⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 6: Chapter 6

Zubaina tun komawarta Kano ta bubbuga wa duk ‘yan uwanta waya ta ce lallai-lallai duka gobe su hallara gidan Zahra gaban Mama.
Mama Fatu wadda tun jiya da Zubainah ta dawo daga Dandume ta tsaya a Kaduna ta labarta mata abin da ta gano, Mama Fatu ke fama da zazzabin shock. Kwarai labarin ya yi mata kyakkyawan duka, tun jiya ta ke istigfari cikin ranta tana kara raina kanta, izza na fita, tsoron Allah da nadama na mamaye ta.

Tun jiyan ta ce da Zubainah ta kai ta Dandume domin ta nemi gafarar Safiyyah da iyayenta,
Zubaina ta ce, “wa? Ai ni kunya ba za ta bar ni in koma ba Mama, ku da rashin kyautawa ni da ji muku kunya.
Kuma yanzu sai ki ce ga ki kin zo bada hakuri saboda Safiyyah na da juna biyu?
Habawa Mama! In maye ya manta!
Ai in ido da kwalli baki da jambaki, ni kam ba zan sake kara saka kafata a gidansu Safiyyah ba.
Roko daya zan yi miki, ki cire ma Zayyan kandagarkin da ki ka saka masa na zuwa inda Safiyyah ta ke, domin ya samu ya je inda ta ke, ko don ya nemi gafararta”.
Mama ta kada ta raya a kan Zubainah ta raka ta Dandume, amma Zubainah ta murje ido da girman Mama daga idonta tace, “Mama wanda ya ja ruwa shi ruwa kan doka shi kadai, ni dai ina jin kunyar Ammin Safiyyah, ko mahaifinta ban nema ba, don haka ba zan iya raka ki ba”.

Zubaidah ce farkon isowa washegari kafin su Zaytoon. ‘Ya’yan Mama bakidaya sun hallara a gabanta. Mama na daga kwance cikin katifa a dakin da Zahra ta bata, ta dubi ‘ya’yanta mata duka su biyar a zazzaune a gefe da gefenta, Zayyan ne kadai babu, ta dubi gundulmin kafarta da crutches dinta dake gefe, sai kawai Mama ta fashe da kuka.
Da farko ta ce musu, “Hakika na zalunci Baffa ta hanyar shiga lamarin gidansa, na zama fitinanniyar uwa marar godiyar Allah da surukar da Allah ya hada ni da ita, yau na ga aya yaran nan, wai Safiyyah da ciki ta fito daga gidan Baffa”.
Mama ta ce, “Ku ne kawayena, ku ne abokan shawarata, kune ‘yan uwana mafi kusanci, kuma ko me na yima iyalin Zayyan tare da ku ne, don haka dukkanmu za mu dunguma zuwa ga Safiyyah da iyayenta mu nemi gafararsu. Son samu mu roki alfarmar dawowarta garemu”.

‘ya’yan Mama daga wadda za ta ce, Mama ni dai bazan iya zuwa ba, sai mai cewa Mama babu ruwana ke kika fara kiranta Diyar Alaramma, ni ma shi ne na kama”,
Sai kuma wadda za ta ce, “nan duniya Mama ban taba ganin mai hakuri da jarabar suruka irin Safiyyah ba, domin ta jure wa gorinki da kaifin halshenki Mama.

wajen wulakanta martabarta”,
Yaya Zubaidah ta ce,
“Mama cewa nake ba ke ki ka zabo Azeezah da kafarki ba, ban ga ranar da zuwanta gidan Baffa ya yi miki ba, abinci wannan na marassa lafiya bazata iya baki ba, a matsayinki na wadda ta haifa mata miji! Balle mu ‘yan uwansa idan mun ziyarcesu.
Na rantse da Allah banda arzikin Baba Murtala da ranar nan sai na jibgi Azeezah, dukan da ko uwarta bata taba yi mata ba, kan diban karen mahaukaciyar da ta yi mana da muka je duba ta da bata da lafiya. Da karuwancin data yiwa Baffa a gabana, shikuma ya biye mata. Mama ‘yar bariki kika aurawa Baba da sunan ‘yar babban gida. ‘yar taka haye a barikin amma ba ‘yar na gada ba. Wato bata gaji barikin ba a duniya ta dauki abinta.
Ba mu gaya miki ba ne Mama, don mu muka dauki kafa muka je musu”.
In ji Yaya Zubaida tana hawaye.

Haka suka yi ta maida zance a kan rashin mutuncin Azeezah wanda a cewar kowaccensu ta ci arzikin Baba Murtala, in banda haka da yanzu ba wannan zancen ake yi ba.
Zubaina na gefe tana jinsu tana mamakin irin halayen Azeezah da suke fadi, amma laifi guda daya na Sophie cikinsu an rasa wadda za ta zayyano shi. Laifinta daya ne kenan a wurin Mama da iyalinta, wato;

“Baffa na matukar sonta!!!”.

Shine dalilinsu na daukar karan tsana su dora mata.

Nan suka koma fadin irin alkhairorin Safiyyah, wadanda Mama ke gwasalewa a kodayaushe. Da irin ladabi da biyayyar da ta ke yiwa Mama, amma ko kadan Mama ba ta gani. Kawai don Babanta Alaramma ne basu da abinda zasu baki Mama, kuma kina zarginsu da tsubbace Baffa wanda kowa ya san mahaifinta ba irin wadannan malaman bane malamin karantar da addini ne kawai.

Mama dai ta sunkuyar da kai ta kasa musa ko guda cikin abinda suke fada mata yau, a karshe suka yanke shawarar tafiya Dandume dukkansu, suna roko da lallashin Zubaina tayi hakuri ta raka su.
Sun shirya tafiyar a washegari, cikin babbar mota Range Rover, wadda tun jiya Arabi yayi mata (full tank).

Mama suna hanyar shiga Katsina ta kira Zayyan a waya, jin muryarsa ta yi wani iri kamar bai son amsa wayarta. Bata san cikin bargo yake ba tun jiya yana fama da zazzabi da masassara.

A lokacin da yake gaida Mama, muryarsa a dakushe take, sai Mama ta dauka Zayyan ma ya taho daga rakiyarta, ta kara jin firgici da nadama da tsorata da al’amarin Ubangiji.

Tun kafin ya gama gaisuwar Mama ta ce.
“Baffa am, nace kana cikin nutsuwarka dai ko? Na ji ka kamar mara lafiya?”
Zayyan ya ce, “Mama lafiyata kalau, kaina ne dai yake dan ciwo”.
Ta ce,
“Ayya Baffa sannu! Na janye kalamaina kaji Baffa, kaje ka maido matarka in kana da bukatar zama da ita. Da albarkata da yawun bakina.
Ka yafe min Baffa, na shiga rayuwarku, ka yi kokari ka dawo da matarka cikin albarkata ta haihu a dakinta”.
Ba don Mama ba ce cewa zai yi da ita, “ta baya ta rago”, koko ya ce.
“Mama mun riga mun baro kari tun ran tubani”.
Wani irin bakin cikin Mama ya ji ya zo ya lullube shi, wanda a can baya bai taba jin irinsa ba.

Mama jin Baffa ya yi shiru, sai da ta sha jinin jikinta, murya na rawa ta ce, “Baffa kana kan layi? Ka yafe min Baffa, ka yafe min, na tabbata ban kyauta ba, ta hanyar shiga hurumin iyalinka…”.

Da sauri Zayyan ya katse Mama, jin alamar tana kuka,

“Mama ko me ki ka yi a kaina kin isa ne, kuma ko me ki ka yi gare ni ko iyalina shi ne daidai ni a wurina.
Damuwata daya ce Mama, ta yadda har cikin Safiyyah ya kai tsayin wannan lokacin ban taba sani ba”.
Ya dakata yana sauke ajiyar zuciya, kafin ya ci gaba da cewa.
“Mama duk abinda ki ke tunanin kin yi mana ba daidai ba kona rashin kyautawa, wanda na sani da wanda ban sani ba, Mama na yafe miki shi, ina rokon Allah ya sa Safiyyah ta yafe mana bakidaya, yasa jinyar nakasarki ta zame miki kaffara!”.

Mama ma daga can bangarenta sai da ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta share hawaye da mayafinta, jin Zayyan ya yafe mata ya rage mata nauyin zuciya. Ta sanar da shi suna hanyar isa Dandume yanzu, za ta je neman gafarar iyayen Safiyyah da nema masa yardarsu a kan komen Safiyya.

A kofar gidan Malam Usman, direban Mama Arabi da ya tuko Mama da ‘ya’yanta ya kashe mota, su duka kokarin taimakawa Mama suke ta fito daga mota, da taimakon “Crutches” dinta hagu da dama, tana dogarawa suka yi sallama a tsakar gidansu Safiyyah.

A nan tsakar gidan su Safiyyah wanda ya sha shara tsaf ko alluranka ce ta fadi za ka tsince abarka nan da nan, sabida tsaftarsa. Nana Safiyya ce zaune da tirtsetsen cikinta a gabanta, tana sauraron radiyo, makaranci marigayi Ahmad Isa na karanta mata littafin HASNA’U ‘YAR NAJERIYA tana sauraron labarin Hasna-Zabiya. Ammi na madafi tana girkin dare suka ji sallamar Mama da ‘ya’yanta a tsakar gidan su.

Safiyyah ta dago ido cikin amsa sallamar masu shigowa, don ko daya bata kama murya ba, sai ta ga wata mata kamar Mama na dogara crutches da kyar da kafa daya, kamar dai Mama amma a zuciyarta ta kasa gasgata cewa Mama ce ta shigo da kafa daya.
In banda ganin Zubaidah da ke tare da ita da bazata gane Mama bace, to ganinsu gabadaya yasa ta kara tabbatar da cewa da gaske Mama Fatu ce.
Ammi ta amsa sallamar masu shigowa daga kitchen ba tare da ta san ko su waye ba.
Bayan dan lokaci sai Ammi ta fito daga cikin madafin tana ce ma Safiyyah dake zaune a inda take kamar an kafeta da ganin masu shigowa, wadanda ko a mafarki bata taba yin na zuwansu gidansu ba. Ammi tace.

“Kin tsaya kina kallon baki ba ko shimfida balle kiyi musu maraba, halan gyangyadi kike a zaunennan Nana Safiyyah?”
Sauran maganar malakewa ta yi a makoshin Ammi itama, ganin wadanda ke shigowa ‘yan Rafindadi ne, ga Mama a kan crutches tana dogarawa da kyar take cira lafiyayyar kafar. Ammi ta hadiye wani zazzafan miyau a wuyanta, sannan ta kawo zuciyar musulunci ta dorawa ranta, ta saisaita kwayar idonta a kansu tace.
“A’ah, mutanen RafinDadi ne yau a gidan namu? Sannunku da zuwa, maraba lale marhabin”.
Ta shimfida musu katuwar tabarma Mama kamar ta nitse cikin kasa don borin kunya, ganin cikin Safiyyah ya yi tororo a zaune kamar zai fasa zani.
Zubaina tace ma su Zahra da ke tsaye suna kallon Sophie kamar an zare musu lakka.
“Ke Zaytoon kuna zama ne ko juyawa zaku yi?”

Da sauri suka fara zazzaunawa a shimfidar da Ammi ta yi musu. Ammi kin zama ta yi a gaisa yadda suka zata, kamar yadda Mama ke kokarin su gaisa, sai kakarin maganar take yi amma ta kasa fidda kalmar da zata bada ma’ana ko daya daga bakinta.
Kai tsaye sai Ammi ta wuce zuwa turakar Malam, ta barsu a wurin suna raba ido a tsakaninsu.
Mama dai idanunta ne suke ta kyaftawa su kadai cike da nadama, ta kasa cewa Safiyyah komai, itama kuma Safiyya tun amsa sallamarsu da ta yi sai ta sunkuyar da kai, sakamakon wani mulmulallen bakin ciki da ya zo ya tokare ta a makoshi.
Ganin Mama cikin wannan halin na rashin kafa ya kara ma Safiyyah tsoron Allah, amma bai wanke mata tsohon radadin Mama ba, tana tunanin ta tashi ta bar wurin Malam da Ammi suka fito a tare.
Wannan ya baiwa Safiyyah damar mikewa da kyar da dafa bango ta shige dakin Ammi, ta barsu a wurin tareda su Malam.
Karshen kaskantuwa da kunya Mama ta ji a ranta, wai yau Safiyyah ce ta wuce ta gabanta bata ko gaishe ta ba? Lallai girma ya fadi. Da ma kuma shi mutunci madara ne, in ya zube ba ya kwaso.
Safiyyah kuwa tana shigewa daki har da kullo kofa, tareda sanya sakata. Zuri’ar Mama! Allah ya yi mata katangar karfe da su kawai. Darajar umarnin musulunci Mama ta ci, da har ta amsa sallamarta, amma ai an ce shimfidar fuska ta fi ta tabarma.
Malam na isowa wajen su daga can gefensu Hajiya Fatu ya zauna, kan kujerar roba a tsakar gidan, su Zubaida na ta gaishe shi yana amsawa a nitse yana duban Mama yaga ba kafa daya ya tuna Baba Murtala ya gaya masa tayi jinya, ya ce,
“Assha, subhanallahi! Hajiya Fatu jinya aka yi haka?”
Mama sai kawai ta rufe fuska da mayafinta ta saka kuka ganin Ammi ta yi komawarta kicin, ta ci gaba da girkinta bata kara bi ta kansu ba.

Mama ta jima tana kukan nadamarta a gaban Malam Usman, wadda ko kusa bata taba zuciyarsu shi da Ammi ba, sun dai zuba ido da kunne suna kallo da saurarenta don jin da wacce tazo kuma yau, kafin ta ce,
“Malam na san ban isa in ce na zowa Baffa biko ba, amma na zo in baku hakuri in kuma nemi gafarar Nana Safiyyah.
Hakika ba ni da bakin cewa komai illa ku dubi Allah da albarkar rabo da aka samu kusa Safiyyah ta yafe min.
Ni wata irin mai dimbin laifi ce ga Safiyyah daku bakidaya, wadda tun a gidan duniya naga ishara, na kuma yarda rabon da Safiyyah ta samu a yanzu, bakomi bane face ayar Allah ne a gare ni.
Yau zan fada da baki na hakika na dade ina zaluntar Safiyyah amma wallahi na yarda kaina da Baffa na zalunta”.

Mama ta dakata tayi sharbe, ta share hawaye da gefen mayafinta, Ammi dai na jiyo su daga kitchen ta hau tsaki a fili tana cewa a ranta, ta baya ta rago dai Hajiya Fatu!
Tana iya jin sanda Malam ya bude baki ya yi bismillah ya kori shaidan da a’uziyya, sannan ya gyara zamansa a kan kujerar roba ya soma ce da Mama.
“Ni bazan ce komai ba Hajiya Fatu, tsakaninku ne da ita Safiyyah, shi dan Adam ai ajizi ne, ga ku ga Nana Safiyyah din, ku yi sulhun matsalolinku a junanku, don ni wasu ma har yau ban san su ba. Bata taba kawo min kararki ba. Allah yana son masu sulhu don har yace “sulhu alkhairi ne”, amma tabbas baya yafe hakkin wanda aka zalunta”.
Daga haka Malam Usman ya mike yana karkade babbar rigarsa yana cewa,
“Hajiya Fatu zan shiga daga ciki, Allah ya kara lafiya, Ya sa jinya ta zamo kaffara”.
Ammi ta fito daga kitchen ta ga Safiyyah tuni ta rufe kofarta bam! Albarkacin idon Zubaina Ammi ta dan zauna suka gaggaisa, Mama ta ce.
“Hajiya Hafsatu ku yi hakuri ku gafarce ni, ba akan abu daya ko biyu ba a’a, akan komai, ba tare da na ce komai akan laifuffukana gareku ba. Na yarda ni azzalumar suruka ce wadda ba ta da kara da kana’a akan ‘ya’yanta kuma mai tsananin son kanta da biye wa KAWAR ZUCIYArta”.

Mama ta dan dakata tana share hawayenta tareda kokarin shirya abinda zata fada next, sai Ammi ta ce.
“Madalla da yau ki ka zo har gabanmu da kanki kika tabbatar mana da bakinki cewa kin zalunci Nana Safiyyah. Allah yana son masu afuwa, amma ni Hafsatu uwar Safiyyah ba zan taba manta halin da Nana Safiyyah ta zo min ba cikin dare har duniya ta nade.
Hajiya Fatu kina da ‘ya’ya mata, sai in ce Allah ya yi wa kowa hisabi daidai da abin da ya aikata”.
Mama da ‘ya’yanta jikinsu ya kara yin lugub, don Ammi har cewa ta yi, “fulatanci fa ba hauka ba ne Haj. Fatu, kara ne. Amma kowa ya haifi da ya san darajar shi, kuma yana son abinsa, ba ke kadai ce kika haifi Da ba, sannan aure da yayi masa don ibadar Allah ne da bin umarninsa ba don yaje yayi bautar suruka bane ko dangin miji.
Ni Hafsatu kada Allah ya ba ni duk wata dama da zan cutar ma surukaina akan suna auren yarana”.
Yaya Zubaina ganin kukan Mama ya karu, sai hakan ya taba zuciyarta, don uwa-uwa ce, da farko ba ta yi niyyar saka baki ba, taji dadi da yau Ammi ta janye kara gefe tace tana son ‘yarta, amma yanzu dai itama Zubaina tausayin tata uwar yasa itama ta magantu.
“Ammin Safiyya, ai ba’a tona rubabben kwai, yarwa ake yi.

In aka ce neman afuwa aka zo da neman sulhu, to sai a bar kaza cikin gashinta yafi alkhairi.
Yafiya muka zo nema Ammi, babu batun tono abinda ya riga ya shige.
Sannan Ammi ina son sanar daku cewa, ku cirewa Baffa kullacin ku, wallahi Baffa (Zayyan) ba shi da hannu a komai. Yana son Safiyyah har abada! Komai da ya yi, ya yi shi ne bisa umarnin Mama don tsira da biyayyar mahaifiyarsa.
Yau ga Mama ta zo da kanta tana neman afuwarku Ammi, ta yarda tayi laifi, muma ‘ya’yanta masu tarin laifuka muna taya ta bada hakuri da neman sassaucinku”.
Ammi tana ganin mutuncin Zubaina har gobe, saboda Zubaina taso Safiyyah saboda Allah a cikin duka ‘ya’yan Mama. Ammi ta ce “wannan ai tsakaninku da Nana Safiyyah ne, mu meye namu a ciki? Kamar yadda Malam ya ce, nima haka na ce tsakaninku ne da ita”.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *