyayyarsuda jikisa ya shiga cikin nata, ya rungume Safiyyah tsam-tsam a jikinsa lokacin da zai tafi, Safiyyah na iya jin yadda kirjin Zayyan ke bugawa ba sassauci yana gaya mata cikin kunnenta.
“Saurara Sophie kiji irin bugun da kirjina ke yi, ba komai bane sonki da tsananin sha’awarki ne”. Ko daga yadda jikinsa ke bari cikin mararin samunta da yayi cikin jikinsa yau, ta yarda da abinda yake fadin. Zayyan ya samu gangara domin gabadaya Sophie ta saki jikita dashi yau, yayi kissing dinta sosai a kasan wuyanta, kafin ya gangara zuwa saman lips dinta, ya sumbaceta son ransa har cikin tsakiyar bakinta da wani launin (French kiss) da shi kansa bai san yadda ya aiwatar dashi ba, karo na farko a soyayyarsu.
A ranar ya gaya mata ya san ‘fear’ dinta, “I obviously know your fear” don na karanceshi tsaf a tsakiyar idanunki, ko baki fada ba na gane tsoron daren farko kike ji, amma kullum Safiyyah kisa a ranki ni ba abinda yasa na aureki kenan ba, kuma soyayya ba cutarwa bace.
Na aureki ne don ina sonki Sophie, ba don sha’awar wani abu a jikinki ba, ina so in rayu dake ne, daga nan har karshen rayuwata.
Ina fatan ki zama uwar ‘ya’yana a duniya da lahira kuma matar dana ke so in rayu da ita har a aljannah.
Da wannan nake so ki kwantar da hankalinki ki tare a gidanki kinji Safiyyah, nayi miki alkawarin bazanyi komai ba sai ranar da kika shirya karbata a matsayin mijinki, barin rayuwarki, kuma bisa amincewarki da yardarki da goyon bayanki kadai zan kusanceki”.
Bayan kunya da taji yau kamar tace kasar ta tsage ta shige har da tausayinsa da karin soyayyarsa. Sukayi wata irin rabuwa mai sanyi a zuciyoyinsu, Zayyan yana kara kashe mata zuciya da kalamai masu sanyaya ruhi da Batasan ya iya bama.
Ganin kwana biyu Safiyyah ta fara samuwa ta amince ta kwantar da hankalinta, sai iyayenta suka durfafi shirin kaita gidan mijinta a Zaria.
Malam yace baya son bidi’a mara tushe. Don haka baya son taron biki. Zayyan zuwa lokacin ya maida hankalinsa ya kammala project dinsa yayi (defense, both internal and viva).
Ya fito a sahu na farko cikin zakakuran dalibai da suka fita da (first class) su uku kacal a tsangayar Architecture, daga jami’ar Ahmadu Bello, don haka yana gamawa ABU suka daukeshi aiki sharp-sharp a matsayin Assistant Lecturer.
Lecturing has been his dream career…. saboda a komai so yake ya gaji Babansa. Don haka ba bata lokaci ya karbi offer din da godiya.
Dan madaidaicin gidan da Baba ya kama musu flat ne a Samaru daidai su. Two bedroom flat da parlour daya, sai kitchen da balcony da harabar adana mota guda daya.
Akayi sa’a daga Zayyan har Safiyyah masu saukin tunani na rayuwa ne. Iya abinda mahaifinta yayi mata dashi taje gidan mijinta. Ba abinda Zayyan ya saka a gidan har ledar tsakar daki su suka saka abinsu.
Safiyyah ta shigo gidan Zayyan da tsaftatacciyar zuciya, soyayyar su gwanin sha’awa, takamaimai in za’a dora mata wuka a makoshi, bazata ce ga abinda ya sata son Zayyan ba da bashi matsayin barin rayuwarta (miji) da gaggawa haka ba, cikin abinda bai gaza shekara ba, kawai tana son duka halayensa. A wannan lokacin kam shima da kansa ya san Sophie babu soyayyarsa irinta aure mai girma a ranta, sai ko halayensa da kamalarsa data ke so fiyeda komai nasa.
Sai ya fara da koyawa Safiyyah yadda zata yi masa so na soyayyar aure gradually. Saboda aurensu yazo ne unexpectedly daga Allah, wato daga zuwa gabatarwa tsakanin iyaye sai Ubangiji ya aiwatar da kirarinsa na “kun fa ya kun” a kansu.
Don haka da Safiyyah ta tare abu na farko da Zayyan ya fara yi shine ya fara da janta a jiki, ya maida kansa dan aikinta, komai tare sukeyi na ayyukan gida, suna yi suna hira yana bata dariya kamar ba shine mara far’ar nan a filin Allah ba.
A hankali ya fara koya mata yanda zata zauna dashi cikin tarairayar abinda yake so da gujema wanda baya so, Zayyan ya koya mata sakin jiki dashi cikin launin soyayyahrsa mai shiga rai.
Alal misali a ranar da Safiyyah ta tare da yake Zayyan ya riga ya lura da fear dinta akan first night.
Sai ya hadiye duk wata zalamarsa irin ta kowanne sabon ango a wannan ranar, ya dinga lallaba Sophie da tatsuniya da labarin Magana Jari ce, saboda shi yayi karance-karance na adabin Hausa tun yana secondary school, ya bata labarin cewa yana cikin Hausa Club and Society har Debate na harshen Hausa ya sha zuwa ya wakilci makarantarsu. A haka labari ya kaiwa Sophie karo a ranar har tayi barci a jikinsa bata san lokacin da tayi ba.
Hakika ta sara ma Zayyan wajen iya sadaukarwa, ga iya kalaman soyayya da lallashin mace, irin kalaman da ya baibayeta dasu da asubahin ranar bayan sun sallaci sallar asubah a jam’I su biyu. Suka koma gado suka kwanta idonta cike da barcin gajiya amma hankalinta bai kwanta ba, ganin shi bashi da niyyar yin barcin safen, sai ma yaja duvet ya rufe ta har zuwa kirjinta, ya sukuya saman kanta yana mata kalamai masu kwantar da hankali da nuna mata cewa shi bashi da matsalar komai yau a kan hakan. Bama ya jin sha’awar komai (he’s overwhelmed with happiness and excitedness) da shigowarta rayuwarsa, yace ta saki jikinta tayi barcinta ta huta Zayyan zai mata tausar kafar da zata sat aji dadin barci. Tun tana dar-dar da shi har ta yarda da gaske yake, ya soma yi mata tausar ta hanyar jan zara-zaran yatsun kafarta a hankali, tausar namiji na ratsa Safiyyah bata san yaushe barci ya soma fizgarta ba.
Daga bisani da ya tabbatar tayi nisa a barcinta sai ya jefa pillow a kan kilishi ya koma can ya kwanta, yana kallon barcin Safiyyah da yadda take sauke numfashin barcinta cikin nutsuwa. Da gaske da akace wai wasu matan, sun fi kyau idan suna barci, ya yarda da hakan yau akan ‘Sophie’, wato Safiyyah is a sleeping beauty”.



