Chapter 5: Chapter 5
Azeezah is always ready to welcome him ya sani dama, ita ya san ba za ta ki hada jiki dashi wai don ya fito daga dakin Sophie ba. Safiyyah sarkin bakin kishi.
Hakan ce kuwa ta faru kamar yadda ya yi hasashe Azeezah shi kawai take jira, ta matsu, ta kai makura wajen kewarsa, kadan ya rage taje ta fiddoshi daga dakin Safiyyah, nan suka dora amarcinsu daga inda suka tsaya wane na satin baya.
Safiyyah aka bari da kwana cikin kunar zuciya da bakin cikin Zayyan data kasa sabawa da shi har yau, in ta tuna yana dakin wata mace cikin mayafi guda da ita. Ji take kamar ta kurma ihu ta fita daga gidan. Ko da wannan feeling din aka bar diya mace a kan kishiya ta tabbata ya ishe ta jihadin bin Allah da umarninsa a zaman aure. Tunda shi yayi musu umarnin su aura su kara din.
Amma tana mai jin cewa Zayyan ya tafi daga zuciyarta yanzu, tanada yaqinin ba zai taba dawowa kan matsayinsa na baya a zuciyarta ba.
Ita yanzu babbar damuwarta cikin da ta ke buri. Ta ke fata da addu’ar samu kullum Allah ya bata tareda Zayyan, a ina za ta samo shi, tunda ta haramtawa kanta hanyar samoshin? Wato tunda ta hakura da Zayyan Bello gabadaya??????
Ya kama yau Safiyyah zata karbi girki kasancewar Azeezah in Zayyan yana gida ba ta barinsa ko na minti biyar, zata hana shi komai sai aikinta, hatta fitarsa aiki yanzu ya rage saboda fitinar Azeezah.
Tana cikin sati na biyu da tarewa amma kullum amarcin nasu sabo yake dada komawa.
Duk yadda Safiyyah ke tunanin abinnasu mai wucewa ne wato zasu gaji su rage abin ya wuce da saninta, domin Azeezah na amfani da kayan mata, wanda ya sa ita bata gajiya da shi. Kodayake a halittar Azeezah ko bata yi amfani da kayan mata ba, to mai yawan bukatar miji ce, ga iya gado, ga iya salo, ga iya juya miji a shimfida cikin gayu da ‘nude’ kwalliya mai daukar hankali.
Ta wannan fannin kam sai mu ce Azeezah Murtala ta cimma duk wasu expectations dinsa, har ta zarta. Shi mai son Sophie ta dinga sa masa ýan ‘Lingerie’ ita Azeezah in suna tare abin ba a cewa komai, domin kullum ita kam in suna tare su biyu idan har ba ‘nude’ zata zauna masa ba, to ‘Bikini’ ne ma a jikinta.
Da yana da bukata da bashi da ita, in dai yana gidan Azeezah sai ta dulmiyar da shi a duniyarta, gabadaya ta canza tsarin rayuwarsa, zuwa yadda ta ke so, har shi da kansa yanzu yake tambayar kansa ko shin a da wane irin rayuwar aure yake yi da Sophie da ba enjoyment???
Shi kam yanzu ya san yana dandana zumar aure, Safiyyah bai san da me zai kwatanta kidahumancinta a wannan fannin ba, one and only thing da ya sani shine, watau yanzu yake dandana dadin aure yadda yake so.
Ba zai ce yanzu ya san ya yi aure ba, don hakan zai zama tamkar cin fuska ne ga Safiyya, amma kusan a badini gaskiyar kenan.
Hakika ya samu Azeezah daidai da ra’ayinsa, kai ya tabbata Azeezah Murtala ta kereshi, tayimasa fintinkau (at being romantic) don shi da kansa jiya da dare yace ta barshi ya huta please, (he is not a sex machine) yana bukatar hutu yau.
Yau da Safiyyah za ta karbi girki bayan Azeezah ta kare kwanaki biyunta, Zayyan na shaving gefen fuskarsa da clipper a toilet dinsa don rage gargasar gefen fuskarshi data kara cikka, ba share sajen yake ba a’a gyara shi yake yana rageshi da shaping dinsa da tsadaddun kayan askinsa na ‘Argan’. Azeezah ta leko.
“Baby!”.
Ya ce, “Na’am Honey!”.
“Ka zo ka kai ni inci burger mana kafin lokacin shigarka barci?”
Zuwa lokacin ya kammala abinda yake yi, daga shi sai nickers, yana wanke kyakkyawar fuskarshi mai cike da gargasa cikin ‘sink’ ya ce,
“Kada kisa mu yi dare kuma, Sophie da wuri ta ke barci please”.
Azeezah ta kalle shi kawai a sheleke, shida Sophien daya ambata, ta ce,
“Whatever! Koma dai menene ni dai ina son cin burger yanzunnan”.
Ta fada tana miko masa farar shirt dinsa tare da trouser data dauko masa daga wardrobe, ya san rigimar Azeezah, tunda ta ce haka ko za su kai sha biyun dare suna jayayya ba barinshi za ta yi ba sai ya kaita din.
A hanzarce ya sanya kayan da ta miko masa din. Sannan ya ce, “To mu je, amma don Allah Azeezah kada mu shiga lokacinta, kin ga is almost past 8pm fa. Yayar taki lallabata nake yi, kullum a wuya ta ke”.
Azeezah ta dan tale baki suka fito daga toilet din, ta kunna burner, ta zuba turare tana fadin ya jira ta ta yi ‘kabbasa’ tukunna kadan kafin su fita.
Yau dai yayi ta maza ya musanta, don karo na biyu kenan data ce ya jirata tayi kabbasa sannan su fita, ya ce, “Zeezah, bana son kina fita da kabbasa dinnan, babu kyau fa, mace ta fita waje musamman cikin maza tana baza kamshi mai tada hankali haka.
Kamshi tsiraici ne ga mace, haba haka fa turarennan yake binki duk inda kika yi a matsayinki na matar aure.
Ni fa ina da kishin iyalina, ban ga Safiyya tana fesa turare don za ta fita ba balle ta turare jikinta wai Kabbasa”.
Azeezah ta ce, “Habawa Malam! Ai ni bana iya fita cikin jama’a ban yi kabbasa ba, sai in ji kamar warin kashi nake yi.
Ina ruwana da bagidajiyar matarka? Sunanmu ma da ajinmu ba daya bane balle ka dinga wani comparing dina da ita”.
Bai ji dadin maganarta ba, amma da yake har lokacin cikin giyar amarci yake sai ya kasa cewa komai, har ta gama suka shiga daya daga cikin hamshakan motocinsa dake adane a rumfar adana motoci.
Ashe bai gma ganin bacin rai ba, again, wani dan yalolon-share-sharen gyalen da Azeezah ta yafo suka fito bashi da maraba da wanda take yafawa kafin aurensu, irin Shantily dinnan, wanda dashi da babu, duk daya, amma a wannan lokacin Allah bai bashi ikon tankawa ba.
Ya dai ji takaici da kishin hakan a ransa.
Azeezah ke jan motar, shi Baby din na Azeezah an hutar dashi, yana gefenta yau baya tuki, yanata danne-danne cikin wayarsa tana faman zuba masa hirar soyayya, abinda Sophie bata taba yi masa ba watau tuka shi a mota, haka suka fice daga gidan suka dauki hanyar Blue-Cabana.
Safiyyah na ta jiran shigowar Zayyan, tunda yau tana ankare cewa girkinta ne, ko babu komai ta yi kewar ganinsa kwana biyu tanaso ta dan saki ranta ko yaya ne idan ta ganshi.
Zayyan har gobe sunansa Zayyan a gare ta, Habibin da bata hada shi da kowa da komai a muhimmanci, kuma zuwa yanzu kullum tana kokarin gaya wa kanta Zayyan bai mata laifin komai ba.
Wannan jin zafin nasa da take yi tana so ya wuce, a halayyar Safiyya babu kullata babu riko, a sanda aka yi mata abinda ya taba ranta to zata nuna canji sosai, in ya wuce shi ke nan. Amma kwarai yau zuciyarta da sauki yau a kansa.
Saidai me? Tun karfe takwas ta yi wanka ta soma shirin tarbarsa yau. Abincin da tayi masa ma na musamman ne yau. Amma me? Sai jin motsin tashin motarsa tayi zai fita daga gidan.
Hakan ya sa ta daga labule don dai ta san yana cikin gidan tunda yamma da ya dawo, kuma Zayyan in ya dawo gida da wuya ya ke sake fita in ba wani muhimmin uzuri ne zai fitar dashi ba.
Ta daga labulen window dinta kenan ta gansu suna fita a mota shi da Azeezah.
Zayyan din da ba ya iya zuwa ko kofar gida bai gaya mata zai fita ba. Wannan bai dame ta ba kamar shiga lokacinta da Azeezah ta yi wanda in itace ba za ta yi mata haka ba, don ta tabbata wannan fitar ta Azeezah ce, ba tasa ba ce.
Don kawar da tunanin abin daga ranta kada ranta ya baci sai ta kira Ammi suka kafa hira. Nan Ammi ke gaya mata dawowar Yaya Sheikh da matarsa Assafe da hidimar kayan dakin su Sabah da ya yi musu.
Da farin ciki sosai Safiyyah ta ce,
“Ammi da gaske? Yaya Sheikh ya dawo gida kenan kwatakwata?”
Ammi ta tabbatar mata, tace amma tayi-tayi dashi ya ce bazai zo wajenta a Abuja ba, sun koma Lagos, yana fushi da Zayyan tunda ya yi mata kishiya.
Murmushi Safiyyah ta yi ta ce, “To ai ko Anti Assafen da ya kawo min na gani. Haka nan na ji ta kwanta min, tunda kina ta fadin kirkinta”. Ammi ta ce “gaskiya ne. Assafe mutuniyar kirki ce, kyale shi zan lallaba shi ya barta ta zo miki daga baya”.
Hirar da suke da Ammi ne ya sa lokaci ya ja sosai bata ankara ba, sai misalin karfe goma sha biyun dare ta ji motsin shigowar motarsu gidan.
Kuma ko da suka dawo Azeezah ta sake hilace shi da sumba a cikin mota sai da suka kwashe wajen rabin awa da yin parking kafin su fito.
Da kyar dai ta kyaleshi tana kumburi ya samu ya taho sassan Safiyyah.
Safiyyah na jinshi yana shigowa sai ta daga kai tana kallon agogon bango.
Har ya shigo idonta na kan agogon. Shi ma da ya shigo suka hada ido, ya ga abinda take kallo, sai da ya ji babu dadi.
Yana so ya ce wani abu, amma dai yayi shiru, can kuma ya maze ya ce, “I’m Sorry. Nayi latti ko?”
Jin bata amsa ba sai ya shiga undressing kansa don ya shiga wanka.
Wani bakin ciki ya kama Safiyyah don ta tabbata ba haka Azeezah ta kyale shi a motar bama, wannan jaraba har ina? Wanda kuma ta tabbata lokacinta ne. Yarinyar nan ta zo da wani salo na raini da fitsara, ga girman kai kamar diyar Tinubu, don ko sau daya ba ta zo inda take da sunan su gaisa su san juna a matsayinsu na matan miji guda ba.
Ko irin amana din nan da ake yi na al’ada ita kam ba su yi mata ba. Sai habaicin su Yaya Zubaida kadai data ji ta more. Tana wannan tunanin Zayyan ya fito wanka. Tana kallonsa yana shiryawa shirin kwanciya tana jin abubuwa da yawa a ranta.
Musamman sanda yana a Zayyan dinta ita kadai Safiyyah, ko kuda bai gittawa a tsakaninsu, bata son ko tuna cewa yanzu yana da wata macen mai irin matsayinta a gefe.
Ji ta yi hawaye na son kwace mata, because ko makaho ya shafa ya san yanzu Zayyan ya rage damuwa da ita.
Ya kammala shiryawa cikin fararen pajamas dinsa ‘yan gidan (Ralph Lauren), ya dube ta da murmushin lallashi. Ya zauna a gefenta har kafafunshi na gugar nata.
Wani abu da ya jima bai yi ba wato irin wannan zaman ya jingina da ita, which is one of his hobbies, ya tallafo kafadunta yana cewa cikin tashin hankali.
“Wannan wace irin bakar rana ce da ni da Sophie muka tsinci kanmu? Mun koma bakin juna? Wace irin mummunar kaddara ce ke tare dani haka???”
Maganarsa ta yi wa Sophie fami a kan gyambonta, gabadaya zuciyarta ta narke, ta karye ta idasa ragargazowa kasa, rauninta ya bayyana gabadaya akan fuskarta, bata san sanda ta fada kirjin Zayyan ta saka kuka ba.
Zayyan ya saka dukkan hannayensa ya rungume Safiyyah da su, Allah kadai ya san yadda ta ke jin zuciyarta a wannan lokacin. Kishi ba abu ne mai sauki ba a zuciyar diya mace, balle ga mace irin Safiyyah da ta bada dukkan soyayyarta da yardartar ga Zayyan Bello. A yau Safiyyah na kara jinjinawa duk macen da ta samu kanta cikin wannan halin.
Zayyan namiji ne da idan ya soma lallashin mace sai ta ji duk duniya babu sarauniyar mata tamkarta….
To haka yau ma da yake lallashin Sophie a kirjinsa, ta duk wata hanya da ta dace miji masoyi ya lallashi matarsa, amma Safiyyah duk wani lallashi nasa guda daya daidai yake da karawa wuta fetur. Ba miji irin nata mace ke iya rabawa da ‘yar uwarta mace ta sauki ta zauna lafiya ba.
Kai ita sai yanzu ma ta ke jin kanta kamar ta samu bacewar basira ne na wucin gadi, lokacin da Zayyan ya zo mata da maganar auren da har ta bashi yardarta.
Ko kuwa wani sihirin ne Azeezah tayi mata ta yarda a aurota farat daya, yanzu kuma al’amarin ya fi karfin zuciyarta? Duk wani kokarinsa na ya samu hadin kan Sophie yau ma abun ya faskara, ta kasa jin sha’awar kasancewa da shi.
Domin kamar an kara nesanta zuciyarta daga duk wata sha’awa ta diya mace akan mijinta.
Ba don komai ba sai don ko yaya ta rufe ido Zayyan ta ke hangowa manne jikin Azeezah a kan idanunta….
Abin da ya kai su da soma kokawa don matuka Zayyan ya gaji da lallashinta, sosai yake son Safiyyah ta ba shi dama yau. Yana ganin in ya samu ta saki jikinta da shi yau koda sau daya ne zai gusar mata da wannan shingen (barrier) da ta saka wa zuciyarta a kansa.
Ya soma kai wa makura da halayyar nan tata, ya fara gajiya da kokawar don baya son ya saka mata karfi, sai ya rike hannayenta duka biyu cikin nasa, ya fiddo manyan idanunsa waje sosai ya saka su cikin nata, murya a dakushe ya ce,
“Safiyyah, are you fighting me?”
Sophie ta girgiza kai, hawaye na bilbila, cikin murya mai ban tausayi ya ce,
“Then let the bygone be bygone, ki bani dama in nuna miki how much I missed you! Sophie, kinsan you are my comfort zone, inaso ne in nuna miki matsayinki bai canza da komai ba, domin na har abada ne kin ji!.
Har gobe kina nan a SOPHIE dina, my first and everlasting love Safiyyah. My Alter ego. Arch. Safiyyah Dandume!!!
Ki barni da karin aurena kawai, in bar ki da darajarki da martabar da na riga na baki. Ko mata guda uku na karo, na rantse Safiyyah matsayinki ba zai taba canzawa ba, believe me, trust me, give me another chance…..”.
Cikin kokarin hadiye wani sabon kukan tausayin kansu gabadaya da ya taho mata ta sanadin kalamansa ta ce.
“Zayyan, kayi hakuri ka ji? I find it difficult to trust something called LOVE again, don haka don Allah ka je ka fada a inda za a yarda da kalmar.
Ni kam soyayya ta gama yaudarata. Ina cikin wata sabuwar duniya a yanzu, wadda bana bukatar soyayyah.
Ka bar ni in cigaba da zaman aure na sunnah kawai, don cikar mutunci na da kamalar addini.
Amma duk lokacin da ka kara maganar wani abu wai shi SO a tsakaninmu, ko ka hada jiki da ni, wallahi ji nake tamkar ka zuba min narkakkiyar dalma ko garwashin wuta a jiki da zuciyata”.
Zayyan ya soma harzuka, duk da haka cikin kokarin danne harzukar ya koma wa’azi, inda yace cikin taushin murya da nuna amsar laifi.
“Safiyyah, Allah Ubangiji da Ya bani damar in kara aure, ya san za ki iya dauka, kuma za ki iya jura shi ya sa Ya bani damar in yi har guda uku bayan ke. Layukallifullahu nafsan illa wus’aha. Amma idan wannan rayuwar kika zaba mana wai don na kara aure ba ki yi mana adalci ba ni da ke.
Yes! Na kara aure don radin kaina, amma wallahi don in nemo miki mas’laha ne da kwanciyar hankali a cikin rayuwar aure dani. Ki yarda ko kada ki yarda, this is the sole reason, ina so ta haihu in karbi Dan in baki (ya kantara karya irin tasu ta maza, don bazai iya ce mata she is not that romantic ba kwata-kwata, saboda kunyarta a gado ya masa yawa, ya hanashi morar kuruciyarsa, she is not doing anything special to get his attraction irin yadda yakeso yake mafarki, zai zama tamkar yaci fuskar Sophie dinshi) don haka gara a tafi a hakan.
Abu daya ya sani cikin kowanne hali ko yanayi Sophie ta kasance ita yafi so kuma ita ke da mukullin zuciyarsa. Ita yake yiwa SO mai tattare da respect da ganin kima, yana mata kauna mara algus. Kuma a jikinta ne kadai yake jinsa a sake, a karramce, a alkince. Sannan a mutunce. Don haka yace.
“Ki yafe ni Sophie, ki dawo da ni a gurbina, insha Allahu ba zan baki kunya ba, zan yi kokarin kamanta adalci.
Kada ki haramta min Sophie dina akan abinda Allah bai haramta min ba, ba pleasure kadai nake samu daga gare ki ba, you are my whole comfort zone, my shield kin sani”.
Zayyan dai ya jima yana amfani da kalaman da ya tabbatar za su sanyaya zuciyar Safiyyah. Har ya kasance Sophie ta rasa kalmar kara challenging dinsa.
Dole ta fara russuna, ta kyale shi ta bashi hakkin aure, amma fa wani abu guda daya; shi yake yin komai, shi yake sarrafata, Safiyyah sai yadda ya juya ta, ta zame masa kamar kayan wanki, ta kasa agaza mishi da komai. Tana ganin cewa, Zayyan ya gama yayinta kawai, he is forcing himself to be with her, tunda ya samu yarinya sabon jini, karshe a gayu da Naira, irin wadda Mama ke buri wa Baffanta.
(A ganina wani kuskure da uwargidaje ke yi kenan, cewa miji da ya kara aure ya gama yayinsu, bayan a zahiri abin ba haka yake ba. Allah daya halicci namiji yayi masa baiwa da babbar zuciya, da yake iya adana soyayyar kowacce matarsa ba tare da son kowacce ya shafi na dayar ba. They all have reason na kara mace amma ba lallai rashin so ko gushewar soyayyar Uwargida ba.
Wani zubin kuma kuskure kalilan na macen cikin gida shi yake bude wa namiji kofar son karo auren kamar yadda ta faru da Zayyan da Safiyyah).
A hakan da suka kasance din kuma, ba tareda Sophie ta agaza masa da komai ba, sai aukin kuka dana ajiyar zuciya da jika shi da hawaye, wata irin gamsuwa da bai taba samu a tareda Safiyyah ba ya samu a hakan yau, a yadda take naturally, ba tare da ta taya shi komai ba.
Har a zuciyarsa kishin nata ya koma kumbura masa kai, ya ce a ransa, shi dan gata ne na karshe a gun matansa; Mai tsananin kishinsa da sonsa, da mai tsananin sha’awarsa da tattalinsa.
Ita Azeezah plays almost all the roles a kan gadon aurensu, ba tare da ta damu da martaninsa ko taimakonsa ba sai ya so. In dai ta samu yadda ta ke so ita shikenan, in dai za ta samu kansa.
Ita kuwa Safiyyah she is not romantic at all, kuma ba ta nuna zalama a kansa, shi ta ke bari da playing most of the important roles a kan gadonsu. Kai yau ya lura da wani abu guda daya ma, Safiyyah ba ta san wani abu wai shi ‘ectasy’ ba, ko gamsuwar kanta, in dai shi zai samu yadda yake so falillahi hamdu; Typical matar bahaushe, da ba ta baiwa sexual life dinta muhimmanci a rayuwarta ba, sai neman ‘ya’ya, ita dai ta haihu sai kace mage.



