Chapter 14: Chapter 14
Da ya gaji da zama a falon Sheikh ya mike zai tafi, yama rasa wa zai baiwa yarinyar ya kai ta cikin gida.
Haka ya fito da ita a hannunsa. Sai da ya fito kofar falon ne ya ga mai rainon nata tsaye a bakin kofa tana jiran ya fito ya bata Aayah.
Ya mika mata ita, har zuwa lokacin Aayah barci take yi, ya kuma baiwa Maman Ada kyautar kudin da shima baisan adadinsu ba, ya ce,
“Na gode Madam, please take care of Aayah!”.
Maman Ada da farin ciki ta amshe kudi, tace,
“I will, Alaji!”.
Zayyan bai yi fushi ba, da ya koma masaukinsa sai da yayiwa Yaya Sheikh godiya ta whatsApp a lambarsa, da ya karba a gurin Sabah, ya ce,
“yana masa godiya da hidima da dawainiyarsa ga Aayah, idan Sheikh ya huce zai dawo su fahimci juna zuwa jibi”.
Tafiyarsa da kwana daya Mama da team dinta suma suka zo gidan Yaya Sheikh, su kam ko ganinsu Sheikh bai yarda yayi ba, kuma Sophie ma bata gidan, ya ce a ce musu bayanan, bayan kuma yana nan din, har sai da Assafe ta ji tausayin Mama ganin yadda suka girbi hanya all the way dada Katsina har Lagos da kafarta daya da kyar, amma Sheikh kememe ya ki yarda ya gansu, don yace shi bashi da abin ce masu, bakin alkalami ya bushe.
Safifi ita tayi zabinta bashi yayi mata ba. Don haka ita Assafe ta karbe su sosai, ta kuma kawo musu Aayah.
Mama na mika hannu don ta amshi Aayah, yarinyar ta zabura ta callara kuka mai gigitarwa kamar Mama ta dala mata wuta, ta makalkale a jikin Assafe cikin firgita.
Wannan al’amari ya tsorata Mama. Ba Mama kadai ba, dukkansu ‘ya’yanta saida jikinsu yayi sanyi, don kememe Aayah ta ki yarda Mama ta dauke ta.
Don haka Mama da kukanta ta bar gidan Dr. Ridhwan Dandume, don gani tayi tamkar an labartawa Aayah komai a kanta.
Gidan Baba Murtala suka sauka a Lagos din. Don haka can suka kara komawa, suka labarta masa komai da ya faru yau a gidan Yayan Safiyyah cewa yaki yarda ya gansu, Mama na kuka akan jikarta ‘yar Safiyyah da Baffa na gudunta.
Baba Murtala duk fushinsa da Mama yau ya ji tausayinta, ganin tana kuka shabe-shabe, ya ce gobe za su je gidan Sheikh din tare dashi, ko baza a dawo ma da Zayyan Safiyyah ba, to a kawo karshen wannan diramar da ta ki ci ta ki cinyewa, wato su yafewa Mama laifinta, don ta samu peace of mind ko lafiyarta ta inganta.
* * *
Dr. Ridhwan (Yaya Sheikh) yana zaune a ofis dinsa da safe yana duba fuskar wayarsa, sakon Zayyan Bello ya shigo masa.
Sai da Sheikh ya ji wani dan guntun tausayi ya tsirga a ransa, amma haka ya cije yana gayawa kansa Safifi ta dandani fiye da abinda Zayyan Bello yake dandana yanzu, lokacin da ya kara aurensa na son zuciya da rashin adalcin mahaifiyarsa, da lokacin da ya sako ta ba da laifinta ba, ya jaza mata rayuwar zawarci da duk diya mace ke gudu.
Wata zuciyar na tunasar da Sheikh cewa, Zayyan biyayya ya yi ga umarnin mahaifiyarsa, sannan karin aure da ya yi ba haram ya aikata ba, amma shi a karan kansa daban yake da sauran maza, watakila don ya rayu cikin larabawa ne, yana kallon mata da daraja da kima ba yadda sauran mazan hausawa suka dauke su tamkar rigar sakawa ba, na zasu iya aura su saki a duk sanda suka so, su kuma maida su a sanda suke so, balle ace a kan favourite dinsa Safifi.
Shi ya san kansa, akan mutuncin Safifi baya uzuri, zai yi komai don nemowa Safifi lasting solution, da farin ciki a rayuwarta ta gaba. Amma hakika ya fara tausayawa Zayyan wannan karon.
A take ya kawar da tausayin daga ransa, ta hanyar gayawa kansa shi ma kansa abun tausayi ne a soyayya, ba Zayyan da ya dade da actualizing tashi soyayyar ba, ya kuma tankwabar da ita a kan radin kansa.
Washegari again, Assafe ta sanar da shi yana da baki, da ya tambaya ko su waye aka ce Alhaji Murtala da Mama Fatu, salati yayi irinna shiga uku, shi kam wannan naci na ‘yan Rafindadi ya soma isarsa. Ko shine madaurin auren Safifi sai haka. Kafin ya je inda suke, dakin Sophie ya fara zuwa a matukar fusace. A kanta yakeso ya sauke komai.
A yadda Yaya Sheikh ya shigo mata daki ba ko sallama tana kokarin daura kallabi a kanta, ya sa ta cewa,
“Subhanallahi! Yaya Sheikh lafiya?”
Don bai taba shigo mata daki babu sallama ba gashi Assafe bata nan.
Wani irin kallo Sheikh ya yi mata wanda saida Safiyyah ta ji a jikinta, domin kallo ne da bai taba yi mata irinsa ba, wanda ya ruda Safiyyah, duk ta dabarbarce.
Ya ce, “Safifi!”.
Ta amsa da,
“Na’am Yaya Sheikh”.
Ya ce, “Yau zuwa na yi ki gaya min tsakaninki da Allah kina son komawa auren Zayyan ne?”
Wani irin duka a kirji tambayar Yaya Sheikh tayi mata. Kai tsaye ta hau girgiza kai murya na rawa, ta ce,
“A’ah, ai na riga na yanke hukunci na”.
Sheikh ya yi mata wani wofantaccen kallo, ya ce,
“Ko? Na auren almajirin Babanki ko?”
Safiyyah ta kalleshi a razane, yace Yes, na auren almajirin gidanku.
Amma duk da hakan da saninki Zayyan yake takuramin shi da ahalinsa?
Baki kuka hada keda shi akan ku uzzura min ko? Har in gaji in mayar masa da ke ko yaya abin yake?”
A yanayin da Sheikh yake magana cike da rigima ya kara tsorata Sophie, ya kidima ta, ta soma rantsuwa a kan bata da contact da Zayyan tun barinta gidansa. Bata taba wata personal magana dashi ba.
Ba karamin namijin kokari Sheikh ya yi ba wajen sarrafa kansa, da dawo da nutsuwarsa. Yana gayawa kansa ya bar Safifi…. ta ci gaba da zama kanwarsa, ya bar Safifi… saboda Assafe, ya bar Safifi saboda Allah da halaccin Assafe, in ya so ya ci gaba da zame mata garkuwa a komai kuma babban Yaya makwafin uba, bango abin jingina…
Ba don haka ba da ya kawo karshen wannan taqaddamar ta hanyar zama alternative!.
Jikin Shiekh da hannayensa har wani kyarma suke yi, ya dauki Aayah da ke gefe tana kuka ganin Ummanta Safifi ma kuka ta ke yi.
Ya ce, “Safifi I’m sorry for how I react, I’m just tired da nacin Zayyan da iyayensa ne.
Tambayata ta karshe da zan miki kafin in je in ga Alhaji Murtala yau ita ce, kina son HAROUN?”
Wannan wata tambaya ce da ta zo ma Safiyyah a bazata, don haka ta kasa nemo amsarta tashin farko. Ta shiga laluben amsar a ciki da wajen kwakwalwarta amma ta rasa.
Sheikh ya tsayar da idanunsa cikin nata yana jijjiga Aayah a kafadunsa, ya ce, “Amsarki, ita za ta bani ilmin abinda zan je in gayawa Alhaji Murtala na karshe, domin mutum ne mai daraja a idon kowa, ba zan yi wasa da hankalinsa ba. Kina son Haroun?”
Safiyyah ta dauke idonta daga kallon Sheikh saboda abinda take hangowa cikin idanunsa da suka rikide yau mai girma ne ya kuma firgitata (tsagwaron kishi!), kai kamar ba idanun Yaya Sheikh ba, sun juye bakidaya zuwa abinda sam ba ta son gasgatawa cewa shine ke cinsa a zucci, don haka Safiyyah ta yi maza tace da karfi,
“YES! Capital Yes, ya fi min Zayyan sau dubu, (da wannan abun data ke kokarin fahimta daga Yaya Sheikh gara tace tana son Haroun), tace “kuma zan zauna da shi saboda Allah, zan masa biyayya iyakar iyawata!”.
Sai kawai Sheikh ya juya bayan ya mika mata Aayah, yayi mata wani kallo, da yasa Sophie kusan sakin fitsari a wandonta daga tsaye, sannan ya juya ya fita daga dakinta, zuwa dakin da aka sauki Mama da Baba Murtala.
In takaice miki a haka na hadu da dangina na uwa da uba a Geidam. Dukkansu talakawa ne da ke cikin rufin asirin Allah. Babu jimawa kanin mahaifin nawa ya bani auren diyarsa Ambashyr, wadda ta kammala NCE a lokacin.
Safiyyah na girma cikin soyayyarki wadda Allah bai taba bani ikon furta miki ba. Ko in ce na girma da ‘inferiority complex’ akan soyayyarki, kullum ina jin cewa ban isa ba, ban kai na aure ki ba, a matsayin ki na diyar Malam.
Allah shi ne shaida ban taba son wani abu a duniya sama da Safiyyah ba. Kuma ban taba rasa wani abu ya yi affecting dina psychologically and socially kamar auren Safiyyah ba. Rana daya na samu labarin an bada aurenki wa wani Zayyan.
Na yi jinyar zuciyata, na yi Allah wadai da kwauron bakina, don ni tun a lokacin tsammani nake akwai soyayya tsakaninki da Yayanki Ridhwan (Sheikh) shi za’a baiwa aurenki, in na yi la’akari da irin kusancin dake tsakaninku.
Ashe ban sani ba, kallon kitse nake yiwa rogo, domin sai bayan da Zayyan yayi min kwaf daya ne na gane cewa babu komai tsakaninki da Sheikh sai zumunci, tunda ga shi an tsallake shi an baiwa bare ke.
Na auri Ambashyr bayan na farfado daga naushin da aurenki yayi min. na kuma sha baqar wahala kafin na iya sakata a raina. Biyayyarta da hankalinta da yawan ibadarta sun taimaka mata, wajen samar mata muhalli a zuciyata, bayan na ‘yan uwantakar data hadamu.
Haihuwarmu ta farko nasa ma ‘yar sunanki, wato Safiyyah, wadda kullum na kalla ko na kira ta gabana sai na tuno ki, na tuno son da na yi miki, kuma tana tuna min ke kwarai da irin kuruciyarki don kusan halinku daya na hutsanci, Safiyyah ga turjiya ga rigima, ga rashin barin ko ta kwana. Mai bi mata ita ce Tasnim, sai autarsu Aisha.
Ambashyr tana da labarinki fiye da yadda kike zato Safiyyah, ta san cewa a rashinki na aure ta, kuma muka zauna lafiya cikin soyayya da mutunta juna. Akwai abin da Ambashyr ta taka wanda ya sa zamanmu ya dore, kuma nake mutuntata shi ne, “hakuri” da duk wani weakness dina ko kuskurena.
Ta san komai a kanki, kuma ko da na gaya mata batun mutuwar aurenki itace ta karfafe ni da in cire ‘inferiority complex’ din da na jima da sakawa zuciyata a kanki, wannan karon in gwada sa’ata, ko da ta hanyar Ammi ne.
Don haka ina da kyakkyawan fatan cewa Ambashyr bazata baki matsala a zama dani ba Safiyyah, duk da cewa ba gari daya zan ajiye ku ba”.
A nan Engnr. Haroun ya dubi Safiyyah da dan murmushi, ya ce, “Ina fatan yanzu kin gama sanin Haroun ciki da bai Safiyyah? Ina rokon alfarmar ki ci gaba da rikon Aayah a gidana, har girmanta”.
Har Haroun ya gama bata labarinsa, Safiyyah idonta na bisa wayarta, tana kuma saurarenshi, amma zuciyarta bata tare dashi….
Ta tafi ga wani bakon tunani na daban mai neman fasa mata zuciya da kwanya.
Tunaninta ya tafi ga yadda nan gaba zata iya hada jiki da sunan auratayya dashi, ko waninsa, alhalin bata taba tunanin saka wani da namiji a ranta da jikinta da irin hakan ba, kai bata taba mafarkin physical contact da Haroun ko waninsa ba, bata taba sha’awar wani Da namiji a duniya ba ZAYYAN BELLO ba…!!!
Tunanin da ya sa ta ambatar sunan Allah a fili kuma da karfi,
“Yaa Sattaru sutrukal jameel!”.
Wanda hakan yasa shi dan dakatawa da magana, domin ya fahimci Safiyyah dai tana jinsa ne, amma ruhinta baya tare da shi, she is lost… a cikin wani tunanin daban.
Ganin hakan ya sa ya ce mata zai wuce masaukinsa, ya kwanta ya huta, ya lura shes occupied da wani tunanin daban, gobe kafin ya wuce Yobe gun Baffansa zai shigo su yi sallama.
* ** **
ZAYYAN
Ya kai gwauro ya kai mari a tsakiyar kayataccen falonsa, tun bayan gama wayarsu da Mama ya kasa zama haka ya kasa tsayuwa. Ya kuma kulle kofar shigowa falonsa don ma kada Azeezah tazo ta dame shi.
Wadda a safiyar ranar wani al’amari mafi muni ya afku tsakaninsu, mai tsananin da ya kai shi ga tunanin daukar matakin kaurace mata, ko sakinta, a bar ta batun maganar cin arzikin Baba Murtala haka, in ya cigaba da yi mata uzuri da Baba Murtala tana abinda taga dama watarana za’a haifi nadama mara amfani.
Sai dai kuma anya zai iya kara sakin mace a rayuwarsa? Koda da wasa ne koda kuskure? Duba da abinda sakin mace ya janyo masa a rayuwarsa har yau kuma ya kasa gyara kuskuren farko?
Kwanaki uku baya kadan Azeezah tace masa za ta asibiti. Daga baya ta kira shi ta ce masa an bata bed rest na kwana biyu.
Haka nan zuciyarsa taki kwanciya da wannan kwana biyun da ta ce zata yi a asibiti, don baiga alamun wani ciwo a tareda ita ba, don haka ya bari ta tafi da kamar rabin awa kafin ya dau mota yabi bayansu, asibitin da yasan Azeezah na zuwa wanda private ne mai tsada can ya bisu.
Yana shiga harabar asibitin da Azumi ya fara cin karo a reception, tana ta fama da rigimar Shaheed dake ta kukan ta kai shi gun Daddy.
Ai kuwa yana hango shi ya yi wata zilliya daga hannun Azumi, saura kadan ya fado kasa, dole ta sauke shi a kasa ya taka da gudu suka yi zo mu gama da Babansa, ya dauke shi a kafadunsa.
Azumi ta tsugunna tana gaida shi, bai amsa ba ya tambaye ta ko ina Maman Shaheed? Sai ta yi masa nuni da ofishin likitan data shiga. Bai san me ya sa ya ji gabansa ya hau faduwa ba, lokacin da ya doshi ofishin Dr. Kenny.
Ofisan dake kula da fice da shigen marasa lafiya a ofishin likitan kuma ya mike ya tafi don kai file din Azeezah record room.
Kawai Zayyan ya samu kansa dasa kai ofishin, tare da bude kofar cikin nutsuwa, wadda aka bari slightly ajar, amma bai shigar da gangar jikinsa ba.
Ji yayi ana gardandami tsakanin likita da Azeezah. Likitan na cewa, sai da yardar mijinki zan juya miki mahaifa, ita kuma tana cewa, ai in dai shi ne ba zai taba yarda ba. Ita kuma ta riga ta tsorata da sake haihuwa dashi, kada ta kara haifo Da mai lalurar Cerebral Palsy.
Ta ce, “Likita ka fadi ko me kake so kawai, zan biya ka, na yi maka alkawari sai abinda ka yanka min, in dai ka yarda za ka yi min aikin nan a yau”.
Likitan da ke kallonta kamar tsohon maye, ya ce, “Ajiyaaaa! Bazaka iya biyana ba, domin bana bukatar kudinki ni”.
Ta ce, “To me ka ke so?”
Likitan wanda ba bahaushe ba ne, amma ya dage hausa yake mata, babu kunya ba tsoron Allah duk da kasancewarsa ba dan addininta ba, ya ce, “Ajiyaaa, I only want to have you here…”
Ya nuna mata gadon dora marassa lafiya, sannan ya yi kasa da murya, ya ce, “Ka bani kanka, make love with me even once (kiyi soyayya dani ko sau daya ne), zan baki mamaki Ajiyaa, you are extraordinarily beautiful, and looking youngishly ravishig…”.
Azeezah ta dabarbarce don duk iskancinta rabonta da bin wani namiji da sunan iskanci tun bayan aurenta.
Likitan ya taso yana takawa zuwa gabanta, amma ko motsi ta kasa sai jikinta da ya fara rawa. Har likitan ya iso gabanta tana zaune a kujerar da ke fuskartar teburinsa, wata zuciyar na ce mata ta yarda kawai, yaushe rabon Zayyan ya gamsar da ita? In ma ta samu da roko da zubda kai da naci ya kula ta, to ko ya tara da ita kamar akan dole yake yi. Ai tun bayan tafiyar matarsa even his sexual behaviour ya canza, in ma ta dan samu din kenan.
Shaidan ya ci gaba da bugawa Azeezah gangarsa, yana kawata mata halittar shaidanin Arnen likitan, tana kamanta shi da Zayyan dinta. Ko kafar Zayyan bazai kama ba amma ai shi ya jawo mata. A karshe zuciyarta ta amince mata a kan ta yarda kawai, komai ta fanjama-fanjam, ko don ta sharewa ranta kewar Zayyan, ta kuma huce haushin da Zayyan ke guma mata akan abinda yake hakkinta ne yanzu, amma sai ta zubda ajinta, ta ja kanta a kasa… ta rokeshi da kuka da hawaye, shima kuma ko tayi hakan ba lallai ta samu yadda take so daga gareshi ba.
Azeezah ta san cewa tana da halittar nymphomania, amma bata san ta yi mata tsananin da har za ta iya cin amanar aure ba sai yau. Duk iskancinta ya tsaya a Zayyan, tun rabuwarta da tsohon saurayinta na makaranta a kasar Cyprus, wanda shi ya fara lalatata, don haka ta shiga rudani tsakanin amincewa ne ko a’a? A karshe ta yanke shawarar amincewar akan bata da zabi.
Azeezah na shirin baima likita amsa cikin fadawa tarkon shaidan a wannan dan takaitaccen lokacin Zayyan ya bankado kofar ofishin da wani irin karfi da kuzari.
Likita na kokarin kama hannun Azeezah dake zaune gabansa cikin kujera tana makyarkyata na tsoro da rashin sabo, Zayyan ya furta da karfi,
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un!”.
Wanda ya sa Azeezah juyowa zuwa bakin kofa cikin kaduwa, tsoro da firgici. Sai ga Zayyan a bayansu, wanda bata san tsayin lokacin da ya dauka tsaye a wurin ba. A wannan lokacin Zayyan ba abinda ya tuna sai ayar Ubangiji (SWA) da ta ke cewa,
“Wancananka wadanda idan musiba ta same su suke ambaton, innalillahi wa’inna ilaihi raji’un….”, don haka ita kadai ya maimaita, har sau uku, idonsa cikin na Azeezah.
Wadda tsabar kaduwar data yi da ganinsa a lokacin yasa sai kawai ta mike tsaye zumbur, ta kurma ihu na babu gaira babu dalili, tsabar firgicin data shiga da tashin hankali zaisa ta tarawa kanta mutane.
Da sassarfa Zayyan ya juya ya bar ofishin likitan, absent-minded, Azeezah ta biyo shi da gudu babu ko takalmi a kafarta. Shi kuma likitan ya yi tsamo-tsamo a inda yake kamar tsumma a cikin mai. Ba abin da yake ji sai career dinsa.
Don da alama mijinta ne kuma babban mutum ne. Amma ba wai nadamar abinda ya so ya aikata ba, don ba yau ya fara neman matan aure ba.
Ko kafin ta fito harabar asibitin, domin ta cimmasa, tuni ya yi mugun ‘reverse’ ya karci kasa da motarsa ‘Brabus’ ya bar cikin gate din asibitin, ko Shaheed tunda ya baiwa Azumi shi a reception bai kara waiwaya ba.
To fa shi ne tunda ya shigo falonsa ya kulle kansa, bai kara fita ba, sai faman safah da marwah, ya kasa tsaye, ya kasa zaune, ya kasa ma ko wanne irin tunani, ya rasa ko wanne irin hukunci da zai yankewa zaman aurensa da Azeezah.
Maganar ya saki Azeezah ita tafi komai zauna masa a rai, saboda ko ya ci gaba da zama da ita wannan abun da ya ji ya kuma gani, ba zai kara bashi kwanciyar hankali a cikin aurenta ba.
A wannan karon, zai janye tsakaninsa da Baba Murtala ne ya ceci mutuncinsa, addininsa, tsarkin zuri’arsa da darajar aurensa.
Maganar ya kyale wannan deadly kuskuren na Azeezah saboda Baba Murtala ma ba ta taso ba. Magana ce ta tsakaninsa da mutuncinsa da kuma amanar shikansa Baba Murtala din da take hannunsa.
Baba Murtala bai rufeshi ba, kuma har ga Allah bashi da hakkinsa, tunda tun tashin farko ya gaya masa Azeezah bata kwarai bace a cikin ‘ya’yansa amma ya biyewa KAWAR ZUCIYARsa yace yaji ya gani don yana son yaji dadin rayuwarsa da wata macen bayan tasa.
Yana cikin wannan mawuyacin halin, sai ga wayar Baba Murtala din, kamar ba zai dauka ba sai dai ya lallashi zuciyarsa ya fi karfinta sannan ya dauka, duk da baya cikin mood na iya yin magana.
Kamar Baba Murala ya san hakan, bai nemi gaisuwarsa ko jin maganarsa ba, ya ce,



