Chapter 8: Chapter 8
Sai ya yi shiru.
Malam yace,
“na’am, Zayyan yaya dai?”
Duk da amsar malam bata yi masa dadi ba haka ya daure. Ya fizgo furucin da yake ganin dashi ya dace ya tunkari Malam a wannan lokacin.
“Malam da ma na zo gaida ku ne!”
Malam yace “madallah, mun gode da gaisuwa madallah, yaya iyalin da fatan suna lafiya”.
Zayyan ya dukar da kai, yau shi da Safiyyah bai san wa yafi wani iya stammering ba, domin shima ya zama stammerer, lokacin da ya hau ce da Malam cikin in’ina.
“Malam ku amince cewa kaddararmu kenan ni da Safiyyah, wadda Allah ya riga ya rubuta mana, wallahi Malam ban yi da gangan ba”.
Malam ya yi murmushi ya ce, “Ni ma na yarda Zayyan ba ka yi da gangan ba. To amma ni me ka ji na ce? Na fi ka sanin cewa kaddararku kenan, tunda komai mukaddari ne.
Shiyasa ma baka ji na nemeka ba, ban kuma amsa kiran wayarka ba don nafison kazo gabana da kanka ka jaddada mun, cewa Nana Safiyyah ba matarka bace yanzu, mun karbi wannan kyakkyawar kaddarar da hannu bibbiyu, Ya Rabb! Allah ya baima Nana Safiyyah ikon cinye ta, kai kuma Allah ya baka ladan biyayyar mahaifiyarka, ka sani wanda yayiwa Uwa biyayya akan duk abinda take so, baya tabewa!”.
Malam da zuciya daya ya fadi maganarsa, amma shi Zayyan da yake cikin guilt sai ya ji tamkar Malam ya fada da harshen damo, kunya da nauyin iyayen Safiyyah ba zai daina jin su ba, watakila har duniya ta nade.
Malam ya kawar da komai daga zuciyarsa. Ya tambayeshi lafiyar Shaheed. Ganin yadda duk Zayyan ya kasa sakewa yau a gabansa, nan ya gayawa Malam Shaheed din yana lafiya ya baro su Abuja.
Amma ko kadan Malam ya ki ya yi masa zancen da yake son ji, wato ya ki yi masa zancen Safiyya ko maganar cikinta.
Daga bisani yace dashi,
“Ai kwanaki su Hajiya Fatu sun zo, ashe Hajiya ta sha jinya haka?”
Zayyan ya ce, “Umh!”
Malam ya ce, “Kaffara, insha Allahu”.
Sai duk suka yi shiru. Malam ya tuna tarin alamajiran dake jiransa sai ya shiga tattara littattafan gabansa don barin falon, dalibai sun cika makil a zaurensa, suna jiran ya fito su fara karatu.
Zayyan ya lura Malam so yake ya fita, sai ya rasa ta ina ma zai fara. Da a can baya ne Malam zai iya dakatar da dalibansa zuwa wani lokacin, saboda ya tattauna dashi, musamman in ya lura da cewa yana so su tattauna a kan wata muhimmiyar maganar ne.
Amma yau ga Malam yana son tashi ya bar shi a wuri, sai ya ji duk gaba daya ya muzanta.
Malam ya kammala tattare littattafansa, yace,
“To Zayyan zan shiga bada karatu, ga Ammin naku tana tare da bako”.
Zayyan bai san sanda ya dago fuska fal damuwa ba, ya ce,
“Malam na san ka fi ni sanin cewa duk dan Adam mai kuskure ne, balle ni da kuskuren nawa na yi shi ne a cikin biyayyar UWA.
Ka yi hakuri Malam ka daure ka zauna ka saurare ni, ko na minti biyar ne don Allah Malam…
Ni nasan da Baba Bello yana raye da duk abinda ya faru bai faru ba. I need your guidance and prayers Malam! Tun barin Sophie rayuwata komai ya jirkice min Malam. Na daina nutsuwa akan harkokin nema na, na daina jin dadin komai a gidana, iyalina sun kasa jin dadi na, gani nan ne kawai. Ko ban ci arzikin komai ba in ci arzikin Baba Bello ka maidomin Sophie mu raini cikin danmu tare”.
Malam jikinsa ya yi sanyi, amma duk da haka yaga cewa yau ya kamata yayi ma Zayyan raddi ko yaya ne, daidai da abinda yace masa yanzu. Makaho bai san kana kallonsa ba sai ka zungure shi. Iya kawaici da kara yayi wa Zayyan da Hajiya Fatu a matsayinsa na Uban da ya san cewa Da na kowa ne, amma yau ranar data dace ya dan maida martani ce ko ba mai zafi ba.
Ya ce “Yanzu ne kuka tuna marigayi Bello Rafindadi mutum ne mai kima a idanun kowa?
Ko kuwa son haihuwa da ya rufe muku ido a baya kai da mahaifiyarka shi ya sa kuka mance da amanar Safiyyah da ya sha baku kuka keta mata haddi, kai da mahaifiya da ‘yan uwanka?
Malam ya ce, “To shi ke nan Ridhwan, hakan ya yi, Allah ya kawo ka lafiya, don dama ina nemanka ne”.
Ridhwan ya ce, “Ina fatan komai da kowa lafiya dai ko Malam? Ya wajen ‘yan Abuja dasu Sabah masu haihuwa?”
Malam ya ce, “Ridhwan a kan kanwarka taka ne Nana Safiyyah dama nakeson ganin naka…”
Kawai sai ya kashe wayar ya bar Sheikh da sake-saken to me ya samu Nana Safifin?
Sheikh shikadai yake kiran Safiyyah Safifi.
Kamar yadda ya alkawartama Malam, yana sauka a filin jirgin saman Kano sai ya dauko shatar taxi da jakar kayansa ta kawo shi har Dandume.
Already Malam ya gaya wa Ammi batun zuwan Sheikh yau, don haka sun yi shirin tarbarsa sosai ita da auta Rayha. Don Safiyyah bata aikin komai bata cas bata as sai ci da kwanciya ko motsa jikinta bata son yi.
Rayha akwai kokari, don duk ayyukan gidan nan ita ke yi wa Ammi. Ammi kuma tayi girki da kanta komai yawansa bata so a saka mata hannu.
Yau Safiyyah ta je ante-natal tun sassafe, ba ita ta dawo gida ba har Yaya Sheikh ya dade da isowa gidan.
Dr. Ridhwan Usman Dandume (Yaya Sheikh) da Malam da Ammi suna falon Malam bakidayansu, kasancewar yau Alhamis ce. Malam din bashi da dalibai, malam ya kwashe komai tun ranar da Safiyyah ta zo musu cikin dare wutsiya a zage. Ta kwana bata yi magana ba, bata ce musu komai ba. Har zuwan su asibiti daga baya da Ammi, da bayyanar maganar cikinta, da kuma tabbatuwar saki da ya shiga tsakaninta da Zayyan a yanzu.
Ridhwan yayi zugum! Amma tun daga saman goshinsa har yatsan kafarsa, wani irin jibi ke tsattsafo masa (zufa), deep down inside him, kuma wani irin mazari yake yi.
Da Malam ya zo wajen zuwan Innar Zayyan, Hajiya Fatu gabansu ban hakuri, Yaya Sheikh bai san sanda ya mike tsaye ba, ya ce, “Malam daina yimin zancensu haka. Rainin hankali ne dasu of the highest order!.
Ai tunda ta yi wannan kuskuren tasa ya saketa ta, to matar nan ta yi ta gama insha Allahu Malam.
Safifi ta dawo gida, hannun masu kaunarta yanzu. Na roke ka Malam kada ka kara bari wani cikin danginsa ko shi da kansa ya kara tako mana gida daga yau don Allah Malam, na san ka da sanyin rai, ba wuya an kalallameka da dadin baki, wallahi in Zayyan ya kara zuwa gidan nan sai na yi kararsa.
Tunda dai ya sake ta shi ke nan, kurunkus.
Idan Safifi ta haifi dan dake cikinta ma na rantse nata ne ita kadai. Ban taba ganin mutane marasa mutunci ‘yan rainin wayo irin Zayyan din nan da mahaifiyarsa ba.
Kuma don rashin kunya sai suka zo gabanku, suka ce ta koma ko me? Saboda yanzu ta yi juna biyu ko? Malam ban sanka da raunin zuciya ba, nadai sanka da saurin yin uzuri sau saba’in, na roke ka kada ka bari mutanen nan su yi galabar zalunci a kan Safifi a karo na biyu.
Ka godewa Allah data dawo gida lafiya ba su hada ta da tsarabar ciwon damuwa da na hauka ba.
Ai ni Malam wadannan surukan naka ban yarda da cikar imaninsu ba, wanda zai ja da cewa haihuwa ta Allah ce bata mutum ba, yin Allah ce ba iyawar mace ko ta miji ba, to ba gidan zama bane a ganina. Malam ko kuna so ko ba kwa so auren nan ya kare, ko da kuwa Safifi na son komawa”.
Shaikh magana yake cikin fushi da bacin rai tamkar Malam ne Zayyan din. Ko kuwa ance ga Mama Fatu a gabansa.
Malam ya ce, “Kwantar da hankalinka Ridhwan, ai surukinsa ma ya zo wato aminin ubansa baban amaryar, kuma abinda na gaya masa shi ne, ni bani da hurumin maida auren Safiyyah a halin yanzu, tunda sunanta bazawara, kuma har ga Allah iya hukuncina kenan.
A wannan karon komai na rayuwarta yana hannunta, zan ba ta cikakkiyar dama ne da addini ya bata, ko shawara bazan baiwa Nana Safiyyah ba”.
Yaya Sheikh ya ce cikin fushi,
“Ai ko Safifi tana da ‘guts’ na nuna tana son komawa wannan kurkukun soyayyar nata, sai idan ba na numfashi a kusa da ita”.
Ko abincin rana lafiyayye da Ammi ta ajiye masa ya kasa ci, ya shiga dakin Ammi da suka gama magana da Malam ya zauna, kawai sai ya zurawa zanen hoton Safiyyah da ke dakin Ammi ido, wanda Safiyyah ce ta zana kanta da kanta. Kyakkyawar fuskarta data yi reflecting Nana Safiyyah ta gaske na tuna masa kacaniyar kuruciyarta da dabdalar yarintarsu gaban Ammi cikin kauna da soyayyar Uwa.
Ko a baya da ya zuba ido kan bacin ran da Sophie ke ciki a gidan Zayyan, a dalilin rashin haihuwa, don bashi da yadda zai yi ne, tunda a karkashin auren Zayyan take. Amma a yanzu? Ya yi rantsuwa sai inda karfinsa ya kare wajen kwato wa Safifi ‘yanci daga komawa kurkukun Zayyan da mahaifiyarsa, da kuma wajen ganin ya samar mata da dauwamammen farin ciki da canjin rayuwa.
Yana wannan tunanin sai ga Sophie ta shigo dakin mayafi da jaka a hannu, tana tafiya da kyar. Ridhwan ya daga ido yana kallon kanwarsa Safifi da tsohon ciki yau, wanda a yanzu ya shiga watanninsa takwas cif. Cikin ya yi tororo, ya yi tsini kamar na haihuwar yau ko gobe.
Sophie na cewa,
“Wash! Ammi kafata!” Ammi tace “sannu, ai gara ki dinga motsa ta din in ba haka ba kika zo haihuwar ke zaki gayawa aya zakinta”.
Ta yi ido hudu da Sheikh a zaune a falon Ammi, ya tasa warmers din abincin da Rayha ta jere masa a gabansa ya ko kasa bude ko daya.
Safiyyah na shigowa dakin ta ganshi sai fuskarta ta washe da fara’a, ta ce, “Yaya Sheikh? Saukar yaushe? Wata sabon gani, barka da zuwa mutanen Arkansas, ina ka baro min Antina Assafe?”
Sheikh ya harare ta sosai daga sama har kasa, ya kuma ki bata amsar tambayoyin data jero masa ko daya, har ta gaji da tsayuwa ta samu kujera mai cin mutum guda ta baje a cikinta. Ta duka kadan tana gaida Yaya Sheikh.
“Yaya Sheikh inata magana ina ta maka barka da zuwa ka kyaleni”.
Safiyyah ta fada a shagwabe, ya yi kamar ba zai amsa ba sai kallonta da yake cikin mamaki da tausayi. Da kyar ganin fuskarta ta soma shiga damuwa da kin amsa ta da yake ta yi, ya ce, “to ni Safifi me zan ce miki banda na gode? All this while kina gida gabansu Ammi, cikin wannan mawuyacin halin, ni da Assafe ba wanda ya sani?
Hakan yasa na san matsayin mu a gunki ai yanzu, kuma da sannu zan wayar mata da kai akan ta ragema ranta damuwa da lamarinki, don ita ba nan kusa ta aje matsayinki a gunta ba, babu ranar Allah da zata fito ta fadi bata ambaceki ba, na dauka mune mutane na farko da zasu fara sanin Zayyan da yafi sauran maza iya daukar wanka ya gama cika alkawarin soyayyarsa?”.
Ya fada cikin gatse da dakewa.
Safiyyah ta langwabar da kai ta ce, “Yaya Sheikh, wallahi ba ni da laifi, ni meye nawa a cikin wannan maganar? Wannan ai tsakanin ka dasu Ammi ne”.
Ya ce, “Kema har da ke, meye a ciki in kin dauki waya kin gaya min auren wahala ya kare in Ammi taki gaya min? Kodayake na san kunya ki ke ji yau ki ce min da bakinki wanda ya fi ni kyau, boko da gayu, da iya daukar wanka, yau ya gaji da in’inarki ya sallamo ki ko?”
Safiyyah ta wara idanu waje tana kallon Sheikh da budaddun idanu na jin haushi, kamar ba ita ta fadi wannan maganar a gare shi shekaru goma sha hudu da suka gabata ba.
Mantawa take yi Yaya Sheikh bashi da mantuwa sam, in dai a kan bakar magana ne, data sani ko kusa ba ta furta masa wannan zancen daya kasa mantawa tun tana budurwa ba.
Yaya Sheikh ya ga fuskarta ta muzanta, duk sai ta bashi tausayi, ga nauyin ciki, duk cikin ya kumbura ta ya kumbura siririn hancinta. Safifi will forever remain his favourite sister, she has a special place in his heart, amma yau da ya ganta cikin wannan halin na dakon tsohon ciki, fuska ta kumbura, hanci ya bude yayi fadi irin na masu tsohon ciki, ji ya yi ba wanda yake son ya dauwama yana kallo a duniya kamar Safifi.
Hira yake so su yi a kan yadda rabuwarta da Zayyan ta afku, amma ya kasa tambayarta komai. Itama sai tayi shiru, ta sunkuyar da kai tana wasa da zara-zaran yatsun hannunta.
Daidai lokacin Ammi ta ceci shirun nasu, wato ta shigo tana ce masa, ya je Malam yana kiransa.
To bayan fitarsa ne sai ta gayawa Ammi yadda suka yi da likitarta, ta ce mata (CS) za su yi mata ranar cikar EDD dinta, (pro lapsed umbilical cord) aka gani a scan din yau ya sauka cervix ya tare Babyn.
Ammi ta shiga jimami mai yawa, ta ce, “Bana son fida a haihuwa wallahi, amma tunda suna ganin ita ce mafita kuma ta zama dole, to Allah ya sa a yi lafiya ya budi idanunku keda jariri lafiya”.
Dr. Ridhwan ya dawo dakin ya zauna, bayan ya sallami malam, sai Ammi ta gaya masa batun CS da likita tace za’a yi mata next month.
Dr. Ridhwan ya ce dole a canza asibiti a koma babban asibitin Katsina, tun kafin lokacin.
Da Rayha ta kammala girkin dare ta zubo ta kawo ma Yayan nasu za ta fita, ya ce ta zauna a gefensa.
Rayha ta nemi waje can gefen Yaya Sheikh ta zauna, ya ce, “Wato ke Rayha kin gagari su Ammi ko? Anyi-anyi ki fidda miji kin ki. Malam ya gayamin ya rasa gane inda kika sa gaba”.
Rayha ta sadda kai cikin damuwa, tana cewa, “Yaya Sheikh na dade da gayawa su Ammi, a kara min lokaci”.
Sai Sheikh ya ce.
“Ko zan san dalilinki Rayhanah?”
Sai kawai Rayha ta rufe fuska da mayafinta, ta soma kuka, har abin ya baima Sheikh tsoro, don bai ga abin kuka cikin tambayar da yayi mata ba. Rayha ta ce,
“Yaya Sheikh ni yanzu ba zan iya auren kowa ba, ina duba da rayuwar Yaya Safiyyah ne.
Ka duba ka gani dai Yaya Sheikh, wane irin so ne bamu ga Yaya Zayyan ya yiwa Yaya Safiyyah ba, yana matukar sonta kamar me, amma mahaifiyarsa ta hana su zaman auren.
To ni ma akwai wanda muka yi alkawarin aure da shi tuntuni yana Russia ne yana karatu, to Yaya Sheikh mahaifiyarsa na raye, ina tsoron matsalar uwar miji don duk son da miji zai maka idan uwarsa bata son ka aikin banza ne.
What of idan nima nazo ban haihu da wuri ba fa? Ko kwata-kwata ban samu haihuwar ba? Aka zo aka sake ni nima aka tara mu gaban Ammi again? Bana son sakin aure Yaya Sheikh, bana so a kira ni bazawara”.
Sheikh da Safiyyah duk suka yi murmushi, jin tunanin Rayha akan abinda ya samu Yayarta, at the same time duk suka ji babu dadi suma a kasan ransu.



