⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 10: Chapter 10

A washegari ya kamo hanyar Dandume cikin matsanancin farin cikin addu’ar da Mama tayi masa. Ga na jin dadin saukar Sophie lafiya, ga na farin cikin yau zai dauki danshi da Sophie a duniya.

A gidan mahaifinsa ya fara sauka wato a Rafindadi, don Sabah ta gaya masa suna asibiti CS akayi mata, ta rokeshi kada yazo asibitin, za’a ce itace ta fada masa, ya bari sai an gaya masa officially, duk dokinsa da zumudi haka ya hakura ya kwana a Rafindadi don bazai so Sabah ta samu matsala da ‘yar uwarta a kansa ba, duk da wajibi ne a gaya masa amma sunyi delaying gaya masa din, kuma Sabah bata so Safiyyah tasan ita ta fara fada masa.

Sai data kwana uku da haihuwa sannan aka sallame su suka koma gida. Kannenta Sabah da Rayyah duk suna tare da ita, da nasu cikin na haihuwa yau ko gobe.

Sai lokacin aka buga ma Zayyan aka gaya masa Safiyyah ta sauka baby girl suna gida, uwar da ‘yar duk lafiya, Sabah itace ke ta buga waya tana fadawa ‘yan uwa saukar Sophie, tuni har Anti Dije ta samu labari, Assafe kuwa tuni ta yi landing da dirka-dirkan jakunkunanta tun kwana uku kafin tiyatar.

Koda Zayyan ya iso gidan daga Rafindadi basu dade da dawowa gida daga asibiti ba, amma yau ma ba ta canza zani ba. Wato iya inda Malam ya saba saukarsa nan ya sauke shi a falonsa, duk dokinsa na ganin Sophie, Malam Bai bada fuska ba, sai kawai yayi waya cikin gida ya ce a kawo Baby ga babanta yazo ya ganta.

Abun yayima Zayyan ciwo matuka, da Malam bai ce Safiyyah ta kawo Baby da kanta ba, shikuwa Malam bai ga dalili ba, Rayha ce ta zo da Baby din nannade cikin blue cotton shawul ta kawo masa ita.

Kada kaso kaga wani irin riko na soyayyar uba da Zayyan yayi ma Babyn a cikin kirjinsa, idanunsa fal kwallar kaunar Babyn data kasa zubowa, domin ji yayi tamkar Sophie ya rungume, ga kamshin turaren jikin Sophie na (RUUS COLLECTION) wato ‘attraction humra’ din jikin Safiyyah da ya dade da sani manne a jikin yarinyar.

Zayyan ya kurama Babynsu shi da Sophie ido, bai san lokacin da ya fara tasbihi ga Ubangiji gwanin tsara halitta yadda yake so, ganin yadda Babyn ta debo komai na Mamansa Barumiya Haj. Fatu Rafindadi.

Wani karin abun mamakin hatta yatsunta na kafa da hannu duk kamar Mama Fatu tayi khaki ta ajiye nata.

Malam ya dan kalleshi yace, “Zayyan ka yi mata khutbah mana da sunan da ka bata”.
Amma Zayyan tsabar jin nauyin Malam, kansa ya sadda kasa ya ce da Malam,
“Malam ai tuni na baku wannan damar. Asa mata suna mai albarka”. Malam ya ce, “To alhamdu lillah, zan yi mata khuduba da suna AYATULLAH!”.

“Aayah! Aaayah!” Zayyan ya maimaita a hankali. Kada dai Malam zambo yake musu???

Da kyar Zayyan ya iya bada Ayaah ga Rayha, bayan awa guda tana hannunsa, data soma kuka da mutsu-mutsun neman nono.
Kwana biyar da haihuwar Aayah, Zubaina da Zubaidah suka iso gidan Malam Usman da kayan barkar dangin uba rankatakaf, duk wani luxury na uwa da ‘ya sai da Zayyan ya yi, bangles wannan na zinare mai goma sha biyu sirara Zayyan ya sako ma Sophie.

Ga jewelery set biyu na gold. Duk (push gift) dinta ne.

Su Assafe sun karbi kayan sun aje a gefe, don already Yaya Sheikh ya saya musu komai na amfanin su, Assafe ta kawo tun kafin haihuwar. Karbar da suka samu daga dangin Safiyyah ba yabo ba fallasa, ta dai fi babu za’a ce kawai.
Aka kawo musu Baby, bayan Rayha ta basu ruwan sha, da suka karbi Aayah, Zubaidah da Zubaina baki suka bude, har suna hada baki wajen cewa.
“Masha Allah, yau ga photocopy din Haj. Mama, wannan ai kece carboncopy din Maman Rafindadi”.

Wannan magana dasu Zubaina suka fada ta shiga kunnen Safiyyah. Don ita bata ma taba tsayawa ta kalli fuskar Aayah sosai ba balle ta tantance kamanninta.
Tun daga lokacin Safiyyah ta soma wani hali akan ‘yarta wanda Ammi ce kadai ta lura da shi; ta dawo bata son shayar da Aayah, musamman da daddare da babu idon kowa a kansu, bata manna yarinyar a jikinta sam. Gefe sosai take kaita. Haka yarinyar za ta yi ta callara kuka, Safiyyah naji taki ko motsin daukanta balle kuma ta bata nono, saboda kwatakwata ba ta son kallon fuskar Aayah.
Da farko da ko daukanta Sophie bata yi, sai aka dauka ko kunya ce irin ta Dan fari, amma sai Ammi ta lura ko ‘eye-contact’ na uwa da Da Sophie bata yi da Babynta.

Wani irin abu take ji a ranta, a duk lokacin da ta ga fuskar Aayah da kyawawan idanunta masu kama da na Mama Fatu.

Daga Ammi sai Anti Dije ne suka lura da wannan condition din da Sophie ta ke ciki bayan haihuwarta, har Anti Dije ta soma tunanin ko (postnatal depression) ne ya samu Safiyyah.

Ta kai ta kawo a washegarin zuwan Zayyan ganin Aayah, kememe Safiyyah taki shayar da yarinyar, bayan an dawo mata da ita daga jikin Zayyan din, domin nan take ta shaqi kamshin ultraviolet (paco rabanne) a jikin Aayah.

A daren ranar sai da suka kai ruwa rana ita da Ammi da Anti Dije a kan ta ki ta shayar da yarinyar, yarinyar tayi kuka har ta gaji tana hadiyar rai da tsotson hannunta.
Anti Dije tausayi ya isheta, ta dubi Safiyyah cikin bacin rai tace “tunda abin naki haka ne ba imani a ciki, to zan danneki in fiddo nonon in baiwa yarinya abincinta”.
Safiyyah ta soma kuka kawai kamar ranta zai fita, kuma ta ki karbar Aayah din, wadda Ammi ke ta jijjigawa saboda kukan yunwa.
Karshe Assafe ta sa aka sayo madarar jarirai mai kyau, a take ta hada ta a sabuwar feeding bottle ta soma baiwa Baby.
Ta roki Ammi da Anti Dije kan su kyale Safiyyah da maganar bada nono zuwa gobe da safe.

Amma a daren ranar Ammi ta kasa hakurin wayewar garin, taje ta gayama Malam duk halin da suke ciki da Safiyyah akan shayar da Baby Aayah.

Malam hankalinsa ya tashi sosai, da safe ya zo da kansa har dakin Ammi ya tadda Safiyya an cika mata plate da gasasshen nama mai ruwa-ruwa, ya ji albasa da yajin daddawa tana ci hankalinta a kwance. Tunda an kyaleta da maganar bada nono.

Malam ya zauna a sanyaye, Safiyyah ta bude baki tana gaida mahaifinta. Malam ya katse ta ta hanyar daga mata hannu yace.
“Ki rike gaisuwarki Nana Safiyyah bana bukata, tunda butulci kike so ki yi wa Ubangijinki!”.
Hankalin Safiyyah ya yi mugun tashi da kalaman Malam, ta soma kukan nata da baya yi mata wahala yanzu.
Malam ya ce, “Ki rufe min baki, in ba butulci za kiyi ma Allah ba me ki ke nufi da azabtar da baiwar Allah?
Allah ya baki diyar bayan fidda rai da samunta, amma saboda mahaifinta ya sake ki bakwa tare, mahaifiyarsa bata sonki, shine za ki saka wa Allah da haka?
Ina mai jan hankalinki da cewa laifin wani ba ya shafar wani, balle kankanuwar halittar Ubangiji da ba ta da hakkin kowa, in kikayi wasa hakkinta sai ya kaiki wuta, tsakanin iyaye da ‘ya’ya ma akwai hisabi
Ki koyawa zuciyarki afuwa da rangwame in an saba miki, kullaci ko ramuwar gayya ba halin musulmin kwarai bane, in dai an bata maka ka nuna fushin ka shikenan ba sai kayi ramuwar gayya ba”.
Malam ya mike ya barta a gurin tana cigaba da kukanta, ta rasa abinda ke mata dadi.

Ranar Asabar ana saura kwana biyu suna Zayyan ya zo, domin ya bada abun bukatar radin suna, duk da Malam yace masa a’ah, shi ba’a taron suna a gidansa bayan yanka rago da radawa jariri suna. A can dai falon Malam inda ya saba zama in yazo yau ma ya zauna, Malam yana kofar gida da dalibansa sabida zafi ya hanasu zaman falon karatun sai sukayi shimfidar tabarma a kofar gida, Zayyan mutuniyarsa Sabah ya kira a waya, ya ce “kanwata ina falon soron Malam, na zo ganin lovely Aayah”. Sabah tace,
“toh Baban Ayah, right away gamunan nida ita, yanzu na gama shiryata”.

Tun ranar da aka yi haihuwar nan da Zayyan ke sintirin zuwa ganin Aayah, bashi Dandume bashi Abuja, amma ko inuwar Safiyyah bai taba gani ba.

Malam jiya sai da ya ce masa ya rage zuwa, yace dashi, hanya ba kyau ga nisa, ka yi limiting zuwa mana ko zuwa sati-sati ne? Amma ba kullum kana hanya haka kamar tsuntsu a sama ba”.
Shikuma Zayyan murmushi kawai yayi, a ransa yace “Malam bazaka gane ba”.
Sabah ta kawo masa Aayah cikin shawul mai daraja, da kayan baby masu kalar green yau a jikinta, baby Aayah ta yi matukar kyau kamar ka sace ka gudu. Yau Zayyan ya yi rantsuwa a ransa bai barin gidan Malam Usman sai ya ga Sophie, ya yi mata barka.
Da yake Sabah abokiyar zancensa ce, har gobe Sabah bata canzawa Zayyan ba, hira sosai suka yi yau ma, ya karbi Baby yayi kissing forehead dinta, yana ce ma Sabah “matas, yau so nake a yi mun alfarma, in shigo cikin gida inyi ma su Ammi barka.”
Yayi kasa da murya sosai yace mata.

“Sabah yaya SOPHIE?”.

Sabah ta ce, “not fine really, Yaya Safiyyah sam ba daidai ta ke ba, tun jiya take kukan fadan da Malam yayi mata akan kin shayar da Baby Aayah, ina na taba jin ka haifi Da da kanka kace kuma bazaka shayar dashi ba sai duniya ta taru akanka?

Kodayake na ji su Anti Dije na fadin ko postnatal depression ta ke yi ko me oho? Saboda kwatakwata fa bata daukan baby fah, breastfeeding dinta sai ance za’a danneta, don rannan kam bayan tafiyarka sai madara Anti Assafe ta hada ta bata”.

Sabah na bayar da labarinta bada wata manufa ba, Zayyan na jin zuciyarsa na tsinkewa, tsigar jikinsa na wani irin tashi saboda bacin rai, matukar tashin hankali Zayyan ya shiga a lokacin, kada Safiyyah ta kashe masa ‘ya akan laifinsa, ya ce da Sabah cikin rikicewa, a lokacin idanunsa sun kada sun rine sunyi ja.
“Sabah, don Allah don darajar Annabi SAW ki taimake ni, ki ce ma Ammi ina so in shigo in yi mata barka”.

Hatta jijiyoyin kansa sai da suka fito rada-rada, a lokacin da yake ma Sabah wannan magiyar. Diyarshi ce kwalli daya da Safiyyah ta haifo masa bayan wasu shekarunsu na soyayya masu yawa, kuma takeso ta kashe da yunwa, saboda laifinsa… tunda an hana ta zubar da cikinta.
Ganin Sabah ta tsaya tana tantamar ta je ne ta fadawa Ammi sakonsa ko a’a? Ya ce, “Sabah, nine fa, Yayanki Zayyan, in baza kiyi min wannan alfarmar ba na rantse zan shiga cikin gidan yau, har dakin da Safiyyah take zaune, ko babu izinin kowa, kiyi wa Allah… ki bar ni in yi wa Sophie barka Sabah… barka kawai zanyi mata, ko godiya ne in samu in yi mata.

Na san ba ni da kalmar bada hakuri… ko idon da zan dubi Safiyyah dashi, amma ina da kalmar godiya a gareta da zan iya bayarwa koda bazata karba ba!”.
A yanayin da yake maganar ya kusa saka Sabah kuka, amma ita kanta Sabah ta san cewa ba ta isa ta je ta ce ma Ammi ko Sophie Zayyan zai shigo musu su gaisa ba, ba tareda Ammi da Sophie sun ci ubanta la’ada waje ba.
Sabah ba ta taba jin tausayin Zayyan tun rabuwarsa da Safiyyah irin yau ba, tun rabuwarshi da Yayarta Safiyyah dukkansu kannenta kowaccensu ta dau fushi dashi amma banda Sabah. Haduwar jininta dana Zayyan bana yanzu bane.
Don haka kawai sai Sabah ta tari aradu da ka, ta share hawayen da suka cika idonta ta juya masa baya, kafin ta ce, “Yaya Zayyan ba sai ka shiga ba, dan dakata kadan, zan turo maka Yaya Safiyyah yanzu, ka ji?”.
Sabah na wucewa cikin gida Zayyan ya kara gyara zaman Baby a jikinsa, ya rungume diyarshi a kirjinsa tsam-tsam yana tofe ta da addu’o’in neman tsari daga dukkan sharri dana bakin mutane, kamar zai maida ita cikinsa don SO!
“Diyar Safiyyah ce… Diya ta ce da Sophie ta haifa mun….”.
Haka zuciyarsa keta raya masa. Yanata hasashen ko yaya kamannin Sophie ya koma yanzu? Bayan hidimar daukar ciki data haihuwa???
Shi ya san Safiyyah mai kyau ce, Allah daya halicceta ya kyautata surarta kamar ita ta zabawa kanta halitta, har abada kuma ya san kyanta bazai dishe a idanunsa ba ko kamanninta su canza masa, koda ‘ya’ya goma ta haifa, sabanin wasu matan da idan sun yi haihuwa daya hatta ‘body strucure’ dinsu canzawa yake yi. Safiyyah nada wata extraordinary halittar jiki, da cikin mata dubu sai an tona kafin a samu irin ta. Tanada suffa da zubin halittar matan kasar Ethiopia.

Cikin kowanne yanayi dai zai riski Safiyyah walau na tsufa kona kuruciya mai saka canzawar halitta, bazai taba daina marmarin ganin Safiyyah ba, da dokin ganinta tsaye a gabansa. Balle yau da dokin da yake ji na ganin nata na dabam ne, har wani irin ignition yake ji a ilahirin jikinsa.

Sabah ta shigo cikin gida, dakin Ammi ta nufa kai tsaye gabanta na dar-dar, inda ta tadda Safiyyah ita kadai a dakin tana shiryawa cikin daya daga kayan fitar suna da Anti Assafe ta dinko mata daga Lagos.

Wani lafiyayyen Voile ne kalar (lemon green) da ratsin ruwan goron fulawa jikinsa Safiyya ke sakawa, wanda aka yiwa dinkin wata hadaddiyar riga (fitted gown), dinkin ya sha adon farin stones sai walwali yake yi duk kankanin motsin data yi.

A wannan lokacin Safiyyah ta rame, jikinta ya zama danye shataf, irin danyantakar jego, fatar jikinta ta kara yin fresh, tayi haske kamar an mata wankan inji don santsin da fatarta ta kara, bata shafa komai a fuskarta ba sai jar powder (Elizabeth Arden) da (lip gloss) mai taushi. Safiyyah ta fito a Nana Safiyyarta ta baya, kamar bata taba aure ba. Ta gyagije daga gajiyar daukar ciki data ‘postnatal depression’ din daya sameta bayan haihuwa.

Sabah ta dake abunta tace ma Sophie cikin ko in kula daga bakin kofa,

“Yaya Safiyyah kije Malam yana kira a falon karatunsa”.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *