Chapter 2: Chapter 2
“na baku minti goma duk ku bar min gidana”.
Azeezah dake tahowa a bayansa ba tareda ya sani ba sai ji yayi tace,
“Wallahi sai dai mu bar gidan ni da su gabadaya. Ke Janet, in ni na kawo ku ku zauna, in kuma shi ne ya kawo ku tun daga Lagos sai ku tafi”.
Janet da Bunmi, tuni sun soma hada kayansu don Zayyan ya yi rantsuwa minti goma ya basu, ko ya sa security dogs din Estate su fitar masa da su daga Estate dinsa gabadaya.
Abin ya bawa Azeezah haushi da dariya, ta ce cikin gatsali da tinkaho,
“To sai ka ma diyar Alaramma gorin Estate amma ba ni ba”.
Ta juya ta wuce dakinta cikin tafiyar kasaita tana kada masa bom-bom, sittin-saba’in dari-da-hamsin.
Idan har ya taba nadamar auren Azeezah, to yau ne. Don ya yarda sam bai da kima ko daraja a idanunta. Bata da tarbiyya bata san na gaba da ita ba balle mijin aurenta.
Sannan tarin arzikinsa (is ridiculous) a idanunta, saboda bai kai kuma bai kama kafar na mahaifinta ba, kuma ta san cewa daga shi har danginsa mahaifinta ne silar kafuwarsu a (real estate) don haka ba wata fuffuka da zai mata, ko jan ido a matsayinsa na mijinta, da zai sa ta yi masa biyayya ko ya daga mata hankali. Shi ba komai bane a wurin Azeezah face abokin jin dadin rayuwa, mai dauke mata lalurar ‘yan adamtakarta, don (he doubt) yanzu ma idan Azeezah ba ta bin wata hanyar ta samu abin data saba samu da ya daina bata tun tafiyar Safiyyah, kuma bata damu ba kamar da.
A irin yanayin halittarta da ya sani dai abin da mamaki.
Ya jima yana kallon bayanta a kofar dakinsu Janet da duwaiwakanta da take juyawa cikin izgili kamar suna zaginsa, wadanda a baya ba abinda ke fizgar hakalinsa ya bi bayanta kamar rakumi da akala kamarsu. Amma yau har ta kule a sassanta bai ji komai ba ransa ba sai bacin rai, duk wata sha’awar diya mace ta barshi, tun tafiyar Sophie.
Yana tunaninma Safiyyah da ruhinsa ta tafi gidan iyayenta ta bar gangar jikinsa tareda Azeezah.
Ya jima cikin wannan halin kafin ya kada kai, ya juya zuwa nashi sassan shi ma cikin mutuwar jiki. Don haka tafiyar Sophie ta hargitsa gidan Zayyan gabadaya, ba kuma Safiyyah kadai sakin ya shafa ba, har da Azeezah da komai ya kare a kanta tunda kuwa ta shafi jin dadin zamanta da Zayyan.
** **
Mama na asibiti likitocin ABUTH sun dukufa kan neman mafita akan gyambon kafarta, don haka da Zubaida ta tambaye ta ko ina Zayyan, Azeezah bata bata lokaci ba wajen ce mata ita rabonta da Baban Shaheed tun jiya da da daddare. Yana guest house acan ya kwana. Bai shigo sassanta ba kuma da safe, ita ma ba ta je nasa ba, saboda ya korar mata masu raino.
Ta rasa yadda za ta yi da Shaheed ita kadai. Sai rigima yake mata.
Zubaida ba ta ko saurare ta ba, da kalaman sangartarta, dan yaron kwalli daya bazata iya rarrashinsa da kanta ba, a matsayinta na uwarsa, yanzu kam bata matsalar Azeezah ta ke ba, ta lafiyar uwarsu Mamansu Haj. Fatu take. Don haka Yaya Zubaidah ta ce.
“Ki tashi yanzu ki je ki tadda shi a inda yake, ki fada masa Mama na ABUTH, in a critical condition, ya bar duk abin da yake yi ya yi joining dinmu a can”.
Azeezah ta ce, “Me zai hana ki zo ki same shi da kanki ne? Ni fa ba’a bani order, kowa ya ji da abinda ya dame shi”.
Ta ja dogon tsaki ta kashe wayarta tana mita,
“Kamar a kansu aka fara UWA a duniya, kowannensu bai da zance sai na Mamansu, kowa ya bude baki cikinsu “Mama, Mama, Mama yen-yen-yen! Maman nasu fitinanniya da ita, ta zo kawai ta kashe aure, ta barni da KARMA, daga zuwa jinya da ganin likita ta janyo min bacin rai kala-kala, ta tafi ta barni da karbar bulalar bacin rai”.
* * ****
‘Ya’yan Mama mata duka suna kanta a asibiti ba wadda bata taho ba, in ka cire Zayyan da ba su san a halin da yake ciki ba har yanzu.
Tunda likitan ya ce sai sun zo da babbansu namiji sannan zai tattauna dashi a kan lafiyar kafar Mama, tunda sun ce akwai namiji babba a cikinsu, dole Zubaidah da Zubainah suka kamo hanyar Abuja kawai, don su tadda shi ido-da ido ya gaya musu kome yake nufi na yanke alaqa da kowa.
Arabi direban Mama ne ke jansu a motar mama Toyota Prado, sune tafe basa ko magana da juna fatansu kawai suyi arba da Baffa, tun daga Zaria har suka tadda Guzape suka shiga cikin Sunset Estate.
Ba su iso gidan ba sai yamma lis, kasancewar ba su fito daga Zaria da wuri ba. Suna shiga Sunset Estate Zubaida ta ce.
“Ai ba wata doguwar magana in mun yi sa’ar ganin Zayyan kawai ya shigo motar nan mu juya tare dashi komai dare.
Zubaina na taho daga rakiyar Azeezah, wallahi ba zan kwana a gidan nan ba, yarinya karama ta dinga yi min diban albarka.
Dazun ba ki ji rashin kunyar da ta yarfa min a waya ba, daga tambayarta ko ina Baffa? Yarinyar nan a haife na haifeta”.
Zubainah wani irin kasaitaccen murmushi kawai ta yi, uffan bata ce mata ba, ta ce a ranta,
“Dadina da gobe saurin zuwa…
Yo musamman ga ma’abota bin kawar zuciyarsu”.
Zubaida ta ce, “Kuma kin ga in Mama ta ji sauki sai ki yi mana jagora gidan su Safiyyah, muje dukkanmu mu basu hakuri, ko zasu yarda susa tayi hakuri ta dawo, na tabbata sakin ba mai yawa yayi mata ba, bazai wuce daya ba in dai Baffa ne, na san tana ganin mutuncinki, haka iyayenta, mu kam ai “ta baya ta rago!”.
Ta yi zugudi! Tana kallon Zubaina cikin nadama, kamar itace uwar Safiyyah, idanunta sun cika da kwallar dana sani da aka ce tana keya.
Jin Zubaina bata ce mata komai ba sai ta kara karya wuya tace.
“Damuwa ta a kan sakin Safiyya wallahi Baba Bello! Da yana raye ina za a fara wannan danyen aikin?
Ni dai na san ban so Safiyya ba, a tsayin zamanta da Baffa, ban kuma taba kyautata mu’amala tsakanina da ita ba.
Amma duk da haka ban taba yi mata fatan a saketa ko yi mata fatan zawarci da kuruciyarta ba, don na tabbata Baffa na yi mata so na hakika”.
Zubainah ta yi murmushin takaici, har yanzu dai ba ta ce komai ba. Tana mamakin wai da ma Zubaida ta san sunan Safiyyah na ainahi, fada ne kenan bata yi saboda raini da wulakanci sai dai a ce “diyar Alaramma”, yadda ta gada a bakin Mama Fatu.
Amma yau sai Safiyyah ta ke kiranta. Wato yau Sophie ta zama mutum! Tunda finally ta bar musu Baffansu!!!
Kai tsaye guest house din Zayyan din suka tambayi maigadinsa ya nuna musu, suka soma danna kararrawa ba kakkautawa.
Shi din ne kuwa ya taso ya zo ya bude, cike da mamakin wanene da yi masa wannan rashin hankalin haka?
In Azeezah ce knocking ta ke yi, kuma a yadda ya bata mata rai da korar su Janet ya san ba za ta neme shi nan kusa ba.
Yana budewa sai ya yi arba da yayyunsa, Zubaidah da Zubainah.
Kowaccensu zuciyarta saida ta motsa, ta tabu da ganin yadda Zayyan ya rame, ga wata kasumba da gargasa da ya tara a sajensa da suka cika masa fuska, ya koma cikin irin yanayin daya shiga a lokacin rashin Baba Bello, Allah kadai yasan ko tun yaushe rabonsa da duba madubi da yin askin fuska.
“A’ah, su Yaya Zubaida, ku ne? me ya sa ba ku yi min waya ba ai da ba sai kun taso da kanku ba”.
Harararsa Zubaida ta yi, Zubaina kam ta kasa cewa komai, Zubaida tace “dama kana da waya ashe?
Ni ba ni hanya in shiga daga ciki, na kwaso gajiyar zaman mota”.
Ya ba su hanya suka wuce cikin falon, kowacce ta nemi lafiyayyar kujerar falon ta zauna tana kokawa da tausayin condition din da taga kanin nata a ranta.
Duk da Zubaina cike take da shi, amma yadda ta sameshi kadai ya sa bata yi korafin komai ba, bata yi zancen komai ba sai na Mama, ta ce masa sun zo ne su wuce tare da shi ABUTH, Mama na cikin wani hali da ta ke bukatar dukkaninsu tare da ita.
Duk da cewa Mama ce sanadin shigarsa cikin halin da yake ciki a yanzu, Mama ce silar aikata aikin da ya zame masa dana sani tun ranar da ya aikata shi, Mama ce mujazar duk abubuwan da suka faru da shi cikin iyalinsa, kuma itace mai alhakin rugujewar rayuwar gidansa a halin yanzu.
To amma lafiyarta tafi komai muhimmanci a gare shi.
Bai ce wa su Zubaida komai ba, bayan su ba shi minti ashirin yayi wanka ya shirya.
** **
Zubaida, Zubaina, Zayyan tunda suka dauko hanyar Zaria sun karanta magana a tsakaninsu, kowanne abinda yake sakawa a ransa dabam ne, Zubaina ji ta yi zuciyarta na narkewa cikin tausayin kanin nata, wanda a baya ta ci alwashin idonta idonsa, sai ta yi masa wankin babban bargon biye wa Mama da yayi ya aikata wannan danyen aikin.
Amma ko da suka yi arba da juna duk ta mayar da makaman yakinta cikin kube, ta koma tunanin hanyar da za ta bi ta taimaka masa, wato ta dawo ma da Zayyan farin cikinsa wanda ba komai bane banda Sophie dinsa.
Likitan Mama da ya tabbatar da zuwan Zayyan a gabansa washegari, sai ya hada su duka, wato ‘ya’yan Maman ya yi musu bayani dalla-dalla cewar mafitar lafiyar Mama guda daya ce a wannan gabar, shine, a yanke kafarta guda daya da ciwo ya shafa, sugar ya gama aikinsa a lafiyar Mama da jin ciwonta, dan ciwon da Mama ta ji da karfe a bandaki take tunanin ba komai bane ya koma ‘diabetic foot’.
In ka cire Zayyan da ya rufe fuska da tafukansa ya soma wani irin gumi (zufa) dukkansu matan kuka da kururuwa kawai suka saka, aka rasa mai sanya hannu cikinsu don gudanar da wannan aiki. Don Zayyan ya ki saka hannu sam.
Zahra tace cikin rishin kuka “wallahi na gudo da Mama daga asibitin Abuja ne don suma sun gaya min kwatankwacin haka, ina ganin sune basu san aikinsu ba, tunda private hospital ne, amma ashe ban tserar da Mama daga wannan kaddarar ba, na yi gudun gara na tadda zago, daga can din zuwa ABUTH”.
Zayyan tunda ya rufe fuska da tafukansa hawaye yake yi, wace irin kaddara ke bibiyarsu haka?
Ko dai tun ba’a je ko’ina ba, alhakin Sophie ya fara taba farin cikin iyalin Mama da ita kanta?
Kuma a karshe dole yana ji yana gani, haka ya saka hannu don a yi wa Mama aikin yanke kafarta ta hagu.
Babu wanda ya ke tunowa a lokacin da aka fito da Mama daga dakin theatre sai babansu, wato mahaifinsu late Arch. Bello Isyaku Rafindadi.
Wanda duniya ta shaida suma kuma ‘ya’yansa sun shaida babu abinda yake so a duniya yake tattali sama da Mama Fatu! Dasu ‘ya’yansa. Yana cewa, gara da Allah bai tsawaita rayuwarka zuwa yau ba Baba! Da zaka ga Fatiman ka a keken guragu ba.
Allah shi ne shaida in zai karar da duk abinda ya mallaka a duniya don a barwa Mama kafarta zai yi hakan, amma duka likitocin sun tabbatar da cewa, babu wata mafitar bayan wannan. Ko birnin Sin zasu kaita.
** **
Jikin Safiyyah dai ya ki komawa daidai tun zuwanta Dandume, wani zubin itada Ammi ko barci basa iya yi cikin dare, ita ke ciwo Ammi ke jinsa a nata jikin da jinyarsa a ruhinta.
Daga baya Safiyyah ta koma komai ta ci sai ya dawo. Abin ya damu Ammi kwarai da gaske, kuma a matsayinta na babba har wani tunani na daban ne ya darsu a ranta, wanda bata barshi ya yi nisa ba, ta yi maza tasa sanda ta fatattakeshi.
Tana cewa, kanta gara ta kai Safiyya asibiti a binciki hakikanin me ke damunta, watakila shawara ce ko zazzabin taifot, don duk ta dashe kamar mai fama da shawara.
Da farko da Ammi ta ce ta dauko mayafinta su tafi asibiti, Safiyya tirjewa ta yi don ta tsani allurar malaria. Sai da Ammi ta yi mata jan ido tukunna ta ce ko ta tashi su je cikin lallami, ko ta je ta nemo likita har gida ya zo ya duba ta yayi mata allurar.
Dole Safiyyah ta janyo hijabinta jikin kyauren Ammi suka kama hanyar asibiti tana ta fushi.
Likitar da suka samu tana dubata a lokacin sai ta tambaye ta ko yaushe rabonta da ganin al’adarta?
Safiyyah ta yi dan tunani kafin ta ce, ko last two month ta yi al’ada. Likitar ta yi dan rubutu a file dinta kafin ta ce mata, ba za ta ce komai ba sai Safiyyah ta dawo gobe da safe. An dauki jininta za’a duba.
Tun daga lokacin Ammi ta kara yarda da nata tunanin da take fatattaka da sanda, amma dai ta ce, bari su bi umarnin likita. Safiyyah kuwa ba ta kawo komai a ranta ba, a haka suka koma gida.
Washegari ta tashi yin alwallar sallar asubahi, Ammi ta kara tunasar da ita maganar komawarsu asibiti yau.
Ta ce, “Ban manta ba ai Ammi. Ni kawai allura ce bana so, in dai ya tabbata malaria ce ko taifot gara a bani kwayoyin magani ko guda dari ne zan sha akan a yimin allura”.
A kalla yau din Ammi ta samu ta yi magana, don cikin satin gabadaya Ammi na iya kirga adadin furucinta.
Ammi da Malam sun yarda kawai a ransu Zayyan ya saki Safiyyah ne, ko daga sakon text din da ya rubutowa Malam a daren jiya.
Bayan duk wani attempt dinsa na kiran Malam a waya bai samu yayi doguwar magana dashi ba, Malam din yaki yace in har ba tattaki zai yi ya zo da kansa su magantu ba, ya gaya masa dalilin sako masa diya a motar haya cikin dare duk tarin motocin da ya mallaka a gareji.
Don ko kadan Malam bai ji dadin a yanayin da Safiyyah ta zo musu ita kadai ba, kuma cikin dare ba. Sannan ba wanda ya biyo bayanta tun lokacin daga shi har wani nasa.
A cikin sakonsa na daren jiya ga Malam, Arch. Zayyan Bello Rafindadi, ya ce.
“Hakika Malam ina cikin wani hali na rashin sanin tabbacin kaina. Rokona gare ku Malam shi ne, ku taya ni neman gafarar Safiyyah. Ina cikin takunkumin da ya hana ni zuwa gare ku, amma hakika zuciyata har abada tana ga Safiyyah”.
Daga wannan sakon da ya gani kawai Malam ya san cewa Zayyan ya saki Safiyyah, maiyuwa bisa umarnin mahaifiyarsa, mai yuwa kuma bisa kaddara ta karewar wa’adin aure.
Shi ya sa bai kara takurawa Safiyya kan tambayar me ya kawo ta gida ba, haka ya hana Ammi sake tambayarta, ta lafiyarta suke, data ki daidaito tun zuwanta, amma yacewa Ammi sai ta fara kirga mata iddah.
Zuciyar Malam Usman ta yi duhu sosai, irin na kowanne Uba da aka sakowa ‘yarshi daga gidan aure.
Sun tattauna shi da Ammi yake bata hakuri, ya ce ta yarda shi aure rai ne da shi, idan wa’adinsa ya yi babu mai iya kara masa ko dakika daya ne.
Ammi ba ta iya daurewa ba, sai da ta zubar da hawaye masu zafin gaske, ta ce, “yadda Hajiya Fatu da ahalinta suka tozarta Safiyyah, Allah ka yi musu daidai da abin da suka aikata a gareta. Ba zan taba yafewa Hajiya Fatu ba, domin ta dade tana yadda ta ke so a kan Nana Safiyyah.
Don haka wata irin kulawa mai tsanani da tushe Ammi ke yi wa Safiyyah yanzu.
Ammi ta duba gaban Haroun ba ta ga ko ruwan sha ba, duk da ba cikin nutsuwa ta ke ba haka ta kwalawa Rayha kira tana sauke fadanta a kanta. Rayha na rantsuwar kare kai, ta ce, wallahi ba ta ji shigowar Yaya Haroun ba.
Malam ya ce,
“Kun dade sosai a asibitin, ina Nana Safiyyan?”
Haroun ya dago a hankali yana duban Ammi don jin amsar da za ta bada, sai ta ce cikin jimami,
“Tana ciki, ba ta jin dadi, bari in bi ta in bata magani”.
Ta ce ma Haroun, “Ina fatan dai za ka kwanar mana biyu anan kafin ka wuce ko?”
Ya yi murmushi cikin ginshira irin tasa, ya ce,
“Ammi ai kin san yanayin aikin namu bai barinmu bakunta mai tsayi, yanzu ma tsakuro lokacin na yi, don dai in zo in ga Ammina ko na kwana daya ne.
I missed my Ammi”.



