⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 4: Chapter 4

A hankali ta rarrafa ta bar jikin balcony din, ta koma zuwa dakin barcinta.
Safiyyah ta tsaya a gaban dogon madubin dakinta, tana karewa kanta da halittarta kallo, ta kara kallon kanta sama har kasa, she’s no longer her former self, that beautifull, energetic and elegant Sophie! Domin sai ta ga kamar an kara rage mata girman boobs dinta da fadin kugunta, compared to na Azeezah. Ma’ana dai ta dawo rabin yadda take daga ranar da Azeezah ta tare a gidansu zuwa yau.
Ashe ranar da Azeezah ta shekara tare dasu, suna guma mata wannan bakin cikin, sai dai Malam da Ammi su zo su dauki kasusuwanta a gidan Zayyan Bello???

Don haka washegari Sophie taki bude masa kofar dakinta da safe, ta kuma saka ‘key’ dinta a jiki ta ki zarewa, gudunma kada ya yi amfani da wani key din ya shigo mata.
Da safe ya zo kamar koyaushe ya yi bugun duniyar nan bayan fitowarsa zai fita aiki a makare yadda ya saba fitowa yanzu very late. Safiyyah na jinsa, ta hada kai da bangon dakinta tana zabga kuka mai cin ruhi.
Da ya tabbatar Safiyya ba za ta bude masa kofa ba yau, kuma ya tabbata tana jinsa, sai ransa ya baci sosai, amma duk da haka ya kasa tafiya ya kyale ta don yana jiyo sautin kukanta, ya koma dakinsa ya dauko safayan makullansa ya zo ya saka, ya yi ya yi ya bude key din ya ki shiga, sai ya gane ta bar nata a jiki, Zayyan ya soma magana cikin lallashinta, yana rokonta ta bude shi lafiyarta kawai zai gani ba bata mata rai yazo yayi ba.

Zayyan ya yi ma Sophie rantsuwa kan cewa bai san me ya yi mata ba jiya da ya bata mata rai har haka, yace ta yi wa Allah ta bude masa kofa su gaisa. Bazai iya fita gidan bai ganta bai ga lafiyarta ba.
Safiyyah ta san idan ta sake ta bude ta ganshi a gabanta tana iya ji masa ciwo, ta hanyar mummunan yakushi da faratanta wadanda rashin nutsuwa yasa ta kwana biyu ba ta samu yankewa ba. Don sai ta tabbata ta yiwa fuskarsa kaca-kaca da farata zuciyarta za ta huce daga abinda taji yana yi a waya jiya da wata yarinya. Don haka kin budewar ta rabu da shi, ya fi budewar zame musu alheri.
Ta koma ta jingina bayanta jikin kofar da yake bugawa, hawaye a fuskarta shabe-shabe kamar an kwance famfo.
Shima jingine yake jikin kofar tata, ya kasa tafiya ayyukansa, yana ci gaba da magiyar rokonta kan ta bude, don ya tabbata yau laifinsa babba ne a gun Sophie, yace zai amshi duk wani laifi da ta ke tuhumarsa a kai, zai kuma bata hakuri sai ya tabbata ta huce.
Shi da kansa da ya gaji da tsayuwa da magiya, tsayin kusan awa guda sai ya bar gidan. Ransa a matukar bace da abinda Sophie tayi masa.
** **

BAYAN KWANA BAKWAI
Ya kama yau zai bar hannun amarya Azeezah, wato Azeezah ta gama kwanaki bakwanta da addini ya bata a matsayinta na budurwa, yau zai koma dakin uwargida Nana Safiyyah, tun ranar da Safiyyah taki bude masa kofa basu kara haduwa ba.
Yau Azeezah sukuku ta wuni a gidanta ba kuzari ba walwala, fuska murtuke, sai kumburi take masa, ta tsani wannan Safiyyah din, saboda yadda Zayyan ya damu da ita duk da basa tare, domin baya awanni biyu bai ambaci sunanta ba ko cikin hira ne zai ce mata Sophie kaza…Sophie na son kaza, Sophie bata son kaza.. Ji take kamar ta shaqeta ta mutu ta bar mata Zayyan ita kadai, su cigaba da cin karensu ba babbaka su kadai, da cin duniyarsu da tsinke, ya dauwama tare da ita ita kadai cikin wannan zumar soyayyar tashi, ba zancen raba kwana, wani irin son Zayyan Azeezah take yi yanzu har kamar hauka, kamar ta cire rai ta bashi, wanda a sanda yazo mata da zancen aure bata yi masa irinsa ko kwatankwacinsa ba, saboda jin yanada mata.
Sai tasa a ranta rainon wata zata aura kawai, bai iya soyayya ba. Sai yanzu ne ta san girman kyautar da Allah yayi mata, bayan sanin waye Zayyan din, ba kowa bane sai shalelen Mama mijin Safiyyah wanda ya kamata tace lallai uwarsa ta iya yiwa mata haihuwar miji na alfahari da likawa a goshi, wanda a ko’ina zata yi tinkaho dashi a cikin tsararrakinta, za kuma ta yiwa sauran mata kwalele da kasancewarta matar Arch. Zayyan Bello Rafindadi.

A kowanne wayewar garin Allah ta dubeshi yana barci da ita bisa kirjinsa, ko yana making love da ita sai ta kara jinjinama wautar matarsa, wannan kyauta ce kawai Allah ya dauko ya bata har gidan ubanta, tamkar gasashshshen tsuntsu daga sama, bada tsumi ko dabararta ba, irin dai mijin da take mafarkin samu wanda ko a mafarkinma bata zaci akwai irinsa a duniya ba sai ko a duniyar mafarkin.
Wannan kuma ‘sexual bond’ ne wanda nan da nan yayi binding dinsu together, ko shima ya tabbata zai yi kewar fetsararriyar fitsararriyar maytacciyar soyayyar matarsa Azeezah, bai taba ganin mace ‘expert’ a gado irin Azeezah ba, komai na halittarta da dabi’arta daban dana sauran mata, she’s more than enough for him. In dai don jin dadin rayuwa namiji ke aure, ba sauran muhimman dalilai ba, to Azeezah itace kat! Din jin dadin Da namiji, ta iya tafiyar dashi a shimfida, ya tabbata idan ya koma gun uwargida Safiyyah…. zai yi kewar mayatarta da ‘insatiable sexual nature’ dinta….
Daga karfe biyar na yamma Azeezah za ta fita girki Safiyyah ta karba.
Tun tarewar Azeezah a gidan Zayyan ‘takeaway’ yake sayo musu su ci saboda basu ma da lokacin shiga kitchen, kusan koyaushe suna jarabce da juna. Nympho da Guru. Cin amarcin suke da gaske. Sai dai ya aika order a kawo musu daga ‘Cilantro’ da ke Maitama, wanda shine zabin Azeezah.

Har karfe takwas na dare Zayyan bai bar dakin Azeezah ba, shi da ya kamata ace tun yamma ya bar dakin. To ina sarkin romansiyyar ta bar shi ya fito ma?
Tana can ta manne masa. Sun yi soyayya kamar ba gobe, kamar baza’a ragewa jibi ba. Da kyar da sudin ludayi da magiya Zayyan ya samu Azeezah ta sako shi, lokacin wajen karfe goma na dare.
Shima din idanun Baba Bello ya tuna, suna kallon shi cikin tsare gida, a ranar da yake bashi amanar Safiyyah, da irin nasihar da ya sha yi masa na ya rike amanarta koyaushe suke hira akanta.
Tuni Safiyyah ta yi barcinta, don bata ma da masaniyar cewa yau ne za ta karbi girki. Tunda ba lissafa kwanakin da yayi a gun amarya take yi ba.
Ta kuma rufe kofar sassanta bakidaya tun kafin magariba.
Don haka da nashi keys din ya yi amfani ya shigo gidan, jin komai tsit, sai hucin ‘Air Condition’ bai bashi mamaki ba, don ya santa da wuri take barci, musamman in baya nan, abinda ya bashi mamaki shi ne, da bata san cewa yau za ta amshi girki ba, rashin damuwar Sophie da shi yanzu har ta kai hakan???
Ko cokali bai gani akan dining ba, mai nuna ta tanadar masa abincin dare ko tayi wani shiri na murnar tarbarsa.

Ya hau jan santala-santalan yatsun kafafunta da hannunsa suna bada kara kas-kas, yana kiran sunanta softly, ta hanyar jansa sosai, “Sooophie, Soooophie, please tashi mana, wannan wane irin barcin wuri ne?”.
Safiyyah ta soma kokarin bude idanunta a kansa a hankali, sun yi luhu-luhu don nauyin barcin da ke cikinsu.
Ta yi mamakin shigowarsa dakinta a daidai wannan lokacin, domin da safe yafi shigowa ya gaisheta ya ga lafiyarta ya fita, tun zuwan Azeezah ita da shi basu kara haduwa a irin wannan lokacin ba, sun koma kamar wasu bakin juna.
Ganin ta bude ido sosai ta kuma mike ta zauna. Sai ya zauna a gefen gadon nata yana tambayarta,
“Ko zan samu abinci a gurinki ko yaya ne Sophie? Dare yayi bana son fita, ko yin order daga cilantro cikin dare”.
Safiyyah ta mike zaune sosai tana gyara rufar duvet dinta. Riga da wando ne a jikinta na barci kalar purple masu dan kauri (winter pajamas) na mata, jikinsu kamar na mussa (mage) don laushi. Ta kara jan duvet din sosai ta rufe jikinta ta koma barcinta, uffan wannan Sophie ba ta ce masa ba.

Zayyan ya janye bargon gabadaya ya jefar gefe, ya ce, “Yau Safiyyah gani ki kashe ni kawai ki huta, tunda kin tsane ni, ba kya ko son ganina don na raya sunnar Annabi.
Auren da da yardarki da amincewarki dari bisa dari aka yi shi, to why the sudden changes? Lokaci daya kin canza mini kamar baki taba So na ba!”
Dole Safiyya ta tashi zaune tana mutsittsika idanunta, ta nemi barcin idanunta ta rasa, da alama yau rigima yake ji, kuma ita ta kawoshi, ta ce,
“Babu abin da na canza fa, kawai na fi jin dadin ‘privacy’ ne Malam, kuma wallahi a kwanakinnan banason yawan magana ko hayaniya a kaina”.
Cikin matukar takaici da mamaki Zayyan yace,
“Ni ne malam ko?
Nine mai hayaniya,
Sophie ni kika zabi privacy fiyeda ganina ko, ni din?”
Ya fada cikin nuna kansa da dan alinsa.
Tace, “Sabbeni yi hakuri, idan gaskiyata ta bata maka rai”.
Yau dai yana shan sunaye kala-kala yace a ransa. A fili kuma yace, “To tashi ki bani abinci, shine kawai zai sa na hakura”.
Ta ce, “Na rantse da Allah ban girka komai ba, a cikina ma ban ci ba, balle in ba wani, don na san ba a nan kake ci ba, tunda kana da mai baka yanzu”.
Ya ce a kufule.
“Har yau ranar girkin naki?”

Wata ‘yar dariya Safiyyah ta yi mai baiwa miji haushi, wadda tayi bala’in kular da Zayyan, ta ce,
“Girkina kuma? Ai ni ba ni da girki yanzu a gidannan, wannan sai yara sabon jini, tuni ni na girma da wannan abun, can gasu gada”.
Zayyan ya kulu, iya kuluwa, ya fusata iya fusata ce, “Look Sophie, we are not kids, za ki bani abincin ne ko in fita in saya?”
Safiyyah ta runtse idanunta tana hango yadda Azeezah ta manne shi ta makalkale shi suka shige dakinta suna tsatsibar bakin juna, kawai ta ji bata da wani sauran buri ko SO, ko fata (hope) a kan Zayyan yanzu.
Ta bude jajayen idanunta dake cike da barci sosai a kansa, ta ce.
“Malam! You can go back to where you came from, ku dora daga inda kuka tsaya. Ban yi wani girki da kai ba ni, hasalima bana kirga kwanaki. Rayuwar da aka yi a baya ta kauna da soyayya ba irinta ake yi yanzu ko za’a cigaba da yi yanzu ba. The narrative has changed.
Don haka ni ban san yau zaka zo ba, tunda baka taramu ka ce ga ranar da kowacce zata dinga yi maka girki ba, ko kwanakin da zamu dinga yi a girkin, duk wani abu na al’ada da akeyi na zuwan amarya ni wanne aka yi min a ciki? Da zaisa in san ranar girkina?
Kayiwa Allah Zayyan ka barni, ban cika son tsananta magana ba a kwanakinnan, taimaka min ka koma gun matarka”.

Zayyan ya fusata iya fusata, yau shi SOPHIE ta daina so take kora, don kawai ya kara aure? Ita kuma tana ganin shi bai san me take ji a nata ran ba. Jin dadin da ke cikin karin auren sa kawai ya sani.
Maimakon ya kwantar da kai yayi lallashi, kamar yadda ya kamata, ita kadai tasan yadda zuciyarta ke tarnaki, kadan take jira ta fashe da kuka, auren duk ya fita ranta. Ganin canzawar kamanninta shiyasa bai kara magana ba, sai kawai ya dauki pillow daya a gadonta ya jefa akan Sofa dinta ya kwanta da kayan jikinsa da komai bai ko yi tunanin canzasu zuwa na barci ba a haka yayi kwanciyarsa.

Dama kuma Azeezah ta tara masa gajiya, haka ya samu ya yi ta ramuwar barcinsa cikin sukunin zuciya wanda bai samu yi a dakin Azeezah ba, harda wani irin contentment yake ji a cikin barcin, in ya tuna a dakin SOPHIE yake yau, ji yake kamar ya baro wani bakon wuri da baya sakewa, har lokacin sallar asubahi ya fita Zayyan na barci.
Safiyyah ta tashi ta yi sallah tayi lazumi duk bai ko motsa ba, da farko ta ki tashinsa ne don haushinsa data ke ji, sai kuma ta tuna hukuncin tata sallar in bata tashe shi din shima yayi ba.
Idan kuma ta kula shi ya samu damar yi mata surutun da yanzu ya daina burge ta sam. Sai kawai ta kure karatun Alkur’ani cikin Suratul ‘ANFAL’ daga cikin Digital Qur’an dinta da karfin sauti kamar ta fasa dakin, kuma dole shi ne abin da ya tada shi ba shiri yana mutstsikar ido.

Ya kalle ta tana shafa lotion dinta, fitowarta kenan daga wankan safe. Ruwa yana gangarowa daga cikin gashin kanta data wanke tas da kumfar shampoo din Vegamour. Kewar Sophienshi ta kama shi, ya tuno lokutan walwalarta da far’arta dake sashi nishadi, a baya in wani yace zai iya kwanaki biyu ba tareda ita a gefensa ba bazai taba yarda ba, yau kuwa kwananshi bakwai cif! Bai rabeta ba.
Man data ke shafawa normal lotion ne, shine lotion dinta na din-din-din, wato ‘Nivea Radiant Beauty’, shi take matsa tana shafawa a hankali a gabobinta cikin rashin kuzari, a lallausar fatar jikinta, Zayyan ya shiga matukar kakabi a cikin ransa…. yau Sophie ce babu abinda ya dameta da presence dinsa a kusa da ita? Lallai ya yarda KISHI yana lalata soyayyah!!!
A kasalance da jiri a tare dashi ya mike ya shige toilet dinta. Sai da ya yi wanka sannan yaji kwarin jikinsa, ya fito daga shi sai shorts a jikinsa, yana tsane kansa da towel fari sol.
Sophie ta daga kai tana satar kallonsa, sai taga kamar yau ta fara ganinsa sabida kyan da yayi mata. Ya kara kuruciya, shi dinne dai Zayyan dinta yana nan yadda yake amarya bata gutsirar mata komai a jikinsa ba. Hakanan ta ji kunya ta kamata da suka hada ido dashi, ya kama idanunta ‘red handed’ idanunta suna satar kallonsa, kunyar da ba jimawa ta rikide zuwa tsananin haushi da bacin rai.
Bata san lokacin data yi tsaki ba. Ya ce, “Hey! Ma’am, are you hissing at me? Tunda ba za ki gaishe ni ba, sai satar kallon kyakkyawan Barumen mijinki Zayyan, bari in koma matar ni in gaisheki da dukkan harsunan duniya.
Assalamu Alayki Yaa Habeebty. Good morning Apple of my eyes, good morning my alter ego, my co-architect! Ina kwana masoyiyata? Ekaro, Sabahul khair!”.

Zayyan ya jero gaisuwar cikin yarurruka daban-daban na nasara, larabci, Hausa har da harshen Yoruba. Ya rasa da wane irin language ya kamata ya rarrashi Sophie?
Safiyyah ta yi kamar ba ta ji shi ba, amma a ranta ta amsa na farkon wato sallamar larabcin. Tunda amsa sallama ga musulmi wajibi ne a cikin addini.
Ya kwace ‘lotion’ din daga hannunta, ya matso kadan a tafin hannunsa wai zai karasa shafa mata. Ya janyota jikin shi yana murza mata man a gadon bayanta, murzar tashi mai tarin manufofi wato invitingly da rarrashi yake shafa mata man, yana kallonta da kallon da a baya ke ribatar zuciyarta, ta amsa tayinsa koda bata so. Amma yau cikin sauki ta zame jikinta ta mike daga jikinsa ta bar wajen zuwa gaban closet dinta ta zabi kaya ta sanya.
Kitchen ta nufa da niyyar ta hado masa tea da simple abinda da zata iya, tana rokon Allah ya gafarta mata yunwar data bar Zayyan ya kwana da ita daren jiya, amma jiyan ji kawai ta yi ba zata iya ba shi komai nata ba, ba abinci ba har murmushinta, saboda zuciyarta ta riga ta sallama shi, musamman in ta tuna su biyu keda shi yanzu, su biyu zasu dinga sharing dinsa, sai ta ga babu amfanin komawa kamar yadda suke a baya, sawwa-sawwa dai, soyayyar da ke zuciyarta a kan mijin nata ta riga ta ji mugun targade, ko ta karye, ta kuma goce kashi daga muhallinta na baya.

Ta kawo breakfast har kan dining ta ajiye masa, ta yi kamar bazata yi magana ba ganin yana waya da Yaya Zubaina ne, saida ya kammala ya ce ma Zubaina “ga Sophie din”.
Da farko kamar bazata amshi wayar ba, sai ta tuna Zubaina ce fa. Don haka ta amsa ta gaisheta da respect kamar yadda ta saba gaisheta a waya, Zubaina tace.
“Safiyyah kiyi ta hakuri da Baffan Mama kinji? A wannan dan tsukin babu irin abinda bazaki gani ba na sauyi daga mu’amalarku, saidai ki kauda kai, ki kuma kai zuciyarki nesa, amma in sha Allahu komai na duniya mai wucewa ne, fararre ne kuma kararre, bar shi yayi ta dokin aurensa komai na duniya yanada iyaka, banda ikon Allah, har kuwa da rayuwar bakidayanta watarana babu mai dauwama a cikinta, balle auren da aka yi shi don bin KAWAR ZUCIYA kawai da rainama wani matsayin da Allah ya bashi, ba don Allah ba.
Safiyyah kece zabin Babanmu, ke Baba ya aura masa da kansa, kuma na tabbata ke kadai ce rufin asirinsa, da Baba yana nan da abubuwa da yawa dake faruwa yanzu da bazasu faru ba, don haka kiyi hakuri ki masa uzuri sau saba’in kinji Safiyyah, pleeeease Sophie!
Ba don shi ba, a’ah don ni Yayarki Zubaina, don kuma son ki da Allah kema ya karbi uzurinki!
Don yace min baya jin dadin yadda kike treating dinsa yanzu”.
Safiyyah taji wani iri a ranta, idanunta fal kwallah ta daga su ta dubi Zayyan dake tsaye kanta, wanda idonsa ke kanta a lokacin yana kallon reactions dinta. A sanyaye kuma cike da girmamawa ta amsawa Zubaina da cewa.
“In sha Allahu Yaya Zubaina, bazan baki kunya ba”.

Bayan ta mika masa wayarsa ne ta russuna a gabansa, tace.
“Yaya Zayyan ga breakfast”.
Da matukar mamaki ya dago kansa daga fuskar wayarsa ya dube ta. Ta kauda ido daga saitin inda yake gabadaya.
Ya ce a hankali da matukar karaya,
“Sophie, yau ni ne kuma Yaya? Yaushe na koma Yayanki?”
A hankali ta kalle shi itama, sai taga har ‘yar ramewa yayi, duk da amarcin da yake kwankwada, yana cikin damuwa a kanta. Ta ji wani irin tausayinsa a ranta ganin yadda hatta idanunsa ya fada, sai ta zauna a kujerar da ke fuskantarsa ta ce.
“Laifi ne don na koma cewa Yaya Zayyan? He is no longer my Habeeby ni kadai, wannan mijin mata guda biyu ne. Idan na ce ‘Habiby’ ban sa minjaye ba, ai ya zama na yaudari kaina, na so kaina, ko kuwa?”.
Ya tsayar da idonsa cikin nata, yana mamakin kalamanta, kamar ba yanzu ta cewa Zubaina ta daina ba, ya ci gaba da kallonta har yasa ta sunkuyar da kanta, tana jin kamar idanunsa na mata bulala, ya ce,
“Alright, ko me za ki ce dani, ko wanne irin tunani ne na banza a ranki game da ni, kowanne irin zagi zaki yimin kin yi daidai Sophie, tunda ba zan dake ki sannan at the same time, in hana ki kuka ba.
Amma don Allah Sophie kada ki kara ce min Yaya Zayyan, kin sa yau duk na tsani sunan nawa na yanka, domin bai min dadi ba ko kankani a bakinki, tunda bada kyakkyawar niyya kika ambata ba, gatse ne.
Wai ma shin? Meye laifina ne gare ki, ko don kawai na kara auren da banyi ba sai bisa yardarki? Kin bi kin tsane ni kin fitine ni da bakar magana”.

Safiyyah ta yi murmushi ta ce, “Kada Allah ya nuna min ranar da ni Safiyya zan gaya maka bakar magana Zayyan alhalin ina sani, ai ko ba komai mijina ne kai, wannan kalmar bata canza ba, Allah kuma yace in girmamaka, kawai zancen nan ne na Hausawa da suka ce, idan kida ya canza, rawa ma dole ta canza.”.
Ya ce cikin daga mata hannu, “Ni ba abinda ya canza ni, babu abinda ya gutsirar miki ni kin ji, in kuma ba ki yarda da hakan ba, zo nan mu bambance aya da tsakuwa, in tube yanzu a gabanki, in yaso in nuna miki komai na jikina yana nan yadda yake ko kya sakar min mara in yi fitsari”.
Safiyyah ta kyabe baki, da da ne ya fadi cewa zai tube a gabanta kunya zata ji akan kalamansa, har sai kunyar ta nuna akan fuskarta, amma yau ko a jikinta, ta mike daga inda take zaune, tana tafiya tana magana cikin kunkuni, sai ka saurara sosai zaka ji me take cewa,
“ai wallahi a kai kasuwa. Ba dai ni Nana Safiyyah diyar Ammi da Malam ce zan kara hada jikina dana mijin wata ba. Sharing miji?! Umhh! Ai sai dai in ji shi a labarun hikaya irin na TAKORI.
To me kuma zan dauka a Zayyan din?
Ai ya riga ya koma leftover!”.
Zayyan ya yo kanta, ta shige toilet da gudu, ta murza mukulli. Cewa yake “Silly girl kawai! Da ki tsaya mana in ba tsoro ba? In yaso kiga irin aikin leftover daga sabbin darussan da ya samo a sabuwar makarantar da ya shiga, mai kishin tsiya har dana jaraba, ‘yar rainin wayau kawai”.

Da daddare ma a haka suka kara kwana suna tafka rigima tana gasa masa baqar magana cikin ruwan sanyi. Duk sun koma ma juna wani iri. Da gaske ta kasa ko zuwa kusa da Zayyan, shima ya kasa kusantarta a shimfida balle ya yi sunna da ita yadda ya saba, don ya kasa jin shaukin kusantarta, kamar yadda yake shaukin komawa wajen Azeezah.
Don haka a washegari, ya kama ta gama kwana biyunta kenan, tun karfe goma na safe ya bar sassanta. Bayan ya gaya mata cewa ta jika abunta ta shanye, ita ce da matsala yanzu, shi ya kama dahir.
Maganarsa ta yiwa Sophie ciwo. Don haka ta bashi kyakkyawar amsa da cewa.
“Ni kam ai Allah bai dora min jarabar da zan kasa zama dakai kai kadai ba, har sai na tsallaka na karo wani, bani da wata matsala wallahi daga nan har gaban abada, kafi kowa sani cewa ni ba jarababbiya bace!”.
Sai da ya dauki hularsa da mukullin motarsa ya fice ne ta ji kuka na son kwacewa jarumtakarta, don kuwa daga nan dakinta kai tsaye sassan Azeezah ya wuce, ta yi masa maganin dukkan bacin ran da Sophie ta dirka masa.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *