⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 12: Chapter 12

Washegari ya shirya yayi mata sallama ya tafi Katsina, ita kuma ta yi amfani da wannan damar wajen yin azumi, ta wuni da azumin tadauwi’i a bakinta, tana tunani irin mai cin zuciya. Wai Zayyan ne ya gaya mata da bakinsa yau zai kara aure, don ya samo mata Ds daga gareshi, in ba ta yi da gaske ta yakice al’amarin daga ranta ba zai iya zauta kwakwalwarta.
Ko bayan da aka sha ruwa addu’a ta yi ta musamman a kan in tana da rabon haihuwa da Zayyan Allah ya kawo wannan rabon cikin gaggawa. Don ta tabbata bada wasa yake yi ba, da ya ce yana so zai kara aure. Dansa ko ‘yarsa ne kadai za su maye mata gurbinsa a yanzu da ya fara tunanin kawo wata macen cikin rayuwarsu.

Ta san tabbas daga wannan lokacin ta rasa previous Habiby dinta. Bazai kara dawowa irinna baya ba.
Ko da dai dama daga tafiyarsa Lagos zuwa yanzu ta san wannan ba Zayyan dinta data sani a baya bane, duk da yana kokarin wanke mata zuciya da kalamai na fatar baki, a banza man kare a wurinta.
Bayan ta yi sallar magriba ta sha ruwa, ta samu wayar Aunty Zubaina, tana dauka ko gaisawa Antin ba ta bari sun yi ba, tace,
“Safiyyah kina da masaniyar abin da ke faruwa kuwa, kuma da yardarki da amincewarki ake nema wa Zayyan auren diyar Baba Murtala?”
Sai da ta ji kirjinta ya bada dam! Bana jin maganar karin auren ba a’ah, na jin ko wa Zayyan zai aura. Amma tuni ta sa ma ranta salama don haka ta ce wa Anti Zubaina cikin kasalalliyar murya.
“Ya dai gaya min ko na amince ya kara aure? Kuma jiya-jiya ne muka yi zancen Anti”.

Anti Zubaina ta ce, “To ai an gama komai, gobe za a kai lefe da kudin aure duka. Ya dace yayi miki cikakken bayani, ni banason munafurcin maza in sun tashi fitinar karin aure.
Amma ki bar ni da shi, zan gamu da shi wallahi, ba haka ake fada wa uwargida neman aure ba”.
Kasa cewa komai Safiyyah ta yi, don yanzu ta gama gano dalilin Zayyan na share ta a tafiyarsa Lagos, wato ya yi gam da katar da ‘yar masu kudi burin mahaifiyarsa.
Baba Murtala ya damesu ya shanye Baba Bello a kudi da tarin dukiya balle Zayyan. Ko me suke dashi yau a dalilin taimakon Baba Murtala ne. Safiyyah ta kara jin tausayin kanta, me zata yi yanzu? Kuma me za ta ce a kai, banda yi musu fatan alkhairi?
Ammi kawai ta iya kira jikinta babu lakka, kuma ta kasa hawaye ko taji dama dama. Tana ajiyar zuciya ta labarta ma Ammi komai. A karshe ta ce,
“ki yi min addu’a Ammi, zuciyata tana tafarfasa, Zayyan ya shammaceni, abu ne da ban taba zato daga gareshi ba, saboda na tabbata wannan auren Zayyan zai yi shi ne don radin kansa, babu wanda ya tursasa shi ga yinsa.
Amma Ammi da a ce na haihu ko sau daya ne, ba zan taba damuwa don Zayyan ya kara aure ba”.

Tausayin ‘yar tata ya kama Ammi Hafsatu, ba tun yau ba tana sunsuno ranar faruwar hakan ga Safiyyah, duba da matsalar rashin haihuwarta da yanayin yadda mahaifiyarsa ke alakantarta, harda ita kanta Ammin.
Babu wata mu’amala ta surukuta ko girmamawa ko kulawa da ta ke samu daga Hajiya Fatu a matsayinta na wadda ta wanke ‘ya sukutum ta basu. Babu ko gaisuwar mutunci ta zuwa gida kota waya, rabonta da su hadu ma da Haj. Fatu har ta manta, amma wace ita da za ta hana su aure don su samu haihuwar da Safiyya ta kasa yi musu?
Ammi ta sauke ajiyar zuciya ta shiga lallashin diyarta. Lallashi da karfafawa irin wanda ya dace kowacce uwa ta gari ta yi wa ‘yarta.
Ta ce, “Ki kwantar da hankalinki Nana Safiyya, kishiya ba kanki farau ba, haka rashin haihuwa. Kedai ki yi zaman aure domin bautar Allah ki kyalesu, in ya so tazo ta haifi ‘ya’ya dozen.
Ubangiji Subhanahu wata’ala da kanSa, ya ce Yana jin kunyarku (matan da bai baiwa haihuwa a duniya ba).

Ki dauki karin auren nasa a matsayin kaddararsa da taki, ba a matsayin gazawarki ko kasawarki ba.
Safiyyah na yarda da tarbiyyar da muka baki, kada kiyi amfani da hakan ki muzguna wa mijinki. Ki masa uzuri sau saba’in da Allah ya ce ki yi masa. Albarkarmu na tare dake in Sha Allah ba za ki taba wulakanta a dalilin rashin haihuwa ba”.
Nasihar Ammi ta karfafe ta, ta zuba mata wani kwarin guiwa. Tun daga ranar sai ta maida komai ba komai ba, ta shiga harkokinta.
Koda Zayyan ya dawo daga Katsina bayan an gama komai na aurenshi da Azeezah sosai ya ga canji daga gare ta, ta shiga hidima da shi yadda ta saba.
Ganin haka shi kuma ya saki jikinsa ya ba ta labarin Azeezah kakaf! Da yadda al’amura suka wakana a Lagos, kai har irin hirarrakin da suka gudana tsakaninsa da Azeezah sai da ya kwashe gaya mata.
Kullum yana kwantar mata da hankali, yana kara jaddada mata alkawarin adalci da na girman matsayinta in Sha Allah bai taba canzawa a gareshi. Kowa zai auro zai auro ta ne don ta haifi Da ta bata, shi ba wata soyayya a zuciyarsa bayan tata.
Don haka Safiyyah ta kwantar da hankalinta suka ci gaba da tsare-tsaren auren shi da ita. Maimakon kayan fadar kishiya tsabar kudi ya bata masu yawa, ya ce ta yi duk abin da ta ke so da su, don ya san bata da matsalar sutura.
Ya gaya mata ko sisinsa bai yi ciwon kai ba wajen hada wa Azeezah lefe, duk Mama da Zubaidah ne suka yi masa.

Wannan ya kara tabbatarwa da Sophie yanzu Mama ta yi surukar So. Baffa ya auro mata classy suruka irin wadda ta dade tana masa buri.
**** **** ****
An saka ranar daurin auren Zayyan da Azeezah sati biyu masu zuwa, wata daya da zuwan shi Lagos. Baya kiran Azeezah a gaban Safiyyah, haka ko ita ta kira shi in Safiyyah na wuri bai amsawa.
Ranar daurin auren na matsowa fargabar Zayyan na karuwa saboda silent treatment din Safiyyah gare shi. Ko da can Safiyyah mai biyayya da yakanah ce, da kula da shi, kai dai barta da kunya da nuku-nuku a gado da kin yi masa yadda yake so, da dressing irin yadda yake son ta yi masa. Kullum Safiyyah kara samun nutsuwa take saboda nasihohin Ammi, kullum sai Ammi ta kira ta a waya ta karfafe ta, ta kuma gaya mata wani sirri cewa.
“Babban abinda ke kama miji, yasa ‘guilt’ ya baibaye shi in ya tsiri kara aure shi ne biyayya ba fandare masa ba.
Saboda the more ta yi creating distance a tsakaninsu, saboda kara aurensa, the more amaryar za ta samu damar kara shiga ransa da nesanta shi da soyayyarta, ta kuma samarwa kanta matsuguni a zuciyarsa”.
Har gobe Safiyyah tana matukar son Zayyan dinta, in ma ta ce son ya ragu ko ya tafi to ta fada ne don ta ji dadin bakinta (out of frustration). Don haka Safiyyah ta tattara kishi ta ajiye a gefe, ta kuma barwa ranta cewa ko matar Zayyan ta tare ba dai ta tsaya rigimar kishi da ita ba.

In ma an karfafe shi ya yi auren ne don a muzguna mata, ko a nuna mata iyakarta ta rashin haihuwa, insha Allah za ta rungume ‘ya’yan Zayyan kamar ita ta haife su.
Soyayyar nan tata da Zayyan natural ce, ba abinda zai sameta da yardar ubangiji saboda wani dalili na karin aure da ba kansa farau ba.
Zayyan bai taba yi mata alkawarin ba zai kara aure ba, ya dai yi mata alkawari na soyayya da amana. Don haka yanzu da auren ya zo masa bagatatan tsakaninta da shi sai fatan alkhairi, da addu’ar ya zamo mai adalci a gare su, kamar yadda shima kullum yake fata.
Safiyyah ba ta tashi susucewa ba sai ranar da ya ce ta hada mishi kaya a jakar matafiya zai je wajen kanwarta a Lagos. Daurin aure saura kwana uku lokacin.
Ganin ya dau sabon aski ya shigo da sababbin dinkuna na alfarma, ya ce ta zuba masa a jaka. Cikin dauriya duk ta ke yin yadda ya ce, da ta zo daukar masa turaren ‘Ultraviolet’ ne sai zuciyarta ta idasa tsinkewa.
Zayyan bai lura da cewa jikinta ya hau rawa sannan idanunta sun cicciko da kwalla ba, domin ta bashi baya tana zuge jakar, bayan ta cusa turaren, ya ce.
“Am, Sophie kinga na manta in gaya miki gobe Mama ta ce za’a zo a yi kafin Azeezah don bayan daurin aure da kwana uku Azeezah za ta tare”.

To dama gidan tun sanda aka gina shi tagwayen gidaje ya yi wa kansa a matsayin (semi-detached bungalow) tun sanda aka gina Sunset Estate.
Don haka barin hagu ya bai wa iyayen Azeezah su yi mata kafi.
Ai kuwa washegari an ga barin dukiya a gidan Arch. Zayyan Bello Rafindadi. Wasu ubansu-ubansu royal furnitures kawai ake saukewa daga company a gidan. Su Yaya Zubaida an kasa tsaye an kasa zaune abin nema ya samu wai matar dan sanda ta haifi barawo, kai ka ce diyar gwamna Zayyan Bello ya auro, saboda dukiyar da aka tamfatsa a sassan Azeezah.
A can Lagos an fara biki na alfarma, haka a Katsina Mama ta yi gayya ta fita tsara an soma biki na bugawa a “Ovasion”, za a daura auren Arch. Zayyan da Azeezah Murtala washegari asabar a gidan kakanninta da ke Masari a Katsina.
Bayan ya dawo daga Lagos duk jikinsa ba lakka, saboda sabon nauyin iyalin da ya tabbata zai dada hawa kansa. Washegarin ranar ne daurin aure a Masari zai je Katsina ne inda daga can zasu dunguma zuwa main house dinsu Azeezah. Inda acan za’a daura auren. Safiyyah tun asubah tana kitchen sabida shi yana barcin gajiya tun dawowarsa, kafin ya tashi barci ta shirya musu karin kumallo mai rai da motsi data san yanaso; sinasir da waina da miyar ganyen alayyahu, Ugu leaf da hanta.
Suka karya kumallo a dining kafin ya shiga wanka tana ta faman tsokanarsa wai ya fara kyallin goshi, tun ba’a je dakin amarya ba. Harararta Zayyan yayi ya shige toilet.

Wajen wankan ma ita ta surka masa ruwan wankan, ta zuba turaren wanka mai dadin kamshi na desire dunhill a cikin ruwan, sannan ta ajiye masa bath gel dinsa na Cien a gefe da farin tawul, ta juya za ta ja masa kofar, sai ya riko hannunta cikin marairata da karaya.
“Sophie, karasa ladanki mana ki cuda min baya… na rantse ba ni da karfi yau”.
Dariya ta yi ta ce a ranta, za ka ji karfin sai zuwa dare inta iso”.
Wani abu kamar daci-daci a makogaronta ya taso mata, wani tukuki ya turnuke zuciyarta, don haka ta yi saurin janye hannunta daga cikin nasa ta fice ta rufo masa kofar, tana neman hadiye abin nan da ya yi mata tsaye a makogaro, amma ta kasa.
Tana bude baki don yin magana kuma ta san fashewa za ta yi da kuka, ko harshenta ya lankwashe ko ya karye gabadaya, don haka yi masa shirun ta fice da gudu-gudu shi ne mafi alkhairi a gareta.
Ya yi wankansa tsaf, ba karsashi ko na kwabo a jikinsa, musamman saboda shirun da Safiyyah ta yi masa. Ta kuma yi tafiyarta daga toilet din ko kallonsa bata kara yi ba.
Yana shiryawa a dakinsa cikin wata sabuwar bugaggiyar shadda ‘yar ubansu wadda Baba Murtala ya dinka masa don fitar daurin aure.
Yana so ya kira Sophie ta daura masa links na hannun rigarshi da maballin wuyansa yadda ta saba, ya ji nauyin hakan ya kyale ta. Ko ba komai ta yi masa kokarin da ‘psyche’ dinsa bai taba bashi ba.
Da ya kammala shiryawa ya same ta a dakinta tana faman fiddo kaya daga wardrove tana shiryawa duk don ta maida kanta busy, ta hana kanta zama shiru balle wani mugun tunanin ya sarke ta. Daga bakin kofa ya tsaya hannayensa biyu zube cikin aljihu, ya yi kokarin su hada ido, amma Safiyya ta ki. Ta cigaba da ninke kaya.

Ba ya son ya taba jikinta kada ya jangwalo rauninta, don haka ya yi magana daga inda yake tsaye.
“Mun wuce Masari daurin aure sai wajen dare kuma in taron mata ya watse zan dawo Sophie”.
Safiyyah ta hadiye miyon bakinta ta ce.
“Ällah ya sa a daura a sa’a, Allah ya sa abokiyar arzikinmu ce, Allah ya bada zuri’a mai albarka da ake nema..…”
Wadannan kalaman na karshe ta karasa su ne cikin rawar muryar da ba ta so rauni ya fito a cikinta ba.
Shi kansa ji ya yi ya kasa daurewa, don haka ya shigo cikin dakin sosai ya karasa ya rungume ta, ya ce.
“Ina rokon Allah ya sa zuri’ar nan ta fara samuwa daga gare ki Sophie, ina kara rokonSa ya fidda ni kunyarki wajen adalci.
Ina jaddada rokona gare shi da Ya ba ni zuri’ar nan tare da ke komai rashin yawanta.
Kada Allah ya nuna min ranar da zan fifita wata a kanki, a dalilin haihuwa…”

Su duka jikinsu da muryoyinsu rawa suke yi, Safiyyah na amsawa da “ameen”.
“Allah ya fara kwantar da babyna a nan…” (ya sanya hannu kasan mararta) kafin kowacce mace ta samu wannan babbar alfarmar……”
Fatar bakin Safiyyah na rawa ta kara amsawa da “ameen”.
Da tsakanin mutuwar jiki Zayyan ya bar dakin Sophie, yayin da Safiyyah ta yi zaune dirshan a gefen gadonta ta sanya fuskarta cikin tafukanta rike da singlet dinshi da ya cire, ta cukuikuiye fuskarta a cikin singiletin, amma ba kuka ta ke yi ba.
Karfe hudu na yammacin ranar waliyyai suka daura auren Arch. Zayyan Bello Rafindadi da Azeezah Murtala Babangida, bisa sadaki na burga, wanda Mama ta bayar na wara-waran zinare manya guda uku.
Daga nan aka wuce reception na maza, already amarya tana Abuja tun jiya gidan mahaifinta da ke Katampe.
Sai yamma lis ya dawo Abuja, kuma ko da ya sauka a Abuja bai shiga gidansa ba Park din cikin Estate din ya nufa ya tsaya a jikin ‘railer’ yana tunani, daga baya ya wuce gidan amininsa Habibu Nahuce, daidai lokacin da aka kawo amarya Azizah dakinta.

Abin kunya har da Yaya Zubaida aka yi shimfidar gadon amarya, su Zaitoon kuwa sai yada ma Safiyyah habaici ake ana cewa, uwargida sai kin yi hakuri fah, ah toh Azeezah ‘yar babban gida ce shi ya sa za ki ga komai nata daban.
Kada ki ga furnitures ubansu ‘yan Dubai ki dauka Yaya Baffa ne ya saya mata. Kin san da uba ake ado ba da miji ba”.
Kasancewar Aunty Dije ta zo ma Safiyyah dannar kirji a ranar, ta kuma ji me suka ce, sai ta tashi zaune daga kishingidarta, a ranta tace lallai Zahra da Zaitoon basu da kunya, sai ta ce musu,
“Kun manta kuma wani lokacin abin an ce abin fini uba in fiki miji ne? Allah na tuba Safiyyah tun asalinta ba ta son tarkace ita, dan English parlon nan nata ya ishe ta, tunda ba ‘yar sarki ba ce, ba ‘yar gwamna ko shugaban kasa ba, a’a ita diyar magada Annabawa ce, wadanda duniya bata gabansu”.
Zaitoon ta shaka sosai sai ta bar dakin.
Aunty Dije ta ce, “Marasa kunyar yara kawai, Allah ya hada ku da dangin miji masu irin halinku”.

Sannan ta kara ja ma Sophie kunne a kan kada ta sake ta tanka su ko me za su ce mata, giyar farin ciki ke dibarsu. To Allah na kowa ne, kuma zai iya mata abin da ta kasa.
Sai da ‘yan kawo amarya suka ware Aunty Dije ta kada kan su Sabah su ma suka wuce guest house din da aka yi musu masauki a nan cikin Sunset Estate. Suka yi sallama da ita a kan cewa da safe ba za su shigo ba, sammako za su yi su juya gida abinsu.
To shi ne fa Zayyan bai shigo gidansa ba sai can dare kamar yadda ya faru a farkon littafin, fatansa shi ne Allah ya sa wannan auren da yayi bai zamo (biggest mistake of his life) ba, wato bai zamo babban kuskuren sa a rayuwa ba, maimakon nemo mafita ga matsalarsu shi da Safiyyah.

Kiran sallar asubahi ne ya dawo da shi daga ‘down memory lane’ din da ya tafi, wanda ya kunshi gwagwarmayar kuruciyarsu data soyayyarsu data rayuwar aurensu shi da Safiyyah. Da kuma ranar yau, wato ranar da “Azeezah Murtala” ta tare a gidansa.
Azeezah ta iso cikin rayuwarsu da fatansa na zata zamo maslaha ga matsalolinsu.
Da ya dawo kuma ya dade zaune cikin motarsa saida ya tabbatar ‘yan kawo amarya sun watse, kuma maimakon ya tafi dakin uwargida yayi mata sallama ya wuce gun amarya sai ya zabi ya wuce masterbedroom dinsa, yayi tunanin rayuwar sa da Safiyyah tun farkon fari, because he lacked all the courage na dosar inda Safiyyah take a wannan daren.
Zayyan ya kwanta ne kawai rigingine a gadonsa yake wannan dogon tunanin. Don yanzu da Azeezah ta zama mallakinsa, bakin alkalami ya riga ya bushe sai yake jin kamar yayi kuskure, kuma kamar bai kyautawa Safiyyah ba. Kamar wannan shine kuskure mafi girma daya aikatawa rayuwarsa, maimakon kawo maslaha.

Mu duka ni da ku masu karatu dai mun san cewa “not all that glitters is gold”. Azeezah nada duk abinda yake so a diya mace, while soyayyarsa naga Safiyyah diyar Malamai, amma kuma muna sane da cewa Zayyan ya manta cewa babu yadda za’a yi ka samu rayuwa dari bisa dari daidai da ra’ayinka da burinka, dole kowa yana da irin nasa nakasun a wurin abokin rayuwarsa.
A rayuwa, sau tari idan Allah ya baka wannan zai iya hana maka wancan kamar yadda Safiyyah ta kasance, duk dan Adam tara yake bai cika goma ba, ba duk abinda mukeso daga abokan rayuwarmu muke samu dari bisa dari daga garesu ba.
Duk da haka Zayyan yana da kyakkyawan fatan cewa ‘Azeezah Murtala’, will meet all his dreams in a woman, his expectations and beyond.

Mu biyo Arch. Zayyan da matansa Safiyyah da Azeezah a littafi na uku. Yanzu ne zamu fara labarin Zayyan da Safiyyah. 1&2 shimfida ne.
SUMAYYAH ABDULKADIR -Takori
07030137870
(WHTSP only)
01/04/2025

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *