⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 12: Chapter 12

Ta yi tsaki ta bangaji kafadun Sophie da kafadunta sannan ta shige cikin dakin.
Ashe Zayyan ya iso wurin ya kuma ga abinda Azeezah ta yi.
Mama ma ta gani, amma sai cewa ta yi, “Ke ko Maman Shaheed ina ke ina shafar jikin bakararriya ko da sunan bangaza ne? Su fa daban Allah yake halittarsu har a cikin Alqur’ani Allah saida ya ambacesu, rashin haihuwa ai nakasa ce, cuta ce, sai kin shafo ma kanki jangwam na rashin kwan haihuwa.

Ai ba sai kin shafi jikinta ba, maganar fatar baki ta isa. Girma-girma ne Azeezah, ba girmanki ba ne fada da diyar kananan mutane inma kishi take dake babu yadda zatayi dake, don haka ki rike girmanki kin ji ko?”
Safiyyah ta yi saurin juyowa ta kalli Mama. Da wasu irin idanuwa da suka canza launi, duk wani girmanta da ke idonta na fadowa kasa.
Azeezah da Mama har suna hada baki wajen ci gaba da yi mata diban albarka, Azeezah ta ce, “Mama ana ba ki abinci Mai laqani kina lashewa saboda kin raina wanda nake sawa ake ba ki, sai an zuba miki ayar mallaka an mallake ki kema yadda aka mallake miki Da kwana biyun nan duk na rasa kansa”.
Duk yadda Safiyyah ta kai ga sanyin hali da hakuri yau zuciyarta ta kai kololuwa wajen baci, ta kan juri komai amma banda a taba mutunci iyayenta, musamman da Zayyan ya yi shiru yana jinsu, which means he cannot stand for her a gaban Azeezah da Mama da ke cin mutuncinta. Sai ta juya ta fice daga dakin Maman cikin sassarfa ba tare da ta ce musu uffan ba.
Washegari Mama na jiran Sophie ta kawo mata kunun safe da lallausan kosan da ta ke mata da safe, ko chips and eggs da kunun tamba etc ta maida yawun yunwar safe. Amma yau shiru kake ji kamar an aiki bawa garinsu, har karfe goma babu Safiyyah babu warmers dinta, ta fara tunanin ko Safiyyah ta yi fushi ne don sun mata cari jiya?
Zuwa sha biyun rana yunwa ta fara galabaitar da Mama, ta kira Azeezah wadda a lokacin ba ta gidan ma, tun karfe goma ta fita da kawayenta.
Azeezah ta ce, “Yaya dai Mama?”

Mama ta nisa ta ce, “To ba a kawo min karin kumallo ba har yanzu, ko za ki yi mata magana, ina jin fushi ta yi don mun mata fada jiya, don ni ko lambarta ba ni da ita tsabar yadda bata raina”.
Azeeza ta ce, “Tabdi Mama kina ruwa tsundum, to ni ina ruwana? Bana gidan ma tun safe na je birthday din Sageerah”.
Yawo ya zame wa Azeezah routine yanzu tun bayan arba’in dinta. Wato tunda ta yada wanka. Gashi yau a dakin Azeeza Zayyan yake.
Da yake a dakin Azeezah ya kwana yau kuma da sassafe ya fita kan wani muhimmin project. Mama ta rabu da Azeezah don ta tabbata ba abinda za ta tsinana mata har karfe biyu na rana Mama bata sa komai a cikinta ba, duk ta gama galabaita. Ta kira Zayyan, yana dauka ta ce, “Baffa”.
Ya ce, “Na’am Mama”.

“Ka zo ka maida ni Katsina kafin matanka su hallaka ni da yunwa, na lura duk na tare musu rawar gaban hantsi, yau tun safe ko makwarwar ruwa daya an rasa mai ba ni a gidanka…”.
Mama ta fashe da kuka ta ce, “Haka kawai da gatana da ‘ya’yana da komai za a maida ni almajira a gidan Dana? Na rantse ba ni kara kwana a gidanka, ka zo ka maida ni inda ka dauko ni cikin iyalina, rufin asiri na”.
Hankalin Zayyan yayi matukar tashi, ya bar duk abin da yake yi ya dawo gida. Yana kokarin parking Azeezah ta shigo da tata motar, ta fakata a gefensa. Yau ko Shaheed din ba ta fita da shi ba, gurin su Janet ta bar shi.
Haka ya fito cikin bacin rai, itama ta fito, mayafinta ya kara bata masa rai ga kamshin kabbasa na tashi, ya ce, “Azeezah daga ina ki ke? Kin gaya min cewa za ki fita ne?”
Ba tare da ta dube shi ba, ta ce, “Clinic na je ba na jin dadi, kuma ai ban jima ba”.
Karyar data kantara masa ita tafi fitar tata ba izni bata masa rai.
“Ko ma ina ki ka je nace kin nemi izinina? Ko kin gaya min ba ki da lafiya, ko na taba barin matata ta je asibiti ita kadai?”
Azeezah tayi maza ta daga masa hannu, ta ce, “Please, stop shouting at me… ni ba akuyar daure ba ce ba kuma ‘yar goye ba ce da sai an goya ni an kai ni asibiti. Ka daina hada ajina dana bagidajiyar matarka a kan komai ka ji na gaya maka”.

Daga haka ta wuce shi zuwa gidanta tana kada masa bom-bom.
Da wannan tulin bacin ran na Azeezah ya shiga wurin Mama sai gumi ke yanko masa.
Mama ta ce, “Tsawar me kake ma Azeezah haka? Dududu nawa ta ke, kuma cewa nake abincin nawa ya tashi daga wuyanta ya koma gun Diyar Alaramma? Saboda an yi mata fada shi ne za ta nuna min iyakata a kan abinci ta horani da yunwa?”
Ya ce, “Ki yi hakuri Mama, ba halin Safiyyah ba ne, akwai dai wani abun, amma bari in je in yi mata magana in ji”.
Da bacin rai mai yawa Zayyan ya nufi sassan Safiyyah, sai ya tarar da ita tana cin abincin rana da ta girka iya cikinta. Hankalinta kwance ta ke cin abincinta.
Mama da Azeezah sai ga su sun biyo bayanshi har sassan Safiyyah don ganin irin tanadin da zai yi ma Safiyya na hana mahaifiyarsa abinci.
Ya dube ta da takaici, amma sai ya kwantar da murya ya ce, “Sophie, ina abincin Mama?”,mlyl0
Safiyyah ta dago a hankali ta dube shi cikin idonsa,

“Na dauka wadda ta kwana da miji ita ya kamata ta girka ma Mama abincin yau? Da ma na dauka abin kirki nake yi shi ya sa na yarda nake yi kullum, amma tunda abin ya zama haka ana taba alfarmar iyayena daga abin kirki, kowacce ta dinga yi wa Mama girki ranar girkinta, wato ranar da miji yake hannunta”.
Ya ce, “A takaice dai, ba za ki yi ba ko yaya kike nufi?”
Babu jinkiri babu bata lokaci Safiyyah ta ce, “Eh,haka nake nufi ba zan yi ba saboda ba ranar girkina bane. Tunda har Azeezah ta iya kwana dakinka girkin ma ya kamata ta koya ni ba baiwarku ba ce, ba ‘yar aikin gida bace Zayyan, na gajida abinda Mama take yimun.
Tunda nake yin abincin nan Mama cewa ta ke babu dadi, kuma ba ta taba gode min ko samin albarka ba, sannan duk da haka tana cin abincin, ka taba cewa wani abu a kan kokarina? Ko kuwa da aka ci mutuncina dan kama sunan iyayena a gabanka me ka yi don kare min martabata a matsayina na matarka?”
Zayyan ya ce, “Make it clear Sophie, za ki yi wa mahaifiyata girki ko ba za ki yi ba?”
Cikin wani irin bacin rai Safiyyah ta dube shi shi da Maman, kafin ta ba shi amsa da cewa,
“Na daina, ba zan yi ba, ni ba baiwar Azeezah ba ce, ai ta iya kwana da miji ko, girki ne ba ta iya ba, to ta je ta koya ta dinga yi tunda zaman aure tazo irinna kowacce mace”.

Mama ta fara kuka, ta ce, “Baffa na rantse da Allah ka saki yarinyar nan yanzun nan ko in fita in bar muku gidanku.
Saki uku na yi maka umarnin yi mata, ko ka biya ni nonona da ka sha, ka sake ta na ce tunda ita butulu ce da ba ta san mai kaunarta ba, kuma ba ta ganina da gashi nida na haifa mata kai. Ko ka sake ta ko in fice maka daga gida yanzunnan na yafe wa diyar alaramma kai”.
Safiyyah ta mike ta isa gaban Zayyan ta ce, “Idan kai dan halak ne ka kuma haifu cikin mahaifiyarka Zayyan, ka bi umarninta haka, ka zauna da macen da ta zaba maka. Ka zama halastaccen Da ga Mama, ka bi umarninta!”
Tana fadi tana haki da zufa a gabansa. Idanunta ba alamar hawaye ko digo.
Zayyan ya shiga wani irin rudani da bai taba shiga ba a rayuwarsa.

Gumi yake tun daga goshinsa har yatsar kafarsa. Mama na ci gaba da maimaita umarninta Safiyyah na karfafa shi da ya bi umarnin mahaifiyarsa ya sake ta.
Ba zai iya kiran incidence din cewa ya faru out of bewilderment or frustration ba, kawai ya samu kansa da bin umarninsu su duka biyun; Mamansa da Matarsa, mata biyun da yafi so a fadin duniya.
“Safiyyah na sake ki!!!”
Zayyan ya samu bakinsa da furtawa cikin tangardar harshe da rawar baki. Tamkar ya dauko kalaman ya mayar cikin bakinsa ya hadiyesu. Amma ina! Magana zarar bunu! Ta riga ta fita.
Sophie ta ce,
“Ka haifu dan halas, Arch. Zayyan. Ni kuma yau zan bar muku gidanku insha Allahu ba sai gobe ba, komai dare a kauyenmu zan kwana”.
Ta juya ga Mama tace.
“Don Allah Mama ki aura ma Zayyan mata uku masu haihuwa bayan Azeezah.
Haihuwa in dai da danki Zayyan ce, daga yau na yafe ta kuma bana bukatarta har abada a rayuwata, in kin ga dama ki haifa wa Zayyan ‘ya’ya tunda kin fi kowa iya haihuwa…”
Azeezah ma ta Kara fashewa da kuka, wai Sophie ta zage ta. Bayan har ranta yau kukan dadi take yi.
Safiyyah bata kara bi ta kanta ba, shi ma kuma Zayyan din kallo ta yi masa na karshe, fuskarta kunshe da murmushin da Zayyan ya kasa fassara ma’anarsa. Haka ta zagayesu ta wuce zuwa uwar dakinta.
Duk abin da ta san zai yi mata amfani ta ke dauka tana jefawa a matsakaiciyar trolly dinta. Hawaye babu ko digonsu a idanunta, ta riga ta saka a ranta wannan sakin shi ya fi alkhairi tsakaninta da Zayyan Bello Rafindadi madadin ta kare rayuwarta cikin kaskanci da gorin rashin haihuwa a gidansa.

Kuma koda ta ke hada kayanta don wucewa kauyensu Dandume, addu’a ta ke yi wa duk wata mace mai fama da fitinar dangin miji da lalurar rashin haihuwa a kan Allah ya ba ta maslaha ta alkhairi irin wadda ya bata.
Don sau tari wani auren da shi gwara babu. Ina amfanin aurenta da Zayyan?
Zuciyarta ta yi juriya mai yawan da ita kanta bata zaci zata iya ba a cikin karin auren Zayyan da zamansu tare da Azeezah wanda har a yau ta ke mamakin kanta, ta ke cewa kanta kodai ta samu shafewar tunani ne na lokaci mai tsaho da yasa ta jure kaskancin da ta samu daga zuwan Azeezah zuwa yau??
Idan azabar da kowacce mace ke dandana a kan kishiya kenan, yau ita Safiyyah ta daina aure a rayuwarta.
Ta yarda duk maza sunansu daya. Ba wata kalma wai ita soyayyar gaskiya da ke kewayawa a wannan duniyar da muke ciki a halin yanzu.
Tana kammala zuge jakarta ta daga hannuwanta sama tana yi wa matan duk da Allah ya jarabta da lalurar rashin haihuwa addu’ar, idan haihuwar ba alkhairi ba ce a gare su kuma da uwar miji irin Mama ne da dangin miji irin nata, kada Allah ya basu, Ya musanya musu da mafi alkhairin wato aljannah madaukakiya.
Cikin wannan hali Safiyyah ta baro SUNSET ESTATE jaye da trolly dinta babu ko waiwaye, Estate din da ta zana da hannunta. Tana tafe tana rokon Allah ya kai ta Dandume lafiya don ba za ta iya tuna yaushe rabonta da hawa motar kasuwa zuwa Katsina ba, ko yadda za ta yi ta fita daga garin Abuja a motar haya ma ba ta sani ba.

Safiyyah na tafe gefen titi tana tadin zuciya. Yau ta yarda komai na rayuwa ashe baya dauwama, fararre ne kuma kararre, soyayya bata dauwama a muhallinta haka kiyayya duk masu iya canzawa ne, soyayyar miji gareki bata hanashi bin KAWAR ZUCIYARsa ya kara auren wata macen a sanda yake so duk girman son sa gareki.

Tabbas rayuwa ta yi juyin waina da ita Safiyyah, tun zuwan Azeezah rayuwar su. Amma ta amince barin gidan Zayyan Bello shi ya fi alheri gareta a wannan gabar, gara ta barshi da KAWAR ZUCIYArsu wadda itace, Azeezah Murtala.
Don haka duk yadda za ta yi ta kai kanta gaban talakawan iyayenta da basa hada kaunarta data kowa, wato Malam da Ammi za ta yi, koda da rarrafe ne ko akan iska, tunda ta tabbata tana cikin hankalinta; Rabuwa da Arch. Zayyan Bello Rafindadi bai sa ta fita a hayyacinta ba, bai sa ta tunanin shi ne karshen rayuwarta don ta fita daga daular arzikinsu ba!!!
Tafi yarda da tunaninta na cewa….. yanzu ne rayuwar ta zata fara…. At last she escaped from this prison!
Yanzu ne zata budewa kanta kofofin farin ciki, walwala da ‘yanci wadanda auren Zayyan da gore-goren mahaifiyarsa suka rurrufe mata. Haihuwa kuma in dai zuri’ar Mama zata haifa, to ko a lahira tana rokon kada Allah ya bata haihuwa.
** **

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *