⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 7: Chapter 7

Tabbas da Baba Bello na raye, ba zai watsar masa da iyali yadda Mama tayi ba, alhalin tana ikirarin tana sonsa tana kuma kaunarsa, a matsayin tilon dan data haifa namiji ta kasa taya shi son iyalinsa. Sai yaji idanunsa sun kawo ruwa da hamma a lokaci guda, har Malam ya lura yace su tashi su je su kwanta haka.
Da malam zai koma a washegari yace tunda Safiyyah ta yada wanka, ta kuma samu lafiya zai wuce da Sabah da Rayyah Dandume.
Karon ta na farko da sake haduwa da Haroun kenan, tun bayan aurenta da yazo washegari daukar Malam zasu wuce. Gabadaya Haroun din Malam ya canza mata, ya zama babban mutum, Haroun ya samu cigaba sosai ta kowanne fanni na rayuwarsa, harkar danyen man fetur yake yi yanzu da ‘Dangote Refinery’, saboda abinda ya karanta kenan a jami’ar Maiduguri wato (Petro-chemical Engineering).
Bayan gaisuwarta da Haroun ya amsa ya kuma yi mata ta’aziyyah bai bar wata kalma ta kara shiga tsakaninsu ba. Bai ko kalleta ba, abin ya tsaye mata don kuwa Haroun a can baya yafi kowa shiga sha’aninta ita ke basar dashi. Sanda akayi aurenta kuma ya koma Nsukka yana hada kwalin karatunsa na biyu kuma tun bayan aurenta in zata iya tunawa Haroun bai taba kiranta a waya ko sau daya ba.
Al’amarinta da Yayanta Ridhwan (Yaya Shaikh) shi yafi komai bata mamaki akan na Haroun din Ammi, don in Haroun kishi yake tayi aure ta barshi, alhalin an san yana sonta tun tana karama, itama kuma ta san yana sonata koda bai taba furta mata ba. To Yaya Shaikh kuma fa?

Kalmar so ko kwalli daya bata taba gittawa a tsakaninta dashi ba. Gara Haroun zata ce hatta Ammi ta sha gaya mata son ta yake yi, tun tana karama, amma yana kallon kansa a wanda bai isa ya aureta din ba, kasancewasa almajiri ga Mallam.
A wannan zuwan da Malam yayi ne yake gaya mata cewa anyi auren Yaya Sheikh a Doha (Qatar), ya auri wata Shuwa Arab haifaffiyar Maiduguri da suka hadu a karatu mai suna Assafe.
Da Malam yace zasu tafi tare dasu Sabah Zayyan ki yayi, don yaga yadda zaman nasu ya zamewa Safiyyah abin debe kewa, bata shiga damuwa da tunani saboda kullum suna gefenta suna kwasarta da hirar Ammi, sai ya shigo falon suke musu sallama su shiga dakinsu data basu. Don haka zamansu tare da ita ya taimaka ainun wajen dawowar walwalarta.
Sai ya roki Malam alfarmar ya bar su Sabah su cigaba da zama tare dasu zuwa bayan sallah, don a lokacin an kusa shiga watan Ramadan saura sati guda wata mai alfarma ya kama.
Da kyar Malam ya yarda ya barsu, amma yace sallah da kwana uku lallai-lallai ya gansu sun dawo Dandume.
Malam da Haroun suka kama hanyar komawa Dandume washegari.

Kulawar mijin kwarai irin Arch. Zayyan Bello Rafindadi, da addu’ar caring iyaye masu riko da addini irin nata, sun taimaka matuka gaya wajen dawowar nutsuwar Safiyyah, bayan rashin IVF babyn da suka yi. A kullum yana karfafata da cewa “data haihu, da bata haihu ba shifa yana sonta a haka, she will forever remain his ALTER EGO, sa’annan the only partner da yake son ya rayu da ita a duniyarsa da lahirarsa.
Ba wani abu wai shi rashin haihuwa da zaisa ya juya mata baya. Yana rokon Allah ya taya shi akan hakan. Shi ita ya aura ba abinda zata haifa masa ba da baima sanshi ba.
Cikin kalaman sa na koyaushe Zayyan ya kan ce mata “koda zasu mutu basu haihu ba, bazai taba amfani da hakan ya wulakantata ko ya goranta mata ba, ko ya juya mata baya ba wai dalilin rashin haihuwa.
Ire-iren kalamansa masu dadi kenan da suka taru suka farfado da Safiyyah, ta soma komawa harkokin ta na yau da kullum, bayan rasa dan da suka haifa ta hanyar Dashe (IVF).
A wannan gabar ne kuma bayan dawowarsu SUNSET ESTATE Zayyan ya bata gwaggawaban jari, yace ta soma business din duk da take so, duk don ta kwantar da hankalinta, da kokarinsa na faranta mata, a bisa wuyar data sha wajen samun ciki da haihuwar In Vitro Fertilized Baby dinsu, wanda ya kira da suna a cikin zuciyarsa “Areef”.
***** ***** ****

Kudin project din wani Estate da yayiwa gwamnati ne ya fito a goman karshe na watan Ramadhan, ya samu kudi masu kauri a hannunsa, aljihunsa yayi nauyi sosai. Abinki da Da nagari, ba wanda ya fara tunawa as usual idan ya samu kudi masu kauri a lokacin sai mahaifiyarsa, Mama Fatu.
Tuni ya manta da bacin ran da Mama ta saka shi a ciki watanni kadan baya da suka gabata, don shi duk wata nasararsa a rayuwa, yana fara dangantata ne da iyayensa.
Don haka sune na farko da yake tunawa idan alkhairi irin wannan ya same shi. Yayi ma Baba Bello Sadaqah sannan yayiwa Mama Fatu hidima. Gashi ya jima bai je Katsina ba yayi kewar Mama. Don haka ya samu Safiyyah har daki yake gaya mata cikin farin ciki.
“Sophie kina ina ne? Zo daga kusa ki ji?”
Ta fito daga daki tana daura kallabinta, “gani nan Habiby, wani abu?”
Suka game a karamin falonta, da rabi-rabin runguma, saboda ya taho da sassarfa ne itama ta fito da sauri, ya riko kugunta ya zagayeta da hannayensa biyu yana murmushi irin na namijin da aljihunsa ya cika da albarka a gaban iyalinsa. Yace ma Safiyyah.
“Wannan sallahr so nake zan gwangwaje Mama da wani abu mai daraja, wane kaya ne na kwalliyar mata suka fi kowanne daraja?”
Safiyyah na murmushi ta sakalo hannayenta a wuyansa itama, tace “Gold! (Zinare). Shine karshen kwalliyar mata mai daraja”.

Yace “to Alhamdulillah. Zan sayama Mama sarka da dan kunne da zobe da warwaro na zinare don in gwangwajeta ba zatonta. Na san Mama da son kwalliya. Kudinnan dana gaya miki inata jira su fito na project din Bwari, yau sun fito cikin ikon Allah.
Yace “bana taba manta wata sallah ina dan shekara goma. Baba yazo bashi da kudi isasshe a hannunsa, yace iyalinshi mu hakura da kayan sallah, saboda ya samu yayi wasu abubuwan muhimmai da ‘yan kudin hannunsa.
Mama sai tace “ai ba komai Babansu, Allah ya dada rufa mana asiri Baban Baffa.
Sai ta dauki sarkarta ta zinare ta siyar, tayi mana kayan sallah, ta baiwa Baba ragowar kudin tace,
“kayi duk hidimarka da sauran kudinnan Babansu Baffa”.
Tun lokacin abun ya tsaya min a rai. Don naga wani irin feeling na godiya da bazan taba mantawa ba a fuskar Baba ga Mama. Na kudurce nikuma sai na biya Mama ‘gold’ dinta duk sanda Allah ya bani gwaggwabar dama.
Ya rubuta cheque na kudi masu yawa ya baiwa Safiyyah wadanda har saida suka bata tsoro, yace “Sophie, so nake Mama na tayi gayu da babban Zinare, ta fito kamar tauraruwa Zahra a cikin mata a wannan sallahr”.
Safiyyah ta karba tana jinjinawa halarcin Zayyan akan son iyayensa, tace “amma Habiby, tare da kai zamuje mu zabo ko? Yace “a’ah ni mace ne? Ina nasan design mai kyau? Kawai kije ki zabo, sannan ki sayawa su Zahra suma duka kanana da bai kai na Mama girma ba. Da kuma amaryata Sabah da kanwata ta kaina, Rayyah”.

Nan suka zauna bisa doguwar kujera three seater, yayi mata bayanin yadda yakeson na kowa ya kasance, da sauran mutanen da zasu yiwa kayan sallah a cikin kudin bayan sakon Mama, dama duk shekara ya saba hakan, ‘yan uwanshi kaf da nata, da iyayenta da nashi babu wanda baya yima kayan sallah na gani na fada. Kai hatta dan almajirin gidansu Safiyyah wani yaron dake zama gidansu yana zuwarma Ammi aike mai suna Saminu, ya shaida soyayyar Zayyan ga ahalin Safiyyah, don duk shekara bandirin shaddah baya wuceshi shima, duk sallah karama Zayyan bai mantawa dashi. Balle kuma kannenta uku, wato Sabah da Rayyah da Rayha, koda ba’a hannunsu zasu yi sallah ba ya maida yi musu kayan sallah cikin obligations dinsa (hakkinsa), tun bayan dawowarsu Abuja.
Sosai Safiyyah ta yi masa addu’ar karin budi da nasara cikin al’amuransa, tayi godiya yadda ya dace macen kwarai ta godema mijinta in yayi hidima ta bajinta irin wannan, ta kuma kara alfahari da Habiby dinta domin ya cika dan halas din da kowacce Uwa zata yi fatan haifar mai kaunarta da yi mata halarci kamarshi.
Baya taba iya yin dogon fushi da Mama Fatu (no matter how) yadda zata bakanta masa da halinta.
A kullum fatanta shine na samun ‘ya’yan da zasu yo gadon wadannan nagartattun halayen nasa, Zayyan Bello ya cika dan halas, uwa da ubanshi babu sama dasu a komai, tana addu’ar Allah ya bata ‘ya’ya daga gareshi su gado komai nasa, itama su ji kanta a tsufanta, ko ba don bata da shi ba.

A washegarin ranar suka je wani dankareren shagon zinare suka zabi latest design na set din wani white gold saukar jiya-jiya daga Dubai. Ya lashe miliyoyin kudin da Zayyan ya warewa Mama har da dori. Ta kuma sayawa sauran kannensa dan kunne kowacce yadda yace tayi. Sannan suka zarce kasuwar Wuse market tayi siyayyar komai da ya lissafa mata na kayan sallar jama’arsu, karkashin rakiyar kannenta su Rayyah, kaya ta zabowa su Zaitoon na gani na fada, masu tsada da quality, ta hada ma Mama da saitin turarukan (Aventus for Her) da ya taba gaya mata cewa dashi kadai Mama Fatu take amfani a matsayin nata neman albarkar, ta sayi wani tsadaddden akwati dan karami mai kyau, ta zauna ta jera turarukan nan da saitin (white gold) din a cikin akwatin gwanin ban sha’awa sukayi kyau a cikinsa. Kai kace wata yarinya budurwa za’a kaiwa toshin sallah.
Sannan ta siyowa dukkan kannenshi da kannenta kaya kamar yadda ya tsara.
Da Zayyan ya dawo gida ta nuna masa sayayyar duka tayi masa bayanin na kowa, yayi murna sosai da ganin sakon Mama da kannenshi, ya jinjina ma fasaharta da iya zaben design din zinare. Amma yana bude na su Sabah ya dauki atamfar yana juyawa a hannun shi, ko daga kalarta da rashin nauyinta ya san bata fi atamfar dubu takwas ba, ya dubi Sophie sama da kasa ya hade rai yace.
“Safiyya menene haka? Me kike nufi da hakan?”

Hankalinta ya tashi, ta dauka wani abu ne tayi masa ba daidai ba, sai taji yace yanzu don me zaki siyowa su Sabah kaya masu arha, su Hatoon ki siyo Swiss laces masu tsada, shin akwai bambamci tsakaninsu ne a gurina? Ban ji dadin abinnan da kika yi ba ko kadan, baki kyauta min ba”.
Sai ta soma bashi hakuri, tace “ba haka bane Habiby, kudin ne sunyi kasa sosai, sai naga cewa su Zahra yafi dacewa da wannan, su din kannenka ne da kuke ciki daya, hakkinka ne ka yi musu komai yanzu, musamman da hakkinsu kamar a wuyanka yake, su Sabah kuwa Ihsani ne tsakaninku wanda bai zame maka dole ba”.
Cikin takaicin kalamanta yace “sannu Mrs. Right, Gwanin na iya sarkin iyawa, toh canjin da kika dawo mun dashi me zanyi dashi? Idan har na isa dake ki koma kasuwar nan, abinda kikayi wa su Hatoon, shi nake so inga anyi wa su Sabah…”.
Dolenta suka koma kasuwa washegari aka sake siyo kayansu Sabah, don ransa ya baci sosai a ranar, ya dauke mata wuta da wannan abinda tayi, har saida ta gyara kuskurenta, ta kawo ta nuna masa ta bashi hakuri. Sannan ya sauko, ta hadawa kowa nashi aka aika kayan Katsina. Infact duk kannensa da aka kai musu kayan sun yaba, kowa yayi murna ana ta bugo waya ana yima Yaya Baffa godiya don sun dauka shi da kansa yaje ya sayo masu.
Mama kam kuka ta saka, tace wai yau Baffa ya tuna mata Baba Bello, komai Baba zai saya mata sai ya zabo na kerewa sa’a, don ya san ta da son special abu da basu cika gari ba, Mama tun asalinta mace ce mai son gayu da kashe kala, tana matukar son kayan ado na yayi, tana harka ta jiki sosai da manyan matan ‘yan bokon Katsina, saboda farin jinin Baba Bello.

Da sallah tazo, Zayyan da Safiyyah dasu Sabah suka yi shiri suka wuce Katsina don halartar shagalin bikin sallah kamar yadda mafi akasarin mazauna birnin tarayyah ke yin sallah a garuruwansu na haihuwa.
Gidan marigayi Prof. Bello Rafindadi gida ne da ake yin hidimar abinci ta alfarma duk ranar sallah, gate dinsu a bude yake. Wannan ya shiga wannan ya fita. Ana dafa abinci kala-kala ana bayarwa ga baki da makwabta. Haka ake yi duk sallah tun Baba Bello yana raye. To yau ma hakan ce ta kasance a gidan.
Ya kasance a kowanne washegarin sallah Mama Fatu tana gayyatar matan abokan Baba da kawayenta, suzo gidanta a ci a sha da cimaka ta alfarma da snacks, su wuni sur har yamma suna hira, zaki gansu duka hamshakan mata ne kusan su goma a falon Mama, ana hira ana nishadi, to ko bayan rasuwarshi Haj. Fatu ta cigaba da al’adar tata, ta gayyato mutanenta ranar sallah.
Wannan shekarar ma kamar ko wacce, kawayen Mama sun zo harda matar VC mai ci a yanzu na jami’ar Umaru Musa ‘Yar adua, Safiyyah tazo falon ita da kannenta zasu yiwa mutanen Mama gaisuwar sallah, Sophie ta sha ‘swiss lace’ dinta ‘purple’ me kyau, kannenta Sabah da Rayyah dake biye bayanta sun sako kayan da Zayyan ya siya musu na sallah iri daya sak da na yaran Mama wato su Hatoon, su Sabah sun yi kwalliyar sallah da kayan ne saboda Uncle Zayyan yana gidan, suna so su nuna mishi godiyarsu, ta hanyar saka kayan.
Don yace dasu da yamma in sha Allah idan ya dawo daga cikin gari za’a yi (family picture) harda su kafin ya maidasu Dandume gobe kamar yadda ya alqawartawa Malam. Idan su Zahra da Zaitoon sun iso daga gidajensu. Shiyasa suka saka kayan ba tareda sun kawo tunanin komai a ran su ba.

Suna shiga falon Mama tayi arba dasu, ta kalli kayan dake jikinsu, nan da nan annurin fuskarta ya dauke kaman an aiko mata da saqon mutuwa. Tana tozali da kayan jikinsu Sabah ta danna ashar a zuciyarta, tace a ranta lallai ma Safiyyah da take rainawa ta bari tayi kauri da yawa, ta samu Baffa da yawa, me Safiyyah ke nufi na sakawa kauyawan kannenta kaya irin nasu Hatoon?
Haka suka karaso suka gaishe da Mama da kawayenta Mama na zabga musu harara daga su har Safiyyah din. Hajiya Yabi kawar Mama ta lura da irin kallon da Mama ke musu sai kawai ta bude baki tace.
“Wai ni kam Haj. Fatu, Safiyyah har yanzu bata haihu ba ko?”
A gaban kawayenta Mama tace “tayani tambaya, shiru, har yanzu, tamkar Malam yaci shirwa”. Haj. Yabi ta ce “kuma kuke zaune haka baku tashi tsaye akai ba? A can kan tudu layin gidan iyaye na akwai wani mai bada maganin haihuwa, maganinshi kaifiyyan, in kunaso zan karbo mata”.
Sai ta kalli Safiyyah wadda hankalinta ya soma tashi ranta kuma ya soma baci da jin zancen da suke yi a kanta, ai har abada ba ita ba sake neman haihuwa tawata hanyar balle ta hanyar malaman tsubbu, ta riga ta tuba wa Allah da Habibiy dinta, tace bazata sake ba. Haj. Yabi tace.

“Diyata Safiyyah ina fatan zaki sha maganin in an amso, don magani ne me tsada. Kar na karba kizo baki sha ba”.
Safiyya ta gyada kai kawai amma ko motsi da bakinta ta kasa. Mama ta zucciya da banzan data yi musu, ta daka mata tsawa a cikin mutane tace “baki ji ne ana miki magana kinyi shiru, kar ta kashe kudinta a banza a wofi ta karbo miki maganin baki sha ba.
Ni ban ma cika son harkar maganin gargajiya ba Haj. Yabi, nafi yarda da asibiti, amma tunda na matsu na ga diyan Baffa gara a jarraba can din, ba’a san inda za’a dace ba, tunda anyi na asibitin duk ba nasara”.
Duk sauran matan suka ce “exactly, gara a jarraba na gargajiya”.
Baki daya falon sai ya karade da zancen rashin haihuwar Safiyyah har tsayin shekara goma da aure, kannen sa daga mai biyu sai mai uku, kowacce na tofa abinda take tunanin shi ya hana Safiyyah haihuwa, har da masu cewa ko PCOS gareta, don mafi akasari shi yake hana mata haihuwa yanzu.

Safiyyah da kannenta duk sai sukayi jigum-jigum a zaune, suka rasa abinda ke musu dadi, ba zaginta ake ba amma hakan fallasa ne da gori a fakaice, suka rasa abunda zasu ce, duk Safiyya ta tsargu da kanta, taji kamar tayi wani gagarumin laifi ko abun kunya, wanda al’umma ta kasa yi mata uzurinsa, wani irin kuka na takaici ya taso mata.
Sabah ta fahimci hakan, tayi maza ta kama hannunta suka mike suka bar falon, uffan basu ce ba.
Suna fita Hajiya Yabi ta dubi Mama cikin damuwa tace,
“ina fatan dai ba maganar da nayi bace ta bata ran surukar tamu?”
Mama tace “oho mata, ita ta sani, daga abun kirki? Yarinya sai kafirin zurfin ciki da nuku-nuku, gata da sumumu-kasau irin nasu na ‘ya’yan Alarammomi da ka kan rasa gane zuciyarsu”.
Fitarsu harabar gidan suka ci karo da shi yana kokarin shigowa da hancin motarsa bakar ‘Ford Mustang,’ Arch. Zayyan ya sha adon sallah masha Allah dashi cikin farar shaddah bugaggiyar Wagambari babbar, bugun hannu, ba karamin kyau da kwarjini da kamala shigar yau ta kara masa ba. ta kuma kara fiddo zahirin kuruciyarsa ainun.
Da annuri sosai ya shigo gidan, amma yana ganin fuskarta ya gano akwai abunda ya faru da ya canza mood dinta. Suna tsaye a kofar shiga babban falon gidan itada Sabah. Ya adana motar a parking lot na gidansu a nitse, bai fito ba ya sauke glass na barin da yake zaune, sai ya yafitota da hannunsa, yace.

“Sabah, ku ara min Yaya Safiyyah mana, ku shiga gida zan ganta, gata nan zuwa yanzu”.
Sabah da Rayyah har suna hada baki wajen cewa “Toh! Uncle Zayyan”. Suka juya zuwa cikin gida.
Ganin Safiyyah taki motsawa daga inda take tsaye bayan wucewar su Sabah ciki, sai ya fito ya kama hannunta, dole ta bishi kamar rakumi da akala zuwa motar, ya bude suka shiga gidan gaban motar ya rufe, dama glassanta duka masu duhu ne (tinted), motar tana kunne, don haka AC na aiki. Ga kamshin ‘Car fresh’ din motar mai dadin kamshi da ya hade da kamshin turaren jikin Zayyan na mazan da suka amsa sunansu (Ultraviolet), su suka hadu suka dawo da nutsuwa da salama a zuciyar matarsa Safiyyah, ta jingina kanta a jikin kujerar bayanta, ta hau sauke ajiyar zuciya a jejjere, ba tareda ta ko san tana yi ba.
A hankali Zayyan ya mika hannayenshi biyu ya rungomota jikinsa, bakinshi a kasan wuyanta ya sumbaceta lightly, yace.
“Sophie yaya akayi ne? Wani abu ya faru da bana nan ne? Na ganki moody”.

Safiyyah tayi shiru, haka kawai taji kwalla na kara ciko mata, tace “Habiby, ina so in haihu ne, kuma da wuri!” Yace “Yaa Subhanallah! Ita haihuwar nan ba’a hutawa da yin ta? Tukunnama yaushe aka gama jegonta? Kuma shin me ya kawo zancenta?”
Daga Safiyyah babu amsa, sai ma idonta daya karasa cikowa taf! Da hawaye. Kiris suke jira su sauka kan kuncinta.
Zayyan yayi-yayi ta gaya masa abinda ya kawo zancen haihuwa amma Safiyyah ta ki. Kada ya zama cewa ko ta kai karar Mama da kawayenta wajensa ne.
A karshema da ya dameta da tambaya sai ta kifa kai a kirjinsa ta fashe da kuka mai cin rai.
Bai iya yin komai ba ko hanata kukan a wannan lokacin, banda ya rungumeta cikin kirjinsa tsam-tsam, yana shafa bayanta a hankali cikin lallashi. Ya kuma barta tayi kukanta ma’ishi, yana magana cikin lallashi, kauna da soyayyah masu yawan gaske, wadda ta bayyana kanta a zuciya da tone din furucinsa, Zayyan yace.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *