⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 6: Chapter 6

Kuma a hakan nata sai ya ce ya fi samun comfort da nutsuwa da ita, can kuwa pleasure kawai da excitement yake samu tsurarsa. Sau tari har shiga tunani yake a kan zalamar Azeezah a kan jima’i.
Abinda bai sani ba shi ne, Azeezah na shan kayan da’a masu karfi da suke hana ta sukuni, wadanda kuma Mamanta ta gaya mata su ne kadai ke mallake namiji, kayan mata masu asalin kyau da karshen tsada Azeezah ke amfani da su, duk da haka kuma akwai bambancin halitta tsakaninta da Safiyyah.

Tabbas ya yarda Azeezah ba za ta iya kwana uku ba tare da shi ba, amma Safiyyah ko wata uku zai yi bai kusance ta ba lafiya kalau zata zauna, ba tare da ta shiga wani hali ba.
Wato ba ka sanin halayen mata da dabi’arsu da bambancin halittarsu dana personality dinsu, sai ranar daka tara su a gidanka. Kamar yadda ya fara tarawa. Yanzu kam ya tashi daga Architect dinsa ya koma Farfesan halayen mata.
Zayyan shi kadai yake ta tarawa da debewa a ransa, alhalin yana rungume da Sophie a kirjinsa, bayan sun kammala dabbaqa sunnah. Kafin a jima kadan, ya ji canzawar numfashinta, wanda ya koma sauka a hankali, tabbacin barci ya dauke ta.
Ya gyara mata kwanciya sosai da rufa da duvet, yana karanta addu’ar kwanciya barci yana tofa mata don shi ma barcin yake son yi, bayan ya yi wanka ya fito kawai sai ya hango wayarsa da ke kan bedside da ya saka a silent tana haske, tabbacin shigowar sako ko kira kamar kada ya daga don da ganin Sophie tana jin dadin barcinta, wanda ta dade ba ta samu mai dadi da nutsuwa kamarshi ba.
Sai kuma dai ya ce bari ya duba watakila sako ne ya shigo masa.
Amma yana duba wayar ya ga kiran daga amarya Azeezah ne, sai ya dauka don ya dauka ko ba lafiya ba.

Yana amsawa sai ya ji shesshekar kukanta. Da sauri ya dubi sashen da Safiyyah ke kwance ya tabbatar barcinta mai nisa ne, sai ya bude kofar dakin ya fita zuwa falo yana cewa.
“Zeezah, lafiya? Karfe biyun dare fa? What happened? Why are you calling me now?”
Cikin kuka Azeezah ta ce, “Ni dai ka zo ka maida ni Lagos, ba zan iya kwana ni kadai ba”.
Ya sassauta murya yana cewa, “Haba Zeezah, kada ki yi min haka, kada ki shiga lokacin ‘yar uwarki, kada ki raba min hankali. Ki yi wa Allah ki kwanta ki yi barci, na miki alkawarin idan gari ya waye da wuri zan shigo”.
Azeezah ta kara sautin kukanta tana cewa, “Ni fa kada ka dauka ko kishin wannan bakauyiyar matar taka ne ya hana ni barci, wallahi a’ah, idan ba ka zo ba na rantse da Allah za ka wayi gari ba ka gan ni a gidan nan ba, ni ba zan iya barci babu mijina ba”.
Zayyan ya kara yin kasa da murya cikin lallashi, ya ce, “Zeezah, please…..”
Ta ce, “Ba wani please Malam, ka zo ka ga halin da nake ciki sai in barka ka dawo”.
Ta kashe wayarta bayan ta ce,

“Ina jiranka ka ji Baby, something sweet awaits you Baby…..”.
Cikin wata irin murya mai sace zuciyar namiji, and he couldn’t help it as a Man, kawai ya ji yana so ya je ya ganta din, ba don yana da wata bukata a tare da shi ba.
Ya san halin Azeezah sarai tana iya kafa masa rigimar tafiya Lagos gobe.
Ya sa kafarsa kenan zai bar falon, ya ji motsin Safiyyah ta shiga toilet, sai ya ce wa kansa bari ya yi sauri ya je ya ga wannan rigimammiyar ya dawo immediately yanzu.
Yana shiga sassan Azeezah ya tarar da ita ta yi daidai a kan Sofa cikin irin Bikini dressing din da yake so, kanta ya sha adon yiri-yirin kitso na gashin kanti, ta kanne masa ido guda daga kwancen da take, ta dora kafa daya kan daya tare da yafito shi da yatsunta cikin mayaudarin salo, ta ce,
“Come on Baby!”.

Daga jikin kofa ya tsaya ya ki karasawa, ya ce, “Zeezah me ke damunki ne haka? Kwanan ‘yar uwarki ne fa… Zeezah kina so in tashi a ranar kiyama da shanyayyen barin jiki?”
Mikewa ta yi ta nufo shi tana taunar cingum kas-kas-kas, rakakas-kas, ta rike kugu ta ce,
“Ya Sheikh! Naga alama yau wa’azi ka ke ji..”. Ta fada cikin kanne ido, sannan ta afka masa gabadaya su duka biyun suka zube a kan Sofa, Azeezah ta kankameshi tana begging, har da cewa “ko one round ne……”. Safiyyar da bai kara tunawa ba kenan sai asubahin ranar.

** **

Ko da Safiyyah ta fahimci Zayyan ya bar dakinta ba ta taba kawowa a ranta yana can tareda Azeezah ba, to amma ina zai je a wannan tsohon daren? Allah Sarki! Tsabar yarda da irin sanin data yima Zayyan, saita baima kanta amsa da cewa, watakila yana can bisa computer a sassanshi yana aiki ko ‘idea’ tazo masa, yana can yana Zane a dakin zanensu. Ta san Idea tafi zuwar masa bayan intercourse dinsu.
Daman ta tashi ne don yin Qiyamullaili, sai kawai ta dauro alwalarta ta fito ta sanya kayan sallahrta, ta fesa turare mafi tsada a cikin turarukanta ta dasa sallah cikin nutsuwa kamar yadda ta saba.
Abin da ya kai ta har kiran sallar asubahi, ta bi jam’I daga masallacin Sunset Estate. Ta san yanzu yana masallaci don baya wasa da sallar asubahi. Ilai kuwa yana fitowa daga masallaci kai tsaye sassan Sophie ya taho, ya rasa inda zai sa kansa da guilt din da ya kama shi tako ina.

Lokacin da suka hada ido da Safiyyah, kallo daya ta yi masa ta hango wani irin rashin gaskiya a tare da shi, don a rayuwarshi bai taba jin yayi abinda ya dame shi irin yau ba.
A zuciyarsa ya soma harhada kalaman da zai yi wa Sophie karya da su idan ta tambaye shi ko daga ina yake? Amma me, kin ce masa komai ta yi, ta juyar da kai ta ci gaba da laziminta.
Zuciyarta na gaya mata abinda ta ki yarda da gangan saboda kyakkyawar shaidar da ta riga ta yi masa na cewa shi din masanin ilimin addini ne daidai gwargwado. Bazai taba daukar kwanan wannan ya kaiwa waccan ba. Shi da kansa a ransa yace gaskiya Azeezah hatsabibiya ce sai yayi a hankali da ita.

Kin ce masa komai da ta yi ba karamin taimako ya zamo a gare shi ba, don sai kawai ya haye gadon dakin ya ja duvet ya dukunkune a ciki ya shiga ramuwar bacci yana istigfari.
Sassanyar ajiyar zuciya Safiyyah ta yi ta dauke ido daga kansa, tana fadi a fili ita kadai,
“Idan abinda nake zargi a kan Zayyan ya aikata min yau gaskiya ne, Ya Ubangiji na yafe masa!
Ubangiji kada ka sa Zayyan ya zamo cikin jerin maza masu bin KAWAR ZUCIYArsu, Ka bashi ikon bin umarninKa, ya cika alkawarin da ya dauka na yin adalci a gidansa”.
Sai ya zamo wa Azeezah habit, wato kiransa a waya a lokacin da ta tabbatar yana gurin Safiyyah. Wani lokacin kaifin idon Safiyyah ke hana shi daga wayar Azeezah a duk lokacin da suke tare.
Ta fahimci Azeezah karfi da yaji son canza kyawawan dabi’un Zayyan ta ke yi duk kokarinsa da jajircewarsa na son ganin ya yiwa Safiyyah adalci, wani zubin shaidan da son zuciya na sakawa yana biye wa tayin Azeezah.
Safiyyah bata taba tuhumarsa akan hakan ba, duk da ta fahimcesu zuwa yanzu. Kwana biyun girkinta kyashinsu Azeezah take yi. Abun nasu bai ta’azzara ba sai lokacin da Azeezah ta soma laulayin ciki mai tsanani.
Daga shi har Azeezah din ba wanda ya san cewa ciki ne. kullum Safiyyah yafewa Zayyan take a ranta ta kuma roki Allah Al Gafuuru ya gafarta masa. Ba don komai ba sai don tuna irin dimbin so da halarcin da ya nuna mata a rayuwarsu ta baya.
Aka ce wawa kadai shike manta baya idan gaba ta sauya….. Allah bai halicce ta cikin wawaye ba, ko cikin mata masu yawan korafi ga mazansu akan kishiya. Ke dai barta da kishin mijin a zuciyarta wanda shikadai take iya nuna mawa.
A dan tsukin ne ma ta samu damar tafiya gida bikin kannenta, ta basu filin gidan gabadaya, har cewa take a ranta akan Zayyan dai, wane dare ne jemage bai gani ba! Duk wata mace da zata zo yanzu sudin kwanonta zata dauka, ita ta yi disvirgining dinshi.

Ta samu ya barta tafiya Dandume da nashi gudunmuwar kudin masu yawa ga Malam da Ammi. Ya kuma bata driver da daya cikin motocinsa ‘Bugatti Veron’ daga nan har su gama bikin.
Dangi duka sun hadu, na Malam dana Ammi, kodayake duk dai tsatso daya suka fito. Amare na karkashin kulawar Aunty Dije ita ta musu komai. Dama ita da Aunty Assafe kadai ake jira wadda zata zo daga Lagos.
Don haka daga isowarta gidan Malam ya dauki murnar zuwan Aunty Safiyyah. Ba ga amaren da suka ciccibeta suka daga sama ba, hatta Ammi fuskarta komawa tayi kamar gonar auduga. Tace
“Yaya babba ana hanya shine ba ko waya?”
Dariya tayi, tasa hannu ta rungumo gyatumarta jikinta, cikin kauna da shauki irin na ‘ya’ya ga mahaifansu da suka jima basu gani ba, tace,
“Ammi na, I just want to take you by surprise”.

Ammi tace “to turanceni, baturiya matar mai Zane. Dadinta dai nima yanzu Da na ya dawo Najeriya, ba mai taba ni ya kyale, yanzu sai in kirashi shi in kai kararki, in ce kinzo kawai kina turance min kunne”.
Ammi ta basu dariya sosai, kowa saida ya dara. Tace “Ina fatan Yaya Shaikh, zai zo harda Assafen?” Ammi tace “zasu zo, amma sai ranar dauri aure wato asabar, jibi kenan”.
Biki yayi biki! Gida ya kacame da zumunci Safiyyah ta manta da kowacce damuwa data zo a cikinta. Ta kawo gudunmuwar Zayyan na cheque din kudi ta baima Malam. Malam cikin kakabi yace yayi yawa, shi bazai karba ba.
Yace maza maza ta kira masa shi a take.
Haka ta kira Zayyan ta hadasu da Malam, sukayi ta magana mai kama da jayayya, Zayyan ya kwantar da kai yana rokon Malam yace a barshi yayiwa Sabah da Rayyah kayan daki wannan hakkinsa ne, yace ayi hakuri a bashi damar nan don ya dade da ita a ransa. Malam yace “halan Nana Safiyyah bata gaya maka Yayansu Ridhwan na Qatar ya dawo ba? Ai tuni ya musu kayan daki”.
Zayyan yaji babu dadi, yace “Malam saidai in ka daina Da da ni kaima, saboda nama Safiyyah kishiya, amma a baya in na kawo alkhairi ga kannena su Sabah ba kwa cewa a’ah”.
Malam yayi murmushi yace “ta nan kuma ka bullo don ka daure ni da jijiyoyin jikina ko yaron nan? Dadin abun dan Bello Rafindadi kake, wanda ban taba kalla ba a matsayin Da na ba.
Da wannan nake cewa zan karba amma ka rage, rabi ka yi wani amfanin dasu. Shi ya kafe Malam ma ya kafe. A karshe dole sai Ammi ce ta raba rigimar Malam da surukinsa, don yace yayarda a baima Malam rabi Ammi rabi toh. Amma in ba haka ba in Safiyyah ta dawo masa da su zai yarda don ya mata kishiya ne suka cire shi cikin ‘ya’yansu.

Dole ya rinjayesu, suka amsa da godiya, suka kuma saka albarka tareda yi masa addu’a akan Allah ya bashi ikon yin adalci a tsakanin matansa.
To ranar daurin auren ma Zayyan yayi kokari yazo, dashi aka daura auren su Sabah ko Safiyyah bai gani ba sai waya yayi mata yace “gashi a Dandume, an shafa Fatiha dashi ya juya”, sosai taji dadi domin bata kawo zai zo ba sam, ko ba komai ya nuna kulawa da kara still akan sha’aninta, ya koma Abuja a ranar don gidan nasu ya cika ya batse da dan adam babu ko inda zasu iya kebewa.
Assafe ita kadai ta biyo jirgi daga Lagos. Yaya Sheikh an gayyaceshi wani muhimmin Islamic conference a kasar Tunisia. Haduwar Sophie da Anti Assafe na farko kenan.
Tana ganin ta tun kan a mata bayaninta tace “Kanwata Safifi!” sai Safiyyah ta juyo da murmushi da mamaki don ta san mutum daya a duniya ke kiranta Safifi wato Yayanta, Yaya Sheikh. Tace
“Aunty Assafe! Nice to meet you. Yes, I’m Safifin Yaya Sheikh. My beautiful Aunty naji dadin ganinki. Duk da ina fushi har yau baku zo min ba”.
Assafe tace “kada ki damu kinji ko Safifi, Yayanki har gobe yana nan yana tayaki kishin kishiya, in ya sauko da kansa zaki ganmu ya kawo mu”.
Wani irin haduwar jini ya shiga tsakanin Safiyyah da Assafe.
Kasancewar ‘ya’yan Malam basa irin bikinnan na zamani, shi a gidansa daga Walimah sai wunin biki na cikin gida. Walimar ce dai aka dan fita harabar makarantar firamare ta Dandume aka yi acan tareda Lacca mai ratsa jiki. Ranar Lahadi ne aka wuce da amare gidajensu daya Kaduna daya nan cikin Katsina.

Zuwa Litinin kowa ya watse ya koma inda ya fito. Assafe da Safifi sukayi canjin lambar waya don kwarai suka shaku da juna cikin dan lokaci da alkawarin ziyartar junansu da gaisawa a waya in sun koma garuruwansu. Assafe ta koma Lagos, Aunty Dije Zaria, da Safiyyah da suka kamo hanyar Abuja itada direban office din Zayyan mai suna Halilu, bayan motarta shake da tsarabar Dandume.
Kuma koda ta iso gidan saida ta ware duk abinda ta zo dashi tsaraba ta kira mai aikin Azeezah tace ta dauka ta kai sassansu. A yanzu dai wani irin zama a ke tsakanin Azeezah da Safiyyah, shi ba na doya da manja ba, shi kuma ba na dadi ko shiri ba.
Safiyyah na guje wa duk wani abu da zai sa Azeezah ta raina ta, ko ta yi mata rashin kunya, don tun ba a je ko ina ba ta fahimci Azeezah din nan ba kyalle bace dungu ce, daidai kugun kowa, idonta a bude yake tas, wato ‘yar duniya ce girman bariki mai matukar son rayuwar holewa.
Bini-bini ta ja Zayyan sun fita outing, abin da sam a baya bai dame shi ba. Yanzu kam kusan kullum ne sai ya fita da Azeezah sayayya, ko shan ice cream, ko cin abincin dare a Cilantro.
Hatta a ranakun girkin Azeezah, daga baya daya gaji da cin na restaurant din, ya kan zo ya ce “Sophie kin rage abinci?”
In akwai ta bashi, in babu cewa take da sauki. Abin da ta kasa ganewa shine, Azeezah ba ta iya girkin bane ko kuwa yi ne kawai ba ta yi saboda gayunta, ajinta da class dinnata yasa tafi karfin shiga kitchen ta girkama mijinta abinda zai ci?
Shi kuma Zayyan da yake namijin duniya ne bai taba bada wata fuska da za ta tambayeshi dalilinsa na karbar abinci gurinta ba, alhalin yana hannun Azeezah.
Lokacin da Azeezah ta fara laulayin ciki sai bukatuwarsa da abincin Safiyyah ya karu, ba cikin ma bata iya dafa masa ko indomie, balle yanzu da take cikin halin laulayi da tashin zuciya, dake haifar mata da yawan amai. Fitinarta a kan gadon aurensu ma karuwa ta yi bayan samun cikinta sabanin sauran mata da kan ja baya da miji in sun samu ciki.

Shi kuma kamar sauran maza hakan yasa ya kara likewa Azeezah, har fiye da farkon aurensu, sakamakon karuwar ni’imar jikinta da shaukin abun daya karu gareta, a dalilin yaron ciki.
Shi da Safiyyah tsakaninsu sai karbar abinci, suka kara samun nesanta da juna, wannan closeness din na Zayyan da Safiyyah sai kara yin baya-baya yake yi, weakness dinta da ita kanta ta sani shi ne ba za ta iya barin Zayyan da yunwa ba!
Ko yana kyautata mata ko baya kyautata mata, ko yana yin adalci ko baya yi in ya bukaci abinci daga gareta zata bashi.
Amma wani abu da tayi noticing akanta shine, kullum kara nesanta yake daga zuciyarta, saboda rashin adalcinsa ne a shimfida ko meye ita bata sani ba, sam-sam bata ko iya kiransa ‘Habiby’ yanzu. Don in ta raya sunan ma a ranta wani bakin ciki ke biyo baya. Babban abinda ya fi bakanta masa rai kenan ‘Zayyan’ gadagau da Sophie ta koma kiransa.
Mu’amalarsu ta aure ta gurbata da rashin sakewar Safiyyah dashi, saboda zuciyar Safiyyah ta riga ta gurbace a kansa.
Safiyyah ji ta ke idan ta kira shi “Habiby” ma yanzu kamar ta yi sabo ne ko babban zunubi. Yanzu kam ai Zayyan Habibin Azeezah ne, tunda da ita kadai yake soyayya, ta dade tana son ta koma daidai, wato ta karbi mijinta, ta rungume shi kamar baya, amma hakan ya faskara gare ta, zuciyarta taki dauka. Duk wani kulafucinta na soyayya akan Zayyan yanzu ya yi fiffike ya tashi, ya koma na son samun haihuwa da shi kadai.
Shi ya sa ma take kai zuciya nesa (once in a while) ta yarda da shi in ya cikata da wa’azin zata gurbata masu aure da rashin dabbaqa sunnah, to shine yasa a wasu lokuttan ko ince (once in a blue) ta kan amince dashi, ba tare da ta taya shi da komai ba, ba tare da wani shauki na soyayyah ba sai kawai gangar jikinta da take mallaka masa.

Shi kuma wannan abinda Safiyyah ke masa ya kara bashi damar nesanta daga gare ta, ya kara likewa tareda mannewa Azeezah suka zama tamkar tube da tyre, wadda a kullum ita dokance ta ke dashi, ya bukace ta ko ‘a’ah ita zata yi seducing abinta ta sarrafashi yadda take so ta kwata. Yana mamakin yadda Azeezah ba ta ko son hutu.

Lamarinta har tsoro yake ba shi a wasu lokutan don tafi shi bukata.
Yau very late ya dawo gida kuma a gajiye likis, don ba karamin aiki suka sha ba na renovations din wasu bangarori na Sunset Estate, yau din kuma ya kama girkin Azeezah ne don haka kai tsaye sassan Safiyyah ya nufa, don ya yi mata sai da safe, duk da ya san ta tsani sai da safen nasa, da gaisuwar safensa da yake zuwa yi mata in ba a dakinta yake ba.
A ganinta yana takura kansa yin hakan ne kawai don tana ganin kwata-kwata bata ransa yanzu da yake da yarinya danya sharaf mai iya soyayya. Allah shi ne shaida, itama yanzu Zayyan ba ya ranta kamar da, kullum fili yake kara samarwa a zuciyarta, amma kwadayinta da son haihuwa da shi ya ninka na soyayyar da basa yi yanzu, kaunarta da son haihuwa dashi ya ninka na baya domin jarabta ce Allah ya saka a zuciyarta.
Idan Sophie ta zauna tana tariyo majigin rayuwarsu ita da Zayyan shekaru goma sha biyu da suka gabata, da yadda ta gurbace a yanzu cikin dan lokaci kalilan, a dalilin shigowar Azeezah Murtala cikin rayuwarsu sai ta kara tabbatar da cewa nothing is parmanent in life, including soyayyah….

Duk da cewa tata zuciyar ta sani ba ta san tasa ba, amma ta san kaso tamanin cikin dari na soyayyarta gare shi ta yi melting. Yanzu haihuwa kadai ta ke so a tareda shi ba soyayya ba.
Tana kwance cikin kujera a falonta, falon da ya ji kayan alatu na rayuwa iri daban-daban, amma cewa ta ke a ranta sau dubu gara mata dan tsukukun gidansu na farkon aure, wato dan flat dinsu na haya da Baba Bello ya kama musu a Samaru. Lokacin da suke rayuwar dalibtaka cikin soyayya da shaukin juna.
Yanzu kam da girma ya kunno kai sai zuciya ta gurbata, shaukin da ke cikinta ya koma wani abu daban shi ba shauki na soyayya ba, shi ba feeling na kiyayya ba. Sophie sanye take da fararen kayan barci na riga da wando masu kauri CK. Kasancewar sanyi ya fara karfi sosai a wannan watan an shiga watan February a garin Abuja.
Tunda Arch. Zayyan ya doso sassan uwargidansa Safiyyah, ya tunkaro falonta na farko, baya jin komai sai tashin karatun Alkur’ani mai tsarki cikin kira’ar data fi so wato kira’ar “Sheikh Ahmed Ajmi”. Ga kamshin turaren wutan dakunan Safiyyah na dindindin da ya kama sassanta gabadaya, wato turaren wutan ‘Divine Essence’. Wanda a kullum yake sanya masa nutsuwa da bangarenta, duk sanda ya sako kai ko ya shigo sassanta. A wurin Anti Dije take samu itama, Anti Dije ke yawan sayo masu turaren wutan na ‘Divine Essence’ duk sanda taje Kano a gun Haj. Zulaiha Zubair.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *