Chapter 16: Chapter 16
“Ka saurara min Habiby, zaka balla ni”.
A hankali Zayyan ya sake ta, ya koma kan daya kujerar ya zauna dafe da kansa idanunsa a lumshe, cikin wani irin dadi da ya mamaye ransa, ashe still yana nan a “Habiby?”
Yaushe rabonsa da jin wannan sunan mai dimbin tarihi daga bakin Sophie? Watakila tun wayewar garin Azeezah a gidansa.
Wannan kadai ya ishe shi farin ciki yau, koda kuwa Sophie bata kara kula shi da kowacce kalma ba, a kasalance suka dubi juna zuciya a ragaice, idanun kowannensu yayi jajawur yayi wuri-wuri da kishirwar abin da kewar kasancewa da dan uwansa, kada na Zayyan da suka kankance suka kada jawur su ji labarin irin halin da ya samu kansa bazai fassaru ba…. don jin sa yake yau tamkar saurayinsa dan makaranta wanda bai taba kusantar matarsa Stammerer ba. Ya yarda gangar jikinsa da ruhinsa sun kaunaci Safiyyah, sun kuma so ta ne tun a sanda bai san dadin soyayya ba sai tata, amma yafi kowa sanin dadin sh’awa da biyan sha’awar, a tare da Safiyyah kuwa pure love kadai ya sani mai mwanciya a ruhi, har yazo lokacin da yasan ni’imar aure a jikinta ya san komai.
Safiyya mikewa ta yi da zummar gudu cikin gida tana wani irin jefa masa harara, shi kam ya kasa dauke ido akan ta kona dakika sai kallonta yake yana lumshe ido yana kara budewa, with so much affection in his loving eyes. Safiyyah ta lura da hakan, tana so ta basar da komai, sai ta turo baki gaba tana fadin.
“Ni dai da Malam ya turo ni dakin zaurensa, cewa yayi magana za mu yi ta fahimta, ba cewa yayi inzo a lalube masa ‘ya ba”.
Zayyan ya langabar da kai yana ma Sophie wani kallo mai shiga rai, ya ce,
“Then Malam yana so ne in gaya miki cewa, dalilina na kara auren Azeezah shi ne wannan halin naki, you are not romantic at all Sophie!”.
Zaro ido tayi shima ya zaro mata nasa, ai ba finshi girman kwayar ido tayi ba, daga yau ya daina shakkar idanun nan masu kunyar tsiya, daga inda yake zaune yace.
“Yes, Capital YES! Ni nake son rayuwar jin dadi da ke, amma ke ko oho, sai son ‘ya’ya kamar kaza, alhalin kin ki tsayawa ma ki bi hanyar samo ‘ya’yan yadda ya kamata”.
Ya karasa fadi da murya mai ban tausayi da tausayawa kai, ba karamar kunya da nauyi hade da mamaki maganganun Zayyan na yau suke bata ba, sun jefata cikin dogon nazari da tariyo scenarios din rayuwar aurensu. Zayyan bai lura da ya jefa Sophie cikin wani hali na kaka ni kayin nadama da dogon nazari ba, ya cigaba da cewa.
“Sophie… ina son soyayyah, amma na gane daga gare ki kadai nake sonta….
Sophie ina son romance, ina son love, ina son sex.
Tunda kara aurena da wadda ta iya duk wadannan bai saka mun contentment na zuciya da gangar jiki a kansu ba, ban samu satisfaction din da ya dauke hankalina daga soyayyarkiba bana jin akwai abinda zai sa mun gamsuwa da samunsu, in ba taki soyayyar, kulawar da fahimtar kika fara bani ba.
Yau bari in cirewa Hijabhie hijabinta daga idanuna……. In yiwa kunyar nan tata tsirara…..
Bari yau in yi magana da Hijabhie ba tareda Hijabi ba, tunda haka kike so, ke baki san hannunka mai sanda ba. Sai an yi miki baro-baro da gwari-gwari dallah dallah.
Na farko ni kawai so nake ki fi “tantabara” iya sumba da iya soyayya….. ki gani in zan kara kallon wasu hauragiyar matan a waje har wani abu nasu ya tayar min da hakali. Sophie kinada duk abinda nake so a mace shiyasa na zaboki cikin dubu na kawo Babana, amma kin kasa bani kulawarki a shimfidata”.
Maganar nan da ya yi ta saka Safiyyah jin matsananciyar kunya ta lullubeta, nadama da dana sani suka baibayeta, nauyin gazawarta da gane rashin gaskiyarta muraran suk taru suka haifar mata da sanyin jiki.
Zancen Anti Assafe ya tabbata kenan, Assafe bata karya don ta faranta maka ko don ganin tsinin idanunka.
Da gaske kenan ita ta yi contributing wa manyan matsalolinta ta bakin Assafe, tunda ita a karan kanta ta san bata ko taba yi masa tayin soyayya ba, koda ‘yar sumbar soyayya don radin kanta ba bata taba yi masa ba, shi yake bin abun da roko da dabara don ta amince dashi ko kadan ne, wai ita kunya take ji ba wai bata so bane tunda a gidansu ba’a yi, sauda dama duk magiyar tasa da rokon nasa sai taga dama, ba kuma ya samun yadda yake so haka yake maleji.
Habiby fa yayi hakuri ashe ba ita kadai tayi hakuri dashi ba, itace ummul haba’isin komai na matsalolinta dashi, ba abinda Assafe bata gaya mata kuru-kuru ba, amma da yake fadi yanzu da bakinsa tafi yarda da lapses dinta, tafi jin mutuwar jiki da daukar laifinta sannan da aniyar dammarar gyarawa koda ba duka ba, amma at least zata yi dukkan kokarinta da taimakon Assafe wajen gyara zaman aurenta da ganin cewa ta farantawa Habibynta iyakar iyawarta a koda yaushe suke tare.
Yau Zayyan ya fito ma Sophie ne a namijinsa sak! Marar ta ido, ya zama ‘open’ sosai da ita, irin yadda bai taba zama a bude da ita a baya ba….
Sabida dauka da yake yi komai Sophie take yi ‘nature’’ dinta ne. Kuma a tunaninsa nature din mutum baya canzawa.
A yanzun ma ya bude baki ya gaya mata duka likes and dislikes dinsa ne ba tare da kunya ba, ba kuma don yana da hope ko tunanin zata koma masa yadda yake so ba, duk da yayi noticing komai nata ya canza yanzu tun zuwanta Lagos kamar an wanke mata kwakwalwa, ya san da wuya wai gurguwa da auren nesa Sophie ta canza dabi’arta amma hatta yanayin maganarta yanzu sauya, bashi da dogon burin cewa Sophie zata koma romantic and sexy yadda yake sonta.
Amma a kalla ya cire “communication gap” yau, da ya samu muhalli a tsakaninsu a kan hakan, wata da watanni, shekara da shekaru.
Itama kuma Safiyyah hakan ya sa jikinta yayi sanyi lakwas, lokacin da ya gaya mata irin halin da yake kasancewa a ciki idan ta ki yi masa abinda yake so. Ko ya nemi auratayya da ita taki yarda da gangan wai ya fiya matsa mata.
Ya gaya mata mujazar sha’awarsa da auren Azeezah inda ta samo asali, ta samo asali ne ana I gobe zaiyi wata tafiya Lagos, data yi masa wano mugun horon rowar kanta, yace ya tafi ne cikin wani hali na kishirwar mace, don haka yana ganin Azeezah zuciyarsa ta kawata masa komai na halittarta, ta kuma gaya masa cewa in ya aure ta zai kawo karshen wannan matsalar tasu, tunda ita bata son kula dashi a shimfidarsa.”.
Zayyan ya yi creating wani irin ‘openness’ yau a tsakaninsa da Safiyyah, magana yake ba kunya ba sakayawa, na irin yadda yake hakuri da halinta, yake shan wuya, da yadda yake so su gyara rayuwarsu, ya ce hijabin nan nata in ba cikin taron maza za ta je ba, sam baya maraba da shi a cikin falo da master-bedroom dinsa.
Ya so shi ne a campus din ABU kadai, wanda waje ne na zirga zirga da hadakar maza da mata, amma bai yi zaton har cikin gidansa zata dinga yi masa ado dashi ba.
Kai yau Zayyan ya kusan sumar da Safiyyah don kunyar da yake bata, da barin zancen da yake yi mata, wani ma birona bai iya rubutawa, har gorin kayan barcin da in ya sayo mata don ta saka masa ya gani yaji dadi bata sakawa saidai ma ya nemesu ya rasa a gidansa.
Tun bayan azahar har magriba suna tare a dakin Malam yama manta a Dandume yake cikin surkukin Katsina, kuma bai zo da niyyar kwana ba.
Sallar la’asar ma a cikin dakin ya yi abarsa da yake akwai toilet a falon.
Tun malam na jiransa ya fito su je jam’in la’asar kamar yadda suka samu na azahar tare har ya je ya yi sallarsa ya dawo.
Da magriba ta kawo jiki ne bai ga Safiyyah ba bai ga Zayyan ba, ya yi kwafa ya ce da Ammi.
“Hafsatu kin gani ko? Kin ga abinda nake gaya miki da kin dage da rabasu kece da shan kunya, kuma bakinki zata yi ta gani har abada muddin ace ta shiga gidan Harou, don in ta dade a gidan Haroun to sati daya ne zai dawo miki da ita a bazawara ta biyu. Kina ji kina gani za’a zo a lalata zumunci, da amincin da ke tsakaninki da dan naki, ita kuma a fara kirga mata aure ko ace ta yaudare shi.
Na rabaki da daukar wa masoya fushi ki yafa, daukar dumar magaji da nishi ne”.
Ammi dai baki ya mutu don bata sa a ranta Safiyyah zata yi minti talatin tareda Zayyan ba zata dawo cikin gida. Gasu can sun wuni sur tare.
Malam da kansa ya isa har bakin kofar dakin soron, ya ce,
“Zayyan… Zayyan…”
Safiyyah ta zabura ta tashi daga jikin Zayyan daya cukuikuiyeta cikin jikinsa yana zuba mata labari mai taushi cikin sanyi da taushin murya har gyangyadi ke son daukarta, basu san lokacin magriba ya yi ba.
Ya amsa kiran Malam, yana mikewa tsaye shi ma cikin kasala. Turaren jikin Sophie na ‘Davidoff’ duk ya koma yabi jikinsa, haka itama Ultraviolet dinsa ya dawo jikinta saboda cukuikuiyar da Zayyan ya wuni yi mata.
Malam ya ce,
“A dinga kula da lokacin sallah”.
Ya ce, “To Malam”.
Malam ya kara cewa, “Halan kwana ka zo mana ne yau? Don bai kyautu ka kama hanyar Abuja kuma cikin daren nan ba Zayyan, ha’an?”.
Kunya kamar yayi yaya, Safiyyah don kunyar idon Malam kamar ta nitse a cikin kasa, Zayyan ya shafa kansa yana sosa keyarsa, ya ce,
“A’a Malam, bazan yi tafiyar dare ba, a gida Rafindadi zan kwana”.
Sai Malam ya ce, “To hanzarta ka yi alwalla mu samu jam’I ka wuce, lallashin ya isa haka ko ita jaririya ce sai haka”.
Dariya Zayyan ya yi ya kada wa Safiyyah ‘yan yatsunsa biyu irin see you soon dinnan, sannan ya bi bayan Malam zuwa masallaci.
Da kunya da nauyin kafa Safiyyah ta iya shiga gida. Ammi dai ko kallonta bata daga ido tayi, sabgoginta take yi cikin gidanta, don har ga Allah ta taho daga rakiyar Zayyan da Safiyyah.
Tana yi musu addu’a Allah ya raya zuri’arsu Ya karo musu wasu masu albarka.
Ta yarda Malam mutum ne mai hangen nesa. Ita dama Haj. Fatu ta ke jiye mata ba Azeezah ba.
Idan kuwa Fatu ba ta dau darasi haka ba to tabbas rabo zai iya kashe duk mai ja da yin Allah.
Ko da ta idar da sallar magriba ma Ammi hannu ta daga sama tace,
“Allah ga Nana Safiyyah ka dora ta a kan kowa da rayuwa ta hadata zama da shi, Ka iyar mata abinda bazata iya ba, ka karo mata ‘ya’ya masu albarka, ka kara soyayyarta a zuciyar mijinta”.
Sai a daren yau Safiyyah ta bude sakon Zayyan na cikin wayarsa, wanda a yanzu ta fahimci shi Haroun ya gani har ya yi deciding janyewa aurenta.
To amma wace kalma ce a ciki wadda Zayyan ya fada da ba gaskiya ba ce a zahirinta tsagwaronta?
Each and every single word which Zayyan mentioned in his long essay is ABSOLUTELY right!
Ta so kwarai ta yi auren ramuwar gayya da huce haushi da Haroun ne kam.
Amma so da kauna guda daya ne a duniya kuma na dan Bello Rafindadi ne.
Allah bazai bari ta cuci Haroun ba, domin bashi da hakkinsu duk su biyun. Haroun mutumin kirki ne mai yawan yakanah. Murmushi Safiyyah ta yi da ta tuna me Zayyan ya gama cewa dazunnan,
“wai kasancewarta ‘non-romantic’ shi ya yi mujazar kara aurensa… yanzu ma tana yarda da kowacce kankanuwar kalmarsa akan hakan. Ai ita shaida ce, ko daga zuwan Azeezah ta gama gane hakan. Mutum ne shi da baya karya, baya kuma son a yi masa karya.
Wannan wani abu ne data ke kara so a halayyarsa ta yanzu, kafin a yi haka shi introvert ne, mai barin magana mai nauyi a zuciyarsa don kada ya ci mata fuska, amma yanzu dole dabi’unta da rabuwarsu ya sa ya magantu, ya koyi zama extrovert a gabanta, da ya fahimci barin kashi a ciki ba zai masa maganin yunwa ba.
Ko zuwa neman wata maslahar again ta wata hanyar irin karin aure.
Abu mafi kyau shi ne ma’aurata su zauna su cire kunya, su nutsu su magantu da juna a kan marital life dinsu, kowacce irin matsala ke tsakaninsu in an fahimci juna bazata gagara warwarewa cikin sauki ba, sometimes karin auren is never a solution, but karin matsaloli, kamar yadda ta kasance tsakaninsa da Azeezah.
Ya tabbata matsalolin da ya fuskanta ga aurenta sun fi jin dadin da ya samu yawa, kuma sun fi matsalolinsa da Sophie na baya da ya kasa jurewa yawa.
Yana kuma kan fuskanta har gobe don babu alamar Azeezah zata shiryu watarana ta nutsu irin yadda iyayenta da shi kansa suke mata addu’a.
Kwanan Zayyan uku a Katsina, kullum daga gidan mahaifinsa yake tahowa Dandume, ya wuni surr, kwana uku a jere kenan yana wannan sintirin ya wuni lallashin Safiyyah, da gaya mata yadda yake fatan su rayu yanzu, daga nan har karshen rayuwarsu ko bata canza ba shi yana sonta haka. Falon Malam ya zama falon lallashi da warware kullin zuciya, duk da Safiyyah bata maida masa martani amma a hankali hakan na sawa tana hucewa gradually.
Tana kuma daukar na dauka, cikin ilmin abinda yake so, da wanda ba ya so, da kaifin bakinsa da iya dadin zancensa da kwarewarsa da gogewarsa a soyayya yake ta wanke mata kwakwalwa a tsanake. Abida baiyi a shekaru goma sha biyar din da suka yi a baya ba shi yake yi cikin kwana uku ya kuma yi nasara mai girma ko bata furta ba.
Ya dokantu, ya matsu, ya kai makura wajen neman yardarta a kan tarewarta, amma Safiyyah ta ki saka rana. Ta ce sai ta shirya, idan kuma ya sake ya sa Malam ya takura mata kan ta koma ba tare da ta shirya ba, shi ma ya san sauran.
Wane mutum! Inji mutuwa. Zayyan da ke lallaba ‘yan kayansa wa ya aikeshi kai kara gun Malam? Haka ya jure yana binta a sannu, amma fa ya tsayar da dukkan harkokinsa ya tare a Katsina, baya Dandume baya Rafindadi. Tunda ko banza yana rage zafi a soron Malam ko yaya ne dai, duk da babu martani daga Safifi, duk a cikin punishments dinda ta tanadar masa, kafin ranar da Allah zai huci zuciyarta gaba daya.
Safiyyah ta saka a ranta zata canza abubuwa da dama idan suka tare, za ta yi wa Zayyan biyayya albarkacin so da kauna, zata bashi ragamar gangar jikinta, soyayyarta da zuciyarta iyakar iyawarta. Amma fa bayan ya gama karbar punishment din da take masa a soron Malam.
A zaryar kwana na biyar da Zayyan ke yi na lallashin Sophie, abun ya fara damun Malam, gashi yayi mata alkawarin ba zai matsa mata tarewa ba, sai sanda ta shirya, amma fa in suka shige falon nan baya kara jinsu ko ganinsu sai ya gaji ya kira Zayyan tafiya sallar magariba.
Cikin tsautsayi yau Malam ya zo wucewa ta zauren Allah ya zuko masa maganganun Zayyan kamar a kunnensa ake yi. Zayyan na cewa.
“To shikenan Sweetheart, habibty Sophie, na ji na yarda ba zan sa Malam ya tursasaki ki koma gidanki ba, sai sanda ki ka gama shiryawa, ko ince kika gama hora ni, amma ko kin san cewa ba na iya barci sam idan na koma Rafindadi?
Wallahi Safiyyah kwana nake ina daddakar ruwan kanwa. Mazantaka ta dawo gabagadi. Ya ki ke so in yi da raina ko wata halakar ki ke son ja min again?
Kin yarda mun yafe wa juna, mun fahimci juna mun kawo karshen matsalolin da suka addabemu koda ba gabadaya ba, toh gashin kumar kuma da ake ta min na kin tarewa a gidana na mene ne?”
Safiyyah ta zumburo baki gaba, ta turo kallabi bisa goshi, irin na macen nan dake cin lokacinta a gun miji, ta ce.
“Ai ba ni na zaunar da kai ba, idan da takura ka koma wajen amaryarka mana Habiby kafin na gama kintsawa, I’m sure ta fi ni missing dinka, ni tsohon hannu!”.
Ya ce, “Koh? To bari mu gani da tsohon hannun da sabon hannun wa ya fi wani missing dina?”
Ya fada mata cikin kankanuwar murya, yana kanne idon sa daya, daga haka Zayyan ya dora mata dukkan nauyinsa har saida Safiyyah ta saki ‘yar siririyar kara, dama kuma akan kilishi suke zaun, da azama Zayyan ya juyota ya hade bakinsa da nata ya soma kissing cikin wani nau’in french kiss! Da bai taba yi mata mai zurfi kamarshi ba.
Malam bai kara jin komai ba sai saukar wahalallen groaning na dukkanninsu…
Ai da tuntube da kuma karo da bango Alaramma ya ja baya, ya fasa fita, da kyar ya kai kansa dakin Ammi, ya ce, “Hafsatu… Hafsatu…!”
Daga cikin daki Ammi ta amsa, ta ce, “Na’am, ga ni nan fitowa Malam”.
“Maza miko min mayafin Nana Safiyyah kin ji ko?”
Ammi ta ce, “Lafiya malam?”
Ya ce, “Ki miko min na ce, bana son tambaya”.
Ammi ta miko wa Malam hijabin sallarta ganin ransa a mugun bace, ya karba ya juya da sassarfa ya isa ga kofar dakin zaurensa, daga bakin kofar dakin ya dakata yana gyaran murya.
Safiyyah ta ture angon nata cikin gigita, shi kuwa Zayyan a nitsensa ya mike yana gyara botiran wuyan rigarsa da links din hannun rigarshi da suka bubbude ya nemo hularsa ‘Tonak’ ya sanya akan goshinsa, babbar rigarshi kuwa dama tun shigowarsa bai san inda ya kaita ba.
Da girmamawa ya amsa wa Malam sai Malam ya karaso dakin ya mika wa Sophie mayafinta ya ce.
“Ke! Tashi maza kibi mijinki ku bar min gidana, daga yau kada na kara ganin waninku a Dandume sai bayan shekara daya!”.
Abinda ya baiwa Zayyan muguwar dariya ganin yadda Sophie ta kwalalo ido waje, Malam kuwa shima ya kwalalo mata nasa sai mazari yake yana shirin rufeta da duka, kafin ta yage baki, hannu a ido, ta soma kukan shagwaba tana cewa malam ita bata gama shiryawa ba, ko kayanta bata ko hada ba.
Malam ya ce, “Kowanne shiri ne ku yi shi a hanya, zan sa Amminku ta tarkato komai naki daga baya a biyo ki da dukkan shirginki.
Na jaddada muku kada ku kara zuwar min gida sai bayan shekara, furfurata bata banza bace sakarkaru marasa ta ido”.
Sophie har da dira kafa a kasa tana kuka, a haka Malam ya kora ta soro, Zayyan ji yake kamar ya taka rawa ya rungume Malam yau. Direwa ya yi a kan gwiwoyinsa gaban Malam Usman zaiyi godiya Malam din yace “ya rike abarsa baya bukata” Zayyan yace “to ai Malam banima da kalmar godiyar da zan iya bayarwar, sai addu’a, Allah ya jikan magabata. Allah kuma ya fidda ni kunyarku ta duniya da lahira.
Ni maraya ne, amma kullum na tuno dumbin karamcinku kai da Babana Murtala. Ina jin cewa ban rasa Baba Bello ba, he’s only out of my sight.
Kun yi min Uba, kun yi min Uwa. Ina dada addu’ar Allah ya ja kwananku”.
Malam ya dago shi tsaye da kansa ya raka su har jikin mota. Zayyan ya budewa Sophie kofar gefensa ta shiga ido fal kuka kamar budurwar da za’a kai daki ranar farko,
Malam da kansa ya rufe mata kofa ya ce mata,
“Kin san albarkata na tare da ke ko Nana? To a yanzu ma na umarce ta da ta biki har zuwa gidanki da sabuwar rayuwarku kinji Nana Safiyyah.
Na hana ramuwar gayyar nan da fushin nan daga yau, inaso a kawo karshensu a cikin motar nan, kin ji ko? Ya isa haka”.
Sophie ta gyada kai tana jin karin hawaye. Hakika za ta yi kewar Malam, her extra-ordinary father! Idan Allah ya yi maka baiwa ta ilimin addini ya baka komai a duniya, zai kuma taimaka maka wajen gina lahira da gina rayuwar iyalinka.
A wani irin tuki na hankali da nutsuwa Zayyan ya ja motar da Safiyyah a gefensa, yana tuki yana dan juyowa yana kallonta duk da ta dukunkune fuska cikin hijabinta, a haka har suka fita daga kauyen Dandume, suka hau kan titin da zai fitar da su daga shiyyar birnin Katsinan Dikko gabadaya.
* * ****



