Chapter 8: Chapter 8
Fi’ili, falli da tsurfa ba irin wanda Safiyyah ba ta gani a wurin Azeezah da Zayyan ba, a lokacin rainon cikinta. Kwata-kwata tukunyar abincinshi ta dawo hannunta, Azeezah kuwa sai iya kwana da miji, amma ba ta san hanyar kitchen ba, wai da sunan hidimar cikin Zayyan. Ita kanta kullum a tafe yake wajen sayo mata a ‘çilantro’ ko sauran fitattun gidajen abincin Abuja, don ta ce ba za ta kara yarda ta ci abincin matarsa da rannan ya bata ba.
Mama ta tsoratar da ita cin abincin Sophie, tun daga lokacin da ta samu labarin samuwar cikin. Mama ta kidime ta shiga farin ciki. Ta rasa ina taka saka ina taka aje da surukarta Azeezah.
Rannan suna waya Mama ta ce, sai ta yi a hankali yanzu daga cin duk wani abu da zai fito daga hannun Safiyya, don sun saba surkulle ita da iyayenta, irin nasu na gadon Alarammomi. A bakin Mama ne ma Azeezah ta san cewa Safiyyah diyar Alaramma ce don Mama ko sunan Safiyyah ba ta ambata, sai dai ta ce, ‘diyar Alaramma’.
Ba jimawa Azeezah ta gane akwai baraka sosai tsakanin su Mama da Safiyyah. Wadda barakar daga Mama take, kuma rashin samun haihuwa da bata yi ba har lokacin shine sila.
Kullum Mama cikin aibata Sophie ta ke a gun Azeezah, tana kaskanta matsayinta, tana kiranta da sunaye na kaskanci daban daban, wanda shi ya bai wa Azeezah dama itama, ta kara raina ta, don ta gane bata da wata fada a gun Uwar mijinsu, duk da zama suke irin na ba ruwan wani da wani, amma Azeezah sai ta san yadda ta yi ta yi abinda tasan tabbas zai bata wa Sophie rai. Musamman kiran Zayyan cikin dare a ranar girkin Safiyyah.
Idan a baya yana ignoring calls dinta sabida kaifin idon Safiyyah, yanzu albarkacin cikinta dole yake dauka ko kwance yake da Safiyyah karewa kenan. Ya zama cewa ko me yake yi duk muhimmancinsa kuma cikin kowane hali in dai Azeezah ta yi kiransa zai yi excusing Sophie ya tafi, ya kan ce,
“Kin san irin halin da ta ke ciki, dole ba zan dinga yin nisa da ita ba”.
Sai Safiyyah ta ce, cikin sanyin murya, da karyewar zuciya “I am not against that. Haka ne Habiby, ai ni ban ce a’ah ba, Allah ya sauke ta lafiya ya bamu mai albarka”.
Amma matuka gaya abin nan da Azeezah ke mata yana bata mata rai. Dasu kiss din gaban mota a filin Allah, idan ta rako shi da safe zai fita office, ita kuma Safiyyah ta kasa yiwa kanta fadan daina bude tagar dakin barcinta ta ko don ta bar hango su, duk ranar da ya kwana dakin Azeezah. Azeezah ta san da tsayuwarta shiyasa ma take yin wasu abubuwan.
Duk kuma sanda suke tare, wato Zayyan da Azeezah, Azeezah na kokarin kawo zancen Safiyyah irinna bugun ciki akanta, idan tana tare da Zayyan sai tayi ta hilatarsa don son jin matsayin da ya baiwa Sophie yanzu a gidansa tunda ita ba haihuwa ba ba iya rayuwar aure ba, tace ta lura kanta a tukunya yake kamar bata taba zuwa makarantar boko ba, shi kuma yana yawan kauce wa hakan. Ta hanyar murtuke fuska ya ki tankawa. Ba ya son ana gulmar Safiyyah, ba da shi ba ma ko da wani ne daban sai inda karfinsa ya kare, don ita ai ko da wasa ba ta yi masa nagative zance akan Azeezah.
Kamar yau suna breakfast shi da Azeezah, wanda order ya yi mata daga ‘Blu cabana’, ta ce, “Baby, ya ba ka cin abincin sosai ne?”
Ya ce, “Wannan ai naki ne Zeezah, na san Sophie zuwa yanzu ta gama kunun Tamba dinta mai gardi, zan je na roke ta ko zata sammin?”.
Azeezah ta kyabe baki ta ce, “Wai don Allah Baby, ya ya aka yi ka auri wannan bagidajiyar ne? Sadakarta aka baka? Mace kullum a sunke har a cikin gida, sai ka ganta da hijabi. To be frank, ba ku yi matching ba, kanta a rijiya yake, ba matar wayayyen mutum bace irin ka, can dai ire-iren malaman makaranta”.
Mikewa ya yi da sauri jikinsa har yana bari, yana fadin, “ya isheki haka Azeezah! To bari in gaya miki ai nima nan da kike gani malamin makarantar ne, Zayyan kika sani kika kuma aura ba Bappan Mama dan gidan Baba Bello ba, itace ta auri Bappan Rafindadi tun yana gaban Baba Bello, kuma malamin makaranta wanda bashi da Estate ko daya.
Tukunnama shin wai ke ina ruwanki da matata ne Azeezah? Kina da son kawo min zancenta, tun ina miki shiru ina kaucewa, har kin fara hadawa da cin mutunci wanda bai dace ba. Ko a tandun mai kanta yake tare kika ganmu, kuma na aure ta a hakan ne don ina sonta da gidadancin nata da kauyancin nata da hijabin nata, ke ma ina sonki da gayun naki da kwalisar taki da duniyancin naki da komai, ki gayamin ta ina na kasa son kowacce a cikin ku da nature dinta?”
Tun daga wannan amsar da ya ba ta Azeezah ta ke shakkar sake yi masa zancen Safiyyah, domin taga bacin ransa karara irin wanda bata taba gani ba, wuni guda bata ga murmushinsa ba, shiyasa ta yarda har zuciyarsa ba ya so din.
Suka wayi gari da baki yau a gidansu, Yaya Zubaidah da Zahrah da Zaytoon da yaransu.
Wai sun zo ne duba Azeezah da jiki. To Safiyya ba ta san da zuwansu ba, kuma ko da suka zo sassan Azeezah suka tare, sai ita ce da Zayyan ya gaya mata su Yaya Zubaida sun zo ta hau hidimar shirya musu abinci na musamman, ta kuma sa a gyara musu dakin baki.
Amma ko da Yaya Zubaida ta ji an gyara musu dakin bakin gidan wato guest wing din Zayyan, cewa ta yi ita a sassan Azeezah zasu sauka, kwana biyu kawai za su yi.
To an yi rashin sa’a ranar ya kama girkin Azeezah ne. Azeezah bata hada hidimar shimfidar mijinta a muhimmanci da komai, daga sassan Sophie aka shigo musu da manyan ma’ádanan abinci na alfarma, zuwa falon Azeezah inda acan suka baje, amma sai Azeezah ta dubi mai aikin data kawo tace, “don Allah don Annabi Janet kai musu masaukinsu bana son kamshin dafaffiyar shinkafa”.
Yaya Zubaida ta ji wani iri, amma ba ta ce komai ba.
Da daddare Zayyan ya dawo ya zauna a cikinsu a nan falon Azeezah suke hira da ‘yan uwansa. Hirar yaushe gamo. Don sun dade basu hadu ba. Har karfe goma Azeezah na jira su tashi su barta da mijinta, abu ya gagara. Zubaidah na kara ballo sabon zance. A duniya ba abin da zai sa ta iya raba daki da mijinta in ba dole ba, balle wasu dangin miji da ba ita ta gayyato su ba.
Azeezah tun asalinta ba ta son a takura mata kuma bata son a saka mata ido.
Har goma ta yi su Yaya Zubaida sabuwar hira suke barowa da Arch. Zayyan. Kawai sai Azeezah ta tashi ta shige daki, can anjima ta fito cikin wata fitsararriyar lingerie. Boobs na kyalli sun leko ta sama. Daga bakin kofar dakinta ta tsaya saitin Zayyan, ta ce,
“Honey!”Tare da yin mika irin ta jin barci, tana turo matashin cikinta da ya fara bayyana kansa gaba, ta sake yin hamma ta rufe baki, ta ce, “Honey, bed time!”.
Kunya ta kama Zayyan kamar ya ce kasar ta tsage ya shige. Ya san halin Azeezah kuma sarai in bai tashi ba tana iya yin abin da ya fi haka. Ga kwalliyar ta dauke shi sosai, ya mike cikin borin kunyar kannensa da ke wajen, yana cewa,
“Yaya Zubaida za mu shiga daga ciki, sai da safe”.
Bai kuma jira cewarsu ba ya nufi dakin barcinsu. Suna shigewa Azeezah ta rufo kofa har da maukulli, ji kake bammm! Zubaida ta dubi Zahra, Zahra ta dubi Zaytoon, Zaytoon ta dubi Yaya Zubaida suna zazzare ido, an rasa mai iya cewa komai.
Kowacce ta yi magana amma a zuciyarta cikin cewa “Azeezah ba ta da kunya”. Amma wa ya isa ya kushe diyar masu kudi a wurin iyalin Mama? Not even themselves. Don haka kowacce ta hadiye korafinta.
Zaytoon ta ce, “To yanzu a falo za mu kwana?”
Zubaida ta nisa ta ce, “A’a, mu je wajen diyar Alaramma ta ba mu inda za mu kwana, tun dazu ta aiko a rakamu ai na gwasale, ni mai sabuwar suruka dana yi uwa nayi makarbiya a aurenta amma ashe mara mutunci ce”.
Zaytoon ta ce, “Amma da kunya Yaya Zubaida muje wajen Safiyyah yanzu, tunda muka zo ba mu shiga sassanta ba, ta girko abinci ta aiko mana, shi ma bai sa mun je mun ce mun gode ba. Ta zo da kanta ta gaishemu. Muka amsa a wulakance. Sai yanzu mu kwashi kafa mu je gunta don wadda muka zo dominta ta yarfa mu?”
Yaya Zubaida ta yi tsaki ta ce, “aikin banza kenan. Wa zan ji kunyar? To abincinta ne ko daga gidansu aka kawo? Banza a banza da ita. Da Allah can ku tashi mu je, don ni ban iya kwana a kan kujera ba, ciwon baya ta ke saka ni”.
Ta kara da cewa, “ba laifin Azeezah ba ne, laifin almurinnan Baffa ne, da ya nuna mata ba mu da matsayi a wurinsa ya biye mata babu ko jin kunyata ni da haihuwarsa ne kawai ban yi ba ya bi bayan mace a gabana suka shige daki suka barni a shanye. Don haka gobe da sassafe zan bar masa gidansa”.
Dole kanwar naki haka suka jawo jiki da jakunkunansu suka dawo sassan Sophie, dakin bakin yanatsakiyar gidan kuma basu san ina ne ba. Don haka dole suka fara ma Sophie knocking.
Har ta kwanta ta ji ana buga mata kofa. Ta sako hijab kan rigar barcinta, ta zo ta bude sai kawai ta ga su Yaya Zubaida suna tsaye rai a bace. Ta ba su hanya cikin girmamawa da mutuntawa ta ce,
“Su Zahra ne sai yanzu? Ai tun dazu banyi barci ba ina jiran shigowarku in raka ku guest wing”. Uffan ba wadda tace mata cikinsu.
Ta wuce gaba ta bude musu dakin bakin ta kuma tsugunna a gaban Yaya Zubaidah tana tambayar Zubaidan ko akwai abin data ke so ta kawo mata kafin ta kwanta? Ta san Zayyan ya taba gaya mata she’s a green tea addict, tana shan green tea at night time kullum. Yaya Zubaida tana yatsina ta ce.
“Bana kwanciya sai na sha ‘green tea’ mai zafi”.
Ta ce, “Okey Yaya bari in dafo in kawo miki yanzu, lipton din wanne a ciki? Tetley ko Twinnings?”.
Yaya Zubaidah tace “Tetley”.
Bayan Sophie ta juya ta fita ne Zahra ta ce, “Allah sarki, ita kam ba ruwanta, bata dauki duniya da zafi ba”.
Zubaida ta yi tsaki ta ce, “Wannan sumumu-kasau din? Ba ta da abin yin fuffukar ne. Imagine ace diyar manya ce sabida kyawunta, dubi zubinta da iya tafiya da maganarta na class ne, ai kinsan da an sha kallo da iyayenta wasu ne, ita kuma waccan ko me ta yi ai ta isa ne”.
Zaytoon ta ce, “Ga shi duk ta kara ramewa, kamar kudin guzuri. Na tabbata cikin Azeezah ne yake kara cinye kuzarinta. Ni wallahi yanzu tausayi take ba ni.
I’m putting myself in her shoes as a woman, shekara sama da goma ina tare da mijinda nake so yake sona bamu haihu ba, sai wata gantalalliyar haihuwar IVF, rana daya yana auro wata ko shekara bata rufa dashi ba sai ciki. Is not easy fa, tama yi kokari da bata kwanta ciwo ba”.
Zubaida ta ce, “Kyale mace in alkadarinta ya karye kawai, sanda Zayyan ba ya ta kowa sai tata ai har kyallin goshi take yi saboda cika da koshi.
Amma yanzu bakin cikin kishiya ‘yar manya kadai kuma mai haihuwa ya isa ya karar da ita kamar karan raken takanda”.
Dan Adam kenan! Kada ka taba yi masa abu don ka burge shi, kayi masa don Allah ba don halinsa ba, ko don abinda zai saka maka dashi in return ba. Dubi dai yadda can an wulakanto su sun kasa cewa don me, nan an karrama su sun saka da cin namanta. Ba godi bare an gode. Anya?
Washegari suka mayar zasu koma Katsina kawai sun fasa yin kwanaki biyun, saboda Zayyan har karfe sha biyu na rana ba su saka shi a idonsu ba balle ‘yar mulkin. Tun karfe takwas Sophie ta kai musu karin kumallo mai rai da motsi. Kunun gyada kunun Acca, zazzafan Tea, kosai da toasted bread data gasa da kanta da farfesun kayan ciki haka ta shirya ta kai musu.
Babu kunya babu tsoron Allah suka nade hannun riga suka kwashi gara suka side hannuwa sukabar mata filasanta anan.
Har shabiyun rana ta buga, zuwa lokacin Yaya Zubaidah ta gaji da jiran zuwansa ta ce su Zahra su tashi su tafi haka. Da ma direban Mama Malam Muntari ne ya kawo su kuma a gidan ya kwana, sai da suka fito suka dan shiga falon Safiyyah a dosane suka ce mata zasu wuce yanzu, tana kokarin basu sautu gun Mama na kayan data hada mata a babbar leda ta H-Medix sai ga shi ya shigo.
Ya yi bala’in daukar wanka ya hade cikin shudiyar Wagambari Caftan tamkmar sabon ango da wata lallausar farar hula Tonak a kansa. Ya soma baiwa Yaya Zubaida hakurin rashin fitowarsa da wuri, ya ce “Azeezah ce ba ta jin dadi, shi ya sa bai samu fitowa ba sai yanzu”.
Ya kawo kudi masu kauri ya bai wa Zahrah da Zaytoon ya ce a yi ma yara tsaraba.
Yaya Zubaida kuma yace ta nemi iznin Baban su Juhaina (maigidanta) cewa ya biya musu umara zasu tafi itada Mama da Zubaina nan da sati hudu. Duk don ya wanke mata zuciya yana sane da cewa jiya sun bata mata rai shi da Azeezah.
Suna jiran ganin Azeezah tazo musu sallama ta musamman ko ta bada wani muhimmin abu a kaiwa Mama kamar yadda Sophie ta bada manyan turaruka da turmin ‘julius holland’ guda biyu ta ce a kaiwa Mama. Amma Azeezah ko keyarta basu gani ba da sunan ta zo musu sallama.
Tana gidanta ta rufe sassanta ruf don a cewarta Zahra da Zaytoon sun faya saka ido. Ita kuma Yaya Zubaida ba ta da kauda kai a kan Zayyan kamar wata uwarsa.
Ko kyalle bata basu ba, balle tace agaida Mama uwar mijinta da ta turosu su duba mata jikin Azeezar.
Hasalima ko keyarta ba su kara gani ba tunda ta ja mijinta daki daren jiya, shi da Sophie ne suka raka su gaban mota suka shiga suka tafi. In ma sun ji haushin rashin kulawar da Azeezah ta yi musu da wulakancin ta to sun bar abun a ransu, ba wanda ya iya gaya wa Mama don Azeezah ce bata laifi.
“Ai ‘yar manya ce, dole akwai class”. Haka Yaya Zubaida keta ce musu a hanya.
Tunda dai za ta haifa ma Baffa dan kansa kafin ya fara furfura, ni ta gama min komai”.
Inji Yaya Zubaidah again.
Kuma koda suka je gaban Mama basu kushe Azeezah ba ko fadin tayi musu wani abu da basu ji dadi ba.
Wannan ta wuce.
Bayan Assafe ta koma Lagos shima Yaya Shaikh ya dawo daga Tunisia, sai take labartawa maigidannata Dr. Ridhwan (Yaya Shaikh) labarin haduwarta da (favourite sis) din shi Safifi a bikin su Sabah, a very beautiful damsel and an easy going stammerer! I like her from our first meeting and I love her stammering. Yaya Sheikh yayi murmushin jin dadin jin Assafe na yabon Safifi, har tana jin dadin in’inarta, yace “don’t dare call her an easy going stammerer, kura ce da fatar akuya wannan mai in’inar a wasu lokuttan, domin Safifi in ta botsare wallahi babu mai iya tankwarata sai Allah.
Bata da fushi, bata da saurin yinsa, amma tabbas Safifi tanada wani irin riko idan an zalinceta ko an bata mata. Kuma sai ta rama hankalinta ke kwanciya. Zaka dade kana mata laifi baka san kana yi ba, sabida bazaka taba ganinsa a tare da ita ba, bazata nuna maka ba, bata nuna fushi akan komai, bud deep down inside her, taraka take a kasan ranta.
Ranar duk da Stammerer Safifi zata fashe maka, sai ka gwammace kida da karatu, bazata yi maka da dadi ba, ko yaya tsakaninku yake Safifi bata yarda a zalunceta.
Mai iya mata in tayi fushi sai ni da Ammi ne kadai ke iya lallabata”.
Nan ya shiga baima Assafe labarin kuruciyar Safiyyah da irin rikon addininta. Yadda ta haddace Al’qurani tun tana da shekaru goma sha biyu. Daga yadda kullum Dr. Ridhwan ke baima matarsa Assafe labarin Safifi har ya zamanto Assafe ta haddace komai na halayenta da dabi’unta, tayi wa Sophie farin sani bayan wanda tayi mata a gidan biki, ta kara saninta a bakin Yayanta mafi kusanci da ita a lokacin kuruciya.
A lokacin Assafe na aiki da FIRS a garin Lagos, kuma ta yi ta yi ya kawo ta Abuja ko ya barta ta je da kanta ta kwanar ma Safifi bayan bikin bikin su Sabah da wajen watanni shidda, amma Ridhwan ya ki. Ya rasa dalilin da ya sa ba ya son zuwa gidan mijin Safiyyah tunda yayi concluding a ransa Zayyan baya kaunar farin cikin Safiyyah, baya tausayinta, a karan kansa ya san ba kishiya da aka yi mata ne kadai ya sa ya ki zuwa ba, ya kuma hana Assafe.
Tun fil azal Safiyyah daban ce a wurinsa. Tun Ammi na masa tuni kan ya je yasada zumuncinsu har ta gaji ta bari, ta ce ma Assafe duk sanda suka zo Katsina again za ta saka Rayha ta kai ta har gidan Safiyyah ta kwana.
A kasan ransa Ridhwan yana ji wa Safiyyah ciwon rashin haihuwa kamar yadda yake jin nasa. Ya san yadda ciwon abun yake. Sai dai shi bai dauka da zafi ba, balle har hakan ya tunzura shi ya kara aure, a ganinsa Zayyan bai san darajar Safiyyah ba sam. Shiyasa baya marmarin zuwa gidansa. Duk da Ammi tace wai wai wai wasu mazan da yawa nada dalilinsu na kara aure, ba lallai rashin son uwargida bane.
To ina ga idan Ridhwan ya zo ya ganewa idanunsa irin rayuwar da Sophie ke yi yanzu a gidan Arch. Zayyan Bello Rafindadi?
Cikin Azeezah na girma, fi’ilinta na karuwa. Zayyan na kara ja baya da ita. ‘Yan uwansa na kara uzzura mata.
Lokacin da cikin Azeezah ya shiga watan haihuwa kuwa suka soma jido sayayyar Baby da na maijego shi da Azeezah, kai sai ka rantse da Allah katafaren shago za su bude a cikin gidan. Wani abu a halin Azeezah da Zayyan ya lura da shi shi ne tana da son wadaka da dukiya. Ga son rayuwa ta kecewa tsara da son kece raini. Zai iya cewa bukatun Azeezah ba wai sun fi karfin aljihunsa ba, amma sam bai saba da irinsu daga Safiyyah ba.
Amma tunda a lokacin ji yake ko me ya yi ma Azeezah bai biyata wahalar cikin da ta ke dauke da shi ba. Shi ya sa yake kokarinsa kan jiki kan karfi yake saya mata irin suturun da ta ke so da manya-manyan designers din kayan kwalliyarta. Azeezah is a classy Baby, komai nata sai azababben designer.
Kwarai aljihunsa ke girgiza da sayayyar haihuwar da ta ke yi tana tarawa in sun shiga boutique na jarirai. Sayi banza sayi wofi harda wanda bazai ma jaririn wani amfani a halin yanzu ba. Bayan wanda aka kawo mata akwati shida bi-da-bi daga gidan iyayenta.
Mama ma ba’a barta a baya ba ta lodo lesika na fitar suna da atamfofin jego da kayan jariri don ita kam yanzu ne za a haifa mata jika dan Baffa! Yo Dan Baffa ai shi ne jika a gidan Bello Isyaku Rafindadi, ba a haifa ba, ba kuma za a haifi mai matsayin na Baffa ba acikin jikokinta sai ‘ya’yan gidan wasu, wato jikokinta na ‘ya’yanta mata.
Amma ko da aka kawo wa Azeezah akwatin mama ta bude, tana daga zaune da tirtsetsen cikinta a gabanta, a bakinta cingum ne na hubba-bubba tana taunarsa kas-kas-kas. Ta daga wata atamfa cikin kayan Mama Zayyan yana zaune gfenta sai cewa ta yi.
“Gaskiya kayan mama duk masu arha ne, ni ai bana daura irin wannan”.
Zayyan ya dago da manyan idanunsa daga kan wayarsa ya dube ta, kamar zai yi shiru, sai ya kasa, ya jefeta da gatse.
“Sai ki bai wa wannan tsohuwar da aka kawo miki zaman dabaro, ita ai zata saka”.
Azeezah ba ta san gatse ya yi mata ba, ta ce, “Ko masu aikin gidan nan sun yi fitar suna da su ba! Af, ka ga na manta Umm Nihla ta kawo min tallan materials din da ta ke kawowa daga Malaysia, ina so na dauki guda biyar, materials ne ‘yan ubansu Baby, masu kyau da quality, don Allah ka kai ni in zaba mana? sunansu “Malaysian fabrics.ng”, kuma ana iya tuntubar Malaysian Fabrics a lambar waya (07020695644) don sayen hadaddun materials dinsu daya ko sari”.
Da yake ya ji haushin abin da ta yi wa bajintar Mama gare ta, sai ya ce, “Ba inda za ni a daren nan, wai ke ina za ki kai suturu ne?
Ayi mace sai ka ce diyar Qaruna don kashe kudi, bakida wata magana sai ta sayen suttura, ni Sophie ba haka ta ke ba, ke kam dai, kyale-kyalenki ya wuce kima”.
Azeezah ba ta taba harararsa ba sai yau, ta ce, “da baka ganni kal-kal ina sheki ba, ai da ba ka ce kana sona ba.
A haka ka gan ni ka aura, a haka zan ci gaba da rayuwata. Don’t ever never compare my class with your typical local wife please. Ta yi karatu amma kamar haihuwar kauyen cikin jeji. Na tabbata rashin gayun ne ya sa ka kasa zama da ita ita kadai, amma don so kana sonta. Adadin sonka da mutum adadin yawan ambatonka dashi”.



