Chapter 7: Chapter 7
Da nashi makullin ya yi amfani wajen shiga falon Sophie, jin motsinsa ya sa Safiyyah juyowa daga kan allon talbijin inda take kallon tashar wa’azi ta Sunnah TV, duk wani aikin sharholiya bazaka ga Safiyyah ciki ba sai abinda zai amfaneta, kamar kallon finanai ko raye-rayen banza, yana shigowa ya ce,
“Sophie dear barka da wannan lokaci,”.
Fuskarta kadaran-kadahan ta amsa tareda bashi hankalinta.
“Barka da dawowa Yaya Zayyan”.
Yayi kuta, yana zama a gefenta, ya ce, “Zan kai kararki wajen Allah haka, in ki ka kara ce min Yaya Zayyan”.
‘Yar dariya Safiyya ta yi, ta ce,
“Na maida kalamaina, angon Azeezah”.
Ya basar ya ce, “Kin rage abinci? Yunwa nake ji”.
Ahap! Ta san abinda ya kawo shi kenan. Don haka ta dubeshi ta kasan ido, ta cure lebbanta kadan ta ce,
“Da sauki!”.
“Kamar yaya da sauki? Babu ne?”
Cikin mamaki Safiyyah ta ce, “bai kamata in maka wannan tambayar ba, don ba hurimina bane ba, amma abun naka da daure kai, ta yaya kana hannun wata kullum sai kazo kace in baka abinci? Wai shin matar taka ba ta dora tukunya ne?”
Ya ce, “Na san da tukunyar tata, amma na fi sabawa da taki”.
Wannan rainin hankali da yawa yake. Safiyyah tace a ranta. A nutse ta dubeshi, yau dai ta yi ta-maza ta ce,
“Ko ina da shi yau ba zan bayar ba, tunda ba ni ke da alhakinsa ba”.
Cikin mamaki Zayyan yake kallonta yanzu, ya ce, “Sophie, you are always changing, daga Safiyyahta da na sani zuwa wata aba daban, very rude to me!”.
Ya tallafo kafadunta jikinsa, ya ce, “Kullum ina addu’a, matsayina na baya ya dawo a zuciyar Safiyyahta, ta yarda cewa Zayyan dinta na nan yadda yake, ba abinda zai gutsurar mata shi. Ba wadda zata rabata dashi, saidai a shiga alfarmarta.
Nasan abun da kamar wuya wai gurguwa da auren nesa, matsayina nada ya dawo!”.
Sai ta ji idanunta sun kawo ruwa. Ta yi kokarin mikewa don barin jikinsa ya mayar da ita ya zaunar a cinyoyinsa. Ya saka tafukan hannunsa cikin nata ya cigaba da magana cikin wani irin yanayi na tausayin kai.
“Safiyyah karin aure kaddarata ne, amma ke ce sila.
Hakika ina jin kunyarki kan abinda zan fada miki yanzu. Ke kika yimin sanadin karin aure ba tare dana taba raya hakan a raina ba.
Da ace kin barni na fita a gamshe dake cikin dadin rai, kin kashe min kishirwata kin bani farin ciki ta hanyar tarairayar bukatuna a ranar, wallahi da ban je Lagos naga Azeezah har naji sha’awar aurenta ba.
Duk da nasan Allah ya riga ya rubuta min auren ta amma akwai sakacinki, wajen sauke nauyina da ya rataya akanki. Ki yi hakuri ki bani dama ki ga kokarina wajen son yi miki adalci, ki dawomin da matsayina na masoyi ba wannan matsayin da ki ka bani yanzu ba, wanda Allah shi ne shaida akan ba na jin dadinsa”.
Sophie ta zare hannunta daga cikin nasa, a hankali ta mike tsaye, hawaye suka balle mata, wani na korar wani, domin hakika ta tuno ranar. Wato ana I gobe zai tafi Lagos kiran aikin Baba Murtala. She treated him badly. Ta danne masa hakki kuma bata bishi ta kyakkyawar hanyar da zata kwantar masa da hankali ba duk da Allah ya sani period take a lokacin. Kuma tayi shiru bata fada masa uzurinta ba har gobe.
“Ina rokon Allah SWA kullum ya ba ni ‘courage’ da ‘fortitude’ din yin hakan Yaya Zayyan. Wato in dawo maka da girman matsayinka na farko dake zuciyata. Amma wallahi na kasa! Ko nayi kokarin hakan a lokuta da dama bana cin nasara. Ka taya ni addu’a nima, domin hakika ina bukatarta.
Bana jin dadin zuciyata ko kankani. Na dade da yi maka uzuri a kan karin aure, damuwata daban ce da wadda ka ke zargi; haihuwa nake so Yaya Zayyan da kai, bana so in mutu, ba ni da dan kaina tare da kai”.
Gabadaya zuciyarsa ta yi laushi, ya mike ya isa gareta ya toshe mata baki da tafukansa jikinsa yana rawa, sannan yayi azamar rungume ta cikin jikinsa ya matseta, ya ce, “addu’ar dana ke yi kullum bazan daina ba, ba kuma zan gaji ba; “Rabbi Hably min la dunka, zurriyyatan dayyibah, Allah ka bani ‘ya’ya masu albarka tareda SAFIYYAH kafin kowacce mace.
Sophie don’t give up. You are still in your thirties. Tunda dai an tabbatar mai cutar PCOS na iya haihuwa koyaushe Allah ya sa aka dace. Muna addu’a muna karawa insha Allah za mu ci wannan jarrabawar tare”.
Ya sunkuce ta kan kafadunsa kamar ya dauki yaro karami, yana tafe da ita daga falo har bedroom dinta har kuma kan tsakiyar gadonta ya kwantar, ya lullube ta da lallausar duvet dinta. Shi da ita idanuwa sun kada. Soyayyarsu ta dawo fal zukatansu. Yanzu tausayin juna suke ji. Shi yana tausayinta ita tana tausayinsa. Hakika aure kaddararsa ce wadda su duka basu isa su canzata ba.
Da kyar ya iya barin dakin Sophie a yau, jikinsa duka rawa yakeyi bai san dalili ba, haka nan kawai ya ji gabansa na bugawa fat-fat like something strange is going to happen to him today…..
** **
Yana shiga sassan Azeezah sautin wakar mawakiyar turanci ta kasar Amurka ke tashi, wai ita “Mariah Carey”. Bambancin da kullum ke akwai tsakanin Sophie da Azeezah a bayyane yake, daya tayi hagu daya tayi dama. Wannnan tayi gabas wannan tayi yamma; Religious and Elite. Komai nasu opposite din na juna.
Yanzu ya gama jiyo karatun Alkur’ani a sassan Safiyyah wanda ya sanya masa kyakkyawar nutsuwa da shiga hayyacinsa. Nan kam sai “Mariah Carey” dasu “Beyonce” cikin wakar tsantsar soyayya ke aiki. Individual difference dinsu kullum kamar an tsaga kara yake.
Sai me? Yana shiga dakin Azeezah ya jiyo kakarin amai daga toilet. Da sassarfa ya karasa, Azeezah ya gani male-male cikin amai a dandaryar kasa, tamkar mai amayar da ‘yan hanjinta. Tana jin motsinsa sai kuka kamar na fitar rai.
“Baby, ka maida ni Lagos zan mutu”.
Ya ce, “Subhanallahi, Zeezah me ki ka ci haka?”
Ya taimaka mata ta mike, ya hada mata ruwan wanka mai dumi a jacuzzi, ya taimaka mata ta yi wanka ya maido ta daki. Da kansa ya gyara wajen duk kyankyami irin nasa. Ya dage su tafi asibiti a daren a duba ta, Azeezah ta ki yarda. Sai ma kuka da ta saka masa, wai ita ce ke amai kamar wata kazama, tun safe ta ke fama da shi irin azababben aman nan mai wahalarwa, kore fatau.
A kanta ya kwana yana ta jinya da biye wa shagwabarta. Abu kadan in aka yi mata ko ya same ta za ta ce Lagos za ta tafi, shi kuma ya tsani furucin nan. Don haka da sassafe yana dawowa daga masallaci ya takura mata suka tafi asibiti.
Likitar ta tambaye ta ko ta yi fitsarin safe kafin ta fito? Tana kwance a kafadunsa ta ce, a’ah.
Ta ce, to ta shiga bayan gida ta yi ta kawo mata cikin ‘yar robar da ta mika mata.
Babu wani dogon bincike ba dogon turanci, ciki ya bayyana kansa watanni biyu a jikin Azeezah Murtala. Shi da ita duk suka dubi juna, shi a rude, ita fuska a dame, don fisabilillahi cikin ya zo mata bagatatan a lokacin da bata shirya ba.
Allah kenan! Mai yin yadda yaso ba tareda bawa ya tuhumeshi dalili ba.
Bata aure shi ita don haihuwa ba, balle irin wannan haihuwar haka da gaggawa ba. So ta ke kawai su yi ta cin duniyarsu da tsinke, ciki ai ya zama barrier. Kuma abu ne da zai raunata soyayya da jin dadinta.
Itama ba ta san ita mayyar Zayyan bace sai bayan aurensu da ta san zahirin sirrikan da ke tare da mijin na Safiyyah. Ta yarda Arch. Zayyan Bello Rafindadi dan baiwa ne, ‘one in million’ ne. Allah ya kashe ya kawo mata har gida.
A wannan dan tsukin ta ke son bijiro masa da zancen su dan fita honey moon ko zuwa ‘TinCan Island’ ne su dan huta da sa idon matarsa, sai kuma ga wannan sabon al’amari da bata maraba dashi.
A gaban likita Zayyan ya kai goshinsa kasa ya yi sujjada. Ba abin da ya zo ransa a lokacin sai “Sophie”, ya ce, “Yau Safiyyah ta yi Da, amma a ransa.
Ya sha mamakin ganin yadda Azeezah ta bata rai ta hade girar sama da ta kasa, ba sai ya tambaya ba shi ma da hankalinsa ya gane ba ta yi maraba da samun cikin nan ba.
Don haka bai ko tambaye ta me akayi mata take fushi ba. Likita ta hada ta da kwayoyin magani da za su taimaka mata kawai, don ta ce amai sai lokacin da ya ga damar tsayawa in cikin ya yi kwari kamar wata uku ko hudu.
A mota yana tuki yana ta hamdala a ransa kamar ya yi fiffike ya tadda Safiyyah, Azeezah na faman cin magani da turbune-turbune. So ta ke ta ce da shi ita gaskiya ba ta shirya haihuwa yanzu ba, amma ba fuska. In fact tana iya gane how excited he is da samuwar cikin nata ko daga sujjadar da ya yi a gaban likita.
Da wata sabuwar kulawa ya bude wa Azeezah kofar bangarenta da dayan hannunsa, ya ce, “Maman Baby ko sai na fito na dauke ki ne yau?”
Kamar mai jira ya tanka mata, sai ta daddage ta fashe da kuka, ta kuma ki fitowa daga motar.
Hankalinsa ya yi tashin da ya sa shi dauko ta kacokam ya dora a cinyarsa, ya rungume ta sosai yana magana cikin wani yanayi.
“Azeezah ba kya son haihuwa da ni ne?”
Budar bakinta sai cewa ta yi,
“Ni ba haihuwa da kai ne bana so ba, haihuwar ce ban shirya mata ba kwata-kwata yanzu gaskiya.
Har yaushe aka yi auren namu da zan fara raino kuma? Physical structure dina ma canzawa zai yi da wurwuri, sannan in na haihun ka rage shiga jikina a yi ta nanika min yaro da aikin kashi”.
Ta share Ido ta face hanci ta ja sheshsheka.
Da yake Zayyan dan duniya ne irinta, sai ya ce, “Kwantar da hankalinki Zeezahta, ni ma ai ban gama cin amarcina ba. Yanzu daurewa za ki yi, ki yi hakuri ki haifa mana shi, ko shayarwar ba sai kinyi ba, sai a bai wa Safiyyah ta shayar ita tayi ta fama da aikin kashin”.
Ya sa hannu ya shafi kirjinta ya lumshe ido, ya ce, “Ni ma bana son wannan valley of happiness din nawa ya rankwafa, na fi so ya yi ta tsayuwa ina kadasu yadda nake so”.
Tuni ya samo kan Azeezah, don irin hirarrakin data fiso kenan, yayi ta koda kyawun halittarta, ta sakalo hannun ta wuyansa tana murmushi, ta sumbace shi a kunci da lebbansa. Ta ce,
“Honey, ka yi alkawarin ita za ka bai wa da zarar na haifa? Ni gaskiya bana son hidimar yara. Har yanzu fa ban kai shekaru ashirin da biyar ba”.
Ya ce, “Yadda ki ke so haka za a yi Zeezah, ki haifa ki bata”.
Kuma bai gaya mata gaskiyar cewar matarsa Sophie is desperate da son samun haihuwa ba, don kada ta samu hanyar yi mata gori watarana.
A haka suka karasa sassan Azeezah kamar ya maida ita cikinsa don kulawa.
Wato bai san yana matukar son haihuwar haka ba shima, sai yanzu da aka yi cikin ba zato ba tsammani a gidansa.
Ji yake a ransa ko da Azeezah za ta ce sai ya biya ta za ta yi masa rainon cikin,Kuma sai ya biya kudin nakuda zata haife masa dansa a shirye yake ya biya duk abin da zata nema.
Wannan a ganinsa nasararsu ce shi da Sophie, kuma tun ba a je ko ina ba aurensa da Azeezah ya zamo maslaha ga matsalolinsa shi da Safiyyah kamar yadda yayi fata.
Yana kai Azeezah daki ta ce yunwa ta ke ji, ga shi ba ta ko son ganin abincin. Ya ce,
“To yaya kenan za a yi da kai baby? Kana jin yunwa kuma ba ka son ganin abinci. Ba ni minti goma ina zuwa”.
Sannan ya sumbace ta a goshi ya fita, yana cewa, “Take care Maman Baby!”.
Duk wanda yake tunanin haihuwa bata karawa mace kima da matsayi a gun mijinta ya dai fada ne kawai. Ga Zayyan dai ya kara susucewa a kan Azeezah har fiye da farkon aurensu.
Sassan Safiyyah ya doso da sauri-saurinsa har yana tuntube, tun daga falonta na farko yake kwala mata kira,
“Habibty! Sooooophie!!”
Tana fitowa suka yi arangama a tsakiyar dakinta, ya sunkuce ta ya hau juyi da ita a tsakiyar dakin kamar itace tayi cikin, murnarsa da farin cikinsa a fili irin yadda ba ta taba gani a tare da shi ba.
Kafin ya dire ta a tsakiyar gadonta jiki na rawa, ya zaro test result din Azeezah yana nuna mata, yana yi mata kwakwazon yau ta yi Da, Azeezah ta tabbatar masa da ta haihu ko shayar da dan ba za ta yi ba za ta bata shi.
Safiyyah so ta ke ta nutsu kafin ta san amsar da za ta ba shi a kai. Wani irin abu ta ji ya darsu a zuciyarta mai kama da cakar allura a kirjinta, wanda dacinsa ya fi na madaci, zafinsa ya fi na harbin kunama, kuma ba kishi bane ba hassada ba.
Sai dai nan da nan ta soma neman taimakon Allah a kan ya cire rabon shaidan daga zuciyarta.
Zayyan ne fa! Yake gaya mata yau an samu ciki na haihuwa a gidanshi, da wauta irin tashi kuma yake gaya mata cewa wai ita za a haifa a baiwa.
Ta taya Habiby dinta murna na zai ga dan kansa baka da zuci, ta kuma tausaya wa kanta, da ya kasance ba ita ta kawo masa wannan sanyin idanun da yake marari ba.
At the same time ta kara gasgata zancen kawarta ta asibiti Ammara, da ta ce,
“Karya yake da ya ce haihuwa ba ta dame shi ba. Yana dai pretending ne don samun kwanciyar hankalinki”.
Safiyyah ta dago rinannun idanunta tana kallon Zayyan da su. A lokacin da yake kara bata tabbacin cewa ko shayar da jaririn ta ce ba za ta yi ba, “ke za ki shayar min da shi Sophie”.
Sophie rasa me za ta ce ta yi. Da kyar ta iya cewa,
“Ällah ya inganta mana”.
Zayyan ya rungume ta a kirjinsa wanda ya baiwa hawayen idanunta damar sulmiyowa a gadon bayansa ba tareda ya gani ba.
“Sophie, na kara imani yau, ashe dai ba sha’awa ce kadai ta kai ni ga auren Azeezah ba, zazzafan rabo ne, wanda zai kawo karshen matsalolinmu nida ke. I never expected her to get pregnant this soon”.
Safiyyah ji ta yi kamar ta rafsa ihu don bakin cikin da ya lullube ta, ita ba abin ta ce “innalillahi wainna ilaihi rajioun” ya ce ta dauki farin cikinsa masifa ba. Haka ta ci gaba da sauraron tatsuniyoyinsa irin na wanda yayi shekara goma Sha biyu bai samu haihuwar fari ba, har yana cewa bai taba ganin mace mai kirkin Azeezah ba, da har ta amince ta bar wa ‘yar uwarta mace Dan da za ta haifa. Shi kan Azeezah ta gama masa komai, tunda ta cika ma Sophienshi burinta.
“Ina rokonki Sophie ki taimaka min mu kula da ita, har Allah ya sauke ta lafiya”.
Safiyyah ta yi namijin kokari wajen daurewa surutansa, kai ka rantse a baya ba a taba yin ciki an haife a gidansa ba. A matsayinta na ‘yar Adam kuma diya mace hakika ta taya kanta da kanta kishi, wanda kumallon mata ne da a kullum cikinsa ta ke rayuwa, tun ranar da ya kawo Azeezah gidan a matsayin matarsa.
Yanzu kuma ga matsayinta ya karu zuwa na uwar ‘ya’yansa. Ita kuma ko yaya sunanta a gidan Zayyan yanzu?
Sai da ya yi bidirin murnarsa ya gaji sannan ya ce, ta je ta karasa wankanta, ta zo ta ba shi wani abun mai sauki ya kai ma Azeezah ta ci tana jin yunwa, kuma wai ba ta son ganin abinci a kitchen dinta.
Safiyyah ta koma toilet da niyyar karasa wankanta, amma sai ta jingina a jikin kofar, ta daga kanta sama, hawaye suka kece mata kamar famfo. Mafarkinta na samarwa Baba Bello magaji na farko, kuma sanyin idaniyar da uba ke samu ga Zayyan a dan fari, Allah bai sa ya zamo gaskiya ba.
Ko kafin ta gama wankan ta fito ma shi har ya soya ma Azeezah plaintain da kwai ya dauka ya fice.
Sai ta daina mamaki don Zayyan na nuna zumudi a kan haihuwa yau. Kayan sallarta ta saka ta shimfida dardumar sallah ta feshe ta da turaren ‘musk’ ta yi sujjada, ta ce,
“Ya Allah ka yi min yadda ka yi ma Annabi Zakariyyah, Ka ba ni haihuwa ko a tsufana ne”.
Daga lokacin ta sa ma ranta cewa, insha Allahu ta daina damuwa a kan rashin haihuwa, tabbas Allah bai manta da ita ba,kamar yadda bai manta da Annabi Zakariyya ba, haka sanda Ya ga damar bai wa Azeezah Da daga Zayyan bai manta tana nan ba.



