⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 9: Chapter 9

Yayi ta jinjinawa kansa yana sarawa kansa da kansa tareda kissimawa a ransa, ko yaya akayi ya iya yima Sophie wannan bajintar? A dai wannan daren mai dumbin tarihi da ya dade yana jiran isowarsa, wato a darensu na farko? Ya jure bai kusanceta ba duk karfin sonsa gareta, da dokinsa na zuwan wannan ranar?!

Shi da kansa sai ya baiwa kansa amsa da cewa saboda sonta da kaunarta da yakeyi sun rinjayi sha’awar. Kasancewarta cikin kwanciyar hankali rana ta farko a gidansa zai fiye masa duk wani pleasure da zai samu a cikin daren.
Bai auri Safiyyah don biyan bukatar gangar jikinsa ba, kaunarta yake yi har cikin bargonsa, wata irin kauna mai yawa, don haka son farin cikinta tareda shi a zaman aurensu ya rinjayi komai.
Kuma yana so ya zama mai fada da cikawa a gareta. Wato in yace zaiyi abu, ya tsaya ya tabbatar yayi, in yace bazai yi ba, kada ya canza. Kwanciyar hankalinta dashi yana gaba da komai. Washegari daga shi har ita, a ranar sai suka zamewa juna kamar wasu bakin juna, ta kasa hada ido dashi tana ji a jikinta kamar tayi masa laifi data ganshi kwance akan carpet, wato ya bar mata gadon ta kwana ita kadai cikin sakewa.
Tare sukayi girkin breakfast, Zayyan na firar dankali Safiya na juye Ruwan zafi a tea flask, tana masa dariyar wai ya iya firar dankali, yace “meye abin mamaki? Wai baki san ni kanin mata bane, kuma Yayan mata ba? In kawayen Mama suka zo gidanmu ce min suke na mata-na matan Mama.

Don haka ki daina mamaki don kin samu kwararren mai firar Dankali a gidanki, ba abinda ban iya ba na kitchen, in gaya miki.
Kafin a yiwa su Yaya Zubaida aure duk makyuyata ne. Mama tafi sakani tayata aikin kitchen fiye dasu”.
Nan ya shiga bata labarin halayen ‘yanmatan gidansu daya bayan daya, cewa Zaitoon da Zahra sun fi baiwa gayu da kwalliya muhimmanci fiyeda aikin gida, Hatoon kuwa auta ce sangartacciyar Mama, da irin kyuyar Yaya Zubaida akan aikin gida, yanzu zata kirkiro ciwon ciki na karya don Mama tace ya karba ya mata aikin, don haka duk wani aikin kitchen na Yaya Zubaida kusan shi yake yiwa Mama Fatu.
Yace Yaya Zubaina ce kadai ke dan tabukawa, kafin a aurar dasu, itama sai in baya nan”.

A haka suka soya dankalin turawa (irish) da kwai, suka dafa shayinsu yaji kayan kamshin gargajiya kanumfari da citta, suka juye komai a plate guda, suka dauka zuwa falo, yana sakale da ita a kugunsa tanata jin kunya.
A plate daya suke ci, Zayyan ya cako irish da fork ya kai bakin Safiyyah “ha’an, bude nan in baki a baki!” Kunya sosai ta kamata, ta rufe ido tana ‘yar dariya ta rashin sabo, wani abu da wani namiji bai taba yi mata ba, bayan Yayanta Yaya Sheikh, wato bata abinci a baki.
Shima Yaya Sheikh din tun tana ‘yar kankanuwa ne, sanda tana junior secondary, Yaya Sheikh na yawan bata abinci a baki, kuma a gaban Ammi, musamman in tana fushi, ko Ammi ta bata mata rai. Zayyan ya lura ta tafi tunani, yace.
“Sophie tunanin me kike haka? Bude idonki ki dubeni, wannan kunyar fa dole ki ajiyemin ita a gefe zuwa sanda zan bukaceta, amma ba na bukatarta yanzu sam. Ta yi min yawa.
Yanzu so nake in zama ke ki zama ni, mu gina trust a tsakaninmu, mu zama confident din junanmu, muyi rayuwa ta shakuwa, fahimtar juna, amana da soyayya.

Sophie kin san daga jiya na zama naki kin zama tawa? To kiyi wa Allah ki daina yimin rowar kyawawan idanunki in muna tare, kina wannan boye sun, domin su nafi son gani koyaushe, inta tozali da (silverish eye ball) dinki. Daga su sai in’inar (stammering), su nafi so fiyeda komai naki. So open your eyes and look straight into my eyes ko naji dadi, ki kuma bude min dan bakin nan ina so in ciyar dake yau da hannuna, ki kuma yimin ‘yar in’inar ko kadan ce inji mana?”.
Ai bata san sanda tasa dariya ba. Shi kuma daman hakan yake so, ya dawo da attention dinta gareshi, don ta tafi tunani, sam ta manta yana wurin, sai ya cigaba da kambama dadin in’inar tata, wadda yace tafi masa duk wata muryar zabiyoyin larabawan da ya sani dadi (Arab musicians) su Nancy Agram.

Dariya take yi sosai, ta shagaltu da dariyar shima ta shagaltar dashi cikin kallonta da shaukinta, tace “wannan kuma “C” ce Malam, don ka san bazan iya waka bane kake mun ba’a”.
Da rana ma tare suka yi girkinsu inda sukayi lunch mai saukin girkawa, jollof din shinkafa tayi musu da taji daddawa da naman saniya. Tun anan Zayyan ya fara gane kwarewar Safiyyah a girkin hausawa ne, ba girkin turawa ba, tunda har tasa daudawa a jollof. Sai ya bashi wani irin aroma da dandano, da bai saba ji ba, kuma ya masa dadi, Ammi ta musu wannan horon bakidayansu ita da kannenta su Rayyah, sau da dama Ammi in suna gida basa makaranta sam bata shiga kitchen. Su take barwa komai na girkin gidansu da hidimar tsaftar gidansu.

Tun Safiyyah na dar-dar da angon nata Zayyan Bello Rafindadi, har ta gama sakankancewa Zayyan dai baya neman komai daga gareta sai sabo, shakuwa da soyayyah, wato so yake su saba a wannan lokacin, kwanciyar hankalinta da sakin jikinta dashi yafi bukata fiyeda gangar jikinta. Soyayyar da bai nuna mata kafin aurensu ba, ita yake nuna mata yanzu gangariya, a halin yanzu baya jin kunyar ya zauna daga shi sai (shorts) a gabanta, tayi ta jin kunya kamar tace kasar ta tsage ta shige ta kuma kasa sakewa, fitsarar Da namiji da bai nuna mata a makaranta ba yake zuba mata gangariyarta yanzu, a tsakar gidansu cikin dakin aurensu. Misali yace ta zo ta cuda shi a wanka, ko sai sun yi wanka tare, amma sai ta gudu ta buya ko tace girki take zai kone in ta tafi.
Tafi-tafi daga kwana bisa kilishi har suka koma kwana gado daya, ba tareda ta gano wani abu makamancin faruwar wannan tsoron nata daga Zayyan dinta ba.
Gabadaya ta soma sakewa dashi yanzu, ta kuma sakankance ta saki jikinta sosai dashi dari bisa dari, ta yarda da angon nata, cewa shi daban yake, baya cikin layin irin mazan da Anti Dije ke lissafin Ustazai a waje, Devilish a cikin gida, ita mijinta bawan Allah ne mai son ta da yawan tausayinta, da gudun duk abinda zai wahalar da ita bazai iya wannan al’amarin da ita ba. Ke dai barshi da yawan tubewa a gabanta batareda yaji komai ba.
Cikin sati biyu kacal Zayyan da Safiyyah suka wani irin dinke tamkar sun shekara da aure.

Sai ga Sophie har ta kan rabi jikinsa ta kwanta ba tareda ta san lokacin da tayi hakan ba, in hirar falo tayi dadi kenan.
Shikuma ya fara amfani da wannan damar yace kitso zai yi mata, duk yabi ya cukurkude mata sassalkan gashinta ya cukuikuiyeshi da kalba. Ga Safiyyah Masha Allah da gashin Katsinawan Dikko. Suka manne da juna tamkar tube da tyre, sallah kadai ke rabasu, in zai tafi masallaci, shima sai taji wani iri kamar in ya fitan bazai dawo ba. In ya fita din kuma zuciyarta na kansa. Allah-Allah kawai take taji motsin taba kofarsa ya dawo gida.
Tafi-tafi daga sanda suka samu kansu dumu-dumu cikin sumbatar juna ma su duka biyun basu ankare ba, sabida feeling irinna kowanne lafiyayyen dan adam da ya soma aiki a jikin kowannensu.
Safiyyah bata farga data fara kamuwa a tarkon angon nata Zayyan ba, sai ranar da kiss mai zafi irin (hot kiss) ya ratsa a tsakaninsu….
Daga shi ya zarce da shafar sassan jikinta kota ina da kyar ta iya kwatar kanta a ranar.

Wata ranar Asabar wani (accidental French kiss) ya faru tsakaninsu na wucin gadi. Hakan ya faru dasu ne ranar bisa dining area, ta kona mishi dan yatsa da ruwan zafi garin zuba mishi tea bata sani ba. Nan Malaminki Zayyan ya samu hanyar da ya dade yana neman samu bai samu ba, ya jangabe rike da hannunsa yace sai ta tsotse dan yatsan zai daina masa zafi, “zafi yake mun sosai kamar fatar ta daye Sophie”. Ai kuwa Safiyyah a rikice, ta taqarqare ta kai dan yatsan bakinta ta hau tsotson babban dan yatsan ba tareda ta san tarko ne ya dana mata ba, kiss din da ita ta fara jinsa a jikinta kafin shi, tasirinsa ya tafi abruptly ya ratsa har tsakiyar kwakwalwar Safiyyah data Zayyan din kansa.
Lokacin da tsotson y afara yin tsotso, sai jikin kowannensu ya fara dauka, suka dubi juna a rikice, a gigice, idanuwa sun birkice da sha’awar juna, duk tayi arousing dinsu, kallon da yayi mata a lokacin da barauniyar rungumar da ya yi mata ba shiri, shi ya tayar da dukkan emotions dinta na diya mace, ta kasa koda wani kwakkwaran motsi na kwatar kai.

Shi kuma haduwar fatar jikinsu wuri guda ya kara birkita shi, nan suka bige da sumbatar juna a urunce, a yunwace kuma a susuce….
A wannan ranar dai da kyar suka kwaci kawunansu a hannun juna, ba tareda komai ya wakana ba.
Matsananciyar kunyar shi data biyo bayan hakan ta hanata sakat har wayewar gari.
Daga ranar ta saki jiki aka soma shan zumar soyayyah, har Zayyan ya soma aika manyan sakonninsa kadan-kadan cikin dabara irin tasa.
Soyayyar sa mai sanyi, wani lokacin zazzafa, ta tsayawa Safiyyah a rai, ta rike ran Sophie akan mijin nata, soyayyah ta wasannin ma’aurata (romancing) kawai yake gwada mata zallarta, mai tsayawa a ran diya mace, irin ta namijin da ya san kan love, ya kuma yarda da kansa da matsayinsa a zuciyar matarsa, cewa shi abin so ne ga matarshi, da kowacce irin mace data fada komarsa.

A wannan dan tsakanin Zayyan ya nunawa Safiyyah cewa shi mai tsananin sonta ne, kuma yayi hakuri mai yawa da ba duk maza zasu iya kamarsa ba, tunda ya aureta yake tattalinta da gujewa tsoron nata, don duk halin da zai shiga baya wuce limit din da ya san Sophie bazata iya dauka a lokacin ba, wannan shi yafi komai samo masa kanta nan da nan, ta yarda dashi akan hakuri da hadiye sha’awa dari bisa dari, zata iya bugun kirji tace shi daban yake, wato ya bambanta da sauran mazan da Aunty Dije ke bada misalin rashin hakurinsu akan matansu a cikin gida bayan aure. Zayyan ya kasance namiji mai tsananin wayau da hikimar iya sace zuciyar matarsa….
A hankali yasan yadda yayi yasa tsoron nasa ya fara barinta, har ta zama addicted da yawan sumbar da yake mata, da nau’ikan romancing dinsa kala-kala da yake yawan aika mata a ko’ina suke cikin gidansu, har a kitchen bai barinta, bai raba ta da jikinsa, ta zama addicted to his touches, koyaushe har jirace take daya sumbacetan, ko ya rabi jikinta ko yaya ne.
Da haka soyayyar su ta aure ta bunkasa, ta soma zama flamboyant.

Hatta wanke wanke Safiyyah nayi Zayyan na dauraya, yana aika mata kiss a kasan wuyanta yana zuba mata hira, wannan ba damuwarsa bace wai don ya tayata aikin kitchen (as long as) Safiyyah zata daina tsoronsa da aka saka mata.
Da kyar yake iya fita yanzu, ko ya fita cikin makaranta baya jimawa. Sallah ma shi yake musu jam’inta, sai yace wai tafi lada. Duk don kada ya fita yayi nisa da Safiyyahrsa.
Hutun sati uku office suka bashi na aure. Gashi ba wuya a wurin Allah har ya lamushe su, cikin kulawa da tattalin Safiyyah da inganta rayuwar aurensu da soyayyah mai wuyar samu.
Ranar da Sophie tayi kwana ashirin da daya da tarewa ne wato ranar da hutunsa ya kare yace ta shirya ya kaita Katsina ta gaida Baba Bello da Mama Fatu.
**** **** ****

Hausawa suka ce wai komai nisan jifa kasa zai fado. Kuma sannu sannu bata hana zuwa saidai a dade ba’a je ba. Sannan suka ce wai komai wayon amarya….. watarana irin wannan……na zuwa!!!
Ranar mai dimbin tarihi a garesu ta kama Asabar ce, kuma ta karshen wata. Don haka ana sanitation a gari, wanda yasa basu fita kofar gida da wuri ba, sai wajen karfe goma na safe.
Safiyyah ta shirya tsaf cikin wata makubar Egyptian Jilbaab dinta. Ta kawo bungles ta zubawa hannun hagunta ta fito tsaf da ita, kamar baqar balarabiyar Saudiyyah.
Tun jiya yayi musu shatar Taxi da zata kaisu har Katsina, mai taxi ya iso kofar gidan ya kirashi yace ya iso yana waje.

A daren ranar Safiyyah tayi wa Mama dambun nama mai dan yawa da cake da (milk doughnut), tun Asubah ta tashi tana karasa aikinsu, ko Zayyan bai san aikin me take tayi a kitchen tun duku-duku ba. Da suka yi sallah barcinsa ya koma. Saida gari yayi haske ya tashi yayi wanka a gurguje, ya dauki wata dakakkkiyar shaddarsa fara sol, getzner. Ya fesa turaren sa dayake amfani dashi tun na lokacin wato UltraViolet (Men) samfurin Paco Rabanne.
Har sun fito zasu shiga mota bayan Zayyan ya saka kwanukan data shirya abubuwan da zata kaiwa Mama a ciki a bayan motar. Sai Safiyyah ta tuna tayi mantuwa.

Ba wani abu ta manta ba cajar wayarta ce da kayan kwalliya data sayawa autar Mama (Hatoon), tayi excusing dinsa ta koma cikin gida, tana komawa daki ta sunkuya a kasan kujera tana neman charger dinta.
Da Safiyyah ta juya baya tana tafiya kamar wanda akayi wa wahayi a wannan lokacin sai kawai ya ya samu kansa da dagowa a slow ya kalli bayanta… tana takawa bayanta yana kadawa dari da sittin, dari da saba’in, duk da cikin jilbab take, kirjinnan ya ciko kamar zai fashe, don har wata ‘yar kyakkyawar kiba Sophie ta kara a gidansa cikin sati uku, saboda samun kyakkyawar kulawarsa da soyayyar mijin da bai son ta wahala, duk wani aikin energy zai karba yayi mata, tafiya take cikin wannan takun nata mai kamar na mage mai yanga (cat-walk). Zayyan ya hadiyi wani whalallen miyau, ji kake, muqut, cikin tasowar sha’awar da bai taba ji ba a rayuwarsa.

Amma a haka ya basar ya maida kai ga wayar hannunsa yace a ransa “yarinyar nan kin dade kina cin lokacin ki a kaina. Ko maza nawa ne irina masu sadaukar da farin ciki da jin dadinsu, ga samun kwanciyar hankalin matansu?
Sai kuma wani irin bakon tunani ya zo masa, na idan suka mutu a hanya fa shi ko Safiyyah, ba tareda ya taba tabbatar da sunnar Manzo data rataya a wuyansu ba shi da ita, kawai sabida gudun zuciyar matar tasa? Wannan fa ya tashi daga neman hadin kanta da kwanciyar hankalinta, ya koma kamar shakkarta yake yi??

Shin Safiyyah zata rabu dashi ne idan ya dabbaqa sunnar aurensu? Ko sakinsa zata yi? A gidansa fa take. Iyakaci tayi fushi dashi duk ranar da hakan ta faru. Sai wata sabuwar sha’awa da fitina mai tsanani da bai taba ji ba akan Safiyyah suka zo suka rinjayi duk wani tunani da ‘self-control’ da ya mallaka a lokacin.
Yayi kokarin ya shanye komai har suje Katsina su dawo, amma ina! Al’amarin nema yake ya zama out of his control a cikin taxi. Ya kasa sukuni sam a zaunen da yake, sai muskutawa yake yana sake muskutawa. Da yaga haza, wato zaayi abin kunya in Safiyyah ta fito sai kawai ya fito daga motar, ya fidda kayansu daga bayan motar ya sallami Mai taxi da kudi masu kauri, yace yayi hakuri sun fasa tafiyar sai wani satin ya dawo suje.
Ya dauko kayan girkin nata ya mayar matasu kitchen daya bayan daya.

Sophie na dagowa daga leka kasan kujera tana neman charger taga Zayyan tsaye a bayanta kamar sojan badaqqare, har sai da jikinsu ya gogu da na juna garin dagowarta.
Ganinsa a bayanta unexpectedly yasa Safiyyah ta dan tsorata, musamman ganin yanayinsa na lokacin, saida gabanta ya fadi, mummunar faduwa domin ta dauka wani abun ne ya faru a irin kallon da yake mata, ta soma kokarin magana cikin in’inarta….
“Ah! Zay…,yan.. Habi-by…. Lafiya dai ko? Ai da ka jirani yanzun….zan.. Yanzu zan fitoooo… “.
Sauran maganar makalewa tayi a makoshin Safiyyah, sakamakon irin rungumar da Zayyan ya kai mata intensely, ba shiri ta hadiye sauran abarta, domin idanun Zay–yyan dinda ta kasa karasa ambatar cikakken sunansa yau saboda firgita, sun tashi daga na normal Habiby dinta data sani mai lallabata, ya fito mata a namijin zakinsa sak! Yanayinsa ya nuna muraran cikin yanayi na matsananciyar bukatuwa yake da ita, yanayine da ita dai ta kasa fassarawa, don bata taba ganinsa cikin kwatankwacinsa ba. Wani yanayi ne da ko me zata ce, kuma ko zata yi yau don son ya daga mata kafa… zuwa wani lokaci, hakika ba zaiyi wani tasiri ba.

A lokacin nan Zayyan ya hautsine mata ya koma mata a namijin Kure, wadanda basa ji basa gani a lokaci irin wannan.
Ko daga yanayin hot kisses dinsa na yau, wanda ya sha bambam dana kullum wajen daukar zafi, Sophie ta san yau dai ta kare mata, karyarta ta kare a hannun dan mutanen Rafindadi, shima tasa ta kare, wanda hakan yasa ta tausayawa kanta da kanta tun kafi mai afkuwa ta afku… At the same time, Zayyan yayi kokarin dan hadawa da lallashinta, yana kuma bata baki da tausasan lafuzza na cewa hakan bazai cutar da ita da komai ba, duk cikin son da ya samu kansa da yi mata ne, yana kokarin cimma burin gangar jikinsu. Amma shima zufa yake. Shi kansa baya cikin hayyacinsa, kamar wani wanda aka yiwa wahayin lallai-lallai ya amshi sadaqinsa a yau, kuma a yanzu, da farar Safiya, in ba haka ba zai iya rasa ransa.
A cikin kalamanshi na ranar da Safiyyah zata iya tunawa har cewa yayi ta yi masa alfarma, ta bashi dama (koda ta iya yau ce kadai) domin ya gwada mata girman son da yake mata a aikace.
Manyan idanunsa da suka canza launi suka kuma kankance sun gama gaya mata manufarsa ta yau mai kankat ce, ba sauran ragayya a tsakaninsu.
Koda bai fayyace da fatar bakinsa ba, emotions dinsa sun gama nunawa.

Jin saukar dumin hawayenta kan kafadunsa, gabadaya sai ya shiga damuwa, da kyar ya iya cewa “Sophie, kiyi hakuri kinji, kiyi min alfarmar yau kadai, haka rayuwar kowacce mace ta gada ba rashin so bane, ba rashin tausayi bane, shine cikar manufar hakikanin son da nake miki. Shine kuma hanyar da zata bamu zurri’a tsarkakakka mai albarka nida ke.
Ji nake yau in ban sameki ba mutuwa zanyi Nana Safiyyah!” Shima sai nasa hawayen suka digo a gadon bayanta.
Kalamanshi sun bata tsoro. Kuma koda ace Zayyan bai furta hakan da bakinsa gareta ba, idanunsa da rawar da jikinsa keyi wajen shige mata, sun gaya mata yau mai rabata da Habiby sai Allah kadai, wanda ya kulla wannan zazzafar soyayyar tasu.
Duk wata sha’awa da ya tara ta wata da watanni, duk wani feeling daya dade da zama tamkar gyambo ko tsatsa a gangar jikinsa da zuciyarsa, sai yau ya samu suke ‘healing’ daya samu Safiyyah yadda yake so a kan gadon aurensu. Maganganunsa na karshe kafin ya maidata cikakkiyar matarsa da zata iya tunawa shine da yace “tayi hakuri” and he mean it. Ba abinda zai iya mata a lokacin bayan ban hakurin.
Zayyan yace tayi hakurinnan sau ba adadi yafi cikin carbi, tun tana kirga adadin ban hakurin har ta daina, because he cannot speak any fluent language today, sai baragada, irin wannan;
“I neeed yhuhh badly today…I am so so – sorry Sophieeeeeee”.

Gabadaya yau Habiby umarnin jikinsa da zuciyarsa kawai yake bi, ba abinda take so yayi ko ya bari ba….
Duk wani uzuri da kauda kai da kawaici ya gama yi mata su a can baya.
Yayi mata bajinta da sadaukarwar da maza matasa kamarsa da yawa bazasu yiwa amarensu ba, musamman wadanda suka aura da gumin soyayya.
Dole kanwar naki, Safiyyah yau tayi saranda! Ba dogon musu ta mika wuya ga bautar aure bautar Ubangiji.
Zayyan ya zama mijinta na hakika yau, kamar yadda ya taba ce mata a soron gidansu watarana zai zama …. In bata manta ba ai dama ya taba ce mata bazasu dawwama a haka ba tunda ba auren Yaya da kanwa suka yi ba!
Ya kuma taba cewa “akwai ranar da bazai saurareta ba, kansa kawai zai taimaka, kansa kadai zai tallafawa a ranar”. To kenan ga ranar tazo.
Ya zamanto cewa rokonta da magiyarta na ya tausaya mata, ya biyar da ita a sannu ma ba ya bari zuwa wani lokaci ba basu yi tasiri ba sam a tare da Habiby, daga yadda gangar jikinsa yaso tafiyar da ita, domin basu taimaka ba ko kankani wajen samar mata rangwame ko yaya yake daga Habibin nata.

And that was how their first night happened, a very passionate night, they had a wonderful love making, ever! Wanda daga ranar yayi binding dinsu together suka zama cikakkun Zayyan da Safiyyah da a yau yake bada labari.
Tarihin aurensu ya fara ne daga wannan muhimmiyar ranar da ya karbi budurcinta cikin girma da daraja.
Domin a ranar ne ya goge duk wanan ‘fear’ dinta akan aure, ya cire hijabin nan na kunyar Safiyyah da take sawa tana lullube tsakaninsu.
Safiyyah sai taga komai ba’a yadda take zato da hasashe ba. Kuma ba’a yadda Aunty Dije ta suffantashi gwanin ban tsoro da saka fargaba a zuciyar amarya ba.
Bata sani ba Zayyan ya biyar da itane (in a very gentle manner) har ya samu ya gamsar da kansa, duk da irin kidimewa da rikicewar da ya samu kansa a lokacin na kasancewarsa virgin shima. Yet yana gayawa kansa yabi a sannu (no matter how) ta wahalar dashi, kada yayi hurting dinta is her first night. He wouldn’t take it as a revenge! A haka har ya samu ya karbi abinda yake kulafucin karba, wanda duk wani mijin kwarai ke burin karba daga matar kwarai irin Safiyyarsa….
Macen kwarai data kai mutuncinta gidan miji kadai zata gane irin yanayin da suka kasance ciki a wannan muhimmiyar ranar shida Safiyyah.

Don haka tafiya Rafindadin da ba’ayi kenan a ranar ba, a gidansu suka shiga Rafindadinsu, sai a sati na gaba. In fact, hakan ya janyo saida ya kara sati daya akan hutunsa, domin satin sai ya koma na jinyar amarya Safiyyah da cigaba da more romon soyayyah tsagwaronta, amarci yake diba son ransa, saida ya fanshe duka hakurinsa, koko muce satin ya zamar masa satin “Shahr Al-asal” (honeymoon) a larabce da kuma turance.
A cikin kwana bakwannan gradually dai Zayyan ya maida Safiyyah cikakkiyar matarsa ta sunnah, wadda duk sanda ya zo da bukatarsa da safe ne koda dare koda yammaci, zai samu abinda yake so har da kari, ayi masa welcome wholeheartedly babu kailula.
Matsalarsa daya da Safiyyah taki karbar irin sutturar da yake sha’awar ganinta a ciki kullum, kuma bata masa irin kwalliyar daren nan ko irin (dressing) din da yake son gani a jikinta sabida kunyarta da gidadancinta, ko muce saboda irin ‘orientation’ dinta da ‘background’ dinta wato hakan ya samo asali ne da irin ‘decent upbringing’ dinda ta samu.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *