⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 2: Chapter 2

Zayyan da Safiyyah ne zaune a gaban teburin Dr. Muwadda a ABUTH. Duk wata babbar lalura ta rashin lafiya kota ‘medical check-up’ iyalin Baba Bello sun fi ganewa zuwa ABUTH, sun fi yarda da kwarewarsu. Da wuya ka ga sun canza asibiti sai ‘on emergency case’. Don haka takanas Zaria suka taho daga Abuja, bayan samun appointment na ganin kwararriyar likitar mata Dr. Muwadda Abdullahi Shinkafi.
Likitar ta yi ma Safiyyah duk wani bincike da bature ya tanada ta hanyar tasatasai (test-test), sannan ta koma kan Zayyan shima ta bincike lafiyarsa tsaf. Kwana uku a jere suna zarya a asibitin ana gwaje-gwaje da aune-aune, inda sukayi masauki a Zaria Guest Inn, kafin fitowar sakamakonsu.

Ranar da aka tattaro sakamakon suna waiting room na ganin likitar, kafin a kirasu ofishin likita Safiyyah saida ta zaga bayi ya kai sau uku, saboda fargabar abinda likiciyar zata ce mata.
Shikuwa Zayyan ko a jikinsa, don ya riga ya sakawa ransa haihuwa ba ita kadai ce farin ciki tsakanin shi da Sophie ba.
Akwai tsantsar soyayya mai haddasa farin cikin da walwala, wadda ta riga ta haifar da fahimtar juna mai girma a rayuwar aurensu.
To na meye zai damu kansa kan abinda Allah bai ga damar basu ba???

Sakamako dai ya nuna cewa Safiyyah ce mai matsala bashi ba, tanada lalurar PCOS (polycystic ovary syndrome). Likita Shinkafi, ta kira matsalar Safiyyah da suna ‘unexplained infertility’ na sanadin matsalar PCOS.
Ta dorata kan treatments masu kyau na masu lalurar pcos, da magunguna masu tsada wadanda zasu iya taimaka mata tayi conceiving idan tanada rabo.
Tun a hanyarsu ta dawowa Abuja Safiyyah ke fakar idonsa tana dauke kananan hawaye a idonta, alhalin yana tuki. Ya saka musu karatun Al’qurani a cikin motar cikin qira’ar Salah Bukhatir, a cikin karatun ne Sheikh Bukhatir yazo ayar da take addu’ar samun zuri’a dayyibah cikin Suratul Furqan. Ya karanto ayar nan cikin qira’arsa ta hafsu mai dadin sauraro;
“Wallazeena yaquluna Rabbana hablana min azwajina wa zurriyyatana qurrata a’ayunin wa ja’alna lil muttaqeena imaama…”.
Sai kukan Sophie ya kasa boyuwa a wannan gabar, domin ta kasa cotrolling dinsa, ta soma sheshshekarsa a fili tana bin Ayar tana maimaitawa cikin kuka.
Kuka sosai Safiyyah ke yiwa Zayyan a cikin motar har saida kukannata ya soma rikitashi, yace cikin rawar murya.
“Safiyyah kina so in zubar damu a motar nan ko?”

Ta girgiza kai, ita tafi kowa sanin yadda Zayyan baya son kukanta don fitar dashi yake a hayyacinsa. Amma yau dole tayi kuka a gabansa. Ashe-ashe itace mai matsalar! Kukan nata ya karu, fiyeda na baya. Ba shiri Zayyan ya faka motar a gefen titi.
“Sophie, so kike ki daga min hankali akan abinda banida ikon baki shi ko? So kike in dorawa kaina damuwar gazawata da kasawata ga baki farin cikin da kike so?”
Safiyyah ta girgiza kai tana share wasu hawayen da suka kawo mata caffa da gefen gyalenta, tace “ba haka bane Habiby, inaso ne ko yaya ne nima in ga dan kaina, wanda zai zama fruit to our love. Nima in zama UWA inyi experiencing abinda ake ji a motherhood.
Shekaruna kullum gaba suke yi, har gashi ina neman dosar shekaru talatin banida Da ko daya. Kuruciyarmu kullum karewa take yi, ba baya take komawa ba.
In ban haihu yanzu ba sai yaushe Habiby? Sai na kai menopause? Banida sanyin idaniyar da kowa ke alfahari dashi wato DA. Banida bakin da zan kira kaina Maman wane ko Maman wance.
Kaima da kanka Zayyan watarana zaka tsaneni, tunda na kasa maida kai UBA. Ta hanyar ajiye maka abinda kowanne uba ke fatan samu”.
Karo na farko da yaji Safiyyah ta kirashi da suna ZAYYAN wanda ya nuna tashin hankalinta a fili yake, bata ma san ta fada ba, a kwanakinnan ya fahimci Safiyyah ta zama desperate ga son haihuwa kadai.
Zayyan ya rungumo Safiyyah sosai a jikinsa, ya ma manta a kan hanya suke, ya sumbaci saman goshinta zuwa karan hancinta, ya ja birki yayi togaciya a lips dinta, inda yayi mata kykkyawar sumba mai zurfi. Yace “Sophie ni ba abinda zaisa na tsaneki, haba Safiyyah, haba Sophie na, nifa Safiyyah na aura ita kadai bada tunanin zata haihu min ko bazata haihumin ba.

Ta yaya kuma don baki haihu ba sai in tsaneki akan lalura, bayan daidai gwargwado nasan cewa Allah ke bada haihuwar nan?
Kada ki kara wannan shirmen tunanin bana so, abinda ni Zayyan na yarda dashi shine haihuwa ta Allah ce, da ya bamu da bai bamu ba you will forever remain my alter ego!”
Da haka yayi ta lallashinta har ya samu tayi shiru tana ajiyar zuciya a kan kirjinsa. Can kuma tace “Habiby, babbar damuwata itace PCOS dinnan yanada magani ne ko a’ah, ni da ace ma tace unexplained infertility kadai ne, sai inga kamar zan fi samun sauki a raina fiye da ace mun PCOS gareni. Ni ban gamsu da binciken wannan likiciyar ba, don a tarihin zuri’ar gidanmu kaf! Babu mai PCOS”.

Zayyan yace da karfafawa “to hell with PCOS and whatever! Ni Zayyan Sophie kawai nake so, haihuwa in Allah ya kawo ina maraba da ita, haka in bai bamu ba, muna cikin godiyarsa as well.
Ya hada hannuwansa biyu yana rokonta. “Chapter closed, don Allah Sophie. Bana son kara jin zancen haihuwa a bakinki daga yau. Kuma kada ki kara kai mu gaban Likita”.
Amma ina! Safiyyah bata hakura ba saida tayi bincike ta hanyar tuntubar wadanda ta sani akan kwararriyar likiciyar matan da tafi kowa kwarewa a Arewa, nan aka bata labarin Dr. Hadiza Shehu Galadanci, ta jihar Kano.
Ta samu labarin Dr. Galadanci ne ta hanyar Anti Dije, ta kudire in ta samu Zayyan ya kaita Zaria bikin Ni’iman Anti Dije sai ta biya Kano ta ga Dr. Galadanci tunda kwana uku zata yi a Zaria. Watakila Dr. Shinkafi bata san aikinta ba, ita a zuri’ar su Ammi ba mai PCOS, kuma ance shi mostly gado akeyi.

Hakan ce ta faru. Lokacin bikin diyar Anti Dije Safiyyah ta samu Zayyan ya kaita har Zaria, daga nan sukayi sallama shikuma ya wuce Katsina gun su Mama, a can zaiyi hutun karshen mako, ita kuma ta ci biki a cikin ‘yan uwanta, duk da bata da walwala, ga kannenta duka sun zo suma daga Dandume.
Biki yayi biki gida ya cika da dangi da abokan arzikin su Anti Dije, ita da su Sabah daki daya suka kwana, washegarin saukarta a Zaria Safiyyah sai ta zare jiki ta tafi Kano ita kadai ba tareda Zayyan ko wani nata ya sani ba, ta hau motar Kanoline daga Zaria, daga nan ta nufi asibitin Standard da Anti Dije ta bata labarin a can aka yi mata maganin barin ciki data yi ta yi shekarun baya .
Da tambaya da taimakon wayewar kanta sai ga Safiyyah akan layin mata masu son ganin Dr. Galadanci.
Bata sha wahalar samun asibitin Standard ba, saboda babban asibitin kudine da yayi kaurin suna ga matan Kano.

Duk da Sophie bata taba zuwa Kano ba sai wannan karon. Hakan bai sa ta rikice ba. Mai Keke Napep ta dauka drop tace ya kaita Standard na Tarauni. Shikuma da yake ya riga yasan asibitin nan da nan ya kaita ya zabga mata kudi.
Safiyyah ta bude file ta biya duk abinda aka cajeta na ganin Prof. Dr. Galadanchi, kasancewar Safiyyah sammako tayi bana wasa ba, daga Zaria zuwa Kano, yasa karfe goma na safe ma tana cikin garin Kano. Aka dorata akan layin da mata uku ne kacal a gabanta.
Ta samu kujera ta zauna a waiting lounge na ganin likiciyar, bata dade da zama ba wata farar mata da ba zata fice tsararta ba itama tazo ta zauna a kusa da ita, bayan tayi wa Safiyyah sallama. Sai zuba kamshin Humra matar take.
Suna nan zaune matar na amsa waya lokaci-lokaci, can kuma ta jefa wayar a kyakkyawar Jakarta, cike da shishshigi ta dubi Sophie, don taga kalar hutu sosai a jikinta itama, ita kuma dama da irin kalar wadanda take kawance kenan, sai ta hau jan Sophie da hira kadan-kadan babu alamu na bakunta, ko irin yau ta fara ganinta dinnan.
“Baiwar Allah sannu fah. Na ce sannu fah. Halan kema matsalar rashin haihuwa ce ta kawo ki ganin Dr. Galadanchi?”
Safiyyah sai da taji gabanta ya fadi, matar tayi murmushi ganin irin kallon da Sophie tayi mata na mamaki, sai tace,

“yo meye abin mamaki don na canki matsalarki? Ai daidakun mata ne ne da sukazo Standard da ba matsalar data kawo su kenan ba, musamman masu fama da lalurar (PCOS)”.
Sophie ta bita da kallo kawai, don bata ma san menene ‘PCOS’ din ba ita har yau, bata taba jinsa ba, sai a bakin Dr. Muwadda Shinkafi. Ta ce a ranta,
“wasu matan dai Allah ya zuba musu surutu da shiga sharo ba shanu!”.
Matar bata san tunanin da Sophie ke yi a kanta ba, ta cigaba da cewa.
“Alhalin basu san cewa wahalar da kansu kawai suke yi a banza ba. Ni dinnan da kike gani wane kalar asibitine banje neman haihuwa ba, kasashen duniya manya da kanana babu inda bamu taka don neman haihuwa ba nida maigida na.
Mun zubar da dukiya da lokacinmu kamar me a yawon asibiti, duk a banza.

A karshe dole nabi hanyar da ta bulle dani, yanzu haka yara na biyu. Wannan zuwan kuwa na zo ne likita ta rufe min bakin mahaifa in samu in huta da haihuwar haka ko na shekara biyu ne, yarana kuma su kara girma”.
Safiyyah sakin baki tayi tana kallon matar, wadda ta laqawa suna “fadi ba’a tambayeki ba”. Hankalinta ya dan fara daukuwa ga abinda matar take labarta mata, amma bata gane zaurancen hanyar da take nufi ta bi, wadda ta bulle da ita din ba.
Zata so taji wannan kowacce irin hanya ce, da har haihuwar tazo ta isheta tana neman dakatarwa, ko itama ta gwada, ko Allah zai sa ta dace.
Safiyyah sai ta saki jiki da matar nan wadda tace sunanta Ammara, nan suka shiga hirar haihuwa, kamar sun dade da sanin juna, abinki da irin ka gamu da mai irin ciwonka, wanda ya rigaka samun waraka.
Ammara tace “shekaruna ashirin da aure kafin na samu haihuwar yaran da nake dasu yanzu. Kema kinsan mun sha damuwa nida maigidan”.
Safiyyah kuma tace “ita kuma shekara takwas kenan da aure, ko bari bata taba yi ba”. Sai hira ta kara mikawa tsakaninsu akan hakan.

Ammara tace “haka kawai naji kin kwanta min a rai, gaki kyakkyawa ga kuruciya ga hankali, ga hutu, banda haka banida sakewa da bakin fuska sam.
Naga damuwa baro-baro a tare dake, haka kawai yarinyar ki dake zaki bar ciwon damuwa ya kamaki a banza saboda haihuwar da samunta ruwan sha yafi ta saukin sha.
‘Yar uwa ki rabu da wani yawon asibiti ana cin kudinki a banza, kibi hanyar da zata bulle dake kawai.
Rayuwar nan saida dan kaucewa sannan ake ganin daidai”.

Ta kara saka Safiyyah a duhu, har ta kai da tambayarta “dan kaucewa kamar yaya shin? In ji dai ba kauce hanya ta addini ba?”
Ammara tace “kusan hakane, amma ba sosai ba, zauna nan ‘yar uwa kiyita walagigin bin likitoci suna jagwalgwala miki mahaifa suna cika ki da surutan wofi, kuma basu da maganin da zasu baki ki haihun”.
Nan ta bude wayarta ta nuna mata hotonta tare da maigidanta da kyawawan yaransu maza biyu kanana kamar haihuwar kwanika, nan ta kara brainwashing Safiyyah wadda a lokacin nan ba abinda ta dauka a matsayin farin ciki da kwanciyar hankalin dan adam sama da ‘ya’ya.
Haka Ammara tayi ta kwance kan Sophie, tana kara zurmata ga bin irin hanyar data bi ta samu haihuwa. Wadda har zuwa lokacin ta ki fitowa fili ta fadeta sai indirectly take maganar.
Allah sarki Sophie, ita da kanta bata san ta zama desperate ga son haihuwa ba sai yau. Ta yadda har ta dan rasa kyakkyawan tunaninta ta kuma kasa zurfafashi, tarbiyyar shekaru kusan 28 da ilmin addini da mahaifinta Malam ya bata basu sa ta yi tunanin meye ita wannan hanyar da ake ta muku-muku da ita ba’a fito da ita fili an gaya mata ba?

Haka ilmin bokonta duk bai yi amfani a wannan lokacin ba. Biyan bukata kawai take nema.
Ammara tayi nasarar yiwa Sophie famfo mai yawa a wannan danzaman nasu, har take ce mata ta rabu da zancen kawai na mijinta (Zayyan) da yake cewa shi bai damu ba, tace zance ne kawai na mazan da ke son kwanciyar hankalin matansu, karya yake yi yace wai bai damu da haihuwa ba karya ne, maza sun fi mata son ‘ya’ya.
Ta kara jefa Sophie a tagumi da damuwa mai tsanani. Tace “da yawan alfarmomin da take samu yanzu a wurin mijinta (wanda babban dan siyasa ne a jihar Kano) a baya data kasa haihuwa bata samesu ko guda ba”.
Tace mata “saboda matsalar rashin haihuwa taga bala’in dangin miji kala-kala, dana uban miji, don mahaifiyarsa ta jima da rasuwa.
Tace bata samu daidaito da martaba a idon su ba sai bayan data yi musu haihuwar fari, Da namiji, tace uban mijinta ya kafa mata karan tsana, har ya taba yin umarnin da aka saketa saki daya, tace da Safiyyah “a karshe dana ga ba sarki sai Allah sai na bazama, na hada da (dan kaucewa) sannan na samu biyan bukata.

Wadda a halin yanzu ta sayomin kwanciyar hankali a gidana, da zama lafiya da miji na da ubansa da ‘yan uwansa.
Nice tauraruwarsu, tunda na aje masu ‘ya’ya kuma maza”.
Safiyyah wadda a cikin kowanne harafi na labarin da Ammara ke bata soyayyarta da da burinta da haihuwa na karuwa (to an extent), haka tsoron ta da rashin samunta shima yana ta kara ninkuwa. Har taji a ranta ko dai itama ta bi hanyar data bulle da Ammaran, komai tsananinta?
Wadda har yanzu dai bata kai ga yi mata bayaninta baro-baro ba, aka kira Safiyyah ganin likita, Ammara tace zata jirata ta fito itama ta shiga ta fito, sai su karasa maganar.
**** **** ****

Safiyyah a teburin Dr. Galadanci. Bayan ta gaya mata matsalarta na cewa shekarun ta 8 da aure babu haihuwa babu alamarta, likitar tayi mata ‘yan tambayoyi na cewa ko ta taba ganin likita akan matsalar? Ta ce eh, sun je ABUTH da mijinta ba jimawa sun ga gynaecologist, sai Dr Galadanci ta nemi ganin result din ABUTH din.
Sakamakon Safiyyah na ABUTH shi likitar ta karba ta fara budewa, sai taga cewa ba wani banbanci da duka gwajegwajen da itama zatayi mata. Duk da haka Dr. Galadanchi tayi nata binciken yadda ya kamata ta kuma ce Safiyyah ta koma reception ta dan jira fitowar sakamako.
Wannan gap din na jiran sakamako ya baiwa Ammara da Safiyyah damar sake hadewa a waiting lounge suka dora daga inda suka tsaya kafin sakamakon Safiyyah ya kammala.
Safiyyah ta kasa maida kwadayinta kan haihuwa da labarin Ammara, har tace da ita don Allah ta gaya mata kowacce irin hanya ce hanyar data bi ta samu haihuwa, Ammara tace “da dan wuya fa, amma in har kin yarda yafi komai sauki, tunda dai ba a garinnan na Kano kike ba zuwa kikayi kuma a yau zaki koma inda kike, mafi kyau shine a yau muje na raka ki, da zafi-zafi akan bugi karfe ‘yar uwa, daga can zaki samu motar Zaria tunda kan titin Zaria ne kauyen yake dama, ba sai kin dawo ta Kano ba zaki samu mota daga can har Zaria. Tafiyar mintuna talatin ce kacal daga Kano zuwa kauyen na Daka-Tsalle.

“Kauye kuma?” Safiyyah ta tambayi Ammara, ta ce “Eh a can ne malamin yake. Koyaushe aka je kuma ana samun shi saidai layi”. A can kasan ran Sophie taji dan tsoro, ta ji fargaba da darsuwar wani abu, saboda dai ta fahimci komai yanzu, wato ta hanyar bin malamai ake samun haihuwa. Amma data tuno gore-goren Mama Fatu da ‘ya’yanta, ta kuma tuna cewa ‘ya’ya fa zata samu itama kamar kowa, sannan wadanda su kadai ne zasu dorar da soyayyarta da Zayyan dinta, da kara mata matsayi a zuciyarsa data mahaifiyarsa ta daina kyararta, kuma sune kadai (‘ya’yan) zasu tsaya tare tare da ita a ranar da kowa ya gujeta ko ya juya mata baya ko ranar da bata da karfi ko ta tsufa, amfanin haihuwa da ‘ya’ya yanada yawan da bazai kidayu ba, sune zasu kula da ita idan bata da lafiya, sune….sune…sune komai na uwarsu kamar yadda suka zama sanyin idaniya ga Ammi, aminanta abokan shawararta, itada Sabah, Rayyah da Rayha.

Amfanin haihuwa yanada yawan da bazai lissafu ba, kuma damuwar rashin ta yana da girman da zaisa ka gane dalilin halin yanayin dokantuwa da desperation din da ita Safiyyah ta samu kanta a ciki.
Har sai ranar daya faru gareka, wato ranar daka budi ido shekarunka kusan goma da aure babu ko barin ciki balle batan wata a tare da kai sannan zaka gane irin yanayin data ke ciki.
Sakamakon binciken Dr. Galadanchi dai ya nuna kusan abu daya dai dana Dr. Muwadda Shinkafi ta ABUTH. Bakinsu yazo daya cewa; polycystic ovary syndrome (pcos) shi ya hana Safiyya ovulating.
Fasihiyar Likitar tace “amma ki kwantar da hankalinki ke da mijinki duk kuna da kwan haihuwa, nashi kwan lafiya kalau yake. Amma naki kwan baida kwaliti (inganci) a dalilin cutar ‘polycystic ovary syndrome’.
PCOS cuta ce wadda ‘cyst’ wato ‘maruru’ yake fitowa a cikin ‘ovary’ din mace (wajen kwan haihuwa) wanda yake hana mace ‘ovulation’ har hakan ya haifar da rashin haihuwa. Akwai mata da yawa dake fama da lalurar pcos wadanda basu san sunada shi ba, haka akwai da yawa da alamun pcos ko daya baya nunawa a jikinsu, misali daga cikin alamominsa akwai fitowar gashi a kirji kona kasan fuska da sauransu.

Kinada pcos wanda alamominsa basu nuna a jikinki ba. Kuma babu alamun cewa naki na gado ne. Pcos an fi gadonsa, amma akwai wadanda keda shi ba tareda sun gada ba. Ana kuma iya maganceshi a hankali.
Ta taimaka mata da shawarwarin da suka kamata ta bata, ta rubuta mata magunguna masu kyau da tsada da zasu taimaka mata ta dauki ciki da taimakon Ubangiji dana treatment data dorata akai. Ta kuma bata lambar wayarta don su dinga communicating kai tsaye ta waya ba sai tazo ba, akan duk wani cigaba da aka samu ko akasinsa, tace ta yarje mata kiranta kai tsaye.

Dr. Galadanchi tace ita tana ganin matsaloli na pcos iri-iri daga mata wanda ke hana su haihuwa. Tace “a yanzu dai babu likitan da zai ce miki ga hakikanin lokacin da zaki iya samun haihuwa sai dace, maigidanki na bibiyi nashi results din daga binciken ABUTH ya nuna lafiyarshi kalau, don haka kada ki fidda rai, da taimakon Allah zaki iya haihuwa a sanda Allah ya nufa with treatment, ki dage da shan magungunan nan dana rubuta miki”.
Wannan bayani ya kara jefa Safiyyah cikin damuwa maimakon ya sanyaya mata, har fiyeda damuwar da result din ABUTH ya saka ta. Wannan ya sa ta kara amanna da maganganun kawarta ta Standard, wato Ammara, tun kafin ta baro gaban teburin likitar.
Na cewa ba abinda likitoci zasu iya kullawa wanda baya haihuwa, sai dai su saka ka kayi ta asarar kudinka wajen sayen kwayoyin banza, da surutun wofi mara tabbas wadanda bazasu taimaka maka da komai ba.

A iya hange da tsinkayen Sophie na lokacin sun amince ta yarda da shawarar wannan matar kawai, in dai hakanne kadai hanyar da zata samar da haihuwa gareta da gaggawa, akwai alamun gaskiya sosai a cikin maganganunta, saboda babu alamun karya ko damfara a tare da ita, ko wani alfanu takeson samu daga gareta, face taimako da haduwar jini, don da ganin ta tafi karfin neman komai a wajen wani.
Allah shaidarta ne akan cewa tayi addu’a kuma tana kan yi, ta sha duk wasu tsadaddun magungunan da Dr. Shinkafi ta rubuta mata na tsayin lokaci, wadanda ta duba ta ga duk kusan irin wadanda Dr. Galadanci ta rubuta mata yanzu ne ba wani banbanci mai yawa. Amma Allah bai sa ta dace ba. Watakila mafitar kadai itace wannan da Ammara ta kawo.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *