Chapter 4: Chapter 4
Mama bayan Zayyan ya kawo mata crutches ta amsa tana shi masa albarka.
Sai Zubaina ta kira shi a waya a lokacin. Zubaina ta turke shi kan yau sai ya gaya mata saki nawa ya yi ma Sophie.
Zayyan ya dukar da kai kasa, ya kasa dagowa, kamar Yayarsa Zubaina na kallonsa, amma idanuwansa sun kada sun yi jazur. A lokacin da yake wayar nan da Zubaina yana zaune gaban Mama. Mama ba ta yi magana ba, duk da a (hands free) ya saka wayar da Zubaina, tana jin komai, hankalinta ya tashi ainun ganin yadda jijiyoyin kan Zayyan kansu suka bayyana, makwallatonsa ke motsi yana komawa da kyar.
Zubaina ba ta san halin da yake ciki ba, ta ce, “To Zayyan rokona da kai shi ne, ka dakata da zuwa gidana da kace zaka yi gobe. Saboda wallahi na tuna saki ukun da aka ce kayi ma Sophie, wallahi Allah mugun baci raina yake yi, zuciyata kufula ta ke yi inji kamar in rufe ka da shegen duka.
Da wannan nake rokon ka akan ka saukaka min, ka daina zuwa Kano gidana, insha Allah zan samu lokaci in je Dandume in gaida Safiyyah, ina addu’ar Allah ya sa zuwa yanzu ta samu mijin da ya fi ka komai da komai, don ina irge da cewa tuni ta gama iddarta sama da watanni biyu”.
Zayyan yana satar kallon Mama, ko za ta ce wani abu a kai, tunda dai komai ya faru da shi ya faru ne bisa umarninta. Yana son gamawa da Mama lafiya, yana son biyayyarta ta kai shi aljanna, shi ya sa ya bi umarninta, amma tun ba a je ko ina ba, komai ya zo yana haunting dinsu su duka family din.
Duk yadda ya so Mama ta ce wani abu wanda zai sa ‘yar uwar tasa ta daina ganin laifinsa Mama ta ki yin magana a kai. Cructches dinta da ke zube a gabanta kawai ta ke bi da kallo.
To daga can ne ya dawo gidansa goshin magriba, yayi sallah ya shiga wanka.
Fitowarsa kenan yana sharce kansa daure da tawul iya kugunsa, ya ji an murda kofar dakin nasa.
Ko da bai juyo ba kamshin turaren darenta da ya sani kadai, mai tada hankalin Da namiji wato ‘Dior’ (midnight poison) ya gama gaya masa cewa Azeezah ce.
Daga fitinanniyar lingerie din da ke jikinta yanzu ya san meya kawota, a ransa yace mace sai jarabar Da namiji kadai ta sani. Bai san sanda ya yi tsaki ba, shi kam baida ra’ayin komai daren yau, ta bar shi yaji da damuwar da ya kwaso a gun Mama, da wadda Zubaina ta jefa shi a ciki wai kada ya kara zuwa gidanta.
A hankali ya ce,
“Azeezah, ban hana ki shigo min turaka ba sallama ba?”
Ta yi har! Da idanunta a kansa, kafin ta kyabe baki ta ce cikin taunar cingum,
“Sai me? Dadin abun dakin mijina ne ni kadai yanzu, ba tare da kowacce karabiti ba yanzu, balle a dinga sa min waigi da takunkumin sai na yi sallama”.
Ta dube shi invitingly lips dinta na motsi sanda ta iso gabansa bai ankara ba sai da ta kama towell din da yake daure da shi, za ta zare, bayan ta kai masa wata wawiyar runguma.
Rike towell din Zayyan ya yi kam, ya ce, “Zeezah meye haka? Sallah fa zan yi, kin bata min alwallah”.
Azeezah na kici-kicin kwace towel, Zayyan ya daka mata tsawa.
“Stop it Zeezah, bana son wasa, na ce miki sallah zan yi ko? A yi mace sai fitina kamar Ayu?”
Maganar da tsawar sun bakanta wa Azeezah rai, amma ta sha zafafan magungunan mata, dana mallakar miji a gado ba boka babu mallam, da suka sa bazata iya hakuri da shi a yau ba, sai ta kankame shi ta koma begging.
Zayyan wanda gaba daya yau a hautsine yake, ga damuwar Mama za ta koma tafiya kan ‘crutches’ din da ba ya so, ga kalaman Zubaina wadda ya tabbatar duk cikin ‘yan uwansa ba mai kaunarsa kamarta, da ta ce kada ya kara zuwa inda ta ke sai ya gaya mata ko saki nawa ya yi wa Safiyyah da bakinsa tukunna.
Shi kansa ya kasa tuna ko saki nawa ya yi ma Sophie a lokacin, sai yanzu yake cewa saki daya ne ba biyu ba, ga muguwar addu’ar da Zubainah ta yi masa na wai Allah ya sa zuwa yanzu Sophie ta samu wanda ya fi shi komai.
Don haka ba ya jin zai iya ma Azeezah komai yau, don bakidaya zuciyarsa a jagule ta ke.
Angije ta ya yi da karfi, ganin tayi nasarar kwace masa towel din kamar mayya, ya ce,
“Sau nawa zan gaya miki ba koyaushe ne nake cikin mood na yin abinda kike so ba?
Sau nawa zan gaya miki I’m not your sex machine, ki dinga barina ina nutsuwa da hutawa?
Shin don wannan kawai ake aure ne Zeezah?
Cikin sauran hakkokin aure da na kyautatawa miji wanne ki ke yi a ciki da har mutum zai ji dadin bauta ma jikinki kullum kema?
Ba ki san cina ba, ba ki san shana ba, ba ki san a ina nake samun abinda zan ci ba, tunda Safiyyah ta bar ni.
Ibada wannan ta cikin dare ba kya barina inyi ta yadda ya kamata, sai abinda kike so kullum ayi ta abu kamar cin tuwo? To yau, I am not in the mood, ba abinda zan iya miki, please! Leave me alone, ki je ki yi sallah ya fi miki alkhairi”.
Azeezah ta gama zuwa wuya, don idan bai yarda ya bata hadin kai a yanzu ba, komai na iya faruwa da ita.
Bayan asarar kudinta na sayen wani maganin mata na matsi kudi na gugar kudi har dubu dari uku da hamsin, ga shi tunda ta samu ciki komai ya kara sukurkurce mata, ba za ta iya barci yau in Zayyan bai amince mata ba.
Duk taurin zuciya irin na Azeezah na rashin son zubda class, da jin kai, amma yau ta hadiye takamarta, ta tsugunna a kan gwiwoyinta, tana rokonsa ya ba ta hakkinta.
Mirsisi Zayyan ya ki, komawa ya yi toilet da dogon tsaki a bakinsa, ya sako alwala ya saka farar jallabiyyarsa kar sabuwa dal, ya dauki casbaha ya fice masallacin Estate don tasa ya yi missing jam’in magriba already, ga shi har an yi kiran sallahr isha’i.
Yau Azeezah ta yanke wa kanta shawarar tafiya Lagos na gaske, ba na barazana irin wanda ta saba ba.
Tana kuka ta bar dakin Zayyan zuwa dakinta ta soma watso kayan dake cikin wardrobe dinta kamar sabon tabin hauka, Zeezah a dabi’arta bata iya controlling bacin rai ba, nan take ta dauki wayarta ta kira Alex John, wani ma’aikaci a filin jirgin saman Abuja, yaron Baba Murtala ne, shi yake yiwa Baba Murtala booking din duka tafiye-tafiyensa na cikin gida Najeriya.
Ta fada ma Alex, ya yankar mata ticket din Lagos yanzu-yanzu, ya duba sannan ya kirata ya ce, babu jirgi a daren nan sai dai na safe karfe shida, ta ce ya yankar mata.
Da yake part din Zayyan da na Azeezah da ‘yar tazara bai ma san yaushe ta zari mota ta bar gidan da asubahin fari ba.
Shaheed da Azumi ya kwana ranar, Azeezah bata ko bi ta kansa ba, ta gayawa kanta ai ba da shi ta zo gidan ba, kuma babban abun da zata yi ma Zayyan ya bakanta masa rai ta rama yadda ya bakanta mata shine, ta tafi ta bar masa Shaheed da ‘yan aiki.
** **
Hajiya Nana ta ce, “Inata magana Azeezah kin min banza? Keda wa kika zo? Ina Zayyan din? Ina kika baro maigidan nawa kuma? Yaron dake shan nono!”
Azeezah sai kuka take bata ce ma Mamanta komai ba.
Gaban Haj. Nana na faduwa tana tunanin ko wani abu ne ya samu Shaheed din, ko sakin Azeezah Zayyan yayi saboda ya fara gajiya da halinta da tun farko aka gaya masa.
Azeezah ta ki magana, wanda hakan duk ya kara dugunzuma zuciyar Hajiya Nana.
Sai ga Baba Murtala ya shigo dakin cikin shirin fita. Tun daga bakin kofa yake jiyo tashin kukan Azeezah, ya karaso da sauri dakin Hajiya Nana yana cewa,
“Lafiya? Kamar Azeezah nake gani da sassafen nan? Me ya faru, ina Zayyan din da takwarana?”
Azeezah ta mike da gudu zuwa gaban Baba Murtala zata rike shi cikin kuka ya dakatar da ita ta hanyar ja baya da daga mata hannu, ya ce, “Akul! Ki ka taba ni, sai kin fara gaya min me ya kawo ki ke kadai?
Don ni dai Zayyan bai ce min kina tafe ko zaku zo ba”.
Tace, “Baba ni wallahi na gama aurensa, banni komawa”.
Baba Murtala ya ce, “To sannu mijin Zayyan tunda auren a hannunki yake, shashashar wofi… na tabbata Zayyan bai san kin taho ba”.
Ya zaro waya yana kiran layin Zayyan cikin tsananin bacin rai.
A daidai lokacin karfe goma na safe, Zayyan ya fito kenan Azumi ta tare shi dauke da Shaheed dake ta kuka tun daren jiya. Ya yi maza ya karbe shi yana cewa,
“Wa ya taba min Babana haka?”
Ta ce, “Mamansa yake nema, tun jiya rabonmu da ita”.
Zayyan ya yi sak! Yana son tuno me ya faru, kuma ina Azeezah ta je haka da sassafe, sai ga kiran Baba Murtala ya shigo wayarsa da ke hannunsa.
A ladabce ya amsa, bayan ya zauna a three seater, yana jijjiga Shaheed a cinyoyinsa. Suka gaisa shi da Baba Murtala, Baba Murtala na iya jin kukan Shaheed, sai Baba Murtala ya ce.
“Da saninka Azeezah ta taho Lagos da sanyin safiyar nan?”
Zayyan ya yi ajiyar zuciya, cikin mamakin Azeezah da rashin kunyarta, yanzu akan wannan abun na jiya ta kama hanya ta tafi gaban iyayenta, to taje ta ce musu me? Tace ya ki kwanciya da ita ko me? Don rashin hankali da rashin tarbiyyah ko don me?
Ya nisa cikin jin nauyi mai yawa ya ce,
“Wallahi Baba ban san ta fita ba. Ba yadda za a yi na barta ta zo har Lagos ita kadai”.
Baba Murtala ya ce, “To daure ka zo yau, ba zan saurare ta ba, sai ka zo”.
Zayyan kunya kamar ya yi yaya, yana da muhimman ayyuka da suka fito da shi a safiyar nan, amma haka ya ce ma Azumi ta hada masa kayan Shaheed za su fita.
Bai sha wahalar samun jirgin Lagos ba, a Nmadi Azikiwe International Airport. Kafin ya iso Baba Masari direban Baba Murtala yana filin jirgi yana tsumayin isowarsa.
Hajiya Nana ma ta ki sauraronta, ta ce sai Zayyan ya zo, don ta santa ba kan-gado ne da ita ba. Tunda har ta taho ta bar yaron da ke shan nono da masu aiki.
Azeezah tunda ta zo gida ta ke ma iyayenta kuka ko ruwa bata sha ba. Duk da Hajiya Nana ta damu, don ta lura tana ta tofar da miyau kuma duk ta dashe jikinta ya yi danye, alamu dai na karamin ciki sun gama bayyana a tare da Azeezah, alhalin ko yaye Shaheed ba ta kai ga yi ba.
A zuciyar Hajiya Nana tana ta mamakin irin wannan kaddarar haihuwa akufi-akufi da ke tsakanin Zayyan da Azeezah, bayan an ce ya kwashe sama da shekaru goma da aure bai samu haihuwa ko daya ba.
Sai wajen la’asar Zayyan ya iso gidan, Hajiya Nana ta yi maza ta amshi Shaheed daga hannunsa ta bashi abincinsa yaci, ta sa aka yi masa wanka. Baba Murtala ma ranar bai je ko ina ba, yana jiran zuwan Zayyan din.
Hajiya Nana ta shirya abincin rana, ta ce, Azeezah ta kai wa Baba Murtala da Zayyan falonsa.
Ai tsalle Azeezah ta yi ta dire ta ce, tunda Zayyan yana falon ba za ta kai ba. Hajiya Nana ta saki baki hade da salati tana cewa,
“Ni in sa ki aiki ki ce ba za ki yi ba Azeezah?”
Ta ce, “Mama ai saboda na gama aurenshi ne, ki sa ni kowane aiki zan miki, amma ban da na wannan dan wulakancin…”
Mari Hajiya Nana ta kaiwa Azeezah, amma kafiya da dokin zuciya da Azeezah ta hau ba ta kaima Zayyan abincin nan ba, cewa ta yi ma Mamansu,
“Zayyan kura ne da fatar akuya, amma mugu ne, don burinsa shi ne ta mutu”.
Hajiya Nana ta yarda Azeezah ba karamin fushi ta yi da Zayyan ba, sai ita da kanta ta kai wa Baba Murtala da Zayyan abincin.
Bayan Hajiya Nana ta dawo ne sai cikin kuka Azeezah ta ce ma Hajiya Nana,
“Mama a kan Zayyan ki ka mare ni? Don ba ki san me yake yi min ba, alhalin ba ni na kar masa zomon ba, Mamansa ce, amma duk komai a kaina zai kare?”
Hajiya Nana ta ce, “Ki je ki gaya wa ubanku yana kiranki, ni babu ruwana. Ai san da ku ka kulla auren Zayyan din ma ke da shi ku ka kulla, ba da ni ba”.
Ta dauki Shaheed ta goya shi don tunda suka zo Azeezah ta ki daukansa balle ta bashi nono.
Azeezah da Zayyan a gaban kotun Baba Murtala.
Baba Murtala ya tambayi Zayyan laifin me ya yi ma Azeezah? Zayyan ya dukar da kai kasa, ya ce,
“Baba wallahi ban san laifin da na yi mata ba banda cewa da na yi ta je zan yi sallar magriba jiya.
Daga nan ban sake ganinta ba, sai da safe mai aikinta ta kawo min Shaheed, sai kuma kiran wayarka”.
Azeezah ta galla masa harara ta ce, “Munafuki dai bai ji dadin halinsa ba, ka fada wa iyayena gaskiya kawai cewa tunda matarka ta tafi ka daina kwanciyar aure da ni”.
Ba Baba Murtala ba, hatta Hajiya Nana salati ta dauka, shi kuwa Baba Murtala ya rarumi abinda hannunsa zai iya dauka ya makawa Azeeza a baki, wanda bunch of keys dinsa ne. nan da nan bakin Azeezah ya haye yayi suntum. Hajiya Nana ta zare jiki ta bar falon tana ta roka wa Azeezah hankali a cikin ranta.
Sai Baba Murtala da Zayyan ta bari a wurin kamar su nutse don kunyar juna. Bayan Baba Murtala ya kori Azeezah daga gabansu.
Baba Murtala ya san Azeezah ba ta da kan-gado, amma bai san hankali ma ba ta da shi ba sai yau.
Amma sai ya shanye komai, ai Zayyan dansa ne na halal, babu kunya ko surukuta a tsakaninsu, ya nutsu sosai, ya ce,
“Zayyan me ke faruwa? Shin abin da ta fada din haka ne ko meye ya faru tsakaninku?”
Zayyan ya ga cewa in ya yi shiru Azeezah zata zubar masa da mutunci ne a idanun Babansa mai kaunarsa, sai ya muskuta cikin dakewa da shanye kunya, ya dubi Baba Murtala.
“To Baba, ita auratayya din ba sai da kwanciyar hankali ake yinta ba? To ni bani da shi, tunda na rabu da uwargidana rabona da kwanciyar hankali Baba, ga mahaifiyata babu lafiya har ta kai ga an yanke mata kafa daya ka sani.
Ba a jima da faruwar duka wadannan iftila’in a gare ni ba Baba, a jiya na sayowa Mama crutches don ta samu ta dinga motsawa, a daren ranar ina cikin wannan damuwar, na hawan Maam crutches da kalaman ‘yar uwata a kaina, ita kuma Azeezah tazo ta tirkeni, itama ta san ba haka rayuwata ta ke ba, da wanne zan ji?
Da rashin Safiyyah tare dani dana faro dukkan rayuwata da ita, na saba da ita ko da rashin lafiyar Mama da harta kai ga nakasa, Mama data rage min a duniya?”
Ita Azeezah ba ta san komai ba sai wannan, ni kuma na gaya mata ni ba inji ba ne, ina da abubuwan da suka hana min nutsuwa a yanzu”.
Baba Murtala ya ce, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un. Ina ina ni duk wannan ya faru? Me matarka ta yi maka ka sake ta?”
Zayyan ya dukar da kansa kasa, Baba Murtala couldn’t believe it, da ya ga hawaye sun biyo kuncin Zayyan, sharr! Don ji Zayyan yake kamar gashi ne a gaban Baba Bello, yana tuhumarsa dalilin sakin Sophie.
Tun tafiyar Sophie Zayyan bai yi kuka ba sai yau. Ya yi kuka, ya yi kuka har ya ji sanyi a ransa, Baba Murtala bai hana shi ba, bai kuma lallashe shi ba, sai da ya bar shi ya fidda tsatsar ransa ta cikin hawayensa.
Duk wata nadamar sakin da kewar Safiyyah sai yanzu suka hudo ta cikin hawayensa. Safiyyah is not only his first and everlasting love, but his comfort and peace of his life. Rashinta ya maida shi kamar rikitacce ko kuwa zautacce wanda ya rasa hakikanin ina yake masa ciwo a jiki da zuciyarsa kuma ina yasa gaba yanzu. Ya koma tamkar bai san abin da yake yi ba, tun barinta rayuwarsa ya jirkice.
Hakika Safiyyah ta tafi Dandume ne da zuciyarsa da ruhinsa, ta bar wa Azeezah da kowa gangar jikinsa, ya yi ta yin abinda gangar jikin ke kawata masa, har gashi ya gaji, tun ba’a je ko ina ba KAWAR ZUCIYAr ta fara ginsar shi.
Hakika ya yarda soyayya a zuciya ta ke, ba a gangar jiki ba.
Sha’awar jima’i ita ce a cikin gangar jikin dan’adam, kuma da an yi satisfying dinta shi ke nan, but pure love irin wanda yake yiwa Safiyyah, will forever remain in its place.
Sai da Baba Murtala ya tabbatar Zayyan ya gama amayar da nadamarsa, da bakin cikinsa cikin kukansa, kafin ya ce yana so ya ji duk abinda ya faru har ta kai ga sakin da kuma adadin sakin.
Tiryan-tiryan Zayyan ya soma gaya wa Baba Murtala komai, tun haduwarsa da Sophie a jami’ar Ahmadu Bello, da yadda Babanshi ya so Safiyyah, ya kuma aura masa ba da son ran Mama Fatu ba saboda in’inarta, saboda kuma diyar malamai ce against the wish of his mother.
Rayuwar da suka yi ta fahimta da soyayya cikin kalubale na rashin samun haihuwa, da taskun Mama ga Safiyyah a kan hakan sama da shekaru goma. Hatta batun IVF baby dinsu Zayyan ya gaya wa Baba Murtala tare da irin rawar da Mama ta taka wajen raba shi da Safiyyah.
Da furucin da ta yi masa na in bai sake ta ba ko idan ya sake ya bita gaban iyayenta bayan tafiyarta.
Baba Murtala bai iya ya ji karshen ba ya dinga jero “hasbunallahu wa ni’imal wakeel, ya ce, “Ba ku kyauta ba bakidayanku, amma Fatu ita ce babbar mara kirkin.
Kai kam ai biyayya ka yi, kuma insha Allahu zan yi iya yina in ga cewa an gyara auren nan.
Ba da ni za a taru a ci amanar marigayi rabin raina Bello Rafindadi ba”.
Baba Murtala da kanshi ya je ya kira Azeezah ya cicci mata mutunci, ya ce, ita da rashin kunyarta su kiyaye shi. Ta goya danta ta bi mijinta yanzun nan su bar masa gida, ya yi rantsuwa ba za ta kwanar masa a gida ba.
Hajiya Nana ta yi kokarin lallashin Baba Murtala da kokarin ganin ya kyale su zuwa gobe da safe, amma ina! Zuciyar Baba Murtala ta gama karyewa a kan Safiyyah.
Ya kara rantsewa sai sun bar masa gida daga Zayyan din har Azeezah ba ya son ganin ko daya a gabansa.
Haka Azeezah ta fito gida dauke da danta, Baba Masari direban Baba ya dauke su.
A airport din Murtala Muhammad suka yi kwanan zaune ga sanyi ana busawa, shi ke kula da Shaheed din, Azeezah taki kula su, har wayewar gari suna waiting lounge, ya lullubeshi da babbar rigarsa, don sai washegari suka samu jirgin da ya maida su Abuja.



