Chapter 10: Chapter 10
Shi da ita sai ya shirya fita tsaf da safe in zai fita aiki yake dan lekowa ya yi mata sai ya dawo, ba tare da wani attention dinsa gare ta ba. Dan hugging din nan, dan kisses din nan da ya sabar mata na ‘good morning’ koda bazata yi masa martani ba duk yanzu ba shi da lokacin yi mata su, kullum cikin sauri yake shigowa sassanta ya kuma fita cikin saurin, don Azeezah da Shaheed sun kwace duk wani lokacinsa da attention dinsa, ko lokacin kansa bai da shi yanzu in ya dawo gida sai na hidimarsu, sai ya sakata agaba take yarda ta shayar da yaron saidai tasa abashi madara in baya nan. Don haka sosai yasama Azeezah da Shaheed ido da kulawarsa, wadda ke gefensa kuwa wato Safiyyah shi da kansa ya yarda kimarta da darajarta a idanunsa ne suka sa yake iya takurawa kansa ya gaishe ta yanzu, ya kuma ga lafiyarta sharp-sharp ba wai wata aba bukatar aure ba, inda ba Safiyyah dakhila bace a halitta, da zuwa yanzu ta zama cikin matsin rashin kusantar miji a tare da ita, domin Shaheed da Azeezah sun dade da kwace fadarsa.
So dai an ce guda daya ne baya taba canzawa koda raiya baci, kuma bakin da duk ya furta so baya taba dawowa ya maida shi kiyayya, don haka har gobe ya san yana son Sophie.
Ko arba’in ba su yi ba, ta sallami Baba Atika, sai masu rainon Daddynta su biyu a dakin masu aikinta. Su suke dafa wa kansu abinda za su ci su yi ma yaron wanka su kula da tsaftarsa da komai na shan madararsa, shan nononsa ba wani sosai bane, sai anga idon ubansa a gida.
Ranar da Baba Atika ta koma ita da Gogan kamar an cire musu takunkumi, don Goggo tana matsa mata da sa ido, da jan kunne, na ta kula da yaronta ta kyale ubansa data ke kira wani Baby bata ko jin kunya, tace kicema Da baby kicewa ubansa Baby gardi dashi, to yanzu da kika haihu ai kya daina ce masa wani Baby kada ya koma yi miki kukan jarirai. Kullum sai Baba Atika tace kar ta sake ta koma wa miji sai yaronta Shaheed ya iya zama ya yi wata uku ko hudu.
Don haka da ta gaji da saka idon Goggonta ta tattara ta ta koma Masari. Zayyan na dawowa a ranar suka balle sabon amarcin karni.
Safiyyah na kallon ikon Allah ta zuba ido ta ga ko yaushe Zayyan zai yi hankalin dawo mata da girkinta, shiru! Kake ji wai malam ya ci shirwa, ko kuma kamar an aiki bawa garinsu.
Ta yi alkawarin baza a taba ce masa don me ba? Ko ya dace ya bata girki. Ai shi ba jahili bane ba kuma yaro bane. In ya so ya koma can har abada ya hadiye dansa da matar da yake so. Hakika Allah ya sa mata dangana, da kau da kai a kan sha’anin Zayyan da Azeezah yanzu.
Haihuwa kuma yanzu ta daina daga mata hankali, ta yarda wanda bai da rabonta a duniya tunda har Ubangiji da kanSa Ya ce Yana jin kunyarsa, to tabbas zai samu babban rabo a lahira, wanda bai samu a gidan duniya ba.
Don haka duk wani desperation na son haihuwa yanzu ya bar ran Safiyyah ta koma cikin nutsuwarta sosai. Ta auri ibadah kuma.
** ***
Jikin Mama Fatu dai ya ki dadi a can Katsina, don haka yau asabar ya dauki iyalinsa gabadaya don su je Katsina duba Maman.
Da farko Azeezah cewa ta yi ba za su hada tafiya da Safiyyah ba, sai dai su je shi da ita, daga baya ita ta je.
Karo na farko da ya yi kokarin nuna mata rashin yardarsa a kan abinda ta ke so, ya ce, “Tare za mu je, tare nake so mu je mu duba Mama, bana son yadda ki ke kokarin raina Safiyyah, tunda gaba ta ke da ke”.
Azeezah ta zumburo baki gaba, ta ce, Äi dai na haihu duk da kankantar tawa, ita ko sai zaman kashe zane da cika masai, miji ba ya ta taki kin like ko zaman me ta ke a gidannan har yanzu. Oho!
Wallahi ina ganin rashin zuciya nikam, don ni dai ba zan taba zama da mijin da baya bani kwana ba, a yi magana kadan ka ce Safiyyah alhalin ban ga me ta ke tsinana maka ba, tunda ka aure ta.
Ita ba haihuwa ba, ita ba iya kula da miji ba. Babu alamun tana iyawa da kai. Ko daga yadda ka like a nan na tabbata ba ta cika mace ba, muna mata ce, ko mun rako mata.
To fuffukar me za ka yi min don na ce ba zan hada hanya da ita ba?”
Maganganun Azeezah maimakon su yi masa zafi sai suka zame masa tamkar tuni ga girman hakkin da yake takewa, da girman zunubin da yake aikatawa na hana Safiyyah girki, tunda ya yi Dan kansa.
Bai ce wa Azeezah komai ba don ta gama da duk wani Ego dinsa ba tun yau ba, tunda ta bashi Shaheed, ba ya son haurawa da ita, yanzu ta ce sai ya kai ta Lagos. To balle yanzu da ta zame masa uwar iyali dole ya lallaba ta ko don future din Shaheed.
Azeezah za ta cigaba da cin wannan alfarmar, daga nan har gaban abada. Sai kawai ya girgiza kai ya russuna ya dauki yaron daga cinyarta, ya ce,
“Muna jiranki a mota, in kin gama shiryawa”.
Kuma a ranar ya kudure a ransa da sun dawo Katsina, zai baima Sophie girkinta. Tunda ga Azeezah kanta ta goranta masa, kamar a kansa aka fara haihuwa.
Ko da ya gaya wa Safiyyah za su tafi Rafindadi duba Mama, ba ta ce komai ba, banda ya bata mintuna ashirin ta shirya. Tana ta sake-saken ko me ya samu Maman Rafindadi?
Da jimawa ya taba gaya mata Mama na fama da sugar da kafa a tsaitsaye, amma bai taba kwantar da ita ba sai a wannan lokacin. Ko kafin Safiyyah ta gama shiryawa ta fito Azeezah ta riga ta shiga motar ta kame a gefen damansa, Shaheed na rungume a jikinsa sai taunar cingum ta ke kas-kas-kas ta rufe rabin fuskarta da faffadan sun glass din ferfetch.
Tana sanye da wani ‘army green swiss lace’, da akayiwa dinkin zamani na budaddiyar gown data sha ado, sai wani dan shara-sharan mayafin rakani gantali. Takalmin kafarta kadai abun kallo ne in aka yi la’akari da kyawunsa da tsadarsa, ta ci uban attachment na gashin kanti, wanda in ba gaya maka ta yi ba, ba za ka taba gane cewa Azeezah sakawa take akai-akai ba. Tun daga wajen motar har cikinta kamshin kasaitaccen kabbasanta ne.
Matar gaban goshin miji dai, ta saka wa a gaban mota, saboda ajinta da iya ado da iya shan kamshi. Duk wanda ya kalle ta sai ya kara. Wannan ita ce zahirin irin macen da Mama ke yi ma Zayyan inkarin ya aura, ba tun yau ba, tun kafin ya gamo stammer dinsa, wadda zasu yi tinkaho da ita da iyayenta, ba kuma zasu ji kunyar nunata a ko’ina cikin mutanensu da sunan matar shalelen Mama Zayyan ba, to gashi sun samu daidai da ra’ayinsu kai har fiyeda kintacensa shima akan mace ‘yar kwalisa, don Azeezah Murtala is beyond their expectations.
Safiyyah ta fito tsaf cikin sky blue Egyptian Jilbaab, wanda ya dace da LV bakin flat shoe din kafarta. A hannunta bakar jakar mata ce itama LV (Louis Vuittion) mahadin takalmin kafarta. Tun daga nesa ta hangi yadda Azeezah ta kame a gidan gaban mota kamar itace uwargida, tana taunar cingum da gayya da daurinta ture kaga tsiya. Murmushi ta yi tun daga nesa, ita da kanta ta ce, “masha Allah da matar Habiby, an iya ado na nunawa duniya kawa da wadata, irin ‘classy’ matar da su Mama ke ganin ita ce ta dace da zaman gaban motar Zayyan ba ni ba.
Ba ta da wani sauran buri a kan Baffan Mama yanzu. Tana zaman aure ne don shine cikar kamalarta. Da cikar mutuncin iyayenta. Tana mai jiran duk hukuncin da Ubangiji ya ga dama tsakaninta da Zayyan Bello Rafindadi. Wani kwayan mutum guda daya da ta taba so a rayuwarta, kuma ya nuna mata cewa duk maza ba su da maraba. Duk wadda ta ce namiji uba ne za ta kwana marainiya.
Ba wata magana Safiyyah ta yi musu sallama a cikin motar sannan ta shiga ta rufe. Ko da Zayyan ya karaso yana fadin “excuse me, ku dan gafarceni na tsaya amsa waya ne, mu je ko?” Ya juya yana duban Sophie, sai ya ga ta yi masa wani irin kwarjini musamman da ta tsuke baki da fuska, bata bashi wani impression akan fuskarta ba. Maganar da zai yi mata ma kasawa ya yi, domin a shiga ta mutunci da kamala ba hadi ko na kwabo tsakaninta da matarsa uwar dan sa.
So yake ya ce, Ya za ta zauna a baya? Azeezah ya kamata ta koma baya, amma yadda duk suka cika fam suke neman fashe masa a mota dole ya hadiye maganarsa, ya ja motar kawai sannu a hankali suka fita daga harabar gidansu zuwa gate din Sunset Estate.
Suna tafe a hanyar zuwa Katsina, Zayyan na tuki, Azeezah na kula da rigimar Shaheed, har Zayyan ya ji guilt na yadda Sophie ta yi dif a motar sai wasan game kawai ta ke cikin wayarta.
Ya ce, “Zeezah, ki baima Sophie Shaheed ta taya ki da shi mana, ki huta kadan, tunda kin ki dauko mai rainon mu taho tare”.
Azeezah ta yi maza ta ce, “No, Daddy ya san hannuna, kara rikicewa zai yi in ya ji shi a bakon hannu”.
Shi da kansa sai da ya maimaita maganar a ransa.
“Safiyyah ce bakon hannu? Koma bayan da rashin haihuwa ya janyo ma Sophie mai yawa ne a wurinsa, tunda yau gashi yau ana kiranta bakon hannu a cikin iyalinsa…. duk da haka ai sakacinsa bai yi yawan da za a kira Safiyyah bakuwar hannu a cikin iyalinsa yayi shiru ba.
Shi dai yasan yayi auren nan ne don ya samawa Safiyyah sauki da maslaha daga matsalolin gidansa, amma sai karin wahala, bacin rai, bakin ciki da tarin koma baya kadai Safiyyah take dada samu. Maimakon a samu long lasting maslahar da ake nema abubuwa su ragu, a’ah kullum sai karuwa suke kaman ana izawa wuta fetur.
“Sophie is not a stranger, she is my family too”.
Ya bar zancen zucinsa ya subuto ya fito fili, sarari, har Azeezah ta ji. Safiyyan ma ta ji.
Ba ta kuma ce komai ba, sai kara manne danta da ta yi a kirjinta alamar ba ta bayarwa din. Ko me zai ce.
In ma akwai wani sirri da Azeezah ke da shi da ya sa Zayyan ba ya iya kwabarta, ko yi mata fada, ko yi mata raddi mai zafi ko makamancinsu, to fa ba boka ba ne ba malam ba, tsabar iya tafiyar da shi ne a shimfida da gyaran kanta da ta ke yi da magungunan mata na garari, irin nasu na ‘ya’yan manya da Hajiya Nana da kanta ta ke nemo mata, don ta kan ce Azeezah sai da gyara za ta zauna lafiya da miji, tunda ba kan-gado ne da ita ba, ba nutsuwa ba kwantar da kai ba.
Duk abin da ya zo bakinta za ta kwaba maka ba ruwanta da girma, shekarunka ko matsayinka, shi ya sa Zayyan har ya daina damuwa da rashin taushin lafazinta a wasu lokutan, in ba bukatar kanta ce ta kawo ta ba da wuya ka samu sassanyan lafazi daga gare ta.
Safiyyah ba ta ce komai ba duk da yana kokarin saka ta a hirarsu shi da Azeezah, sai dai ta amsa masa a gajarce har suka zo Katsina suka kama hanyar shiga Rafindadi.
Wani ikon Allah duk ‘ya’yan Mama suka tarar sun zo suna tare da Mamanm har da Yaya Zubaina, ‘ya’yan Mama suna ji da ita kowa ya sani, duk da Mama na jin jiki sai da ta ce daga kwance, “Baffana miko min Baba Murtala in ga girmansa, in ji duminsa a kusa da ni”.
Ya mika mata Shaheed gefenta tana shafa fuskar cikin kauna, ta ce, “Baba Murtala haka ka yi wayau? Azeezah me ki ke ba shi haka?”
Gabadaya hankalin Mama da na ‘ya’yanta yana kan Shaheed, kamar ba su lura da Safiyyah tare da su ba.
Ban da Yaya Zubaina da ta nuna mata wurin zama a gefenta, ta ce, “Zauna nan kusa da ni kinji Safiyyah”.
Ta zauna a gefen Zubaina ta tsugunna tana gaida Mama, sai a lokacin Mama ta ankara da ita, abun mamaki, yau Mama fuska a sake ta ke amsawa, tunda ko ba komai ta gama karya alkadarin Safiyyah yadda ta ke so a halin yanzu. Ba ta da power, ba ta da sauran fada a ji, tamkar zaman bora da mowa, to na me za ta damu da wata Sophie a yanzu?
Wannan shi ne tunanin da Hajiya Fatu ke yi, amma duk da haka a ranta tana jin bai isa ba. Tunda ko makaho ya shafa idanun Baffa har yanzu zai ga girman Sophie da kimarta da darajarta da basu gushe ba cikin idanunsa. Soyayyar ce dai babu tabbacinta, ko kuwa tayi rauni, haka dokinsa irinna na da da ita duk babu shi yanzu sun yi fiffike sun koma kan Azeezah da danta, shi kadai da Ubangijinsa suka sancewa har yanzu yana son Safiyyah ko a’ah??
Tarba ta musamman ‘ya’yan Mama suka yi ma Maman Shaheed yadda suke kiran Azeezah, abinci kala-kala aka saukesu dashi. Safiyyah kam ta kama kanta da ganin rawar jikin da suke da diyar Baba Murtala kamar yaro ya ga ubangidansa, ita kuma tana faman shan kamshi da zuba class kota ina.
A karshe Zayyan ya roki Mama kan zai canza mata asibiti su tafi Abuja tare ta ga kwararren likitan suga, zai so su je ABUTH to amma saboda masu jego, ya ce gara ta je gidansa a Abuja su kula da ita acan har taji sauki.
Da farko Mama ta ce, a’a, don ba ta taba zuwa gidansa na Sunset ba tun tarewarshi da Sophie, ta ce ita ba ta zama gidan surukai. Amma Zayyan ya dage inda ya ce,
“Mama in ba ki je gidana mun samu albarkarki ba waye zai je? Wa muke da shi ni da Shaheed a duniya da ya wuce ki? Ki yi hakuri Mama da kin samu sauki za mu dawo da ke gidanki”.
Azeezah dai ba ta ce komai ba, amma har ga Allah bata so ya ce su koma tare da Mama Abuja ba.
Safiyyah kuwa wa yake ta tata? Ai da wanda ya isa yake kuma da fada ake shawara, don haka ita ido ne nata.
Ta so ta biya Danduma Zayyan ya ce, ta yi hakuri sai za su dawo da Mama Katsina, don ko tafiya Mama ba ta iyawa sosai, ya ce a gobe-gobe yake so ya kai ta Nizamiye a yimata kyakkyawan treatment.
Don haka washegari tare suka juyo Abuja gabadayansu yayin da ‘ya’yan Mama kowacce ta koma gidan mijinta.
Sun iso gida lafiya, Zayyan ya bude wa Mama ‘guest wing’ din gidansa wanda ba ya tare da na kowacce matarsa, a tsakiyar gidan yake.
Washegari ya dauki Mama sai asibitin Nizamiye inda ba bata lokaci likita ya ce sugar ya ci karfin Mama, dole ta bi doka wajen cimakarta ta kullum ta kuma kula da shan maganinta.
Nan likita ya bada tsatstsauran tsari na irin abincin da ya yarda Mama ta dinga ci yanzu, diet dinta duka ya canza shi, da tsarin shan maganinta akan lokaci.
Da suka dawo gida suna sassan Azeezah, ya yi mata bayanin da likita ya yi, da irin abincin da za ta dinga yi wa Mama yanzu. Ba don komai Zayyan ya dora alhakin abincin Mama a wuyan Azeezah ba sai don ya ga yadda Mama ta ke sonta, ta kuma fi sakin jikinta da Azeezah sosai a kan Safiyya.
Azeezah ba ta ce ba za ta yi ba, amma a ranta ta ce, ko uwarta Hajiya Nana ta san ba ta son harkar wahala, balle wani girki na diabetic, mai ka’idoji, don haka ta sa mai rainon Shaheed Janet ta dinga yi wa Mama abincin safe, rana da dare.
A daren ranar shi da kansa ya yi wa kansa fada, ya yi ma Azeezah da Shaheed sallama ya ce, daga yau su koma raba girki ita da Sophie. Ko don Mama da ke gidan yanzu ta tabbatar yana adalcin da ya dace.
Ya ce ko da ma shi don Shaheed ya samu koshin lafiya ne da kulawa ya dauki alfarmar tarewa a gunsu, don ya santa ba iya kula da Shaheed din za ta yi in aka barta ita kadai ba. Yanzu kuwa Shaheed masha Allah don haka su koma raba girki na kwana bibbiyu.
Azeezah kyabe baki ta yi, ta ce, “Yadda ka tafin hakanan za ka tattaro ka dawo. Don wannan muna matan taka, ba class dinka bace ko ka ki ko ka so.
A juri zuwa rafi dai, kuma a yi dai mu gani idan tusa za ta hura wuta”.
Ya san Azeezah ta kware da iya bakar magana, shi ya sa ba kasafai yake biye ma rashin kunyarta ba, ya tattara abubuwan da zai bukata daga dakin Azeezah ya nufi sassan Sophie.
Safiyyah ta idar da sallar isha kenan ta ji takun Zayyan ya durkako dakin barcinta. Yana tafe yana waya da babban abokinsa Alhaji Habibu Mustapha Nahuce. Habibun yake cewa in ya maida Mama ganin likita a Nizamiye ya fada masa, don ya gaya wa Ummu Abdallah wato matarsa (Dr. Rahinah Omar Girei – NA HUCE) tunda a Nizamiyen take, za ta taimaka a dinga kula sosai da Mama tunda lalurar Mama ba bangarenta ba ne, ita Otorhinolaryngologist ce.
Safiyyah na ninke hijabin sallarta Zayyan ya shigo dakin. Kamar daga sama ta ke jiyo tashin muryarsa a sassanta a lokaci irin wanda bai saba shigowa ba yanzu, wato bayan isha’i. Ji ta yi wani kwantaccen bacin rai ya taso mata daga kasan zuciya. Ba ta san ta dade da kullatar Zayyan a kan alfarmar da ya nema ta yi masa ba, yau kwana arba’in saboda matar so ta haihu, rabonta da shi 42 days cif. Ko ita ke jinin bikin sai haka. Ji ta yi idonta har rufewa suke don kansu tsabar bacin rai da fushin zuciyar da ya yunkuro mata.
Kamshin kasaitaccen turarensa na Ultraviolet (Paco Rabanne) ya mamaye dakin, turaren da a can baya yake sanyaya mata zuciya, ya sa ta amsar tayinsa ko ba ta yi niyya ba, amma ga dukkan mamakinta yau ji ta yi da turaren da mai turaren duk jinsu da ganinsu ya bakanta mata zuciya bakikirin, don al’amarin Zayyan ya koma zallar rainin hankali.
Ko me ya zo yi mata yau kuma? Namiji dai bai da kunya a dabi’arsa, zai iya cewa girkinta ya dawo mata dashi fa, bayan wucewar kwanaki arba’in da yi masa haihuwa.
Tana ninke kayan sallar ta amsa masa sallamar daidai lokacin da ta kai karshen addu’ar da ta ke karantowa a bakinta,
“Rabbi hably min ladunka zurriyyatan dayyiba… wa ja’alni min ladunka sultanan naseera’.
A kasalance Zayyan ya isa gare ta ya rungume ta ta baya, with so much kewa, ya dora habarshi saman kafadunta, bakinnshi kasan masangalin dogon wuyanta da ya jima bai ji dumin wurin a jikin sajensa ba.
Wani irin shock dukkaninsu suka ji da haduwar fatar jikinsu, kamar rana ta farko kenan da ya dora hannunsa a jikinta. Ya shiga goga fuskarsa da sassalkan sajensa a kasan wuyanta. Bata bata lokaci ba Safiyyah ta dakatar dashi ta hanyar zame kanta daga rikonsa don bata ga dalilin hakan daga gareshi yanzu ba, abun nufi; mai mace ‘yar gayu yarinya danya irin Azeezah, mai cikin haihuwa, iyayenta masu hannu da shuni, ai ita ta dace da samun wannan alfarmar tasa yanzu, ba ita ‘yar dukununu, ‘yar talakawa kuma Malamai ba. Da basu ajiye ba balle su basu.
“Please and Please, irin wannan wasan, ya dade da shudewa ko ince ya dade da zama tarihi tsakanin Zayyan da Safiyyah”.
A yanzu za ta iya cewa, Zayyan ya so ta ne a lokacin da bai san abin da ya dace da shi ba, ma’ana ita din ba komai ba ce a gare shi yanzu face matar “ladan noma”. Wadda Babansa mutumin kirki Prof. Bello Isyaku Rafindadi ya aura masa cikin mutunci don ta zame masa matar rufin asiri ba matar so ba.
Mahaifiyarsa ita ta san irin macen da ta dace da shi, kuma ga shi nan ai ta aura masa har sun hayayyafa. Sai yau ta ke tambayar kanta shin ko zaman me ta ke cigaba dayi yanzu a gidan Arch. Zayyan Bello daga ranar da ya dakatar da ita a girki ya baima Azeezah da danta zuwa yanzu?
Tunda har ta kai ta kawo an zo gejin da Zayyan ya daina raba kwanan aure da ita, saboda matarsa ta haihu, ita ba ta haihu ba.
Ba hawaye ne ya zo mata ba, a’a wani irin fita ranta Zayyan ya kara yi kwata-kwata. Ta yadda har ta kasa kallon ko saitin fuskarsa balle ta ce masa sannu da zuwa ko makamancinta, wadda ba ta rabo da bakinta a baya muddin ya shigo sassanta.
Abinki da namijin da ya riga ya san matsayin da yake dashi a gurin matarsa, matsayin da yake da tabbacin ko mai zaimata cikin ajizanci ko cikin sani ba mai canzawa ba ne a tare da Sophie in dai a kansa ne, ya riga ya san kowane irin kuskure ya yi mata mai yafuwa ne, mai wucewa ne a gurin Safiyyah, musamman a yanzu da ya zo yana son gyarawa da kyakkyawan yaqini na cewa ba zai sake maimaita kuskurensa ba.



