Chapter 1: Chapter 1
KAWAR ZUCIYA 2 Chapter 1
Sumayyah AbdulQadir
07030137870 (whatsapp only)
[email protected]
[email protected]
“Rabbana hablana min azwajina wa dhuriyyatina qurratu a’ayunin wa ja’alna lil muttaqina imaama”.
SADAUKARWA NE GA
“TAKORI’S LOUNGE”.
Ina alfahari da kasancewa tare daku har tsayin wannan lokacin. Allah da ya hadamu haka, a inuwar al’arshinsa ya barmu tare cikin Alherinsa… har zuwa ranar da muka daina numfashi.
-Sumayyah Abdulkadir
01/01/2025
KAWAR ZUCIYA ( Littafi na 2
Wani abu da ya ja hankalin Mama akan Safiyyah shine har zuwa wannan lokacin Safiyyah ba haihuwa, ba ko batan wata balle a saka ran samuwar ciki. Duniya kam daidai gwargwado suna cikinta itada mijinta suna juya jin dadinta son rai, itada Zayyan basu nemi komai sun rasa ba, amma haihuwa shiru kake ji ko sama ko kasa kamar an aiki bawa garinsu, tuni anyi auren duka ‘ya’yan Mama saura Hatoon, itama din da saka ranarta a kanta.
Mama tana Katsina bata zuwa Abuja, amma kullum Zayyan yazo gabanta sai ta yada zance akan rashin haihuwar Sophie, in kuwa suka hadu, Mama sai ta fada mata baka koda ta cikin ruwan sanyi ne akan rashin haihuwa. Amma Zayyan bai taba damuwa da korafin Mama ba. Hasalima shi mantawa yake da wata haihuwa saboda yawan hidimdimun dake kansa.
Har ya zamana Safiyyah bata marmarin abinda zai kawo ta Katsina, Mama tayi nata, su Zubaidah suyi nasu gorin, rannan Zubaidah take tambayarta “wai sau nawa ake yi musu kwasar masai a shekara?”
Safiyyah ta dubeta cikin rashin fahimta ta ce “kamar yaya?” Sai Yaya Zubaidah ta gyara zama cikin izgili, da shakiyanci, tayi dariyar rainin hankali tace mata.
“Yo dole in miki wannan tambayar. Don na san a wata guda kike cika masai da kashi, tunda kin gaza kasaye Da ko ‘ya ko guda daya, shine nake mamakin ina kike kai buhunhunan abincin gidanki da basa ko shekara sun kare in ba masai ba?”.
Wannan magana ta yiwa Safiyyah ciwo. Har ta kira mahaifinta a waya a ranar tana kuka, tace “Malam kayi min addu’a Allah ya bani haihuwa idan inada rabo”. Kuma sune kalaman da suka sa ta fara kwadayin son haihuwar itama. Amma da fari bata ko damu ba.
Malam Usman kuma yace “Zan yi miki addu’a Nana Safiyyah, Allah ya baki mai albarka, daina kuka kinji baya saka komai kuma baya hanawa. Komai kika ga ya faru da rayuwar bawa haka Allah ya riga ya rubuta masa. Idan haihuwa alkhairi ce zan roka miki ya baki, idan ba alkhairi bace a gareki ya baki abinda ya fita alkhairi”.
Idan kuwa sune suka zo Abuja yin wata hidimarsu suka sauka a gidanta to har su tafi babu alkhairi a tsakaninta da ‘ya’yan Mama, sai gori da bakar magana da habaici cikin lumana. Yanzu sun bar kiranta diyar Alaramma sai “Barren Lady”.
Ko su ce “‘Yar kauyen Dandume an sha jar miya an yi bulbul. Amma har yau babu Da ba jika a gidanmu balle musa ran zamu samu mai sunan Babanmu”.
Cikin wasa da Dariya kadai zasu gaggasa mata magana mai sosa rai akan haihuwa, wanda sai ta yi wata yana damunta a rai. Har ta soma tsangwamar kanta da tunanin shin ita me ya hanata haihuwa ne??? da gaske “Barren” din ce ita???
Zayyan bai taba sanin wannan sunan da Zubaidah ta kirata dashi ba, don koda wasa shi bai taba damuwa ko ankara da rashin haihuwarsu akan lokaci ba, duk yawan korafin Mama a wurin yake tashi ya barshi bai taba sakawa a ransa ya dameshi ba. Sannan yawan harkokin dake gabansa ma basu barin shi ya tuna wai bashi da Da a gabansa, haka korafin Mama bai taba sawa yayi zancen haihuwa da Safiyyah ba, sai wannan fateful ranar, da Mama ta zaunar dashi tace.
“To Hatoon dai, an saka ranar aurenta, nikuma bazan iya zama nikadai a gidannan ba, babu Da ba jika, sai ka san inda zaka samomin ‘yan dugui-dugui da zasu dinga taya ni zama da debe min kewarta”.
Zayyan bai gane me Mama ke nufi ba yace “Au toh, sai na je na dauko miki Baba Ladidi daga Rumah, ta cigaba da zama anan bayan bikin ko?” (Kanwar mahaifinta data riketa).
Mama ta zabga masa harara tace “Ladidin ce ‘yan dugui-dugui?”
Shi har lokacin Zayyan bai gane ba, sai da Mama tayi masa fashin-baki, tace.
“Humm! Ita diyar Alaramma ashe ‘bakarariya’ ce ka auro? Sai uban ladabi da uban sunkuyar da kai da bazai amfaneni da komai ba? Shin ko kana kirge da shekarun aurenku? Babu wata albarkar aure kota bari a gidanka Baffana?”
Dariya sosai yayi yace.
“Mama rigima, menene kuma bakarariya?” Mama ta fassara masa cikin gatse, “juya” mana (wadda bata haihuwa). In maka da turanci; BARREN! Da Larabci kuma ince ‘Aaqira’. Tunda kai hausa bata isheka ba?”.
Sai yayi shiru. Kamar a lokacin ya fara jin Safiyyah bata haihu ba har yau. Jim kadan kuma ya daure yace,
“to Allah bai kawo mana ba Mama, zamu baiwa kanmu abinda Allah bai bamu bane?”
Mama ta katse shi tace “kada ka dorawa Allah, saidai in tsarin iyali take yi, don taci duniya da tsinke, ko kuma bata da mahaifa sam a jikinta, ko bata da kwan haihuwa.
Ni kawai jika nake so, ba kuma na kowa cikin ‘ya’yana ba sai naka Baffa”. Yayi zugudiii yana kallon ta kafin yace cikin shanye damuwa,
“duk ‘ya’yan da su Yaya Zubaida suka tara miki a gidannan Mama basu isheki ba? Sai nawa kadai kike jira? Ko jiya kince min Zahra ta haihu, Zaitoonah ta kusa, in kawo akwatin kayan barka…”.
Mama tace “bazaka gane ba Baffana, naka daban ne, ina son ganin ‘ya’yanka gabana. Allah shine shaida ko dama can nikam Allah ya shaida diyar Alaramma ba wani sonta nake ba, don dai Allah ya jikan rai Baba ya daure maka gindin aurenta ne, ba kuma wai na sota daga baya bane, illa yadda naga baka korafi akan ta, tana maka biyayya daidai gwargwado kuma, ya tabbatar min kana samun kwanciyar hankali a tare da ita, shiyasa na zauna lafiya da ita har wannan lokacin.
Amma akan matsalar rashin haihuwa shekaru takwas da aure yanzu Baffa?! Dole a ji mu a kan ‘drum’ nida ita, da kai dake daure mata gindi, zamu hau samu fado nida ku, na rantse da Allah Baffa.
Duk cikin jikokina da kake ikirarin an haifa min, ka gayamin in akwai wanda zaiyi bearing sunan Bello Rafindadi in ba naka ‘ya’yan ba???
‘Ya’yan wasu ne ba nawa ba, naka sune nawa. Ko kuwa so kake daga kanka ya zama cewa bayan Bello ya yanke?”
Anan inda sukayi maganar nan da Mama, anan wurin ya barta, don bai ji Tauhidi da technology da ikhlasi a cikinta ba shi, sai kace su zasu halicci dan cikin jikinsu. Bai ko tashi da zancen a ransa ba. Rigima da digimin Mama wanne ne bai sani ba?
Ko wace irin kalar rigimar ta in tanason wani abu ne bai sani ba? Babu! Baba Bello ya sha fadi cikin raha cewa Mama rigimammiya ce, bai kara yarda da irin rigimar tata ba sai yau data dawo kan rashin haihuwar Safiyyah ta saki layin korafinta na baya na malunta da mallakarsa a minjaye.
Tun kuma bayan rasuwar Baba rigimarta a kansa shi Zayyan din ta karu. Komai shi komai shi. Bata ko iya sati biyu bata saka shi a idanunta ba yanzu zata bashi query akan Safiyyah ta rike mata shi.
Kenan kuma yanzu rigimar tata ta dawo kan haihuwarsu kenan ko?
Toh banda Allah wa zai bada haihuwa a lokacin da aka kayyade maka, in banda abin Mama?
Yana tafe akan hanyarsa ta komawa Abuja daga Katsina yake wannan tunanin, yau dai Mama ta saka shi a damuwa dolen dole, bayan ya baro Mama a safiyar yau ya kamo hanya. Wasu gungun shanu ke tsallaka titi saura kadan ya kwashe kafafunsu sabida tsabar tunani, Allah ya taimakeshi ya kauce musu, ya dafe sityari sosai.
Wani ikon Allah kamar Safiyyah tasan meke faruwa tsakaninsa da Mama a Katsina jiya a kanta, kodayake kamar hadin baki, a dan tsukin itama rashin haihuwar damunta yake yi sosai.
Ya shigo gidan yanata sallama bai ji motsinta ba. Ya duba dakinsa da nata duk bata nan, kuma bai ji alamar zubar ruwa daga toilet ba.
Duk da haka yace bari ya duba nata toilet din, sai ya murda kofar toilet dinta, Ilai kuwa, a can ya sameta zaune dirshan a dandaryar kasan tayal din bandakin, ta hada kai da guiwa da wani siririn abu rike a hannunta.
“Sophie?”.
Zayyan ya kirata a tausashe, with concern and love in his voice tone, kuma cike da fargaba, don baya raba dayan biyun kuka kashirban Safiyyah take yi mai tsanani.
“Me kike yi anan haka? Meke faruwa haka?”
Ya tambayeta yana takowa zuwa cikin toilet din. Safiyyah bata amsa ba sai ma jin zuwansa da tayi yasa kukanta ya karu harda da gunji da jin shigowarsa.
A hankali kuma cikin faduwar gaba Zayyan ya tako har zuwa gabanta, yasa hannu ya zare abinda ke hannunta ya duba, nan ya gane Pregnancy Test Strip ne (PT Strip).
Ya mikar da ita tsaye. “Hey! Is this Pt strip? Me kikeyi dashi to? Tell me, are you pregnant?”
Ya dago ta ya tallafota ya fito da ita zuwa falo. Ya kwantar a jikinsa yana tambaya.
“Safiyyah menene hakan? Na kasa ganewa. Menene wannan abun, me kike yi dashi a toilet kamar wata likitar mata?”
Saida ya zage sosai da lallashi da banbaki, ta tabbatar ya shiga damuwa irin wadda take ciki, sannan ya samu ta daina kukan. Ya rungumeta sosai a kirjinsa, ya barta ta kwanta lamoo! Kawai tana sauke ajiyar zuciya. Suka baje a dandayar falo. Kamshin Ultraviolet (Paco Rabanne) dinsa yana ratsasu tare, yace “Safiyyah kin dagulamin lissafi, na kasa gane me ya faru dake, kin tsoratani daga dawowata. Ba ko sannu da zuwa? Please explain. Kin sani a duhu!
Wani abu ya faru da bana nan? Me ya sameki kike kuka? Me kuma kikeyi da PT Strip? Wani ya zo ya gaya miki wani abu ne daga Katsina?”
Duk yabi ya sha jinin jikinsa akan zancen da suka gama jiya a kanta da Mama.
Da kyar ya samu motsin bakin Safiyyah inda tace “ba wanda yazo nan. Period dina ne yayi jinkiri, inata murna ko bukatata a wurin Allah ta shekara da shekaru ta biya, ko Allah ya amsa min roko na, shine nayi pregnancy test, but it shows “negative” yau ma kamar kullum”.
Murmushi yayi ya tallabo habarta saman tafin hannunsa, ya sumbaci saman lips dinta lightly, yace,
“ke likita ce da zaki yiwa kanki PT ko karambani da giggiwa na nemowa kai damuwa irin naki Sophie? Haba Nana Safiyyah! Da ilmiki na addini kike damuwa akan abinda kinsan nufin Allah ne? Ko na taba ce miki na damu ki haihu yanzu?”
Ido fal hawaye Safiyyah ta dago tana kallonsa da takaici, ba tun yau ba ta san shi ba abinda ya dameshi da rashin haihuwarta, most important abinda yafi baima muhimmanci shine ‘soyayyah’ da kuma a inganta masa shimfidar aurensa, tunda kullum yana samun yadda yake so dinnan kuma a shimfidarsu, batareda wani cikas din ciki ko hayaniyar yara ko kailular dake cikin shayarwa ba kuwa me zai dameshi?
Ko kuma don ba shi ake cewa “Barren Lady” ba.
Amma tana kirge da cewa aurensu ya tasarma shiga shekaru takwas bata taba ko batan wata ba, sai a wannan lokacin da period dinta ya dan yi delaying.
Itama da farko ai bata damun ba, amma banda yanzu da take neman kaiwa shekaru talatin, don data kokantawa Ammi damuwarta kan matsalar rashin haihuwar nan a can baya Ammi cewa tayi wai “lokaci ne”.
Ta kuma kara da cewa komai data gani a duniyar nan yanada lokacinsa, in Allah ya nufa. Ta cigaba da gayawa Allah kawai, amma kada tasa damuwa a ranta, ta kuma saka a ranta ba haihuwa ce kadai farinciki ko alkhairin rayuwar aure ba, zama lafiya ma cikin soyayyar miji wani abu ne, ba kuma itace kadai ke samar da zaman lafiyar aure a duniya ba, sannan ba ita ce zata kaita aljannah ba”.
Wadannan kalaman na Ammi suka sa tun daga lokacin Safiyyah ta sanyawa ranta salama, amma kwanan nan abun ya zo yana barazana ga kwanciyar hankalinta, musamman saboda gorin ‘yan uwan mijinta, da uwar mijin kanta, duk sanda ta tuna shekara takwas ba ribar aure tsakaninta da Zayyan, wanda shi zai zama sanyin idaniya a garesu, ya kara dankon soyayyar tasu, sai taji wata irin damuwa ta lullubeta.
Musamman saboda habaicin da Mama da ‘ya’yanta suke sakar mata directly and indirectly.
Ta jima tana sayen PT Strip a boye, bada saninsa ba tana gwada kanta, in taga babu komai haka zatayi kuka a toilet ta gaji ta wanke fuskarta ta fito, ta shiga harkokinta.
Ya zamanto cewa Safiyyah ko dan ciwon kai take yi ko zazzabi sai ta roki Allah yasa laulayin ciki ne. Haka zata shige toilet yin PT, amma kullum amsar daya ce “negative”.
Safiyyah ta fara tunanin ko bata gamsar da mijinta ne shiyasa ta kasa daukar ciki? Gashi ita bata yarda da wani abu wai shi maganin mata ba. A hankali abin har ya zamar mata tamkar ‘desperation’ ba tareda sanin Zayyan ba, don ba kowanne lokaci damuwar take zuwar mata ba, musamman in suna tare, sai idan ta kadaice ko tana tare da danginsa. Na yau ne kadai Allah yasa ya ritsa da dawowarsa.
Don haka Zayyan yau ya sha mamaki don bai taba ganin Safiyyah cikin wannan yanayin ba, jage jage da hawaye gashin kai a hargitse zaune dirshan a tayal din toilet. A saninsa matarsa Safiyyah macece jaruma, mai tawakkali kuma, da iya shanye damuwa komai girmanta.
Da kyar ya samu ya lallabi Safiyyah ta daina kukan amma ta bullo da sabuwar rigimar cewa dole suje asibiti a binciki lafiyarsu. Tace duka tsararrakin aurenta daga mai ‘ya’ya uku sai mai biyu. Hatta Zaitoon da Zahra da aka aurar a bayan bayanta sun haihu wannan shekarar.
Zayyan sai ya fara harzuka, ya dago da mamaki ya dubeta, yace.
“Safiyyah ban fahimce ki ba, haihuwar abin competition ta koma? Ko kuwa don ace kema kin haihu kikeson haihuwar?
Ban sanki da haka ba sam. Kada shaidan ya samu gurbi kuma. Don idan don dayan biyun wannan ne kike son zuwa asibitin, to ni ba inda zanje, sai kije su rakaki inda aka basu nasu maganin haihuwar ki karbo naki”.
Haka suka kwana a ranar baram-baram kowa zuciya a kusa, a ganin Safiyyah Zayyan bai damu bane sam da rashin haihuwarsu, saboda bashi ake yiwa habaicin yana cika masai da kashi ba.
Rashin nuna damuwar tasa akai ya kara ninka tata damuwar, don a ganinta damuwar ba tata bace ita kadai, tasu ce su duka, inda alkawari.
Haka ya jefa filo akan center carpet na dakin barcinsu yayi kwanciyarsa ya rabu da ita. Yanata sake-sake a ransa. Ko dai wani yayi musu labe ne yaji kalaman Mama Fatu shine yazo ya tseguntawa Safiyyah ta waya ya daga mata hankali?
Kalmar Mama ta ‘bakarariya’ ko shi tayi masa babu dadi.
Yana wannan tunanin ya ganta ta cikin dan hasken dim light din dakin, ta mike a hankali ta shige toilet, ta dauro alwallah ta fito, ta canza sutturar jikinta daga rigar barci zuwa hijabin sallahrta, ta shafa turaren ‘musk’ a hannayenta.
Safiyyah ta fuskanci gabas ta tada sallah.
Yana daga cikin manyan dabi’un Sophie dake burgeshi. Suke kuma kara mata matsayi a ransa. Cikin halin farin ciki ko akasinsa, bata bari shaidan ya jagoranceta ko ya rinjayeta tayi wani abu ba daidai ba. Tafi gane tayi sujjadah ta gayawa Allah kukanta.
Haka yaga ta raba dare a kan abin sallarta, shima kasa barcin yayi, yana jin tsigar jikinsa na tashi da kukanta, tana kuka tana yiwa Allah kirari, tana kambama shi cikin sujjadarta ta hanyar kururuta girman izzarsa da buwayarsa, cikin rokonsa itama ya bata haihuwa, kamar yadda yake baiwa daukacin bayinsa. Ta san ba wai ya manta da ita bane”.
Daga kwancen da yake Zayyan ya tayata amsawa a ransa da;
“Ameen, idan alkhairi ce a garemu da addininmu Safiyyah Allah ya bamu!”.
Ganin yau bata da alamar sanya hakarkarinta a katifa har goshin asubahi, balle kuma yasa ran zata bi ta kansa, yanzu tafi son samun ‘ya’ya akansa ma kenan, humm. Mata iyayenmu!
Hakan yasa ya ji kishi a ransa na ko ta haihu ‘ya’yansu zatafi so a kansa. Duk kulawar da take masa kansu zata koma. Shi kuma ta rage kulawar da take bashi, haka ya hakura yayi barcinsa ya kyaleta yana tunani mara hujja. Ya manta ko inji ne yana son hutu musamman idan bashi da service.
Washegari suna karya kumallo ya daga kai daga kurbar tea kadan ya dubeta da kulawa, sai yaga duk ta zabge a dare daya, saboda daurawa kanta damuwar da ya kira ta babu gaira babu dalili.
Yaga cewa shi dai a karan-kansa da bakinsa bai taba cewa “Sophie, meyasa baki haihu ba har yanzu? Ko sai yaushe zaki haihu min? Ko me ya hanaki haihuwa, ko ni Zayyan ina son haihuwa” ko ire-iren accusations dinnan marasa dadi makamancin wadannan da ake yiwa wadda ta samu jinkinrin haihuwa koda wasa bai taba hadashi da ita ba, to na menene zata bi ta damu kanta shima ta saka shi a damuwa rana daya?
Domin sanin kanta ne rashin walwalarta tabbas ta san dole zaiyi tasiri akan tashi walwalar.
Tana ta faman juya cokali a cikin tea ta dan dago, jin yayi clearing voice dinsa, sai suka hada ido, kuma duk sai ta bashi tausayi. Ganin ta ko kasa kurbar ruwan shayin da ya hada mata, sai juya cokali take a cikinsa. Zayyan ba tareda dogon tunani ba yace.
“Na yarda, muje asibitin a duba mu Sophie. In dai shine abinda zai baki kwanciyar hankali, na lura dake jiya ko runtsawa bakiyi ba.
Don haka on one condition zamu je gaban likita; duk abinda sakamako ya nuna, inma nine da matsala ko kece da matsala kada ki daga min hankalinki ki yi tawakkali ki karbi kaddara”.
Ai kuwa ga mamakinsa nan da nan Sophie ta ware. Ta kurbe shayin da gaggawa har tana kone bakinta. Ta furzar da ruwan zafin a gefe da sauri, yayi mata sannu. Tace “Habiby nagode, tashi mu tafi”. Yace “dole ki gode min mana Sophie, tunda kin ci ni da yaki.
Ni Zayyan ban taba fatan zuwa teburin likita wai da sunan neman haihuwa ba, because I believed time ne bai zo ba. Kuma nasan dukkunmu lafiyarmu kalau tunda kina regular period”.
Safiyyah bata saurareshi ba tuni tayi daki ta hau shiryawa.
**** **** ****



