⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 5: Chapter 5

Yau dai Safiyyah ta kasa jurewa, Zayyan barin rayuwarta ne da bazata iya rayuwa babu shi ba, duk ta rame ta zaftare ta dawo rabi, dama jikinta ba wani jiki bane na azo a gani, gainin zata mutu a daki da damuwa sai ta tunkareshi yau, ta same shi a master bedroom dinsu yana changing zai shiga wanka.

Safiyyah ta tsugunna a gabansa hawaye na tsiyaya a idonta, tace “wajenka nazo Habiby, zan yi karin bayani, koda bazaka yarda dani ba, na rantse maka da Allah asibitin mata ne kawai naje a Kano don a duba lafiyata, a ganomin me ya hanani haihuwa. Don na kasa gamsuwa da binciken wannan Dr. Muwadda din, don ni dai ban taba jin wani abu wai shi (pcos) a dangina na uwa ko na uba ba.
Nayi tunanin in nace maka daga gidan Anti Dije zan je Kano asibiti again bazaka barni ba, musamman da yake kace kar na kara yi maka zancen komawa asibiti, which I find it difficult to obey (wanda na samu kaina da kasa bin umarnin)”.
Nan ma shiru, Zayyan baice komai ba, kokarin zagayeta yake ya wuce toilet ta sake shan gabansa, ta rungume shi tsamtsam tana hawaye “tace don Allah kayi hakuri ka yafeni Habiby, I can’t actually explain exactly what happened to me that day… (bazan iya fassara hakikanin abinda ya faru dani a ranar ba) amma abun yafi kama da toshewar basira ….!”.

Ya dago manyan idanunsa da nan da nan suka kada ya dubeta, saida hantar cikin Sophie ta kada, har ‘yan hanjinta saida suka hautsina da ganin bacin ran dake kwance cikin idanunsa, yace.
“Safiyyah kece kuwa? Is it really my Sophie? Haihuwar da dole ake samunta ne haka? Har da zanyi magana ta karshe akai kice ta yi miki wahalar bi?
Lallai shaidan yana son taka rawa a tsakaninmu akan maganar haihuwa, kuma sai akayi yaya bayan nan?
Sai Tsimbirbira din ya ja ki dakinsa zai miki cikin haihuwa ki haihu, tunda ni mijinki ban iya ba…, ko saboda ni na kasa saka miki kwan haihuwa ko….?” Safiyyah ta kusa samun dan karamin hauka a lokacin, da wannan furucin nasa, da hanzari ta kai yatsu ta toshe kunnuwanta, kuka har da sheshsheka da majina tace.

“Maganganunka sun yi min tsauri Zayyan. Ni dai na rasa me ya sameni a ranar, amma na yarda shaidan ne, na rantse da wanda raina yake hannunsa bai taba ni ba, ban shiga dakin da yace in shigo ba na samu kaina da gudowa. Habibi ko Ubangiji ana masa laifi a bashi hakuri, ya yafe, (why not you Habiby?)
Ka yi hakuri ka yi min uzuri, koda da uzrin bacewar basira ta wucin gadi ne kadai”.
Zayyan ya dago ya kalleta, Safiyyah ta kara fashewa da kuka tace “ka yarda wallahi komai nakeyi don mu haihu ne Habiby. Ina son ‘ya’yanka, ina son samun ‘ya’ya daga gareka koda guda daya ne, shiyasa na zama “desperate”, amma na tuba daga yau na hakura, na bi Allah na bi ka. Bazan kara zuwa ko’ina ba sai da izninka.
Ta makalkaleshi kamar kyanwa, tana yamutsa shi kamar Baby a jikin uwarsa. Gabadaya Safiyyah ta jefa shi cikin wani tunani hade da tausayinta. Ya kuma gane da gasken gaske son haihuwar kawai take a ranta, in kuma bai taimaka mata ta samu ba, watarana zata jefa kanta a halakar da ba zata iya fita ba shima ta jefa shi, tunda an fara da bin kawaye gidan boka.

Tun daga lokacin ne, ya shiga tunanin neman solution ga wannan matsalar tasu, don hankalin Safiyyah ya kwanta, shima ya huta da kwarzabar da yake sha a wajen Mama Fatu, akan zancen rashin haihuwarta. Ba don rashin haihuwar Safiyyah ya dameshi ba, ko ya zame masa matsala a cikin son da yake yi mata, ko ya zama nakasu a cikin rayuwar aurensu ba. Sai don kawai ya samo musu kwanciyar hankali bakidayansu.
Dole ya sauka daga fushin nasa, yasa hannu ya dagota ya tallafota zuwa jikinsa, amma bakinsa da ya tafi yake sumbatarta kusufa-kusufa, bai yi shiru da yi mata nasiha ba, akan ta barwa Allah maganar haihuwa. Don shima ta fara saka shi a damuwa da son haihuwar tun abin baya damunsa sam.

A wannan dan tsakanin Zayyan da Safiyyah bakidaya suka fada wani hali na soyayyar samun DA ta kowacce hanya, duk iya tunaninsa ya rasa mafita akan yadda zasu samu haihuwa, ga Mama Fatu ta kara bude wuta da matsa mata lamba a dan tsukinnan da ‘ya’yanta mata suke ta ajiye ‘ya’ya, don kuwa hatta su Zahra sun haife mata jikoki saura shi, sun sake haifewa kowacce karo na bibbiyu, su da akayi aurensu bayan-bayan na Safiyyah. Maganarta dashi yanzu babu hira mai dadi irinta baya kullum sai korafi da shagube akan rashin haihuwar Safiyyah har fargabar zuwa gaida Mama yake yi. Bata wata hirar arziki dashi kamar da sai slogan dinta na gates cewa bakarariyar matarsa har yanzu dai babu labari. Tace bata ga riba cikin aurensu ba sai faduwa da asarar ciyarwa da bautar da yake yiwa mace.
Wannan magana da Mama Fatu tayi ta razana Zayyan da Safiyyah, wanda shi ya kara rura dimautarta da dokinta ga son haihuwa helter-skelter, abinda ya kaisu ga yin bincike na ilmi akan yadda ake samun haihuwa da gaggawa ga mai matsalar lalurar PCOS.
A garin binciken nasu ne a teburin likitoci daban-daban, kowanne likita saidai ya kawo shawarar cewa suyi (IVF) wato (In vitro Fertilization) da aka fi sani (dashen haihuwa) da harshen Hausa.
Safiyyah duk da dokin abun ya cikata wato IVF din, don wannan ne karo na farko data ji ‘hope’ na zata haihu, in dai Dan kanta ne da ya fito daga jikinta kuma na Zayyan to ko ta wace hanya ce tana maraba da samuwarshi, indai addinin musulunci bai haramta ba, duk da haka basu yi saurin amsawa likitocin ba, sannan basu gayawa kowa ba, saida sukayi nasu binciken na addini ta hanyar neman fatawa daga daga malamai daban daban, sannan sukayi bincike sosai a yanar gizo suka tabbatar IVF baida illa daga fuskar addini, da kuma tabbacin da suka samu daga likitoci na cewa kashi 25-30% na attempt din farko ana samun nasara.

Duk irin bayanin da yayiwa Mama Fatu, na cewa sun je asibiti shida Sophie, kuma suna kan zuwa har gobe, da bayanan da likitoci suka yi akan matsalar rashin haihuwar tasu, amma ya boye sirrin matarsa inda yace ance matsalar su (unexplained ifertility) ne shi da ita duk lafiya suke, hakan bai sa Mama ta tausaya ko ta tausasa kalamanta akan kaddarar Safiyyah ba. Tace.
“Fadi gaskiya kawai ka auro “juya” Baffana, ba wani ‘unexplained infertility’, tunda dai a shekaru kusan takwas da aure ta gagara haifa maka Da ko guda daya, ai JUYA ce kenan, musamman da babu bari ba batan wata mai nuna alamar haihuwa.
Wannan makauniyar soyayyar da kake yiwa diyar Alarammannan tayi yawa Baffa, na fadi na kara fadi meye ribarta? Ribar kowanne aure ai haihuwa ce, tunda bata da mahaifar haihuwa kuwa, aurenta babu riba a cikinsa sai asara”.
Ta kai ta kawo a yanzu Safiyyah ko gidansu Zayyan ya gagareta zuwa, bata iya shiga sha’aninsu na biki kona haihuwa, bama sa gayyatarta, abun nasu babu kawaici babu tausayi da alkunya, kai sai ka rantse da Allah ita zata halicci dan a mahaifarta. Idan kuwa tayi kuskuren zuwa wani sha’ani na iyalin Mama, kamar sunan haihuwar ‘ya’yanta Zaitoon da Hatoon da akayi recently, yadda kasan mujiya haka take komawa a cikin su, saboda wulakanci da kaskancin da suke mata, ga yada mata mummunar magana cikin habaici a gaban kowa, akan rashin haihuwa kai sai ka rantse a kasuwa ake sayar da haihuwa.

A kodayaushe sukayi waya da Ammi kuka take tana labarta mata irin mawuyacin halin da take ciki da uwar mijinta da ‘yan uwansa, Ammi ba abinda zata iya a kai banda ta kwantar mata da hankali, kullum tausarta kawai takeyi, tace ta kara hakuri kan wanda take yi, matsalar rashin haihuwa ba a kanta aka fara ba, ba kuma kanta za’a kare ba, kada kuma ta fidda rai. Saboda yadda Safiyyah ke gaya ma Ammi Hafsatu halin damuwar da take ciki da dangin mijinta, har auren Safiyyah ya soma fita daga ran Ammi, don ta kan ce a ranta sam Uwar Zayyan uwar banza ce, bata da Ikhlasi. Kamar bata haifi ‘ya’ya mata ba itama.
Amma a matsayinta na uwa bata nunama Safiyyah hakan ba, amma a ranta ta fara tsanar auren yanzu, don kwatakwata Safiyyah ta rasa nutsuwa da farin ciki a cikinsa, tsakaninta da mijinta lafiya kalau amma zuciyarta babu dadi, duk da ganin zaman daular da take ciki da kowa dake nesa da ita yake yi mata baya sata zama cikin nnutsuwa. Yes, da gaske Safiyyah tana cikin daular miji domin Zayyan kullum kara buda masa nasibi cikin harkokinsa Allah yake yi, har wata ‘yar kiba ya aje ta musamman irin ta kasaitattun mazan Abuja, masu murza naira da jin dadinta son rai. Ita kuma Safiyyah kullum ka ganta kamar marar lafiya kamar kudin guzuri, bata da karsashi da walwala a cikin tsararrakinta.
Ya nutsa sosai ga tunanin mafita a garesu. Har zuwa lokacin da Safiyyah ta kara bijiro masa da zancen baya, wato bukatarta na suje wani asibitin kudi a Kaduna, bisa shawarar da likitoci suka bata akan suyi (In vitro Fertilization).
Sai ya shiga tunanin ko hakan za’a yi kawai don Safiyyah ta samu kwanciyar hankali ta rike Da a hannunta? Su kuma huta da gori da fitinar Mama Fatu?
A daren suna waya shida Mama, yake yi ma Mama maganar cikin damuwa,

“Mama yanzu saboda Allah kinji dadin hakan? Mama uzzurawarki ga son Sophie ta haihu kota halin kaka, yasa Safiyyah fara tunanin muyi IVF kawai”.
Mama ta tambayeshi cikin halin ka’in kula ko meye IVF din?
Nan ya yi mata bayanin cewa “Dashen Da a mahaifa”.
Mama ta zabura, tace “to ba dai cikin zuri’ata ba, amma in kun ga shi zai fishsheku to kuje ku yi tayi.
Indai mutum yace ra’ayin Bature zai biyewa shi ya jiwo, shi dama kowa yasan halakakke ne, ku zai halakar ba ni Fatima ba”.
Mama bata hana ba, amma ta nuna matsalarsu ce yin IVF ba tata ba. Don haka shi da kansa ya yarda suje Kaduna a yi musu Dashen, don itace kadai last hope din su.
Basu kara bi ta kan Mama akan zancen ba, suka shirya suka tafi Kaduna da niyyar ayi musu dashen haihuwa.
A wani babban asibitin kudi a Kaduna wai shi (Nisa Fertility and Gynae Center Kaduna) akayi ma Safiyyah da Zayyan dashen Da (IVF), sosai suka tsaya suka naqalci ilmin abun, ta yadda suka gane komai akansa, kafin su yarda aka yi mata.
**** **** ****

RANAR DASHEN
Safiyyah ta sha ‘yar wuya wajen yi mata dashen IVF, amma ta dade tana gayawa kanta babu wani dadi a duniya da ya wuce (samun Dan kanka).
Shikuma uban gayyar ba kananan kudi ya kashe akai ba, amma ya gayawa kansa shima gara su haihun, wato su samu Dan ko daya ne a rayuwarsu, in ba haka ba bazai taba samun kan Safiyyah ba. Haka Mama bazata barsu su huta ba.
Na farko idan har ba haihuwa tasamu ba bazata taba dawowa ‘Hijabhie’ dinsa ta baya ba, bazata dawo musu da farin cikin su irinna baya ba, da kulawar soyayyarta da yake ta kewa yazu dare da rana. Shima kuma ba zai huta da kwarzabar Mama data su Yaya Zubaida ba, duk dai akan rashin haihuwar matar tasa, itama Sophie bazata taba hutawa da gorinsu da wulakancinsu da habaicinsu ba wanda basa ko gajiya, kuma shi yafi komai saka mata inferiority complex. Kai sai ka rantse haihuwar nan kudi ake sakawa a sayota da arha a bakin titi, ko iyawar mutum ke bashi ita.

Abin farin ciki a garesu kuma shine kamar almara, daga attempt na farko, cikin ikon Allah watanni uku da yin dashennan aka tabbatar da zaunawar ciki na wata uku a jikin Safiyyah Usman (Mrs Zayyan Rafindadi).
Duk da cewa a mafi yawan lokuta kashi 25-30 cikin 100 na masu yin IVF a karon farko ne kawai ake yin nasara. Amma yiwuwar nasarar na karuwa bayan an sake gwadawa sau da dama.
Dole Likitocin suka rike Safiyyah a asibitin har tsayin watanni hudu don a samu cikin ya zauna da kyau, hutu zallah Safiyyah keyi a gadon asibiti, ta wanke goma ta tsoma biyar. Zayyan ya dauki nauyin komai na kulawarta da hutunta wato ya tsaya ma Safiyyah.
Samun miji tsayyaye akan damuwarka da bukatunka ma kadai irin Arch. Zayyan Bello Rafindadi, ba karamar sa’a bace ga diya mace. Ta wannan fannin kam Safiyyah tayi sa’a, ta kuma ta yi sa’a, ta yi wa mata ‘yan uwanta da yawa kwalele, na sa’ar samun mijin da ya tara wadannan qualities din. Shi Zayyan a halayyarsa da babi’unsa akwai kyautatawa iyali, he’s a caring husband, baida son kansa, baida mugunta, abin hannunsa kakaf! Na iyalinsa da ‘yan uwansa ne, mutum ne mai kulawa, mai tattalin farin cikin iyali, sannan mai sonta da tausayinta da son kwanciyar hankalinta, in ka dauke matsalar mahaifiyarsa Mama mace marar kawaici da rashin maida surukin da baiyi mata ba nata, da ‘yan uwansa mararsa kara da zumunci ga Safiyyarsa, da kiyayya da raini gareta maras dalili, to da sai ace Safiyyah tafi matar gwamna sa’ar rayuwar gidan miji kam, saidai kawai matar gwamna ta nuna mata firda-firdan motoci da kantamemen gida da rashin hutu da rashin kwanciyar hankali.

Yo kiyayyarsu maras dalili mana? Don ta ko’ina ta duba ta hanga dalilin kiyayyar Mama da ‘yan uwan Zayyan a gareta, bata iya ta hango ta ina ta kuskuro su kota ragesu ba, bata ga hujjarsu mai ma’ana na kinta ba, iyaka kokarinta kullum tana yi wajen kyautata musu, duk wani abu da ya zama hakkinsu ne a wuyanta Safiyyah babu jinkiri tana kokarin saukeshi ba sai Zayyan ya fada ko ya sani ba, ba kuma sai ya saka ta ba, hannunta a mike yake kullum ga kowa nasa, wajen kyauta da yawan alkhairi, balle ga su dangin mijinta da haihuwarsu barkar haihuwarsu ko bikinsu baya wuce alkhairinta, kuma sai tayi babbar bajinta take jin dadi, kai har da wanda ba hakkinta ba, Safiyyah yi musu take, saboda kaunar data ke yi ma Zayyan. Amma Mama Fatu da ‘ya’yanta babu ragayya ko kankani a tsakaninsu, babu godi bare an gode kawai don bata haihu ba, ko tace Allah bai bata haihuwa dasu ba, babu mai yaba kokarinta, bata da wani farin jini a idonsu saboda ubanta ba mai kudi bane, ba mai Mulki ba, kuma ba mai irin tsarin rayuwarsu ta ‘yan boko ba, babban dalilinsu kuma na yanzu an doshi decade bata haihu da dansu ba (shekara goma).

Sosai cikin jikin Safiyyah ya bayyana kansa a watanni na biyar da yin dashensa, Safiyyah abin nema ya samu wai matar Dansanda ta haifi barawo, tafi Zayyan So da dokin isowar IVF Baby dinsu.
Zancen nasarar IVF da suka samu ya kai kunnen Mama Fatu daga bakin Yaya Zubaina, kasancewar komai Zayyan zaiyi sai yayi shawara da Zubaina. Yanzunma ya damka mata alhakin fara hada musu kayan haihuwar Baby ne inda yace, ta hada komai (unisex) don yaki yarda ma ayi scan a gano musu jinsin jaririn, yace shi kome Allah ya basu abin so ne da kauna da tattali a gareshi, walau mace walau namiji.
Safiyyah tun samun cikin ta bata je Katsina ba, kuma basu hadu da Mama ba, don Zayyan ya hanata tafiye-tafiye tun fitowarsu asibiti, wato tun zaunawar cikin. Ta kan dai kirata a waya tayi gaisuwar da bata wani tasiri wajen canza matsayinta a gun Mama Fatu.
Don haka Mama bata san cikin IVF ya kankama ba.
Har saida Zubaina tazo ta sameta kan wane shiri ya kamata suyi na haihuwar matar Baffa, kuma ince ko ta bada dakan yajin haihuwa da sauransu, don dole suyi gagarumin shiri, su yi duk abinda ya kamata a haihuwar Baffan Mama ta farko, bayan kwashe shekaru goma ba’a samu cikin ba.

Ta cigaba da gayawa Mama cikin farin ciki da taya dan uwanta murna,
“yanzu kinga Mama cikin taimakon Allah IVF din da sukayi (dashen haihuwa) kamar da wasa ya zauna”.
Ina wuta Mama Fatu ta jefasu shi da Safiyyah? Don babban ashar Mama ta saki, tana cewa “Safiyyah ta ja mata Da ga halaka, saboda bakin cikin ta kasa haihuwa ta hanyar da Allah ya tsara, saboda tana bakin cikin kada ya auro wata ita ta haifa masa naturally.
Mama bata taba zaton maganar da Zayyan yayi mata watannin baya cewa wai ta tunzura Safiyyah ga son yin IVF zasu aikata din ba, ta dauka magana ce kawai ta fatar bakinsu. Shiyasa bata wani hana su sosai tun a lokacin ba.
Mama tace ita ko a zamanin jahiliyyah bata taba jin inda aka haihu haihuwar dan halak ta hanyar Dashe ba.
Tace dan Dashe ba cikin zuri’arta ba, duk da Zayyan ya gaya mata tun kafin ayi bata taba daukar zancen wani serious ba, sai bayan data ji sun aikata din kuma ya zauna. Ta fitini kanta da zage-zage. Zubaina ta rasa yadda zata yi ta ganar da Mama IVF ba haramun bane a addinance.

Tace a ranta Mama kamar wadda bata yi ilmin zamani ba? Koko ace ta take sanin, saboda son ranta.
Mama ta kafe akan ra’ayin ta na cewa ba dai cikin zuri’arta za’a ajiye dan Dashe ba. Har ita Zubainar Mama ta hadasu ta zage tas, tace itace babbar munafuka da ita kadai ake kulle-kulle a gidan Baffa, ita dashi duk an saka sunansu a minjaye su duka an shanye, to su kam wato itada sauran ‘yan uwansa sunfi karfin gidan Alaramma.
Nan da nan kuma Mama ta figi wayarta ta kira Safiyyah. Don ta kasa hakura da zancen IVF.
Safiyyah na zaune a falonta, ta saka tirtsetsen cikinta a gaba, wanda kullum taji motsi a cikinsa sai tayi tazbihi ta tsarkake kudura da iradar Ubangiji. Kunun gargajiya na “Tamba” take sha a kofin Mug, wayarta tayi ruri.
Koda ganin yau Mama da kanta ta kirata, Safiyyah farin ciki taji mai yawa, ta dauka a dokance cikin matukar girmamawa har da russunawarta, ta dauka sannu da jiki Mama zata yi mata, don tun fitowarta daga asibiti basu yi waya da Mama ba. Don ko kiran Mama tayi don ta gaidata Mama bata amsa kiranta sai taga dama. Kuma gashi yau ta kira ta da kanta ba sako ba. Don haka yau Safiyyah da taga kiran Mama cikin wayarta ba karamin farin ciki taji a ranta ba.
Amma tana dagawa da sallama jin gurnanin Mama kadai ta cikin wayar yasa taji gabanta ya fadi, mummunar faduwa.

Ta hadiyi miyau da kyar tana amsa wayar Mama cikin ladabi mai girma, Mama ta basar da gaisuwarta da ladabinta tace,
“Sannu Hakimar Baffa! Babbar mace Hakima a gidan Baffa! Ko ince sannu Hakimar Dandume ‘yar Mallam jikar Alaramma. Ni ba kira nayi don mu gaisa ba, kira nayi inji dalilin kawomin Dan dashe cikin zuri’ata mai tsafta.
Ashe karyar Malanta kuke babu sanin Allah cikin lamarinku, ki gayamin Ayar da ta ce in ka kasa haihuwa kayi dashen ciki, ko wadda tace dashen ciki ya halatta, zan so kwarai sanin dalilinki na baiwa kanki abinda Allah bai ga damar baki ba, saboda tsoron kada Baffa ya sake ki ne ko don kada ya kara aure da wadda zata haihu?
Da zai yi dayan biyun wadannan din da tuni bai yi ba? Yau kuke tare dashi? Ko yau aka fara jiran haihuwar taki?
Shin ana aure dole ne Safiyyah, ko Baffana shine autan maza da kika bi kika laqe masa haka? Alhalin bazaki amfanar dashi komai ba?
In kina nufin ‘ya’yan dashe zaki ke kawomin cikin jikokina kuma in amsa kin yi kuskure, don bazan amsa ba, ba dai ni Fatuma ce zan goya dan Dashe a bayana da sunan jika ba.
Don haka tun wuri ki nemi Kakar diyanki in kin haifa a can Dandume, bani Fatun Bello Rafindadi ba, don ban yarda da halaccin haihuwarsu a addinin musulunci ba……”.

Safiyyah kasa karasa sauraron Mama tayi, ta saki wayar a kan kujera tana fidda hawaye masu zafi.
Ba cin mutuncin Mama gareta ne ya sata kuka ba. Face jin a fakaice Mama na son tabo mutuncin iyayenta, cewa basu san Allah ba. Alhalin su ko sanin anyi dashen ma basu yi ba.
Zayyan bai san da wannan wayar da Mama ta bugowa Sophie ba, itama kuma bata gaya masa ba, ita kadai ta bar abun a ranta yayi ta cinta wanda ya sabbaba mata sabuwar damuwa kuma.
A rashin saninta shima Mama ta kira shi har gabanta, tayi masa nasa wankin babban bargon akan Dashe da suka yi kwatankwacin nata, tace “ya bata kunya ya rasa mazantaka, ya bari Safiyyah ta mayar da shi waina a tanda, sai yadda taga dama take juyashi, tunda har ta ja shi suyi dashen Da da ilminsa da komai babu iznin ita data haife shi.

A karshe ta gaya masa cewa “wannan dan ko an haife shi ba jikanta bane, na Alaramma ne shikadai”.
Maganar nan tayi masa zafi kwarai, Mama na son sheganta masa Da ne tun ba’a haifeshi ba ko yaya? Wannan cikin da yadda yake son sa tun bai zo duniya ba? Ya kidima ya shiga rudu, ya shiga tashin hankali mai yawa akan kalaman Mama.
A iya saninsa ya gayawa Mama zancen zasu yi IVF, kuma bata yi wani mummunan umarni a kai ba. Cewa tayi kawai in sun ga shi zai fishshesu to suje su yi.
Don haka tunda ya dawo gida a ranar Safiyyah ta kasa gane kansa, amma koda wasa bai gaya mata komai ba akan zuwansa Katsina, itama kuma ta ja bakinta tayi shiru bata gaya masa wayar da suka yi da Mama akan cikin ta ba.
Haka kowannesu ya bar abun a ransa yana damunsa, har zuwa sanda suka manta da shi suka cigaba da shirin taryar Baby dinsu, cike da wata irin soyayya ta daban ga yaron, ko yarinyar, tun bai zo duniya ba.
**** **** ****

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *