⚠️

JavaScript is Disabled

This website requires JavaScript to function properly.

Please enable JavaScript in your browser settings and reload the page.

Chapter 13: Chapter 13

Bata ƙarasa gida ba ta haɗu da Juwaira hannunta riƙe da warmer, kallonta ta yi sai kuma ta ce“Hajiya zaki kai wa?” gyaɗa mata kai ta yi, ta yi saurin karɓa tana faɗin “bari na kai mata” murmushi Juwaira ta yi dan daman ba son zuwa take ba ta ce“yauwa Yaya, nagode miki daman kallo nake” daga haka ta juya ta nufi hanyar gida, taɓe baki Maimoon ta yi sannan ita ma ta juyo ta nufo gidan Hajiya Babba. Koda ta dawo zaune ta sameta tana cin abincin har sannan ta ajiye warmer sannan ta ce“ba zaki jira a dinga kawo miki abinci ba sai ki dinga ci ko?” murmushi ta yi ta ce“to ai duk ina ci idan aka kawo min ɗin, yanzu wannan gobe da safe shi zanci”

“ɗumamen abinci zaki ci?” jinjina kai Hajiya ta yi ta ce“eh” Maimoon tana faɗin “tab ni ba zan iya ba” ganin ta nufi sama ya sanya ta ce“ina kuma zaki je?” zata bata amsa kenan sai ga Abba ya shigo shi da Abdusammad, Maimoon ta kallesu jiki a sanyaye ta ce“Abba an ganta?” girgiza mata kai ya yi yana ƙoƙarin zama kan sofa ya ce“a’a Maimunatu” kamar zata yi kuka ta ce“allah sarki, Allah yasa ba ɓata tayi ba” kallonsu Hajiya ta dinga yi sai kuma ta ce“wane ba’a gani ba?” furzar da numfashi ya yi daga bakinsa kafin ya ce“Nana ce!” da sauri ta miƙe tsaye tana kallonsa ta ce“Nana kuma? Yaushe? Kuma a ina?” Hajiya Babba ta jera masa tambayar da tashin hankali sosai akan fuskarta. Abdusammad ne ya ce“Ki zauna Hajiya sai a miki bayani” jiki a sanyaye ta koma ta zauna ta zuba musu idanu tana kallonsu.

Tana hawa saman ta buɗe ɗakin ta shiga, kwance ta hangeta dan haka ta ƙarasa ta taɓa ta ta ce“ke Nana tashi” buɗe idanunta ta yi sai kuma ta tashi zaune tana kallonta ta ce“mene ne?”

“yanzu zan sauka nace na gan ki, gasu Abba nan a ƙasa” jinjina kanta ta yi sai kuma ta ce“zazzaɓi nake ji Maimoon” hannunta ta kai wuyanta ta ji zafi sosai ta ce“sannu daman baki da lafiya?” lumshe idanu ta yi ta buɗe sannan ta ce“a’a yanzu kawai naji zazzaɓin” sannu kawai ta ce sannan ta mike ta ce“bari naje kar ace a na daɗe” daga haka ta fice daga ɗakin. Da gudu ta sakko ƙasa tana fadin “Abba! Abba! Abba!” tsaye ta same shi yana kallonta ya ce“lafiya dai Maimuna?” sama ta dinga nuna masa da hannunta kafin ta ce“Nana! Nana tana sama daman” da wani irin mamaki suka dinga kallonta, Abba ya yi gaba ya haura saman da sauri, ɗakin Hajiya ya buɗe yaga bata ciki, ya sake buɗe ɗayan, turus ya yi a wajen yana kallonta ganin yanda ta juya baya, a sanyaye kuma yace

“Nana!”

Da sauri ta juyo ta kalleshi, ya ƙarasa ciki yana kallonta ya ce“yaushe ki ka zo nan? Me yasa baki je gida ba?” muryarta a sanyaye ta ce“Abba banida lafiya, tun safe nake nan kuma na kasa tashi” ta ƙare maganar hawaye na zubowa kan fuskarta, Hannunsa ya kai wuyanta ya ji zafi sosai ya janye hannun dai dai sanda Hajiya Babba da Abdusammad suka shigo ya riƙe hannunta ya ce“sannu to, taso” miƙewa ta yi ta jingina da jikinsa tana lumshe idanu, Hajiya ce ta ƙaraso gabanta ta riƙeta tana faɗin “ke daman kina nan? Me ya sa baki sakko ba? Baki da lafiya?”

“wai ashe bata da lafiya ne, ta zo ta kwanta kuma bata tashi ba, bari muje a dubata” Hajiya Babba ta ce“koda naji, sannu kin ji takwara” gyaɗa mata kai kawai Nana tayi, Abdusammad dake tsaye jikin ƙofa ya harɗe hannayensa a ƙirji ya ce“kawai bari na tafi da ita Abba sai na dubata zuwa an jima na dawo da ita” Girgiza kai Abba ya yi ya ce“a’a Abdusammad, ka gaji dayawa tun ɗazu ka ke wahala kawai na kira likita a waje ya dubata” murmushi ya yi ya ce“babu komai Abba” daga haka ya ƙaraso wajen, hannunta ya riƙe suka fito daga ɗakin, Maimoon ta sauke ɓoyyayiyar ajiyar zuciya tana dafe ƙirji. Sai da suka fito Abba ya nufi apartment ɗinsa dan sanar da Amma sannan ya saki hannunta ya ce“muje ko” babu musu ta fara tafiya a hankali har suka ƙarasa gidansa, A parlon suka sami Zahra da Noor tana ganinsu ta miƙe tsaye tana faɗin “Alhamdulilah, a ina aka ganta? Nana ina ki ka je?” kafin ta yi magana ya riga ta ya ce“wai tana kwance ɗakin Hajiya ne tun safe bata da lafiya” girgiza kai Zahra ta yi ta ce“ayyah sorry kin yi, sannu Nana” gyada mata kai kawai ta yi, bai sake cewa komai ba ya ja hannunta suka bar wajen.

Ɗakinsa suka shiga, ya mayar da ƙofar ya rufe da key sannan ya jingina da jikin ƙofar yana kallon bayanta ya ce“keee!” a ɗan tsorace ta juyo saboda yanda taji ya kira sunan nata, ya dinga kallonta sai kuma ya ƙaraso wajen yana tafiya cike da izza, in a very calm voice ya ce“ina ki ka je?” da ɗan mamaki ta dinga kallonsa, ya yinda ƙirjinta ke wani irin bugu na tsananin tsoro da fargaba, cikin rawar murya ta ce “Bab..bba..babu inda naje, ina Apartment ɗin Hajiya tun safe kuma…”

Cak maganar ta tsaya saboda zazzafan marin daya sauke mata a fuska, ta runtse idanunta tana jin kamar idanunta sun makance, nan da nan fuskarta ta yi wani irin jaa, cikin zafin nama ya fizgota ta faɗo jikinsa, ya sanya hannunsa na dama ya riƙe gashin kanta da kyau cikin tsananin ɓacin rai da kakkausar murya ya ce“ina ki ka je nace!?”

Azaba da tashin hankali su ne suka hanata bashi amsa, ya hankaɗata ta tafi ta faɗi kan tiles, ta saƙi ƙara saboda azabar data mata yawa, belt ɗin da ke ajiye gefen drawer ya ɗauko ya shiga naɗeshi a hannunsa yana kallonta ya ce“sai kin faɗa min in da ki ka je tabbas!”

Ganin da gaske dukanta yake shirin yi ya sanya ta buɗe baki cikin shessheƙar kuka ta ce“dan Allah uncle ka yi hakuri, wallahi babu inda naje” ko rufe baki bata yi ba taji saukar belt a bayanta, ta dafa wajen tana wani ƙandarewa cikin tsananin azaba, ya durƙusa dai dai tsayinta ya riƙe kanta yana kallonta yana huci ya ce“ina ki ka je? And wane wanda ya sauke ki” kasa basu amsa ta yi sai jan numfashi take tana dafe ƙirji, ya saketa sannan ya yi kwafa, wurgi ya yi da belt ɗin sannan ya ce“bari naje na kira Abban sai ki fadi in da ki ka je a gabansa” daga haka ya juya zai bar ɗakin, cikin zafin nama ta tashi da gudu ta ƙarasa inda yake ta riƙe ƙafafunsa tana kuka ta ce“dan Allah uncle kada ka faɗa masa, wallahi dukana zai yi, dan Allah ka yi haƙuri” cak ya tsaya amma bai juyo ba, ta ɗora fuskarta jikin ƙafarsa ta dinga rera wani irin marayan kuka.

Juyowa ya yi ya kama hannunta har gaban gado sannan ya zaunar da ita ya ɗan durƙusa dai dai fuskarta ya ce“shikenan ba zan faɗa masa ba, faɗa min ina ki ka je? Me ya sa ki ka yi ƙarya? Yaushe ki ka koyi ƙarya Nana?” yanda ya yi tambayar ya sanya jikinta ya sake sanyi, ta sunkuyar da kanta bakinta na rawa ta ce“dan Allah ka yi haƙuri, wallahi gidan su ƙawata naje, kuma na san idan na faɗawa Amma ba zata bar ni ba shiyasa…”

Kasa ci gabawa ta yi ganin irin kallon da yake mata, ko bai faɗa ba ta san ya gane ƙarya take faɗa masa, dan haka ta cigaba da hawayenta. Numfasawa ya yi kafin ya tallafi fuskarta da hannunsa ya ce“ba zaki daina min ƙarya ba ko? Ni ki ke tunanin za ki yiwa ƙarya ban gane ba Nana? Kina cikin hankalinki kuwa?”

Girgiza kanta ta dinga yi sai kuma ta sanya hannunta na hagu ta goge hawayen sannan ta ce“ka yi haƙuri” sakinta ya yi ya koma gefenta ya zauna sannan ya ce“tell me ina ki ka je?”

Shiru ta yi tana tunanin abin da zata ce masa wanda zai yarda da ita, dan ko karen hauka ne ya cijeta ba zata taɓa faɗa masa gaskiya ba, dan haka ta shiga tunanin irin ƙaryar da zata masa. Gyaran muryar da ya yi ne ya dawo da ita daga tunanin da take, without looking at her ya ce“ina jin ki” wasa ta fara yi da fingers ɗinta cikin shessheƙar kuka ta ce“makarantar mu naje” kallonta kawai ya yi da neman ƙarin bayani, dan haka ta ci gaba da faɗin

“Daman ƙawata ce ta ce min an fara bada admission a Aun University, to shi ne nace zan je na tambaya yanda ake yi, kuma nasan idan na faɗawa Amma ba zata barni ba, cewa zasu yi ba zamu ci gaba da karatu ba, shiyasa..” ta ƙasa ƙarasa maganar saboda kukan daya tawo mata, kallonta kawai yake ba tare da ya ce komai ba, ganin ya yi shiru ya sanya ta ɗago ta ɗan kalleshi sai kuma ta sake sauke idanun ƙirjinta na bugawa da sauri.

“To me ya sa ki ka kai dare? Sannan wane wanda ya ajiye ki a bakin gate?”

Kamar daga sama haka taji tambayar tasa, ta ɗan yi shiru kafin ta ce“da naje ne aka ce sai na jira saboda basa nan, shi ne na dinga jira har yamma sannan aka ce min ba zasu zo ba ranar, to bayan na fito kuma babu kudi a hannuna sai nafara tawowa a ƙafa sai bayan magrib sannan na haɗu da wannan mutumin yaga ina kuka shi ne ya ce mene ne na faɗa masa shi ne ya ce bari ya kawo ni gida”

Ta ƙare maganar cikin sanyin murya tana mai fatan samun yardarsa. Jinjina kansa ya yi sannan ya ce“saboda haka yasa ki ka yanke shawarar ki yi ƙarya a gida? Bayan kin ɗagawa kowa hankali? Kin san me kuwa babu inda ban saka an duba ba amma ba’a same ki ba, amma kina tunanin zan yarda dan ance kina ɗakin Hajiya” ya ɗan yi murmushi sannan ya ci gaba da faɗin “kina tunanin har kin yi girman da zaki dinga yin ƙarya ko? Har kin san mene rayuwa ko?” girgiza hannunta tayi ta ce“a’a wallahi uncle, ka yi hakuri ba zan sake ba dan Allah” tashi ya yi yana furzar da numfashi kafin ya ce“duk ranar da ki ka sake fita ba’a sani ba sai ran ki ya ɓaci fiye da tunanin ki Nana, I’ll show you the other side of me, so take care” daga haka ya nufi hanyar waje da sauri, da idanu ta bishi har ya rufe ƙofar sannan ta sauke ajiyar zuciya tana dafe ƙirji, muryarta na rawa ta ce

“Allah astagfirullah, Allah ka yafe min”

Sai kuma ta kai hannunta kan fuskarta, wani irin raɗaɗi taji wanda ya sanya ta runtse ido a fili ta ce“wayyo” sannan ta tashi da sauri ta ƙarasa jikin madubi, kallon gefen fuskar ta ta dinga yi ganin yanda ya yi jajur dashi ya ɗan kumbura, ta tura baki sai kuma ta ce“kuma sai ya dakeni” ta ƙare maganar a shagwaɓe, buɗe dakin aka yi ya shigo ta juya da sauri ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta, taɓe baki ya yi sai kuma ya ce“zo ki tafi” kamar zata yi kuka ta ce“uncle kaga fuskata” ta yi maganar tana nuna masa gefen daya maretan, haɗe rai ya yi ya ce“to sai aka yi Ya ya?”

“zafi yake min” ta ce a shagwaɓe, kamar ba zai magana ba sai kuma ya yi alamar ta zo da hannunsa, ta ƙarasa a hankali ta sunkuyar da kanta, tallafo fuskarta ya yi da hannunsa ya dinga kallon wajen ganin yanda ya yi jajur, hannunsa ya kai ya matsa gurin, ai ko kamar jira take ta fashe da kuka tana yarfe a hannu, haɗe rai ya yi yana kallonta ya ce“Quiet” shiru ta yi tana hawaye, ya ja hannunta suka fita daga ɗakin. A parlon ya samu Zahra zaune tana jiransu, ta miƙe ganin sun ƙaraso ta ce“sannu Nana ya jikin?” a sanyaye ta ce“da sauƙi Aunty Zahra” daga haka ya nufi hanyar waje da sauri.

Har Apartment ɗin su ya rakata sai da ta kai balcony sannan ya ce“kin ji abin da nace miki ko?” gyaɗa masa kai ta yi a hankali, ya juya ya bar wajen sannan ita ma ta juya, tan ƙoƙarin knocking ƙofar parlon taji an ce

“Nana”

A hankali ta juyo tana kallonsa sai kuma ta ce“Yaya Sultan” Ƙarasowa wajen ya yi yana tafe a hankali hannunsa zube cikin aljihun trouser ɗin da ke jikinsa, ya tsaya a jikin balcony ɗin yana kallonta ya ce“daga ina ki ke?” kamar mara son magana ta ce“daga wajen uncle nake, shi ne ya rakoni yanzu” Sultan ya bi inda ta kalla ɗin dan har sannan ana gano Abdusammad ɗin, sai kuma ya mai da idanunsa kanta ya ce“yanzu kin zama yar gidan uncle ko?” ɗan murmushi ta yi ta ce“a’a fa yau a gidan Hajiya Babba na yini da daddare naje wajensa” jin jina kai ya yi sai kuma ya ce“nagane, to je ki gida dare ya yi” Toh kawai ta ce sannan ta murɗa handle ɗin ƙofar ta shige ciki. Sultan ya ɗan jima a wajen yana tunani kafin daga bisani ya juya ya ci gaba da tafiya, koda ta shiga parlon bata sami kowa ba dan haka ta nufi daƙinta kai tsaye, bata fi 2mins da shiga ba Amma ta buɗe ɗakin ta shigo tana kallonta a fusace ta ce“ wani sabon rashin hankalin ki ka fito dashi na fita baki sanar ba? Dan baki da lafiya shi ne yake nufin ki je ki yini a can? Ba zaki iya dawowa gida ba? Kin fi so ki ɗaga min hankali ki hanani sukunin rayuwa?”

Shiru Nana ta yi tana sauraren faɗan Amman dan daman ta san sai ta yi mata, ganin yanda ta yi tsaye bata ce komai a ya sake fusatata dan haka ta ce“wato ga mahaukaciya na magana ko? Shi yasa kina ji ki ka min banza!” girgiza kanta ta yi a sanyaye ta ce“dan Allah Amma ki yi haƙuri, ba zan sake ba”

“Ai daman kin iya bada haƙuri, tun da kina da baki, to ki ci gaba kar ki fasa ja min magana Nana! Ki ci gaba idan ma so ki ke jinina ya hau saboda ke ɗaya to ki yi, kar ki fasa!” ta juya ta fice daga ɗakin tana buga ƙofa, ita dai Nana da idanu kawai ta bita sai kuma ta ƙarasa gefen gadonta ta zauna tana sauke numfashi.

Around 9pm ta fito daga ɗakin dalilin wata irin matsananciyar yunwa da taji, dan kwara kwata yau bata ci abinci ba, ta ƙarasa parlon tana kallon Amma da ke zaune tana kallon wani Film da ake haskawa a Arewa24, zama ta yi gefenta ta jingina kanta da jikinta kamar zata yi kuka ta ce“Amma yunwa nake ji, yau ban ci abinci ba” zafin da taji a jikinta shi ne ya sanya ta ɗago tana kallonta, sai kuma ta kai hannunta wuyanta tana faɗin “zazzaɓi ki ke?” gyada mata kai kawai ta yi, Amma ta ce“kin sha magani?” a sanyaye ta ce“eh uncle ya bani” tashi kawai Amma ta yi ta nufi kitchen da sauri, ita kuma ta kwanta akan kujerar tana lumshe idanunta. After 5mins ta dawo hannunta riƙe da plate mai ɗauke da farar shinkafa da miya wadda taji naman kasuwa, ta ajiye akan table ɗin sai kuma ta ƙarasa wajen freezer ta dauko mata ruwan roba da lemo ta ajiye suma sannan ta kalleta ganin yanda ta rufe idanunta ta ce“tashi ki ci abincin” a hankali ta buɗe idanun nata sai kuma ta tashi zaune ta jingina da fuskar kujerar tana sauke numfashi. Amma ta zauna gefenta sannan ta miƙa mata plate ɗin abincin ta ce“ci” kamar zata yi kuka ta ce“Amma ki bani a baki ba zan iya ci ba” kallonta kawai Amma ta yi sai kuma ta ɗauki spoon ta ɗiba abincin ta kai bakinta, buɗe bakin ta yi Amma ta yi mata bismillah sannan ta fara bata, ta dinga lumshe idanunta saboda daɗin da shinkafar ta yi mata. Sai da ta cinye tas sannan ta ɗauki ruwan tasha, Amma ta kalleta ta ce“ko na da ɗa miki?” girgiza kanta ta yi ta ce“na ƙoshi, bacci nake ji” ta yi maganar kamar za ta yi kuka, jinjina kai Amma ta yi ta ce“to tashi ki ke ki kwanta” gyaɗa kanta kawai ta yi sannan ta tashi ta bar wajen, koda ta shiga ɗakin kan gado kawai ta faɗa ta yi kwanciyarta dan a gajiye take sosai dan haka yasa nan da nan bacci ya ɗauketa.

****
Washegari around 6:00 na yamma Zahra ta sakko ƙasan hannunta riƙe da wata babbar leda tana kallon Siyama ta ce”gashi ki kai mata, ki ce size ɗin idan bai mata ba sai ta bayar a rage” to kawai Siyama ta ce sannan ta karɓi ledar ta ce“na tafi”

“ki gaida gida, ki cewa Umma wai Noor ta ce zata zo ta mata kwana biyu kafin mu shige” murmushi Siyama ta yi ta ce“to shikenan ko da mun tafi tare ai” Girgiza kai Zahra ta yi ta ce“a’a dai ki fara sanar da ita” to ta ce sannan ta nufi hanyar fita daga parlon ita kuma Zahra ta zauna kan sofa tana jawo wayarta.

Tafiya ta dinga yi cikin estate ɗin tana kalle-kalle, ko ina gwanin ban sha’awa, in dai maganar kyau da tsari ne to M-Shuwa Estate na kan gaba, ta lumshe idanunta a fili ta ce“nan bada jimawa ba nima zan shigo cikin wannan duniyar, ya ilahi can’t wait” ta ƙare maganar tana wani irin murmushi. Tun daga nesa take kallonsa cike da farin ciki, murya can ƙasa ta ce“yauwa daman an ce zan gan ka” daga haka ta ci gaba da tafiyar ta tana kallon wani wajen daban, ganin sun kusa dab da dab ya sanya ta ɗan matsa gefe ta yanda zasu haɗu, sai da taga ɗan taƙin da ke tsakanin su bai fi ta mutum ɗaya ba sannan ta gurɗe hills ɗin ƙafafunta da gangan ai kuwa ta faɗi ƙasa tare da ledar kayan. Da sauri Safwan ya kalli wajen jin faduwar abu, ganin mace ce ya sanya ya ƙarasa da sauri yana kallonta cikin sanyin muryarsa ya ce“subhanallahi sannu” ɗagowa ta yi tana masa wani irin kallon ƙurilla kafin ta ce“yauwa thanks” daga haka ta shiga kwashe abayoyin da suka faɗo, tsugunawa ya yi ya tayata kwashewa ya zuba cikin ledar ba tare da ya kalleta ba ya ce“ki dinga tafiya a hankali” jinjina kanta ta yi fuskarta ɗauke da murmushi ta ce“tom in sha Allah nagode sosai” daga haka ta miƙe tana kaɗe jikinta, jinjina kansa ya yi sannan ya yi gaba abin sa. Ta dinga bin bayansa da kallo tana jin wani irin sanyi a ranta sai kuma ta yi murmushi a fili ta ce

“wow wannan shi ne haɗuwar” ta yi dariya mara sauti sannan ta zaro wayarta daga jaka, numbern Mom ɗinta ta yi dialing dan ba zata iya jira sai ta koma gida ba, ringing ɗaya ta ɗauka daga ɓangarenta ta ce“Siyama ba zaki dawo ba ne jiran ki fa nake masu kayan sun zo” murmushi ta yi ta ce“Mom Albishirinki?” Aunty Khadijah ta ce“goro mene ne?”

“Na haɗu dashi”

Da sauri ta tashi daga zaunen da take ta ce“haba da sauri haka? Daman malam ya ce zaku haɗu, yanzu ya ku ka yi?” Siyama ta lumshe idanunta kafin ta ce“ya tafi ma, yanzu nima zan dawo, sai mu san me zamu yi nan gaba” Aunty Khadijah ta jin jina kanta ta ce“haka ne kuma ki yi sauri ki dawo ina jiran ki, bari na kira Baturiya na sanar mata, daman na san aikin wannan malamin ba dai kyau ba” toh kawai Siyama ta ce sannan ta kashe wayar ta numfasa sannan ta ci gaba da tafiya..

Bayan kwana biyu wajejen ƙarfe 9:00 na safe Zahra ta fito daga ɗakinta hannunta riƙe da waya, sai da ta rufe ƙofar sannan ta kai wayar kunne cikin sanyin murya ta ce“dan girman Allah Aunty ki rufa min asiri, so ki ke aurena ya mutu ne?” daga ɗaya ɓangaren Aunty Khadijah da ke zaune kusa da wata ƙawarta ta ce“kamarya aurenki ya mutu? Saboda kin ce wa mijin ki ga yarinya a bawa ƙaninsa sai aurenki ya mutu?” Zahra ta girgiza kanta kamar zata yi kuka ta ce“baki gane ba, wai ya za’a yi na cewa Doctor ga mata ya bawa Safwan? Bayan nasan basa haka, kuma ma bama wannan ba Safwan fa an riga da an yi maganar aurensa, yanzu ma maganar da nake miki sauran sati uku bikin wallahi tallahi, to kin ga idan na bijiro da wannan maganar ai kamar ban yi daidai ba” taɓe baki Aunty Khadijah ta yi a ɗan fusace ta ce“kin ga shikenan bana buƙatar taimakonki zan yi da kaina, kuma idan ma baƙin ciki ki ke kada Siyama ta shigo ta ci irin arzikin da ki ke ci to wallahi sai dai ki mutu”

Zahra ta buɗe bakinta tana jin jin karfin hali irin na Aunty Khadijahn, jin bata sake magana ba yasa ta ɗan kwantar da murya ta ce“ni fa Aunty ba haka nake nufi ba, kin ga…”

Tsaki ta yi sai kuma ta kashe wayarta, Zahra ta mai da wayar hannunta ta dinga kallon screen ɗin da mamaki, can kuma ta numfasa sannan ta koma ciki.

Can ɓangaren Aunty Khadijah ta kalli ƙawar tata mai suna Kaddu ta ce“kin ji baƙin halin ko? Kin dai ji abin da ta ce da kunnenki, ai wallahi ba zata taɓa yarda ta haɗa su ba! Wannan mai baƙin halin”

Kaddu take zaune ta hakimce akan kujera ta ce“na ji kuwa, amma ki kwantar da hankalin ki, wallahi sai ya auri Siyama, haba sai ka ce ba yar mu ba ce”

Aunty Khadijah ta dinga kallonta can kuma ta ce“to ai kin ga yaron ne kamar akwai tsari a jikinsa, ki ga fa duk irin aikin wannan malamin amma ya kasa tasiri akan sa” tsaki Kaddu ta yi tana watsa hannu ta ce“dallah bar maganar wannan malamin, wake ta irin waɗannan? Ai wannan daman ba aikin malami ba ne, ni na san inda zamu je wallahi ko a gobe ki ke son ya auri Siyama sai ya aureta, me kuma aka yi aka yi shi?”

Gyara zama Aunty Khadijah ta yi tana murmushi ta ce“ke ƙawata taɓani da alkhairi, wai da gaske ki ke dan Allah? Ina ne?” wani shu’umin murmushi ta yi kafin ta ce“ke dai ki bari zamu je ki gani da idon ki” Aunty Khadijah ta sauke ajiyar zuciya sai kuma ta ce“har naji sanyi a raina wallahi, kai wannan abu” Kaddu ta yi murmushi sai kuma suka ci gaba da wata hirar.

****
Ranar Saturday misalin ƙarfe 4:20 na yamma ta fito daga ɗakin tana gyara zaman jakar hannunta a kafaɗarta, Amma da ke ajiye drinks a freezer ta ɗan kalleta sai kuma ta ce“kin shirya?” gyaɗa mata kai ta yi bakinta ɗauke da murmushi ta ce“eh Amma, yanzu zan tafi” sai da ta rufe freezern sannan ta mai da Idanunta kanta sosai tana kallonta, wata doguwar rigar material up white ce a jikinta mai zanen flowers manya-manya, ɗinkin boubou wadda bata kama jikinta ba, sai ta yi rolling jersey veil baƙi, babu kwalliya a fuskarta amma ta yi tas da ita sai sheƙi take. Amma ta ce“driver ne zai kai ki?” jinjina kanta ta yi kafin ta ce“eh ai Maimoon ma ta ce zata je, wai perfume ɗinta ya ƙare” Toh kawai Amma ta ce sai kuma ta nufi hanyar daƙinta, da idanu Nana ta bita har ta shiga sannan ta ɗauke kanta, bayan minti biyu ta fito hannunta riƙe da Atm card ta tana miƙa mata, amsa Nana ta yi sai kuma ta ce“yauwa Ammata”

Average Rating: ☆☆☆☆☆ 0.0 (0 ratings)

Leave a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *