Chapter 6: Chapter 6
Cikin Safiyyah ya shiga watanni na bakwai, karkashin kyakkyawar kulawar likitocin ta, kulawarsu, tattalinsu da burinsu duka ya koma kan cikin. Wani abun mamaki Zayyan din da a baya yake cewa bai damu da haihuwa ba blah blah blah… sai gashi da akayi wa Sophie dashen Dan, sai yazo yafi kowa son shi, da dokin a haifa masa shi ya dauka.
Har dakin da Babyn zai rayu bayan an yaye shi daga nono Zayyan ya ware a kusa da nasu shi da Safiyyah.
Ya zuba komai na bukatar yara ‘toddlers’. Mama Fatu dai ko me yasa? Daga baya bakinta ya mutu akan batun cikin, bata kara aibatawa ba, bayan wancan wankin babban bargon data yi musu. Ganin dukkansu sun dauke mata kafa.
Wannan ya biyo bayan ranar da tayi arba da Safiyyah da tirtsetsen cikinta a gabanta, aka ce Uwa-Uwa ce ba’a sake ki saidai uwardaki, shi da kansa ya hakura da abinda Mama tayi masa ya dauko Safiyyah da tsohon cikinta musamman ya kawo ta don ta gaida Mama, daga ranar bakin Mama dana ‘ya’yanta yayi la’asar daga gorin Sophie ta kasa haihuwa, sun yarda ko yaya ne dai ashe akwai kwan haihuwa irinna kowacce ‘ya mace a jikinta, suka gasgata jita-jitan da suke ji din, na cewa tabbas ta samu ciki daga bakin Zubaina, wanda a da suka kasa yarda da gangan.
Saboda a ranar ta same su bakidaya a gidan mahaifan nasu (banda Zubaina), suna tsaka da family meeting kamar yadda suka saba tare da Baba Murtala akan habakar Estates dinsu na nan Katsina, da sauran fannoni na cigaban rayuwarsu data ‘ya’yansu masu tasowa.
Baba Murtala wanda shine makwafin Ubansu a halin yanzu, duk meetings din da suke yi a karshen kowanne wata in dai yana gari da shi a ciki, akan rayuwarsu data ‘ya’yansu data Estate din ‘ya’yan Mama ake meeting din, a kowacce asabar din karshen wata, inda Baba Murtala yake shige musu gaba a komai, don kula da habakar dukiyarsu da cigaban rayuwarsu.
Duk da Mama ta amsa gaisuwarta, ta kuma ganta da tirtsetsen ciki ta kasa cewa a ranta “Alhamdulillah Baffa zai haihu”, haka ta kasa cewa “Allah ya raba lafiya” saboda can a kasan ranta tana jin wani iri babu dadi, saboda tuntuni ta riga ta sakawa kanta wani negative thought haka (gurbataccen tunani) akan ‘In-vitro Fertilization’.
Mama in ta tuna dan Zayyan dinta na farko a duniya, haihuwar Baffanta na fari dan dashe ne (IVF Baby) ne sai taji gara ma bai haifa ba.
Yawan korafin Mama akan rashin halaccin IVF yasa Zayyan ya sake bazama neman fatawar Malamai mabambanta, amma kamar can baya, har yau bai ji fatawa sahihiyar da ta haramtashi ba. Saidai malamai suce surrogacy shine haramun (wata ta daukar ma mace cikin da sperm din mijinta ta haifar mata dan saboda ita bazata iya haihuwa ba).
Amma a duka binciken da yayi na addini akan In-Vitro Fertilization, amsar da yake samu shine;
“IVF is permissible in ISLAM with the condition that it involves the gametes of the married couple and adheres to the sanctity of the marital union, aligning with Islamic principles of lineage preservation”.
Ma’ana; Dashen haihuwa ya halatta a muulunci bisa sharadin cewa kwayayen haihuwar da za’ayi amfani dasu su kasance na ma’auratan ne, don a kare martabar aure da samar da zuri’a tsarkakakkiya kamar yadda dokokin musulunci suka tanada”.
***** **** ****
“The IVF Mother”
A wannan lokacin da cikin ta ya shiga watanni na takwas Zayyan baya nisa da gidansa. Haka duk inda yaje Safiyyah na ransa, baya awa biyu bai kirata a waya don tabbatar da lafiyarta ba.
Tun cikin nada wata bakwai Zayyan da Safiyyah da taimakon Yayarsa Zubaina sun gama tanadar duk wani abinda jaririn zai bukata, shi da Yaya Zubaina suke shirye-shiryensu ba tareda sun saka Zubaidah ba, har feeder da gadon baccin jariri yana nan sun ajiye a cikin dakin sa. Kuma komai suka tashi saya sai sun zabo ajin farko na ‘yan gatan jarirai.
A ranar da cikin Safiyya ya shiga watan haihuwa ba yadda Safiyyyah bata yi da Zayyan ya maidata Dandume ta haihu a can ba, ya kafe yaki amincewa.
Yace “kina wasa ne kema yarinya.
Ya kamata ki san cewa we have to take extra care of this Baby, tunda dai kin ga da yadda Allah yasa aka sameshi. Bazan barki ki koma Dandume haka kawai inje kiyi haihuwar gida ba, lallai sai a asibitin da ake kula daku anan tun farko zan bari ki haihu, in yaso Ammi ta kawo wadda zata kula da ke gidannan, to wannan kuwa, bazan ki amincewa ba, hankalina ma zai fi kwanciya in ya kasance muna tare koyaushe, fiyeda ina nan nesa, ku kuna can Dandume”.
A can gidan su Safiyyah Ammi tuni ta soma hada kayan haihuwa, su yajin jego, garin yin kunun kanwa da kanwar kanta duk ta tanada da sauransu, haka ta hada su rankatakaf ta daure jiran haihuwa kawai ake.
Da EDD dinta ya rage saura sati biyu shida kansa ya roko Ammi ta basu mai zaman jego. Sai Ammi tace Sabah da Rayyah su shirya su koma Abuja su taimakawa Yayarsu, don masha Allah ‘yan matan Ammi sun horu, ba abunda basu iya ba na manya kasancewar su rainon Tsoffi.
Har Rayha autar su ta girma Ammi bata san komai na hidimarta da rainonta ba, Sabah da Rayyah ne suka yi raino da hidimarta. Haka in Anti Dije ta haihu su suke mata komai da babba ke yiwa Maijego harda saka ruwan wanka.
Haihuwar Safiyyah daban ce da sauran haihuwa shiyasa iyayenta basu takura ta dawo gida ta haihu a gabansu ba.
Zayyan daga baya ya yiwa su malam bayanin IVF na asibiti aka yi mata, kuma malam a matsayin shi na babban malami bai yi challenging IVF ba, ya dubeshi ta kowacce fuska ta addini bai ga inda ya zama haramtacce ba.
Don haka ya bisu da addu’a da fatan Allah ya sauki Safiyyah lafiya.
Yanzunma Sabah da Rayyah data turawa Safiyya tana da tabbacin zasu iya, shiyasa ta turo su tunda Anti Dije bazata bar gidanta taje jegonta ba, amma hankalinta bakidaya yana kan babbar ‘yarta mafi soyuwa a ranta “Nana Safiyyah”. Dare da rana tana yi mata addu’ar sauka lafiya da samun saukin nakuda a kowacce sallahr farillarta.
Da murna da doki sosai su Sabah suke shirin tafiya Abuja, don kwatakwata tun komawarsu Safiyyah can bai fi sau biyu suka taba zuwa gidan Yayar tasu ba, shima dubiyarta suka je da bata da lafiya, na farkon kuma sun je ganin gidan ne sanda zasu koma can da zama, malam baya barinsu sam, don kowacce da maganar aurenta a kanta in ka dauke Rayha autar Ammi.
A motar haya su Rayyah suka tafi Abuja su biyu. Tun kafin su iso Safiyyah ta ware musu dakin da zasu sauka cike da dokin ganin kannen nata, ta aje masu duk abinda ta san zasu bukata, wannan shine zuwansu Abuja karo na biyu tun dawowarsu Safiyya nan daga Zaria.
Sabah dama tafi Rayyah baki, kuma tafi duk sauran kannenta faram-faram da jama’ah. Tunda Zayyan ya je dauko su a tashar Jabi tana gidan gaba Rayyah na baya, shida ita suke hirar tsokanar juna a cikin motar. Zayyan yana tsokanarta da amaryar robarshi, tazo bikon shi, taga baya zuwa zance yanzu, Sabah tace “haba dai inzo bikon ka, na dai zo taron Da na wallahi, kaima kasan kayi min tsufa Yaya Zayyan”, Zayyan yak ama baki ciki dariya da mamaki yace “really? Rayyah, yaushe ‘yar kauyen matar nan ta kile haka?”
Rayyah dai dariya take tana jinsu. Sabah ta kara cewa “Saboda Allah Rayyah nida nake da sarbadeden saurayi irin Jabir a gefe, yaro matashi me jini a jika, dan late twenties, me zan yi da Yaya Zayyan? Wannan kayan tsufan ai sai Nana Safiyyah”.
Zayyan ya tuntsure da dariya harda bugun sityari yace “amma kin yankeni! Saina gayawa Sophie, kina kira ma darling dinta tsufa tun yanzu”.
Tunda su Sabah suka zo gidan suke wani irin kula da Safiyyah da komai na kulawar gidan ya koma wuyansu, ko tsinke basa bari ta kawar, ko abinci taci nan zasu kawo mata ruwa ta wanke hannu daga zaune. Zayyan kuma ya wadatasu da kayan dadi suke ta fama, duk fitar da yayi ya dawo sai ya riko musu abinmotsa baki, musamman Rufaida Yughurt da Rufaidah Shawarma da Pizza din Dominos da suke matukar so.
Yanzu kam kowa yaga Sophie ya san dan cikin ta ya gama duk wani shirye-shiryensa na isowa duniya. Tashi sai da dabara kwanciya ma haka.
**** ***** ****
Safiyyah ta fara wata irin naquda mai matukar wahala ranar wata Litinin, Zayyan baya gida yaje supervising ginin wani sabon Estate da yake ginawa a unguwar Jahi. Kasancewar tunda watan haihuwar Sophie ya kama baya yarda yayi nisa da tsakiyar Abuja.
Sabah ta kira shi a waya ta gaya masa yazo su tafi asibiti Aunty Safiyyah fa ta fara nakuda.
Nan da nan daa inda yake ya kira asibitinta suka tura motarsu ta daukosu daga gida, shikuma ya bar komai da yake yi a Jahi, ya karya kan motarsa yayi kwana zuwa asibitin. Suka iso kusan a tare da motar asibitin data dauko su Safiyyah.
Har da shi aka hadu aka gungura gadon Safiyyah zuwa dakin haihuwa.
A cikin awannin da basu gaza uku ba Safiyyah ta haifo santalelen yaron ta namiji mai kama da shi sak. Akan idanunsa, kanta bisa cinyoyinsa, yana mai tayata nishin haihuwar cike da tausayi kamar tare da shi suke labour, yana karanto addu’a yana tofa mata. ganin halin da Sophie ke ciki a wannan lokacin ya kara masa son Mamansa Haj. Fatu, yau ya yarda haihuwa ba karamin al’amari bace ga mata, gashin kanta ya wargaje akan cinyoyinsa yana supporting dinta da kalamai na karfafawa, bai gushe ba yana mata addu’a har ta haifo masa Danliti, kuma photocopy dinsa, bulelen yaro lafiyayye mai kama dashi sak.
Amma me? Likitoci sun yi sun yi yaron yayi kuka bayan isowarsa abu ya faskara, stillbirth!
***** **** ****
Zayyan sai ya rintse idanunsa a hankali, daidai sanda tunaninsa ya zo nan, yana mai tuno kyakkyawar fuskar jaririn da ya gani a ranar, dan su shi da Sophie, sai ya ji komai na memories din wancan lokacin ya dawo masa sabo. Wato lokacin rayuwarsu daga shi sai Safiyyah a gefensa. Amma a hakan ya daure ya cigaba da tunano al’amuran da suka gabata din, a kokarinsa na nemo maslaha da warwara, wadanda duk ba masu dadin tunawa bane a gareshi.
Abin kunya da bakin cikin da yafi kowanne girma a gareshi shine, daga Mama har yaranta duka aka rasa wanda zai zo ya duba Safiyyah a asibiti, balle su jajanta ko yi musu ta’aziyyah na yaron da suka rasa, alhalin sunfi kowa sanin halin da suka shiga da wahalar da suka sha akan cikin wadda bazata lissafu ba kafin samunsa, da wadda suka sha bayan samuwarshi, in ka cire Yaya Zubaina da ta kira su a waya, tayi ta lallashinsu, ta kuma tunasar dasu muhimmancin yarda da kaddara da tawakkali akan jarrabawar Ubangiji kowacce iri ce.
Saboda Baban Muntaqa baya barinta tafiye-tafiye sosai, amma kwarai taso zuwa har Abuja din, har lokacin Zubaina a garin Kano take aure. Kullum sai ta doko musu waya ta bata lokaci ta lallashesu, tana tunatar da su muhimmancin yin hakuri, da tagomashin da Allah ya tanadarwa wadanda suka rasa ‘ya’yansu suna kanana, tace kada susa damuwar hakan a ransu. Allah da ya basu wannan din, a lokacin da suka riga suka fidda rai da samun haihuwa, shi zai kuma basu wani kota IVF dinne cikin kudura da buwayarsa.
Daga shi har Safiyyah a wannan dan tsukun kusan zautuwa sukayi a zuci da zahiri, saboda duk wata soyayyarsu da burinsu da kawar zuciyoyinsu ya koma ga zuwan Babyn nan duniya, sun gama tanadin irin tattalinsa da zasuyi cike da soyayya da kauna na iyaye, da kuma tarbiyyar da zasu bashi duk sun gama tsarawa. Kai har makarantar da zasu kai yaron sun zaba tun bai zo duniya ba saboda tsabar dokinsu ga isowarsa.
Kwarai su kadai suka san irin wahalar da suka sha kafin Allah ya basu shi ta hanyar ‘In-Vitro Fertilization’. Da irin spending din da sukayi akan samuwar cikin da rainonsa. Hakika tattalin arzikinsa ya girgiza akan haihuwar babyn nan da shirin tarbarsa.
To ina ruwan Allah! Kana naka shima yana nashi. Kuma nasa shine gaskiya. Duk jarrabawar da yayi nufi ga bayinsa shi ya san ladan daya tanadar musu akanta, zai kuma baiwa bayinsa wannan ladan a duniya ko a kiyama, akan hakurin da suka yi, in har sun yi hakurin dominsa ne sun tsarkake shi.
In kaga wadannan ma’auratan a wannan lokacin na makokin jaririnsu, sai sun yi matukar baka tausayin da nan da nan zai saka ka zubda musu hawaye.
Domin sun rasa duk wani karsashi na jikin dan adam, da kuzarin su na cikin gida da waje. Can zaka hango su tsakiyar makeken gadon su manne cikin jikin juna, suna faman sauke ajiyar zuciya ba mai iya baiwa dan uwansa baki. Ba mijin ba, ba kuma matar ba, ba mai iya lallashin dan uwansa koda da kalmar “sannu” ta fatar baki ne. Wannan ya faru bayan an sallami Safiyyah daga gadon asibiti.
Babban bacin ransa yadda Mama dasu Ya Zubaida duk suka yi shakulatin bangaro dasu. Abun yayi matukar bashi mamaki da tsoro, bai yi zaton kiyayyarsu da Sophie ta kai haka ba, tunda in akan haihuwa ne ai gashi ta haifa musu Allah ne bai barshi ba. Tun daga lokacin ya fahimci kiyayyarsu da Sophie maras dalili ce, amma ya zaiyi?
Abun ya tsaye masa a rai kwarai. Ya san tun fil azal jinin Mama bai hadu dana Sophie ba, amma bai taba tunanin abun ya rikide zuwa tsana tsagwaro irin wannan ba har a gun kannensa da babbar Yayarsa, da har zata dau ciki watanni tara ta haife dan babu rai, amma su kasa ko jajanta mata su kasa zuwa su kuma kasa kiran waya wannan abun ya tsaye masa a rai fiyeda zatonsu.
Abinda shi bai sani ba, tun daga lokacin da Safiyyah ta yanke shawarar yin Dashen haihuwa saboda gorinsu da tsangwamarsu, daga lokacinne kuma ta samu rashin son da suke yi mata ya rikide ya kara matsayi zuwa tsagwaron tsana, dama kuma sun sha alwashin koda ta haifi dan da rai tunda ta hanyar IVF ne ta samu cikinsa bazasu taba rika mata shi a matsayin Da kamar sauran ‘ya’yansu kuma jikokin Baba Bello ba. Saidai ta kai Dandume su Alaramma su goya mata.
Bai manta da lokacin da ya kira Mama ba, tun suna asibitin da Safiyyah ta haihu kafin a sallameta, ya gaya mata Safiyyah ta sauka, amma yaron ko shurawa bai yi ba.
Yasa hankaci ya tsane idanunsa ba tareda Mama ta san idonsa ruwa yake fiddawa ba, budar bakin Mama sai cewa tayi, “yo daman wannan dan nata irin sauran ‘ya’yan mutane ne da za’a zaci dole zai rayu? Dasa mata shi fa akayi ta karfi da yaji, to meye abun mamaki ko damuwa don ya zo babu rai?
Shin in tambayeku; ku duka kaida Safiyyahr, wai ana yiwa Ubangiji dole ne akan abinda bai ga damar bayarwa ba? Matarnan taka Safiyyah ‘juya’ ce Baffa, na kara fadi gaskiya juya ce, ku yarda ko kada ku yarda kuma ya rage naku.
Da zata haihu da tuni ta haihu kamar yadda kowacce mace ke haihuwa naturally. Idan ka sake yarda aka yi Dashen haihuwar Da da maniyyinka Baffa Allah ya isa ban yafe maka ba!
Tunda dai mata masu haihuwar nan ta gaske ba karewa suka yi a duniya ba!”.
Wannan maganar ba karamin firgita shi da gigita shi ta yi ba, da sauri ya cire wayar a kunnensa ya duba yana tantamar anya Mamansa Haj. Fatu ce wannan? Kodai wrong number ya kira?
Sai a lokacin ma ya tuna cewa ai ko sau daya Mama Fatu tun samun cikin Safiyyah haka siddan bata taba kiransu tace Allah ya inganta ba, ko Allah ya sauki Safiyyah lafiya, a lokacin da take goyon cikin.
Ance ba’a fushi da iyaye, amma hakika Zayyan ransa ya sosu sosai da attitude din mahaifiyarsa, abunda Mama Fatu tayi ga iyalinsa bai taba zaton uwa zata yi shi ga dan data haifa ba. Har hakan yasa ya dan dauke kafa daga Katsina, na dan wani lokaci.
Ya maida hankali ga taya su Sabah kula da lafiyar Sophie, su su kula da ita daga safe zuwa dare, shikuma ya yi nasa jegon daga dare zuwa safe.
A lokacin da Sophie take jegonnan ne kuma ya fahimci wani abu a halittarsa, wato jikinsa baida jimirin hakuri da rashin matarsa na lokaci mai tsaho.
Kusan kullum Safiyyah na barci irinna masu jego, shi kuma yana fama da shan ruwan kanwa, domin kwantar da sha’awarsa ta da namiji, kwarai ya kan gaza hakuri da ita cikin dare, baya kuma son ketare iyakar Ubangiji don har lokacin jinin biki Safiyyah take yi.
Ga Safiyyah da kunya, ire-iren hanyoyin nan na kwantar da hankalin miji a yayin biki ko al’ada nauyinsu take ji, wani irin nauyi abun yake yi mata, sosai take jin kunya in ya nuna mata irin abubuwan da yake so tayi masa wadanda su kadai zasu iya kwantar da hankalinsa, duk kokarinsa na fahimtar da ita shida ita babu sauran kunya ta wannan fannin, shekara goma ba wasa ba, ta bude idonta suyi irin rayuwar data dace dasu amma Safiyyah kunya da nauyi da gidadanci basa barinta, irin dai upbringing na gidan manya data riga samu da kuma rashin good socialization da zai bata damar samun exposure akan kula da miji, ko irin ‘yan karance-karancennan na zamani da ake daukar ilmin rayuwar aure a cikinsu Safiyyah bata yi. Kaidai barta a karance-karancen da zai zurfafa ilmin ta na Architecture.
Ganin karatun hikayoyin soyayyah take a matsayin bata lokaci ko rashin tarbiyyah. Not because she doesn’t love him. Amma ta gaza sanin hanyoyin kula da bukatunshi na aure yadda ya kamata, alhalin karshen duk wani so da soyayyarta ta diya mace a duniya tasan na mijinta Zayyan Rafindadi ne.
A’ah ita dabi’arta na kunya, russunar da ido, da kana’a, nature dinta ne da Allah ya halicceta dasu tun fil azal, kunya da kawaici da rashin zaqewa akan sexual relationship dinsu. Komai shi yake yi a gadon aurensu. Ita saidai ya barta dasu rufe ido da ji masa kunya, da kiran sunansa. Wannan ba zai zamo abun mamaki ba, in aka yi la’akari da irin (decent upbringing) din da Safiyyah ta samu a gida.
Har Sophie ta yada wanka Zayyan bai je Katsina ba, ya kuma gama shirya surprising dinta da tarewarsu a sabon gidansu dake cikin shahararren Estate dinsa da ya kammala, wanda sai yanzu Allah yayi kammaluwarshi, watau SUNSET ESTATE, Estate dinsu shida Safiyyah dake GUZAPE. A ranar data yada wanka wato ranar da ta kwana 40 da haihuwa ya shirya komawarsu gidan.
Cikin ikon Allah a ranar sai ga mahaifinta Malam Usman da kansa a gidansu ranar da suke shirye-shiryen tashi. Haroun ya kawo shi har Abuja tun daga Dandume, a motar Haroun din.
Nan suka shiga hidima da bakuntar babban bakonsu Malam, Zayyan da Safiyyah da su Sabah kowa hidima yake da zuwan Malam, su dora wannan tukunya su sauke wannan, ana wadata malam da cimaka ta alfarma. Ya wuni sur tare dasu cikin kauna da soyayyahr Uba mai girma, ya yi musu nasiha da wa’azi sosai akan muhimmancin karbar jarrabawar Ubangiji kowacce iri ce, komai dacin ta, da ribar dake cikin hakan watarana.
Ya tunasar dasu tanadin da Ubangiji yayiwa iyayen da suka haifi da ya koma. Tare dashi aka tare ranar da yamma SUNSET ESTATE. Ya kwana tare dasu a sabon gidan a ‘guest wing’ Haroun kuma a hotel ya kwana, kusan kwanan zaune sukayi ranar suka raba dare a falon Safiyyah shida Zayyan da Safiyyah, yana mai basu sirrin addu’oin neman biyan bukata, abinda ya tadowa Zayyan kewar Baba Bello. Suka kasa tafiya suje su kwanta har asubah suna like da Mallam.
Zayyan ya kara jin kansa maraya sosai da soyayyar da Malam kema Safiyyah, sai yanzu yafi jin kewar Baba Bello, ya san da Baba yana raye da abubwan dake faruwa da yawa basu faru ba, da tuni shi da Safiyyah sun ga gata a wannan haihuwar tasu, da kauna da tattali, a wannan lokacin da ba abunda suka fi bukata fiyeda kaunar iyaye da support dinsu.



