⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 1: Chapter 1

KAWAR ZUCIYA 4

Shi kuma da yake Rakumi da akala ne a cikin taron mata, ya biye musu, ya saki Safiyyah, matar da Zubainah ke da tabbacin sun ci amanar Baba Bello a kanta.
Abinda Zubaina ta ji a ranta a lokacin ba zai misaltu ba, amma a fili sai tace.
“Ai shi kenan. Kowa yayi da kyau, zai ga da kyau Ya Zubaidah, tunda kun cika aikinku hankalinku zai kwanta yanzu, Mama Allah ya ba ta lafiya, don kuwa ciwonta ba na sugar bane kadai har dana bin kawar zuciya, wanda shima ciwo ne mai zaman kansa dake bukatar magani, da kuma shaidan la’ananne dake taka rawarsa a tare da zuciyar Mamanmu.
Ke kuma Ya Zubaida wallahi ba zan taba yarda babu hannunki ba, ai komai tare kuke yinsa ke da Mama.
Kada ku manta muma nan duka mata ne kuma mun haifi ‘ya’ya mata, ba fata nake mana ba Ya Zubaidah amma….”.
Zubaida ta katseta zata soma rantsuwar cewa babu hannunta, Zubaina tayi maza ta kashe wayarta zuciyarta na tafarfasa.
Zayyan din ta shiga kira ba kakkautawa, amma ko da ya ga kiran Zubaina ne ya san kwanan zancen a wannan lokacin.

Don haka Zayyan ya ki dagawa. Don bashi da abinda zai ce ma Yaya Zubaina, ya yarda yayi disappointing dinta, yayi fatali da tarin nasihohinta gareshi akan rike Safiyyah. Ita kadai ce ke bin foot steps din Baba Bello cikin ‘ya’yan gidansu, ta kuma rike koyarwarsa. Amma gashi harda shi din yau dukkansu sun taru sun bijirema tarbiyyarsa da koyarwarsa.
Ba abinda yake so a yanzu irin a kyale shi daga kowacce irin magana, a bar shi ya tattauna da zuciyarsa shi kadai, ya kuma yi jinyarta, kan ciwon da ya ji mata.
Ba aikin da na sani Mama da Safiyyah suka taru suka sa shi aikatawa ba, a’ah, sun saka shi yayi hukunci ne bisa dokin zuciya da tunzurawarsu da tursasawarsu, hukuncin da ya tabbatar ya gama destroying farin cikinsa da gidansa, ba don yana da “Shaheed” ba. Wanda zai kalla koyaushe ya ji saukin ciwon kuskuren da ya aikata. Yake kuma da tabbacin wannan kuskuren zaiyi ta haunting dinsa har zuwa karshen rayuwarsa.
Jin dadin Zayyan daya ne, in ya tuna a zuciyarsa saki daya ne yayi. Da wannan fatawar Zayyan ya dogara a yanzu. Yake son kowa ya kyale shi da kowacce magana da kowacce hayaniya kan abinda ya aikata a halin yanzu, har sai ya gama tunanin hanyar gyara barnarsa, daga nan sai ya nemawa kansa mafita.

Yana fatan zai gyara kuskurensa bada jimawa ba. Zai dawo da Safiyyah rayuwarsa. Yanzu nema ya kara yarda da sunan da yake kiran Safiyyah dashi a baya “HIS ALTER EGO….”. domin ji yake tamkar rabin jikinsa ya mutu. Safiyyah barin rayuwarshi ce bayan kasancewarta ginshikin nutsuwarsa, tunda gashi tunda Mama tasa shi korar Sophie daga gidansa ta kuma hana shi bin bayanta ya rasa nutsuwa ya rasa jin dadin rayuwar kota yaya.
Na farko dai ga Azeezahr a cikin gidansa, ga gayun nata, ga iya kwanciyar tata, gaba daya yanzu sun daina burge shi, kamar sanda Safiyya ke cikin gidan.
Bai kara jin sha’awar kusantar Azeezar bama. Sabida zuciyarsa kamar bata da ruhi. Itama Azeezah, tunda ta lura (he is more than depressed), ta tattara shi ta ajiye a gefe, ta baiwa banza ajiyarsa, ta kama gantalinta cikin gari zuwa gidajen kawaye da bukukuwan dangin Mamanta na kece raini, kullum bata wuni a gidan kamar ta ci kafar shanshani saboda yawo.

Mama ba ta san Zubaidah ta yi mata riga malam masallaci ba a gurin Zubaina, Zubaidah ta kira Zubaina da safiya sun yi rabuwar rashin arziki daga Zubainah, don ko kadan taki sauraron uzurin Yaya Zubaidah da rantsuwarta na cewa wai babu hannunta a sakin da aka yima Sophie, tayi rantsuwa kan cewa ita bata ma je gidan Baffa ba, a waya Mama ta gaya mata amma Zubaina taki yarda ta saurareta. Tace a komai bakinsu daya itada Mama.
Mama bata san sunyi haka ba ita kuma ta kira Zubaina da Yammacin ranar da suka yi waya da Zubaidah da safe.
Cikin damuwa da halin da Baffa ke ciki yau, don ya shigo da safe ya gaisheta ya fita, ta ganshi kamar wani karkuzu, sabida kasumba da rashin gyara. Mama ta ce da Zubaina, lallai-lallai ta zo ta mayar da ita Katsina, yau bata kara kwana a gidan Baffa. In yaso ya kashe kansa don soyayya.

Ta cewa Zubaina. “Wai Baffa sabida kawai ya rabu da matar da baya amfanuwa da ita, kuma ta ci mutuncin uwarsa shikenan ya kashewa kansa da iyalinsa walwala da rayuwa”. Zubainah bata ce komai ba, don ita tun fil azal mai matukar biyayya ce ga iyayensu amma Mama bata ganin biyayyarta, Mama sam bata yin harkokinta da ita, sai ‘yan gaban goshinta su Zubaidah da Zahrah ‘yan abi Yerima asha kida, saboda ita Zubaina kullum tunaninsu ba daya bane da nasu, in an yi gabas Zubainah yamma zata yi, saboda influence na auren miji mai addini, ya sa ita ba ta daukan komai yadda Mama da sauran ‘ya’yanta ke daukan rayuwarsu.

Tun suna kanana kuma jininta ya fi haduwa da na Zayyan, ita ta yiwa Mama goyonsa, ta tayata rainonsa. Duk da shekaru biyar kawai ta bashi, amma Zayyan ya sha goyo da majanyi a gun Zubaina.
Mama uwarta ce, mahaifiya, komai bakin halinta komai munin halinta uwarsu Zubaina sunanta, kullum tana tuna hakan tayi mata uzuri. Ban da haka da wata ce ba Mama ba, yau da ta bata kyakkyawar amsa.
Da tace da ita don me ta ke gudun zaman gidan Baffan nata kuma? Ai kawai sai ta maye gurbin Safiyya, ta hanyar share dakinta ta zauna a gidan Baffa tunda burinta ya cika, ta raba soyayya ta gaskiya da amana, ta guntile kauna da yardar da Late Baba Bello yake ma auren Baffa da Safiyyah.

Zubaina ji ta yi hawaye ya balle mata, ta ajiye wayar Mama, ba tare da ta bata amsar komai ba, ta san halin Baffa a halin yanzu, privacy yake so, da wuya ya daga kiranta, kuma da wuya ya tattauna matsalar nan da wani, zai bar abin ne a ransa har ya cutar da shi.
Ta rasa wa za ta ji tausayi tsakanin Zayyan da Safiyyah. Ta kuma rasa dalilin Mama na son barin gidan Baffa yanzu haka cikin damuwa bayan burinta a kansa ya gama cika.
Me yayi saura? Banda Mama ta zauna tare da Azeezahr da ta ke so gida daya ta dangwali daular diyar masu hannu da shuni, tunda ta raina nata arzikin, in yaso suyi ta lelen son Baffa su kadai itada Azeezarta?
Duk yadda Zubaina ta so ta danne bacin ranta ta je Abuja a washegari ta dauki Mama ta mayar da ita RafinDadi kamar yadda ta bukata, Zubaina kasawa ta yi, don bakin ciki take ji sosai a ranta, sai Zahra ta yi wa waya itama, ta fada mata bukatar Mama na wani cikinsu yaje ya dauketa daga Abuja ya mayar Rafindadi, don zuciyar Zubaina a matukar bace take da Zayyan da Mamansu Haj. Fatu.

A karshe dai Zahra da maigidanta ne suka je Abuja suka dauko Mama ba yadda take, don kuwa kafin su zo Mama ciwon data ji a kafarta ya kara ta’azzara ya ja ruwa, kafar tahaye suntum, ba wata kulawa da ta kara samu a gidan Zayyan tunda taji ciwon da karfen shower a bandaki, a matsayinta na mai ciwon sugar ya dace a kula da ciwon, hatta magungunanta na suga da bp duk sun jima da karewa Zayyan bai sayo ba, don baya fita ma bai san halin da Mama ke ciki ba, bayan kulawar da Safiyyah ta bata bata kara samun wata kulawar ba.
Zayyan ba ya gidan sanda su Zahra suka zo suka dauke Mama, haka Azeezah ta fita birthday din aminiyarta Sakinah Sambo .
Daga nan Sunset Estate kai tsaye Zahra ta ce da mijinta Ubaid su wuce da Mama asibitin da take zuwa kawai a duba ta, don ganin yadda kafarta ta koma. Zahra ta kira Zayyan sau ba adadi gabadaya wayoyinsa a kashe suke, kuma ba su samu Azeezah a gidan ba itama sai su Janet da yau suka yiwa Mama dafadukan taliya matsayin lunch, duk ta dankare a warmer, su kadai suka samu a gidan, wanda halin da Mama take ciki yau bai barta ta ko dandana abincin ba, sai su Janet din suka barwa sallahun cewa sun zo sun tafi da Mama idan Zayyan ya tambayesu..
** **

Zahra da Mama a kwance a gadon likitan da ke duba Mama, yana dressing gyambon kafarta, likita yayi fada yayi masifa kamar zai ari baki, kuma kamar zai duke su itada Zayyan da baya wurin, yace zai iya karar Zayyan da ‘yan uwansa kan sake da lafiyar mahaifiyarsu, tunda ba cikin rashi suke ba, cikin wadata suke, sai sakaci da rashin kula har ciwo ya zama gyambo”.

Likita ya furzar da iskar takaici daga bakinsa yace. “yanzu gashi Mamanku ciwon ya zamar mata diabetic foot, ya zama (diabetic neuropathy), gashi har ya koma (diabetic angiopathy), bata shan magani ba’a kulawa da ka’ida wajen cin abincin ta yadda mukayi umarni.

Zahra ta firgita ta kuma tsorata da abinda likitan Mama ya ce a karshe, gashi yanata kiran wayar Zayyan a kashe, a wauta irin tata, sai ta yi shiru ba ta gayawa kowa cikinsu ga abinda likita yace a karshe a kan kafar Mama ba. Hankali tashe ta ce masa za su koma su yi shawara da sauran ‘yan uwanta, su dawo washegari kuma zata nemo Yaya Baffa su zo tare.
Jiki na rawa Zahra tazo ta samu mijinta Ubaid a reception tace sun gama su wuce, don ta gama tsorata, sai kawai ta wuce da Mama gidanta, bata gayawa kowa cikin ‘yan uwanta me likitan ya ce ba, don zancen ma ba za ta iya furta shi ga kowa cikin ‘yan uwanta ba, wato sauran ‘ya’yan Mama ba. Hatta mijinta Ubaid bata gaya masa ba.

Kwanan Mama bakwai agidan Zahra kafa ta soma fidda ruwa mai doyi, Zahra na kuka tace ma Ubaid su canza wa Mama asibiti su maida ta ABUTH, shine asibitin da mahaifinsu yayarda dashi, can suke zuwa kuma acan ake duba su dukkansu tun Baba Bello na raye.
Don Zahra na ganin tamkar Doctor karya yakeyi, kawai bai san me yake yi ba.
Don haka ko da Zubaina ta kira ta don jin halin da Mama ke ciki, ce mata kawai ta yi ta canza mata asibiti, ita tafi gane ABUTH, suna hanyar Zaria yanzu haka, ita da Ubaid da Mama din.
Zubaina ta sunsuni wani abu mara dadi cikin sautin Zahra da ke rawa, don haka ta nemi iznin mijinta Malam, washegari ta kamo hanyar Zaria, uwa ba wasa bace ko da kuwa ta buzuzu ce.
Ta kuma kira ta gaya wa Zubaidah, Zaitoon da Hatoon duk su taho ABUTH su kula da mama su kyale Baffa, tunda ya daina kunna waya, sallamamme, jefaffe.
Kai Baffa ya sha zagi ba adadi gun Zubainah yau, data kira wayarsa karo na sau ba adadi ana cewa switch off.

Amma Zubaidah ta kasa kyale Zayyan din, don hakika ta damu da son sanin halin da yake ciki. Ita Zubainah abun ya hadu da fushi da takeyi dashi mai tsanani, da ya biyewa rigimar Mama ya aikata abinda duk cikinsu babu mai iya gyarawa.
Zubaidah ma ta gwada kiran wayarsa sau ba adadi ana ce mata a kashe, sai ta kira Azeezah.

Azeezah na hakimce a dankareren falonta, ta dora kafa daya kan daya tana cin gugguru da corn flakes din kellogs tana wata irin tauna rakakau-rakakau irin ta wanda duniya ta yiwa dadi, taci ado har ta gaji haka Shaheed dinta dukkansu (looking good), ta amsa wayar Yayan mijin nata, suka gaisa rimi-rimi, ta tambaye ta Shaheed, a lokacin ya dameta da rigima sai ta kanga mata kukansa a wayar. Yaya Zubaida ta ce,
“Ayya aminin Baba sarkin rikici, a shafa min kanshi. Babanshi fa? Ko yana kusa?”
Azeezah, wadda duk guilt ya cika ta, da dauke Mama da su Janet suka gaya mata an zo an yi, ta tabbata ‘ya’yan Mama sun raina kulawar da ta ke bata shi ya sa suka dauke uwarsu. Hatta a muryar Zubaidah taji canji. Ba wai ta damu ba ne, hasalima, ta fi nono fari a wajenta don tana ganin zaman Mama gidan ma ya taimaka wajen hana Zayyan nutsuwa a kan iyalinsa, for quite a long time.
A ganinta ba damuwar sakin da ya aikata ba ne kadai yake damunsa ba, a’ah, ciwon Mama da yawan korafinta na dare daban na safe daban shima yana damunsa.
Ta tuno abinda ya faru ranar da Zahra ta dauke Mama. Da daddare Zayyan ya shigo daukan wasu abubuwa nashi zai maida guest house, da sauri ta bi bayansa har masterbedroom dinsa, yana kokarin suncewa zai shiga wanka, tana gaya masa wai Zahra tazo ta dauke Mama, ko uffan bai ce ba yasa kai ya wuce cikin toilet.

Azeezah bata daddara ba, ta sake biyo shi a baya, ta ce,
“Baby, ba ka ji me na ce ba ne? wadannan marasa kunyar kannen naka sarakan iyawa da kankanba, sun zo sun tafi da Mama ko tsinkenta ba su bari ba, Allah ya gani na fita hakkin Mamanku, don ba abin da ban ce su Janet su yi mata……”.

A fusace Zayyan ya juyo kamar mayunwacin zaki ya dallawa Azeeza harara, da idanunsa da suka kada suka yi jajawur, ya ce.
“Saboda ba uwarki ba ce ko? Na gode Azeezah… !
Kuma ina tabbatar miki wadannan dirka-dirkan kabilun masu najasa da ki ka tara min a gida ki san na yi da su. Yau duk su tattara su bar min gidana, ki kula da Shaheed din da kanki. Ba zan lamunci yaro ya tashi a hannun arna ba”.
Azeezah ta kalle shi shekeke! Tana tabe baki cike da raini, sannan ta zumburo baki gaba, ta ce, “Sannunka amma, na ga karfin halinka na korar min ‘yan raino.
Kai dai kawai kace za ka yi huce kan-dami a kaina, to ai ba ni na kar zomon ba balle a bani ratayarsa.
Ba ni na sa ka saki matarka ba, Maman ce, don haka in ba ka huce a kanta ba, kada ka sake ka huce a kaina.

Kuma dai ka san daga inda ka dauko ni ba gidan rainon yara bane…, nafi karfin aikin gida da raino, a’ah, gidan hutu ne zallah ka dauko ni, don haka dole in rayu da mai raino da mai aikin gida.
In ka ga dama Malam ka mayar da hannun agogo baya, wato ka dawo da matarka, ai ba’a kaina take zaune ba, ko na samu Baby ya dawomin daidai nima, na san duk tafiyarta ce ta maida kai masifaffe”.
Zayyan bai kara tanka mata ba, ya shige yayi wanka zuciyarsa na tafarfasa…
Da gaskiyar Azeezah ba ita ta kar zomon ba, kuma inama zai iya dawo da hannun agogo baya!
Tun tafiyar Safiyyah sai yau yaji wani irin bakin ciki kamar zai fashe a makogaronsa. Koda ya fito wankan jallabiyyarsa kawai ya zura yasa bed shoe ya fito.
Ya tadda su Janet a dakinsu suna gugar kayan Shaheed da suka wanke suna gulmar Azeezah cikin broken english dinsu wai ta fiya gantali ga mijinta kyakkyawa mai naira son kowa amma bata kula dashi bayan tasa an saki kishiyarta mai kirki da yawan alheri, bai nuna yaji me suke fadi ba sai ganinsa suka yi a kansu, ya ce,

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *