⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 9: Chapter 9

Safiyyah ta dade da sanin cewa rayuwarta mudubin dubawa ce ga kannenta mata, shi ya sa ta yi ta hakuri, da wasu abubuwan da yawa a gidan Zayyan, ba ta san ma su Rayha suna hankalce da rayuwarta irin haka ba, sai Yaya Sheikh ya girgiza kansa ga Rayha yace,
“Rayha ba lallai abin da ya faru da dan uwanka kai ma sai ya same ka ba. Kowa da irin kaddararsa. Besides, zawarci ba shi ne karshen rayuwa ba, sannan ba abun kunnya bane, ba shi ne karshen farin cikin diya mace ba. Wani auren da cigaba da zama cikinsa gara rabuwar.
A irin wannan lokacin, abinda macen da kaddarar zawarci ya sama ta ke bukata shi ne, soyayyar iyaye data ‘yan uwanta, da kuma nema mata hanyoyin da za ta yi adjusting, ta kuma samu rayuwarta ta gaba tafi ta baya bata farin ciki.

Sau da dama mutane ne ke sanyawa zawarci ya munana ga mace, ta hanyar canza mata, don ana ganin rayuwarta ta fado kasa warwas daga wannan lokacin, ko kuwa ace ta ci baya. Amma ni a wurina a lokacin ne mace za ta bude wa kanta wasu sababbin kofofin na ci gabanta, muddin za ta tsoraci Allah ta kiyaye mutuncin addininta. Kada ta yi amfani da shi wajen ganin cewa ta samu ‘yancin cin duniya da tsinke, ko baiwa maza barkatai fuska da sauransu.
Da sannu zata ga kyakkyawan sauyi, musamman idan ta hada da addu’ar kada Allah ya barta da dabarar kanta, ya yi mata jagora a cikin rayuwar zawarcin, iyayenta da ‘yan uwanta kuma su bude zuciya su karbe ta fiye da sanda rayuwar gidan miji take gara mata.
Rayha ki gogewa kanki wannan tunanin, kada in kara jin wannan maganar wai saboda an saki Safifi alhalin mijin yana sonta, ko saboda tsoron irin uwar mijin da zaki samu shikenan ke ba za ki yi aure ki raya sunnah ba? Duk da na san ke auta ce, akwai gabunta kuma su Ammi ba son tashinki suke ba, shi ya sa daga Malam har Ammi suka zuba miki ido kina ta kara girma a gabansu.

Ya sunan yaron da kuka yi alkawarin, kuma a ina iyayensa suke? Meye sana’arsa?

Rayha ya fada masa, tace kuma dalibin medicine ne bai fara aikin komai ba. Yaya Sheikh yace,
“Ba ni lambar wayarsa zan yi magana da shi don in ba da gaske yake ba ina so ki wuce da karatun shari’ah da addinin musulunci a jami’ar da nake yiwa aiki”.
Safiyyah ta ce, “Yaya Sheikh kai ma ka san Malam ba zai bari autarsa taje har Arkansas ba. Nima da yaya na samu ya barni naje nan da Zaria balle ace auta ta tafi har Arkansas?”
Yaya Sheikh ya ce, “ai jiya ba yau ba ce, dole Malam ya karbi zamani da abinda yazo dashi.

Ku bar ni da shi, gakunan an fara sako masa ku gara ya baku tushen rayuwa mai kyau akan auren zamaninnan da bashi da tabbas, bari dai in gama magana da shi yaron ta Malam mai sauki ce”.

“Sunansa Abdullah Muhammad Jalloh, jikan Hakimin Dandume ne”.

In ji Rayha.

Aka bar maganar autar Ammi aka koma ta shirin haihuwar Safiyyah.

Washegari Yaya Sheikh ya ce, duk abin da ake bukata na haihuwa a rubuta masa, in ya koma Lagos Assafe za ta sayo ta kawo, kada a jira wani Zayyan ko a waiwaye shi.
Washegarin ranar kuma ya canza wa Safiyyah asibitin da za ta ci gaba da zuwa har sai ta haihu, kuma inda za a yi mata CS, in ranar da suka saka za su yi mata aikin tazo.

Sheikh ya yi shirin komawa wajen iyalinsa da niyyar sai ana saura kwana uku za a yi wa Safifi aiki za su dawo Dandume shi da Assafe, tare da duk abinda Rayha ta rubuta masa na bukatar haihuwar Safiyyah, itama Sabah ta tambaya ta bata list din, kuma yayi magana da Abdullahi Jalloh, inda ya tabbatar masa shi da Rayha sun dade da kulla alkawarin aure a tsakaninsu, saura shekara uku ya kammala MBBS dinsa ya dawo gida, amma kafin nan iyayensa za su zo, a gama komai, a bada kudin aure.
Sai Yaya Sheikh yace ya yarda, amma shi ma yana son a yi masa alfarmar auta ta fara nata karatun digirin kafin ya gama nasa MBBS din, tunda degree a Arkansas shekara uku ne shima.

Yace don ba za su barta a gida tana zaman jiransa har tsayin shekara uku bata komai ba, kuma nan da nan Abdullahi ya yarda da hakan.

An saka engagement din Rayha da Abdullahi, kafin kowamar Yaya Sheikh Lagos. Wanda saida ya kwashe sati daya wannan karon a gida Dandume. Yana komawa kuma ya sa Assafe ta fara sayayyar kayan haihuwa dana maijego.
Safiyyah ta gaya masa hatta waya bata zo da ita Dandume ba, can ta baro ta a gidan Zayyan.

Don haka Sheikh bai manta ba har da dalleliyar waya yasa Assafe ta saka mata a cikin kayan haihuwa, don ya ce ma Safiyyah idan ta haihu, dole ta rike waya itama kamar kowa baya son wata damuwa kuma.

Malam Usman har kuka ya yi ranar da Sheikh zai koma Lagos, ya ce masa,
“Ridhwan Allah bai sa na haifi Da namiji da kaina ba, amma dan uwana ya haifa min kai, ko yau na koma ga mahaliccina ba ni da fargaba a kan ‘ya’ya mata da na bari Ridhwan, don na san suna da Allah kuma suna da kai, Sheikh. Allah ya jikan (Yaya Abubakar), hakika haka ya rike zumunci shi ma har mai rabawa ta raba mu, ban taba kukan rashin mahaifi ba, duk kuwa da cewa mu din bamu girma tareda iyayenmu ba (yana nufin mahaifin Yaya Sheikh mai rasuwa malam Abubakar Dandume).

Tafiyar Yaya Sheikh Lagos da kwana biyu kacal yasa Assafe ta soma sayayyar haihuwa.

To a can suma su Zubainah da Zahra kamar su kashe kansu don sayayyah a boutiques, Yaya Zubaida ta hana su tambayar Zayyan komai su suke ma Safiyyah sayayyar kayan barka daga aljihunsu.

Yaya Zubaida take ce ma sauran ‘yan uwanta, “kun ga dai wannan ce damar da muke da ita kadai wajen nuna wa Baffa kauna da nadamarmu, na hana masa zaman aure da muka taru muka taimakawa mama tayi da wadda yake yiwa so na hakika, kada mu barshi ya yi sayayyar haihuwar Safiyyah, muyi komai da kanmu kan jiki kan karfi. Duk da su (Safiyyah da iyayenta) bazamu burge su ba, amma at least Baffa zai ji dadi”.

Don haka dukkansu ‘ya’yan Mama su biyar din da ita kanta sun bude bakin aljihu, suna ma Sophie sayayyar haihuwa na ‘yan gata, na garari.

Shi kuwa Zayyan a nasa bangaren wasu uban boxes da ya riga ya ciko da kayan jarirai unisex tun daga Saudiyyah su ya fiddo yanzu, banda kudi kamar na hauka da ya turawa Yaya Zubainah ya ce ta sayi duk abin da ya dace na haihuwa, ta hada da wadanda yayo ajiyarsu daga Saudiyyah ta kaiwa Sophie Dandume.

Zubainah saida tausayi ya kamata, domin ta lura tamkar Zayyan baya cikin hayyacinsa, ko daga irin tsadaddiyar sayayyar da ya jibgo, na kayan jarirai da na uwar masu karshen tsada, sannan ta san kullum Zayyan kafarsa na sunturin zuwa Dandume, sai dai ya fake da ya zo gaida Malam. Malam bai taba bada fuskar da zai tambayeshi Safiyyah ba saidai su gaisa yace masa zai fita bada karatu haka zaka ga Zayyan ya taso ya shiga motarsa tsamo-tsamo abin tausayi.

Haka zai yi ta kawo abubuwa na bukatar rainon ciki, yasa alamjirai su shiga dasu cikin gidan, amma duk zuwan da Zayyan ke yi Dandume, Sophie ba ta taba bari ya ganta ba, saidai taji labarin ya zo ko taga ana sauke kaya daga motarsa a tsakar gidansu, shi ma Malam babu fuska daga gare shi, da har zai tambaye shi izinin ganin Safiyya balle Ammi da in ta ji Malam ya ce Zayyan ya zo gidan ma, ya kawo kaya ya tafi, sai tayi mita da masifa ita kadai. Ammi ranta baci yake yi da sayayyar haukar da yake musu wadda Safiyya ba ci take ba bata ko budawa, sai store Ammi ke musu ma’adani, haka zata wuni tana faman tsaki da mita fadin,
“Malam kai ka bada fuska Zayyan yake neman maida mutane mayunwata”.

Shi kuma sai ya yi murmushi ya ce, “Har gobe Zayyan Dana ne, saboda marigayin mahaifinsa. Kuma hakkin ciyar da Nana Safiyyah a wannan lokacin yana wuyansa, don haka kome zai kawo yayi ta kawowa in baku ci ku bada sadaqa”.

ABUNDA AKA DADE ANA JIRA YA ISO!

An cirowa Safiyyah lafiyayyar ‘ya mace, ranar wata Litinin, kasancewar har gobe Sabah tana shiri da Zayyan a ranta don Zayyan ya kyautatawa Sabah ta kasa manta alherinsa. Itace tun a asibitin bayan an fiddo Safiyyah daga dakin tiyata an shirya baby tsaf cikin ‘pink’ din tsadaddun kayan babies cikin sayayyar Assafe, baby ta cusa duka yatsanta a baki tana tsotso, Sabah ta dauke ta a hoto da wayarta, nan da nan ta faki idon kowa ta tura hoton wayar Zayyan ba tareda ta kara da bayanin komai ba.

Arch. Zayyan yana gida a ranar bai je ko’ina ba, saboda bacin rai, sakamakon abinda ya wayi gari yau yaga Azeezah ta yi masa.
Tun dawowarsa daga Saudiyyah bai bude ‘safe’ dinsa ba sai yau, kasancewar tafiyarsu Jamus da Mama ta matso.

Bayan tafiyarsa Saudiyyah daya dawo bata gaya masa maganar birthday din data yi ba, sai yanzu ya samu labari. Yau da ya duba ‘safe’ dinsa kuma sai ya tarar babu kudin, ta kwashe komai, cikin ma’aikatan gidan wani ya turo masa hotunan birthday din gabadaya.
Azeezah ta shirya fitinannen ‘pool party’ na fitsara na mata zalla a gidanta, ta bada ‘dress code’ na badala, wai a ganinta dukkansu mata ne ta gayyato, amma abin takaicin shi ne, wadanda aka hayo don dafawa da raba abinci (caterers) masu kula da walwala da jin dadin taron har da maza a cikinsu, mata kawayenta data gayyato sun saka kayan swimming suna cikin ruwa akayi hotuna na fitsara don ‘pool party’ ne akayi.
Asalin kudin kuma ya canza su zuwa dollars ya ajiye ne da niyyar zai kai Mama Germany da su a duba lafiyarta, ga shi har ranar tafiya asibitin sun saka musu, babban abinda ya kular da shi duka kudin ta kwashe, duk wasu shirye-shirye na visa sun kammala sai sayen tikiti da tafiya ya rage musu, ya gama shirya zai kai Mama a yi mata (general check-up da prosthetic leg).
Yau da ya duba ‘safe’ dinshi don kwashe kudin zai kai su banki ya biya charges na asibitin, ya kuma yanko tikitin tafiyar tasu ya ga Azeezah ta kwashe su gaba daya.

Da matsanancin fushi Zayyan ya isa dakin Azeezah har huci yake, tana shiryawa za ta fita don ita kwatakwata bata iya wuni a gida bata fita ba, tana daura kallabi a kanta irin ture kaga tsiya, bakinnan ya dauki jambaki da santsi abin ba’a magana.

Tun daga falo Zayyan yake kwala mata kira. Yana shigowa dakin ya yi kanta. Ya na cewa,
“Zeezah, halin bera kuma ki ka koma?”
Jin abinda yace sai Azeezah ta yi wani harrrr! Da idanunta, cuno baki ga daurin ta yadda ta ke yi a gaban goshin ta ya zauna, kafin ta ce,
“Baby! Ni ce mai halin beran? Cewa nake abunka nawa ne? ko mutuwa kayi nida Shaheed kadai keda komai naka?”
Cikin bakin cikin kalamanta, da takaicin halinta ya ce,
“Abin da ki ka yi wa ‘safe’ dina me sunansa?”

Ta ce, “Ai wallahi kai dinnan ba ka da arzikin da zan yi maka sata. Kawai na dauki kudin mijina ne, halaliyar Da na, na yi harkar gabana dasu.
Tunda ai tun farko na tambayeka ta lallami ka hana ni, na gaya maka tun kafin ka tafi cewa ina so zan yi ‘25th birthday party’ dina”.
Sai ya matso daf da ita rike da wayarsa yana nuna mata fitsararrun hotunan da ke ciki, ya ce, “Birthday ko badalar da ki ka shirya wa ‘yan iskan kawayenki? A gidana Azeezah? Gidan aurena? Kika gayyatomin wadannan ‘yan iskan?
Azeezah kin wuce da sanina, amma tabbas sai hotunan nan sun je gaban Baba”.
Azeezah tace, “Da kai da munafukin da ya turo maka hotunan kun yi kadan ku hada ni da mahaifina…”
Bai ankara ba ta fisge wayar ta rotsa ta da kasa, shi kuma ganin ta’asar data yi masa, ba wayar yake ji ba muhimman abubuwan sa dake cikinta da komai nasa, don bacin rai bai yi wata-wata ba ya kai mata kyakkyawan mari.

Da sauri Azeezah ta dafe kuncinta, don har taurari saida taga sun gilma mata. Yace “Tir! Da tarbiyyar da kika yi wa kanki Azeezah. Don wallahi ba Babana ne ya yi miki ita ba, tabbas Baba ya haife ki amma bai haifi halinki ba.
Ya gayamin dama amma ban ji ba, na biyewa KAWAR ZUCIYA”.
Azeezah ta kama kuncinta ta rike, ta ce, “Ni ka mara baby? To wallahi ka daki aurenka”.

Bai tsaya ba ya juya da zummar ya bar dakin, don ya tabbata in ya ci gaba da tsayuwa a gurin yana iya jibgarta.

Ya sunkuya yana tattara wayarsa da ta rotsa a kasa, saboda quality din wayar wargajewa kawai ta yi, amma ba ta farfashe ba.
Ya harhada wayar ya zauna yana regaining consciousness bayan ficewar Azeezah daga dakin. Ya ce, “Ya Allah kai ne shaida a kan ban auri Azeezah don dukiyar mahaifinta ba, sai don raya sunna. Ya Allah ka shirye ta in mai shiryuwa ce, Ka ba ni kwarin gwiwar rike ta da saita ta saboda mahaifinta, Ya Allah Ka sauki Sophie lafiya, Ka huci zuciyarta sanyin idaniyata su dawo min”.
Kawai sai ya tashi ya bar gidan ya kama hanyar Kaduna wajen su Mama don ya sanar da ita batun tafiyarsu Germany sati uku masu zuwa.

Yana fita daga gidan ko minti goma ita ma Azeezah bata kara a gidan ba tasa aka yi mata booking din jirgi, ba jimawa ta fice, ta bar gidan sai Lagos.

A kan hanyarsa ta isa Kaduna Zubaina ta kirashi a waya ta ce,
Baffa komai ya kammala na kayan haihuwa fa, nida Ya Zubaidah, Zaytoon da Zahra da Hatoon mun hutasheka, yaushe zaka zo ka gani?”.
Ya ce, “To Ya Zubaina nagode muku, ai sai ki kai kawai ko? Ba sai na gani ba wallahi. I trust you my sister kin fini son Sophie ai?”

Zubaina tayi dariya tace, “ to shikenan. Ni da Ya Zubaida za mu je mu kai, tunda yau ko gobe Safiyya na iya haihuwa, in har lissafin da nake yi daidai ne tana cikin watan haihuwarta”.

Sun yi sallama da Zubaina ya aje wayarsa a gefen damansa ya ci gaba da tuki, yana ta jin shigowar sakonni a wayar ta whtsp amma bai bude wayar ba, sabida kada ya raba hankalinsa, sai bayan shigarsa gidan Zahra a Unguwar Sarki, aka yi masa iso zuwa dakin da Mama ta ke.
Zayyan yayi sallama a dakin, nan ya samu Mama a kwance bisa gado ta rasa abinda ke mata dadi. To zuwan Baffa sai ya sa mata jin karsashi, Mama ta yunkura ta tashi zaune fuskarta ta cika da yalwar fara’a, ta ji sauki sosai amma jikinta kullum ba kwari saboda rashin kafa guda ya kassara karfinta.

Mama ta ce, “Baffa kai ne tafe kuma ba ka kira ka fada kana hanya ba?”

Zayyan ya zauna a gefen Mama ya sa mata filo daga bayanta yadda za ta ji dadin jingina suna gaisawa.

Karar shigowar sako cikin wayar da ke aljihunsa ya sa shi dauko wayar. Ya sha mamaki da ganin pop in na sako daga “SABAH DANDUME”.

Yaushe rabon da Sabah ta ko gaishe shi duk irin shirin da ke tsakaninsu? Don haka da hanzari ya bude sakon nata ta manhajar Whatsapp.

Mama na ta magana tana tambayarsa Shaheed, ta lura Zayyan ya zama absent minded, Zayyan sai wani irin murmushi yake yi da Mama ba ta taba ganin irinsa a fatar bakinsa ba. Kai za ta iya cewa tun rabuwarshi da Sophie rabon da ta ga murmushinsa, sai yau. Ashe hotunan beautiful Baby ne Sabah ta sambado masa.
Mama na ta magana har ta gaji ta yi shiru daidai lokacin da Zayyan ya dungura a gaban Mama ya fadi ya yi sujjadah a gabanta.

“Ikon Allah!” In ji Mama,

“Me ke faruwa ne wai Baffa?”
Zayyan sai hawayen farin ciki suka billo daga karshen idonsa, don ji ya yi kamar yau ne aka yi masa bushara ta farko da samun haihuwa.
Yasa hanky ya gogesu, sannan ya cewa Mama, “Mama Allah ya albarkaceni da samun karuwar diya mace. Sophie ta haihu”.
Wato a wannan lokacin Mama ji ta yi kamar ta nitse a kasa, alhalin ba Safiyyah a wajen. Ta ji kunyar Allah, ta ji kunyar kanta ta ji kunyar idanun danta.
Daidai lokacin da ya mika mata wayarsa mai dauke da hotunan Babyn da Safiyyah ta haifa masa, Mama rasa ya zata yi ta kalli hoton tayi, saboda kunyar duniya da ta lullube ta.
Shi kuma gogan bai tsaya lura da reaction din Mama ba ya mike zumbur yana kokarin saka takalmansa. Haka yasa su hagu da dama. Jikinsa har mazari yake yi yace wa Mama “to Mama sai na sake shigowa, Zan wuce Dandume yanzu Mama, wace addu’a za ki yi mana nida Baby da Sophie?”

Mama ta runtse ido cike da tausayi da nadama, hawaye suka Ciko idonta, ta ce, “Baffa Allah ya dora ka akan Safiyyah da iyayenta. Allah ya raya abinda kuka haifa. Ya sa kuna da rabon sake zama tare ku raini ‘yarku a tsakiyar ku”.

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *