⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 9: Chapter 9

Kasancewar gidan Arch. Murtala babban gida ne na zamani ginin (Bungalow) a shiyyar Ikoyi har da tankasheshen sassan baki, anan Baba Murtala yasa aka saukeshi.
Saida yayi sallahr azuhur yayi wanka ya huta, sannan Baba Murtala ya turo Seyi, don yayi masa jagora zuwa cikin gida wajensa.
Har falon da iyalin sa kadai ke shiga Baba Murtala yayi umarni ga Seyi ya kai shi.
Baba Murtala dai kamar ya hadiye dan nasa saboda kulawa da maraba, ya rasa ina yaka saka ina yaka aje da shi, duk sanda yazo gidan haka yake nan-nan da shi, Zayyan na shirin zama akan kilishi Baba Murtala yace “zo zauna nan a gefena kaji Zayyan, Da na na kaina, kullum na ganka ji nake kamar da Bello nake tare.
Ka jima ba ka zo gidan naku ba, yaushe rabon ma ka zo har na manta, bana jin duk kannenka ka san su gabadaya”.
Ya dauki waya ya kira maidakinsa Haj. Nana Aisha, wadda ita kadai ce matarsa tun ta lalle, yace da ita “Da na Zayyan ya iso. Maza a Shiryo abincin rana a kawo mana nida shi, muna karamin falona”.
Daga nan inda suke zaune Zayyan na iya jin muryar Haj. Nana tana kwalawa daya daga cikin ‘ya’yanta mata kira.
“Azeezah! Azeezah!”

Daga can nesa ya jiyo amsawar Azeezah din, da wata ‘yar gayun murya ta yanga da lalaci, tace.
“Na’am, I am coming Mum”. (Ma’ana ina zuwa Mama).
Ta fito daga dakinta ta iske Maman nasu a kitchen, tana shiga Haj. Nana ta hau fada “sai ki kule a daki da waya a hannu, ki barni da aikin abinci nikadai ko, na rasa mace irinki Azeezah, komai naki kamar bana mace ba, sai kwalliyar banza da iyayin wofi kika sani, amma harkar kitchen data hankali ko oho, ni Nana Aisha ina tausayawa mai tsautsayin mijin duk da ya kwashe ki”.
Azeezah ta zumburo baki, kafin tayi dariya, bata dai ce komai ba. In da sabo ta saba da wannan gorin na Mum dinta. Abin haushin har Daddy haduwa suke suyi tayi mata gori. Cewa ita muna mata ce. Duk abu na matan kwarai baza’a sameta ciki ba sai chatting a waya da midnight call. Mum din tace,

“ki dauki abincin da na shirya daga dining ki kaiwa Daddy da bakonsa a falonsa, na kai dining yace a kai musu falonsa”.
Azeezah ta ce “toh” sannan ta juya don cika umarnin mahaifiyar tata tana cewa a ranta ko waye wannan bakon da Daddy ya kai har karamin falonsa wanda su kadai ke da access din shiga wajen.
Tana tafiya cikin rangaji tamkar reshen bishiya ko hawainiyar da bata son taka kasa don yanga da iya takun tafiya. Tamkar budurwar Dawisu don class da iya ado.
Haj. Nana tace kiyi sauri mana, kina wannan tafiyar taki kamar ta hawainiya, yace a kai da sauri. Shi da dan sa ne dan wajen marigayi Bello Rafindadi.
Kiyi maza kai musu, kizo ki rakani saloon Agege”.

A bakin kofar shiga falon ta tube takalminta dauke da katon tray ta shiga falon, saida ta shiga sannan ta tuna bata yi sallama ba, tayi maza ta koma tayi sallamar ciki muryarta ta ‘yan gayu, don tasan kadan da aikin Baba ya dizgata gaban bakonsa, akan rashin sallama.
Ilai kuwa saida Baba Murtala ya ce “da baki koma kinyi sallamar nan ba Azeezah da tamu ce dani da ke”.
Zayyan ya dago kai daga kan wayarsa yana kallon ‘yar gayun yarinyar dake shigowa. Bata da tsayi can kamar Safiyyah amma tafi Sophie kakkauran jiki irinna ‘yan ajebo, ya sake kallon ta karo na biyu yana tuna sanda ya santa lokacin aurensa da Sophie da suka je Rafindadi tareda Mamanta Haj. Nana lokacin bata fi shekaru goma sha biyu ba, lokacin ko kirgen dangi bata fara ba, yayi mamaki da yaga itace yau tayi wannan girman haka na farat daya?
Yanzu akalla zata yi shekaru ashirin da biyu, komai na budurci da hutu ya nuna a jikinta.

Ta shigo da tankareren tray din da gidajen manyan masu kudi kawai zaka ga irinsa, ta ajiye akan center table din dake gabansu, ta gaida shi a gajarce ko amsawa Zayyan bai iya yayi ba, sakamakon wani tunani maras tushe da ya zo ya sarkeshi a nan take.
Tunani ne yazo masa cewa. Ba don ba don ba, ai da ya gwada cewa Baba Murtala ya bashi auren ‘yarsa Azeezah ya kara da ita, in yaso ta haifa masa Da, ya dauka ya baima Sophie ta rike ta rainar masa a matsayin nata, a huta matsalar haihuwa dake damun Sophie.
Abinki da namiji wanda ya fito daga gida cikin kishirwar mace, a take ransa ya kyasa masa Azeezah. Yayi ta kawata masa suffofinta.
Ba Azeezah ba da take zukekiyar yarinya mai class, wanke hannu ka taba, da iya gayu da takun tafiya mai jan hankalin da namiji, a wannan lokacin ko wadda bata kaita komai bama Zayyan ya gani kyasawa zaiyi a ransa.
Saboda wawakeken gibin da Safiyyah ta bari a ransa daren jiya da yau da safe kafin ya fito daga gida.
Sanye take da fitted gown ta wani bakin lace mai adon ruwan gold, rigar ta bi dirin jikinta ta kwanta sosai, ta fidda duk wani tudu da kwari na jikinta, a kanta kananun kalba ne na karin gashi (attachment) wanda in ba gaya maka tayi ba bazaka taba gane cewa sakawa tayi ba, ta yi ado dashi ta dunkuleshi ta baya, wani kuma ta zubo dashi gefen fuskarta.

Baba Murtala ya lura da kallon ‘yar shi Azeezah da Zayyan yake tayi a sace, har ta juya zata bar dakin, tana gaida shi amma tsabar yayi nisa a tunani bai ma ji gaisuwar tata ba.
Tunani kawai yake yana sake cewa a ransa “ba don ba don ba! Ai kawai da ya gwada neman aurenta”.
Baba Murtala yayi murmushi yace “kanwarka kenan, marar kan gadon gidan, “Azeezah!”.
Duk cikinsu itace sai a hankali, komai sai an kwabeta na rasa mai yasa bata taso da kan gado ba, ita ba ta fari ba ita ba auta ba.
Ko don ita kadai ce mace a cikinsu?”

Azeezah ta ciji lebe tasan mawuyaci ne dama Baba bai dizgata ba shiyasa bata so Mum ta saka ta kawo masa abinci falo musamman idan yana tare da baki.
Baba Murtala yayi murmushi yace “tana gaisheka” nan da nan ya shiga nutsuwarsa ya yi maza ya canza fuska ya mayar da ita ya dinke tsaf, ya amsa a gajarce kuma ciki-ciki. Azeezah bata damu ba, ta juya zuwa kofa, duk dakin ya bade da kamshin wani sassanyan turaren Humra na mata data shafa, mai sanyaya rai. Zayyan ya bita da kallo, kugunta kamar zai karye don shape, sai kadawa bom-boms keyi kamar da gayya take juya jikinta.
“Yaa Subhanallah” inji Zayyan a zuciyarsa. Baba Murtala ya lura dan nasa ya tafi da yawa sai ya cetoshi da cewa,
“bisimillah Zayyan, mu ci abinci ko?

Muna da wuraren zuwa da yawa a yau, da abubuwan da zamu fara gabatarwa fal. Don haka ka ci abinci ka koshi ka ji ko.
Na gaya maka two weeks project ne, so probably zaka zauna anan Lagos har kwana goma sha hudu”.
Zayyan ya gyada kai, ya nutsu ya maida hankalinsa ga Baban nasa, ya bude warmers din alfarma da Azeezah ta ajiye musu ya fara serving dinsu shi da Baba, kowa a faranti daban.
Baba Murtala ya kasa shiru da canzawar yanayinsa. Don gabadaya walwalarsa ta dauke.

“Zayyan are you okay? Azeezah ce fa, kanwarka ta gidannan naga kamar baka gane kanwar taka ba, last week ta kammala karatun digirinta a Cyprus ta dawo gida”.
Zayyan yaji kunya tunda Baba ya gane kalar kallon da yakema diyarsa, a fili yace “umh” kawai, don jikinsa yayi sanyi kuma, a ransa yace “karewar hutu a kasar waje tayi karatu. To akul! Dina”.
Suna cin abinci Baban ya shiga bashi labarin diyarsa Azeezah, a lokacin da tana kankanuwa, yace hasali duk cikin yaransa Azeezah daban ta zo, itace bata da kwakwalwar karatu sai ta giggiwa, kullum ta karshen aji take dauka a makaranta.
Ya samu ta gama sakandire da kyar da sidin ludayi, sai tasa rigimar ya kaita waje tayi karatu don sakamakonta bai yi kyau ba, da kyar ya samu wata makarantar kudi (private university) ta dauketa a kasar Cyprus, shi yasa da ya kaita makarantar ya barta ta karanci abinda malaman jami’ar suka zaba mata (Make up Artistry) sabida kanta bai jan karatu sam.

Kuma da yake tana da interest akan kwalliya din tun tana karama hobby dinta ce, ta tsaya ta maida hankali ta kawo masa dan shakwa-shakwan certificate na zama professional Make-up Artist.
Yace komai Azeezah tayi sai an yi mata gyara, komai sai an saka ta a hanya, kuma bazata rike na yau ba gobe sai an maimaita, in ba haka ba sai an ga kuskure da wauta a ciki, ya tambayi Zayyan, shin ko ya taba ganin yarinya mai gurgun bahagon personality irin na ‘yarsa Azeezah?”
Sai kuma yagirgiza kai, cikin alhini yace.
Ba don kamar ta daya da ni ba, da tabbas nace canzawa Haj. Nana ita akayi a asibiti, don dakikiya ce ta gaske Azeezah”.
Abun ya baiwa Zayyan matukar dariya, musamman ta sigar da Baba yake bashi labarin kamar da sa’ansa yake hira, har sai da Zayyan ya murmusa, ya ce “haba dai Baba!” Yace “Allah Zayyan Azeezah halinta sai ita, ni dai nan kusa ban taba ji ko ganin yarinya mai son rayuwar jin dadi na rashin kangado da son kyale kyalen duniya irin Azeezah ba.

Itace ta biyun karshe a cikinsu, amma kamar diyar fari sabida tsabar wauta da rashin sanin ya kamata, duk cikin ‘ya’yansa yace babu mai son duniyarta, da son rayuwar hutu da jin dadi zallah na wuce kima irin Azeezah.
Can Baba Murtala yace “a kullum in lamarinta ya dameni ina gaya mata bamu zo duniya don mu huta ba, babu wani jin dadi ga dan adam a wannan rayuwar sama da ya bautawa Allah ya nemi abin rufin asirinsa, hutu sai a aljannah, jin dadi zai dauwama ne kadai idan ka bautawa Ubangiji da lokacinka da lafiyar daya baka. Ka tsare sallolinka.
Kullum nayi gabas, ita sai tayi yamma, in nayi kudu, sai tayi arewa. Kamar bani na haifeta ba. Bata gado halin kowa cikin mu ba tsakanin ni da Haj. Nana wajen sanin abinda ya kamata a rayuwa. Halinta na son kyale-kyalen duniya sai ince a rariya Azeezah ta tsinci abinta.
Yace daga Ashraf sai Aman sai ita. sai kuma autansu Saifullahi, suke nan yake dasu a gabansa yanzu. Babban dansa Walid ya jima da rasuwa a dalilin cutar koda, haka mai binsa mace Taqiyyah ta rasu gun haihuwa.
Zayyan ya muskuta cikin jinjina labarin Azeezah da mahaifinta yake bashi, a cikin yanayin sautin Baba Murtala yana nuna matukar bakin cikinsa da damuwarsa akan halayen diyar tasa cikin karyewar murya irin ta mahaifin kwarai da ya damu da tarbiyyar ‘ya’yansa, ya kuma tsaya ya karancesu sosai, dukkan dabi’unta yace ko kadan baya sonsu, kuma basa masa dadi a rai, ba yadda zaiyi da ita ne, ya kasa canzata, da ana sayarda halin kwarai da ko nawa ne ya saka ya sayawa Azeezah ya canza mata halayenta, sai Zayyan yace a ransa.
“Allah daya gari bambam kenan! Ita wannan komai nata ‘opposite’ din na Nana Safiyyahrsa!

Sophie abinda bata so kenan wato kwalliya, gayu da kyale-kyalen zamani, Safiyyah bata damu taji dadi ba, ita dai tayi ibadah, kuma ta kan ce duk wani abu da zai janyo mata idon mutane kanta, ko ya zame mata kyalkyalin da zai ja hankalin maza a kanta, ko ya janyo idon mutane gareta wanda har zaisa suyi mata kallo na biyu, bata maraba dashi.
Watau Safiyyah bata son ta burge kowa don a wurinta ido guba ne.
Komai da Baba Murtala yace halin Azeezah ne sai ya ganshi kishiyar na Safiyyah in one way or the other. Duk yadda ya so ya yakice tunanin Azeezah da labarinta tun a wurin hakan bai samu gareshi ba.
Har karanta wasikar jaki yakeyi shikadai. Yana comparing and contrasting halayen nasu. Yace Safiyyah mai kokari ce, kuma zaqaqura a harkar, karatu abin mamaki ita kuma wannnan Babanta yace dakikiya ce.
Safiyyah mai gudun duniya wannan mai matukar son duniya, da son jin dadin dake cikinta. Yayinda Sophie ko kadan bata damu da jin dadi ba.
Baudaddun halayenta da yaji daga bakin Babanta yana mai kuka dasu, shi a matsayinsa na namiji sai suka bashi sha’awa, sabida wasu exceptional characteristics ne da bai saba ji ba, akwai abin so da sha’awa a cikinsu duk da haka, is rare a samu irinta, shi sai yaga ba matsala bane halayen nata face abin sha’awa tunda mace ce. Karewa ma su suka ja masa wani sabon attraction akan Azeezah Murtala, wanda yasa ya shiga damuwa da lamarinta, madadin yaji baya sonta ko ya tsani halayen nata. Kwalliya ai abar so ce ga Da namiji, haka yake so Sophie ta koma, mace ‘yar zamani mai ji da class da gayu, amma ita kullum sai Hijabi.

Yayi ta tunanin yadda yaga Azeezah take twisting jikinta in tana tafiya kamar tarwada a cikin ruwa, kai kamar da gayya take juya lafiyayyun cikakkun mazaunanta suna wani girgiza cikin tafiyar da hankalin mai kallonsu.
Tunanin halittar Azeezah da ya samu kansa ciki ya kuma dinga yi masa dadi ne yasa bayan ya koma masaukinsa, sai kawai ya kwanta rigingine ya ki kunna wayoyinsa kwata-kwata, don ma kada a katse masa tunanin da yake ciki a lokacin.
Yanata karfafa kansa kan me zai hana ya gwada yiwa Baba Murtala maganar ya bashi diyarshi Azeezah ya aura? Shi yana son kwalliyar, yana son kyale-kyalen nata, shine abinda ya rasa a nasa iyalin, da kuma….. Azeezah kawai ta burgeshi. Kuma ga dukkan alamu AZEEZAH MURTALA ta hada duka abubuwan da ya rasa a gidansa.
Safiyyah ta fado masa a rai, a lokacin da yaji kwanyarsa ta lullube da tunanin auren Azeezah, yana ta tuna jerarrun hakoranta, kissable lips dinta. Wani irin a jere ya hau sakin ajiyar zuciya ba sassautawa, yana gayawa kansa koma wane irin tunani ne ya samu damar kutsowa cikin rayuwarsa akan wata diya mace daban bayan Safiyyah a yau, Safiyyah ce sila, ita ta bada kofa, ta bashi dama, ita ta jawo masa koma menene.
Data watsar dashi daren jiya ya kwana da fushinta, ta barwa matan duniya shi akan titi suke daukar hankalinsa, taki alkinta masa sha’awarsa, sabida rigimarta na son wata haihuwa da bata isa ta baiwa kanta ba, karshe ta barshi stranded (a ragaice) bisa titi yana satar kallon ‘yammata.

Hausawa ma sunce “sai bango ya tsage kadangare ke samun kafar shiga”. Don haka kara aure da diyar Baba Murtala gareshi yanzu ba zai zama laifi ba, don kare kansa daga fadawa wani hali na daban. Shi kadai yasan yadda ya wayi gari jiya da Sophie ta juya masa baya taki tallafarsa. Sophie taki ta gane shi mai tsananin son kasancewa da mace ne, haka halittarsa take, son samu matarsa Safiyyah ta daina saka kunya irin wadda ita Safiyyah ke sakawa a tsakaninsu, tayi kokarin gyara (sexual life) dinsu, ta maida hankali a kanta fiye da komai ta hakura da batun haihuwa tunda Allah bai ga damar basu ba, amma a’ah ita Sophie yanzu ba soyayyarsa ce a gabanta ba, kullum hankalinta naga kulafucin son samun Da tareda shi, ita dai ta samu haihuwa ta kowacce hanya, hankalinta ya tashi daga kan wajibinta (kula da aurenta) zuwa abinda ba wajibi ba (neman haihuwa).
Haihuwa idan Allah bai ga damar bata ba wa ya isa ya bata? Yayi duk iya kokarinsa akan Sophie ta yarda da hakan abu ya faskara. A wannan lokacin Arch. Zayyan Bello, ya tabbatarwa kansa cewa yanada bukatar kara aure, musamman da yake da tabbacin kowa zai aura zata bi bayan son da yake yiwa uwargidansa Safiyyah ne.
A duk yadda nature din Safiyyah yake yana son abarsa a haka, yana darajjata, yana daukaka martabar al’amarinta a duniyarsa da cikin rayuwarsa fiyeda na kowacce mace, bayan wadda ta kawo shi duniya (Mama), amma yau ya tsinci kansa dumu-dumu da son kara aure bayan Safiyyah, amma ga wani hanzari; macen duk da zai aura, zata zamo masa matar biyan bukatar gangar jikinsa ne kawai, sabida ta wannan fannin Safiyyah ta gaza, amma soyayyarsa da kaunarsa har abada suna ga “stammerer Hijabhie dinsa ta gargajiya wato Arch. Safiyyah Usman Dandume”.

Sannan kowacece Allah ya rubuta zai aura, ko da kuwa Azeezah dince ko watanta, idan ta haihu Safiyyah zai kyautarwa abinda ta haifa, in sha Allahu.
Wannan wani alkawari ne da Zayyan yayi da zuciyarsa yau, bayan samun kansa da sha’awar kara aure, zai haifi Da da matar ya mallakawa Sophie, in dai Dansa ne halalinsa to zai kyautar dashi ga Safiyyah. In fact, sai sun yi da wajewa/yarjejeniyar nan da kowacece Allah ya rubuta masa zai aura, kafin ya yarda ya aureta.
Zai fito fili ya gaya mata shi ba don rashin haihuwar matarshi ko rashin sonta ne yasa zai kara aure ba, kawai dai…. Kawai abar kaza cikin gashinta inji Zayyan, amma ‘infatuation’ na son kara aure ya sameshi, irin wanda ka iya faruwa da kowanne lafiyayyen Da namiji, mai cikkar lafiya da cikkar kurucciya kamarsa, ga wadatar arziki da yalwar jin dadin duniya da yake ciki a wannan lokacin, yana da damar auren mace fiye da daya, da addini ya riga ya bashi, duk son da yake yiwa Safiyyah bazai hana shi cika sunnah ba yanzu, watakila yawan son da yake mata shi yake sawa Safiyyah ke ganin yana matsa mata, soyayyarsa ta yi mata yawa, shi kuma ke sakawa take garashi yadda takeso in yazo da bukatarsa gareta kamar ta samu gare-gare abin wasan yara.
Ya tuna rabon da ya gaisa da Mama Fatu yau kwana biyu kenan, don haka ya kunna daya daga wayoyinsa da ba’a sanshi sosai da layin ba, don ya kira Mama su gaisa, Safiyyah kam ya riga ya bata hutu bazai ko kirata ba.Amma yana kunnawa sakonta na shigowa har guda uku a jere.

A cikin sakonta na farko afujajan take tambayarsa saukarsa lafiya a jihar Ikko, da yanda ta damu da ya bude waya taji lafiyarsa suyi magana ko yaya ne.
A sakonta na biyu kuma tace “tayi regretting laifinta, tana so ya bata dama ko yaya ne in ya dawo tanaso suyi magana, ya bata dama tayi repenting. A cikin sakon ta gaya masa uzurinta na ranar ‘mood swings’ ne irin na zuwan al’ada (jinin haila) amma tayi nadamar yadda ta kasa yi masa bayani ko biyar dashi ta yadda zai fahimta!”
‘I’m so SORRY Habibiyyyy!”

Zayyan kasa bata amsa yayi, ya kuma kasa kiranta, yana blaming dinta da duk wani hali na sha’awar Azeezah daya riga ya tsinci kansa a ciki yanzu babu gaira babu dalili.
Ya share Safiyyah bai bata amsa ba, domin hakika ta kai shi bango har fiyeda zatonta, maza zasu iya jure kowanne irin bahagon yaren matansu amma banda (sex denial). Duk da haka shi Zayyan ya tabbatarwa kansa a kowanne hali kuma cikin kowanne yanayi sunansa Arch. Zayyan Bello, mijin Safiyyah Usman Dandume, babu abinda zai canza title dinnan, balle har don tayi masa wani laifi ya canza mata shi, ko ya canza matsayinta a wurinsa….
Kullum yana gayawa kansa ya dinga yiwa Sophie uzuri, uzuri sau saba’in kafin yayi mata hukunci da tauye hakkinshi a shimfida da take yi yanzu, tunda a can baya ai ba haka take ba (while she was in her twenties). Tsananin son haihuwa data sakawa ranta a yanzu da frustration na rashin samunta, shi yake ta canza halayenta daga (normal behaviors) dinta daya riga ya shaida zuwa wasu halaye kala dabam, da sukasa ta fidda ranta akan kowa da komai har dashi kansa.
Domin a halin yanzu Safiyyah ta kallafa ranta a kan son samun Da dashi ta kuma baiwa son haihuwar muhimmanci har fiye da soyayyarsu mai tarihi da kuma rayuwar auratayyarsu.
Ya kira Mama ne da niyyar su gaisa kawai, don sun kwana biyu basu gaisa din ba. Mama Fatu ta amsa da farin cikin jin muryarsa, don sun kwana biyu basu yi waya ko ganin juna ba, bai je Katsina ba, Mama ta kira sunansa “Baffan Mama!” tana cewa cikin tsokana.
“Ni Baffan Mama ina ka shiga ne kwana biyu ko wayarka babu balle kyallinka? Ko Hakimar taka diyar Alaramma ta murza kambu, ta hanaka zuwa Katsina wannan watan kwata-kwata?”
Yace “haba dai Mama, haba don Allah, nifa dadina dake kenan, zargi da zato mara tushe a kan Sophie.

To ni bama tare ma, ina Lagos gidan Baba Murtala tana gida Abuja ita, muna wannan project din dana gaya miki zamu yi kwanaki nida Baba”.
Sai kuma ya sassauta murya ya ce cikin lallashi.
“Don Allah don Annabi Mama ki dinga kyautatama Sophie zato. Mama don Allah. Ba wanda ya isa ya hanani zuwa inda kike”.
Mama cikin gundura da zancen tace “to naji, yaushe zaka dawo daga Lagos din?” Zayyan yace “ganinan dai Mama, amma Baba yace zan jima, akalla zamu kai sati biyu anan kafin kammala project dinnan”.
Cikin subutar baki za’ace ko zarar bunu, Zayyan ya nisa ya ce cikin rage sauti kamar mai tsoron kada wani ya ji shi ya furtama Mama abinda ke ta yawo a ransa.
“Mama yau sai na ga yarinyar gidannan, kanwata Azeezah, ta wajen Haj. Nana Aisha, ta girma fiyeda zatona, kawai naji ta kwanta min, har naketa cewa a raina “ba don ba don ba….???”
Zayyan ya hadiyi miyau da kyar, sai yayi shiru kadan na wucin gadi, yua kasa karasawa. Mama tayi gyaran murya tace,
“ehem, ina jinka Baffa, ba don ba don ba me?”

Yayi ta maza yace “Na ce da sai na yi wa Baba Murtala zancenta, in ji ko bai yi mata miji ba?”.
Mama Fatu ta yi kabbara a ranta har kabbarar tata fito fili bata sani ba, cikin kokarin hadiye dokinta da zumudinta ga zancen, kada ya gane girman excitedness dinta, ta ce,
“Ina zuwa Baffa”.
Sai ta katse wayar tasu, ta fadi gaban Ubangiji ta fuskanci gabas ta yi sujjadah akan goshinta ta ce.
“Allah na gode maKa da Ka nuna min wannan ranar ina raye, ranar da alkadarin diyar Alaramma ya karye a zuciyar Baffa.
Yau Baffa da kansa ya ce min ya ga wata mace daban yana so bayan diyar Alaramma ba tareda na saka shi kona tursasashi ba”. Mama har ta share hawayen farin ciki da gyalenta. Ta rasa ina zata tsoma ranta don dadi da farin ciki.
Saida ta nutsu, sannan ta yi gyaran murya ta sake kiransa, with so much excitedness Mama ta ce,
“Baffa har yanzu kana kan layi?”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *