Chapter 3: Chapter 3
Watakila Allah ya nufeta da zuwa Standard Hospital ne yau don ta samu mai taimaka mata, don haka bari kawai tayi kundumbala ta bi shawarar Ammara, wannan dogon bayanin na likitoci ya isheta, bata ko son sake jinsa.
Tana wannan tunanin sai ga Ammara dinma ta fito itama daga ofishin likitar, take gayawa Safiyyah cikin far’a,
“an daure min bakin mahaifa (IUCD insertion), muna iya tafiya yanzu”.
Suka fito tare, Ammara ta bude motarta wata kankanuwar (Peageout 507). Ta bude ta shiga ta kuma mika hannu ta budewa Safiyyah kofar gefenta tace,
“in har kin yarda da shawarata kin kuma yarda bazan cuce ki ba, to kawai ki shigo mu wuce in kaiki Daka-Tsalle. Daga can zan saki a motar Zaria”.
Without a second thought Safiyyah ta amincewa ranta bin Ammara gidan malami. Ta kama murfin mota ta bude tashiga ta zauna ta rufe kofar.
Ammara ta fizgi motar da gudu suka harba kan titi. Suka bullo ta Tarauni suka hau kan Titin Naibawa Zaria Road, wanda titi ne da zai kai ka har garin Kura, ya kuma mike dakai babu shan kwana har Daka-Tsalle.
Suna tafe a hanya Ammara na tuki tana kara yi mata famfo irin na matan masu kudi da suka saba da harka da malaman tsubbu. Take ce mata “ta saki ranta, ta ganta kamar ace “kyat!” ta zura da gudu. Tace ai da yawa yanzu mata wayayyu sunfi ganewa zuwa wajen malaman tsubbu akan duk wasu matsaloli da suka sha musu kai ba haihuwa kadai ba, ke har rashin lafiyar da aka rasa gane kansa da gindinsa malaman kauye sunada maganinsa, hakan yafi musu sauki fiye da su dauwama cikin bakin ciki da ciwon, bacin rai da inferiority complex, irin na rashin daukar ciki da haihuwa kamar na kowacce mace, da kuma bibiyar likitocin da bazasu kulla musu komai ba sai karerayi da surutan banza.
Tace Allah na tuba duk da ana cewa zuwa wajen malaman tsubbu haramun ne, to ai Allah mai afuwa ne mai gafara, bayan bukatarka ta biya kawai sai kayi sahihin tuba, da niyyar bazaka sake aikatawa ba, ba shikenan ba?”
Safiyyah sai ta soma shakkah, ta soma tunanin anya ita a matsayinta na Safiyyah diyar Malam Usman wanda ya koyar dasu Tauheedin cewa ba’a yiwa Allah wayo, kuma ba’a tursasashi, saidai ayi ta rokonsa, anya wannan hanyar ta dace da ita?
Idan ta bulle da Ammara, itama zata bulle da ita ta samu haihuwa?
Ba duka abinda yayi wa ‘A’ ne yake yiwa ‘B’ daidai ba.
Anya ma wannan hanya ta kaucewa kamar yadda Ammara ta kirata ta arziki da Alheri ce a gareta? In Ammi da Malam da Zayyan suka ji ta taka kafafunta wajen bokaye neman haihuwa wane irin hukunci zasu yi mata? Tunda dai taji ana daga baya sai ta tuba ta shiga rudani.
Amma as a desperate and hopeful as she is da haihuwa, sai tace bari dai ta daure, in har zata samu haihuwa shi Allah Gafurun Raheemu ne.
Daidai lokacin da suka isa dan karamin kauyen, daga can nesa Ammara ta faka motar tace gangarawa zasu yi cikin gonar can dake gabansu, har su tadda waccan bukkar da suke hange daga nesa.
Haka suka dage zannuwansu sabida duwatsu suka soma taka tudu da gangare suna shiga cikin gonar.
Cikin sa’arsu basu sha wahalar samun dogon layi bama, mata biyu suka tarar akan layin, don haka suka zauna har suka gama suka fito kafin suma suka saka kai a bukkar.
Jikin Safiyyah ya soma sanyi da ta yi arba da irin abubuwan dake cikin bukkar, da babu kwana-kwana ko wani shatale-tale sun fi kama da kayan tsafi.
Babu Ayar Alqur’ani ko daya ko Gafakarsa, irin na shigifar mahaifinta, wanda shima yake amsa sunan malami kuma ake zuwa wajensa neman taimako.
Nan Qaho ne da kawunan matattun dabbobi, can korrai ne da busassun matattun tsuntsaye, da fatun namun daji babu kyan gani sai doyi suke, korayen cike da wasu bakaken abubuwa marassa kyawun gani a cikin kowacce kwarya suna motsi, wanda hakan ya baiwa bukkar smell mara dadi mai hamami da wari, daga saman bukkar kuma an sakale konannen kan Damisa, abun dai zallah kyankyami. Saida ta hadiye numfashinta.
Wani dukunkunannen mutum ne zaune a kan fatar Akuya, dan tsurut dashi kamar (Dwarf) wato (Wada).
“Ku koma ku shigo da kafar hagu, kuma kada ki kara yi mana sallama.
Tuni ai Tsimbirbira ta san da isowarki Safiyah ‘yar Usmanu da Hafsatu matar Zayyanu”. Bokan yace da Safiyyah cikin fushi.
Saura kadan Sophie ta saki fitsari a wando, ko ta taka da gudu ta koma. Ammara ta gane hakan, sai ta rike hannunta cikin karfafawa ta jata suka koma suka yi yadda yace din.
“Maraba – lale da uwargidan Zayyanu. Magajin Bello Rafindadi masu kashin arziki na gidaje har ‘ya’ya da jikokinsu.
‘Ya’ya tsakaninki da Zayyanu akwai su, saura taki kadan su riskeku.
‘Ya’Ya fal! Har sai kince sun isheki”.
Safiyyah ta kara tsurewa, jin ya ambato sunan wadanda suka haifeta da Zayyan, kuma har sana’ar gadon gidansu Zayyan din ya sani, zuwa yanzu ta fara gayawa kanta gaskiyar lamari gidan BOKA ta kawo kanta, bama na malaman Tsubbu ba, irin masu aiki da aljanu da rauhanai don gani har hanji, wadanda kullum Malam yake gaya musu ziyartarsu don neman biyan bukata halakace babba. Domin mu’amala dasu “shirka ne”.
Suka yi zaman Rakuma a gaban sa, kamar masu neman gafara. Ammara tace da shi “itama dai ba sai na fada ba na sani, tazo neman haihuwa ne itama. Allah ya taimaki Tsimbirbira a taimaka mata, saboda yadda naji dadin taimakon da aka yi min na cika alkawarina na kawo duk mai bukata.
Itama gata na kawo ta Tsimbirbira ta share mata hawaye (wa’iyazu billah). Haihuwa kawai take so, walau mace walau namiji, da gaggawa”.
Tsimbirbira ya fashe da dariya yace “tuni ai labarinta ya iso garemu da bukatarta tun kafin isowarta.
Abu daya zuwa biyu muke bukata daga gareta; jan zakara da jar kaza (fingi-fingi) da za’a hada kwanciya, sai kuma kwan haihuwarta da maniyyin mijinta. Za’a yanka bunsuru a baiwa Tsimbirbira jinin, mu zamu dauki kwan haihuwarta da kanmu, bayan kwana biyu kuma zata dawo ta kawo mana na mijinta, wanda shine mahadin da za’a hada maganin da zan bata.
Shekara bazata zagayo ba sai ta haifi ‘yan biyu maza biyu zar”.
Safiyyah was shocked and frightened yanzu kam, don ta gama amanna ta kusa fita daga addinin musuluncima gabadaya, saboda rashin tawakkalin ta da Zayyan ya jaddada mata karba da muhimmancin yinsa ga musulmi.
Kamar yaya ta bada kwan haihuwarta ta ina za’a dauke shi? Da sperm din Zayyan kuma, ko ta wace hanya hakan zata yiwu?
Don haka ta juya a firgice ta dubi Ammara da fuskar tsoro da firgici mai yawa.
Nan Ammara ta kashe kunya tayi mata bayanin da a baya bata yi mata ba dalla-dalla. Ta yi mata ‘yar rada (whisper) a kunnenta.
“Ai dama na gaya miki sai an dan kauce hanya, sannan za’a samu biyan bukata, ke zaki san yadda zakiyi ki kawo masa duk abinda ya bukata, na jikinki kuwa zaku shiga daga cikin shigifar can ne ya dauka, ta hanyar saduwa dake! Mijinki ba ganewa zaiyi ba”.
Safiyyah ido ya raina fata. Boka ya mike ya shige dan dakin wai yana jiranta, ta bishi da kallon razana da firgici mai yawa cikin kyawawan idanunta.
Ammara ta shiga convincing dinta cikin kyakkyawan lafazi cewa “is just a simple thing, bai fi ya tara dake na ‘yan mintunan da basu gaza biyar ba, kokari zaki yi kawai ki jure ki daure warin jikinsa, don kin ganshi dan tsurut dinnan amma ba karamin fitinanne bane, and you will enjoy him morethan your husband…..”.
A wannan lokacin ne Safiyyah ta samu kalmar “Innalillahi wa’inna Ilaihi Rajioun” ta fado cikin kwakwalwarta, bakinta kuma yayi maza ya kama, ya furtata a fili.
A hankali ta runtse idanunta. Nutsuwarta da tsoron Allahnta suka dawo jikinta. Taji ta tsani haihuwar ma bakidaya in dai son ta ne yau ya kawo ta ga wannan halakar.
Ta tuno tarbiyyar da dattijan iyayenta suka kare rayuwarsu a dorata a kai. Sun kuma sha gaya mata akan damuwarta na rashin haihuwa cewa babu mai baka abinda Allah bai ga damar baka ba.
A yau a bayan idon Ammi, Malam da Zayyan gashi rashin hakurinta ya kawo ta ga halaka har guda biyu; shirka da zina, zinar ma da aurenta….. yau ga inda rashin tawakkalinta, da rashin jin lallashin mijinta ya kawo ta, wai za’a yi zina da ita da aurenta…. kuma da wannan kazamin mushrikin.
Kafin Ammara ta ankara Safiyyah tayi wuf! Ta mike ta kama hanyar fita bukkar. Tana fitowa kuma sai ta taka da mugun gudu. Gudu take da gaske tun karfinta kamar mai gudu akan iska, ita kanta bata san ta iya gudu ba sai yau, domin gani take kamar Bokan zai biyota ko yasa rauhanansa sau daukota su maida masa ita kota wane hali.
Gudu take babu waiwaye har ta samu ta fita daga gonar, ta shiga ainahin cikin kauyen Daka-tsalle.
Jama’ar kauyen na kallonta sai gudu take kamar wani ya biyota, ba tareda ta san inda take jefa kafarta ba, ba kuma ta waiwaye, tana rokon Allah in mafarki ne take yi saboda damuwar rashin haihuwa yayi gaggawar farkar da ita haka daga wannan mummunan mafarkin.
Gudun neman tsira, nadama da ceton Imani Safiyyah ke yi, wanda yafi kama da gudun famfalaki, har ta hau kan babban titin kauyen, ba tare data sani ba. Bata lura ba wata mota kirar Honda ta taho da gudun gaske duk kokarinta na kaucema Safiyyah hakan bai samu ba. Direban kawai ganin Sophie yayi ta fado gabansa, yayi kokarin cin birki ya hango trailer a bayan sa, dole ya zabi bige Safiyyah don ceton kansa da motocin dake bayansa, wadanda cin birkinsa a lokacin zaisa trailer din ta danne su gabadaya.
Haka ya kwashe Safiyyah ya jefar a gefen titi, sannan shima ya gangara gefen titin ya tsaya yana ambaton “innalillahi wainna ilaihi rajioun”.
***** ***** *****
Motocin da ke tahowa daga bayansu duk suka yi wucewarsu babu wanda ya tsaya, yamma tayi sosai, burin kowa ya kai gida ko gari mafi kusa kafin shigowar dare.
Sai tsirarun mutanen da abin ya faru akan idon su ne suka kawo agaji, suka rufu akan Safiyyah da aka wancakalar a gefen titi, suka taimaka masa aka saka ta a motar wanda ya bigeta din. Wani dattijo ya shiga gaban motar don nuna musu asibiti mafi kusa. Safiyyah kwance a bayan motar, aka doshi babban asibitin garin Kura da ita.
Da kyar likitocin suka yarda suka amsheta saboda babu report din ‘yansanda, wanda ya buge tan yace basu hadu da police ko daya ba daga Daka-Tsalle har suka iso Kura, don haka asibitin ne suka kira police aka rubuta report, shikuma ya biya kudin duk treatment din da ya kama za’a yi mata.
An yi sa’a Sophie bata samu karaya ba amma dai akwai gocewar kashin kafa dana hannu, sai kananun raunika da kukkujewa, abinda ya daukesu har bayan isha’I ana mata treatment kafin Safiyyah ta fara dawowa hayyacinta.
**** **** ****
A can kuma Tudun wadar Zaria, wato gidan Anti Dije, hidimar biki data jama’a bata sa Antin ta gane Safiyyah bata nan tun sassafe ba. Sai bayan azahar da Rayyah kanwarta ta gane rashin dawowarta gidan, ta tuno tun safe data ganta tana shiryawa lokacin su Sabah suna barci ita kuma ta farka tace mata zata dan fita ne, amma yanzu zata dawo, to bata dawo din ba.
Kuma har la’asar ta kawo kai Safiyyah bata dawo ba wanda hakan yasa kannenta da suke tare a daki daya duk suka damu, suka soma kiran wayarta ana cewa “not reacheable”.
Daga bisani Sabah ce taje ta samu Anti Dije cikin kawayenta cike da damuwa, a lokacin ana shirin tafiya Mother’s Eve. Tace.
“Anti Dije, ko Yaya Safiyyah ta gaya miki inda zata je ne? Tun safe fa data fita bata dawo ba, kuma bata gaya mana ina zata je ba”.
Anti Dije ma sai a lokacin ta ankara tun safen itama bata ganta ba, jama’a ne suka sa hankalinta bai kai wurin ba, tace
“to ina Safifi zata je haka tun safe bata gayawa kowa cikinmu ba? Amma kira Zayyan ki tambayeshi, bazai kasa sanin ina taje ba, babu inda zata je bada saninsa ba, in kin bibiya ma suna tare”.
Sabah ta kira Zayyan, bugu daya ya dauka suka gaisa yana ta tsokanarta da amaryar robarsa, yadda ya saba tsokanarta don ita ke bin Safiyyah a haihuwa, amma bata biye shi a wasan ba yau, cikin damuwa tace,
“Yaya Zayyan, aunty Safiyyah ta gaya maka inda zata je ne in bi bayanta?”
Yace “kamar yaya? Ba kuna gidan Anti Dije ba?” Sabah ta kara shiga cikin rudu, ta ce “eh, duk muna can, kuma tare muka kwana da ita a daki daya, amma da safennan tace ma Rayyah zata dan fita bazata jima ba, amma har zuwa yanzu karfe hudu bamu ganta ta dawo ba, kuma wayarta bata shiga, Anti Dije tace watakila kuna tare a kiraka a ji”.
Shima ya tuna da safe wajen karfe goma sun yi waya da ita, lokacin isarta Standard Hospital kenan, tace masa “she will call him back” bata jinsa sosai, saboda tana cikin mutane, sai ya dauka ‘yan bikin gidan Anti Dije take nufi. Nan kuwa a lokacin tana magana da kawarta ta kan layin asibiti Ammara ne. Tun daga lokacin kuma bata kira shi din ba, shima kuma yaje Batsari gidan Yayarsa Zubaida ta tsare shi da zance irin nata na kullum, wato na kushe rashin haihuwar Safiyyah har yau. Don ma har yau basu san wanene mara haihuwar tsakanin shi da ita ba, da bai san ya zai kare dasu ba.
Zubaidah tace “sun lura Safiyyah ta tsare gabansa da bayansa, ta hana shi auren diyar kowa, ta shiga rigar arziki tana wadaka son ranta, tana bakin cikin kada wata tazo ta ci, ta hanashi auren da zai karu dashi sai tatse shi suke itada iyayenta kamar hanji.
Ita kuma Safiyyar ta kasa tsinana masa komai tunda har yau ta kasa mayar da shi Uba, cikakken namiji mai iyali kamar kowa.
Tace “kwarai zan so sanin me Safiyyar nan ta taka da take juyaka har haka Baffa, ita ba wani shahararren kyau ba, ita ba aji ba (class) ita kuma ba iya kwalliya ba, kullum ka ganta cikin ragga, wai ita me addini, ko sabida sun saka sunanka a minjaye sun wanke sun baka ka shanye ta bakin Mama?”.
Tsaki yayi “mtssw!”. Ya mike yayi bakin kofa ya hau saka takalmansa. A karshe dai basu yi rabuwar dadi ba shi da Yaya Zubaida, don har yace mata ba zai kara tako kafarsa gidanta ba, shi zumuncin Allah ne ya kawo shi baizo don ta aibata masa mata ba.
Ire-iren yadda yake kare martabar Safiyyah dinnan a wajen danginsa, yana matukar kara mata bakin jini a wurin ahalinsa bakidaya, ba tun yau ba.
Bacin ran Yaya Zubaida ne yasa bai kara kiran kowa a waya ba ranar, har itama Sophien, ya juyo zuwa gida Katsina, inda cikin rashin sa’a kafin ya kai ga isowa Rafindadi Yaya Zubaida ta kira Mama Fatu ta mata korafin ya yi mata rashin kunya akan bakarariyar matarsa, don kawai tace yazo Batsari ya ga ‘yammata gasu nan fululu, ya auri mai haihuwa. Shine ya zageta tatas (a cewarta).
Don haka yana dawowa Mama ma ta dira a kansa, tace matsayin Zubaidah agareshi yafi na duk wani kwashe-kwashensa da zai zageta sabida mace, Mama ta kara masa zafi bisa zafi, bai samu sararin sake kiran Safiyyah ba saboda kuncin ran da suka hadu suka saka shi.
Da faduwar gaba a ransa kadan yace da Sabah “yana zuwa”. Sai ya kashe nata kiran, ya soma kokarin gwada kiran layin Safiyyah.
Abinda dai ake gayawa su Rayyah din shima shi aka shiga gaya masa wato “not reacheable” wanda hakan yayi matukar tada hankalinsa, domin ba abinda ya zo ransa a lokacin sai kidnapping.
Dama dai yau tun safe yake fama da faduwar gaba, don haka jikinsa ya gama bashi ba lafiya ba, jikinsa har tsuma yake a lokacin, yace Sabah ta hada shi da Anti Dije.
Sun dade suna magana na cankar ina zata je, don itama Anti Dije duk da tana cikin sabga yanzu hankalinta yafi daukuwa ga ina Safiyyah ta shiga, ta tabbatar masa bata san ina Safiyyah taje ba, kuma bata da kawaye a nan Zaria. Cikin fara shiga damuwa Zayyan yace, to gashinan tahowa Zariyan yanzu, su hadu su san abin yi, in cigiya zasu bada su bada cigiyarta, da report ga ‘yan sanda.
Kwarai hankalinsa ya soma tashi. Don haka akan hanyarsa ta zuwa Zaria daga Katsina, tuki kawai yake amma hankalinsa baya jikinsa. Da tunanin ina Sophie zata je babu sanin sa, ba izninsa?
Yaushe suka fara ‘yar haka shida Safiyyah?
Me take boye musu shi da ‘yan uwanta da Antinta?
Babu irin tunanin da bai yi ba akan ina Safiyyah zata je haka ba tareda ta gaya masa ko kannenta ko Antinta ba, a dai wannnan rayuwar da muke ciki ta kasarmu Nijeriya, ta insecurity da insurgency (rashin tsaro da ta’addanci)?
Amma ko kusa bai kawowa ransa cewa Safiyyah zata iya zuwa wani wuri ba tareda izninsa ba, yardar da yayi mata da amincin dake cikin aurensu masu yawa ne, don haka ko kusa Zayyan bai kawo a ransa bata ji nasiharsa ba, da yace su dauki tawakkali akan maganar haihuwa, cewa da yayi sun rufe batun haihuwa da gaske yana nufin hakan baka da zuci, bai zaci ta saka kafa ta wofantar da zancensa ba.
Ko yaya Zayyan zai ji a ransa, in yaji cewa Safiyyah ta yi kunnen uwar shegu dashi ne ta kama hanyarta ta fita duniya neman haihuwa ta kowacce hanya???
**** **** ****



