⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 2: Chapter 2

Mala’iku suna masu la’ana ga macen da ta titsiye miji ya saketa babu dalili. Haka wutar jahannama na nan tana jiran marabtar wanda ya kashe kansa saboda raunin Imani akan kuncin rayuwar duniya.
Kenan cikin abubuwan nan da mata ke yi a irin wannan ranar da itama ta samu kanta, ita a matsayinta na cikakkar musulma, a ma’auni na hankali da tunani duk basu dace da ita ba.
Ta tuno mahaifiyarta Ammi Hafsatu, ta tuno Malam wato mahaifinta mutum mai kawaici da gudun bacin ranta, da kannenta wadanda duk mata ne Rayha, Sabah da Rayyah, ita kadai ce farin cikinsu kuma babbarsu Yayarsu, su duka ‘ya’ya mata ne a gun iyayensu, itace kuma mai karfin cikinsu, saboda basu da Yaya namiji da suke ciki daya, to ko don su Safiyyah ta baiwa kanta ‘hope’ na cigaba da rayuwa a gidan mijinta Zayyan, da hakurin zaman aure da kishiyar da Allah ya rubuta mata, don dai tasan itace ‘role model’ din kannenta. Kuma da bakinsu sun sha fada mata hakan, cewa ita allon kwaikwayonsu ce, suna fatan samun rayuwar aure mai nagarta da miji nagari ta kowacce fuska irin nata.
Hakan yasa Sophie ta cigaba da wahalallen juyi a kan gadonta, cikin rashin samun mafita har goshin asubahi, ta cigaba da karbar radadin da zuciyarta keyi ita kadai, musamman in ta tuna cewa; shi din a yanzu, wato maigidanta Arch. Zayyan Bello Rafindadi, da take kuncinnan da shiga tashin hankali a dominsa, a halin yanzu bai san tana yi bama, bai san halin da take ciki ba a kansa. Zayyan bashi da lokacin ta. Karewama, yana can cikin wata rayuwa ta mayafi guda cikin sabon farin ciki da sabuwar rayuwarsa, in Safiyyah ta tuno hakan, sai radadi da suyar da zuciyarta ke yi su karu, su ninka fiyeda farko.

Kuka wani abu ne mai saka rahma da salama a zuciyar bawa, wanda a can baya baya yiwa Safiyyah wahala, amma yau ta kasa ko digar da silin hawaye balle taji sauki, watakila hakan ne ke kara ma ranta azabtuwa.
Lallai yanzu ta yarda “kishi” abinda ta raina a baya, gaskiya ne ba karya bane, yau ita Safiyyah ta yarda tasirinsa a zuciyar mace abu ne mai girma. A rayuwarta ta can baya kuwa bata dauke shi a bakin komai ba, yanzu Safiyyah ta yarda mata kadan ne kuma kalilan cikin dubunnai, ke nasarar iya tsallakewa sharrinsa….
Koda limamin ‘Sunset Estate’ Imam Abdulghaniyy, ya kira sallar asubahi akan ido da kunnen Safiyyah ya kira. Tana kwance har lokacin tana wannan lissafe-lissafen da karanta wasikar jaki, har Imam yayi kiran sallahr farko.
Da kyar ta iya tashi daga kwanciyar taja kafa ta isa toilet, ta dauro alwallah. Wallahi data kalli idanun ta a mudubi, kasa shaida su tayi, sakamakon kumburi da kankancewar da sukayi. Alhalin ta san bata digar da hawaye ko guda daya ba.
Wato kukanma dan gata ne ita bata ko samu (privilege) din yinsa ba, amma idanunta sunfi shigar borkono yi mata radadi da yaji yadda take jinsu, sakamakon rashin barci da kuncin da suka kwana cikinsa.
Bayan ta dauro alwalah saita fito dakin nata, sannu kan hankali Sophie ta isa ga tagar dakinta ta dage fararen (curtains) din dakin, jin motsin ana taba gate dinsu da Asubahin fari.

Ta hango shi cikin farar jallabiyya kar, da carbi a hannunsa yana kokarin bude gate din gidansa, a kokarinsa na samun jam’in sallar asubahi a Sunset Mosque, wanda bai taba wuce shi in dai yanada lafiya kuma yana cikin Estate dinsa bai je ko’ina ba.
Kenan yau ma zuwan amarya baisa ya makara sallah ba. Safiyyah ta bishi da kallo har ya fice, a perfect gentleman dinda ya daina burgeta daga jiya zuwa yau. Ta lumshe idanunta tana kissima abubuwa masu nauyi da suka faru tsakaninsa da Azeezah a daren jiya, har da wadanda ‘pure sense’ ma bazai dauka ba, amma ita sai zuciyarta ta zarme, ta shiga hasko mata hakan, wato ta tafi ga nuno mata abubuwan da suka wakana tsakaninsu jiya tamkar a majigi, shida amarya Azeezah, wadanda ta tabbatar Zayyan zai iya, dama wadanda shi a karan kansa ya san bazai taba iyawa da kowacce mace ba Safiyyah din ba.
A hankali Safiyyah ta sauke labulen da sauri, sakamako zuciyarta data shiga wani irin zafi da radadi da ganin data yi masa, kai harda tiriri kirjinta keyi da tunanin cewa “he had sex with another woman other than his alter ego” ya kusa sanyata sanya kururuwa ita kadai a daki, ganin kamar Zayyan ya juyo yana kallon saitin tagar dakinta bayan ya bude gate din ya fita yasanyata hanzarin sauke labulen ga barin kallon fitarsa, ta kuma bar bakin tagar gabadaya.
Kwarai Zayyan ya ga sanda ta sauke labulen nata daga kallon fitarsa. Ya girgiza kai kawai, yasa kai ya fita zuwa masallacin.

Safiyyah! Safiyyah! Safiyyah! Zuciyarsa ta ambaci sunan har sau uku. The only woman… Da ya yarda zuciyarsa na so tsakani da Allah, ba don wani dalili ko wani kyale-kyale na biyan bukatun rayuwa ba. Har ga Allah bai yi laifi ba don ya kara aure, duba da tarin matsalolinsu, amma damuwarsa itace ita Safiyyah a yaya zata karbi al’amarin yau? Duba da cewa basu taba raba makwanci ba sai yau.
Tuni har ya makara, saboda dakatawar da yayi a hanya yana tunani, sanda ya shiga masallaci tuni Liman Abdulghaniyy, har ya kabbara sallah, kuma yau bai samu sahun farko ba kamar yadda ya saba samu kullum.
Saida gari ya soma wayewa yayi dan shaaa! Haka, wajejen karfe shidda na safe sannan Zayyan ya baro masallacin zuwa cikin gida, bayan lazimin mintuna talatin da ya zauna yi. Kai tsaye gidan uwargida Safiyyah ya doso.
Zuciyarsa fal tarin bakin sababbin al’amura, wadanda shi kansa ya rasa ta ina zai fara musu, a matsayinsa na wanda ya wayi gari matsayin mijin mata biyu! Abinda ko a mafarkinsa bai taba zuwa ba, na cewa zai iya hada rayuwa da wata mace bayan Sophie.
Safiyyah itace ‘definition of love and peace’ a gurin shi, ba yadda zaiyi ne. Aurennan kaddararsa ce, tabbas.
Zayyan ya sa ‘spare keys’ din shi ya bude gidan Safiyyah, ganin ta garkame kofar da mukulli, haka yayi ta bude kofofin data rurrufe har ya tadda dakin barcinta.
Yayi sa’a ba mukullinta data bari a jikin kofar don ma kada ya shigo, sabida ta fita falo ta dauko hijabin sallarta ta koma daki shine yasa ta manta bata rufe kofar da key ba.
Ta mike daga kan abun sallahrta kenan da zummar komawa gado ta kwanta, ko ta samu wannan karon baccin yazo, sai taji motsin ana bude kofar dakin ta, sanin kanta ne kuma babu wanda keda (spare keys) dinta sai shi maigidanta, Arch. Zayyan Bello Rafindadi. Kanin Zubaidah da Zubainah, Yayan Zahra da Zaitoon, shalelen Mama Fatu dan gaban goshin marigayi Baba Bello.

Da ya shigo sai ya kunna fitilun data kashe, hasken kananan kwayayen lantarki masu haske ya dallare masa kumburarrun idanun Safiyyah, wadanda suka kankance suka yi jazur kamar an gumbuda musu dakakken attarugu. Yayi daidai da lokacin da ta dago, suka hada ido. Sai ta ga nashi idanun shima a kumbure, sun kankance sunyi ja kwatankwacin nata ko fiye ma da nata. Babu alamun ya samu barci shima, ko idanunsa sun samu hutun daya dace ace ya samu irin na sabon ango.
Bai ce komai ba sai yasa hannunsa ya kamo nata, bata ki biyoshi ba, ba musu tabiyo shi suka fito tare zuwa karamin ‘living room’ dinta, ya zaunar da ita bisa cinyoyinsa, ya rungumota ta baya ya dora kanshi bisa wuyanta ya lumshe ido, yasa remote ya kunna tv, ya zabo musu wani movie na soyayya da akeyi a Netflix, yadda ya

manneta jikinsa haka jarumin ya manne matarsa yana zuba mata kalaman soyayya masu sanyaya rai, sai kawai ya tsayar musu da wajen da jarumin ke cewa “you are my alter ego Susanne”, anan Zayyan ya soma janta da hirar karfin hali irin nasa. Ga wani kirari na babu gaira babu dalili da ya fara yi mata yau;
“Na gaida uwargidan Zayyan da tashi, Sophie Safiyyah ikon Allah, Sarautar matan duniya bakidaya!”.
Sannan ya tallafo fuskarta cikin tausasan tafukan hannunsa, yace “Goodmorning Sophie, good morning apple of my eyes, good morning to my alter ego!”. Ya bata kyakkyawan ‘peck’ a kasan wuyanta da kuncinta, yana mai taba masangalin wuyanta, wanda yaji ya dauki dumi, zau!

“Yaa Salaam, Sophie zazzabi? Wai menene ke damunki haka? Kin ga idanunki yadda suka koma kuwa?
Jiya haka kika rufe kofa bamu yi sallama ba, koda na dawo kofarki a rufe take naji tsoron tayar dake barci kada in saki ciwon kai”.
Ya kantara karya, bayan shi a karan kansa kasa ko dosar kofar shiga sassanta yayi saboda jin nauyin idanunta. Gabadaya ya manneta a kirjinsa, yana squeezing igiyar bra din bayanta, abin mamaki Safiyyah ta kasa sakin jiki dashi sam, ta kasa jin dadin matsar da yake mata ko kadan, ganinsa take kawai wani sabon mutum ba Zayyan dinta ba. Mijin wata mata!
Janyewa ta soma yi da karfi. Kukan da bata yi ba tun daga lokacin da Zayyan yace mata zaiyi aure, har zuwa fara maganar auren, da kudin fadar kishiya da ya bata, zuwa jiya da amaryarsa ta tare. Tsabar bakin ciki da tunawa data yi Zayyan ya tara da wata macen daren jiya bayan ita…. sai a lokacin ta samu wani mugun kuka mai cin rai da azaba da fizgo daga zuciyarta zuwa makogaronta ya balle mata gabadaya.

Zayyan shi kam ya rasa ta ina zai fara lallashin Sophie yau, sai kawai ya ja ta ya rungume a jikinshi sosai, ya barta tayi kukanta mai isarta, amma ganin ta kasa yin shiru, na tsayin lokaci, sai zuciyarsa ta soma tabuwa, ta shiga raurawa, yana shafar gadon bayanta a hankali yace.
“Don Allah Sophie ki bar kukan nan haka, gaya min me nayi miki da zafi daga jiya zuwa yau kika koma kamar ba ke ba, me ya faru dake daren jiya naga idanunki sun kumbure kamar baki runtsa ba?”
Safiyyah tace “don Allah don Annabi Zayyan ka kyaleni, ka koma inda ka fito, saboda ganin fuskarka kadai na yimin fami mai yawa, ka jiwa zuciyata ciwo Zayyan, wanda har abada bazan daina jinsa ba …
Saida ka bari na riga na saba da kai all this time, kai kadai na sani na kuma aminta dashi, komai dina naka ne, komai naka nawa ne. Ni nasan kaddararka ce aure biyu, amman ban taba sanin haka nauyin kaddarar yake ba saida ta sameni, ban taba tsammanin haka da wurwuri kaddarar zata zo mana ba”.

Safiyyah ta tashi daga jikinsa tana kuka wiwi tayi dakinta. Zayyan ya bita dakin nata, yana kiran sunanta softly, yace “Sophie please, ki saurareni, ki tsaya mu fahimci juna, ni na dauka wani laifi nayi miki da ya janyo hakan, wani abu ya faru ne a jiyan da ban shigo ba? Ko wani nawa ya gaya miki magana mara dadi data janyo miki bacin rai haka, cikin taron matan da akayi jiyan?”
Safiyyah ta dago ta dube shi idanu fal hawaye, tana kara jin tsanarsa da kishinsa (at the same time), taji tausayin kanta, a ranta tace “lallai maza basu da kunya (kada Habiby yaji labari)”.
A fili kuma tace “ina rokonka alfarmar don Allah ka fita ka barni, na rantse da wanda raina yake hannunsa ko ganinka bana son yi yanzu.
Bana bukatar kadaicewa da kowa a yau, sai Allah. Ka yiwa Allah ka fita min a daki, ka barni, bana son ganin fuskarka”.

Zayyan cikin tashin hankali yace “naji zan fita Sophie. Amma inaso in san ko nayi miki wani laifi ne mai girma haka, wanda ni ban sani ba?”
Saboda shi dai ya san jiya da safe lafiya kalau suka rabu, sanda zai wuce daurin aurensa.
A zuciyarta Safiyyah tace “lallai Zayyan ya raina laifinsa, wato shi bai san ma cewa auren da yayi kadai ya dagula mata dukkan lissafin rayuwarta ba? Ya kara mata dimbin damuwa bayan wadda take ciki ta rashin samun haihuwa, shekaru goma sha da aure. Tace.

“Bana son shiga hakkinka Zayyan da kalaman dake binne a zuciyata, wadanda na tabbata bazasu yi maka dadi ba, amma don Allah ka saurara min haka. Tunda nace ka fita, to ka taimaka min ka fita”.
Zayyan ya yarda har zuciyarta iyakar gaskiyarta kenan, tunda har yau take ambatar sunansa na yanka, gatsau, ba sakayawa; ya fita ranta! Ya gama fita ranta!! Babu sauran son shi a zuciyarta!!!
Hakika tana bukatar ya kauce ya barta din, wani lokacin mace tafi bukatar ‘privacy’ fiye da lallashi, wanda a irin wannan lokacin lallashin bazai yi wani tasiri ba, sai ma dai ya kara mata bacin rai da tsanarsa.
Sai kawai ya juya da baya da baya har ya fice daga bedroom dinta, dara-daran idanunsa da suka canza launi kamar su fado a kanta, don kallon so da firgicin da yake yi mata da idanu warwaje, cikin tashin hankali.
Jin yayi tuntube da dokin kofa yasa dole ya juya cikin raunin zuciya da kasala, a sanyaye ya bar dakin Safiyyah.

Yana tafe zuwa bangarensa na cikin gidansa, kansa a kasa yake tafiya cikin damuwa mai tsanani, ya kasa dosar dakin Azeezah har yanzu, saboda ganin mood din Safiyyah, idanunsa har rufewa suke don kansu, a haka yake cira kafafunsa da kyar zuwa master bedroom dinsa.
Yana isa dakin ya haye gadonsa da rarrafe kamar mai jin zazzabi, ya kwanta rigingine tsakiyar lallausar gadon dabdalar rayuwar aurensu da kuruciyar soyayyarsu shi da Safiyyah, yana addu’ar dai Allah yasa wannan auren da yayi bai zamo ya fidda kaunarsa kwata-kwata daga zuciyar Safiyyah ba. Domin dai daga yadda take behaving yau kadai, ya tabbatar masa matsayinsa ya ragu a gun Safiyyah, koko yace, soyayyarsa tayi fading a zuciyar Safiyyah. Gashi kuma SOPHIE din itace SOUL dinshi, watau (ruhinshi) bakidaya…
Ganinta cikin wannan yanayin kadai ya fara haifar masa da nadamar yin auren. Har yake cewa kansa “Why? In the first place, me yasa bai hakura da Sophie ita kadai dinsa ba? In ya so yayi tunanin wasu hanyoyin da zasu cike masa gurbin matsalolin nasu? Ba dole sai ta hanyar kara aure ba? Amma ina! Bakin alkalami ya riga ya bushe koko yace alkalamin kaddararsu ya riga ya rubuta.

BAKIN DOHA
Jirgin Qatar Airways, wanda ya taso daga Doha din Qatar, ya sauke Yaya Sheikh da maidakinsa (Assafe) yau a birnin Kanon Dabo, inda daga nan suka yi shatar taxi zuwa Katsina ba tareda Shiekh ya gayawa su Malam Usman saukarsa ba. Yaya Sheikh, wanda sunansa na yanka (Ridhwan) kamar yadda muka sani a baya ya dawo gida bakidaya wannan karon, bayan kwashe shekaru goma sha biyar yana aikin karantarwa a jami’ar addinin musulunci ta Hamad Bn Khalifa University (HBKU) dake birnin Doha.
Can na hangoshi makale da matarshi wata kyakkyawar matashiya mai suna Assafe, wata kyakkyawar babarbariya son kowa, suna saukowa daga matattakalar jirgin Qatar Airways.
Assafe na makale da hannunshi suke saukowa, dukkansu sun yi wani fresh jawur dasu. Shi dama tun asalinsa Yaya Sheikh wankan tarwada ne ba baki bane. Ga kuma sa’ar samun mace mai kulawa dashi irin Assafe. Yana sanye da farar jallabiyya mai tsada ta larabawan Misra, akansa farar hula ce (casual attire) din mutanen Cairo.

Ridhwan har yau yana nan da dabi’unsa yadda yake tun yana saurayi, wato Ridhwan (Sheikh) mutum ne shi mai tsananin tsare gida irinna gadon malanta, da iya rike girma, amma mai saukin kai ga iyalinsa da kafatanin ‘yan uwansa mata, kowa da ya san shi ya san hakan, baya hada kaunar ‘yan uwanshi ‘ya’yan Ammi da komai. Wato Ridhwan Mutum ne mai son farin cikin kowa nashi..
Daga Malam har Ammi sun ga Yaya Sheikh da matarsa ne katsahan kamar daga sama suna sallama a tsakar gidansu.
Habawa! Sai gidan ya kacame da murnar dawowar babban Yaya, Yaya Sheikh. Hatta makwabta da suka ji labarin isowar Sheikh sai shigowa suke yiwa Ammi barka da dawowar danta. Kowa ya san son da Ammi ke yiwa Yaya Sheikh, dan dan uwan mijinta data raina a hannunta, daban yake dana ‘ya’yan data haifama. Assafe kuma ga ta da mikakken hannu, don kuwa kowa yazo yi musu sannu da zuwa sai ya fita da tsaraba gwaggwaba.
Yaya Sheikh sunyi bala’in dacewa da juna shi da Assafenshi, gata nan wanke hannu kafin ka taba sai sheki take, dukkansu kamar larabawan Qatar. Assafe fara ce tas, don usulin Mamanta Shuwa ce, Babanta kuma babarbare.
Sabanin Yaya Sheikh wankan tarwadan Ba-Katsine, zama da larabawa ne da sa’ar samu hadaddiyar mace irin Assafenshi, shi ya kara wankeshi ya kuma haska shi tas.
Assafe ‘yar manyan mutane ce a Maiduguri, mahaifiyarta Sister din Shehun Borno ce, mahaifinta kuma shine Arijinoma (Zanna) of Borno. Sune asalin kabilar barebari na Maiduguri. Karatu ya kai ta Qatar, suka hade da Yaya Sheikh a jami’ar da yake aiki, wanda malaminta ne, tarayyar da har ta yi sanadin aure mai albarka a tsakaninsu.

To tun isowarsu Yaya Sheikh hatta su Sabah basu zauna ba, gidan Malam Usman ya kara albarka, su Sabah nata kokarin kula da Antinsu Assafe. Wadda accent din hausarta keta basu dariya. Yaya Sheikh kuma ya nanikewa Ammi a Kitchen, tana kokarin hada musu abinci na alfarma, shikuma ya kasa ya tsare yanata yi mata labarin bayan rabo.
Dakinshi na da, wanda a yanzu shi ne sitting room din Malam aka sauke su, su Sabah da kannenta sun sha tsarabar Abayoyin Qatar kala-kala ‘yan ubansu daga Anti Assafe.
Yaya Sheikh da uwarsa Ammi kuwa, basu samu zama su kadai sun yi hira sosai ba sai a washegarin ranar dawowarsu, da ya shigo gaishe ta da safe, a dakinta na cikin gidan.
A gefen gadon Amminshi ya zauna, ya harde kafafu daya bisa daya suna kara gaisawa da Ammi, ta tambaye shi Assafe, ya ce ai tunda ta koma barci bayan sallar asubah ko juyawa ta kasa. Ammi ta ce,
“Ai tayi kokari ma, akwai gajiyar zaman jirgi kam a tare da ita amma haka tayi ta hidima da makota, gashi ta sha gajiyar mota daga Kano zuwa Katsina”.
Sai ya ce, “Kuma duk da gajiyar tamu Ammi bana so in kara kwana ban ga Safifi ba (Safiyyah), yaranta sun kai nawa yanzun?”
Ammi ta nisa cikin ‘yar damuwa, irin ta an maka fami akan damuwarka, ta ce, “Ta yaya za’a yi a ce kanwarka Nana Safiyyah ta haihu ko daya, amma a kasa gaya maka??

Allah bai bata ba har yanzu kamar ku take. Sai yawon asibiti. Da jimawa har dashe aka yi mata, yaron yazo babu rai. Muna dai addu’a, in tanada rabo Allah ya bata, don hakika tana cikin damuwa a kan rashin haihuwa, musamman da sanadin hakan cikin satin nan mijin ya kara aure da ‘yar ubangidansa”.
Yaya Sheikh ya furzar da iskar hucin bacin rai daga bakinsa, ya yi tsaki, ya ce,
“Matsalata da mazan Hausawa kenan Ammi, musamman ‘yan Arewa, shi yasa wallahi nake girmama balaraben mutum, da al’adunsa, ya san darajar soyayyah! Ya san darajar matar da ta aure shi tun baida komai tun bai zama abin sha’awa ba.
Halan dai kudi yayi bayan nan? Don nasan dai tun yana dalibi Safifi ta aureshi.
Ta ina Balarabe zai kara aure don Allah ya jarabce su ko matarshi da rashin haihuwa?
Ai saidai shima ya hakura, ya tayata jin abinda take ji su cigaba da soyayyarsu.

Amma ba dai ya auro wata, don tashi bata haifa ba. An nuna mata ita bata da amfani kenan, kuma ciwonta ba nasa bane, nata ne ita kadai. Ina soyayya anan?
Abin haushin Ammi da Allah ya yi mana umarnin mu kara aure sai da ya yi togaciya da cewa, in za ka iya adalci.
To da yawan mazanmu na Hausawan nan ba adalcin suka iya ba, a yi ta cusawa mata bakin ciki fisabilillahi ana jibgesu a psychiatric Ammi a kan abinda Allah ke bayarwa ba kokarinsu ba.
Mu gamu ni da Assafe, muna neman namu shekaru taran tare da aure babu haihuwa, amma ban taba kawowa raina in kara aure don hakan ba, duk da na san cewa matsalar tata ce, amma ai aka ce, ‘ka so wa dan uwanka abinda kake so wa kanka’.
Na aure ta a bansan za ta haihu ko ba za ta haihu ba. Na mori kuruciyarta, sai kuma don Allah bai nufeta da samu haihuwa ba in tsallake ta in kawo wata, wato ni wata ta haifa mun, ita ko oho ko?
In yaso koda damuwa da bakin ciki zasu kasheta su kasheta kenan ko?”
Ammi ta yi ta dariya, tana cewa,
“Ridhwan, Shehin Malami, kada dai ka ce min taya kanwarka kishi ka ke yi?”

Juyar da kai Yaya Sheikh yayi gefe, ya kyabe baki yace “ko daya Ammi, but I’m feeling for her, ina saka kaina ne a ‘shoe’ dinta, Safifi is my favourite Sister kin sani, gaskiya wannan Zayyan din bai yi ba, yadda Safifi ke sonshi da tutiya da shi bai yi mata adalci ba”.
Ammi ma taji wani iri a ranta, taso ta gayawa Ridhwan Uwarsa ma bata sonta, danginsa duka fama take da kwarzabarsu, sai tayi tunanin zai kara tsanar auren Safiyyah dinne kawai, sai ta nisa, ta sake sassauta murya ta ce.
“Ku yi masa uzuri mana, Zayyan mutumin kwarai ne, nan kusa ban ga miji mai nagartarsa wajen kula da iyali ba, shi kadai ya san dalilinsa, kuma kada ku manta yana da damar kara uku ba ma daya ba bayan Nana Safiyyah.
Ya danganta da ra’ayin mutum, ka yi masa addu’ar Allah ya bashi ikon yin adalci tsakaninsu ka ji ko Ridhwan?”
Yaya Sheikh ya ce, “Ammi, na fasa zuwa gidan nata, ba zan iya ganinta cikin damuwa ba.
Assafe ma ba za ta je ba, wallahi na tsani auren nata!”.

Ammi ba tun yau ba ta san halin Yaya Sheikh a kan Safiyyah, ba ya hada damuwarta data kowa cikin gidannan, don haka ne sai bata yi mamaki ba da ya dauki dumi a kan al’amarin yi mata kishiya don bata haihu ba. Sai kace kan kanwarsa aka fara kishiya.
Ammi ta yi ta kokarin nusar da Sheikh cewa ba rashin so ko rashin adalci kadai ke sa wasu mazan kara aure ba.
Wani kaddararsa ce, wani yanada hujja ko dalili kwakkwara. Wadanda addini kansa ya yarda dasu.
Ba kowa ne don yana son matarsa zai zauna da ita ita kadai har karshen rayuwarsa ba.
A karshe Ammi ta ce, ko ba zai je ba, ya bar Assafe ta je gidan Safiyyah, su Sabah su raka ta su san juna. Ridhwan ya mike zai fice, don hirar ta gundireshi ma, saida ya kai bakin kofa ya juyo yace.
“Ammi ko zan kai Assafen ma ba yanzu ba, tunda ba a dade da tarewar amaryar tata ba.
Bari sai zuwa wani lokaci in ta warware daga abinda aka kunsa mata”. Shi kawai bai son ganin damuwar Safifinshi.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *