Chapter 1: Chapter 1
NAANAH
AUN Academy, Yola.
1:25pm
Ranar ta kasance ta musamman, rana ce da kowacce daliba yar SS3 ke jira tun farkon shekara wato graduation day. Harabar makarantar ta cika da hayaniya, kiɗa-kiɗe da iface -iface sai tashi yake ta ko’ina. Girls ɗin boarding school ɗin suna ta zagaye da juna, wasu suna ɗaukar pictures da wayoyinsu, wasu kuma suna rubuce-rubuce a jikin graduation gown: “Don’t forget me please,” “Call me when you get home.”
A cikin dormitory kuwa, akwati da jakunkuna sun cika ko’ina. Wasu na ta nannade kayan da ba su riga sun shirya ba, wasu kuma suna jiran iyayensu su zo ɗaukarsu.Kowacce yarinya idan ka kalli fuskarta zaka ga farin ciki mara misaltuwa.
A bakin wani hostel suke tsaye, Yan’ mata guda uku, farare masu kama da juna, suna sanye da rigunan graduation suna magana da juna. Da gudu ta ƙaraso wajen tana jan trolley ɗin hannunta, ta tsaya gabansu tana haki.
“Kin gama packing komai?”
Ɗaya daga cikin yan matan ta tambayeta, gyaɗa mata kai ta yi tana goge gumin daya tsatsafo, Ɗaya daga cikinsu ta matso kusa da ita ganin how weak she looks ta dafata ta ce“Ko wani abun yana maki ciwo Nana?” Girgiza kanta ta yi cikin sassanyar murya ta ce“a’a I’m fine kawai na matsu naje gida ne” Hameeda ta jinjina kanta kana ta ce“oh really, to ai dai duk saurin ki sai kin jira ko?” Nana ta ɗan kwaɓe fuska ba tare da ta ce komai ba.
Komawa ta yi ta jingina da bango suka ci gaba da kallon jama’a, iyaye sai zuwa suke ana ɗaukan yara. Wata budurwa ce ta ƙaraso wadda ba zata shige 16yrs ba ta rungume Nana tana kuka ta ce“you know what Nana? Zan yi missing ɗinki.. dan Allah karki manta dani kinji” Kukan itama ta saka tana sake ƙanƙameta. Sai da suka ci kukansu sannan ta janye jikinta tana goge hawaye ta ce“Daddyna yazo tafiya dani, Dan Allah Nana ki zo Kano watarana kinji” cikin shessheƙar kuka ta ce“Zan zo in sha Allah bestie” sake rungume juna suka yi sannan ta janye jikinta ta maida idanunta kan yan’uwan Nana dake tsaye ta ce“Hameeda, Maimoon, Amrah Allah ya ƙaddara saduwarmu”
Murmushi suka yi a tare suka ce”Amin Khadijah, ki gaida gida” ta ɗaga musu hannu sannan ta kalli Nana ta ce”bestie na tafi”
“Ki gaida Mommy”.
Daga haka ta juya ta tafi tana ɗan waiwayenta. Tana barin wajen Nana ta sake fashewa da kuka, tasan zata yi kewar Khadijah fiye da komai, ƙawarta tun Jss1 har SS3 duk wanda ya san Nana a Aun to tabbas ya san Khadijah, yanda bata ji itama haka take bata ji, ko sanda suna Juniors senior ɗinsu basu isa suyi dealing nasu ba, har suma suka zamo seniors kuma aka basu muƙami, Nana ita ce Amira ta Aun ita kuma Khadijah ita ce health prefect. She wish a ce garinsu ɗaya da Khadijah da tabbas tasan amintarsu zata ɗore, amma yanzu kasancewar suna mabanbantan gari ta tabbata ba lallai bane su ci gaba da ƙawance.
“Ke Nana ki zo zamu tafi”
Muryar Maimoon ta dawo da ita daga tunanin da take, kallonta kawai ta yi sai kuma taja trolley ɗinta ta yi hanyar parking space na makarantar. Tana tafe student na mata magana, wasu su kirata da Amira, wasu kuma su ce A-shuwa. Har sun yi gaba sai kuma Maimoon ta dawo taja hannunta tana faɗin “Kina son a tafi a bar ki ne ko Nana?” banza ta yi mata ta ci gaba da janta suna tafiya har suka ƙaraso gaban babbar motar ƙirar Lexus jeep, black colour sai kyalli take. Tsayawa duk suka yi an kasa samun wanda zai yi knocking ƙofar, Hameeda ta ɗan kalli Nana murya can ƙasa ta ce“je ki buɗe” da sauri Nana ta kalleta sai kuma ta ɗauke kai. A ƙalla sun ɗauki 3mins suna tsaye kafin Maimoon ta yi shahada ta ƙarasa ta yi knocking glass ɗin gaban motar, a hankali glass ɗin ya fara yin ƙasa, zaune yake cikin motar idanunsa sanye da shade glasses black, fari ne tas mai dogon hanci sannan ga beauty beard data cika fuskarsa. Sanye yake da wata dakkakiyar shadda milk colour sai kyalli take, Maimoon ta ɗan ja numfashi kafin ta ce”Ya..Yaya Sultan”
Shiru ya yi bai bata amsa ba, dan babu alamar ma yaji abin da ta faɗa, ta sake cewa “Yaya mu shigo?” Sai a sannan ya juyo da gaba ɗaya fuskarsa ya kalleta, Asalin kyakkyawan bafulatani mai cikar kamala da sura. Ya zare glasses ɗin idanunsa still looking at her ya ce”ance muku ni driver ne da zan tsaya ina zaman jiranku right?”
Da sauri suka shige motar sanin halin jarabarsa. Nana ta dinga kallonsu ganin sun cike backseat ɗin motar, ta tsaya kamar statue. Maimoon ce ta mata alama data shiga da ido, ta girgiza kanta kawai sai ta fashe da kuka, bin ta ya dinga yi da wani irin mugun kallo kafin ya yi kafa ya kunna motar. Da sauri Amrah ta ce”ke ba zaki shiga ba?”
Cike da masifa ta ce” to ina zan shiga? Ba yan duk kun cike motar” kallonta suka dinga yi, Maimoon ta kalli front seat ɗin ganin babu kowa ya sanya ta ce”baga gaba nan ba, ki shiga mana”
“Ni bana son zama a gaban namiji”
Da sauri ya kalleta sai kuma ya sauka daga motar, zagayowa ya yi inda take ya ɗago fuskarta a zafafe ya ce”Kee ni abokin wasanki ne?”
Fashewa ta yi da kuka ta riƙe gefen kanta ta ce” ni bana son gaba wallahi, ni a baya zan zauna”
Bai sake magana ba kawai taga ya fizge hannunta ya buɗe motar ya turata sannan ya koma ɗaya side ɗin, shiga ya yi ya kulle motar gaba ɗaya sannan ya yi mata key suka bar harabar makaranta. Kuka ta dinga yi kamar wadda aka daka, Hameeda ta dinga kallonta tana tsaki. Sun yi nisa Amrah ta ce”wai ke dallah can ki yiwa mutane shiru, wa ki ka fi iya shagwaɓa?” A fusace ta juyo baya tana kallonta fuskarta caɓa-caɓa da hawaye ta ce”ba zan yi ba ɗin, ko na shiga harkar ki?” Harararta Amrah ta yi amma bata ce komai ba. Nana ta murguɗa baki sannan ta juya ta ci gaba da kukanta.
M-Shuwa Estate,
No. 1–50, Off Girei Road,
Dougirei, Yola North LGA,
Adamawa State, Nigeria.
Tun daga bakin titin ƙaton symbol yake maƙale da sunan M-Shuwa Estate, Suka dinga kallon titin cike da murna da farin cikin dawowa gida, A bakin wani katon gate suka tsaya gate ɗin ya dinga zugewa da kansa sannan ya danna hancin motar cikin estate ɗin, M-Shuwa Estate shi ne sunan dake maƙale jikin wani dogon gini wanda yafi kowanne tsayi a cikin gidan, gidaje ne birjik a ciki kowanne ɗauke da fenti fari da zinariya, kusan duk gidajen kansu ɗaya, guda ɗaya ne wanda ya sha bambam dasu, yafi kowane gida girma da tsayi. Akwai ɗan ƙaramin clinic cikin estate ɗin, hakana akwai islamiyya a ciki da kuma masallaci wanda ke haɗa duk al’ummar dake cikin estate ɗin. Wannan estate ɗin mallakin wani babban attajiri ce wato Alhaji Muhammad Shuwa, Babban mai kuɗi a cikin Adamawa dama Nigeria baki ɗaya, yana da ƙanne guda uku, Alhaji Ahmad Shuwa, Alhaji Kabeer Shuwa, sai kuma ƙaramar wato Mariya Shuwa. Sun kasance ƙannensa wanda ya raina da hannunsa sakamakon rasuwar da iyayensu suka yi tun suna ƙananu, shi ne wanda ya kula dasu har zuwa girmansu ya kuma aurar dasu bayan shima ya yi aure, ya auri wata bafulatanar mata wato Hajiya Khadijah, Mace mai halin kirki da kuma sanin ya kamata. Alhaji Muhammad Shuwa ya gida wannan estate ɗin ne domin samun ci gaba da kuma zumunci a tsakanin ahalinsa, yana da ya’ya guda shida huɗu maza biyu mata, mazan sune Abdusammad, Aliyu, Hameed, sai kuma Safwan. Yayinda matan sune Fatima da kuma Hafsa. Duk wanda ya san tarihin estate ɗin an sansu akan halaye nagari, nagarta da kuma kamewa. Hakan yasa mutane da dama ke sha’awar haɗa zuri’a dasu, sai dai ba’a samun damar haka domin a family na Muhammad Shuwa i junansu suke aure, tun yarinya na ƙarama ake mata miji a cikin gidan, da zarar ta kammala makarantar secondary sai a aurar da ita, wannan tsari an fara shi ne tun samuwar estate ɗin, kuma har zuwa yanzu tsarin yana nan, duk da Alhaji Muhammad Shuwa ya mutu shekaru goma sha biyar da suka gabata, a lokacin Nana tana da shekara ɗaya a duniya. Ba za’a taɓa cewa baya raye ba idan har aka yi la’akari da irin yanda suke gudanar da rayuwarsu cike da tsari. A yanzu Alhaji Kabeer Shuwa shi ne matsayin M-Shuwa domin shi ne wanda yake bin sa, daga shi sai Alhaji Ahmad wato mahaifin Nana. Kuma Hajiya Khadijah ita ce wadda take zartar da hukunci har yanzu a cikin gidan sannan kuma kowa yana bin ta koda baya so…
A bakin wani katon duplex ya yi parking, suka sauka daga motar da gudu kowanne ya nufi apartment ɗinsu, sai da suka gama sauka sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar amma ga mamakinta sai ta ji shi a rufe, ta juyo ta ɗan kalleshi taga danna wayarsa yake hankali kwance, muryarta na rawa ta ce”ka buɗe min zan tafi gurin Amma” shiru ya yi mata, ta dinga kallonsa kafin ta sake cewa”Yaya Sultan ka buɗe min zan sauka” ɗago kansa ya yi ya ɗan kalleta, idanunta sun cika taf da hawaye ya ajiye wayar ya gyara zamansa yana kallonta ya ce” me ki ka ce ɗazun? Ba zaki zauna kusa da namiji ba” ɗauke kanta ta yi ta dinga kallon compound ɗin gidan wanda ya cika da shuke-shuke. Hannunsa ya sanya ya jawota ta juyo da sauri tana kallonsa, tuni hawaye ya fara zubowa kan fuskarta ta ce”dan Allah Yaya ka bar ni, ka rabu dani na tafi” hannunta ya kama duk biyun ya riƙe cikin nasa still looking at her ya ce”Nana ni ki ke sharewa ko? Baki sona ko? Ni Yayanki dan nace ina sonki shikenan ki ka daina zuwa inda nake ko, ki ke gudana ko?” Fashewa ta yi da kuka ta shiga girgiza kanta tana cewa”Ni Yaya ka barni na tafi, ka barni naje naga Amma”
Hannunsa ya sanya ya goge mata hawayen sannan ya ɗan hura mata iska a fuska, lumshe idanunta ta yi saboda ƙamshin mouth listener ɗin daya daki hancinta. Ya ɗago fuskarta yana kallonta sosai ya ce”kin san yanda nake sonki kuwa Nana? Ina son ki amince na aureki kin ji, zan je na faɗa Hajiya Babba nasan ba zata ƙi ba Nana, na aureki muyi rayuwarmu cikin farin ciki, kinji cutie ɗita”
Kallonsa ta dinga yi can kuma ta janye hannayenta daga nasa, ta juya tana kallon waje ta ce”ka buɗe min mota na fita” yanda ta yi maganar a sanyaye ya sanya ya ɗan kalleta, ya sauke numfashi sannan ya yi unlocking motar. Da sauri ta buɗe ta fice ko takan jakarta bata bi ba, ta nufi hanyar apartment ɗinsu da gudu. Sultan yabi bayanta da kallo yana jin wani irin so da ƙaunar yarinyar a cikin ransa.
Yana shirin sauka daga motar idanunsa ya sauka akan wani yanki, ɗauka ya yi ya dinga juyashi kafin ya warware a hankali
“Karki manta dani, ina sonki Nana! Ina son ki! Sannan ina muradin na aureki, dake zan ƙare rayuwata, ki jirani! Wait for me NAANAH!”
Sultan yaja dogon numfashi ya sauke har sannan idanunsa na zube kan yankin, ya karanta rubutun yafi sau biyar kafin ya linke ya ajiye gefe, ya sauka daga motar kai tsaye kuma apartment ɗin su ya nufa. Knocking ƙofar ta dinga yi kamar zararriya tana kiran “Amma! Amma!” Kusan mintuna biyu kafin azo a buɗe ƙofar, wata farar mace ce fuskarta ɗauke da mabayyanin murmushi take kallonta, ihu ta saki sannan ta rungumeta tana wata irin dariya. Amma tayi murmushi ta ɗagota tana kallonta ta ce” Yaushe zaki girma Nana?” Langwaɓar da kai ta yi ta sake rungumeta tana cewa”nayi missing naki ne fa Ammata” girgiza kai kawai Amma ta yi ta janyenta daga jikinta ta yi ta ce”to shigo ciki” gyaɗa mata kai ta yi sannan ta nufi cikin parlon da sauri. Tamkar wadda ta warke daga ciwon makanta haka ta dinga bin ƙaton parlon nasu wanda aka ƙawata shi da abubuwan more rayuwa. Ta lumshe idanunta saboda ƙamshin turaren wutar daya game ɗakin mai matukar daɗi, daman in dai ana maganar tsafta da ƙamshi to Amma ƙarshe ce.
“Idan kin gama kallon sai ki shiga ciki ki yi wanka ki zo ki ci abinci”
Amma ta ƙare maganar hannunta riƙe da remote tana rage gudun ac. Kallonta Nana ta yi ta ce”Amma me ki ka dafa?” Ganin irin kallon da ta yi mata ya sanya bata sake cewa komai ba, ta nufi hanyar ɗakinta. A hankali ta tura ƙofar bedroom ɗin nata, ta dinga taka fluffy rug ɗin dake shimfide akan tiles, sanyin ac da kuma turaren wuta ya daki hancinta, ta sauke ajiyar zuciya. Ɗakin nata neat and organized, royal bed ɗinta madaidaici a tsakiyar ɗakin mai shimfiɗe da farin bedsheet,sai katon teddy bear a gefe. Daga can kusurwar ɗakin a saman study table an jera littattafai na makaranta,da yar ƙaramar fitilar karatu a gefensu. Ko ina tsaf yake tamkar tana rayuwa a ciki, duk da bata nan hakan baya hana Amma gyara mata shi kullum. Ta ƙarasa ta zauna gefen gadon ta jingina da jikin fuskar gadon ta ja idanunta ta rufe tana jin wata irin nutsuwa na saukar mata. Kasancewar ta gaji sosai ga kuma yanayi mai daɗi data samu ya sanya bacci ya ɗauketa a wajen.
Iska ta dinga kaɗawa a hankali, yanayin sanyin da ake ciki ya sanya taji ta takura, ta haɗe jikinta waje ɗaya. Kallonta ya dinga yi kamar ya samu tv, ganin ɗalibai na sauri ya sanya ta ɗago narkakkun idanunta ta kalleshi, murmushi taga ya yi, ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba. Gyara tsaiwarsa ya yi still looking at her ya ce”Kin gaji?” Ta girgiza kanta, kallon right hand side ɗinsa ya yi ya hango Senior master dan haka ya maida idanunsa kanta ya ce”yanzu zaku tafi?” Nan ma ta girgiza masa kai, ɗan haɗe rai ya yi kamar tana ganinsa ya ce”hala kina fama da ciwon baki ne?” Da sauri ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta girgiza kanta murya a sanyaye ta ce”sai an zo ɗaukarmu” Sir Junaid ya sauke numfashi sannan ya ce”yanzu idan ki ka je gida a ina zan dinga ganinki? Zaki dinga fitowa mu haɗu? Ko ni zan dinga zuwa estate ɗinku?”
Ji ta yi gabanta ya yi wani irin faɗuwa, ta kalleshi hawaye kwance cikin idanunta ta ce”i wish so, amma ba zai taɓa yiwuwa ba, ba za’a bar ni na fito ba idan har na koma gida. Bama fita, duk abin da muke so sai dai a kawo mana, idan kaga mun fita waje to sai dai da yayyenmu maza ko kuma uncles ɗinmu and…”
“And what?” Junaid ya yi saurin tambayarta.
“Ba za’a bari ka zo gidanmu ba, ba zan sake ganinka ba idan har na shiga cikin M-Shuwa estate!”
Nana ta ƙare maganar cikin rauni. Ya dinga kallonta bai ce komai ba, ta ɗago kanta ta kalleshi sai kuma ta sake sunkuyar da kan, Junaid ya numfasa sannan ya ce”kenan me ki ke nufi Nana? Na rabu da ke? Na rabu da soyyayar da nake miki tsayin shekaru shida? Na bari ki auri ɗan danginku? Na haƙura dake! Kin yimin adalci kenan?”
Ta girgiza kanta hawaye na zubowa kan farar fuskarta ta ce”Ya zamu yi haka ƙaddara ta zaɓa mana, ban isa na bijirewa gidanmu ba, ban isa na sauya abin da suka ginu akai ba! Ban isa…”
“Ki min shiru Nana! Kimin shiru! Just keep quiet!”
Junaid ya daka mata tsawa yana nunata da yatsa, shiru ta yi ta kafeshi da manyan idanunta. Ya dinga huci kamar zaki kafin ya ɗauke kansa yana kwafa ya ce”Ba zan bar ki ba, sai na tabbatar dana sameki a matsayin mata, wallahi tallahi Nana ba zan bari a rabani dake ba! Ina sonki! Ina sonki! Ina sonki Nana!”
A firgice ta buɗe idanunta, ta dinga kallon ɗakin tana zare idanu, hannunta ta sanya ta dafe ƙirjinta jin yanda yake wani irin bugu. Amma dake tsaye kusa da press tana linke wasu kaya data shigo dasu ta ce”lafiya?” Ta girgiza kanta murya a sanyaye ta ce”babu komai” Amma ta ɗan juyo ta kalleta sai kuma ta ce”tashi kiyi wanka, ki zo parlon ina jiranki” gyaɗa mata kai ta yi sannan ta sauko daga kan gadon ta nufi toilet tana tafe kamar babu laka a jikinta. Amma ta bita da kallo sai kuma ta girgiza kanta ta mayar da press ɗin ta rufe sannan ta fice daga ɗakin.
After 20mins ta fito daga toilet ɗin jikinta na ɗigar ruwa, ta ƙarasa gaban mirror ɗinta tana gyara ɗaurin towel ɗin jikinta. Ta ƙurawa kanta kallo a jikin mirror ɗin, Nana fara ce tas kuma asalin bafulatanar yarinya, tana da kyau mai sanyi da ɗaukar hankali, hancinta dogo har bakinta, idanunta manya manyan kamar zasu yi magana, bakinta ɗan ƙarami kuma jajur dashi, gashin girarta a cuccure kuma mai yawa, haka ma gashin idonta zara-zara. Babu yanda za’a yi ka yi mata kallo ɗaya ka ɗauke idanunka, wannan shi ne sirrin duk wata budurwa a cikin dangin Shuwa, Allah ya yi musu kyau daga mazan su har matan.
Shiryawa ta yi cikin wata doguwar riga ta atampa ɗinkin A-shape, ta ɗaura ɗankwalin sannan ta shafa lip gloss a bakinta, she looks so quiet, ta kalli fuskarta a madubi a fili ta ce”nayi kyau sosai” ta ƙare maganar tana murmushi sai kuma ta fice daga ɗakin da sauri. A parlon ta samu Amma zaune tana karanta wani littafi, Ta ƙarasa ta zauna kusada ita, ta ɗora kanta a gefen kafaɗarta a shagwaɓe ta ce”Ammata nagaji sosai” ba tare da ta kalleta ba Amma ta ce”ɗagani ki ci abinci sai ki huta” ɗago kanta ta yi tana kallon Amma ta ce”Ba hutawa zan yi ba wajen Hajiya Babba zan je” kallonta kawai Amma ta yi babu yabo babu fallasa ta ce”i see” sannan ta miƙe ta nufi kitchen.
Ko rabi bata ci ba a abincin plate ɗin ta miƙe duk yanda ta yi missing girkin Amman kuwa, ta miƙe tana riƙe da robar exotic tana sipping, ganin tana shirin yin waje ya sanya Amma ta ce”haka zaki fita babu ko mayafi?” tsayawa ta yi tana kallonta ta ce”Amma wajen Hajiya fa zan je, yanzu zan dawo” daga haka ta yi waje da sauri, Amma ta bita da idanu sai kuma ta girgiza kai ta ci gaba da abin da take.
Tafiya ta dinga yi tana yan waƙoƙinta na turanci, kowane gida a rufe yake, kai tsaye kuma gidan Hajiya Babba ta nufa. Babban duplex ne dan yafi kowane gida girma a cikin estate ɗin, ta dinga kallon gidan fuskarta ɗauke da annuri dan rabonta da Hajiya Babba wata shida kenan, ta ƙarasa da sauri ta murɗa handle ɗin ƙofar, karo suka ci, ta yi baya tana dafe goshinta. Tsayawa ya yi a jikin ƙofar ya harɗe hannayensa a ƙirji yana kallonta. Ta ɗago ta kalleshi sai kuma ta ɗauke kai tana tura baki, hannunsa ya sanya kamar zai taɓa ta, ta sake ja da baya. Harararta ya yi kana ya ce”gashi zan cire miki” hannunta ta shafa a gefen fuskarta taji gashinta a waje, da sauri ta mayar dashi cikin ɗankwalin ba tare da ta kalleshi ba ta ce”zan shige” ɗan murmushi Sultan ya yi sannan ya ce”to shige malama” daga haka ya koma ciki. Ɗago kanta ta yi ta kalleshi sannan ta shiga cikin parlon.
Wani irin ihu ta saki data hango Hajiya Babba zaune kan sofa, ta tafi da gudu ta faɗa jikinta tana dariya ta ce”Hajiya Babba, nayi missing ɗinki” murmushi Hajiya Khadijah ta yi ta ce”takwara so ki ke sai kin ƙarasani?” Ɗagata Nana ta yi ta zauna gefenta tana cewa”Ni na isa Hajiya Babbarmu mai Makkah da Madina” Hajiya Babba ta dinga kallonta tana murmushi ta ce”shikenan an gama makarantar” Nana ta gyaɗa kanta tana kwance ɗankwalin kanta ta ce”Eh mana, mun zama manya” Dariya irin ta manya Hajiya Babba ta yi sannan ta ce”ai yanzu yan’uwan naki suka shiga ciki”



