Chapter 3: Chapter 3
A ranar ne da daddare yake gaya wa Ammi da Malam ashe wani gwaggwaban aiki ya samu anan Nigeria wanda ya sa shi barin Hamad Bn Khalipha University Doha, ya dawo gida gabadaya. Ya ce. Babbar jami’ar nan ta duniya “University of Arkansas” ce ta bude wani reshe nata a kasar Nijeriya a jihar Lagos, don karantar da bangaren Islamic Shari’ah, to shine suka bani shugabancin reshen. Ya ce nan da sati daya, bayan mun dawo daga Maiduguri na kai Assafe ganin gida za su yi moving zuwa Ikko.
Ammi da Malam suka yi addu’a da fatan alkhairi, sukayi farin ciki kwarai da dawowar Sheikh kusa dasu. Ammi ta ce, amma anya zasu iya zaman cikin kabilu su da suka fito daga cikin larabawa?
Dariya Sheikh yayi ya ce, “Ammi ba inda neman abinci ba ya kai mutum, aiki ai ya gaji haka.
A hankali zaki ga mun saba”. Daga nan suka koma maganar shirin auren Sabah da Rayyah, wanda ya kusanto, inda ya ce zai dauke su a weekend su je su zabi kayan dakin da yayi musu kyau tare da Assafe.
Satinsu daya a Dandume suna sayayyar auren su Sabah, Yaya Sheikh ya taka rawar gani ta babban Yaya, ya musu kayan daki na zamani na fita kunya. Inda Malam ya ba su nashi kudin masu dama a saya musu kayan kitchen da sauransu.
Bikin Sabah da Rayyah saura watanni biyu. Sabah za ta auri wani Tijjani ma’aikacin bankin Guaranty Trust a Kaduna. Sun hadu ne a wurin bikin kawarta. Rayyah kuma wani dan canji mai yawan zuwa wajen Malam ayi masa addu’a ne ya ganta, sunansa Sulaiman, ya roki Malam alfarmar ya bashi aurenta. Malam ya ba shi damar ya nemi soyayyarta kamar yadda ya yi ma sauran surukanshi. Sun jima tare har Allah ya hada hankalinsu.
Da yake dama Safiyyah shekaru biyar ta baiwa Sabah ya sa dama ba tsaran juna bane su, haka tsakanin Rayyah da Rayha shi ma shekaru biyar ne. Haihuwar Ammi tamkar tsari haihuwar ‘yan gayu.
Dr. Ridhwan Abubakar Dandume da maidakinsa Assafe suka wuce Maiduguri don Assafe ta ga gida, ta gana da iyayenta. Satinsu daya a Maiduguri (main house) dinsu Assafe wato gidan Shaihun Borno na lokacin, daga nan suka tare a gidansu dake Victoria Island a Lagos. Bai kai Assafe Abuja ba.
** **
A GIDAN ARCH. ZAYYAN BELLO
Har karfe sha daya na rana, wato har rana ta fito hantsi ya dubi ludayi Arch. Zayyan yana dakinsa a kwance, sai ka rantse da Allah ba sabon angon da aka kawowa sweet 16 daren jiya ba.
Kwata-kwatsa ya rasa laka da kuzari a jikinsa, bayan ba haka ya kamata ya kasance ba. Fisabilillahi amarya ce tun jiya a gidansa amma ya kasa ko dosar inda take.
Wayar da ke aje kan bedside dinsa ce ta soma tsuwwar neman agaji. Ta yi burarinta har ta katse Allah bai bashi ikon dagawa ba, saboda yadda Safiyyah ta dagula masa lissafi da wannan botsarewa ta farad daya da ta yi masa.
Bai san damuwarsa da Sophie ta wuce duk yadda yake tunani ba, bai san Sophie itace kadai farin cikinsa da kwanciyar hankalinsa ba sai yau. Bai san girman matsayinta a ransa ya kai na ya kasa enjoying amarcin da ya dade yana jiran ranar zuwansa ba sai yau, kawai saboda ganin halin damuwar da take ciki, akan karin aurensa. Ya lalata dokinsa da farin cikinsa.
Ya kara tabbatar wa kansa Safiyyah barin rayuwarsa ce, his alter ego, sannan duk wani farin cikinsa yana cikin walwalarta da yardarta.
Mai kiran bai fasa ba har abin ya dame shi, ya mika hannu ya dauko wayar da zummar kashewa, sai dai kuma sai ya ga sunan Azeezah wanda ya yi saving dinta dashi daidai da yadda bakinsa yake ambatar sunan nata koyaushe watau ‘ZEEZAH’ baya fadar ‘A’ din.
Ajiyar zuciya yayi, sannan ya daga kamar baya so. Hatta numfashinsa da kyar yake sauka a cikin wayar.
Ya amsa a kasalance, da murya can kasa, kamar baya son yin magana sai bisa dole, ya ce, “Hello! Ina kan layi”.
Cikin dumbin mamaki da takaici Azeezah ta ce,
“Zayyan, lafiya dai ko?”
Ya ce, “Umh, me kika gani?”.
Ta ce, “Say it aloud kawai, baka murna da isowata rayuwarka, tun jiya fa aka kawo ni gidan nan, amma ko kyallinka ban gani ba balle kalar idanunka”.
Ta soma kukan shagwaba wanda ya sa shi tashi zaune nan take. Ya ce, “Sorry Zeezah, wallahi tun daren jiyan nan a kwance nake bana jin dadi, kin gan ni ko breakfast ban samu ba har yanzu. Rabona da ko digon ruwan sha tun jiya da safe kafin in tafi daurin aure, shi yasa kawai na kwanta don bana cikin mood din da ya kamata in zo miki”.
Azeezah ta shiga damuwa, nan da nan ta ce.
“Kana ina in kawo maka paracetamol?”
Kamar bazai amsa ba saboda babu mai shigar masa masterbedroom banda Safiyyah, sai ya tuna itama fa yanzu matarsa ce, matsayinta daya da Sophie dinsa, ajiyar zuciya Zayyan yayi, yace.
“Ki zo ina masterbedroom dina, daura da kofar shiga sassan Safiyyah”.
Ta ce, “Ok toh! Ba ni minti goma in yi Kabbasa, ina zuwa”.
Sai ya mike ya shiga wanka, ya dan ji kwarin jikinsa, domin da ruwa mai zafi sosai ya yi wankan, cikin jacuzzi.
Ya fito daure da faffadan towel a kugunsa yana tsane tarin gashin kansa da karaminsa fari kal, sai ga sallamar Azeezah a bakin kofa.
Ba tare da ya juyo ba ya amsa mata da,
“Yes, come in”.
Ta shigo da karamin tray da ta shiryo kayan tea dana hot coffee a kai. Da kuma gorar ruwan faro mara sanyi da sachet din paracetamol.
Kan bedside ta dora, sannan ta dago tana kallonsa yana tsane jikinsa mai cike da gargasa. Wata yaloluwar rigar barci ce a jikinta pink color babu abinda ba’a hangowa a jikinta. Ta yafo mayafi akanta. A zuciyarta tana yaba kowacce kankanuwar halitta ta mijin nata, tace a ranta ko matarshi wace irin sauna ce da har ta barshi kallon ‘yammata a waje???
Murmushi yayi da ganin irin kallon da ta ke masa, sai ya samu kansa da buda mata hannuwa, domin ba haka ake karbar amarya ba sai a gidansa.
Yana sane da cewa ta kwana ta kusan wuni bata ko sa keyar ango a ido ba, shi ko kazar amarci da ake kawowa bai yi tunanin kawo mata ba, balle yaje dakinta, Amma ita ta tsaga billenta na amarci ta nemeshi, wannan kunyar ce ta sa shi cewa,
“Come on my dear Zeezah”. A wani irin slow Azeezah ta tafi gare shi, ya bude hannuwa da kirjinsa ya sanya ta. Sai ga Azeezah ta kankame ango ram! Kamar ba amarya ba.
Tuni Zayyan ya mance da damuwar da ‘Safiyyah’ ta haddasa masa, kwakwalwarsa ta soma canzawa sakamakon irin kissing dinda Azeeza ta soma yi mishi cikin tsakiyar bakinsa.
Tunda yake rayuwar aure da Safiyyah, bata taba seducing dinsa ba, bata taba cewa tana needing dinshi a karan kanta ba, sai dai shi ya nema, kafin ta amince ma sai ya sha wuya da magiya wani lokacin.
Yau ga shi an maida shi dan kallo, ko kuwa Rakumi da akala a hannun matarsa. Sai ta yadda ta ga dama haka Azeezah take sarrafa shi, bata barshi yayi mata komai ba, bayan ta gama kwace sitiyarin dukkan rayuwarshi a tafin hannunta…..
All his expectations and beyond, da dukkan mafarkansa a kan romantic sexual-life, yau dai gashi ya same su a gun Azeezah Murtala, har fiye da tsammaninsa.
A fahmtarsa Azeezah nympho ce a halicce, sannan ta san sirrin sarrafa Da namiji, Azeezah gwana ce wajen iya salo-salo na kwanciyar aure ba nuku-nuku ba kunya ba jin nauyinsa…
Yau Zayyan da kullum yake fama da Safiyyah ta yi masa kaza da kaza tana ki, tana sunne kai saboda kunya da nauyin soyayyarsa da take ji, yau shi ne ya koma ‘BABY’ a bakin matarsa, sai yadda aka sarrafa shi, aka juya shi tamkar waina a tanda. Aka lailayeshi aka tsotseshi kota ita ba’a saurara ba. Al’amarin da ya dauke su awanni biyu currr! A filin daga, ana fafatawa da gogewa juna hadda, na dimbin sha’awar juna da suka tara tun haduwarsu suna dannewa.
Shi da kansa bayan komai ya lafa, Azeezah ta shiga wanka a toilet dinsa, sai ya shiga wani irin tunani, ya kuma fada a damuwa, ya ce a ransa, ko dai Azeezah ta taba sanin Da namiji a rayuwarta?
Shi bai ji wata gargada ta budurci ba.
Tunda aka haife shi bai taba jin inda amarya sabon aure a daren farko ta yiwa ango abinda Azeezah ta yi masa yau ba.
Kai shi fa bai yi niyyar yin komai da ita da safiyar Allahn nan ba, amma… at their very first night, ita da kanta ta ja ra’ayinsa….
Na biyu ta nuna enjoyment dinta da abun matuka, tare da nuna samun satisfaction dashi fiye da kima, muraran ba sakayawa, ta nuna masa a yunwace take, ba kunyar idanunsa tayi seducing dinsa ta samu abinda take so, a matsayinta na budurwa wadda ta yi auren fari, kuma ta dandani rayuwar jima’i karo na farko a rayuwar aurenta. He became extremely devastated.
Yana kara tambayar kansa anya? Ko dai… Azeezah… ba virgin bace???
Saboda shi dai bai taba jin inda aka yi haka da amarya ba a daren farkonta gidan miji, in dai budurwa ce. Kai har bazawarar ma ta kan kwatanta kunya a ranar farko da sabon miji.
Ya tuno yadda ya sha fama da Sophie, a satittikan farko na aurensu, kafin ma ta yarda a yi first night da ita, shi ma sai da ya shammace ta a karshe, ya mamaye ta a inda ba za ta iya kwatar kanta ba.
Azeezah har baya son tuna irin ‘dirty talks’ din da ta dinga yi masa da ihunta, masu nuna extreme enjoyment dinta dashi da sonta da abun a fili.
Sophie kuwa kukan azaba ta dinga yi a sanda ya karbi budurcinta. Kai shi ya kasa tantancewa ma a irin yanayin da ya samu Azeezah, is she truly a virgin ko a’ah? Bai tantance wannan ba.
Ajiyar zuciya ya saki a lokacin, jin motsin Azeezah tana fitowa daga toilet, naked da ita, irin yadda bai taba ganin Sophie ta tsaya a gabansa ba, ashe shi dinnan karamin dan bariki ne, ustaziyar matarsa yakeso da barikin kawai ba sauran mata, ko kuwa yace ustaziyar mace mai bariki yake so, yau dai gashi ya gamu da wadda ta fishi son barikin da iya shi har tasa shi yana jin kunya, yana ganin tabarar mace ganin idonsa, ko daga yadda akayi ta lailayeshi daren jiya kamar jariri, amma ai karya yake karyarsa ta sha karya yace he didn’t enjoy it.
Ko jin nauyin sa babu Azeezah take tafiya zuwa gabansa tana girgiza tana sharce gashin kantin kanta da wani katon mataji (comb) wanda ba ko shakka ya san na Safiyyah ne ta dauko a toilet dinsa.
Baki bude yake kallonta har ta iso, Azeezah ta kashe masa ido ganin ya kura ma kasaitaccen kirjinta ido, wadanda suke tamkar su fashe don cika har kyalli suke, ta ce.
“Baby yaya ne? Wannan sassanyan kallo haka?”
Shiru ya yi, kafin ya ce,
“thank you for the love Zeezah. I really appreciate. Amma me ya sa ki ke amfani da matajin da ba naki ba, bakisan ko na waye ba kuma?”
Bata bashi amsa ba, ta zo ta haye bisa cinyoyinsa tana jijjiga kafa a jikinshi. Ta tallafo keyarshi da hannayenta biyu, tula-tulan dukiyar fulaninta da suka fi komai tsole masa ido a ganinsa na farko da ita, sun rufe masa fuska ruf.
Nan Azeezah ta kara gigita shi. Bai kara yi mata zancen matajin matarsa ba. Ganin ya zarme sai ta jaye kadan, cikin kissa da salo na jan rai, ta ce.
“Baby, ruwan wankanka zai huce, mu je in yi maka wanka da kaina”.
Zayyan ya riga yagama gigicewa ya ce, “Zeezah…. please….”. Don dai shi bai taba samun irin wannan abubuwan daga ustaziyar matarsa ba.
Azeezah ta dago ta dube shi da murmushin da ya wuce zallar soyayya sai ko ninkin sabon So da sabuwar sha’awar Zayyan tsagwaronsu cikin idanunta, kamar ba yanzu ya gama kawar mata da su ba… she need more from all indications.
Kamar ya tambayeta wani abu, sai kuma ya fasa. Kada yaje ya janyowa kansa salalar tsiya tayi fushi, haka kawai ya katsewa kansa daddadan amarcin da yake kwankwada.
Ya so ya tambaye ta ko a ina ta iya ‘seduction’ din miji yarinyarta da ita? Abubuwa da yawa data yi masa ya sha mamakinsu, duk da dama tace masa ita ba kifin rijiya bace tun kafin ya aureta amma bai zaci ta wannan fannin take nufi ba.
Azeezah ta shayar dashi buhunhunan mamaki, dana sexual enjoyment and satisfaction irin wadanda yake mafarki. To tuhumar ta mecece kuma? Meye amfaninta me zata sa ko ta hana?
Ya tuna cewa a zamanin nan da muke ciki na yanar gizo ma, ai babu bukatar tuhuma a cikinsa ga yaran zamani, balle ga wadda ta tashi a kudu, ta kuma yi dukkan karatun digirinta a kasar Nasara.
Shi dai kawai gara a bar kaza cikin gashinta, ya ci gaba da kwasar amarcinsa kawai, ai shi yake son hakan, sauran ya barwa Allah ba amfanin tone-tone.
In ma ta taba sanin namiji ai ba abun mamaki bane, kuma me zai iya yi akai yanzu? Ba haka yake son mace ba fitsararriya a gado? To ga dai Azeezah Murtala ya samu, ta zo masa har fiye da kintacensa.
Sai ya zamanto cewa daga wannan ranar, Zayyan ya fara canzawa, effect na sexual ectasy ya fara dibansa, tun yana kokarin adalci da saka Safiyyah a ransa har ya fara dainawa, ya zamanto cewa bai kara sha’awar hada jiki da kowacce mace ba bayan Azeezah Murtala.
Don ita kadai take da structure din macen da yake so, da kuma iya tarairayarsa yadda yake mafarki a gado, duk abubuwan da yake so a shimfida Azeezah ta hada ta kuma kware a kansu, wadanda tsayin shekara gomansa na rayuwar aure bai samu ba sai yanzu. Don haka gabadaya Zayyan sai ya susuce, ya zama mijin da baya ji baya ganin kowa a gabansa yanzu sai Azeezah dinsa.
A bisa magana ta hakika Azeezah ta gama kidima dan mutanen Rafindadi da manyan koramun dadinta, fiye da tunanin mai karatu. Ta susuta shi ta fidda shi a hayyaci da nutsuwarsa, tana shayar da shi zallar madarar soyayyar da bai taba sha a rayuwar aurenshi ba.
Kai kace Azeezah bata da wani abu mai muhimmanci a duniyarta bayan jima’i. Kodayake ibadar Allah bata gabanta. Sallar asubahi sai rana ta fito gatsau, sau tari ma sai ya tuna mata.
‘Nympho’ ce ta hadu da ‘Guru’ mai karatu me kake tunani? Domin shi ba ‘Architect Guru’ kawai bane, he is also a romantic guru.
In suka kule a masterbedroom dinsa sai su kai azahar babu ko motsinsu a gidan.
Ko fita Zayyan ya daina. Duk wasu ayyukansu masu muhimmanci ya dakatar dasu sabida ya baiwa Azeezah lokacinsa da gangar jikinsa. Wannan abu bai baiwa Safiyyah mamaki ba, don tafi kowa sanin waye Zayyan akan diya mace. Mamakinta daya ne na yadda mu’amalarsa da ita ta canza daga rana ta farko daya shiga hannun Azeezah ta soma ja baya. Wannan damuwar da yake yi akan damuwarta duk ya watsar.
Don da sadaka yanzu aka ce ya je yana begging Sophie don ta kwanta da shi irin da, shi ya san ba zai je ba. Ga inda aka maida shi jariri, Baby sama, Baby kasa, har shayar da shi ake da manyan boobs kamar jaririn gaske. Zayyan fa ya tafi da yawa Allah kadai zai tarowa Sophie shi.
Safiyyah na gefe tana ganin abu, tana kuma kara shaida ko waye Da namiji, da farko kamar Zayyan zaiyi adalci, amma da aka kwana biyu sai abun yafi karfinshi, don yanzu Zayyan da kyar da sudin ludayi yake iya takura kansa ya zo dakinta, ya yi mata gaisuwar safe, itama din a gurguje. Idan kuwa fita yayi harkokinsa ba ya iya awanni biyu cur bai dawo gida ba.
Ba don komi ba sai don irin ‘Dirty Talks’ din da ake damunsa da su a waya, wadanda su kadai sun isa hana shi sukuni da nutsuwar da zai yi aikin neman abinci dake gabansa, dole sai ya dawo gun amarya Azeezah an kashe mata lalurorinta. Don har ta fishi bukata.
Wani sirrin Azeezah da bai sani ba shine tana amfani da kayan da’a masu karfi wadanda Sophie bata ko san da irinsu a duniya ba, bata kuma da hanyar samu ko sanin irinsu, na ‘ya’yan manya ne irinsu Azeezah, sannan tana amfani da turarurukan jiki ‘oil perfumes’ masu kama jiki kwarai su fidda maigida a hayyacinsa, wato turarukan ‘yan gayu na “The Harems Scents” (ana iya tuntubarsu don samun wannan turare a 08038774430), suna da reshe a jihar Gombe, amma suna aikawa ko’ina cikin Nijeriya).
Azeezah ta yarda da turarukan “The Harems Scents”, kuma tana ganin amfaninsu, tayi amanna da cewa turarukan jiki ne na musamman na matan da suka san sirrin mallakar miji da jikinsu, ba boka ba malam, wato su ‘Addictive Ambergris, YSL Libre da Kayali Elixer.
Wadanda mahaifiyarta Haj. Nana ke mata ordersu daga wajen kawarta (Haj. Zainab Mukhtar), kai tsaye suke aiko mata har gidanta a Sunset Estate tun daga Gombe.
Yau da safe Zayyan ya shigo dakin Safiyyah cikin shirin fita, to a lokacin tana toilet tana wanka, sai ya dan zauna ya dosana a gefen gadonta yana jiranta, don duk runtsi ba ya iya fita da safe bai ga lafiyarta ba, duk da ba kula shi take sosai ba, ko ya zo tsakaninsu kawai gaisuwa ce ta addinin musulunci, don ko kusa da shi Sophie bata iya zuwa yanzu, balle a kai ga gogar jikin juna, har lokacin amarya Azeeza ba ta gama kwanaki bakwanta da addini ya bata ba.
Shima kuma baya dosarta ko ya naniketa tana dojewa kamar da.
Yana zaune yana jiran fitowar Sophie. Wayarsa ta yi ruri daga cikin aljihunsa, bada wani tunani ba ya amsa a handsfree, daidai Safiyyah ta fito daga wanka. To da yake ya bata baya bai ga fitowar tata ba, sai ya amsa….
“Zeezah yaya dai?”
Ta ce, “Baby, ya za ka fita yau da wuri ba ka yi min wanka ba?”
Murmushi yayi ya ce, “Sorry Baby, ina sauri ne za ni wani supervision na wani estate da gaggawa, yanzu zan dawo in miki kin ji Baby?”.
Ta ce, “To ni dai Baby gaskiya ban yarda ba ka zo, I’m thirsty gaskiya, ka bar ni sai Zikiri nake, wallahi kamar in biyoka…., kafin ka dawo sai gawata in ba ka zo an yi ko ‘one round’ yanzu ba….”.
Azeezah ce ta fadi kalaman nan wadanda suka kusa saka kunnen Sophie kurumcewa, ta yi suman tsaye na wucin gadi, ta kai yatsunta biyu ta toshe ihun da dodon kunnenta ya kama yi mata, na amsa kuwwar kazaman kalaman Azeezah ga mijinta rabin ranta Zayyan yau a kunnenta.
Zayyan sai zuba murmushi yake yana sosa kai da hularsa, he became 100% aroused! Ya ce, “Okey-okey Baby please, hold on, gani nan zuwa yanzu, ba wani nisa na yi ba kinji Baby?”.
Da haka ya fice dakin Safiyya ko waiwaye babu. La shakka Zayyan ya manta abinda ya kawo shi dakin nata ma a lokacin, haka yama manta da mai dakin zata iya jin su, tunda a handsfree ya saka kiran, kuma ya manta har sunansa na yanka a lokacin nan da Azeezah ta murda kambunta, ta gama sukurkuta shi da dirty talks dinta data saba tun zuwanta.
Yana ficewa Safiyyah ta taka a hankali zuwa balcony dinta.
Tana tsaye jikin railing din barandarta tana hango shi ya nufi kofar shiga sassan Azeezah har lokacin suna waya shi da ita kamar zai shige cikin wayar, tun ma kafin ya isa kofar tata Azeezah ta fito daga ita sai wata fitinanniyar lingerie suka game a bakin kofa suka manne jikin juna, Azeezah ta dane gadon bayansa shikuma ya goye ta suka shige sassanta suna kissing juna.
A hankali Sophie ta russunar da kwayar idanunta kasa, sai wasu zafafan hawayen suka digo dis-dis! A kan babban yatsan kafarta, lebbanta suka shiga wani irin karkarwa cikin kokarin shanye kuka, wannan kadai ya nuna halin azabar da ta samu zuciyarta a ciki a wannan lokacin.
Sannan hawayen jinsu ta ke kamar tsakuwoyin barkono a idanunta, sun kuma ki daina zuba balle tsakuwoyin su daina cakar mata idanunta, suna neman makantar da ita daga wannan ‘scene’ data gani tsakanin Zayyan da wata mace, amma a take sai ta shiga gayawa kanta da kanta cewa Zayyan bashi da laifi.
Wannan ita ce hakikanin rayuwar da Zayyan ya dade yana so su yi, ire-iren abubuwan da yake so ta dinga yi masa kenan, for over a decade amma bata bashi hadin kai ba. Because she’s not that romantic in her nature!
Wannan itace irin macen da Habiby dinta yake kulafucin samu. Me ido a tsakar ka, me za ta yi yanzu da zai dawo da soyayyarta a zuciyar Zayyan? Babu! Ba’a bari a kwashe daidai. Ta baro kari tun ran tubani.
Zayyan ya kara sire mata, irin sirrr! Dinnan. Domin ya tabbata yanzu shi mutum ne mai bin “kawar zuciya”. Wato irin mutanen da duk abinda zukatansu suka kawata musu akan mace sai sun sameshi sun dandana hankalinsu ke kwanciya.
Ta tsani sake ganinsa, ta tsani sake jin muryarsa, balle sake hada jiki dashi. Da tanada yadda zata yi da hakika ta dakatar da shi daga kawo mata wannan munafukar gaisuwar safen, wadda babu abinda ta ke kara mata sai bakin cikinsa, da kunar zuciya akansa.



