⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 5: Chapter 5

Alhaji Murtala Babangida Masari ne kwance a bayan mota Hyundai direbansa Masari na tuka shi zuwa garin Dandume. Bayan ya sauka a filin jirgin saman Kaduna. Da tambaya daya zuwa biyu ba kuma tare da da shan wata wahala ba aka kai su har kofar gidan Malam Usman Dandume.
Tunda suka yi magana da Zayyan a kan Safiyyah, Baba Murtala ya zama restless, ji yake sai ya maidowa Zayyan matarsa ko da wannan shi ne kokari na karshe da zai yi wa rayuwar dan nasa, kafin barinsa duniya.
Malam Usman ya karbi bakon nasa, kyakkyawar tarba, irin wadda ya saba yi wa bako ko da kuwa bai sanshi ba, kamar yadda ya faru yau da zuwan Baba Murtala.
Falon soro na gidan Malam Usman ya kaishi. Sun yi gaisuwa irin ta musulunci, kuma irin ta manya ta hanyar yin musabiha da junansu. Malam yasa aka kawowa Baba Murtala ruwa da lemo, sai Alhaji Murtala ya dauki ruwan yana budewa yana ce da Mlam, “ai ni ka ganni nan Malam, bana shan lemo, da duk wani abu mai zaki sabida tattalin lafiya”.
Kafin ayi haka Malam ya ce da Baba Murtala.
“Ga shi kuma tsufa ya sa na manta fuskar, ko kuwa in ce shekaru sun yi nisa sun saka ban shaida ka ba”.
Sai Baba Murtala ya yi murmushi ya ce, “In har ba ka manta Bello Rafindadi ba, to nima bai kamata ka manta ni ba. Tunda kuwa ni na karbarwa Zayyan auren Safiyyah a hannunku”.
Malam ya ce, “Allahu akbar! Allah ya jaddada rahma a gare shi, Allah ya bamu guzurin tadda su. Tabbas da suna raye da abubuwa da yawa da suka faru a yau da basu faru ba”.
Baba Murtala ya ce, “Kwarai da gaske, amma in babu Bello ni ina raye, zan kuma yi kokarin gyara kuskuren da iyalinsa suka tafka, in har za ku bani dama.
Na ji wautar da suka taru shi da uwarsa suka aikata. A yau da yawun bakinsa na zo ina nema masa komen matarsa.
Kamar yadda kuka saba hakuri da halinsu, to ku kara Malam, ku yi hakuri Safiyyah ta koma dakinta, tunda alhamdu lillah ya yi saki irin wanda za a iya gyarawa, duk da na san ba’a bari a kwashe daidai.
Ku kara mana dama ko da ta karshe ce insha Allahu ba za a kara maimaita kuskuren da aka aikata a baya ba. Zan sa ido, kuma yanzu ita Hajiya Fatu ma ta lafiyarta ta ke, ciwon sugar ya sa ta rasa kafarta daya, har yanzu kwance take tana jinya”.
Malam yana girgiza kai cikin tausayawa ya ce, “Subhanallah, Allah ya kiyaye gaba, Ya bata lafiya, Ya kuma sa jinya kaffara.

Amma wallahi a wannan karon ba ni da hannu a yi wa Safiyya aure, ko komawarta gidan miji, tunda bazawara ce, sai abin da ta zaba.
Tsakanina da ita addu’a, amma ko shawara ba zan bata ba. Duk hukuncin da ta yi wa rayuwarta shi za mu karba, mu kara mata karfin gwiwa a kansa”.
Malam ya kasa gayawa Baba Murtala cewa Safiyyah na da ciki, don ma kada Zayyan ya ji, ya samu hanyar cewa ya maida ita, tunda ya zama cewa har yanzu tana cikin zimmar aurensa.
Shi kuwa Malam a yau ba shi da sauran fata a kan zaman Safiyyah da Zayyan, domin ya ga irin halin bakin cikin da Safiyyah da mahaifiyarta suka kasance a cikinsa, tun dawowarta gida.
Har zuwa yanzu kuma acikinsa suke rayuwa, wato Safiyyah da Ammi, Safiyyah bata koma daidai ba, haka Ammi. Cikin da ta ke dauke da shi a halin yanzu bai sa ta farin ciki ba, bai dawo da walwalarta da kazarniyarta ba, bai wanke dattinsu dake lullube a zuciyarta ba.
Har Baba Murtala ya bar gidan Malam Usman bai samu wata amsa mai inganci daga mahaifinta ba, bai kuma ba shi damar a kira Safiyyah ya ganta ba, duk da ya ce ma Baba Murtala zabi a hannunta yake.
Daga Dandume Baba Murtala Kaduna ya nufa gidan Zahra, ya sauke fushinsa da bacin ransa a kan Mama Fatu, ya kirata da sunaye kala-kala ciki har da mai bin KAWAR ZUCIYA ta kuma danne farin cikin danta. Ya yiwa Mama Fatu wankin babban bargo, har sai da Mama ta yi kuka da idanunta. Don bata taba zaton Baba Murtala ya iya fushi ba balle irin wannan bacin ran.

Watannin cikin Safiyyah takwas yanzu harda karin sati daya, tuni ta san EDD dinta daga asibitin Dandume, tsayin lokacin nan duka Yaya Sheikh in yayi waya dasu Ammi ko Assafe ta kira su ba su taba ce musu Safiyyah na gida ba, ba don komai ba sai don Ammi ba ta son Safiyyah ta gusa daga kusa da ita, ta fi son ta ci gaba da kula da ita da kanta tunda haihuwar fari ce, har Allah ya sauke ta lafiya kafin ta sanar da Sheikh, in yaso daga nan sai su yi shawarar abin da ya dace da ita.

Shi kuma Dr. Ridhwan (Yaya Shaikh) duk tsayin lokacin Allah bai sa ya zo Dandume ba, kasancewar yayi tafiya zuwa Arkansas na tsayin watanni shidda. Ammi kuma ta san halin Assafe sarai, daga ita har mijinta, a kan Safiyyah basu da namba two, Assafe tana jin zancen mutuwar aurenta bazasu bar mata Safiyyah ba, cewa zasu yi zasu tafi da ita wajensu, duk da auta Rayha na debe mata kewa sosai, koda Ammi ta dan fita hankalinta na kan Sophie. Allah-Allah take ta dawo gida.
Hatta Sabah da Rayyah dake gidan mazajensu da farko basu san auren Safiyyah ya mutu ba, Ammi ce musu ta yi matsala suka samu ta ki yarda ta koma, ta kuma gaya musu Safiyyah ta samu rabo, wanda ko shi Zayyan bai sani ba.
Sabah ta yi ta rokon Ammi kan ta barta ta fada masa, amma Ammi ta ki, ta gargade ta sosai kan kada ta shiga abin da ba’a saka ta ba, don Safiyyah ba farin ciki ta ke da samuwar cikin ba, a lallabata ta haife shi lafiya.

Yamma lis, sati daya da zuwan Baba Murtala Dandume, a cikin gidan Malam Usman. Safiyyah na zaune a rumfar Ammi tana yanke akaifar hannunta da nailcut, ta sha wankan juma’a sanye cikin brown karamar atamfa Chiganvy, an yi mata budaddiyar fitted gown da ta sake sosai a cikinta irin dinkin masu tsohon ciki, cikinta ya fito sosai ya yi das a jikinta gwanin sha’awa. Wani uban juyi da jaririn ya yi a cikinta, da ta kurbi locozade da ke aje gefenta, sai da ya baima Safiyyah tsoro.

Ba ta san ya ciki yake ba before, amma tana mamakin kazarniyar nata cikin, kullum cikin binta da naushi da juyi yake. Mai nuna shi lafiyayye ne.

Sallamar da ta ji a bakin kofa ta sa ta dagowa a hankali, kodayake tun kafin ta dago din, ta riga ta shaida mai muryar.
Tana daga idonta dan ganin mai sallama sai idonta cikin na Yaya Zubaina, Zubaina-Zubainarta.

Safiyyah da Zubainah suka yi ma juna kuri da ido, na wasu ‘yan sakanni, Zubainah ta saki jakar hannunta ta fadi kasa, saboda firgici, mamaki da al’ajabin ganin Safiyyah da tsohon ciki, turus! A gabanta, gashi ta yi kyau, ta yi das da ita, cikin ya mata gwanin ban sha’awa. Zubaina tace a ranta yau me take gani ne? Safiyyah ce zaune gabanta da tsohon ciki, ko dai daya ce cikin kannenta masu kama da ita da aka yiwa aure of recent?
Safiyyah na son bude baki ta ambaci sunan Yaya Zubaina, at least ko sannu da zuwa ne ta yi mata, domin ko zata ki duban kowa cikin zuri’ar Zayyan banda Zubaina, Zubaina ta so ta ta kaunaceta from day one. Amma ta kasa furta mata komai sai ido data bi ta dashi.
Yau watanni shidda kenan da zuwanta gida rabonta kuma da ganin wani da ya shafi tsohon mijinta Arch. Zayyan Bello da ‘yan Rafindadi duka.

Zubainah sai ta fashe da kuka wiwi, ba tareda ta nedmi ba’asin komai ba, ta karaso da azama ta rungume Safiyyah, da dai ta tabbatar itace ba Sabah ko Rayyah ba, domin akwai wani tabon sujjadah a goshin Safiyyah wanda su kannenta basu dashi, haka kwarjininta da haibarta, ita kadai ta mallakeshi a cikin mutanen gidansu. Zubaina ta rasa kukan me ta ke yi, na farin ciki ko na bakin cikin abinda mahaifiyarsu da dan uwanta suka aikata? Tabbas wannan ciki na Safiyyah sunansa AYAH!
Ammi da ta shigo dakin daga kicin ta riske su cikin wannan hali, Safiyyah kuka Zubaina kuka, ita Safiyyah ganin Zubaida yayi mata fami ne a ciwon da ya samu sauki a ranta, at least ganin Zubaina ya tuno mata da Zayyan da Mama Fatu, wasu kwayan mutane guda biyu da basu yi mata adalci ba a rayuwarta! Ammi ita ke rarrashin Zubaina, ta ce,

“To ya za a yi da hukuncin Allah Hajiya Zubainah? Shi aure rai ne da shi, in wa’adinsa ya cika babu tsumi babu dabara, kada ki dora ma kowa laifi a cikinsu, aure Allah ya kawo wa’adinsa a lokacin da rabo ya zo.

Me zamu cewa Ubangiji banda godiya? Komai Ya yi, komai yaga damar ya kasance mu a wurinmu shi ne daidai”

Zubainah na share hawaye da gefen gyalenta, ta rike hannun Safiyyah katamau a cikin nata. Kamar tana tsoron kada su Ammi su kwace ta. Ta dubi Ammi idonta fal hawaye ta ce,

“Ämmi shi ne ba ku gaya mana ba, kaicon mu bakidaya da rashin waiwaye bayan aikata kuskure tsayin lokaci.

Wannan kadai ishara ne a garemu na cewa auren Safiyyah da Zayyan bai kare ba.
Ta kara da cewa “Ya Jamilal Munzar! (Ya mafi kyawun masu gani)”. Hakika ni Zubainah yau na yi kyakkyawan gani, na ga abinda ya sa ni farin ciki sama da komai a rayuwata”.

Hakuri za ku yi kawai Ammi, Safiyyah ta koma gidanta ta haifi danta ko ‘yarta a dakinta”.
Ammi ta ce, “Inah! Ai babu wannan maganar Hajiya Zubainah, kada ki fara kawo abinda ba zai yiwu ba. Idan Safiyyah ta koma gidanku ma ai ji zan yi don ta yi ciki ne yanzu ku ka canza tunani. Ina! Ai tuni bakin alkalami ya riga ya bushe.
Allah ya yi wa kowa hukunci daidai da abin da ya aikata”.

Ammi ta soma matsar kwalla tana tuno labarin da Safiyyah ta bata a kan Mama Fatu, da irin cin zarafin da ta yi wa rayuwarta shekara da shekaru. Zuciyar UWA ta motsa, ta ji hatta Zubaina bata son gani a gabanta, Zubaina na iya karantar dacin ran dake cikin kalaman Ammi, tana girgiza kai ta mike.

Da kyar ta iya sakin hannun Safiyyah, Safiyyah ta ki bari su kara hada ido da Zubaina don kamanninta duk sun juya mata zuwa na Zayyan sak! Musamman idanunsu. Dama su biyu suke kama da juna a gidansu. Wanda a halin yanzu ko inuwarsa ba ta fatan sake gani a rayuwarta.
Zubaina na gyara lullubinta ta dauki jakarta ta ce, “Ni zan koma Safiyyah, Allah ya sauke ki lafiya.
Ammi Allah ya huci zuciyarki!”.

Daga haka ta fice, Ammi ta yi dan tsaki tana fadin,
“Ni ai ban so suka sani ba har sai kin haife inyaso su dauki dansu ko ‘yarsu su bamu waje, Allah ya hada kowa da rabonsa daga nan”.

Safiyyah dai ba ta ce komai ba, har direban da ya kawo Zubaina Dandume ya ja motar suka bar kofar gidan Malam Usman.
A bayan motar jikin Zubainah har rawa yake yi lokacin da suka hau kan kwalta itada direba, tana wata irin ajiyar zuciya, ta fara danna lambar wayar Zayyan, yatsun hannunta kamar zasu tsinke don karkarwa.

Bai dade da dawowa gida ba daga cikin Estate, ya dan je ne ya taka kafarsa sakamakon dan matsa masa da take yi kwana biyu da tsuka, kasancewar duk abubuwan da ya saba yi a baya, yanzu bai cika yinsu ba, ko kuwa ya daina gabadaya, kamar jogging da suke zuwa kullum da safe da yamma shi da Sophie, hatta exercise da yake a cikin gida a gym dinsa duk ya bari yanzu, so jikinsa baya masa dadi kamar da, a kwanakinnan dole yake dan fita, duk taku daya in yayi yana jin amsa-kuwwar sautin hirarrakin Sophie masu dadi da raharta a kunnuwansa irin wadanda ta saba yi masa idan suka fita jogging.
Har yace a ransa.
“Allah mai zamani!”
Yana shigowa falonsa duk yayi gumi yana tsanewa da tawul da zummar suncewa ya shiga wanka, sai ga kiran Zubaina ya shigo wayarsa. Da sunanda yayi saving din lambarta da harshen larabci;
“Ablah!”
Wato Yayata, ya bayyana akan screen dinsa.
Da ya dubi fuskar wayar sai da ya ce, “Yaushe rabon da Zubaina ta yi masa waya?” Sakamakon fushin da ta ke yi da shi. Yana takawa zuwa cikin master bedroom ya zauna sosai a bakin gadonsa, ya nutsu, sannan ya amsa wayar Yayarsa Zubaina.

“Zayyan… kana ji na?”
Zubaina ta fada, tana haki, kirjinta na hawa da sauka, yace “ina ji Ablah”, ta ce “kullum ka yi sallah ka dinga rokon Allah ya raba ka da aikin dana sani, musamman dana sani mara amfani, wadda in anyi ta bata da amfani, ka rokeshi ya rabaka da biyewa “KAWAR ZUCIYA”, da sauran abinda zuciya ke kawata wa dan Adam mara muhimmanci ga rayuwarsa, ka rokeshi ya rabaka da “gajen hakuri”, ka kuma dinga neman zabinsa kafin ka aikata duk abinda zuciyarka ta kawata maka.

Ka koyi gayawa zuciya “NO” ba komai kike so zan baki ba, sau tari abinda zuciyoyinmu suka fi kwadaituwa dashi ba alkahiari bane a garemu.
Don hakika aurenka da Azeezah ba komai ba ne face bin KAWAR ZUCIYARKU kai da Mama… I’m not against auren Azeezah ko abinda ya riga ya wuce, ko nace auren ta ba alkhairi bane a gareka a’ah, amma kunsa son zuciya da gajen hakuri a cikin yinsa.
Kun biyewa abinda zuciyarku ta afu akai kawai.
Hakika Mama na bukatar istgifari da neman gafarar Safiyyah da iyayenta, in ba haka ba…”
Zubainah ta yi shiru tana haki, sannan ta ce, “Hakki yanzu ya soma bin Mama, da mu zuri’arta, da kai da ka yi biyayya a inda ba muhallinta ba.
Allah ya halatta saki, amma ba Ya sonsa. Allah yayi muku umarnin kara aure amma saboda ibada ba don wasu dalilai na kyale-kyale ko jin dadin duniya ba, naka karin auren na KAWAR ZUCIYA ne. tunda Allah SWA da kansa yace ya ce, ‘la taqnadou min rahmatullah’, wato kada ku fidda rai daga rahmar Ubangiji, sannan ko da ya farlanta yiwa iyaye biyayya a kan umarninsu, akwai hanyoyi da dama da za mu yi musu biyayya cikin hikima a lokaci irin wannan, da suka yi mana umarni mai tsauri irin wannan batareda mun bata musu rai ba, ba kuma tareda mun yi abinda suke so ba.
Let me cut it short, Safiyyah da ciki ka sake ta, ina nufin ta fita da yaron ciki a jikinta, wanda har ya kusa isa haihuwa yanzu.
Kuma wallahi na tabbata da Allah bai kai ni gidan ba, da har ta haihu ba za su bari ka ji ba.
Kowa fa yana son dansa ba Mama kadai ce mai son nata ‘ya’yan ba.
Sai ka san me ka ke ciki yanzu, amma dole ka nuna ka san da cikin, ka kuma yi abin da ya dace a matsayin UBA, ni dai ba za ku yi kuka da ni ba, daga kai har Mama, domin na dade ina nusar da Mama, cewa Da na kowa ne, kaima ina gaya maka ka rike amanar Baba wato Safiyyah a bayan ransa, domin ko me mukeyi Allah yana nuna masa, amma ku duka babu mai daukar nasiha ta sai ta su Zubaidah ‘yan gaban goshin Mama”.

Arch. Zayyan Bello Rafindadi, tun daga sanda Zubaina ta fadi ainahin sakonta, wato Safiyyah da karamin ciki ta fita, ya daina fahimtar sauran maganganunta, banda wannan ya fahimta, jijiyoyin kansa duk sun mike, haka makwallaton wuyansa ya shiga motsi, zuciyarsa ta shiga kai da komowa, tana harbawa da sauri da sauri.
Tsoron Allah ya kara mamaye shi, tausayin Safiyyah ya kama shi, haka tsohuwar soyayya ta soma aikinta, wadda dama kullum a cikinta yake rayuwa, sai karfin tawakkali da kuma ciwon Mama da yanke kafarta da suka zo suka janye tunaninsa daga wannan damuwar zuwa waccan.
A lokacin da Zubaina ta fadi wannan maganar sai da sashen aika sako daga kunne zuwa cikin kwakwalwar Zayyan ya tsaya da aiki na wucin gadi daga kunne zuwa kwakwalwarsa….

Sai ya ga abin da ya kamata ya yi shi ne, ya fadi a inda yake tsaye ya yi sujjadar ban girma ga mahaliccinsa.

Hakika dukkan hikima da buwaya sun tabbata a gare Shi. Bai ga damar ba su haihuwar da suke nema a sanda suke tare ba, sai sanda mai afkuwa ta riga ta afku tsakaninsu.
Zayyan bai san yana hawaye ba, sai da ya ji Azeezah ta ce,

“Lafiya Baby, Maman naku mutuwa ta yi kuma?”

Wani mugun kallo ya sauke idonsa ya yi mata, kafin Azeezah ta ga Zayyan ya tafi kasa cikin sujjadah.
Azeezah ta yi sakare! Tana kallonsa da mamaki da dariya, don ta dauka ya zauce sabida son matarsa, nata cikin wanda akalla ya kai watanni hudu yanzu, itama ya fara tasawa.
Tace
“an gaida Sajjad, Romeo mijin ustaziya Juliet, masu so da amana, masu kauna don Allah”.
Ta kyalkyale da dariya ta sake cewa “Allah dai ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba ya dan yi birgima!”
Bai kulata ba, amma jin taki yin shiru ta barshi ya mori celebration dinsa shi da zuciyarsa yace “Please get out of here!” tace “ba sai ka koreni ba, ba abinda kake tunani ne ya kawo ni ba, don na koyi shan kanwa nima, na sama ma kaina lafiya daga wulakancin ka”.
Tana fita ya shige cikin bargonsa, nan da nan ya hau rawar dari, zazzabi mai zafi ya rufe shi.

A karo na sau ba adadi, yau da dare ya rufe kansa a sassan Sophie, kamar yadda ya kan zo yayi lokaci-lokaci, ya kwanta rigingine rike da wayarsa, soyayya na cin zuciyarsa, ya shiga dialling number din Safiyyah, kamar koyaushe yau ma ce masa aka yi a kashe wayar ta ke. Fatansa yaji muryar Sophie, ko yaya ne a kunnensa, ko ya samu saukin soyayyar dake azalzalar zuciyarsa, koda kuwa zaginsa da ci masa mutunci Safiyyah zata yi.

Daidai inda kafarsa ta ke a lokacin ya ji kamar ya shuri wani abu. Ko da ya duba sai ya ga dalleliyar wayar Sophie ce da ya saya mata da jimawa, ashe a dakin ma ta barta, bata dauka ba.

Zuciyar Zayyan sai da ta yi tsalle daga kirjinsa ta koma, so all this while Sophie babu waya a hannunta take rayuwa?
Sai yanzu ya shiga tunanin shin a wane hali ma Safiyyah ta ke ciki ne bayan rabuwarsu?
“Rainon ciki!cikin bakin ciki”.
Ya baiwa kansa amsa nan take.

Ashe Safiyyah na can tana masa rainon cikin da sai yanzu Allah ya yi nufin bata?
Safiyyah na can tana fama da bakin cikin su shi da Mama, a duka wannan lokacin wajen watanni bakwai, da Mama ta yi masa kandagarki da zuwa inda ta ke……
Ashe Safiyyah za ta haihu! Jinkiri ta samu na alheri?

Da gaske PCOS ba ya hana haihuwa a lokacin da Allah ya nufa.

Ashe zai rike Da daga Sophie…???

Sai ya ji wasu hawayen dadi dana kauna da soyayyah masu dumi suna bin kuncinsa.
Wato shi rai rabonsa ba ya taba karewa, sai ranar da ya koma ga mahaliccinsa.
Ya rasa wa zai kira, Ammi ko Malam, ko kuwa ya kira Rayha tunda ita tana gidan tare da Safiyyah? Ya roketa alfarmar ta hada shi da Sophie a waya?
Sai ya ga duk wannan ba zai fishsshe shi ba, a take ya soma yi wa kansa booking din visa don tafiya Saudiyyah umrah.
Allah ya kamata ya fara godewa, shikadai yake sonsa da rahama da ya kaddari Sophie da samun Dan sa, domin su duka yanzu (Ammi, Malam da Rayha) baida wani muhimmanci a wurinsu.
* * ****

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *