⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 12: Chapter 12

Ikko ikon Allah gari mai tarin albarkatun rayuwa tushen arzikin kasar Najeriya. Tun zuwansu Lagos Sophie ta soma adabo da kowacce irin damuwa. Kwanciyar hankali ya soma maye gurbi, nutsuwarta ta soma dawowa.
To bata komai sai shayar da diyarta, sai wanka, barci da ibada.
Assafe na kula dasu tamkar yadda za ta kula da kanwar da suka fito ciki daya data yi haihuwar fari. In dai ta dawo daga aiki to rainon Aayah da komai nata shikenan ya koma hannunta.
Wani abu da Sheikh da Assafe suka lura da shi yanzu shi ne, Safiyyah ta zama mace mai zafin zuciya, abu kadan sai ya fusata ta, ta daina sanyin halin nan nata, ba ta daukar kowanne irin raini daga kowa.
Mama ta canza dabi’un Safiyyah na sanyi da salama, ta dawo hutsuwarta ta asali, wanda shigarta gidan aure da soyayyar Zayyan ne ya rankwafar dashi, kada dai ka bari abin da ranta ba ya so ya hada ku yanzu.
Tana son Aayah a kasan ranta, amma ta kasa nuna soyayyar nan a zahiri a idon kowa, idan ta tuno wahalar da ta sha kafin ta samu haihuwarta da gorin Mama dana ‘ya’yanta dana Azeezah sai ta ji dama ba ta haifeta din ba.
Assafe kullum tana kokarin nuna mata ta saka ‘yarta a ranta, ta kaunace ta kamar kowacce uwa, ba ta da laifi ko daya cikin duk abinda su Mama da Zayyan kansa suka aikata mata. She is innocent.
Ta kan bata misali da kanta, tace “Safiyyah ni ko guda dayar babu! Zamu iya karar da duk abinda muka mallaka nida Sheikh don mu samu kamar Aayah. Watakila kuma ni har na mutu bazan haifa ba. Ga Shiekh yaki yarda ya kara aure. Duk da ance “La taqnadu min Rahmatullah amma kinsan ni tawa matsalar ba irin taki bace, babbar matsala ce da in ba wani ikon Allah ba bani da rabo a haihuwa. Ki godewa Allah ki ja ‘yarki jikinki”.

Sophie ta daina daukar duk abin da zuciyarta ba ta amince da shi ba, wato Mama da Azeezah sun kangarar da zuciyarta.

Yanzu da ta ke rayuwa a tsakanin Yaya Sheikh da Assafe, Sophie kullum tana ganin yadda Assafe ke tarairayar Sheikh, da yadda suke soyayya mai shiga rai ko a gabanta ne, idan dare ya yi kuwa tana ganin irin dressing din jan hankali da Assafe ke ma Sheikh na musamman, ta yi ta yawo ta gabansa ba abinda ya dame ta da Sophie koda tana wajen, har ila yau, tana ganin yadda Assafe ke kula da mijinta ta kowanne fanni, girki, kwalliya mai jan hankali, kalaman Assafe kawai ga Sheikh sautin su da yanayin fitarsu dabam ne, masu tausasawa namiji ne su sanyaya zuciyarsa komai zafinsa, haka Assafe take a koyaushe tamkar ba indiya, ga kyakkyawar mu’amala tsakaninta da Sheikh da kowa nashi, bata daukar raini daga dangin miji sannan bazata yarda wani cikinsu ya takata ba, amma tana basu hakkinsu na ‘yan uwan mijinta data rataya a kanta a matsayinta na matar Babban Yayansu.
Assafe bata da mugunta ko muguwar kissa, da zuciya daya take zaune da Sheikh da kowa nashi, wai don tana auren dan uwansu bata katangeshi daga yi musu kowanne irin alkhairi. Wannan kuma training din da Sheikh yayimata ne don tun haduwarsu yake gaya mata baisan iyayensa ba da suka haifeshi sai Ammi da Malam, in zata so shi ta so shi tare dasu da ‘yan uwansa.
Daga zamanta dasu Safiyyah ta fahimci cewa ita ashe a gidan Zayyan ba rayuwa ta ke mai kyau a gidan nata mijin ba.
Kuma ta fahimci cewa ita da kanta ta yi contributing ga wasu matsalolin nata. Rayuwar Sheikh da Assafe gabadaya opposite irin wadda take yi da Zayyan ne da danginsa, duk da cewa su su Zubaidah sune da matsala ba ita ba, amma tsakaninta da Zayyan akwai manya-manyan contributing factors daga gareta da suka sa nan da nan Azeezah ta janye shi kamar karamin yaro da aka baiwa alawa a hannu.

Yau Yaya Sheikh ya kawo mata offer na daukarta aikin lecturing a Unilag.
Sun ba ta Assistant Lecturer a tsangayar ta watau (Architecture). Kasancewar Sophie da (second class upper) ta fita daga ABU.
Watannin Aayah hudu kenan da haihuwa ta yi bul-bul da ita gwanin sha’awa tana zama tana kokarin rarrafe, Safiyyah ta fara zuwa aiki ta barta a gida, da yake Assafe ta daukar mata mai raino babbar mace ‘yar kabilar Itsekiri, amma musulma, Maman Ada.

Fara aikin Safiyyah a jami’ar Lagos, ya sa ta yin cudanya da mutane daban-daban, kabilu daban-daban, musamman lakcarori matasa mata ‘yan uwanta wayayyu masu zurfin ilimin zamani da na iya mu’amala, ta fahimci yin kawance da kawaye nagari ashe ba laifi bane karuwa ce a kyautata halayya da zamantakewar dan adam, wannan ya taimaka wa Sophie wajen sanin darajar kanta, da kimarta da martabar kanta, ta yadda a halin yanzu a ko’ina Safiyyah ta samu kanta ba za ta iya kara daukar raini ko wulakanci ba daga kowa, dangin miji marassa mutunci ko uwar miji marar lissafi mai son kai irin Mama Fatu.
Aka ce zama da madaukin kanwa mai kawo farin kai, kullum Safiyyah kara wayewa ta ke da zama da Assafe da kawayenta na wajen aiki, hatta yanayin dressing din Safiyyah ya canza kansa yanzu ba tareda ita kanta ta sani ba, saboda in ta yi dressing Assafe ta ga ba yi mata daidai ba, ko abinda bai mata kyau ba bata shiru, sai ta ce, “Safiyyah gyara nan, cire wannan, saka wannan, canza wannan da wancan, sannan ta hana ta wuni cikin jilbaabs da hijabs a cikin gida, ta ce sai in fita za ta yi cikin maza tana iya sawa, amma ace har cikin mata ‘yan uwanta cikin Hijabhie take wuni kamar matar liman?
Assafe na mamakin ko wace irin rayuwa mijin Sophie ya yi da ita a kudundune? Saboda ta lura kidahumancinta na da yawa, har ta ke cewa Sheikh rannan.

“Ka rage jin haushin Zayyan Hubby, lallai hakika Zayyan ya so Safiyyah, so ba dan kadan ba, daya iya zama da ita cikin yanayinta da personality dinta, I wonder ta yadda yake samun gamsuwa ma daga gareta ko yadda take bashi hadin kai cikin dadin rai. Wata irin mai duhun kai ce kamar bata yi jami’a ba. I’m sorry Sheikh, idan bera da sata… to daddawa ma da wari, kawai ba’a tona bane kuma Zayyan bai buda baki ya fadi yana shan wahala da nature din Safiyyah ba”.
Ta gaya masa cewa, Sophie ko turaruka ba su dame ta ba, in dai za ta yi wanka ta sa ‘roll on’ shi ke nan, wai don kada a ji tashin kamshi a jikinta babu kyau, ta ce, Sophie ko lotion din da ya dace da fatar jikinta ba ta sani ba. Banda Nivea data mayar farillanta bata shafa dan mai mai kyau wanda zai goge fatar jikinta tayi taushi. Ba a maganar cin abinda zai inganta ni’imar jikinta wurin mijinta.Don ta taba gaya mata ita bata yarda da magungunan karin ni’ima ba suna sawa miji ya fitineka.
Ba karamin karatu Assafe ke yi a kan personality din Safiyyah ba, tana kuma labarta ma Sheikh irin bambance-bambancen da ke tsakanin kanwarsa da yake jin haushin an sako masa akan kishiya da sauran matan da suka amsa sunan mata.
Ta ce “taka kanwar muna mata ce (Sorry Hubby), tuni mace ‘yar zamani za ta kwace wa Sophie miji, kaddara ce ta tadda hali. Amma goriba ce a hannun kuturu Azeezah ta kwace.
Shi kansa Yaya Sheikh yana shan mamakin wasu abubuwan da Assafe ta ce dabi’un Sophie ne, watakila don shi namiji ne shi ya sa baisan komai a kidahumancin Safifi ba. Gabadaya upbringing dinta na tashi gaban tsofaffi ne.
Sai yanzu da Assafe ke gaya masa ya dan dinga shakka. Tana kuma ba shi yakinin cewa Zayyan ba karamin so ya yi wa Safiyyah ba. Abu ne mai sauki kwace goruba a hannun kuturu.

Don haka Yaya Sheikh ya budewa Assafe bakin aljihu ya ce ta yi ma Safifi duk wata sayayya da ta ke bukata na amfanin mata. Ya roketa ta zame wa Sophie ‘coach’ ta yadda nan gaba in ta sake aure ba za a sake sako masa ita ba a dalilin kishiya.
Abinda yace din nan ya bai ma Assafe dariya sosai, ta ce,
“Ai ba sai ka roka ba Yayan Safifi, zan hada Safifi ne da Hajiya AISHA LAME wadda handle dinta na instagram shine (lame.ng) kankat kenan wajen abubuwan gyaran jikin mata na zamani.
Zan gayawa Lame tazo ta kawomin duk abubuwan gyaran jikin mata da zasu sa min Sophie ta koma yar gaye. Yadda nan gaba ta wuce raini a gun kowanne namiji har yayi tunanin maka mata kishiya sabida wani dalili ba Zayyan kadai ba. Duk da cewa shi karin aure mukaddari ne, amma a gurin wasu mazan matan su na gida ne suke ingiza su, wanda na tabbata Zayyan na cikin su.

Tun daga wannan lokacin Anti Assafe ta fi jan Sophie a jikinta fiye da baya, ta zame mata ‘coach’ a kan rayuwar aure na zamani, ta kuma sa ta fara karatun littatafai na soyayya na manyan marubuta masu nagarta, tun Sophie na jin kunyar wasu maganganun da Assafe ke mata har ta yarda zallar gaskiya take gaya mata, sai ga Sophie na ta kilewa a hankali, kwanyarta da kofofin da ta rufe wa kanta na son komawa rayuwar aure suna budewa da kansu, har sha’awa jaruman littattafan data ke karantawa suke bata, irinsu Rahinan Nahuce, Aalimahn Mu’az, Fahiman Uwais Shagari, su Rahanen Himu da sauransu. Ga su Maimoon ta littafin Maman Maama dake buga soyayya da mijinta Sultan kamar a cinye juna, littafan Batool Mamman dana tsofaffin marubuta iri iri. A ire-iren haka Sophie ta fahimci cewa ita ba ta iya soyayya ba, (she is not romantic at all) a gidan aurenta, ita kidahuma ce. Typical matar bahaushe.
Zayyan na son soyayya da rayuwar aure ta wayewa, Zayyan wayayyen mutum ne mai son jin dadin rayuwa ne, tana kwatanta dabi’unsa yanzu na son romantic life dana namijin duniya Ibraheem-Heemu, da mijin Raheenah wato Habibu-Nahuce, yana da son romantic sexual life morethan everything in his life, amma da matar da yake so kadai, yana son shi da matarsa su zamo babu shinge na kunya kowacce iri komai kankantarta a tsakaninsu, wato su zama sirrin juna, komai nasu ya koma mallakin na juna.
Assafe ba ta tsaya a nan ba, kusan duk dinkunan Sophie sai da ta canza mata su, don dinkin Sophie ko awo babu haka take aikawa a yi mata su anyhow. Ta koyar da ita ware sutturar fita da ta cikin gida da ziyartar saloon na mata akai-akai.

Ta canza mata hair-care products dinta da wadanda Aisha Lame ta kawo, don ita Sophie kam ko dan steaming dinnan na zamani bata yiwa gashin kanta kullum sai kitso kamar diyar barebari. Abubuwa da yawa dai iri-iri na rainon dattijuwa Ammi, data taso dasu da ta je gidan miji ba ta canza ko daya ba, sai kuma aka yi rashin sa’a ta fada hannun dan bokon zamani watau shi Zayyan din cikakken ‘elite’ ne, wanda bai je kasar waje ko sau daya ya rayu ba, amma ya fi wanda aka haifa a Éurope’ son rayuwar soyayya da ta turawa da matarsa.
To ko Safifi ta fahimci wadannan mas’alolin sun taimaka wajen gurbata rayuwar aurenta da Zayyan? Bayan rashin haihuwa da kowa ke kallo daga waje?
A zamanta da Assafe kam ta fahimta, don Assafe bata bata a rufe ba, cikin dabara watarana ta zaunar da ita suka yi magana a kan hakan duk da cewa da farko Sophie ta noke ta ki yarda ta yi hirar Zayyan da kowa, amma Assafe ta ce mata, “ko ki yarda ko kada ki yarda Safiyyah kece ‘contributing factor’ na auren Zayyan da Azeezah, ba rashin haihuwa kawai ba”, Assafe ta fadi haka ne cikin jimami, lokacin da Safiyyah ta ba ta labarin rayuwarta kaf! Da Zayyan kafin zuwan Azeezah gidan Zayyan Bello.
Sophie na jin dadin lecturing din da ta ke yi, ga Aayah na kara wayau kullum. Beautiful & energetic Aayah, mai tsananin kama da ubanta, tunda kuwa kamannin Zayyan duka na Mama ne kuma su Aayah ta debo.
** **

Yau Sophie ta dawo aiki a matukar gajiye, tun daga nesa Aayah ke bangala dariya a hannun Assafe da ta hango ta tana tahowa. Tana faman zillo daga cinyar Assafe tana mika mata hannu, dauke kai ta yi cikin basarwa daga kan Aayah, tana ce ma Assafe.
“Anti na gaji, lallai Malanta ba sauki ba”.
Assafe ta ce, “Zo nan Safiyyah”.
Sophie ta aje hand bag dinta, ta isa ga Assafe, sai Assafe ta miko mata Aayah ta ce, “Feed her first!”. Don ta lura har yanzu Sophie bata daina attitude a kan Aayah ba, saidai ace ta rage. Ta karbeta ta zauna a gefe ba tareda ta ciro mata nonon ba, yarinyar ce keta kici-kicin cirowa da kanta. Nan Assafe ta soma yi mata nasiha a kan cewa ta lura sam ba ta yi wa Aayah wasa irin na Uwa da ‘ya, me ya sa?

Kawai sai Safiyyah ta ji hawaye a idonta, ganin yadda yarinyar ta kwanta lamau a kirjinta tana tsotso, duk da Assafe ta fi kula da ita, amma ita Aaya ta fi son uwarta. Ta kuma gane ta sosai.

Assafe ta ce, “Abin da ki ke yi ko kadan daukar hakki ne, wadanda suka yi miki daban, wadda ki ke hukuntawa daban. Wannan ‘yar kankanwar halittar Allah son kowa kin wanda bai samu ba, na daina bakin misalin cewa ni ga ni har yau ban samu kamarta ba, kuma hakan bai hana mu rayuwar farin ciki ni da mijina ba.
Ki sawa zuciyarki tawakkali, kada ki gamu da fushin Ubangiji a kan Aayah wallahi”.
To daga ranar ne Sophie ta ke kokarin sakewa ta yi wasa da dariya da Aayah, amma duk sanda Aayah ke barci a jikinta sai ta yi mata addu’a,

“Kada Allah ya ba ki halin mai kama da ke Baby!”.
** **

Ranar wata Juma’ah Ammi ta kira Yaya Sheikh ta fada masa cewa Haroun yana neman address din gidansa yana so zai zo Lagos.
Sheikh a kwance yake a doguwar kujera three seater lokacin, amma sai da ya tashi zaune, ya ce da Ammi.
“Me ake yi a Lagos din Ammi da zai zo gidana?”
Ammi ta yi dariya ta ce, “Ridhwan kenan, ka ajiye bazawara a gidan naka ai dole ka soma ganin jelen zawarawa”.
Yaya Sheikh ba don Ammi ba ce, tsaki zai yi, ko kuma yayi zagi, amma ya ce, “Ammi please…, ki cire kanki daga wannan shirmen. Shi Haroun banda hadama me yake nema a rayuwarsa?
Yana zaune da matarsa lafiya ga albarkar yara sun samu har uku, kawai zai nemi gurbata rayuwar gidansa?
Ina murna Safifi ta samu ta fito daga matsalan polygamy din mazan hausawa, don Allah ku barta ta huta, at least ta yaye yarinyar nan, kafin ma ku soma yi mata ture-turen maza”.
Kwarai ya ba Ammi dariya jin yadda yake maganar da matukar fusata, don ma dai Ammi ce, yana kokarin sakaya temper dinsa da ladabi.
Ammi ta ce, “Maida wukar Yayansu, amma ka sani Malam ba zai kyale ta yadda kake so ba ko? Don mu kadai muka san me muke ciki da nacin Zayyan da na iyayensa.
Ko jiya surukinsa aminin mahaifinsa, ya sake zuwa, tare da dattijai abokan marigayi Bello Rafindadi, sun zo baiwa Malam hakuri, a kan dai ya yarda ya maida auren ta koma dakinta.
Satin da ya wuce kuma mahaifiyar tasa ta sake zuwa ita ma, don haka muna cikin matsin lambarsu, Malam kuma ya ce ba zai zama dattijon banza ba, ba zai zuba muku ido kaida ita ta yi ta zama a gidanka ba aure wai tana yawon aikin office ba.
Don haka malam ya ce, in gaya muku watanni biyu ya ba ta ta yanke shawarar abinda ta zaba, ko auren Haroun ko komawa dakinta”.
Har Ammi na cewa, “Ai Haroun ba bakonmu ba ne, ba kuma bakonta ba ne, don haka babu bukatar bata lokaci wajen fahimtar juna tsakaninsu. Na gaya maka Haroun zai zo da iznina kowanne lokaci daga yanzu, su zauna su tattauna su fahimci juna don a yanke abinda ya dace”.

Sun yi wannan maganar shi da Ammi, amma bai gaya wa Sophie ko Assafe sakon Malam ba. Don ransa ya baci sosai, a ganinsa su barta ta yaye ma, sai kawai ya saka sunan Safiyyah cikin mahalarta taron da zai je sati mai zuwa, ya hau yi musu shirin tafiya Islamic Workshop a Accra (Ghana).
A baya ya tsara shi da Assafe kawai zasu tafi Accra na tsayin kwana uku. Amma don ya kaucewa haduwarta da Haroun sai ya saka ta cikin ‘yan tafiya Ghanan.
Yaya Sheikh haka ya ki turawa Ammi address din gidansa, sai a wajen Assafe ta samu ta aikawa Haroun.

Engr. Haroun ya iso Lagos ranar Alhamis ana I gobe za su wuce Accra. Maigadi ya zo ya ce ma Yaya Sheikh yana da bako daga Dandume. Ko da ya fito ya ga Haroun ne wani siririn tsaki ya saki a cikin cikinsa, ya ce, “Ammi Ho! Ammi rigima”. Don dai ya san ita ta san yadda ta yi ta nemo masa adireshin ya biyo Safiyyah Lagos din.
Ya sa aka kai Haroun dakin baki, ya yi masa sauka ta karramawa. Ya dawo cikin gida yana ta mita wa Assafe, haka kawai wai Ammi ta turo ma Sophie bazawari, kamar an ce a kanta Safifi ta ke zaune.
Assafe tayi masa kallon nutsuwa taga yadda ransa ya baci, sai abun ya bata mamaki ta ce,
“Please Sheikh, what is your problem with that?”

Sheikh ya bude baki da ido yana kallon matarsa Assafe, a ransa yace “kaji min mata da wata fassara ta daban, kafin ya wara hannuwa cikin tabe baki yana fadin.
“wane irin zance ne kike yi wannan? To amsarki itace; Babu! Actually, nothing… banida wata matsala dashi ko don zata yi aure, kawai bana son zancen sake auren Safifi ya gitta nan kusa, a barta ta huta mana, mazan nan na kasar Hausa duka babu korai balle a kwankwasa a tantance na gari a cikinsu.
Shi fa Haroun rigima ce kawai, amma me ya rasa? Lafiya yake zaune da matarsa. Neman karin auren na mene ne kuma? Ni bana son zalama wallahi”.
Assafe ta yi murmushi ta ce, “Kuma dai na ga ba za’a bar maka kanwar taka ka jika ka shanye ba, dole in ta gama hutawar ko bajima koba dade ta koma karkashin wani ba kai ba, be it Haroun ko waninsa, ko tsohon mijinta”.

Bayan dawowarsu daga Accra, a hankali cikin wayo da dabara sai da Assafe ta san yadda ta yi ta canzawa Sophie duka kayan wardrobe dinta, gabadaya sutturunta na fita Assafe ta mayar mata dasu tsadaddun “Hanayan Abayas” da “Yasmine Abayas” irin nata, wadanda yawancinsu Assafe ke yo order dinsu daga Qatar tana sayarwa ‘yan uwanta na maiduguri a kan sari. Don har katon shagon sayar da abayas Assafe ta bude recently a Lagos, wanda daga makerarsu a Qatar da Oman, kai tsaye a boutique dinta suke sauka.

Daga Ghana kai tsaye Katsina suka wuce, suka sauka a Dandume.

Sati biyu kenan da tafiyar auta Rayha karatu Arkansas, don haka gidan yanzu ya koma daga Malam sai Amminsa da almajiran Malam da basa rabo da gidan, da baki masu zuwa ganin Malam kullum, gidansu Safiyyah gida ne mai albarka, wannan ya zo, wannan ya tafi, musamman in ranar bada karatu ce falon soro na gidan kan zama ba masaka tsinke da maza magidanta.

Ammi ta cika da farin cikin zuwansu, ta rasa ina ta ka saka ina taka aje da babbar kawarta, Aayah. Sai faman goyonta take tana ayyukanta da Aayah a bayanta. Tayi kewarsu sosai tunda suka tafi basu zo Dandume koda yawo ba sai yau.

Daga ita har Aayah sun yi bul-bul, sun yi jazur da su, Ammi tayi ta yabawa Assafe tace kokarin nata ne. A daren Safiyyah da Ammi kwana sukayi hira, hirar data ki yiwa Sophie dadi don Ammi ta zama mai kamfen ga Haroun yanzu, magana daya biyu sai ta ce Haroun kaza, mutumin kirkine da ya iya rikon mace, namiji ne tsayayye a gidansa, kuma dai kinga nice uwarsa baki ba matsalar uwar miji.

Safiyyah sai data yi dariya tace “Ammi ni ai yanzu ba Safiyyar da bace, bana tsoron uwar miji in dai irin Mama ce saidai mu zuba. In kuma ta kirki ce zata ga biyayya tamkar in kwanta mata, wannan hutsuwar Nana Safiyyahnki ce Ammi ba SOPHIE bace”.

Kwana biyu sukayi zasu koma Lagos, wato asabar da Lahadi, sabida gobe Litinin Safiyyah nada class da dalibanta, to da za su koma Lagos washegari ne Malam ya zaunar da su a gabansa bakidaya itada Yaya Sheikh.

Malam ya fara da saka musu albarka, ya yabawa Sheikh akan rikon zumuncinsa, sannan ya godewa matarsa Assafe, yace namiji yana zama na kwarai ne idan ya samu macen kwarai, Sheikh ya samu rabin addininsa wato mace tagari, wadda ta ke taya shi kula da zumunci wanda yake dolensa.

A karshe Malam ya ce.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *